Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan......” kasa ƙarasa maganar nai saboda kusancin da muka samu, a dalilin ranƙwafowar da yay har munajin saukar numfashin junanmu, ya ɗaura hannun hanggunsa saman table ɗin, na damar kuwa saman nawa dake kan mouse. Da sauri na rumtse idanuna, tare dayin azamar janye hannuna dake ƙasan nasa, saboda wani mugun harbawa da zuciyata tai. Baice komaiba, shikam ko a jikinsa, saima ƙoƙarin maida video slowly da yay. Nayi matuƙar takura da tsorata da wannan kusancin namu da yay matuƙar yawa, har takai jikina ya fara rawa, idanuna suka ciko da ƙwalla, sam bana fahimtar bayanin da yakemin ma, dan sama-sama nake jin sautin muryarsa.
     Jawaad da duk abinda yake akan sani yayisa ya juyo yana kallonta, ta rumtse idanu zufa dukta tsatstsafo mata a goshi tamkar babu ac a office ɗin. “Hummm” ya faɗa acan ƙasan maƙoshi ya janye jikinsa. A mamakinsa sai yaji ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, hawaye sun silalo saman kumatunta, saurin ɗauke kansa yay tamkar bai ganiba.
         Har bigewa nake da shi wajen rawar jikin miƙewa daga kujerar jin ya matsa, na goge hawayen dake bin kumatuna batare da na bari ya ganiba, gefen tebirin na koma na tsaya kaina a ƙasa nace, “Sir, bara kawai naje can dashi saina ƙarasa tattara bayanan”. Jawaad da har yanzu yake binta da kallo yaɗan lumshe idanu ya buɗe yana ƙoƙarin danne dariyar dake son kufce masa, murya a daƙile yace, “Barshi zan ƙarasa, ɗauka waɗanan files ɗin ki kaima Hafiz, zuwa anjima ki dawo zamu fita”. Bawani fahimtarsa nakeba, kai kawai na ɗaga masa na ɗiba files ɗin na fice cikin sassarfa. A raina banda takaici babu abinda nakeji, miyasa halin mazan wannan zamanin kusan duk ɗayane? Burinsu kawai su taɓa macen da ba muharramarsu ba a matsayin wayewa, ashe shima mutumin nan haka yake ban saniba?, “Aikam na daina sakar masa fuska wlhy” na faɗa a fili cike da takaici.

★★★★

       Ƙarfe biyu muka fita cin abinci ni da Ummie, sai da muka gama nai ƙoƙarin biya sai nagama kuɗin dake jikkar tawa bazasu isaba, kusan koda yaushe Ummie ke biya mana inhar bada Yah Qaseem mukazo ba, sai naga da kunya hakan tacigaba da faruwa ai, ATM ɗina na shiga lalube dan na basu su cire, amma sai shima ɗin dai ban gansaba, gabanane ya shiga faɗuwa, dan bama shi kaɗaiba duk cards ɗina basa ciki kenan tunda a tare nake ajiyesu waje guda, kuma inada tabbacin itace jikkar danasan na fita da ita daga gida last. “Wai mikiketa lalube hakane kamar wata makauniya?” Ummie dake shan ruwa ta faɗa bayan ta ajiye kofin. Guntun tsaki naja ina mai bata amsa da, “Ai namafi makauniya yau Ummie, wlhy banga duk Cards ɗinaba, kuma inada tabbacin anan ciki suke”. Tasowa tai tana tayani, sai dai kumafa da gaske babu ɗin, hankalina yayi matuƙar tashi, “Ummie na shiga uku, a ina na jefar nikam?”. “Bily bazan saniba, amma nasan baki da mantuwa, yaushene rabonki dasu?”. “Ummie A ranar lahadi fa da hannuna na sakasu cikin nan dazan fita”. Tace, “Ai da sauƙima, ki tuna ranar ina da ina kikaje tunda kin tabbatar a ciki suke?”. Zama nai idona cike da kwalla ina tunano dukkan abinda ya wakana a wannan yinin, da sauri na kalli Ummie, “Ummie idanma har yardawa nai to

bazai wuce wajaje biyu ba wlhy”. Ummie tace, “Ina da ina ne?”. “Saloon da wani garden, amma bara na bincika a saloon ɗin dan inada Number ma'aikaciyarsu ɗaya”.
       Ummie ta biya kuɗin muka fito a wajen, sai da muka koma office sannan nai kiran Number danai saving da Ladies mirror, bugu biyu kuwa aka ɗaga, bayan mun gaisa nace, “Dan ALLAH kiyi haƙuri, na kiraki maybe ba'a lokacin daya daceba”. Daga can tai dariya da faɗin, “lah babu komai”. Nace, “Okey ngd, ranar danazo wajen nan naku ina tunanin na yarda wallet ɗina, sam hankalina bai kaiba sai yanzu, ina fatan anan na yardar ɗin?”. tai ɗan jimm na wasu sakanni kafin tace, “Eh tabbas anan kika yarda, amma bata wajenmu, tana masarauta wajen su aunty Amaturrahman, dama sunbar saƙo akan idan kinzo nema a baki card ɗinsu, yanzu yaya za'ai kenan?”. Wani sanyi naji ya ratsani, na sauke numfashi da cewa, “Babu damuwa, idan na tashi aiki zan biyo na amsa, nagode sosai”. ta amsa da “Babu damuwa, sai kinzo”. Bayan mun kashe wayarne na faɗama Ummie duk yanda mukai, daga ni har ita mamaki muketayi na cewar wallet ɗin na masarauta.
          Ban samu kiran boss ba kamar yanda yace zamu fita har lokacin tashi yayi, zuwa nai na sanarma yah Qaseem ya wuce gida ni zamuje nida Ummie wajen wanke kai, yanzunma da damuwa na iskesa, dan haka bai wani jamin zanceba yace mu haɗu a gida. Nidai al'amarin nasa sake ɗauremin kai yay yanzunma, har muka isa Ladies mirror banbar mamakin wannan canjin nasaba. Sosai Ummie ta rikice da haɗuwar wajen, harda ma kanta alƙawarin zuwa wannan weekend ɗin su mata aiki, bamusha wata wahalaba muka samu wadda na kira ɗin, ta bani card ɗin da suka bari. bamu daɗeba muka fito dan magriba ta gabato.
         Ummie ta ajiyeni a gida ta wuce, koda na shiga saina iske an sallamo auntu Shahudah, falon cike da dangin Momy, da sukazo dubata, nidai na gaishesu itama nai mata yaya jiki na wuce, saboda a rayuwata na tsani kallon wilaƙanci, sukuma naga alamar indai ba nasuba to kowa banzane. Wanka na farayi harda wankan tsarki saboda baƙona ya gudu,  na fito na gabatar da sallar magriba nai azkar, ina zaune a wajen har aka kira isha'i, har lokacin inajiyo hayaniyar ƴan gidansu Momy, dukda yunwar da nakeji saina zaɓi haƙura na kwanta a haka, ɗan kayan maƙulashen da yah Qaseem ke yawan siyamin nakan ajiye a ɗaki su nai zamanci, gefe guda kuma ina ƙoƙarin kiran Number jikin card ɗin da aka bani, saida ta kusa tsinkewa aka ɗaga, munyi gaisuwa da wadda ta ɗagaɗin a mutunce dukda bansan wacece ba, kafin na mata bayanin kaina. Nayi mamakin yanda tai saurin ganewa, kai tsaye tace na tura mata address ɗin inda nake kawai, zasuzo su kawomin har gida. Sosai na ƙara mamaki da jinjina ƙyaƙyƙyawar tarbiyyarsu gaskiya, sam basuda girman kai tamkar ba waɗanda suka fito daga babban gidaba. Godiya nai mata mukai sallama, ban zauna ɓata lokaciba na tura mata number dan inada buƙatar cards ɗina su dawo hannuna da gaggawa.
            Jin gidan yayi shiru yasa na miƙe, dan fitar motoci da naji ya bani tabbacin duk sun wuce, ƙaramin hijjab na saka saman wando da rigar kayan barcina kalar ruwan hoda na fito, wata irin muguwar yunwa nakeji wlhy, rabona da abinci tun wanda mukaci da Ummie da rana. Babu kowa a falon duk sun tafi, na wuce kicin hankalina kwance, plates kawai nagani zube wanda sukaci abinci, sai dai babu komai a kulolin duk an cinye, cike da haushi na fara ƙoƙarin ɗora noodles dan bazan iya haƙurin kwanciya banci komai ba, dan danan na kammala dafawa na fito, mamaki ya kamani jin ƙamshin turaren da banyi zatoba, zuciyata sai harbawa take da sauri-sauri, waige-waige na shigayi a falon, saiko idona ya sauka akan wanda zuciyar tawa ke rayamin,  tsaye yake dafe da ƙarfen benen dake falon waya a kan kunnensa, kamar koda yaushe ƙananun kayane a jikinsa, ido cikin ido muka kalli juna, nai azamar janye nawa ina damƙe plate ɗin indomie ɗina daketa tururi, inaji a jikina har yanzu kallona yake, hakan saiya haifarmin da tafiya a hankali kamar wata hawainiya harna shige lungun ɗakinmu ni da aunty Aamilah.
       Jawaad daya kasa ɗauke idanunsa a kanta har saida ta shige sannan ya sauke ajiyar zu

ciya yana lumshe ido da cije lip ɗinsa na ƙasa, sannan ya cigaba da wayarsa, bai wani jimaba sukai sallama ya maida wayar aljihu idanunsa akan lungun da bily ta shiga, cike da kasalar data saukar masa yanzun ya haye saman ya koma wajensu Dad da Alhaji baba da Uncle Nasir da sukazo tare suke tattaunawa.

        Ban kawo komai a rainaba dangane da ganin boss gidanmu, tunda ai dama yayma Dad alƙawarin zuwa, sannan kuma ga aunty Shahudah ta dawo gida itama, abincina naci hankali kwance nai brush na kwanta domin na hutama raina.

       
ALLAH YAY DARE.

              Washe gari safiyar alhamis, koda na tashi sai naci karo da abubuwa uku na farin ciki sun samemu, na farko samun sauƙin aunty Shahudah da har aka sallamo daga asibiti a daren jiya, na biyu maganar aurenta da Boss bayan ansha gumurzu ya amince da ƙyar saboda saka baki da kakansa yay a maganar, na uku tsaida maganar aurena da Yah Qaseem bayan Dad yaje wajen dangin mahaifina ya samesu ashe a jiya da rana, an tsaida aurenmu rana ɗaya dasu aunty Shahudah bayan salla ƙarama da sati biyu. Koba komai na samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, dan nikam abubuwan dake faruwa na wannan lokacin suna matuƙar tsoratar dani da sakani firgici.
     Ban ƙara tabbatar da ina son Yah Qaseem ba sai da aka tsaida ranar auren nan namu, shi kansa wani sake lallaɓani yake da ji dani a yau, dukkan abinda zai saka a gidansa kuma sanda muke tafiya wajen aiki ya nema shawarata, hakama kayan lefe saida yace na faɗi duk abinda nake buƙata, nidai kunyace ta kamani nace kawai na bashi zaɓi.
       Sai dai abu mafi bani mamaki sune jama'ar gidanmu, musamman ma Momy, koda wasa ban taɓa tunanin zata goyi bayan aurena da Yah Qaseem ba, amma sai gashi koda a fuska bata nuna komaiba, saima shirye-shiryen gagarumin biki take na nunama sa'a akan babban ɗanta namiji da zata fara aurarwa. Yah Salman ne kawai da aunty Aamilah sun shafema idanunsu toka suna ƙara faɗaɗa hantarata da muguwar tsana akan ban cancanci zama matar ɗan uwansuba, ƙiri-ƙiri suke nuna hakan babu ko kara a wannan safiya, su Dad dai basu tsawatar musu ba, sannan basu goya musu bayansu ba, Yah Qaseem ne daifa da yay kansu da masifa har saida na roƙesa yayi haƙuri kafin yay shiru muka fito.
    Tom nidai lamarinsu bai ɓatan rai, Alhmdllh tunda wanda zan zauna dashi yana sona, sannan iyayensama suna sona, dansu ƙannensa sunce basayi miye a ciki. A dangima dai akwai ƴan adawa, dan harda inna zainabu faɗa taitama Dad akan haɗani aure da ɗansa da yay kamar yanda Aunty Aamilah take faɗamin cikin gori da tsana, wai acewar inna Zainabu duk ƴaƴan manyan mutane masu kuɗi abokan Dad Qaseem ya rasa wadda zaiso saini? Haka taita jaraba tamkar itace ta haifi Dad ko yah Qaseem ɗin.
       
     Duk wanda ya kalleni a office yau yasan banda wata damuwa tattare dani, dan waɗandama suke faɗin basa ganin dariyata yau sun gani harma da haƙorana, sai dai abinda ya ɗaure kaina da mamaki rai a ɓace naga Boss yau, dan koda nakai masa saƙo office baiko amsa gaisuwataba bayan sallama, sannan harna fito baice dani uffanba, idanunsa jajur, hakama jijiyar kansa duk sunyi ruɗu-ruɗu, duk sai naji babu daɗi, dan koba komai nima ranar danai ciwon mara ya bani kulawa da nuna damuwarsa a kaina, da alama kuma yau shima baida lafiyarne. Kasa zama nai waje guda nakoma office ɗinsa wai naji mike damunsa?, ‘kuji ƙarfin halifa irin nawa’ to aiko dai ban jiyota da daɗiba, dan fatattakoni yay tamakr zai gaggallamin marukama, ALLAH dai ya taimakeni na gudo. A ƙofar office ɗin mukaci karo da gimba kamar a rikice yake, nidai na bashi hanya ya shige ko gaisuwa bamuyiba, sauka nai ƙasa abina ina ƙunƙunai, ban sakebi takansaba har aka tashi aiki kuwa, sai a wajen Ummie nakejin gulmar wai taga boss ya fita ɗazun ransa a ɓace kamar zai tashi sama, ban kulataba ita da zancen nata, dan haushinsa nakeji akan abinda yaymin ɗazun..

        Mamaki yay matuƙar kamani da muka isa gida na iske aunty Shahudahr data kwana biyu a asibiti rai a hannun ALLAH zaune suna hira mai nuni da tsare-tsaren biki, a raina nace, ‘Dama ciwon so ke damunta ashe, ta samu yanzu kunga ta miƙe harda tsara

biki kamar wani auren farko mtsoww’ na ƙare zancen cike da takaicin da bansan dalilinsaba nima. koda nai sallama basu amsaminba sai Momy kaɗai, sannunma ita kaɗai taimin hakama amsa gaisuwata, jikina duk sai yay sanyi, na wucesu ƙwalla na cikamin idanu, nasan dolene saina sake ɗaura ɗammarar haƙuri kam, dan matsalolin dama sukafi haka zasu biyo baya akan aurena da Yah Qaseem, har nai wanka na fito hawaye basu daina gudu a idanunaba, bayan sallar isha'i saima naji gidan tsitt, koda na leƙo iskewa nai duk fita sukai, daga ni sai Yah Qaseem dana iske a d/table yanacin abinci aka bari gidan da alama, zama nai mukaci tare muna ƴar hira, bayan mun kammala ya fita sashensu ni kuma na koma ɗaki nai shirin kwanciya dan barci nakeji kuma. Ina kwance har tara na dare barcin bai ɗaukeniba bankumaji motsin dawowar su Momy ba, sai naji wani tsoro na shigata a hankali, addu'a nai na kwanta ina fatan barci ya ɗaukeni mai nauyi kozan samu nutsuwa, UBANGIJI kuwa sai ya amsa roƙona barcin yay gaba dani babu zato.

          ‘Innalillahi...’ na ambata cikin farkin barci lokacin da abinda ya faru kwanaki huɗun da suka shuɗe dana manta shi gaba ɗaya a raina yake neman maimaita kansa a wannan daren tamkar ranarma a yau, a matuƙar gigice na farka jikina na mazarin rawa haɗe da bugawar zuciya tamkar zata faso ƙirjina ta fito, na fashe da kuka ina mutsu-mutsun fita daga jikinsa, sai dai hakan ta gagara a yau, dan yaymin riƙo bana wasaba, ga bakina an ɗaureshi da yanda bazan iya maganaba . Wata irin siririyar dariya ya saki a cikin kunnena, yauma dai muryar tamkar irin ta wancan ce, “Hhhh sannu Jaruma, yauma na dawo gareki, ranar kinyi nasarar korata ko, to kisa a ranki yau duk gudunki bazaki iya tsereminba, harke wacece da kika isa ruguzani? Nazo miki da lallami ranar amma kikaƙi saurarata, hhhhhh ke baki isa zama matar aureba yarinya saina karɓi abinda yake nawa, gashi kina a cikin yanayin danafi buƙata ma kina haila, kina bani shikenan, dan samunsa bada igiyar aure a kankiba shine yafi komai muhimmanci, bakuma zan sake bibiyarkiba dana samu cikar burina, hhhh bilkisu kece kammaluwar nasarata, kece ƙarashen nasarorina, da dukkan wahalhaluna na tsawon shekaru zan cika nasarata! Hhhh taya kike tunanin zan bari ki kufcemin, ɗaura miki igiyoyin aure tamkar ni aka ɗaure da igiyoyinne, taya zan bari hakan ta kasance ban amshi abinda yake cikamakin nasarorina ba?, abinda naketa bibiya tsahon shekaru kenan, karki yaudari kanki da tunanin ranar kin tsira yauma zaki tsiran, namiki shiri sosai a yau bilkisu, na shiryama wannan ranar, dan tana cikin damammakin da idan na rasasu babbar asarace a gareni, bana asara yarinya sai dai nasara! hhhhhhh!........”
          Duk wannan maganganun da yakemin a cikin kunne na zama tamkar wata gawace a kwance, gangar jikina ne kawai a duniya amma numfashina da tunanina basa tare da duniyar, ba'a maganar zubar hawaye ma dan waɗanan dama ke sakasu fitowa, wata irin hasala zuciyata keyi da kumburar ɓacinrai irin wanda ban taɓa tunanin inada shiba, haka kawai yau nakejin zuciyata ta bushe dukda inajin tsoron ya samu nasarar da yake fatan kuwa, sai dai ban fasa gayama UBANGIJINA ba, addu'a nake kawai ina ƙiyasta tunanin shaidar dazan iya barma koma wanene wannan shaiɗanin, bazanyi sake irin na wancan darenba a yau insha ALLAHU, koda ace zaici galaba a kaina nima saina ribantu dashi da izinin UBANGIJINA.
       Lokacin da naji ya sassauta min riƙon da yaymin yana shirin hawa kaina saina samu damar bada dukkan ƙarfina da yazomin daga mahaliccina wajen ƙoƙarin son tureshi, sam hakan bamai sauƙine a gareni, dan da alama ba ƙaramin mutum bane, danni sam kusani bana kawoshi a jerin aljanu, inada tabbacin mutum ne tamkar ni da rigar shaiɗanu. Wata sassanyar dariya maicin rai da nuna tsantsar mugunta da bushewar zuciya ya saki, tare da komawa gefena ya kwanta da faɗin, “Bara na baki damarki, kafin nai yaga-yaga dake yanda bazaki taɓa ganuwaba a safiyar gobe, na kula tausayin banza nake miki, tsaurin idonki yayi matuƙar yawa yarinyarnan”. Ya ƙare maganar da cire abinda ya ɗauremin bakina. Kukan zuci nake da babu hawaye ina kai masa du

ka ta ko ina da masa gargaɗi cikin zafin rai, “Karka cutar dani dan ALLAH, minai maka kake ƙoƙarin ɓatamin rayuwa?, kaji tausayin maraicina dan ALLAH, kobaka tsoron mahaliccinka ne? ina buƙatar zuwa da martabata gidan mijina tamkar kowacce mace mai mutunci, idan ka ketamin haddi wlhy ALLAH bazai barkaba, zan ƙare rayuwata ne wajen jifanka da munanan addu'oin da koka samu cikar burin naka saiya zame maka musiba, mugu azzalumi, ALLAH ya gagauta tona asirinka dama kosu waye kuke aikatama ƴaƴan mutane ɓarna, ALLAH ya ruguzaku sheɗanu, insha ALLAHU wutar jahannamace makomarku inhar baku tuba kun koma ga ALLAH ba tare da neman yafiyar bayin da kuke cutarwa, la'anannu masu ado da rigar musulunci suna cin dunduniyar bayin ALLAH, insha ALLAH bazaka cika burin nan nakaba koda kuwa kasamu nasara a kaina.........
       Shiiiiii!!!! Ya faɗa yana dannemin baki tare da birkiceni ƙasa ya fallamin wani gigitaccen marin da komaina yay tsaye cak na wucin gadi kafin na ƙwalla ƙara, yasa hannu ya dannemin baki tare da kaina da azabar ƙarfi, kiciniya na fara dan harda hancina ya haɗa gaba ɗaya, tako ina yakushinsa nake dukda babu farce a hannuna sosai, hannunane ya sauka akan wuyansa, jin wani abu a ɗaure kamar sarƙan bit na samu damar fincikarsa da masifar ƙarfi saboda fita a hayyacina da nayi lokacin da numfashina ke gab da barin jikina................✍

Ƴan WhatsApp kuma ga naku saƙon, gaisuwa da fatan alkairi gareku baki ɗaya. Saura kuma yau naji wani yacema Yah Qaseem ko Dad kwarto🙄🚴🏼🚴🏼😍😍😍😘😘😘😍😍.

       

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

        
[12/4/2020, 6:12 PM] HASNA✍🏻: Billyn Abdul:
Page 22

...............“Bazai yuwuba, Ka gaggauta fita!! Ka gaggauta fita!!!” na jiyo wata murya mai amo sama-sama tana amsa kuwwa a cikin ɗakin lokacin da numfashin ke gab da barin gangar jikina. Daga haka ban sake fahimtar komaiba dake a cikin duniya sai wayar gari nai na ganni kwance a ɗakin Momy.
          A hankali na shiga buɗe idanuna da sukaimin nauyi, na shiga bin ɗakin da kallo daki-daki, dan bamma fahimci inda nakeba da farko saboda zan iya irga shigowata ɗakin Momy a tsawon zama gidan, da ƙyar na tashi zaune ina sake mamakin abinda ya kawo ni nan ɗin, hakan yayi dai-dai da shigowar Momy ɗakin.
       “Yauwa kin tashi Bilkisu?”. Kaina na ɗaga mata a hankali, saboda jikina yaymin wani masifar nauyo, na buɗe baki da ƙyar nace, “Momy miya faru na ganni anan?”. Hankalinta nakan ciro abu a cikin drawer ta bani amsa, “Za'a gaya miki daga baya, tashi kije ɗakinki kiyi wanka”. Da “to” kawai na amsa mata na sauka jikina duk yana wani masifar ciwo, ga tunani fal raina, wani abin mamakinma na sake tararwa a folon ƙasa, dan kuwa cike yake da dangin Momy, na gaisar da waɗanda zasu iya jina na wuce ɗaki kaina na kuma ɗaurewa. Akan gadona dake mugun yamutse na fara sauke ido, ‘Kowaye yay masa haka kuma?’ na ayyana a cikin raina, dukda banajin daɗin jikin sai nai tunani bara na fara share ɗakin, gadon na shiga kakkaɓewa, ƙarar faɗuwar abu naji kamar ƙwandala a ƙasa lokacin dana ɗaga zanin gadon, dube-dube na fara, sai dai banga komaiba, sharewa nai kawai na gyarashi tsaf, nakoma shara.  A wajen shararne na sharo abinda ya faɗi ɗazun ashe wajen gado ya shige, Wuri ne kalar ja, sai dai wannan yafi wurin dana sani girma, haka kawai na samu kaina daƙin maidashi a sharar, saima na jefashi cikin jikkar islamiyya ta dake kusa dani, na cigaba da sharata. Da ƙyar na kammala aikin na lallaɓa bayi nai wanka, ganin baƙona ya tafi saina haɗa da wankan tsarki. Ina shiri ina mamakin barcin danai daga daren jiya zuwa safiyar yau ace bamma farkaba kamar yanda na saba a lokacin sallar asubahi dukda bana salla, yanzu hakafa sha biyu ma, ni saima yanzu maganar zuwa aiki tazomin a rai, gaba ɗaya wani iri nakejin kaina tamkar birkitacciya, wayata na shiga dubawa, sai dai kuma ban gantaba, ƙarasa shirin nai da tunanin naje ɗakin Momy na duba ko tana can idan na gama. Sallamar Momyn ce ta kacemin tunani na juya ina kallonta. taci kwalliya cikin rantsatstsen lase ɗan ubansu sai walƙiya yake, ga gwalagwalai ta zuba a wuya da hannu, taimin murmushi irin wanda tsahon zamana da ita ban taɓa cin karo da shiba sai yau, “Bilkisu irin wannan kallo haka” kunya naɗanji, dan haka na murmusa ina mai duƙar da kaina, nace, “Kinyi ƙyaune Momy”. “To nagode sosai” tafaɗa tana zama a bakin gadona da ajiye ledan data shigo dashi a hannu. takai dubanta gareni, “Kinga cire waɗannan kayan waɗanan zaki saka, nasan akwai tambayoyi fal ranki, karki damu zamu baki dukkan amsoshinsu zuwa dare idan baƙi sun tafi, fatanmu dai kizama maiyin biyayya a garemu kamar yanda kika saba, batun zuwa aiki kuma yau bazaki jeba”. Shiru nai kawai ina kallonta, sai kuma nace mata, “To momy, wayata fa?”. Miƙamin tayi tana faɗin “kin ganta nan, dama anata kirankima kuwa tun ɗazun”. Amsa nayi, itakuma ta miƙe ta fita. Da kallo na bita kaina na sake ɗaurewa da abubuwan da ban saba ganinsuba sai a mafarki, ganin ta ɓacema ganina saina sauke nannauyar ajiyar zuciya, wayar na duba, miss calls kam da yawa harma bansan dawa zan faraba, Yah Qaseem, Ummie, Amina, harma da Numbers ɗin da bansan na wanene ba, kafin nayi wani yunƙuri kira ya shigo, sunan Masarauta danai saving ne ya fito ɓaro-ɓaro a jiki, ɗagawa nai muka gaisa a mutunce kamar ranar, daga ƙarshe take sanarmin bayan an sakko massalaci zasuzo kawomin cards ɗina, murmushi nayi ina mata godiya, kafin mu yanke wayar. tunanin yaya zanyi na shigayi, dan yakamata ace koba komai nai musu tarba ta girmamawa ko badan gidan da suka fitoba, to amma yanda gidannan ke cike ta ina zanma fara nikam? Wlhy gaba ɗaya yau kaina ya ɗauki zafi, sam tunanina baya tafiya dai-dai dana sauran mutane. Kasa yin komai daya dace nayi, nai zaune a inda Momy ta barni, niba

n canja kayan datace ba, bankuma miƙe na nemawa baƙin abinda zasuciba idan sunzo balle kuma cikina dake Masifaffen  ƙugin yunwa kamar zanci babu. Ina a wajen har ƙarfe ɗaya ta buga, tashi nai jiki a sanyaye na ɗauro alwala, gabana sai wata iriyar muguwar faɗuwa yake wadda ban taɓa jiba, idan girata ta haggu ta harba sai ta dama ma ta harba, sai kuma inji wata faɗuwar gaba ta biyo bayansu. Haka nai sallar azuhur batare dana fahimci abinda nama karanta a sallarba, dan wasu irin mugayen halittu na rinƙa gani suna zuwa gabana, haka dai na dake raina na cigaba da sallar inata faman kwarar da zufa tamkar wadda take a cikin ruwan zafi, a sujidar ƙarshema sai naji wata iriyar muguwar dariya a ɗakin tamkar za'a fasashi, sai kuma aka fashe da kuka, zuwa can aka kuma saka dariyar datafi ta farko. Na kasa ɗagowa daga sujidar ma gaba ɗaya tsahon lokaci, saida naji an taɓani ne a baya da magana kamar muryar Ummie sannan ALLAH ya bani ikon ɗagowa. Shiru naji ɗakin ya ɗauka sannan bana ganin komai a gabana harna kammala na shafa addu'a. Na sauke idanuna akan Ummie dake zaune da a bakin gadona tana latsa waya, sai dai na kasa cemata komai saboda wani irin yanayi da nakejin kaina mai masifar tashin hankali, jina nake tamkar ana kunnamin garwashin wuta a jiki........
       “Bily! Bilyy!!” na tsinkayi muryar Ummie na faɗa tana girgizani. Kallonta nai na amsa da ƙyar, dan bansanma tazo kainaba, bana gane komai a yanzu bana kuma fahimtar komai hatta da kaina neman suɓucemin ya keyi. Tace, “Na shiga uku,

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment