Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥




Page 59

..................Motoci na alfarma aka aika daga masarauta domin tarbo su Abbu a airport kamar yanda aka aika tarbar su Umm-Anum, sai dai su masarauta aka wuce dasu, inda acan ɗinma suka sami tarba ta musamman da mutuntawa ga mai martaba sarki Sameer Saifudden da iyalansa, harma da ƴan majalissar sarki baki ɗaya. A yanda masarautar take yau ko ba'a faɗa makaba kasan anyi manyan baƙi a cikinta, waɗanda suka isa suka bunƙasa. An baje musu abinci na alfarma na ƙasarmu masu daɗi da daɗaɗa zuciya.

         Tun kafin tafiya ɗakko su Abbu Gimbiya Munaya tasa Amaturrahman ta nema Number Jawaad, amma taƙi shiga sam, ta kira ta Bilkisu kuma ba'a ɗagaba. Hakan ya bata mamaki matuƙa, dan tasan dai ai su Jay ɗin sunsan da zuwansu Abbu, a yanda suka tsara al'amarin kuma daga tarbo su Abbu a airport zasu wuce masarauta ne harsu Umm-Anum ɗin, bayan su Abbu sunci abinci sun huta sai su ɗunguma baki ɗayansu gidan Alhaji Babba, daga can idan dare bai rufaba zasu ƙarasa family house ɗin su Jay. To amma gashi har lokaci ya shige babu Jawaad ɗin babu dalilinsa.
         
          Basu ji halin da ƙasar take ciki ba sai sai kusan isowar su Abbu da awa ɗaya da rabi sannan takawa ya samu kiran waya daga gwamna akan ya buɗe television yaga tashin hankalin da a yanzu shima aka faɗa masa game da manyan mutane da ake ganin mutuncinsu a ƙasar, babban abinda ya razana gwamna kuwa harda wasu a abokansa masu manyan muƙamai kuma a gwamnatin tasa.
             Al'ajabi daya kume sarki lokacin daya buɗe tv kasa ƙwaƙwaran motsi yayi, dan shima ɗin ai akwai waɗanda suke matuƙar gaisawar zuminci a cikinsu sosai..........

_________________
ASIBITI
____________

                  Hankalin su Mom a tashe suna jiran fitowar Dr Tayyeb daga ɗakin da aka saka Mama Badiyya kira ya shigo wayarta daga mai aikinsu. Kamar bazata ɗagaba sai kuma mita tuna oho mata ta ɗaga wayar.
         A matuƙar ruɗe Talatuwa dake kuka ta zayyane mata abinda ya faru game da zuwan wasu mutane da sukace su ƴan sandane har gida suka tafi da kuku da maigadi.
    A tsawace Mom tace, “What!! K bansan shirme da hauka kinji, ubanmi suda suke gida kullum zasu aikatama ƴan sanda harsuzo gida su kamasu?”. cikin kuka talatuwa tace, “Wlhy hajiya da gaske nakeyi, yawwa gama wannan da kikacemin shine babban yaronku nan yazo gidan”. Da mamaki Mom tace, “Waye? Kina nufin Qaseem?”.
       “E...e...eh shi hajiya, wanda hotonsa ke a falo sanye da baƙaƙen kaya tare da Alhaji”. Jikin Momy har rawa yake wajen ambaton, “Da gaske Qaseem, yaushe suka barshi ya fito to? Kinga bashi wayar muyi magana nima gani nan zuwa gidan yanzun nan”. “T..t...to hajiya, bara nakai masa”. Talatuwa ta faɗa tana ɗan gudu wajen bin bayan Qaseem dako kallon inda take baiyiba ya haye sama ɗakin Dad direct. Yana kama handle ɗin ƙofar tana ƙarasawa garesa, da rawar jikin tsoro ta miƙa masa wayar tana faɗin, “Alhaji ƙarami sannu da zuwa, gashi inji hajiya zakuyi magana”. Wani mummunan kallo daya kaɗa hanjin cikinta ya zuba mata, cikin daka tsawa yace, “Ɓacemin da gani kona halakaki wlhy”. Zabura Talatuwa tayi da gudu tabar saman, yayinda Momy kuma taji komai ta cikin wayar, ita kanta tsawar Qaseem sai da ta sakata cire wayar daga kunnenta ma.

        Bata iya cewa sauran ƴan uwanta komaiba ta nufi hanyar fita daga asibitin da hanzari, duk faman tambayarta lafiya? da sukeyi bata juyoba balle ta amsa musu harta fice. Da kanta taja motar tabar asibitin zuwa gida.
       Akan hanyar momy na nufar gida ta fahimci garin babu lafiya, dan kuwa babu abinda take gamo da shi a tituna sai matsanancin holdup. Mafi yawancin inda traffic light suke an haɗa cinkoso a wajen sosai, ga jirage masu saukar angulu da keta yawo na kaikawo a sararin samaniya, wasu ma daf da mutane suke. Ratse ta ringayi ta cikin anguwanni tamkar yanda wasu motocin taga sunayi. Da ƙyar ta samu kanta a anguwarsu, tai fakin motar a ƙofar gida batare data kasheba saboda wani bahagon ruɗani da ta sake karo da shi kuma, ƙofar gate ɗinsu a buɗe take, ga jami'an tsaro sun zagaye gidan, cikin sake shiga ruɗani ta afka cikin gidan da sassarfa tamkar zaga kifa, ananma wasu jami'an tsaron ta sake cin karo dasu a cikin gidan, talatuwa na durƙushe gefe tana kuka ita da mai bayin fulawa.
         “Kai lafiya?”. Mom ta faɗa hajijiya na neman ƙwasarta zuwa ƙasa. Wani cikin ƴan sandanne ya bata amsa da faɗin, “Hajjaju wannan gidan yana a hannun hukumane a yanzun, akwai bincike da za'azo ayi a cikinsa daga yanzu zuwa kowanne irin lokaci”. Cikin tsawa da hucin ɓacin rai, “Mom tace kuɗin ubanwa muka sata to? Muba ƴan siyasaba ba ma'aikatan gwamnati ba, amma za'a turo mana jami'an tsaron binciken almun dahana da dukiyar ƙasa?”.
        “A'a hajiya, mu ba jami'an tsaron almun dahana bane ba, jami'an tsarone na farin kaya, da kuma amincewar Sir Qaseem Ali muke anan  bisa Umarnin Sir Jawaad Abdul-aziz Yusuf”. “Qaseem! Da Jawaad kuma?”. “Hakane hajjaju” ya sake bata amsa kansa tsaye.
       Wata ashariya da momy ta manta tama iyata ta kwaso ta dire bisa ƙasa tanayin wurgi da jikkar hannunta, ta shaƙo wuyan police ɗin tana huci, a take sauran suka zagayeta da bindiga. Murmushi Munkaila yayi yana ɗaga musu hannu alamar su barta, ya kalleta fuska babu wasa zaiyi magana ta tare numfashinsa. “Kai shashasha kasan mi kake faɗa kuwa? Ina Jawaad da Qaseem ɗin suke?”. Ɗan murmushi yay mata yana zame hannunta a wuyansa ya gyara rigarsa, “Sir Qaseem yanzu ya fita, Sir Jawaad kam yana filin daga”. Sake rikicewa kanta ya nemayi, batare data nutsu wajen fahimtar inda batunsa ya dosaba ta fice a gidan tamkar wata mahaukaciya.
      Mota ta sake shiga tabar anguwar batare da tamasan kalar tunanin daya dace ace tayiba, kanta tsaye station ɗin su Jawaad ta nufa, sai dai ɗan karen holdup ɗin da take fuskanta a yanzun ya zarece na ɗazu data riska tsakanin asibiti zuwa gida............

___________________
        JAY-QAS
________________

                Koda tawagar su Jawaad suka iso cikin gari cike suka iske station ɗinsu da manyansu da ƴan jaridu, abu na farko da suka farayi shine gabatar da sallolin azhar data riskesu a can da kuma la'asar da a yanzu aketa yinta.
     Suna idar da sallar ƴan Jarida sukai musu caa aka, Jay dai bai saurari kowaba daga shi har Sir Ahmad da sauran manyansu.
        Cikin son ƙure mutane irin na ƴan jarida ɗaya a cikinsu ya juya ga masu ɗaukar rahoton gidan tvn su yana magana a harzuƙe. “To jama'a kamar yanda kukai hasashe dai hakanne ta kasance, dan kuwa munga alamar rufa-rufar da muka saba gani ga jami'an tsaronmu idan laifi ya shafi manyan ƙasa yau gashi ta tabbata, to ta yayama zasu yarda su buɗe komai wa duniya bayan daga kawunansu sai surukansu da abokan iyayensu dama iyayen nasu. Haka za'a kifemu bayan kwana biyu muji shiru, bayan kuma tarin gawarwaki da mutanen dake a cikin mawuyacin hali da aka amso a hannun waɗan nan miyagu ƙuru-ƙuru duk mun gansu. ALLAH dai ya ƙyauta, dama ba sabon abu bane irin wannan a ƙasarmu ta gado. idan kaga ana yayata mai laifi da cecekuce da tada jijiyar wuya ga jami'an tsaro to talakane ya aikatashi, amma idan su masu faɗa ajinne suka aikata sai a rufe komai ruf da sunan kare mutuncinsu ko maganar shiga kotunsu bakaji balle musan an yanke musu hukunci. To kenan mu talakawa bamu da suturar mutunci ne? shiyyasa ake ƙwance mana zannuwa a kasuwa?”.
        A take wajen ya ɗauki ƙananun maganganun sauran ƴan jaridar, kowa na ƙoƙarin ɗaukar zancen ɗan jaridar nan ya zama sinadarin zazzage tasa maganar dake cin ransa.
         Ganin abun na neman kawo hatsaniya har wasu cikin ƴan jaridar na fassara abun da rufa-rufa Jay ya dawo garesu rai a ɓace. Ɗan jaridar da yay maganar Jawaad ya kafe da kallo idanunsa na sake rinewa zuwa jajur, duk da azabar ciwo da kansa ke masa haka bai hana maida masa murtaniba cikin tsananin ɗacin murya, “Kar kai azarɓaɓi akan garin daka shigo cikinsa baƙo. Karka yankema littafi hukunci abisa bangonsa, duk sharhin da zakayi batare daka buɗe rubutun cikinsaba kuskurene kawai da son zuciya zai biyo baya. Alokacin da jami'in tsaro yake filin daga shi kaɗai yasan wane irin kwazazzabo da ƙalubalene rayuwarsa ke fuskanta, da ace yanda ku ƴan media kuka iya yayata al'amari haka kuke bama jami'an tsaro gudunmawa wajen kare fituntunun da ƙasa ke a ciki da kowama ya zauna lafiya a duniya. Idan ƙoƙarinmu na aiki da jajircewa wajen tsayawa mu tantance ke hantarar ra'ayinka akanmu, to kasani sauyi ba namu bane, kai da irinkane zaku sauya. Duk lokacin da mukejin matsayinmu ya girmama a duniya wajen jama'ar cikinta, tomu samu gazawa akan ƙoƙarinmu ta ɓangaren aikinmu ko kasantuwar ɗaukakar tamu. Daga hakanne zamuga muɗin ba komai bane wajen waɗan nan al'ummar dake ɗaga darajojinmu da girmanmu a bakunansu da muryoyinsu. Daka zama mai ƙoƙarin ruruta wutar da bakasan tushentaba, mizai hana ka ajiye aikinka ka koma gidanka ka ɗaura zani kawai, koba komai ƴaƴanka zasu samu magirkan abinci biyu, shashasha kawai”.
      Tsitt wajen. yayi tamkar ruwa yaci kowa, sai su Sir Ahmad kawai dake murmushi da bin Jay ɗin da kallo tamkar yanda suma ƴan jaridar da sauran jami'an suka rakashi da idanu harya shige.
      Jabeer ne ya matsa garesu cikin ɓacin rai shima, ya sake kallon ɗan jaridar nan da maganar Jawaad ta sakashi duƙar dakai dan yaji kunya sosai da ganin kuskurensa akan kalamansa. “Aikin jarida ba neman kuɗi bane ko shiga rigar siyasa, aikine mai daraja abin girmamawa ga maiyinsa, ita daraja da gaskiya ake samota bada son a sani ba, kai da kayi waɗan nan kalaman kayisune bisa raɗin kanka kawai ko an sakaka badan aikin jarida ya baka damar yin hakanba, kai tsaye kake anan domin neman abinci wa iyalanka dake gida cikin kwanciyar hankali, shiko wannan da kakema gugar zanar cewar akwai kawunsa da surukinsa shiyasa ake rufa-rufa, tare da nasa iyalan ya shiga cikin jejin da baida tabbacin fitowa a raye. Atunaninka akwai sadaukarwar data kai wannan girma kuwa? Ku daina zubarma aikin jarida mutunci dan aikine na masu mutunci a kowanne lungu da saƙo na duniya, sai dai kaicon irinku masu girmama fitina da riritata tai faɗin da zata buwayi wanda kuke tunanin kun tozartar harta dawo ga iyalanku kuma cikin aikin jarida, baka dace da wannan aikinba sam, ya kamata ka ajiyesa ka koma ka saka rigar siyasa, inaga kalamanka da nuna iyawarka zatafi dacewa dacan ɗin”. Yay maganar da watsa musu harara shima yabar wajen.
      Sosai jikin duk ƴan jaridar ya sake yin sanyi, masu ƙara gishiri da magi akan batun sai suka koma gyara harsunansu suna miƙa rahoto mai inganci dan an tunatar dasu abinda suka manta domin kawai neman ɗaukaka da birgewa.

          Duk jarumtar da Qaseem ke arowa yana ƙara ƙarfafa kansa da ita sai hakan ya nema gagara, kalaman Jawaad dana ɗan jaridar nan sun bala'in taɓa ruhinsa da zuciya, yabi bayan Jay hawaye na zurara saman fuskarsa batare da yayi tunanin gogewaba. A jikin ƙarfen lifter Qaseem ya iske Jawaad ya kife kansa dake tsananin sara masa, bai iya cewa dashi komaiba ya wuce zuwa office.
           Ƙamshin turaren Qaseem ɗinne ya fargar da Jay zuwansa, ya ɗago a hankali yabi bayan Qaseem dake kan lifter ɗin da kallo harya gama hayewa, harya maida kansa zai sake duƙarwa sai kuma ya zabura cikin faɗuwar gaba, haka kawai zuciyarsa ta ɗarsa masa wani abu dangane da Qaseem, yariga yasan yanda yake da zafin zuciya. Cikin zafin nama ya haye lift... ɗin shima, ganima yake bata sauri gaba ɗaya, sai faman kallon agogo yake dukda kuwa a mintuna biyu kacal take kaisu.
      Da gudu ya ƙarasa office ɗin Qaseem ɗin, yana taɓa ƙofar ya jita a rufe, hasashensa ya zama gaskiya kenan?, Qaseem ya shiga office domin aikata duk abinda ransa ya raya masa, baya yay ya daki ƙofar office ɗin da masifar ƙarfi, sai dai bata buɗeba amma ta girgiza. “Innalillahi...” ya faɗa yana bubbuga ƙofar da ƙwala kiran sunan Qaseem, sai dai ko sau ɗaya Qaseem ɗin bai amsa masaba, rikicewa Jawaad ya sakeyi, yabar wajen da gudu zuwa office ɗinsa dan ya tuna akwai key ɗin office ɗin Qaseem ɗin a wajensa wanda Sir Ahmad ya bashi ranar domin ɗaukar wasu files a ciki, da ƙyar ya iya gano keys ɗin saboda a rikice yake, yana ɗauka ya dawo da gudu.

      Jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar Qaseem daya samo bullets da ƙyar cikin office ɗin nasa ya ƙara azama wajen ɗurasu cikin bindigar yana kuka shaɓe-shaɓe  da hawaye. yana gama zuba bullets ɗin cikin bindigar  Jay na buɗe ƙofar ya shigo da gudu, saurin ɗaurawa a kansa yay da rawar jiki yana ƙoƙarin saka ɗan yatsansa saman kunamar bindigar jikinsa sai tsuma yake.
     Da matsanancin ƙaraji Jay yace, “Qaseem!!! Karkayiii!!!!!” yay maganar cikin wani irin doka mahaukacin tsalle ya dire gaban Qaseem ɗin da wawurar hannunsa  yay sama da shi harsashin da Qaseem ɗin ya harba ya samu p.o.p ɗin dake office ɗin. Yanda Jay ya riƙe haka Qaseem ma yaƙi saki, sai da suka ƙarar da harsasan duk biyar sannan Jawaad ya ɗauke fuskar Qaseem da mahaukacin mari cikin gushewar hankali.
       Wannan harbi shine ya maido hankalin su Sir Ahmad wajen, yayinda ƴan jarida da sauran mutane suka fara gudu sun zata hari aka kawo.
                “Baka da hankali ne!!!? Wace riba kake tunanin samu a kashe kanka da zakayi Qaseem? Kaifa musulmine! Taya zaka bari tunanin aƙidar yahudu da nasara har takai mizanin tasirin zama a zuciyarka irin haka? kai ƙoƙarin salwantar da rayuwarka da kanka!!! Kasan kuwa hukuncin wanda ya kashe kansa a addinin musulunci?. To sunansa KAFURI!!! kuma wlhy WUTACE zata zama sakamakonsa!!!”. Jay ya faɗa yana huci da nuna Qaseem ɗin da hannu.
        A zabure Qaseem ya hankaɗa Jawaad yay baya yana faɗin, “Bani da hankali Jawaad, wlhy da gaske na haukace, tabbas na haukace, minene amfanina idan na zauna a raye a wannan duniyar da babu komai a cikinta sai ruɗani?!!” ya finciko rigar Jay jikinsa na rawa, hawaye na zuba masa babu ƙaƙƙautawa, “Idan ka hanani kashe kaina mi kakeso nayi Jawaad? Wacce irin amsace dani da zan bama duniya akan mahaifin da nake kallo babu kamarsa a da? Matsayin suruki kawai ya taɓa amsawa a gareka amma akai maka gugar zana da halayyarsa yanzun, to inaga ni da yake mahaifina!!, da wane idanun kakeson na sake kallonsa Jawaad?! Dan ALLAH na roƙeka ka barni na kashe kaina na huta!!”....  Ya ƙare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya da ya saka jijiyoyin kan Jawaad sake mimmiƙewa shima hawayen na taruwar masa a idanu. Jawo Qaseem yay ya rungume a jikinsa suka fashe da kuka a tare.....😭

(Kai jama'a, wlhy zuminci ya wuce gaban wasa komai lalacewarsa😭😭)

        
            Dalilin go-slow da Mom ta riska a hanya yasa ta iso station ɗin a wahale cikin dogon jinkiri, da kutsa-kutsar shiga cikin ƴan jarida ta samu shiga ciki da ƙyar, inda shigar tata tai dai-dai da harbin harsasai biyar da Qaseem da Jawaad sukayi. Da wannan ruɗanin da jama'a suka shiga ta samu damar bin ayarin su Sir Ahmad zuwa office ɗin Qaseem dan ta sani, bata fahimci can su Sir Ahmad ɗin ke yunƙurin zuwaba saida taga sun isa tare da su inda itama ta dosa.
     Itace farkon shiga office ɗin, sai tai tsaye turus tana kallon Qaseem da Jawaad dake rungume da juna da dauraren kalamansu.
         “Qaseem hakan ba mafita bane ɓata ne, ba'a samun hutu da saɓon UBANGIJI bisa ganganci, ka daina irin wannan tunanin”. “Dolene nayi Jawaad, ƙo Bilkisu da tazo a ƙarshen ƙaddarar kunyarta nakeji balle kai da sauran mutane, nayi nadamar kasancewata jininsa wlhy Jawaad”.

        Da sauri Momy tazo ta fincike kafaɗar Qaseem ta matsar da shi baya daga jikin Jawaad, batare da ta tsaya ta gama fahimtar matsalarba, jin sunan bilkisu kawai da tai a bakin Qaseem ya sakata harzuƙa da fassara matsalar akan bilkisun ne komai ke faruwa ma kawai, hawaye na zirar a kumatunta tace, “Qaseem wai mi kakeyi hakane? akan tsintacciyar mage, kake wannan hanƙoron da tura mana ƴan sanda gida saboda cin zarafinmu? Akan butulu da ya wulaƙanta ƴar uwarka har kake iƙirarin mahaifinka ya shirya tarwatsaka? TSINTACCIYAR MAGE! YARINYAR DA MUKA ƊAKKO A TSAKKIYAR RANA! YARIYAR DA......”
        
            “Da haɗin bakinki kenan mijinki ke aikata komai!!” Qaseem ya faɗa cikin matsanancin fushi tamkar zai haɗiye Mom, baya tai da sauri jikinta na rawa, cikin rawar murya tace, “Qaseem anya kana cikin hankalinka kuwa? Miya samu kanka? Ko an sauya mana kai ne?”.
       “Komai ma ya sameni fiye da yanda tunaninki ke baki ke da shi. Tun bansan kaina ba ke da shi kuketa nunamin banida wani maƙiyi a duniya sama da Jawaad, Why?. Mom! Nace Why? Shiɗin baɗan ɗan uwanki bane?, shi ɗin ba mijin ƴarku bane? Miya aikata mai zafine wai a gareku da har yau ban taɓa saninsa ba ni?......”
      “Qaseem!!” Mom ta faɗa cikin tsawa tana fashewa da kuka.
        Cikin ficewar hayyaci Qaseem yace, “Eh ki kira sunana koma sau dubune, gaskiyace bazan taɓa fasa faɗaba, to idanma baki saniba yanzu zan sanar miki, idan kuma kin sani bara na maimaita miki. Ita wannan tsintsiyar magen da kike magana MIJIN naki ya tsintota daga ranar ne dan ya jefata cikin abinda yafi ranar zafi, cikin wuta yay niyyar jefa mata rayuwa saboda cimma burinsa, mahaifinane shi amma nasha zarginsa da aikata abubuwa marasa ƙyau a cikin gidan nan, amma da naso ɗaukar mataki saina gaza hakan, na tabbata dukkan ƴan aikin da akai raping a gidannan shine yay musu.....”
      Tsawa Mom ta daka ma Qaseem jikinta na matuƙar rawa, “Qaseem!! Mahaifinka zaka ƙullana sharri irin wannan saboda Jawaad da Bilkisu?”.
        Da ƙarfi Qaseem ya daki tebir ɗinsa, kayan sama suka tarwatse, ya matsa gab da Mom yana nunata da ɗan yatsa ƙirjinsa na sama da ƙasa na kumburar zuciya. Ya cigaba da faɗin, “Tun kin nuna bakisan komaiba bara na faɗa miki to, tun lokacin da akaima ƴar matarnan Amina fyaɗe a cikin gidanmu na gaskata hakan a cikin raina, domin kuwa lemon da aka ajiye ta sha lemo ne da kaf gidan nan shi kaɗaine ke shansa, hakanma yasa ba'a ajiyesa a fridge ɗin kitchen sai na falonsa kawai, ko a falon ƙasa inhar baya ƙasar kwashewa kike ki maida masa sama, to tayaya akai ranar yaje kitchen har yarinyar ta gani ta ɗauka ta sha bayan shi mai shan ma baya nan? Abu na biyu sai da na ɗauki kwalin lemon a bola naje nai bincike akan ɗan sauran cikinsa na gane magani ne mai ƙarfi aka saka a ciki kuma a ƙalla ya kai kwanaki biyar da zubawa, abu na uku na zauna nayi dogon nazari da tunani harna gano ainahin maganain da akai amfani da shi, sai kuma kwatsam na tunano na taɓa ganin maganin a wajen Dad amma a wancan lokacin sai ya gayamin na ciwon bayane dan na gansa da shine a bazata, da yake kuma ban kawo komai a rainaba sai ban amsa na karanta ba a lokacin. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al'amuransa, sai dai abin mamaki bana iya cewa komai akan dukan abinda zan gani. to bara nama faɗa miki abinda baki saniba, a dukkan tafiye-tafiyensa cikin kashi uku biyu bayinsu yake ba, idan yace yabar ƙasarnan tafiyar sati biyu to kwana huɗu ko sati guda ya keyi ya dawo, da wannan makircin nasa yake amfani wajen aikata laifi a rasa wanene keyi a gidan, Mom ya kamata kiyi tunani da hankalinki, a dukka masu aikinmu uku da akai Raping a gidanmu duk sai baƙya nan ake aikatawa, kuma da anyi washe gari ko kwana biyu dayi Dad yake dawowa.......”
       Ƙasa Mom ta zube tana kallon Jawaad dake tsaye kawai yana kallon tamkar wani gunki, tun fara maganarsu baice komaiba bai kuma motsa ba. hawayene ke kwarara a idanun Mom tamkar an buɗe fanfo.
       Qaseem ya nuna Jay da faɗin, “Kayi haƙuri Jay ka gafarceni, zan faɗi wani abu a kan matarka duk da bata a wajen nan, tunda Bilkisu tazo gidanmu ban taɓa jinta a zuciyata da sunan soyayya ba, sai dai ina sonta matsayin ƴar uwata kawai. Amma tun randa na farka a barci naga Dad tsaye kaina a cikin ɗakina naji duk duniya babu wadda nakeso sama da yarinyar nan, ga wata sha'awarta mai tsanani inaji wadda inhar zata kasance kusa dani sai naji inason taɓa mata jiki, abin mamaki duk wannan sha'awar tata da nakeji ban taɓa jin zan iya lalata mata rayuwaba, ni dai kawai burina na taɓa jikinta ko nayi kissing ɗinta na rungumeta shike nan. Da ya ke kuma yarinyace mai tarbiya ko hannunta bata yarda na taɓa sai ta nunamin ɓacin ranta. Kuma saifa ina a kusa da itane nakejin hakan, amma da zarar bama tare da juna ni mantawama nake da ita gaba ɗaya. A daren da Dad ya fara shigo mata ɗaki har aka tsoratamu da ƙara a gidannan nine na fara fitowa, ni duk zatona mai gadine wani abu ya sama, shiyyasa nai gate kai tsaye, ina isowa maigadi na buɗema Dad ƙofa ya fita a gidan....”
          Dafe kai Jawaad yayi da sauri zuciyarsa na wani irin matsanancin harbawa da sauri-sauri, duk da Dad yake zargi dama hakan bai hanashi jin maganar tai masa nauyiba a ƙwaƙwalwa da zuciya....
         “Ƙwarai kuwa Dad” Qaseem ya bama ya sake maimaitawa yana kallon Mom cikin ido, “A tunaninki mai aƙidar kar ƴan uwansa su raɓesa ne zai ɗakko budurwa kamar bilkisu ya ajeta gidansa dan ya ƙyautata mata rayuwa kawai? Aini tun washe garin da aka kawota gidannan na ganta kuma akai min bayanin zuwanta nasan akwai manufa a zuciyarsa game da ita, sai dai narasa ta wace hanya zan kuɓutar da ita? Wannan mijin naki da kike ji da gani ramin bushiyane daga shi sai ƴaƴansa, ke kuma matarsa kura ce kema daga ke sai ƴaƴanki. Bara na sake maimaita miki shine keta bibiyar rayuwar marainiyar ALLAH akan fyaɗe har cikin gidan aurenta, da yaga bazai cimma burinsa cikin sauƙiba shine ya tafka mana asirin da har nai maganar shirya aurenta duk da a zuciyata sam ba haka bane ba. A gaban duniya ya nuna cewa ya ƙyautata mata rayuwa, zai kuma aurama ɗansa jininsa ita, amma sai ya zagaye ta bayan fage shi da ɗan uwanki Uncle Nasir suka zurmaki a ciki da ɗauraki a dukkan hanyoyin da suka gama tsarawa, ke kuma kika hau saboda baƙya son aurenmu bisa naki gurɓataccen tunanin na jahilci da son zuciya. Kuka ɗakko hayar ɗan fir'auna akan ranar ɗaurin aure za'a aura mishi ita, ni kuma zaɓinku, daga baya sai ace mistake aka samu, shi kuma dama kunbiyasa akan karya sake ya saketa duk bala'in da za'ayi har sai ƙura ta lafa an kaita gidansa. sai shi Dad yaje ya cika burinsa a kanta kawai batare da kowa yasan hakanba har ke kanki. Sai dai UBANGIJI ba azzalumin sarki bane, sannan shi yana dubi da ƙyawawan zuciyoyi masu tsoronsa da biyayya a garesa, ashe Jay

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

1 year ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment