Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta miƙe dan tayi sagafene tana kallonsa da fassara maganganunsa sala-sala.
Sam Jay baiga Rose ba, Bily kanta data ganta halin data shiga yasa tama manta da ganin nata, ruwa ya ɗakko ya bata, babu musu ta amsa, yanda tasha ruwan sosai har mamaki ta bashi, ta miƙa masa kofin tana godiya, baice mata komaiba sai nuni da yay mata data tashi takoma kan kujera.
Nima ina buƙatar hutawar, dan haka na tashi na koma saman kujerar na zauna tare da lumshe idanuna.
Sosai nakeji a jikina kallona ake, ina buɗe idanu muka haɗa ido dashi, ɗauke kansa yay tamkar baniɗin yake kallonba, nima na janye nawa a raina ina jinjina yanda ya ƙware a iya kallon mutum.
Babu wanda ya sake shigowa office ɗin har aka kira sallar la'asar, shine ya fara shiga ya ɗaura alwala sannan yace naje nayi nima, lokacin dana fito tsaye na gansa, bance komaiba na nufi hanyar fita yana biye dani.


Daƙyar Aliyu ya lallaɓa rose suka bar ƙofar office ɗin Jay, kuka take rurus cin ƙarfinta, a zuciyarta tana ayyana matakin gaggawa da zata ɗauka akan Bilkisu nan bada jimawa ba, bazai yuwu tazo jiya-jiya ta samu abinda ita ta kashe shekaru masu yawa tana bibiyaba, dolene kodai ita ta samu, kokima su rasa gaba ɗaya. Da wannan ƙudirin tabar office yau.
Yau tare dashi mukabar office, a ƙasan raina cike nake da tuhumar ina Yah Qaseem ya shiga? Sam bana ganinsa a office tunda na dawo, mike faruwa dashi ne? Inason tambayar boss inajin tsoron buyaginsa. Munyi nisa a tafiya batare daya kalleniba yace, “Jazuga bai mutuba”. Da wani irin matsanancin sauri na juyo na kallesa, harma na manta dawa nake na kafesa da idanu ko ƙyaftawa banayi”. “Malama idanun nan sunmin yawafa”. Kumbura fuska nai na ɗauke kaina jin abinda yace, sai kuma na kasa haƙuri naɗan sake kallonsa na risinar da kaina, cikin zumuɗi nace, “Dan ALLAH da gaske boss?”. yace, “Mun fara ƴar wasane dake?” kaina na girgiza masa dukda nasan bani yake kalloba. Shiru bai sake cewa komaiba, har muka isa masarauta, dukda inason jin ƙarin bayani haka na daure na danne a raina, idan taƙamarsa jan aji gidan ya taras.
A cikin ran Jay wani irin haushine ke cinsa, mamaki da takaicin miskilancinta yake, yayi shirune yaji kozata tambayesa cigaba labarin amma yanda yay shiru itama ta tsuke baki, shikuma inhar ba ita tanema jin yanda akaiba bazai faɗa mataba. Babu wanda ya sake yin magana tsakanina da shi har yasamu guri yay fakin gab da sashen gimbiya, dan yanzu shi babu shamaki an bashi damar shigowa cikin masarauta a duk sanda yaso. Yunƙurin buɗe motar nai ya riƙo hannuna. Daƙyar na iya danne abinda nakeji na kallesa, ganin ni yake kallo sai nai ƙasa da kaina, sakarmin hannu yay yana faɗin, “Saiki jira na gama tunda ba tauneki zanyi ba”. Nidai bance komaiba, ya miƙa hannu sit ɗin baya ya ɗakko leda viva sabuwa. “ga wannan, duk yanda zakiyi amfani dasu na rubuta miki, Karkiyi wasa Miemaa, dan ina buƙatar matata a kusa dani” yay maganar ahankali yana kafeni da idanu, saurin sadda kaina nai dan naji wata irin bahaguwar kunya ne. Jay dake kallonta yay wani lallausan murmushi da cigaba da faɗin, “dolene ta hanyarki zan gano bakin zaren matsalarmu, hakan kuma bazai yuwuba kai tsaye sai da taimakon UBANGIJI”. Kaina a ƙasa nace, “Insha ALLAHU zanyi Sir”. “ALLAH ya tabbatar”. Ya faɗa batare da ya da ɗauke kansa daga gareni.
Nima saina fita a motar ɗauke da ledar da bag ɗina, ta sashensa na zagaya na sake masa godiya sannan na shige, tuni an amshi kayan hannuna tun fitowata a motar.
Jay daya kafeta da kallo ta cikin mota yaɗan lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya lokacin data shige. Shima fitowar yayi. Masallacin masarauta yay salla har isha'i, kafin ya samu damar ganawa da gimbiya a tsaitsaye. Yamata bayanin abubuwa da dama a gurguje, itama ta sanar masa ƴar firar da sukai da Bily da abinda ta fahimta. Duk yanda taso yaci abinci ƙinci yay yauma yaymata sallama ya wuce.
__________________________
Tun daga wannan ranar gimbiya ta sake jan Bilkisu jikinta, riritata take tamkar uwa da ƴa, gefe ɗaya tana koya mata dabarun rayuwar aure cikin hikima kamar yanda itama Mommah tai mata gata, sannan a hankali take fahitar wasu abubuwa daga Bilkisu ta cikin hira. Magungunan da Jay ya kawo mata Amintacciyar baiwar gambiya tsaye take akan Bilkisu dan ganin tayisu kamar yanda ake buƙata, ga maganin sanyi shima da ake bata acewar gimbiya shine matakin farko.
Kullum da safe driver zai kaita office da yamma idan an tashi Jawaad ya ɗakkota ya maidota, dukda babu wata hirar arziƙi a ciki, yakuma daina raɓarta koda wasa, yanzu sam basama haɗuwa sosai a station ɗin saboda baya zama aiki yaymasa yawa, su kansu yana wajigasu da ayyukan sosai.
A haka aka shiga wata mai albarka na ramadhana, manya da ƙananun yara harma da tsaffi kowa ya tashi da wannan ibada a baki cike da ɗoki da fatan kammalawa lafiya. Yayinda Bilkisu ke kallon ikon ALLAH wajensu gambiya dangane da alkairin da ake fita dashi domin talakawa. Abin sai ya birgeta, a cikin ranta tana fatan kwatantawa taji idan zata iya watanara, sannan har yau da take nufar sati na biyu a masarautar bata taɓa gamo da Sarki Sameer ba, Safah ta sanar mata yaje saudia hutawa shida amaryarsa da suke kira Ammi, sai azumi yaje tsakkiya zai dawo sukuma su tafi Umarah



★★★★
Jay da muƙarrabansa sunyi busy matuƙa, ga aiki ga aikin sa kai gana hidimar bayin ALLAH duk ya haɗama kansa, burinsa ya kammala abubuwa da yawa cikin watannan, baya neman Bilkisu ne dan yana tausayinta sosai, ga azumi ga rana dan ruwa bai zaunaba sosai, gani yay ta rame masa a kwanakinan sosai sai tai haske kuma.
Abin mamaki Rose kuma saita shiga ja baya dasu, har takai saida Jay yamata magana da kasa, ranar kam dai yaga taɓara da iyayi, gashi yanaji da azuminsa. Shidai ya lalaɓata kawai dan yana buƙatar nutsuwa baison hayaniya.
Tuni yasa ana bibiyar masa bayan Ɓaleru duk inda ya sanya ƙafa batare da shi ya saniba, bayason kamasa a cikin watannan mai albarka shiyyasa yay tamkar ya manta da al'amarinsa, ga jikin ɗan-fir'auna da har gidan su Shahudah suka ɗauka ya mutu na nata sauƙi da warwarewa.
__________________________
Kwanci tashi babu wahala wajen UBANGIJI azumi yakai tsakkiya, a daren sha bakwai sarki Sameer da Amaryarsa suka dawo, anyi murna da dawowar tasu sosai, dan ranar kam kowa ya shaida hakan a masarautar gagara badau, ranar gimbiya da kanta taima Takawa abincin buɗa baki a kicin ɗinta na sirri da babu mai shiga sai ita saiko Amintacciyar baiwarta. Tunda ta tafi ɓangarensa su bily basu sake jin ɗuriyartaba sai washe gari, sai a randa za'a ɗau azumi na sha takwas ne suka ganta, shima dan tasaka a kira mata bily ne.
Cikin girmamawa na gaisheta kamar yanda na saba, fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa min tare da kamo hannayena cikin nata. “Ɗiyata dama nasa a kiramin kene saboda zaku wuce Umrah gobe idan ALLAH ya kaimu ke da su Amaturrahman, an kammala miki komai insha ALLAH” Dama Boss ya sanarmin tun shekaranjiya, sai dai na nuna mata farin cikina sosai akan hakan itama tamkar bansan da tafiyarba, nakuma mata godiya. Ta cigaba da faɗin, “Naso ace tun farkon azumi kika tafi, sai dai mijinki ya sanarmin hakan bazai yuwuba saboda aikinki, dan akwai wata auntyna matar yayan abokin Takawa tanada makaranta ta musamman domin koyar da amare, ana gyaran jiki da komai a ciki, koya girki da dukkan dabarun zaman aure, itama ƴar nan ƙasarmu ce, dalilin ƙaddara ta shigo rayuwarmu, mun kaita domin neman magani sai yayan abokin Takawa yace shifa yayi mata, wannan shine dalilin zamanta a can itama”. Fuskata ɗauke da murmushi nace, “ALLAH sarki”. Itama murmushi tayi, “Yanzu dai yayi dukkan cuku-cukun daya dace a wajen aikinku insha ALLAH keda nan sai saura kwana biyar tarewarki, inason naga kin zama cikakkiyar mace mai amsa suna mace a fadar mijinta, mijinki babban mutumne sannan yanada wasu sirrika dake kaɗai zaki fahimci kayanki anan gaba, shiyyasa nakeso a gyaramin ke yanda ya kamata domin zukatan maƙiya su girgiza, waɗanda suke ganin baki kaiba su fahimci kin musu zarrah ta har abada kinji”. Hawayen dake ziraromin na share, bansan irin godiyar da zanma wannan baiwaba a rayuwata, itaɗin ta musamman ce a cikin jerin abubuwa masu muhimmanci da suka shigo rayuwata, ALLAH ya biyata da aljannarsa.
Washe garima naje wajen aiki, sai dai yau bashi ya maidoni ba sawa yay sabon direbansa ya maidoni, gobe idan ALLAH ya kaimu kuma bazanje aikiba, dan ƙarfe huɗu zamu wuce, share hawayen dake zubomin nake akan abinda ya faru tsakanina dashi yanzu a office ɗinsa. Na roƙesane akan zanje gidan Dad nai masa sallama, dama tun farkon azuminan naketa masa magiyar ya kaini na gaishesa, bai taɓa kulaniba sai yau da yanema marina a office, yajamin dogon gargaɗi akan inhar na sake masa maganar Dad ALLAH sai ya fasan baki. Sake share hawayen nai zuciyata namin zafi da takaucinsa, ni bansan mi Dad yaymasaba haka da zafi shi da ahalinsa, inason ganin koda mutum ɗayane a cikinsu amma abin ya gagara, sam yanzu bana ganin Yah Qaseem, narasa ina ya shiga baya zuwa Office, mike damunsa? Minene matsalarsa? Haka kawai bazai bar zuwa office ba ai?. Zafin boss yayi yawa, nikuma har zuwa yanzun ban taɓa jin sonsa a rainaba, nasan dai zan iya haƙurin zaman aure dashi amma badan inajinsa a raina da kalmar soyayya ba, bansan miyasa hakanba, har zuwa yanzu Yah Qaseem ne kaɗai a zuciyata, shi nakeso, shi na fara so, sai dai shikuma banajin sha'awar zama dashi matsayin miji, bansan miyasa hakanba shima. Ya ALLAH ka kawomin ɗauki bisa ruɗaɗɗen tunanina daya banbanta dana sauran mutane a yanzu.




Har muka bar ƙasar bana cikin walwala sam, sai wata irin matsananciyar damuwa da na tsinci zuciyata a ciki, wannan dalilin yasa har jirginma ya tashi ban tuna shine hawana na farkoba, Safah na lafe a jikina tana barci har muka sauka. mun sami tarba ta musamman daga wasu manyan mutane da bansan matsayinsu ba, sai dai ina tunanin waɗanda Gimbiya taban taƙaitaccen labarinsu ne ranar, sai dai wannan nafi ƙyautata zaton abokin takawane da iyalansa ba waccan mai makarantar bace da naji nafi ɗokin gani. Ƴan uwa abu mafi ɗaure kaina shine, maimakon najini cikin farin ciki da zuwa ƙasa mai tsarki a karo na farko a rayuwata sai saɓanin hakan ya biyo baya, kallonsu nike kawai tamkar wata sakarai, ƙirjina na wani irin zafi, sai can ƙasan zuciyata kuma nakejin wani irin sanyi dake kawomin sassauci a cikin ƙirjina kaɗan-kaɗan. Darene sosai, dan haka makwanci kawai aka bamu da abinci, nikam bammaciba na kwanta.
______________________________
Yau tunda ya tashi aiki wanka kawai yaje yay a gida ya kimtsa, sabon drivernsa mai suna Sadiq ya ɗaukesa sai gidan Alhaji Babba dan acan yake buɗa baki yanzun kullum, wataran kuma gidan Ummah babba, kokuma gidan Ummah ƙarama idan ta ishesa da ƙorafi. Haka kawai yau yakejin tamkar wani abu dake nesa dashi yana tunkarosa, minene? A ina yake? Itace amsar dakanzo masa akai-akai cikin shauƙinsa.
Shi dai Alhaji babba kallonsa kawai yake amma baice komaiba, sai da suka dawo salla sukai zaman buɗa baki sannan, ya kai dubansa ga Jay da keta juya cokali cikin kofin kuni yana ɗan murmushi. “Wai nikam gwauron nan yau miya saka farin ciki haka?”. Kallonsa Jay yay fuskarsa ɗauke da murmushin har yanzun, yace, “Babu komai Baba, kawai dai”. Murmushi shima Alhaji baban yayi, “Kawai dai haka ka tsinci kanka kaima ko?”. Kai Jay ya jinjina masa yana lumshe ido. Alhaji babba yace, “Nima haka na tashi da farin ciki, sai nakeji tamkar wani abu dana daɗe da rasawa zai dawo gareni, sai nakeji kamar wani abuna mai muhimmanci ya haɗu da abuna mai muhimmanci, sai nakeji kamar wani abun da na daɗe ina neman amsarsane lokacin sanin amsar yayi, a daren jiya nayi mafarkin ƴaƴana guda biyu cikin farin ciki, tabbas Jawaad inaji a raina wani abu mai daraja da haske na matsowa zuwa garemu”. Jawaad sauraren Alhaji babba kawai yake yana murmushi irin wanda ya kasance mai tsada a garesa, ya ɗora kansa a kafaɗar kakansa yana sake ƙawata murmushinsa, “Ya ALLAH ya tabbatar da wannan hasashe naka ya zama alkairi kakana”. Shafa kansa Alhaji babba yay yana murmushi da faɗin, “Amin ya rabbi jikallena, amma yakama ka dawo nan kwanaki goman nan na ƙarshe muyisu tare cikin ƙololuwar ibada, ka ajiye duk wani aiki gefe”. Jay ya tashi zaune sosai yana kallon kakan nasa, yace, “Nima nayi wannan tunanin, sai dai banason takura maka da yawa”. Ranƙwashi Alhaji babba ya kai masa bisa kai, Jay yay saurin kaucewa yana dariya da haɗe hannayensa waje guda alamar na tuba.
Bayan sun dawo daga salla suka iske Ummah babba da ƙarama sunzo, dama sunce yau zasuzo. Jay ya zauna tsakkiyarsu yana dariya da faɗin, “Saini ɗan gatan ALLAH, Ummahs ɗina duka tare dani”. Atare sukai dariya da riƙe hannayensa, Ummah babba tace, “Ja'iri kamar ya wani damu damu?”. Karyar da kai Jay yayi ya ɗora saman kafaɗarta, murya a sanyaye yace, “Idan ban damu da kuba dawa zan damu Ummah?, kuɗin duniyatace, sannan haskena, aikine kawai ke hanani rawar gaban hantsi”. Guntuwar dariya tayi da shafa kansa, ta sumbaci hannunsa tana mai saka masa albarka.
Kasancewar basu da ishashen lokaci suka fara tattaunawa akan maganar lefe da dama shine ya kawosu. Da farko Jawaad yace su barsa zaiyi, amma sukace sam bazai yuwuba, na farkoma dan an nuna musu fin ƙarfine Uncles ɗinsa sukace zasuyi, to wannan kam suma sune zasuyi insha ALLAH.
Jawaad yay shiru yana murmushi dajin ƙaunarsu mai narkar da zuciya na ratsasa, zamansa ya gyara a kujerar daya koma shi kaɗai yana kallonsu, “Nagode sosai iyayena, kun sharemin hawayen maraici tuni, bani da abin biyanku sai dai naita muku addu'oin gamawa da rauwa lafiya, idan na ganku saina manta bani da Uwa, idan kuka kalleni sai nake ganin Mah-mah har yanzu tana tare dani, ida har tabar duniya ina roƙon UBANGIJI yasa ana nuna mata dukkan alkairanku ga gudan jininta, idan tana duniya ina fatan ganinta na bata labarin alkairanku ga gudan jininta, ku......” “Ya isa haka kaji Muhammadu, insha ALLAH inaji a jikina BILKEESU tana raye, insha ALLAH kafin nabar duniya saina ganta” Alhaji babba yay maganar yana share hawayen da suka ɗan zubo masa. Ummah da Ummah ƙarama ma kuka suke, Jay gwanin dakiya babu hawayen zahiri saina zuci kawai.




________________________________
Kasancewar nazo babu tsarki sai yau nake fatan samu lokacin da zamuyi sahur saina duba, naji wani nishaɗi ganin ya ɗauke harda tsallena a bayi, wanka nayo da brush na fito, cikin tsokana Meenal tace, “Gandiya halan yau kin musulunta ne? Naga wanka da asubar fari”. Murmushi nai mata ina zama domin busar da kaina da hand drayer ɗin dana gani saman mirror ɗakin, nace, “Oh da kafira kike kallona?”. Dariya sukayi ita da Amaturrahman dake ƙoƙarin shiga yin brush itama, tace, “Ai kima godema ALLAH ke kina zuwa yana ɗaukewa, ita tana shigowa yana zuwa”. Cikin ɗan zaro idanu na kalli Meenal ɗin, sai kuma na langaɓe kai nace, “Kai harfa kin bani tausayi babie”. Filo ta ɗauka ta jehomin ɗaya ta jefama Amaturrahman. Da gudu Amaturrahman ta shige bayi tana dariya, nikuma na cafe wanda ta tillomin. “ALLAH karkiji wasa meenal tausayi kika bani” nai maganar da ɗan mata gwalo. Ƙwafa tayi da faɗin, “Wlhy duk zan rama, ke saurama ƙiris na raman ai, zaki gane kurankine”. Murmushi nai mata bance komaiba na cigaba da busar da kaina.
Bayan munyi sahur salla mukai muka sake kwanciya barci, mune bamu tashiba sai sha ɗaya, shima tadamu akazo akayi. shiri mukai a gaggauce na tafiya massallaci, nidai Kasa daurewa nai na tambayi Amaturrahman Auntyn da Ummu tace tanada makaranta gidansu kuma na kusa da inda zamu sauka?.
“Lah Bily ai yanzu bazakiga Umm-Anum ba, sun shiga ittifaqi, kinga gidansu nan, duk Ramdhan idan mukazo bama ganinsu muma sai ranar sallah”. Da mamaki nace, “Basu da yara?”. Tace, “Sunada yara biyu mana, mace da namiji, namijin ya girmemu da kusan shekara biyar, sunansa Anwar, sai macen Anum, tare suke shiga ittifaqi. Tunkan na gansu naji sun matuƙar burgeni har ina zumuɗin ganin nasu mai ban mamaki, dan tunda Ummu taban labarin matar a taƙaice saita kasa barin zuciyata. Yanda na iso da ƙuncin zuciya a yanzu sai ba hakaba, fes nakejin raina cike da nishaɗi da farin ciki da shauƙin ganina a ƙasa mai tsarki, santin da banyi a daren jiyaba sai gashi a yau inayinsa, dan har muka isa massallaci bakina bai hutaba, Safah kam bata gajiya damin bayanin komai dalla-dalla. Lokacin dana ganni gaban ɗakin ka'aba sai kawai nakejina tamkar wata sabuwar Bilkisu ce tsaye ba wadda tazo da ƙunci ba, hawaye masu ɗumi na ziraromin bisa kumatu, abinda ban taɓa tunaniba koda a mafarki, wani nauyin zuciya da ƙunci da damuwar da natsinci kaina a gaba ɗaya cikin shekarunan sai naji tamkar an yayesu an zubar tare da ruwan wankan dana samu tsarki ɗazun da asuba. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai ni'ima.
Muna zaune a wajen mutanen kirki, larabawan usul masu ƙyawawan zuciyoyi, bamu rasa komaiba, ibada muke babu wasa dansu Amaturrahman sun horu sosai, sannan sunada ilimin addini suna kuma aiki dashi, Umm-Aban koda yaushe cikin kulawa take damu sosai, nasamu sauyi iri-iri da haske a rayuwata a cikin kwanakinan goma da mukai na Umrah, babu abinda mukeyi banda ibada, duk wata shiririta mun ajiyeta gefe, a kullum safiya bayan sahur muna waya da gimbiya, hakama su Ummie duk saina kirasu, Boss kam ko filashin bai taɓa haɗamu ba, sannan dukkan numbers ɗin ƴan gidanmu bana ganinsu a wayata yanzun, bansan yaya akai hakan ta kasanceba tunda nidai ban gogeba.
Yau take salla, sosai massalacin ke cike, bayan an idar da sallah sai na dingajin juwa, duk yanda naso dannewa hakan ya gagara, bandai sanarma su Amaturrahman ba dan karsu tada hankalinsu, miƙewa nai da nufin na ɗan samu waje inda babu yawan mutane na huta ko zanji nutsuwa sai kawai hajijiya ta kwasheni. Sama-sama na jiyo wata nutsatstsiyar muryar ta ambaci “Yah ALLAH”. Sai jina nai a jikinta. Cikin ɗan larabcin da nakeji kaɗan-kaɗan na tsinci tanama wani wanda bansan ko waneneba magana akan ya bata ruwan zam-zam dake hannunsa. Gabana yay wata masifar faɗuwa jin muryar data amsa mata, murya irin wadda wajan mutum ɗaya na santa, muryar dake sakani bugun zuciya, muryar dake saka jinina gudu cikin jijiyoyi, da ƙyar nai ƙoƙarin ɗaga idanuna dake neman rufewa na sauke a kansa dai-dai ya miƙo ƙaramar goran ruwa wa matar da har yanzu nike a jikinta.............✍



ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.



ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/25/2020, 10:03 AM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Page 36

.................Tabbas muryar iri ɗayace, kamanin ma ɗayane, sai dai wannan farine tas, shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na sake lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar goran ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a gaibun mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi, matashiyar budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta duƙa gabana tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai kuka, magana take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin baki, na kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta  daban. Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai sa'a  itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake buɗewa a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani abu akan fuskata.
        A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina. Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar, babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
      Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har yanzun........
     Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
        Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta, “Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
         Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”.  Cikin sauke ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
          Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
             Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu kamar bansan sunaiba.

        A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai, munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema makwancinsa.
        Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo, dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake

zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin, “Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.

★★★★★★★

          Washe gari tunda safe saiga kira daga Ummu, bayan duk mun gaisa da ita tace a bani wayar.  Daga can tace, “Yauwa ɗiyata ki shirya komai naki danke yau zaki koma wajen Aunty da zama, tun jiya da daddare ma taso shigowa ta ɗaukeki, ki nutsu ki kwantarmin da hankalinki ki

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment