Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koda bawa na gidan yanda suke soba, tsaye take kan tarbiyyarsu daga ita har mai martaba da Mommah. Safah sai ta kwantar da kai cike da shagwaɓa tana lallaɓa jakadiya, harda bata ƙyautar dubu biyar. Baki Jakadiya ta washe, tace, “A uwar masu gida ai dolene nai miki iso, ammafa inhar basa falon farko to saidai kiyi haƙuri anjima saiki dawo.
      Safah tace, “Na yarda, amma dai ba falon farko kawai ba, dan ALLAH harna biyu, dan kinsan inhar Ummu na tare da Abbu bazasu zauna a falon farko ba, nikuma maganace mai muhimmanci zanma Ummu”. Rigimar Safah da Jakadiya ta sani yasa ta amince zataje har falo na biyun. Safah na nan tsaye a ƙofar ƙatafaren falon mai-martaba Jakadiya ta shiga domin mata iso. Iyakarta falon farko tai kira ta wayar landline kamar yanda tsarin Sarki Sameer yake. Munaya ce dake masa tausa ta ɗaga, cike da girmamawa Jakadiya ta isar da saƙon Safah. Daga can Munaya zata fara faɗa akan Safah ta jirata saita fito Sarki Sameer yaymata nuni data bari Safah'n tazo, badan tasoba tabi umarninsa.
        Cike da ɗoki Safah ta shiga kamar yanda Jakadiya ta sanar mata anbata izini, tun daga falon farko har zuwa na uku bata iske kowaba, hakan yasata wucewa ƙaramin falon da bakowa keda lasisin shigarsaba saisu da iyayensu. Tai sallama a bakin ƙofa suka amsa mata kafin a bata izinin shiga. Sarki Sameer na kishingiɗe a ƙasan lallausar daddumar da

aka ƙawata falon da ita, ya zubama ɗiyar tasa da bazata gaza shekaru sha uku ba ido yana murmushi, itama murmushi take masa tana satar kallon Ummu dake zuba mata harara ta gefen ido. Ganin tayi tsaye taƙi ƙarasowa garesu mai-martaba yakai dubansa ga gimbiya Munaya, hannu yakai yanda Safah bazata ganiba ya Mintsineta, gimbiya Munaya ta ɓata fuska irin taji zafinnan, gira ɗaya ya ɗaga mata yana murmushi da cewar, “Kin tsaremin yarinya da ido takasa ƙarasowa, Ummuna kinga zo naji mike tafe dake?”. Da sanɗa Safah ta raɓa gefe taje ga mai-martaba daya tashi zaune sosai, hannunta ya kamo ya zaunar da ita kusa dashi. Safah akwai shagwaɓa da ƙulafucin iyaye, gashi tsiwarta data gada ga Munaya yasa Sarki Sameer ke tsananin sonta sosai, danshi idan tana abu Munaya kawai yake gani a zamanin ƙurciya. A jikinsa ta lafe tana kumbura fuska, cikin raɗa tace, “Abbu dan ALLAH kacema Ummu tabar hararata ni tsoron idanunta nakeyi, kumafa abu mai muhimmanci zan faɗa”. Murmushi mai-martaba yayi, ya maida dubansa ga Ummu data tsume fuska. “Ummu Please kiɗan saki fuska mana, kinga dai tsoron idanunki mukeji”. Yanda yay maganar cikin marairaice fuska ya sakata yin murmushi ta ɗauke kanta daga garesu.
      Safah ta gyara zama ganin Ummu tabar harararta tace, “Abbu kasan miya faru a inda mukaje kuwa?”. “Saikin faɗa Ummuna”. duk abinda suka iske na rikici a gidansu Bilkisu shi Safah ta zauna tsaf ta zayyanema mai-martaba da Ummu, sosai abin ya basu mamaki, sai dai basuce komai akan batunba Ummu tace, “Tunda kin gama faɗa tashi kije idan na fito zanyi magana dasu Amaturrahman”. Sosai Safah ta kumbura harda hawaye, tace, “Abbu kajifa ni bandani za'ayi maganar bayan aunty nace”. Murmushi takawa yay yana mai girgiza kansa, ya shafa kanta yana faɗin, “Ai dolenema ayi magana da magajiyar Ummu, bayan ma kece kika kawo zancen”. Cikin ɗoki tace, “Yauwa Abbunmu shiyyasa nake sonka, bara naje na faɗama Mommah itama”. Kafin wani cikinsu yay magana ta fice da gudunta.
      Ummu tace, “ALLAH dai ya shiryeki Safah, nikam bansan irinkiba”. Murmushi takawa yay tare da ɗora kansa saman cinyarta, yakai hannu ya shafi kumatunta yana mai lumshe idanu, “Dukfa rawan kan Safah a wajenki ta gada, kinsan kawai dai shi ɗan gado idan ya gaji abu saiya zarta mai shine”. Murmushi gimbiya Munaya tayi itama tana shafa kansa, tace, “Kaikuma gashi baka mantuwa yallaɓai”. Sosai ya buɗe idanunsa a kanta yana mata wani sassanyan kallo, cije lips ɗinsa da yay tare dayin ƙasa-ƙasa da murya kamar mai tsoron ajisu yace, “Yallaɓiya ai Sameer bai cancanci mantawa da ƙuruciyarki ba, kin bani wahalafa da yawa madam”. “Kamar yanda nima ka baniba”. Dariya sukayi a tare. Saida suka tsagaita takawa ya tashi zaune sosai idanunsa akan gimbiyar tashi. Yace, “Ban fahimci zancen Safah ba, mike faruwane?”. Cikin nutsuwa gimbiya munaya ta zayyane masa komai akan farkon haɗuwar Bilkisu dasu Safah ɗin a wajen Saloon ɗinta, har tafiyarsu yau domin kaimata l'd cards ɗin da Safah ta zama sanadin ɗakkosu. Shiru baice komaiba tsahon wasu mintuna, itama Ummu bata sake cewa komaiba. Harma ta sakin zancen sai y jeho mata tambaya akai “Toke yanzu mi kika fahimta a zancen nata kenan?”. “Eh to inason nasamu ƙarin bayani wajensu Amaturrahman ne, daga nan sainaga idan maganar nada muhimmancin da zamu shiga ciki, dan na lura a zancen Safah kamar ita yarinyar ba ƴar gidan bace”. Kansa ya jinjina mata kawai, daga nan suka saki zancen suka cigaba da hirarsu.

_________________________________

             
                Kai tsaye asibiti Jawaad ya nufa, Ummie ta wuce gida tun ɗazun bayan zuwansu Batool da Jawaad ya kira Ummah babba ɗazun yace taje asibiti ta kwana a can wajen Bilkisun, babu musu batool ta amsa sukazo tare dasu Ummah suka duba Shahudah da bilkisu, su su Ummah sai suka koma gida akabar batool din anan, da Nabeelah ma ta tubure nan zata kwana tana ta hawaye ganin halin da Bilkisu ke ciki, harda rantsuwar saita rama mata, saida ummah ta lallabata saboda sunyi yawa, kuma Jawaad tunda ba ita yaceba idan yazo ya sameta tasan kaniyarta zaici ne..
      Batool na zaune suna ɗan hira itada maman Amina aka

n abinda ya faru yay knocking ƙofar, a zatonsu Doctor ne ya dawo. Ganin Jawaad ya saka Batool mamaki, dan cayayma Umma sai da safe zai dawo daga inda yaje, zatai magana yay saurin saka yatsansa saman baki alamar tai shiru, shirun kuwa tayi. Ya gaida Maman Amina cikin girmamawa dan dama sunsan juna tun lokacin da take aiki gidansu Shahudah kafin ta barma Amina saboda matsalar ciwon ƙafa data isheta.  Takawa yay zuwa gaban gadon da Bilkisu ke kwance dama tunda ya shigo idanunsa a kanta yake, baya ganin fuskarta saboda ta juyama ƙofar baya. Cikin dabara maman Amina ta fita daga ɗakin.
         Ta inda bily ta juya fuska Jay ya zagaya, tsaye kawai yay ya zuba mata manyan idanunsa da sukai jazur da ɓacin rai, tsawon mintuna uku kafin ya kalli Batool dake tsaye itama tana kallon bilyn. Cikin ɗacin murya yace, “Waye yay mata wannan dukan?”. Itama Batool muryarta da alamun baƙin ciki ta bashi amsa da cewar, “Su Aamilah ne akace, inason dan ALLAH kaci uban yarannan Brother, saboda wannan abin da sukai tsabar cin zaline ai da hauka, yaran gidannan naku sam tarbiyya bata ishesuba na lura, mtsoww!”.
    Baice da Batool komaiba, sai dai yanda fuskarsa ta ƙara tsukewa zakasan lallai ran ƴan maza sun ɓaci, tsahonsa ya rage tare da ranƙwafowa akan bily da duk batasan anaiba, yakai hannun damarsa a hankali gefen kumatunta da yafi ko ina kumbura, motsawa tai tare da yatsine fuska alamar taji zafin taɓawar da yay ɗin, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana mai janye hannunnasa. Tsaye ya miƙe idonsa har yanzu akan Bilkisun yace, “Mi Doctor yace yanzun?”. “Sunyi magana da Ummah, bansan miyace mataba gaskiya”. Bai sake cewa komaiba ya cigaba da kallon Bilkisu na tsahon lokaci, kafin ya sauke numfashi da zare hannunsa ɗaya daga aljihun wandonsa ya ɗauki file ɗin daya gani a drawer gefen gadon, saida yagama dube-dubensa sannan ya ajiye yay ficewarsa batare da yacema Batool komaiba. Itama da kallo kawai ta bisa, haka kawai yau takejin matsanancin tausayin ɗan uwan nata da ya kasance shi ɗaya tilo, babu wa babu ƙani, babu iyaye baki ɗaya sai dangi.

          Magana yaje sukai da Doctor, ko kallon ɗakin da aka kwantar da Shahudah baiyiba yay ficewarsa daga asibitin, daga nan gidan Alhaji baba ya nufa.
         Kiraye-kirayen sallar isha'i da akeyine ya sakashi shiga massallaci, saida aka idar ya shiga gidan. Shima Alhaji baban shigowarsa kenan babu jimawa, Jawaad ya zauna ya gaishesa, amsawa Alhaji baba yay idonsa akan jikam nasa. fuskar Alhaji a ɗaure baba yace, “Daga ina?”. Batare da Jawaad ya kallesaba yace, “Gida”. “Ɗazun kumafa da akaita nemanka a wajen ɗaurin aure?”.  “Aiki naje”. Alhaji baba yace, “Humm aiki? Kenan bakasan miya faru a wajen ɗaurin aureba ma?”. Kan Jawaad a ƙasa dan yaƙi yarda su haɗa ido da kakan nasa yace, “Na sani, ninema na canja list ɗin ai”. Idanu Alhaji baba ya ɗago daga littafin addu'oin dake hannunsa ya kafe Jawaad ɗin da kallo, cikin sake ɗaure fuska yace, “Ai nasan bazai wuce kaiɗinbane daman, miyasa kai hakan?”. Kallonsa Jawaad ya ɗago yayi sai kuma ya ɗauke kansa yana wani ɓata fuska, dama yasan ko kowa bai gano shi bane da wuri Alhaji baba sai ya gane.
      Alhaji baba yay ƙwafa yana maida kansa ga littafin da faɗin,  “A hatsabibancinka dana sani hakan ƙaramin abune a gareka Jawaad, amma ince tun randa mukaje gidan Alhaji Ali akan maganarnan ya tabbatar mana da ɗansa zai aurama yarinyarnan kace ka haƙura?”. “Hakane baba, kamar yanda na faɗa a gabanku na haƙura na barmasa da gasken na haƙuran, sai dai kuma dalilin daya biyo bayane yasa na canja shawara”. Ran Alhaji baba ya fara ɓaci, dan haka cikin zafi yace, “Kasan zan iya saɓa maka ko Muhammad? Har wane irin banzan dalili ka riƙe da  bazakazo ka sanar minba kafin ka yanke masa hukunci? Banason wannan shegen taurin kan nakafa kaima ka sani”. Sosai idanun Jawaad suka sake kaɗawa sukai jajur, jijiyar kansa dukta fito ruɗu-ruɗu, yasan duk sanda zaiyi abu saiya zo ya sanarma Alhaji baba, dan a halin yanzu shine kawai ke iya nuna masa ɓacin rai idan ya aikata ba dai-daiba kuma ya tsawatar masa akan ya kiyaye gaba, to amma akan wannan shi kansa baisan miyasa zuciyar

sa taƙi aminta da ya nema sharar kowaba akan batun har sai bayan ya aiwatar..........
         “Ina maka magana ka tafi tunani”. Jawaad da maganar Alhaji baba ta maido hayyacinsa yay ajiyar zuciya, cikin sanyin murya yace, “Nayi laifi kayi haƙuri, amma zuwa nan gaba kaɗan zaka fahimci hakan danai shine dai-dai baba......”
        “Dai-dai ɗin ƙaniyarka, ka sakar musu yarinya ta auri wanda suka zaɓa mata, shikuma wancan habibun halan shima kaine ka kawosu shi da Azeemar? Tunda kasan har cikin ranka bakason maida yarinyarnan miyasa ka amincemin zaka maidatan?”.
         “Baba nifa bani na kawosuba, su Uncle Nasir pretending kawai suke akan maganar suma, dan sunsan wacece Azeema, tunda da saninsu aka  ƙulla aurama shi Qaseem ɗin ita, sannan sakin yarinyar zai zama babban kuskurene, akwai wani abu da suke ɓoyewa akan yarinyar, ka bani damar bincikosa sanan, na yarda inhar nine banda gaskiya ka ɗauki kowane hukunci”. Shiru Alhaji baba yay yana kallon Jawaad da nazarin kalamansa a ƙwaƙwalwa, kusan mintuna biyu suna a haka shiru kafin Alhaji baba ya ɗauke kansa daga kallon Jawaad ɗin ya maida ga littafinsa, “Ka dainamin ɓoye-ɓoye, ka fito fili kasanar min abinda ke faruwa?”. Ajiyar zuciya Jay ya sauke da faɗin, “Duk abinda zan faɗa a yanzun zai iya zama kuskuren abinda yake a zahirin gaskiya ne, nima a yanzu bakomai na saniba baba, sai dai insha ALLAH zan binciko duk abinda yake a binne nanda ƙanƙanin lokaci insha ALLAHU”. Tsagwaron gaskiya Alhaji baba ya hango a kalaman Jawaad, hakan yasa bai sake cewa komaiba.
          Miƙewa Jay yay ya nufi bedroom ɗin kakan nasa yay kwanciyarsa.
         Alhaji baba ya bisa da kallo har saida ya shige, tabbas ya fahimci akwai abinda Jawaad ke ɓoyewa, kuma da alama yanada alaƙa da Uncles ɗin nasa, bazai matsa masaba akan sai yaji komai a yau, dan yasan idan yana fushi takura masa akan abu sake busar masa da zuciya yake, sai dai yasan duk abinda Jawaad ya dage a kansa to lallai akwai abinda ya hango a cikinsa, shi kansa akwai mafarkan da yake a kwanakinnan suna damunsa, ya kuma rasa ina suka dosa?, abin mamakin shine kullum mafarkin maimaita kansa yakeyi, kayi mafarki sau ɗaya sannan ka sake maimaitashi gobe, har tsahon wasu kwanani dolene kasaka masa alamar tambaya koda kaso tureshi a ranka. Tsahon lokaci yana zaune a falon yana tunani bai shiga ɗakinba sai kusan sha ɗaya, lokacin tuni Jawaad yay barcima shi. Shirin barcin yay shima ya hau gadon, idanu ya tairama Jawaad dake barci fuska a ɗaure alamun cikin ɓacin rai yay barcin, Alhaji baba ya sauke numfashi tare da shafa kan jikan nasa, a ƙasan ransa yanajin tausayinsa, gefe kuma yana jin matuƙar tsoron irin hatsabibancin Jawaad da rashin tsoro, yana tsoron kar wani yay amfani da wannan halayyar tasa ya cutar dashi wataran. Da waɗanan tunane-tunanen fal ransa yay barci shima.

★★★★★★

          Bayan tafiyar Jawaad Maman Amina ta dawo ɗakin, macece ita mai yawan ibada dama, bata wasa da ibada ko kaɗan, dan haka koda ta dawo saita ɗauro alwala takoma gefen bilkisu ta zauna a kujera dan ganin wata irin zufa da Bilkisu keyi mara dalili, gashi sai mutsu-mutsu take kamar wadda aka saka cikin wuta, Batool kuwa tana gadon mara lafiya ɗaya daya rage a ɗakin tai kwanciyarta itama. Addu'oi maman Amina taita tofama bilkisu dan zufar ta bata mamaki da tsoro, gashi akwai fanka a ɗakin tana aiki kuma, bakuma wani uban zafi akeba a garin balle ace, da alama dai mafarki Bilkisun keyi. Ahankali-ahankali gumin ya fara tsanewa daga goshin bilkisu, ta koma sauke numfashi ahankali saɓanin da datake yinsa da sauri-sauri, takuma nutsu waje ɗaya. Tajima tana mata addu'ar har kusan ƙarfe ɗaya kafin ta miƙe ta shimfiɗa abin salla ta fara nafilfilinta data saba a zaune saboda ƙafarta bata jimirin tsaiwa.
        Wani irin sukur-sukur maman Amina keji a ɗakin, tun tana ɗaukar motse-motsen da takejin a wasa hartakai ta fara waige-waige, tabbas tanaji a ranta akwai wani abu a ɗakin da itama bata iya hasasowa ba, tashi tai ta ɗakko jikkarta datazo asibitin da ita ta ciro Qur'anin da tazo da shi, karatu ta fara cikin suratul baƙara, sai motsin da takeji ya ƙara ƙarfi, ɗa

ga kan da zatai sai idanunta yaci karo da wata irin halitta mai kama da ƙadangare yana fitowa daga ƙarƙashin gadon da bilkisu ke kwance, sai dai kuma shi wannan farine fat tamkar babu jini jikinsa, sannan ƙaton gaske kamar kada ta cikin ruwa, jikinsa sai wata iriyar muguwar walƙiya yake tamkar ruwan dake kwance cikin teku, dukda zuciyarta ta girgiza da kallon wannan halitta mai ban tsoro dake nufota sai bakinta bai daina karanto ayoyin alƙur'anin ba kasancewarta jaruma mai dakakkiyar zuciya, tsayawa yay cak a tsakkiyar ɗakin batare da ya ƙaraso gareta ba, ya shiga goga kansa a ƙasan ɗakin kamar wanda ake duka, kafin kuma ya juya bindinsa har gab da ita ya fuskanci ƙofar fita, da gudu ya fice tamkar an masa umarni. Cigaba tai da karatunta har lokacin ta gaza ɗauke idanunta daga ƙofar. Sam Batool batasan wainar da ake toyawaba, barci take kashirɓan, bily ce dai bazamuce ga halin da take cikiba. Sautin karatun alkur'anin da Mmn Amina keyine ya tada Batool, itama samun kanta tai da shiga bayi tayo alwala, ta idar kenan ta miƙe tana gyara ɗan kwalinta zata fito taga wani ƙaton maciji jajur dashi yana silalawa ta Window toilet ɗin zai fita, ƙara ta ƙwalla tare da fitowa a guje jikinta na masifar rawa. Tazo ta ƙanƙame maman Amina dake cigaba da karatu dukda hankalinta yayi masifar tashi da ƙarar Batool ɗin, tanaji a ranta itama wani gamon tai a bayin................✍

Sannu sannu bata hana zuwa saidai a daɗe ba'a zoba. to aljanin daya canja takarda ya bayyana😂, sai muje zuwa domin jin dalilin Jawaad na canjawar da kuma tayaya ya canja ɗin, da alama kuma ya fara bankaɗo wani sirrine da zai bamu hasken sanin ina muka dosa🚴🏼. ALLAH ya daidaita sahun Jawaad akan lokaci😂, bara na fece nidai kafin ya karyani🚴🏼🚴🏼🚴🏼.

Barkanmu da dawowa, ina fatan kunsha weekend lafiya?.


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/9/2020, 4:09 PM] HASNA✍🏻: Rasheeda Usman:
Page 24

Godiya ta musamman ga UMMINRASHIDA CARE FOUNDATION, saƙo ya iso gareni, ina muku fatan  alkairin nima, tare da godiyan bangirma da jinjina, alkairin ALLAH yakai gareku aduk inda kuke. Nagode da wannan girmamawa taku a gareni, duk da har yazu dai bilyn Abdull rarrafe takeyi, Inai muku so irin trillions ɗinnan😍😍😘😘👍🏻

................Jin Alhaji baba ya fara sauke numfashi Jawaad ya buɗe idanu a hankali, juyi yay domin ya tabbatar barcin baba yay nisa tamkar a cikin barci yake, shiru baiji Alhaji baba ya motsaba, yay murmushi tare da sauka daga gadon a hankali, cikin sanɗa ya fito daga bedroom ɗin, a falonma yanayi yana waiwaye harya fice, gudun matsala yasa yabar motarsa anan ya fice daga gidan baki ɗaya, wayarsa ya ciro a aljihu ya duba time, sha biyu saura kwata, ya maida wayar a aljihu yana furzar da iska. Daga gidan zuwa titi babu nisa sosai, hakan yasa ya taka da ƙafa ya samu napep. Saida suka fara tafiya ya sake fiddo wayarsa ya duba saƙon su Jabeer daya shigo tun ɗazun, ɗan typing yayi kaɗan ya tura musu cewar gashinan a hanya.
        Cikin mintuna kaɗan suka iso gidansa na A.Y, sai dai bai bari sun ƙarasa gidanba ya sauka, dubu guda ya miƙama mai napep, yana ya tsaya ga canji amma Jawaad bai saurareshiba yay wucewarsa. Mai napep ya cusa kuɗinsa a aljihu yana faɗin “gaba ta kaini inma bakasan ka baniba”.
        Oho Jawaad baisan yanaiba, tunima ya shige gidan. A falo ya iske su Aliyu, kowa da hidimar da yakeyi,  ya zauna cikin kujera yana faɗin, “Kuyi haƙuri na rikeku anan ga madams suna jiranku a gida”. Hafiz dake aiki a lap-top yace, “Babu damuwa ango, yanzu dai mike faruwa?”.
         Ajiyar zuciya Jawaad ya sauke yana faɗin, “Akan abinda ya farune yau, nasan kuma duk a ƙage kuke da sonjin yadda akayi?”.
       Hakane boss. Suka faɗa a tare idanunsu na akansa.
         Bayansa ya jingina da kujera yana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, cikin ɗacin murya yace, “Kamar yanda nasan tunaniku na akan nine na canja komai hakane, nayi ne saboda labari dana samu daga majiya mai ƙarfi akan abinda Momy ta ƙulla ita dasu mama Atika. A zahiri sun tsaida bikin Qaseem ne da yarinyarnan Miemaa, sai dai  a baɗini sun tanadarma Qaseem mata batare dashi kansa ya saniba. Azeemar da aka ɗaura aurensa dashi ɗiyace ga Gwaggo Hajarah ƙanwar Momy da suke ɗaki ɗaya”.
      Sosai mamaki ya cika zukatan su Jabeer, Hafiz yace, “To amma miyasa sukai hakan?”.
        “Wannan itace amsar da nakeson mu nemo nima Hafiz, har yanzu mamaki baibar ɗawainiya da zuciyataba akan wannan al'amarin, miyasa zasu aurama Qaseem Azeema bayan sunsan ga wadda yace yanaso?”. Jabeer yace, “Nidai a nawa ganin kamar dama basason aurensa da Mami ne, sunsan kuma kosun hanashi bazai hanuba, shine suka zaɓi bi ta bayan fage su haɗa masa guda biyu, zaɓinsu da kuma nashi zaɓin”.  Hafiz yace, “Maganarka akwai ƙamshin gaskiya Jabeer, to amma idan hakane shi Habib ɗinan miya kawosa cikin wannan al'amarin, sannan wanene shiɗin kuma?”.
        Aliyu datun ɗazun baice komaiba yay ƙwafa, “Ni wlhy kusan kawai minake saƙawa a wannan lamarin kuwa; Duk kallonsa sukayi suna jiran ƙarin bayani. ya cigaba da faɗin, “Inagafa su sun tsara al'amarinne akan boss ya auri Shahudah, Qaseem a bashi Azeema, ita kuma Mami su aura mata Habib ɗin, inhar ba hakanne tsarinsuba miya kawo shi habib ɗin a zancen tunda alama ta nuna babu matarsa a cikin list ɗin ɗaurin auren?”. Zaune sosai Jawaad ya tashi idanunsa akan Aliyu, yace, “Aliy wannan maganar taka haka take, abinda yake cin raina anan inhar hakanne to kenan shi Dad bai fahimci Mom batason aure Miemaa da Qaseem ba kenan? Kokuwa shima ta shirya cin dunduniyarsa ne? Tunda ɗiyar ƴar uwarsa ce”. Hafiz yace, “To nima dai abin yasani wannan hasashen, amma kuma idan mukai dubi da yanda ya tada hankalinsa bayan faruwar abun harda suma hakan na nufin baisan su Momyn Shahudah sun shirya hakanba?”.
     Shiru duk sukai suna nazarin maganar Hafiz ɗin, Jawaad ya miƙe tsaye hanayensa duka cikin aljihun wandonsa, kallo ɗaya zakai masa ka fahimci ransa a ɓace yake, yace, “Basu  kaɗai suka shiryaba, hardasu Uncle Nasir, abinda yasa abin ya tsayamin

arai shine, miyasa shi Uncle Nasir zai zama munafuki a tsakaninmu? Shinefa ya jagorancemu wajen Dad ni da Alhaji baba akan maganar Miemaa ɗin, saboda Ummah ta matsa akan sai dai Alhaji baba ya nemamin aurenta tare da Hudah kodan hakan ya zama gargaɗi gareta, kenan yasan shirinsu da Momy, amma kuma ya amsama Alhaji baba cewar muje muyima Dad ɗin maganar a haɗamin auren Miemaa da Hudah? Sannan sarai yasan Qaseem an tsaida masa ranar aure da Miemaa! ɗin kuma?”.
         “To tabbas kam wannan matsalar daga nan take boss, Uncle Nasir yasan komai, amma kam bai ƙyautaba, dan nikam ina bala'in ganin girmansa wlhy saboda yanda ya riƙeka, ashe ba har zuciya bane, wannan wane irin zumincine muke fama dashi a wannan zamanin?, kaga yanda aka cukurkuɗe abu saboda kawai buƙatun wasu dason faranta musu, kuma duk idan kaje ka dawo zaka fahimci ita Mami itace akai shirin sakawa a tsaka mai wuya, miyasa sukaso mata wannan mugun ƙullin to?”.
        Duk hankalinsu suka maida ga Jawaad da yay shiru yana nazarin kalaman Jabeer na ƙarshe akan uncle Nasir da maganar ƙullin da akaso yima Bilkisu. Cikin son maidosa hankalinsa Hafiz ya zunguresa, kallonsa yay. Hafiz yace, “Mi muke ciki yanzun? Dan ko game da Mami muna buƙatar bincike mugano gaskiyar maganar Jabeer, mizaisa suyi shirin cutar da ita?”.
         Guntun Murmushi kawai Jawaad yay ya koma cikin kujera ya zana,  kwantar da bayansa a kujeran yana mai lumshe idanunsa, a hankali ya furta, “Wannan shine dalilin zamanmu anan, dan inaji a raina wannan ƙiyayyar da sukaso nuna mata tawuce naƙin son aurenta da Qaseem kawai, akwai wani abu da bamu saniba, dan haka inason sanin anahinma alaƙarta da mutanen gidan”.
         Jabeer ya ajiye cokali yana faɗin, “Kamar ta taɓa gayamin Dad yayan mahaifiyartane ubansu ɗaya, kaga kuwa bazai wuce Momy ta ƙitaba akan ƴan ubancin dake tsakanin Dad da mamata, sai dai kuma zata iya yiwuwa ɗin akwai wani abu a ƙasa damu bamu saniba harsai mun bincika tukunna”.
          “Kai lamarinfa akwai ɗaurekai, sannan akwai lauje cikin naɗi, aganina tunda basa sonta da ɗansu su rabasu kawai basai sun zalinceta sun haɗata aure da wanda bata saniba”. Hafiz yay maganar cikin takaici.
          Aliyu yace, “Kai dai bar son zuciya Hafiz, amma harma nawa Mami take da za'a mata irin wannan muguntar? Yanzu dai boss mikace kai akan batun? Tunda dai ALLAH yasa ta fita daga tarkonsu, yanzu aikin farko dake gabanmu shine Qaseem da Shahudah, baƙaramin yaƙi zasuyi a kankaba da Mami tunda. Shin Ka sanar musu kaine ka canja sunayen ne?”.
        Jawaad da duk yake saurarensu cike da nazari yace, “Eh na sanarma Alhaji baba ɗazun, na nuna masa nine na canja, nakuma saka masa zancen Azeema ciki, na tabbatar zuwa safiya zai nema su Uncles da maganar,  mukuma sai muyi amfani da wannan damar”.
        “Amma Boss baka ganin ka ɗaure kanka da yawa? Taya za'ai ka amshi laifin kai tsaye bayan bamusan mike a ransuba game da batun?”. .
         Muryarsa cike da damuwa yace, “Jabeer hakan shine kawai hanya mai sauƙi da zamu bama koma waye ƙafa, sannan Bazaka ganeba, rikicin tsohon nan ya wuce dukkan tunaninka, gara nafito na faɗa masa gaskiyar maganar, harfa ya kafamin sharaɗin saina saki Miemaa, yanzu dai nagama da matsalarsa”.
          Dariya sukayi a tare, cike da tsokana Jabeer yace, “To tsakani da ALLAH gaskiya

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

1 year ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment