Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nai dauriyar tattaro dukkan abinda ke raina ina mai kallonsu, “Mama!”. “Na'am Bilkisu ya akai?”. Tafaɗa tana ɗago kanta ta kalleni, Ummi

e ma daina latsa wayar tai ta maido hankali kanmu. Cikin bama kaina ƙwarin gwiwa nace, “Mama dan ALLAH mi yake faruwa? Gaba ɗaya tunanina ya kulle bana fahimtar komai daga kalaman mutane wanzu daga safiyar yau har kawo yanzun?”.
      Murmushi maman Amina tayi, sai kuma ta taso zuwa inda nake ta zauna a bakin gadon, hannunta ta saka ta kamo nawa, har yanzu fuskarta da murmushi, “Bilkisu ya kamata dama kisan miya farun kodan kiyaye girman nauyin dake kanki a halin yanzun, danke ɗin matar aurece da haƙƙinta ya koma kan wani”. Banji komai dangane da kalamantaba face wani mummunan faɗuwar gaba da harbawar zuciya, ta cigaba da faɗin...................
          Wani irin mazarin rawa jikina ya shigayi hawaye na rige-rigen sakkowa akan kumatuna, cikin matuƙar rawar leɓe dana harshe nace, “Mama! Ki..k...kina nu..fin ni aka ɗaurama aure da BOSSS!!!?”. Mama tace, “Bafa bos nace mikiba, Jawaad! Nace”. “Innalillahi....” Na shiga ambata, yayinda Ummie ke ma mama ƙarin bayanin cewar Boss ɗin ai Jawaad nake nufi nima, haka muke cemasa a wajen aiki. Mama tace, “Ayyo, aiban fahimta bane ƴannan”.
        Komai nama daina fahimta, wani irin zazzafan zazzaɓi nakeji yana saukarmin, cikin lokaci ƙanƙani nafara rawar sanyi, tunani kalma ɗaya acikin abinda mama taimin bayani na kasa nutsuwar yi, ni Bilkisu Adam makaho ce aka ɗaurama aure da Boss ɗinmu, JAWAAD ABDUL-AZIZ YUSIF!!? dama na jima zuciyata na kokwanto akan rashin damuwar da bangani a tattare da Momy ba akan aurena da Yah Qaseem, miyasa Momy ta zaɓi rabani da masoyina wanda na ɗauka dukkan yardata na bashi? Bazan ɓoyeba ina ƙaunar Yah Qaseem sosai, sannan ban tsani Boss ba dan yanada nagartar da dukkan macen ƙwarai zataso mallakarsa matsayin mijin aurenta, to amma yaya zanyi da aunty Shahudah da dukkanma ahalina? Wannan kuwa bai zama cin amanaba ga Dad da halaccinsa a gareni?. ‘To ai bake kika ce a ɗaura miki aure da boss ɗinba ko’ wata zuciya ta ayyana min daga can gefe kuma wata tace, ‘Bakuma kowa zai fahimci bakida hannu a cikiba kamar yanda mama ta faɗa miki dangin Momy na ambata hatta da Yah Qaseem dayasha gargaɗinki akan mu'amularki da Boss ɗin’. Sharr na matso wasu hawaye masu zafi da suka cikan ido. A fili na furta, ‘Innata miyasa rayuwa takemin hakane? Miyasa duk yanda naso ƙoƙarin raɓar duniya saita goce mani? Tunda na rasaki keda Abba ban sake hawa dokin da yay daidai da cikar dukkan burukanaba, dana hau matakin nasara sai ƙaddara ta sake zuwa ta datse zaren da nake tafiya da ƙwarin gwiwata a kansa, kune kuka sanarmin duniya ba komai bace face wani filin gwagwarmaya na ƙwanji da zuciya, kune kuka tabbatarmin jajircewa na iya zama babban ƙawance da duniya koda duniyar bata buƙatar hakan, miyasa ni tawa jajircwwar a kullum nisantani take da tawa duniyar, shin gaggawa nake a cikin al'amarina shiyyasa nake durƙushewa kafin nakai kokuwa tawa ƙaddarar kenan kullum a curkuɗe?....”
       “Wannan ai itace tabbatarciyar nasara kuwa Bilkisu, duk ɗan adam ɗin dakeji a zuciyarsa shine kaɗai wane, shine kaɗai za'aita kira wane daga farkon ƙarni har ƙarshensa to ya tabbata akwai ganganci da tarin wauta a al'amuransa, nasarar mai nasara itace ƙalubale, kadingaji kamar baka kaiba, baka cancanci kaiwaba, bazaka ka kaiba, sai kaga watarana ka kai harma ka wuce, lokacin da wani yake ganin ya rigaka ɗauka baka da damar ƙwata babu zato saiya suɓuce masa wajen hura hanci da gadara kai ka tsinta a ƙasa amatsayin shara kaci kai nagartar da har abadan bashi da damar hangokama, wannan rubutacciyar ƙaddarace ga mafi yawan mutane marasa gata, duk wanda ake ganin bai kaiba ko bazai kaiba shike wucewa wataran bilkisu, Jawaad shine mijin da yafi cancanta da nasararki, UBANGIJI kuma yafiki sanin miyasa ya zaɓa miki shiɗin, karki damu da adawa ko tunin kinci amana, a sannu duhun da kike ganin yana binki zai yaye yazama haske, a sannu waɗanda suke ganin keɗin baki cancantaba zaki zame musu hasken da zai mamaye rayukansu, ba'a cika baki da nasara, ba'a cika baki da farawa, ba'a cika baki da iyawa, ba'a cika baki da cancanta, ba'a gadara da abinda baka da ikon dawwamar dashi a hanunka tunda kaima a wajen wa

ni aka amsa aka baka, dagaske duniya rigar aro ce bilkisu, duk taƙamarka da ita da alfahari wataran saika tuɓeta da mutunci koda ƙasƙanci, duk abinda kaga kayi a duniya koka tsinci kanka kafin kai anyi dubunka masu ninkin banikin ɗinsa, bayanka kuma wasune zasu amsa su dama ko kaƙi ko kaso. Dan haka ki godema ALLAH da ni'imar da yay miki na mallakar miji mutumin kirki da bai ɗau duniya komaiba matsayin, dukda tarin dukiya da ALLAH ya bashi tun yana ƙanƙaninsa, shiba duniyar bace a gabansa, dan da itace bazai taɓa rabuwa da ƙyaƙyƙyawa irin Shahudah ba data haɗa komai na gata da nasaba ya ɗaukeki a matsayin ƴar riƙo a gidansu, wadda suke kallo ƙasƙantacciya a cikinsu. Akwai hikima mai yawa a al'amuran UBANGIJI bilkisu da jahili baya ganinsu ta fuskar data dace kinji”.
       Kaina na gyaɗa mata a hankali, dan kalamanta sun sakani jin sanyi a raina, sai dai ina jinjina yanda zan rayu da mutum murɗaɗɗe mai wulaƙanci da ƙasaita irin Boss, aɗan zaman danai dashi na fahimci abinda ba'a sakashiba sam baya burgesa balle ya tsoma kansa. To miya kawosa cikin nawa lamarin ni kuma?.
     Wannan itace tambayar data tsayamin a rai har dare.

_______________________________

                     Zaune yake a ɗaɗɗaure, an ɗaure masa idanu da jan ƙyalle, bakinsa ma a liƙe yake, shi kansa baisan a ina yakeba, abinda kawai ya sani da zai iya tunawa shine.
       Ranar juma'ar da aka ɗaura auren su boss, lokacin da ake tsaka da wannan dambarwa ta neman sanin wanda ya rikita tsarin auren, yabi sahun masu gani da ido babu damar tofa albarkacin baki, har aka gama rikicin massallaci aka nufi gida, baiga boss ɗinsaba, dama baisa ran ganin nasanba a wannan lokacin, ganin su dad sun ɗunguma gida shima saiya hau napep domin komawa gidan ya ɗau jikkarsa ta tafiya gida weekend kamar yanda ya saba, dama sunyi sallama da boss tun a daren jiya, hakan yasa bai damu daya kirasaba koya jirasa. Shiru gidansu boss yake babu wata hayaniya, dan duk suna gidansu Shahudah, Mama Atika da mama badiyya dake fama da jiyyane kawai a gidan sai hadimai da samari waɗanda baza'a rasaba da suka dawo daga wajen ɗaurin aure. Jikkar kayansa ya ɗauka ya fito bayan sunyi sallama da baba mai gadi, cike yake da nishaɗi akan yanda auren ya kasance, Boss ya samu wadda yake masa fata tun sanda ya fara ganinsa tare da ita, yana gab da barin layin wayarsa tai ring, cirowa yay ya duba, gani mamansace yay murmushi tare da ɗagawa yana waige-waige, saida ya tabbatar babu kowa ama kusa dashi balle yay tunanin za'a jisa kafin ya fara maganarsa kai tsaye cikin zaurence kamar yanda suka sabayi. “Mamana albishirinki?”..............✍


Karku rikice, muje zuwa page 27, danjin ina aka dosa, nasan dai dayanku sun fahimci kowanene ma kafin akai ƙarshen zance😉🤫👌🏼.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu. 09032345899 sai kunzo😍😍😍😘.

Musha weekend lfy. Maybe kuma ku ganni lahadi koma gobe idan ALLAH ya kaimu😍😍😍😘.




ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭
[12/14/2020, 6:04 AM] HASNA✍🏻: Billyn Abdul:
Page 27

.................Daga can akace “goro yaron alkairi”. Ya cigaba da faɗin, “Da alamafa damunar bana zatai ɓarna, dan na hangi ɗakunan mutane da yawa sun buɗe ta sama batare da sun fargaba, kuma lallai bular zata zubda yoyon ruwan da zai iya haifar da ambaliya”. dariya ta tuntsure dashi daga can, tace, “Ɗan alkairi kana nufin dai dara zataci gida kenan, ɗan zaki yafara buɗe idanunsa ga rundunar kuraye  masu gudun tseren neman abinci koda bai kasance halalinsu ba?”. “Ƙwaraima kuwa mamana, bana sanar miki wani ƙwai dake cikin ƙaya ya bayyana ba kwanakin baya, kuma duk haɗarin maciji ya gama shawaginsa ya barsa dan ya gagara haɗiya”. “ƙwaraima kuwa ka sanar min da wannan, a farautar zaki yaci karo dashi kenan matsayin abinci?”. “Hhhhh mamana kina birgeni da saurin ramfo zance, to wlhy ina mai tabbatar miki da hakaɗinne ta kasance, tsagerun dawa na tunanin Zaki yafi ƙarfin ruwan ƙwai sai gashi harma yana ƙoƙarin damƙosa cikin ƙayoyi”. “Kai ɗan alheri karka sa farin ciki ya karni yau ɗinan ban kalmashe bakin buhun dana farama ɗureba, yanzu dai ina fatan kana hanyar gidane?”. “Hasashenki baya zama kuskure mamana, mu haɗu acan na baki sauran bayani, dan kuwa garin bita da ƙullin ƴaƴan kura sun rufta damisa da ƴaƴan fadarta a ramin ɗan zaki, shiko ya afka musu ƙasa yasa ƙafa yatake harma da share wajen kwanciya domin buƙatar hutu”. Wata irin dariya ta shigayi mai cike da nuna tsantsar farincikinta data daɗe da mantawa da samunsa, yau ɗan nata ya biyata da daddaɗan labari. tace, “Ɗan albarka wannan zinaran kalamai naka sunfi ƙarfin saurare a salula, garzaya gida nima ina gab da iskoka, dan tun safe na nema alfarma ga Uwargida sarautar mata akan zuwa na duba mai babban suna”.
      “Babu damuwa mamana ina tsumayenki acan, alkairin ALLAH ya cigaba da baibayeki tare da nasarar cigaba dayin haƙo a ramin azzalumai batare dasun fargaba har sai kinkai musu wuya lokacin sungama shiga tarko”.
       Murmushi tayi daga can tana faɗin “Amin ɗan albarka” kafin ta yanke wayar, shima ya tura tasa a aljihun yana murmushi. Cigaba yay da tafiya harya fito titi, napep ya tara takaisa inda motocin ƙauyensu ke tsayawa, duk da garinsu ba ƙauye bane sosai dole muce dashi ƙauye, dan kuwa a ƙarƙashin wata ƙaramar hukuma yake, saidai yamafi l.g ɗin dukkan abubuwan cigaba, gashi a bakin titi kuma babu nisa da babban birin jiharsu. A mamakinsa ana saukesa falletsetsiyar mota na cin birki a gabansa, baiyi mamakin hakanba, dan kasancewarsa drivern boss yanada alaƙa da sanin mutane manya sosai ta fannoni da dama, lokaci-lokaci kuma yakanci karo da wasunsu koda ace shi ya mantasu dan dama dalilin shige da ficin boss na aiki yake sanin nasu. Wanda ke ciki ya sauke gilashi yana murmushi, sosai gimba ya zaro ido irin na bazatar ganin wanda bai zatoba, “Lah Ɓaleru! Dama rai kanga rai? wane mai gangancine yay kasadar baka idanunsa kaketa haska hanya dasu cike da ɗaukar faɗi?”. Dariya na cikin motar yay har yana bugun sitiyari, yace, “Gimba kaidai baka rabo da shaƙiyanci, kasan ɓalerun naka da shige-shige, ko iska ta shafamin lafiya. Daga ina haka zuwa ina?”. Gimba yace, “Wlhy gida nai, zamuje hutun ƙarshen mako domin ganawa da iyali”. Ɓaleru yay ƴar dariya da faɗin, “Mutumina baka wasa da gona, shiyyasa kullum gatanan cikin yabanya take, banga laifinkaba, yi birgimarka ka more mata sune jin daɗin duniyar ai dama. Shigo mu haura dan nima dai can na nufa ɗin”. Babu musu Gimba ya shiga yana maida masa murtanin shaƙiyancinsa, saida suka ɗauki hanya ɓaleru yace, “Nifa mamaki oganka ke bani, gashi jinin manya, ɗan tsohon shugaban ƙasa mai tarin dukiya, shi kansa ƙwaron kansane dan ya tara bayan wanda aka tara masa, amma abin mamaki kamar shima baya mora balleku ƴan muna jira ALLAH ya baka mu samu”. Murmushi gimba yayi, cikin son kare boss ɗinsa yace, “Ai abin nagartace, sai dai irinku ƴan ƙwanta ka mutu mu haye basa ganewa, komai boss yake da tsari a cikinsa, shi bai ɗauki wannan dukiyar da ta tsolema kowa idanu wata tsiyaba, marasa nasaba da itama amfanuwa suke da tagomashinta amma ta ƙyaƙyƙyawar hanya, bai yarda da almubazzaranci ba, amma shi kogine maiba na kus

a harma dana nesa, alkairinsa dake jiƙe dani ALLAH kaɗai yasan iyakarsa, sai dai ba'a iya ganinsa da idon gani saina zuciya”. Wata irin mahaukaciyar dariya ɓaleru ya kece da ita wadda harta bama gimba mamaki, kafin yabi ba'asinta ɓaleru ya jefa masa handkherchief a fuska, daga haka bai sake banbance fari ko baƙiba sai a washe garin safiyar yau daya jisa a ɗaure, idanu a rufe, bakima a ɓame. A zuciyarsa ya ayyana, ‘GADAR ZARE akaimin da wanda na sani kenan?’. Murmushi yay na takaici wanda a zuciya ya kasance dan babu bakin yinsa. Da ƙarfin masifa aka fincike abinda aka sa masa a baki, azaba ta sakashi sakin wani irin gurnani sai dai jarumta ta hanashi nuna gazawa. Yace, “Suwanene ku? Miyasa kuka kawoni nan? Minai muku?”. Banza akai masa babu amsa, yasan akwai mutum tare dashi, dan yana jin hucin numfashi kasancewarsa mutum mai basira da wata ɓoyayyir baiwa. Yay ɗan yi murmushin ƙarfin hali yana mai motsa jikinsa kaɗan, ɗauri akai masa bana wasaba, hakan yasa daƙyar yake iya motsawa. Kusan minti biyir yana jiran tsammani kafin a saka masa abu akan kunne.
         Wata mahaukaciyar dariya aka sanya mai dogon zango daga cikin abinda basirarsa ta ankarar dashi wayace, daƙyar mai dariyar ya tsagaita daga can, kafin ya fara magana a kausashe. “Yaro ashe kaima tsagerane ban saniba, kai wanene daka isa tono abinda ke ɓoye? Ƙaramin naman daji abincin karnuka dakai har kakejin kakai zarra wajen yimana kutse a al'amuranmu? Banida lokacin doguwar magana dakai, yanzu za'a sakeka kai gudun mutuwarka kafin jininka ya zama halattacce ga bakandamiyarmu, wanda kakema aikinma bai isaba balle kai direbansa hhhhhhhhhhhhhh!!!!!”.
           Wata dariya gimba ya kwashe da ita shima, a kausashe yace, “Faɗan sunƙuru alamace tamai tsoro, idan kuncika maza kufito filin yaƙi mai nasara saiya ɗauki kambu, boss kainuwane dashen ALLAH, zakine mai yagalgala mazan da suke kiran kansu mazanma balle ku mata maza masu ɓuya a rumfar..........
         Kafin Gimba yakai ƙarshen zancensa an cire wayar daga kunnensa, taune leɓensa yay da ƙarfi. Kafin a maida masa baki a rufe, Bai sake jin motsin kowaba har yammaci, yana nan ɗaure babuci babu sha tun safiyar jiya rabonsa da abinci, garama ruwa yasha bayan fitowarsu massallacin juma'a, tun yana samun garkuwa daga yawu har shima yay tifƙewar da harshe bai iya juyashi ya zama abun mai gudana, ƙishirwa abune dake saurin illata mafi yawan halitta mai rai, balle irinshi mutum mai matuƙar son ruwa. Alamun duhun magriba da hasashe ne nashi yaji ya sake ɗaure garin, a wannan lokaci yaji an fara kuncesa, har aka gama tas bai motsaba bai kumace ƙalaba. Jansa aka shigayi keeeyyyy har zuwa waje, bashi da ƙarfin kare kansa dan haka ya salama bakinsa ɗauke da addu'a, tafiyar kusan mintuna uku kafin ai wurgi dashi.
      Numfarfashi ya shiga saukewa a gwame, yakai hannunsa da ƙyar ya janye ƙyallen da aka ɗaura masa a fuska, baya ganin komai da ƙyau saboda idanunsa sun kwana sun yini a rufe, ga duhun magriba, saidai ya fahimci dajine yake. Da sauri ya shiga laluban wayarsa dake aljihu wadda suka gaza gani bisa kariyar ALLAH, ya kasance mai saka waya silent saboda baison takurama Boss ɗinsa da shigowar kira, a hankali ya saba da hakan har takai bayama buɗeta koda basa tare, tun ɗazun yakejin sautin shigowar kira dama, daƙyar ya iya ganin Number boss saboda idanunsa basa gani sosai sun masa nauyi ainun. Kai tsaye WhatsApp ya shiga, yay azamar danna recording ya fara magana a galabaice.
         “Boss banjin zankai labari, dan basu kamani dansu barniba, akwai babbar ƙura a gabanka da bazan iya buɗe maka haske a kantaba yanzu saboda ƙarancin lokacin daya ragemin a duya, itace musabbabin shigowata rayuwarka tun fil'azal ka gafarceni da ɓoyewa, dama nabari ka fita daga wannan matsalar rikicin aurenne idan nadawo muyi magana, saidai ALLAH bai ƙaddara hakanba, amma nagodema ALLAH da wadda zata baka abinda yafi nawa tana raye, kai ƙoƙarin zuwa gidan Alh al..alhaji............ Ya kasa ƙarasawa saboda rawar da jikinsa ya fara na tunkarowar wata muguwar halitta  garesa maiban tsoro. Jifa yay da wayar bayan ya ɗaga ɗanyatsansa saƙon ya tafi

kasancewar baya rufe data shi dama can. Baya ya fara jan jikinsa yana karanto duk addu'ar data zo masa, yayinda shikuma wannan halitta ke biyosa danƙyas-danƙyas tana buɗe baki da lashewa alamar dai taga abinci. Babu zato gimba yaji yay baya, ashe wajen gaccine mai zurfin gaske dan akan tsauni suke. Wata irin wahalalliyar ƙara ya saki data bada amsa kuwwa a dajin yay ƙasa.......
       Wata irin mahaukaciyar dariya dahar saukarta ke kamar ƙasar dajin na girgiza ce ta fara ratsa tsaunika, anyita da tsayi kusan na mintuna biyar kafin ta lafa wani irin yare ya biyo baya da muryoyin mutane masu yawa. Duk wanda zai iya nutsuwar saurarar yaren zai fahimci kalaman cikinsa shirkace kawai ake ambato. (Wa'iyazubillah 😭ya ALLAH kasa mufi ƙarfin zukatanmu, ya rabbi ka saka duniya a tafukan hannayenmu karka sata a zukatanmu, kaiconmu, kaicon burikanmu kaicon son duniyarmu).

_________________________________

            Ana sallar magriba su Momy suka koma gida akan su Uncle Nasir zasu zauna da Jawaad domin yasa ɗan-fir'auna ya saki hudah.
          Momy da Shahudah ciki suka shige sukabar Aamilah na waya a barandar shiga falonsu.
             Da mamaki Aamilah ke kallon akwatinan da aka jibge a harabar gidan gaban motar Qaseem, ƙiyyy!! Sautin jawo abu ya karate kunnuwanta, kallon wajen da ƙarar ke zuwa tayi, Qaseem ne jaye da jikkan gana must go irin ƙatuwarnan sabuwa dal, amma tsabar yanda yasa ƙarfi wajen janta har hannu ɗaya ya fincike yana lililo, duk dai ya ganta yiyai tamkar basan da zamantaba, baba maigadi dai tun ɗazun yana hangen Qaseem ɗin daga ɗakinsa, tsabar baison yafito ya gansa ya sakashi aikin tayashine ya sakashi maƙalewa cikin ɗakin yana leƙensa ta Window. Jikkar ya dangwarar ya sake juyawa zuwa sashensu, daga shi sai gajeren wamdo da baƙar singlet datai mugun fidda masa siffarsa ta ƙaƙƙarfan namijin dake cin ƙarfe. Saida taga ya shige kafin ta juya da gudu gulma na cinta har saura kaɗan ta faɗi, ALLAH dai ya ara mata damar dafe ƙarfen da aka ƙawata barandar ƙofar falon nasu dashi, ƙara kwasa tai a gujen ta shiga tana ƙwala kiran Momy dake sama abin duniya ya isheta ga Shahudah tsaye kanta tana ribzar kuka da mata fitsara. Sosai kiran da Aamilah ke mata ya firgitata, ta miƙe zumbur ta fito tanabi matakalar benan da gudu-gudu. “Haba auta wannan wane irin kirane haka kamar wata baƙauya, miya farune shin kikemin kiran mafarauta?”. Baki Aamilah ta cuno bayan ta murguɗama Momy kamar wata sa'arta, kafin cikin taɓara tace, “Kajimin Momyn nan, dama kika samu na taimakeki na kawo miki labarin da ɗuminsa, toga ɗankican yana haɗa kaya da alama barin gidan zaiyi”. Sosai gaban mom ya faɗi, batama tsaya saurararta wanne a cikiba ta fice daga falon da sauri, dafa mata baya Aamila tayi tare da Shahudah data fito idanu a kumbure.
        Qaseem dake ta faman lodama ƙatuwar motarsa kayan yayma momy dake masa magana kallo ɗaya ya ɗauke kai batare da yace da ita ko ci kanki ba. Muryarta har zuga take na alamun ɓacin rai tace, “Qaseem wai badakai nake maganaba? Shin mikukeson maidanine a gidannan kai da Shahudah? shin bazaka nutsu kai ka fahimci uzirinmuba, Na shiga uku ni Aysha, wane irin mugun asiri wannan yarinyar ta haɗaku da shine kaida yaronan Jawaad da kuke ɗaukar kowa ɗan iska akan lamarinta?”. Cikin zafin murya Qaseem yace, “Nifa kin bala'in cikani da surutu hajiya, Please ki barni nai aikin gabana Mtsooww!!”. Ya ƙare maganar dajan wani wawan tsaki yana ɗauke kansa ya cigaba da loda kayansa a motar. Mutuwar tsaye kawai Momy tai tana kallonsa, Aamilah ta kwashe da dariya tana kallonsu, “Faɗan Uwa da ɗa abin birgewa, kucigaba da gashi guys”. Baki Shahudah ta taɓe tana mai juya manyan idanunta alamar zubama Qaseem harara, tace, “Ɗan jaraba duk bakai kaja manaba, wani iyayi da ƙwala kai a farantinne ya kaika nacema banzar yarinyarnan ƙazamiya mara gata, idan da baka maƙale matanba ta gidan uwarwa aurena da naka zasu haɗu ballema har bb ya aikata haka, asararre kawai mai baƙar zuciyar tsiy.....”
     Jikake tasss!! Qaseem da babu wanda ya lura da isowarsa gaban Shahudah ya sauke mata wani wawan mari, ƙasa ta zube tana garsheƙ

ar kuka daja masa ALLAH ya isa, to daman zuciyar ƴan mazan a kusa take, neman wanda zai amayarwa yakeyi, gashi ya samu cikin sauƙi, dan haka ya shigar tamkar an aikosa. Duk ihun da Aamilah keyi da Momy bai sauraresuba, sai ma tsarabar mari Aamilah ta samu itama, Momy kuwa ya hankaɗeta. Qaseem yanada Masifaffiyar zuciya irin wadda idan ta yunƙuro ɗinan sam bayajin bari, dan tamjar zugasama yake, sannan shifa cinnakane baisan na gidaba. Wanna. mugun zuciyan da ALLAH ya basu shida Jawaad itace ta hanasu zama ƙarƙashin inuwa ɗaya, dan kowa yanaji da kalar tasa, kawai shi Qaseem yafi Jawaad saurin fushine, dan Jawaad na dannewa yay kawaici har saika kaisa ƙarshe, amma ga Qaseem sam ba haka bane, sha yanzu magani yanzu, ga kuma ɗanbanzan riƙo saikace dangin kutare🤦🏻.
      Iya gwargwadon iko babu algus Shahudah ta daku harma da Aamilah daya koma haɗawa daga ƙarshe, dama yanajin haushinsu akan abu biyu, dukan Bilkisu da jimata ciwo, saikuma gudunmawar da suka bada akan ai masa aure da Azeema. Daƙyar da suɗin goshi baba mai gadi da kuku suka amshi Shahudah da Aamilah a hannunsa, dan yay musu kaca-kaca abinka da farar fata, Shahudah harda fasa mata baki akai jini sai ɗiga yake. Yace, “ƙananun marasa kunya, daga yau idan harku kun cika tsagerune dan ALLAH kusake shiga cikin al'amurana”. Kuka kawai suke daga su har Momy, babu wanda ya iya tanka masa har kuku da baba mai gadi suka gama loda masa kayansa a motar, sashensu ya koma ya ɗakko sauran tarkacensa ya shige mota ya fice batare da ya sakebi takantaba.

             Kai tsaye gidansa ya zarce, dama harya ajiye mai gadi tun jiya, kodaga waje kasan gidan ya haɗu, ya mugun ƙawatuwa da shukoki masu ƙamshi da daɗi, ga ƙamshin sabon fentima na tashi. Dakansa yayta shiga da kayan, da yake ALLAH yayisa mutum mai hanzari da zafin nama sai gashi ya gama sakasu ciki tas.

★★★★★

       Bayan barin Qaseem gidan babu jimawa Dad ya dawo, iske Momy yay zaune ta zabga tagumi, Shahudah na kwance barcin wahala yay gaba da ita ta ɗora kanta a cinyar momyn. sai Salman da Aamilah dake lido a d/table. duk sannu sukai masa, ya amsa yana zama kusa da momy tare da kamo hannunta cikin nashi. “Humairah mike faruwane?”. Muryarta na rawa tace, “Qaseem ne ya tafi?”. “Ya tafi? Ina ya tafi to?”. “Muma bamu saniba, ya kwashe duk kayansa na gidannan”. Cikin taune leɓe Dad yace, “Bari dai zamuyi magana, yanzu tare nake dasu Alhaji Nasir suna falon baƙi, mun kira yaronan ne da aka ɗaura aurensa da mamana zaizo”. Zumbur Momy ta miƙe jikinta har rawa yake ta ture kan Shahudah batare data tuna tana jikinta tana barciba, tace, “Ya yarda ɗin zaizo Dadynsu?”. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Eh ya amince, drivern Alhaji Nasir ma yaje ɗakkosa”.

________________________________

       

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment