Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

     Bayan Jawaad ya dawo daga sallar magriba shiryawa yay ya amsa kiran da Alhaji babba yay masa, kansa ciwo yake masa, amma bashi da ikon bijirema kiran kakan nasa, ballema yaji muryarsa wani iri kamar yana tare da damuwa, tun da ranama ya fahimci hakan, ya haƙurane kawai ya barsa da yace masa babu komai..
         Fitowa yay yanata baza ƙamshi, sai dai fuskarnan a cinkushe babu walwala. ya tsaya suka gaisa da mai-gadi har yake tambayarsa gimba bai shigo bane?. mai-gadi yace, “Aiko bai isoba Oga, ni harma na fara tunanin ko lafiya? Dan tunda ya tafi bamuyi wayaba kuma kaga har lokacin daya saba dawowa ya shige amma shiru”. Jimm Jawaad yay alamar tunani, dan shima dai tunda gimba ya tafi basuyi wayarba kam, to wannan hargitsicinne ya ɗauke masa hankali gaba ɗaya har bai ɗauki hakan komaiba. Ya ɗan sauke numfashi yana kallon mai-gadin. baba bara dai naje na dawo, idan har lokacin bai shigeba saina nemesa naji mike faruwa?”. Mai gadi yace, “To to ba laifi oga, ALLAH ya maidoka lafiya”. “Amin” Jawaad ya faɗa yana ficewa, sai dai acan ƙasan zuciyar tasa maganar gimba taƙi gushewa.

            A ƙofar gida ya iske Alhaji babba zai shiga massallaci, dan haka yay fakin anan waje ya fito suka shiga tare, bayan sun fito Alhaji baba yay sallama da mutane maƙwaftansa da ragowar ƴan anguwa masu salla anan kamar yanda ya saba, kafin ya kama

hannun Jawaad dake masa shagwaɓan shifa fura zaisha, Alhaji babba ya bada a siyo masa. Alhaji babba dake murmushi ya tsaya yana dungure masa kai, “Kai miyasa idan rikicinka ya motsa babu wanda ka raina saini? Kaje kaima su Mariya mana”. Fuska Jawaad ya yatsine saboda ciwon da kansa ke masa yace, “Nidai ka daina sawa gaban mamana na faɗuwa a darenan, kabama Tanimu ya sayo mani inba hakaba bazan sake zuwa kwana gidanka ba”. Dariya Alhaji babba yay da jan hannunsa suka cigaba da tafiya, yace, “Yoni ALLAH na tuba aina yayeka da zuwa kwanarmin gida, matarka ta jajiba nima na huta da rigimarka hakanan”. Jawaad yace, “Basai na ɗakkota muke kwana anan ɗin tareba”. “Bana gayya, ku zauna gidanku nima aure zanyo”. Ciki dauriya Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya, koba komai yarage nauyin da zuciyarsa tayi da tattaunawa da kakan nasa, shi kansa Alhaji baba sai yaji damuwarsa ta sassauta.

          Bayan sun zauna Alhaji baba ya zubama Jawaad fura mai ƙyau da daɗin gaske da bai rabo da ita ya dubesa, cike da jin daɗi yake shan furan sanyinta na ratsa masa zuciya da ƙirji. “Muhammad kasan miyasa na kiraka kuwa?”. Kallonsa Jay yayi ya girgiza kansa batare da yace komaiba. Alhaji baba ya ɗan sauke numfashi, murya a sanyaye yace, “Akan matarkane” Saida Jawaad ya haɗiye furan daya sha kafin yace, “Matata kuma?”...............✍

Ƙyan alƙawari cikawa, sai dai wanda na ɗauka ni ya gagara cikar dalilin birkicewar wattpad, harna fara canja page ɗinma sai ALLAH ya taimakeni ya dai-dai ta🤦🏻, page ɗinnan kaɗai gareni babu nagobe saboda matsalar wattpad ɗinan ta ɗauki hankalina banyi typing ba, ƴan telegram sunce a turo muku kawai, amma da wuya kujini gobe idan ALLAH ya kaimu zan samu nayi typing ɗin jibi idan munada rabon kaiwa. Gaisuwa ga kowa da fatan alkairi😍😍😘😘.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
        ƊAURIN ƁOYE
      ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
         SAUYIN ƘADDARA
        ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
           BURI ƊAYA
         ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
           KAIMIN HALACCI
           IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
          WUTSIYAR RAƘUMI...
         GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[12/15/2020, 2:54 PM] HASNA✍🏻: Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
Page 28

................Alhaji babba ya gyaɗama Jawaad kai alamar eh ita. Cike da mamaki Jay ya ajiye kofin hannunsa yana tsatstsare kakan nasa da idanunsa cike da sonjin ƙarin bayani.
      Murmushi Alhaji Babba yay masa tare da kamo hanunsa, “Daina tsareni da waɗanan idanun naka ba wani abu bameba, kawai inason sanin dangin mahaifinta ne”. Sassanyar ajiyar zuciya Jawaad ya ɗan sauke, kafin shima ya riƙe hanun Alhaji Babba da ƙyau a cikin nashi, “Baba nima inason saninsu, sonake kawai wannan ƙurar ta lafa itama ta sakejin sauƙine”. Alhaji babba yace, “Kayi tunani mai ƙyau, inason kayi ƙoƙari ka bincika, sannan yaya maganarka da mutanen gidanku? Da kuma maganar shi wanda kasa ya auri yarinyarnan ta wajen Ali?”.
     Murmushi Jawaad ya ɗanyi ya ɗauki furarsa zai cigaba da sha, ganin zai basar da zance Alhaji babba yace, “Nasanfa ka jini”. Ƴar dariya Jay yayi yakai kofin bakinsa, “ALLAH ka iya rigima kaima tsohon nan, karka damu ina sane da komai”. “Nasan kana sane da komai Muhammad, sai dai hankalina ya tashi matuƙa jin ba mutumin kirki bane habibun, kajifa wani suna da Nasiru ya kirashi dashi ranar”.
          Jay yay murmushi kawai batare da yace komaiba.

        Sun cigaba da hirarsu har zuwa ƙarfe tara ya fita, yaso zuwa asibiti, amma ganin dare yayi sai ya haƙura ya nufi gida abinsa. A gate ya tsaya ya tambayi mai-gadi ko gimban ya dawo?. mai-gadi ya tabbatar masa da bai dawoba, ya kira wayarsa kuma gashi tana ring amma ba'a ɗagaba.
      Sosai abin ya ɗaurema Jawaad kai, daga baya kuma ya ajiye tunaninsa akan inhar da safe bai dawoba zaisa abi bayansa garin nasu aga ko lafiya?. Da wannan tunanin yay shirin barci ya kwanta.

_________________________________

             Su Dady sun karɓi baƙuncin surikinsu habib, duk yanda Dad yaso su Momy su zauna basai sunzo falon baƙiba hakan ya gagara, dole ya barsu sukabi bayansa, ba ƙaramin tashin hankali Shahudah ta shigaba da ganin wanda ake kira wai matsayin mijinta, daka gansa kaga cikakken tantiri marajin magana, cike da isa ya zauna a kujerar da aka nuna masa sai wani cika yake da batsewa.
        Ya kafe Aamilah da Shahudah da kallo yana wani lasar laɓɓa tamkar tsohon maye, ko kunyar su Dad bayaji, dama daya shigo babu wanda ya gaida, bama su ishesa kallon arziƙiba.
      “Wace cikar tawa anan?” yay maganar cike da gadara. Babu wanda ya tanka masa a cikinsu, sai Shahudah da Aamilah da suka zuba masa wata shegiyar harara. Ya bushe da dariyarsa mara daɗin ji yana faɗin,  “Dama ace ana auren yaya da ƙanwa wlhy da duk haɗawa zanyi hhhhh! Dana kwashi gara aradu...” cike da tsiwa Aamilah da tafi Shahudah jin hausa tace, “Uwarkane garan shege mai suffan aljanu.....” wata wuta data gitta ta idanunta mai stars ce ta hanata kaiwa ƙarshe, lokaci ɗaya jinta da ganinta ya ɗauke baki ɗaya ta zube a jikin Dad daya tarota. Babu wanda yaga sanda Ɗan-fir'auna ya ƙarasa gaban Aamilah sai ƙarar maruka sukaji kawai.
     A fusace Dad yace, “Kai ƙaramin ɗan tsagera, wanene ubanka da har zaka mararmin yarinya a gabana?”. Kallon dad ɗan fir'auna yay ya watsar, kafin cike da gadara yace, “Sanin ubana a gareka dattijo ai tamkar yankewar numfashinka ne, dama kun kiranine domin kuci zarafina komi? kunga dalla malamai ku bani matata na wuce na fasa zaman....” da sauri Uncle Uwaisu ya taresa cikin lallashi yana bashi haƙuri, amma fir ƴaki sauraren kowa, Aamilah dai ta farfaɗo da ƙyar bayan an zuba mata ruwa, Shahudah na rakuɓe lungun kujera sai tsiyayar da hawaye takeyi jiki na rawa, harga ALLAH tsoronsa takeji, a ranta kuwa ayyanawa take ashe Bilkisu baturiyace, dan ɗan-fir'auna ALLAH ya bashi baƙi, wanda daga gani kasan shaye-shaye ya sake taka rawar gani wajen ƙara masa shi. Da ƙyar suka samu ɗan-fir'auna ya zauna bayan an saka Shahudah da Aamilah sunbar falon, Salman kam yay laƙe kamar baya falon (hege yaga maza🤣😜).
          Duk yanda su Uncle Nasir sukaso lallaɓa ɗan-fir'auna akan ya saki Shahudah yace shifa sam baisan wannan zanceba, dan yanzuma da shirin ɗaukar matarsa yazo yana buƙatar abinsa, tunda yana zamansa aka kawo masa tallansu. Har ƙasa Momy ta duƙa tana kuka da roƙonsa amm

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
a sai dariyar wulaƙanci da cusa haushi yake musu.
        “Kungafa kubar ɓata lokacinku akan roƙonama, tayaya kuke tunanin zanyi sake da wannan babbar kaddarar ne haka, yo ko shugaban ƙasa ai nafishi hura hanci yanzu akan wannan cikar tawa, ku manta kawai a saimin royal bed zan kama hayar gida aje aimin jere gobe, babu damuwa idanma kunkai sati danshi shiri wuyane dashi, ko a hotel mayi amarcin satin guda kafin ku kammala surukai..” ya ƙare maganar da miƙewa yay salute nasu zai fice. Da sauri Dad yace, “Nawa kake buƙata a biyaka ka sakarmin yarinya?”.
      Tsayawa ɗan-fir'auna yayi, ya juyo yanama Dad wani matsiyacin kallo maiban tsoro, sai kuma ya bushe da dariya tare da dawowa da baya. Yace, “Zan iya amsar kuɗi na saketa pale, tunda yanzu na auri ƴarka ka zama pale ɗina nima, ammafa kasani saina ɗanɗana kona sati ɗayane dan yawuna ya biya, a shiryata da safe nazo na amshi kayata, nanda sati biyu saiku cakemin naira miliyan hansin na baku ƴarku, idan haka bai mukuba kuma banida matsala, iyakaci inta mata ciki duk bayan wata tara ta ringa juyen jajayen ƴan dugwi-dugwi irinta, koba komai na samu surukai masu kuɗi nima nan gaba tunda naga jar fatar ake yayi yanzun” ya wani ɗage musu gira cike da barikanci yay ficewarsa.
           Babu wanda bai jiƙe da zufaba a falon, tun fitar ɗan-fir'auna babu wanda ya iya magana sai kuka Momy dake tashi. Salman ya miƙe cikin raɗa-raɗa yace, “Wlhy kuyi ƙoƙari ku biyashi, dan wannan dagani zai iya take mutum ya yanka tamkar ya yanka kazar gidan gona, ku rufa mana asiri dad dan kuwa su momy sun kwaso mana bala'i, wlhy barin ƙasarnan zanyi idan an gama watandarku na dawo zaman gaisuwa”. Ya ƙare maganar da ɗai-ɗai yana kallon ƙofa, da gani kasan a tsorace yake (Kana bani yaji Salman🤣, lusarin banza😠).

WASHE GARI.

             Dad na zaune a harabar gidansa abin duniya ya taru ya masa yawa, tunda ya dawo sallar asuba bai iya shiga cikiba, a daren jiya da ƙyar suka samu Shahudah tai barci, dukta gama fita hayyacinta.
       Baƙon da aka turo daga masarautane ya samu isowa, ya ƙwanƙwasa gate mai gadi ya leƙa, sai da suka gaisa sannan yace, “Magatakarda ne daga masarautar gagara badau, an aikoni domin isar da saƙo ga Alhaji Ali ko yana nan?”. Mai-gadi yace, “Ƙwarai yana nan, sannu da zuwa bara a sanar masa”.
      Sai da baba mai-gadi yay sallama sau kusan uku sannan Dad ya jisa, bai amsaba sai zuba masa idanu da yayi. Baba mai-gadi yace, “Alhaji baƙone wai daga masarauta”. “Masarauta kuma? Ni miya haɗani da masarauta malam Amiru?”. “To Alhaji wlhy ban saniba, yadaice daga can yake”. Da hannu kawai Dad yay nuni alamar baƙon ya shigo. Baba mai-gadi ya koma domin shigo dashi.
          Sai da baƙo ya zauna a kujerar robar da baba maigadi shima ya ajiye masa sannan suka gaisa da Dad, cikin nutsuwa magatakarda ya korama Dad bayani akan gimbiya ta bada umarnin Bilkisu zata koma masarauta da zama har sai ranar tarewarta gidan mijinta.  rasa abinda ma zaice Dad yayi, sai tsurama magatakarda ido yay kamar zai haɗiyeshi dasu. Har magatakarda yaymasa sallama ya tafi bai dawo hayyacinsa ba, sai faman juya takardar hannunsa da magatakarda ya kawo yakeyi, shi yanzu abin tambayarsa anan Bilkisu ce takai ƙararsa masarauta kokuwa Jawaad? Kai yasan halin Jawaad da shegen taurin kai, bazai taɓa kai magana masarauta ba dan tsaurin idonsa bazai barsa ganin ya gaza ba. To amma bai zaton Bilkisu nada irin wannan wayon, kuma itada takema kwance a asibiti. Gaba ɗaya ransa ya kuma jagulewa, cike da sassarfa ya tashi ya shige ciki.

★★★★★★

            Jawaad kam koda ya gama shirinsa na office ya fito sai ya iske Gimba bai dawo ba, mamaki ya kuma cikashi, dan jiya bayan ya dawo ya kira Number gimba har sau biyu kafin ya kwanta amma ba'a ɗagaba, yanzu kam yafara tunanin babu lafiya, akwai wani saurayi a gidan da aikinsa kawai kula da flowers ɗin gidanne, garinsu kusada garinsu gimba yake, hakan yasa Jawaad ya kirashi yanama tsaka da aikinsa na bayin fulawar. Durƙusawa yay yana gaida Jawaad, Jawaad ya amsa da masa nuni ya tashi. “Banace ka dainamin irin wannan gaisuwarba Balarabe, kadaina min wannan durƙuson kamar

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
wani mai neman gafara kaji”. fuskar balarabe ɗauke da murmushi yace, “Alhaji nagode sosai, amma nariga na sabane, koba aiki nake ƙarƙashin kuba aika girmeni nesa”. Girgiza kai kawai Jawaad yayi, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙa masa 3k, “Balarabe ajiye aikinnan naka zakai dan ALLAH kaje garinsu Gimba ka ganomin ko lafiya yake? aikasan garin ko?”. Da sauri balarabe yace, “Eh Alhaji, ai daga garinsu zuwa namu da ƙafama muke zuwa, kuma har gidansa na sani tunda naje sunan yaronsa da aka haifa masa na ƙarshenan mai sunanka”. “Okey Alhmdllh, kayi ƙoƙari kaje yanda zaka dawo da wuri, bani number ka na kira kaga tawa, daka isa kasan halin da yake ciki ka kirani na sani kafin ka juyo”. Cike da girmamawa balarabe yake sauraren number da Jay yake faɗo masa yana sakawa a wayarsa nokia, bayan ta cika ya kira shima jay yaga tashi.

          Mota Jawaad ya shiga, yau da kansa yay driving, kai tsaye asibiti ya nufa, sai da yaje suka gama magana da likita sannan ya nufo ɗakin da Bilkisu ke jiyya. Sallama yay suka amsa, kafin ya tura ƙofar ya shiga.
       Kasa ɗagowa nai in kallesa, dan wata matsananciyar kunyarsa nakeji a raina, cikin girmamawa ya gaida mama, aunty Batool ma ta gaidashi da tsokanarsa, gaisuwarta kawai ya amsa bai maida mata magana akan tsokanarsa da takeba, na ɗago ido kaɗan nai masa kallo ɗaya na janye da faɗin, “Ina kwana”. shiru kamar bazai amsaba, sai da ya ajiye kwalin maganina daya ɗauka yana dubawa sannan yace, “Lafiya ya jikin?”. Ahankali nace, “Naji sauƙi”.
         Jawaad ya ɗauke kansa daga Bilkisu ya maida ga mama, “Mama Doctor ya sallameta, saiku haɗa kayanku, zanje office yanzu, nanda awa ɗaya zuwa biyu zan dawo sannan ai kun kimtsa”. Mama tace, “To to Alhmdllh, ALLAH yasa haka shiyafi alkairi, to amma kayanta fa? Kasan komai yana can gidan”. Ɗan jimm Jay yayi idonsa akan Bilkisun, ya sauke numfashi kaɗan yana ɗauke idanunsa, “Inaga mu manta da zancan zuwa gidansu yazu, bara naje na samo mata wasu kayan kawai”.
         Jin abinda yake faɗama mama yasa na ɗago da mamaki na kallesa, hakan yay dai-dai da shima ya juyo gareni, idanunmu ne suka shige cikin na juna, nai azamar janye nawa da fargabar ina kuma zan koma? Badai gidan nasaba? yanzu har rashin gatana yakai irin haka da.......
    Katsemin tunani yay da cewar, “Dami-dami kike buƙata?”. Idanuna cike da ƙwalla na ɗago na kallesa, ganin har yanzu ni yake kallo saina maida kaina ƙasa, muryata cike da tahowar kukan da nake dannewa nace, “Miyasa bazan koma can ɗinba?”. Banza yay bai amsa minba, hakan yasa hawaye masu zafi suka silalomin akan kumatu. Sautin siririn tsakinsa kawai naji, cikin faɗa-faɗa yace, “Haka na gadama dole kuma hakan za'ayi, idan kuma kika nema dagulan lissafi ALLAH yau ɗinan zaki tare”. Babu shiri na ɗago kai da sauri, wata uwar harara ya zubamin. Dole na maida kaina ƙasa. Wata ƴar ƙwafa yayi, sai takunsa ya biyo baya, kafin naji buɗe ƙofa da rufewa alamar ya fice abinsa. Koda na ɗago sai naga ashe daga ni sai shine ma a ɗakin, sam banji sanda su mama suka fitaba, dukda inajin motsin ruwa a bayi alamar ɗaya na ciki ɗayane ya fita.
         Gaba ɗaya zuciyar Jawaad a jagule take, sai dai jarumtarsa ta ɓoye hakan, shi mutumne tamkar kowa, yana farin ciki yana baƙin ciki, yana shiga matsala yana  shiga tashin hankali, kawai dai ALLAH yayisa mai zuciyar dakiyane kamar yanda ALLAH yay mafi yawan maza da juriya akan abu komin zafin da sukeji akan al'amari. Tafiyar da bata wuce mintuna goma ba ya isa wani haɗaɗɗen boutique, yanda suka tarbesa zai tabbatar maka da an masa farin sani a waje, sai gaidashi suke cike da girmamawa. Wani mai tsananin kama da Jabeer ne ya fito daga wani lungu, ganin Jay ya sashi faɗin, “Yah Jay barka da zuwa”. Kallonsa Jay yay daɗan murmushi yace, “Yauwa Kabeer, ya kasuwar?”. “Alhmdllh Yayah, kanason wani abune?”. Kai kawai Jay ya kaɗa masa kafin ya miƙe a kujerar da yake zaune. Yana gaba Kabeer na biye dashi har wajen da kayan mata suke, tsala-tsalan jallabiya da ƙananun kaya harma da ɗinkakkun atanfofi da shadda duk sunda. Ahankali yake binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, karon farko a rayuwarsa da yazo saima ma

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
ce kaya shi ɗaya, ko sanda suna tare da Shahudah hakan bai taɓa faruwaba, dan ita a tsarinta bata sayen kaya anan saina ƙasashen ƙetare, hakan yasa koda yaga abu ya burgesa baima taɓa wahal da kansa wajen saya matanba.
      Ganin ya kasa ɗaukar komai kabeer yace, “Yah Jay aida ka kira ka faɗi duk abinda kake buƙata bama saika zoba”. Guntun murmushi jay yay masa kawai daɗan taɓa kafaɗarsa, kafin ya fara nuna masa duk abinda yay masa wanda ya ƙiyasta a ransa zaiyi dai-dai da jikinta, saida ya ɗauka kaya kusan kala goma sha biyar, sannan ya ɗauka takalma uku da hijjabai huɗu ya zaɓi akwatin da za'a zubasu. Yasan dolene ƴa mace budurwa kamarta ta buƙaci kayan ciki, to amma shi ta ina zai fara tunda ba sanin seize ɗinta yayba. Kallon sashen da kayan suke yay, gasunan kala-kala kuma duk seize ɗin da kake buƙata zaka samesu, yaɗan yatsina fuska kafin ya nufi wajen, amfani yay kawai da yanda yake hasasota cikin idanunsa ya ɗauka matasu aka haɗesu da waɗancan. Card ɗinsa ya bama Kabeer, ganin kabeer na wani noƙewa akan baza amshi kuɗinba dan harya kira Jabeer ya sanar masa ga Jawaad ɗin a wajen yace karsu amshi kuɗi su rubuta su aje idan yazo zai biya. (Wajen na Jabeer ne, ƙaninsa kabeer ke kula dashi sai sauran ma'aikata). Cikin sosa ƙeya Kabeer yace, “Yah Jabeer yace karna amsa”. Sosai Jay ya kafesa da idanunsa da yau gaba ɗaya babu haske a cikinsu saboda damuwa. “Kiransa kai ka faɗa masa nazo?”. Kasa cewa komai Kabeer yay sai faman susar ƙeya yake, Jay yay gaba a binsa zuwa mazaunin kabeer ɗin da yake shine mai amsar kuɗi. Ɗaya daga cikin yaran wajen ya kira ya duba masa kuɗaɗen duka kayan aka zubasu a akwati, shikuma ya saka card ɗinsa ya cire adadin kuɗin yay ficewarsa aka bisa da kayan.

★★★★★

        Fitar jay babu jimawa a asibiti Qaseem yazo, cike da mamaki Bilkisu ke kallonsa jikinta sai rawa yake dan tunda ta kwanta a asibitin nan sai yau ta gansa, baiko kalli mama ba balle ta samu darajar gaisuwarsa ya finciki hannun Bilkisu dake zaune bayan ta kimtsa suna jiran dawowar Jawaad, da sauri mama ta riƙe Bilkisun da faɗin, “Lafiya kuwa Qaseem? Ina zaka kaita?”. Wani banzan kallo ya mata yana figar bilkisu batare daya tankaba, itako kuka take iya ƙarfinta da roƙonsa ya sake mata hannu karya jimata ciwo, amma sam yaƙi sauraren kowa. Tun suna ɗaukar abin wasa har yanema fin ƙarfinsu, dan Doctor ma yazo ya basu sauran maganin bilkisun shima ta ritata dashi. Rikici bana wasaba ake kwasa da Qaseem har ALLAH ya maido Jawaad asibitin. Tunda ya gabato wajen yakejin hayaniya, cike da mamaki ya shiga dan ƙofar a buɗema take. Idanun sane suka fara sauka akan hannun Qaseem dake riƙe dana Bilkisu, tuni idon ƴan mazan ya rufe, a wata irin matsananciyar tsawa yace, “Qaseem sake mata hannu!!”. shi Qaseem ma sai yanzu yaga Jawaad ɗin, shima a fusace yace, “Anƙi a saki ɗin, koka saketa, koma karka saketa zan wuce da itane”. Saukar wani bahagon bugu kawai Qaseem yaji akan damtsen hannunsa, ai baimasan ya saki hannun Bilkisu ba saboda gaba ɗaya jijiyar hannunsa ta saki lokaci guda saboda azaba, kafin ya gama dawowa hayyacinsa Jay yaja hannun Bilkisu dake kuka sun fice daga ɗakin. Ganin haka yasa Doctor saurin rufe ƙofar ya kulle danya bama jay damar barin asibitin gaba ɗaya.
         Kuka bily take cin ƙarfinta har suka hau titi, jin ta cika masa kunne yasashi taka wani wawan birki da batasan sanda tai tsale ta koma jikinsa ba. Sai jinta kawai tayi zaune ɗare-ɗare bisa cinyarsa ta cusa kanta a ƙirjinsa tare da ƙanƙamesa. ALLAH ne yaso Jawaad ya tsaida motar, da babu abinda zai hana su kife a hanyarnan. Gaba ɗayama sai ya kasa cemata uffan, sai rumtse idanunsa da yay  yana mai cije leɓensa na ƙasa da masifar ƙarfi kamar zai hudashi.
        Jin shiru mun tsaya ga ƙamshin turarensa yay mugun addabar hancina haryazama shine iskar da nake shaƙa ya sani ɗagowa, sosai na zabura ganina a jikin boss ɗare-ɗare, innalillahi.... Na shiga ambata ina rawar jikin sauka, harna koma inda na baro bai motsaba, nikuma ban iya kallon fuskarsa ba saboda tashin hankali da matsananciyar kunyar dana tsinta kaina a ciki. Jin tsahon mintuna biyar yaƙi cewa komai yaƙ

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
i kuma ya cigaba da tafiya yasani satar kallonsa ta gefen ido ina share hawayena da sukaƙi tsayawa. A kife yake kan sitiyari bana ganin fuskarsa, tsorone ya sake kamani, murya na rawa nace, “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy tsorata nayi”. A fusace ya ɗago yana watsamin wani irin harara, yanda idanunsa sukai matuƙar jazur fiye da farkone ya kuma ɗagamin hankali. A kausashe yace, “Idan baki rufemin bakiba saina canja miki kamannin fuska! Saboda na raboki dashi kikemin wani kukan banza da wofi?!!”. Da sauri na shiga girgiza masa kai ina mannewa da ƙofa, dan yanda yay maganar tamkar zai haɗiyeni ɗanyane, ni tun lokacin da naga fushinsa nake tsoron cigaba da ganin hakan. Yay ƙwafa da ƙara zubamin harara, “Share waɗanan banzayen hawayen”. Saurin saka ƙasan hijjab ɗina nai na goge tas kamar yanda ya buƙata, sake ɗauke kansa yay daga gareni Batare da yace komaiba ya tada motar da fusgarta muka cigaba da tafiya.

       Duk da hankalina a tashe yake da yanda yake zuba gudu a titi ban sake gigin yin wani abuba, sai kaina dana tusa a cikin cinyoyina ina addu'ar ALLAH ya kaimu lafiya dukma inda muka nufa.
      A halin da yake ciki yanzu bazai iya shiga masarauta hakaba, hakan yasa yay fakin daga waje, fita yay da waya a hannu, bayason kiran gimbiya dan haka ya maida akalar kiransa ga dattijon nan, bugu biyu kuwa ya ɗaga suka gaisa, Jawaad yay masa bayani a taƙaice. Dattijo ya amsa masa da sujirasa gashi nan zuwa. Babu jimawa kuwa yazo tare da Amaturrahman data rikice da murnar ganin Bilkisu. Basu wani ja zanceba ya basu Bilkisun batare da yace mata uffanba akan hakan, saida ya juya zai shiga motarne ya dubeta sau ɗaya ya ɗauke kansa da faɗin, “Ki shirya gobe zaki koma aiki, zan biyo na ɗaukeki” daga haka yay tafiyarsa. binsa tai da kallo har saida ya tada motar yabar wajen itama suka shiga motar dasu Amaturrahman suka fito da ita.

__

            Asibiti Jawaad yay niyar komawa dan yayma Qaseem dogon gargaɗi, sai dai

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment