Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baƙin cikin abinda tamin ban rikita kainaba a yayin bin bayanta, can na hangota jikin wata farar mota mai ƙyau da ɗaukar hankali, na cigaba da takawa a nutse gareta, ina isa jikin motar ita kuma tana buɗe gaba ta shige, hakan sai ya sakani a duhu, dan bansan kuma wajenwa zanje ba. Saitin inda take na ƙarasa, na ɗan risina yanda zata ganni ina faɗin, “Gani maa!”.
     Kafin ta bani amsa ƙofar murfin baya naga ta buɗe, ita da drivern naga duk sun kalli bayansu, hakanne ya sakani kallon murfin ta waje nima, muryar drivern ta katse min tunani, “Ki shiga” ya faɗa yana nunamin bayan.
      Duk da na shiga ruɗani, ga harbawar da ƙirjina keyi hakan bai hanani bin umarninsaba, koda wasa ban kalli waye a bayanba, na shiga kamar yanda aka umarceni, sai da na zauna ne wani mayen ƙamshi ya samu cikakkiyar damar surɗaɗawa a ƙofofin hancina, da sauri nai ƙoƙarin kallon gefena, gabana ya faɗi dan ganin wanda banyi zatoba, fuskarsa babu alamar wasa kamar yanda na gansa yanzu da mukai karo.....
      “Sai kin gama kallona zaki rufe ƙofar ne?” muryarsa ta daki dodon kunnena babu zato, kaina na girgiza da sauri ina tattaro busashen yawun bakina da ƙyar na haɗiye, tare da jawo murfin motar na rufe. Nama rasa yanda zan fassara wannan al'amarin sam, gashi yanayin dana tsinci kaina ya hana mani damar yin nazarin daya dace da hakan.

         Ɓangaren Rose da Gimba kuwa mamakine fal a rayukansu, gimba shaidane akan bai taɓa ganin rose ta shiga bayan motaba kusa da boss, baima taɓa bata wannan damarba koda a fuskane, idan har kaga wani ya zauna a kusa da shi to lallai sai dai cikin su Aliyu ne, amma yau abin mamaki sai gashi shi da kansa yasa hannu ya buɗema yarinya ƙarama murfin mota, ya kuma bata lasisin zama a gefensa, ‘Anya kuwa?’ ya ayyana akan laɓɓansa yana mai satar kallonsu ta mirror.
     Ita kanta rose a kume take da mamaki, ita duk zatonta wani abun zai saka yarinyar, b

ata kawo a ranta wannan abar zuwan jiya hukumarsu har tanada lasisin shiga cikinsu ba, balle harma ta shiga motar da boss yake ciki, a kusa da shima, shi da kansa ma ya bata lasisin zaman, abinda ita bai taɓa bata fuska a kaiba, ko zaman gaban motar da yakema sai ya gadama yake barintayi koda taso hakan kuwa, idan ko bata mantaba wannan itace shekara ta bakwai cif tare da shi tana aiki a ƙarƙashin group ɗinsa, ‘To mi hakan ke nufi?’ tayi tambayar a zuciyarta.
         Shi kansa Jawaad mamakin kan nasa yake, amma da yake shi kogine babu mai gane gabansa balle bayansa sai bai nuna koda a fuskaba, hasalima tunda suka fice daga station ɗin kansa na duƙene yana danna tab.. Da alama wani abun yakeyi, sai dai ƙamshin turaren bilkisu duk ya addabi hancinsa.
        Kowa da abinda yake kissimawa ransa har suka iso inda yake buƙata, gimba ya samu waje yay fakin, babu wanda yay yunƙurin buɗe motar a cikinsu balle ai tunanin fita, duk suna jiran umarni daga garesa. Shiko yay burus tamkar baiji motar ta tsayaba, sai faman danne-dannensa yake cigaba dayi a tab ɗin.

         Sosai zaman ya gundureni, ba komai ya jawo hakanba sai matsuwar da zuciyata ta samu saboda kusancin dana samu da shi tare da lokaci mai tsayi da hakan bai taɓa faruwa ba, da gefen ido na saci kallonsa, sanye yake da wandon jeans kalar bulu, sai t-shirt fara, ta kwanta a jikinsa luf, dan yanda ƙirarsa ta bayyana ta cikakken mutum mai motsa jiki kawai ya isa baka amsa, dogon hannu gareta, amma ya tattareshi sama ya koma iyakar gwiwar hannun, sai agogon fata baƙi mai azabar ƙyau a tsintsiyar hannunsa da gashi ke kwance na alamar jin daɗi, na sauke idanuna bisa yatsansa dake cakalar tab ɗin, sanye yake da zoben azurfa mai tambarin stone babba tamkar diamond, da gani kasan zoben zaiyi tsada koda ba'a faɗa makaba........
       “Gimba ka tabbatar nanne wajen?”.
     Maganarsa ta katse min dogon nazarin dana tafi na babu gaira babu dalili.
        “Eh wlhy boss nanne, kuma wannan shine dai-dai lokacin da a kullum yake zuwa cin abincin safe shi da abokin nashi, a yanzu haka kuma inada tabbacin abokin nasa na cikin wajen, nanda mintuna ƙalilan zai iya fitowa”.
     Uffan bai ceba, ya kuma cigaba da sabgarsa tamkar bashine yay tambayar aka bashi amsaba, a fuska dai baiyi kama da miskiliba, abinda kawai na fassara halayyar wannan mutumin shine Ɗan wulaƙanci ne lamba ɗaya kuwa, babu wanda ya sake magana tsahon wasu mintuna, bansan mi sauran sukeba, ni dai ina takure ne jikin ƙofa idona a waje ina kallon shiga da fitar mutanen dake fitowa a cikin wajen cin abincin (Restaurant), kasantuwar gilashin motar mai duhune nasan babu mai ganinmu, sai dai mu mu gansa, hakan ya sakani baje idanuna nake kallon komai daki-daki.
       “Yauwa boss ga shinan ya fito” gimba ya faɗa da sauri yana nuna ƙofar shiga da fita na gidan abincin. Nidai kallon wajen nayi, shikam ko motsi baiyiba, bai kuma ɗago ya kalli abinda drivern ya nunaba, sai cewa da yay “Rose! Kibi wancan mutumin, duk yanda zakiyi kiyi magana ta shiga tsakaninku, magana kuma irin wadda zata iya zama mai kusanci”.
       “Okey boss” ta amsa da sauri tana buɗe motar ta fice, sai lokacinne naga ya ɗago kansa ya kalli wajen, ba tare da ya sauke gilashin motarba, “Gimba ka tabbatar ka ɗaukesu a hoto mai motsi” yay maganar idonsa a kansu.
     Saurin amsawa drivern yayi, tare da buɗe motar ya fice da sauri. Gabana ya faɗi dan ganin an barni daga ni sai shi a motar, sai dai nayi ƙoƙarin kamewa gudun karna zubda darajata da akasan ɗiya mace mai tarbiyya da ita, kallonsu na cigaba dayi kamar yanda shima na fahimci hankalinsa na kansu.
          Muna kallo rose ta bigi saurayin da ya fito daga wajen cin abincin yana latsa waya, wayar hannunsa ta faɗi, kusan a tare suka duƙa domin ɗauka, bakin rose ɗin na motsawa, sai dai mu bamajin mi take faɗa, saurayinne yay murmushi suka miƙe tare bayan ita ta samu nasarar tattara wayarsa data tarwatse a hannunta, magana yake mata tana bashi amsa da murmushi saman fuskarta, sai dai shima bamajinsa, ta miƙa masa wayar tana faɗaɗa murmushin fuskarta tamkar yanda shima yake faɗaɗa nashi, bai amshi wayarba

sundai cigaba da magana, sai kuma mukaga suna ƙyalƙyata dariya a tare, hanya ya nuna mata alamar suje, babu musu kuwa tabi umarninsa, tana gaba yana biye da ita har wajen wata Blue ɗin mota, shine ya buɗe mata ta shiga ta zauna sannan shima ya buɗe ya shiga sashen mai tuƙi, munata kallonsu har suka bar harabar restaurant ɗin......
     Numfashi ya sauke a hankali yana ɗauke idanunsa da ga wajen, hakan ya sakani nima sauke nawa a ɓoye ina gyara zama cikin alamar takura, addu'ata da fatana bai wuce drivern ya dawo cikin motarba kona samu sauƙi, babban fatana kuma yace na koma gaba inda rose ta tashi, sai dai har tsahon mintuna biyar da barin su rose gidan abincin baiko motsaba balle ya kalleni, saima kansa da ya kwantar jikin sit ya lumshe idanu, “Ƙil!-ƙill!!” tab dinsa tai motsi alamar shigowar saƙo, bai motsaba, hakan yasa mamaki ya kamani......
        “Ɗauki ki duba mi tace?” ya faɗa ba tare da ya motsaba. Gabana ya faɗi, dan nadai fahimci dani yake, kuma yana nufin tab.. Ɗin tasa zan ɗauka, ganin bai sake maganaba ne ya sakani kallonsa, a ɗarare nace, “Dani kake sir?”.
       “A'a da kaina nake” ya faɗa a daƙile......
     Kafinma ya rufe baki na kai hannu na ɗauki tab ɗin da ya ajiye a tsakkiyarmu, gabana sai wata irin faɗuwa yake tamkar zan haɗiye zuciyata a cikin bakina, madannin na danna ta kawo haske, wani haɗaɗɗen hotonsa ya bayyana, duk da son kallon hoton da naji ya tsargamin hakan baisa na tsayaba, saima mamakin ganin babu lock a jikin tab din ne ya kamani, naja hoton yay sama kawai, a take apps da yawa suka bayyana, baza ido na shigayi wajen neman messeges app, da ƙyar na tsaida hankalina na ganosa, ina buɗewa kuwa da sunan rose na fara cin karo, na buɗe saƙon nata, abinda ta turo bai shige kalmomi hamsin ba.     “boss ya buƙaci nabisa, duk abinda ake ciki zakaji daga gareni”.
       Cikin ɗan rawar baki nakaranto masa kamar yanda ta rubuto da harshen turanci, bai motsaba, bai kuma tanka mani ba, hakan yasani ajiye tab ɗin ina mai satar kallonsa, sai da ya ɓata lokaci kafin ya jehomin tambaya.
        “Ya sunanki?”.
‘Ikon ALLAH’ na faɗa a raina kafin na bashi amsa da, “Bilkisu Adam makaho”.
       Yanda ya buɗe idanu da sauri a kaina ba ƙaramin firgitani yay ba, mayun idanunsa masu saka tsigar jikina tashi ya dasamin, bansan miya bashi mamakiba, sunan nawane? Kokuwa na babana? Kokuwa makahon dana ambata a ƙarshe?. bansan amsarba, bani da ƙwarin gwiwar tambayarsa kuma. Tsahon minti ɗaya da sakanni yana kallona kafin ya janye idanunsa yana motsa baki tamkar mai son cewa wani abu,ni dai ta wutsiyar ido nake kallonsa shi da jin kansa.
       Baice dani komaiba ya buɗe motar ya fita, ajiyar zuciya na sauke, dan fitar tasa sai naji kamar ya bani wani ƙaton filin cin karena babu babbaka ne.......
        “Ko sai an fiddoki?”. Furucinsa ya daki kunnena, da azama na buɗe murfin na fice nima, gani nai ya wani zubomin idanu, bansan mi yake nazartaba daga gareni, sai jefani a ruɗanin zuciya dana takurar kaifin idanunsa da yayi, hakan yaja nai ƙasa da kaina dan bazan jura kallonba.
         Takunsa kawai naji alamar ya matsa daga kusa dani, na saci kallonsa, sai naga yana ƙokarin ciro abu daga cikin but ɗin motar da ya buɗe, nufonin da yayne ya sani saurin ɗauke idona, ya miƙomin farar coat ta mata da tsayinta zai iya kaiwa gwiwa, ban musaba na amsa, sai dai ina buƙatar ƙarin bayani, “Saka” ya faɗa yana wuceni.
      Sosai naketa mamaki, na warware rigar na saka a jikina saman Uniform ɗin dana sanya, sai ya zam rigar ta ɓoye bayyanar ni wacece, baƙin wandon kawai ake iya gani ta ƙasa, daga sama kuwa farin baby hijjab ɗinane ya bayyana, sai rigar ta fiddamin da wani tsari daban daya bayyanar da sirrintaccen kwarjinina da wasu ke iya ambata da ƙyawu. Bai cemin komaiba yay gaba na bisa a baya, dan zuwa yanzu kam na fara fahimtar hallayarsa da hanyoyin maganin zama da shi.
      Sai da muka gabato shiga ƙofar wajen sannan ya tsaya muka daidaita tafiya, ƙasa-ƙasa na tsinkayi muryarsa yana magana.
        “Ki kula sosai, sannan ki tabbatar da yanayinki ya canja tamkar munada dangantaka, idan kikamin shirmen da aikina ya buɗe

lallai sai kinyi nadamar hakan”.
       Sosai maganganunsa suka tsirgamin zuciya, dan kuwa ban gama fahimtar ma'anarsu ba balle manufarsu har muka ƙarasa shiga wajen.
         Wajen yay bala'in haɗuwa, daga gani kasan masu abokan magana a aljihune kawai keda hurumin shigarsa, dan danan akai mana tarba ta mutuntawa, yanda ya ƙawata fuskarsa da murmushi ne ya ɗauren kai, hakan yasani nima aro irin basajar tasa na yafama kaina ina murmushin, ɗaya daga cikin yaran wajenne ya nuna mana wajen zama, bayan mun zauna yake tambayarmu komi muke buƙata.
       Boss ya juyo yana kallona fuskarsa shinfiɗe da wani murmushin da ya kusa zautani, “My princess! Mi kike buƙata?”.
     Wata masifar harbawa zuciyata tayi, kaɗan ya rage ban fallasamu ba, nai azamar haɗiye zuciyata dake niyyar fitowa ta baki saboda salon da yay amfani wajen kiran sunana da yanayin fitar sautin, da ƙyar na iya dai-daita kaina nai wani farin da bansan na iyaba da idanu, ina wani narke murya nace, “Duk abinda ka zaɓa mana yayi my king”.
     Ɗauke idanunsa yay daga kaina, har zuwa yanzun fuskarsa ɗauke da murmushin da ya fidda lotsar dimples ɗinsa masu ɗaukar hankali, ya duba waiter ɗin yana bashi umarnin ya bashi list ɗin abinda suke da shi ya duba.
    Da girmamawa ya amsa yana barin wajen, saurin yin ƙasa nai da idanuna ganin ya maido kallonsa gareni, murya ƙasa-ƙasa yace, “Ina sake gargaɗinki a karo na biyu”.
     Kaina na jijjiga masa ina saurin gyara yanayina. Sallama wata matashiyar budurwa taimana saɓanin wanda yazo ɗazun, sanye take da Uniform ɗin wajen itama, cikin girmamawa ta ajiye goran ruwa biyu da kofuna dake saman tire ƙarami, kafin ta miƙa masa ɗan littafi dake a hannunta. Amsa yay yana dubawa, tare da yin alama da pen ɗin data haɗa masa da shi akan duk abinda muke buƙata, baifi sakan sha biyarba ya miƙomin littafin yana fadin, “Duba yayi?”.
     Amsa nayi ina kuma matse nutsuwata, nai nazarin duk abinda ya zaɓadin kafin na ɗago ina murmushi, cikin salon da bansan nayiba na ɗaga masa gira ɗaya da juya ƙwayar idona kaɗan alamar yayi.
    Idanunsa ya lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana sakin wani lallausan murmushi da yafi na ɗazu.
    ‘Innalillahi....’ Na iya ambata ina saurin maida fitsarindake neman kufcemin.
         Tana barin wajen ya kalleni da sauri, murya ya rage ƙasa sosai, wanda yake nesa damu zai ɗauka soyayya mukeyi, maganar da ya faɗamince ta sakani jinjina masa kai da sauri, ina kuma murmushi, badan tanada alaƙa da murmushin nawa bane, sai dan kawai barin murmushin akan fuskar tawa ya zama tilas saboda kiyaye gargaɗinsa...........✍


🙄saura kuma ai gulmar Jay😏





ALLAH ka gafarta iyayenmu😭🙏🏻Bilyn Abdull 📚:
Barka da juma'a.

  Page 7

.................Mintuna kaɗan budurwar ta dawo da tire babba a hannu, wanda aka jero abubuwan da muka buƙata a kansa.
            Tana ƙoƙarin ajiyewane Jay ya miƙa hannu zai ɗauki ruwan da aka fara kawo masu, a salon da babu wanda ya isa fahimtasa har bily bata kulaba ya tanƙwaɓi tiren ya suɓuce, jikake “Tarats!!! Tass! Tatass!!” kwanikan da suka zube na fashewa, abinda ke cikinsu gaba ɗaya sun koma jikinsu sun wankesu, duk jikinsu ya ɓaci daga shi har bily da bata san mafari ba, a take duk hankalin mutanen dake kusa dasu ya dawo kansu.
              Na ɓata fuska saboda harga ALLAH banji daɗin yanda jikina ya ɓaciba. Cikin langwaɓe kai na kallesa kamar zanyi kuka.
        Da ƙyar Jay yay ƙoƙarin haɗiye dariyar dake neman kufce masa saboda yanda Bily tayi fuska kamar zata fasa ihu, ga mai da yay tsalle harkan fuskarta sai naso yake.
      A fusace  na miƙe saboda ganinma dariya yake neman yimin, dan da gaske haushi naji har raina, maimakon ya mata faɗa amma kuma tsabar wulaƙanci yake neman yimin dariya a cikin mutane, bamma san sanda na fara zazzaga mata masifa akan tayi hakanne da gangan ba, yanda ta rikice ba ƙaramin tausayi ta baniba, amma kuma uwar mi take kallo da zata wankemu haka?, shima jinake kamar na juya na talle masa ƙeya yasin.
           Jawaad ya tsaya kawai yana kallon bakin Bily dake masifa, babu shiri murmushi ya suɓuce masa, ganin tamkar abin nata da gaskene shima sai ya miƙe, cikin son maidota hayyacinta ya nema riƙo hannunta, amma sam taƙi yarda, dan danan wasu ma'aikatan nasu sukazo, da alama suɗin manyane, haƙuri suketa bamu amma naƙi saurarensu, daga ƙarshema nai ficewata, shikuma yay azamar biyoni yana faɗin, “princess! Princess! Please ki tsaya mana”.
     Ƙo juyowama banyiba na nufi motarmu na buɗe zan shige, saurin riƙe murfin yayi yasha gabana alamar hanani shiga motar, ya wani marairaice yana lallashina, wlhy da kunsan yanda zuciyata ke harbawa sanda muke a wannan yanayin da kun bala'in tausayamin, a haka budurwar da wasu ma'aikatan wajen suka iso suka taddamu, haƙurin suka cigaba da bamu, sai da muka ɗan garasu da kalamun cewar bazamu sake zuwa wajenba tunda basusan kimar Customers ba kafin na nuna na haƙura da ƙyar, dan zuwa yanzu na dawo hankalina akan shirinmu.
     Sun buƙaci mu koma wajen a bamu wani abincin amma na tubure akan bazan koma ba, sai dai a haɗo mana takeaway, ba musu suka amince da bukatata, ganin sunbar wajen ne ya sani sauke ajiyar zuciya ina matsawa baya saboda kusancin da muka samu ni da shi neman karya ƙwarin gwiwa da nake bama kaina ya keyi, gashi yay masifar tsareni da idanunsa.
     Shima matsawa yayi, ya nuna min mota alamar na shiga yana zubamin harara, “saurin shigewar nayi kuwa, ya rufemin murfin ya zagaya ɗayan ɓangaren, da sauri gimba dake bayanmu tsaye yana kallon dramar tamu ya buɗe masa, hanasa rufewa yayi, saima ya zauna ƙafafunsa duka a waje. A haka budurwar ta dawo ɗauke da takeaway ɗin da muka buƙata, gimba ya amsa ledojin, shi kuma ya miƙa mata atm card ɗinsa tare da wata takarda yana magana ƙasa-ƙasa, “Saboda baƙwason ya tona muku asiri kuka kasheshi?”.
     A firgice budurwar ta kalli Jay, sai kuma ta hau waige-waige jikinta sai tsuma yakeyi.
    Ya sake faɗin, “Ki daina ɓatama kanki lokaci, akwai address ɗin inda zaki sameta (ya nuna bily) a jikin takardar nan ranar lahadi, yarage naki kizo ko kiƙi zuwa, sauran bayani mahaifinki zanyimawa”.
     Sake rikicewa tayi, jikinta sai wata masifar tsuma yakeyi. Yanda taketa kallonsa a firgicene ya sakani tabbatar da maganar bamai daɗi ya faɗa mataba, tabar wajen da sassarfa, yayinda gimba ya take mata baya domin amso atm ɗin idan sun cire kuɗinsu.
       Wato dai duk yanda nake tunanin aikin nan namu yafi ƙarfin tunanina, irin wannan makirci haka tamkar wani shirin film.
 
          Gimba bai wani jimaba ya fito da ɗan hanzarinsa, motar shiru tamkar babu mutum mai numfashi, nidai takurace ta hanani yin ƙwaƙwƙwaran motsi, danma ALLAH ya soni yanzu a gaba nake ba kamar yanda muka zoba, shiko bansan mi yakeyiba, dan nakasa kallonsa koda ta mirror ne, abinda ya faru a wajen da

wanda nayi keta dawomin a rai, sai naga kamar na zaƙe da yawa, ko a gidan uwarwama na samo ƙwarin gwiwar zuba masifar irin haka?’.
       Sai da gimba ya tada mota sannan yace, “Boss zamu koma station ne?”.
    Shiru bai bashi amsaba har muka fice daga gate ɗin wajen muka hau titi, ni nama ɗauka ko barci yakeyi, sai jinai ya bashi amsa da,
      “A.Y....”
Ban fahimci ma'anar maganarba, amma shi gimban naga kamar ya gane mi yace. Wayata daketa vibration tun ɗazun na kalla, yah Qaseem ne yanzuma, wannan shine kira na kusan bakwai kenan, tun muna cikin wajen cin abinci kiransa keta shigowa, sai dai bansan miyasa nakasa ɗagawa ba, a hankali na sauke ajiyar zuciya jin wayar ta yanke, kasheta nai baki ɗaya ma, dan bansan dalilin kiranba, idan kuma na ɗaga bansan mizance masaba, bankuma saniba ko ɗagawar zai iya zama laifi a wajen wanda muke tare. Isowarmu wani gida mai ƙyau da tsarine ya yanke tunanina, tunda aka buɗe mana gate muka shigo naketa bama idona abinci nidai, gimba ya tsaida mota ya buɗe ya fita, ni dai banyi yunƙurin fitarba harshi aka buɗe masa ya fice, akan idona yabar wajen ya nufi wata ƙofa mai alamar shiga ainahin cikin gidan, na sauke ajiyar zuciya kaɗan ina lumshe ido, fatana yazam shikenan yace a maidani station.........
       Kallon gimba dake bani umarnin shiga nai da sauri, yay murmushi yana sake maimaitamin, “Ki shiga inji boss”.
      Jinai tamkar na fasa ihu, amma bani da ikon cewa ba hakaba, dole na fito ina sake bin harabar gidan da kallo, gimba ne yaymin jagora har ciki, ‘Masha ALLAH’ na faɗa akan laɓɓana saboda haɗuwar da falon yayi, babu kowa a ciki sai ƙamshi mai daɗi dake tashi a cikinsa....
     Gimba yace, “Ki shiga nan saiki gyara jikinki”.
    Murmushi naɗan masa ina jinjina kaina, na nufi ƙofar raina cike da tsoro da mamaki, sai faman tambayar kaina nake ko ina matar gidan? Dan naji gidan tsit. ‘Kika sani ko tare suka shige ciki?’ zuciyata ta ayyana min haka, bakina naɗan taɓe, na tura ƙofar na shiga da sallama. Ɗakine babba, akwai komai na amfani kuma a ciki, sai dana gama ƙare masa kallo kafin na nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton bayine, bayan na rufe ƙofar sai kuma nai tsaye ina ƙarema kaina kallo ta cikin madubin dake toilet ɗin, Toni ta inama zan farane? Ni bawasu kayane dani ba, gashi kayana sun ɓaci sosai, na zare rigar saman da ya bani, wadda kasancewarta fara ta ɓaci sosai, hakama wandona, amma da yake baƙine shi ba gani akeba, sai ƙamshin miya da yake da mai dakemin naso a jikine zaisa ka gane ya ɓaci shima sosai, shawarar cirewa na wanke nayi, dan haka na cireshi a ɗarare.
       Ban fahimci kuskurena na jiƙa wandonba sai dana gama wankesa nanfa tunanin inda zanje na shanya, da kuma ta yanda zanma fita shanyawar tunda bawasu kayanne daniba yazomin. jinai hawaye sun cika idona, ‘Ni balki naga takaina’ na faɗa a hankali ina haɗiye kukan dake neman zuwamin. A bayin na shanya wandon na fito ɗaure da sabon tawul dana gani, na zauna a bakin gadon na rabga tagumi ina addu'ar neman mafita.
     Nai firgigit jin an turo ƙofar kamar a fusace, fuskarta a haɗe ta shigo hannunta ɗauke da leda yellow mai tambarin M&N, cike da kallon tsana ta miƙamin ledar, amsa nai nidai cikin girmamawa amma ina mamakin yanda takemin a ƙasan raina. Juyawa tai zata fice na bita da kallo, sai da ta buɗe ƙofar sannan tace, “Ana jiranki” kawai ta fice abinta.
     Numfashi na sauke a hankali, na buɗe ledar na fidda kayan ciki, wandone da riga duk baƙaƙe, sai baby hijjab fari irin waɗanda nake sakawa, tashi nai na saka kayan, sunmin bala'in ƙyau, sai dai inajin kunyar fita a haka sosai, dan sun wani lafe a jikina dukda dai rigar bata matseniba, bani da zaɓin daya wuce daurewa na fita a hakan kawai, danma baby hijjab ɗin ya rufemin ƙirji, na maida kayan dana cire a jikina cikin ledar harda wandon dana jiƙa ɗin, kaina a ƙasa na fito daga ɗakin, zuciiyata sai harbawa take da sauri-sauri.
           Wani iri naji a raina ganin kusan su biyar ne a falon, sai na kumajina a matuƙar takure musamman saboda kayan dake jikina, ƙarasawa nai cike da aro jarumtar dole ganin su hankalinsuma ba'a kaina yakeba, sallama nai duk su

ka amsa mani, na gaishesu da girmamawa nanma suka amsa, na kula kamar kallon mamaki sukemin irin kamar basuyi tunanina ganina a wajenba, hakan sai ya sakani jin wani iri, na saci kallon dodon nawa, dan tunda na fito baiko ɗaga kai ya kalli sashen da nakeba, yana zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani basarake, idonsa na bisa takardun dake hannunsa, shima ya canja kayansa zuwa farin wando da baƙar t-shirt mai gajeren hannu, rigar ta kwanta masa a jiki, hakan yasa ta fidda ainahinsa na ƙaƙƙarfan mutum.......
       “Bismillah zauna mana”
Oga Hafiz ya katse min satar kallon boss dana shagala yi, kaina na jinjina na zauna a inda ya nunamin ɗin a ɗarare.

      Tun fitowar Bilkisu a idanun Jawaad ne, duk kuma abinda take yana kallonta ta gefen ido, amma babu wanda zai iya fahinta, idan akai dubi da yanda ya maida dukkan hankalinsa ga takardar hannunsa, ɗago idanunsa yay yana kallon Aliyu dake danna lap-top, yace, “Aliy ya buɗe ne?”.
      Girgiza kai Aliyun yayi yana guntun tsaki, ya juya masa fuskar lap-top ɗin da faɗin, “Ni banama zaton yana amfani da accaunt ɗinnan gaskiya, boss wai mizai hana mu aika wani cikinsu kawai, sai naga haka kamar zaifi komai sauƙi da muzauna a bayan fage muna wahal da kanmu, tunda bamu da tabbacin yarinyar zata bamu haɗun kai”.
    Kafin Jawaad ya bashi amsa Rose dake gefensa tanata wani cika da batsewa tai caraf ta

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment