Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nunamin muhimmancin mutane irin Abdul-aziz a cikin masu mulkin ƙasarnan, tun ina ganin suna tunzurashine kawai harna yarda dasu na shiga jerin masu masa addu'a. A haka ya kammala shekara huɗun farko a gwamna aka tsaidashi takarar shugaban ƙasa a bazata. Yaso ya bijire a lokacin kam, amma muka tsaya kai da fata ni da Sadi da Nasir da wasu a ƴan uwansu wajen roƙonsa ya tsaya tunda jama'ane suke buƙatar hakan. Haka ya haƙura dan darajar roƙon da mukai masa. An shiga hidimar kamfen da sauransu har dai gwamnati ta tsaya, Abdul-aziz ya zama shugaban ƙasa. Harkokin mulki sun fara zama da ƙafafunsu yanada watani huɗu, dan anyi naɗe-naɗe ga waɗanda ya dace, ciki harda Sadi wanda ya samu muƙami mai tsokar gaske, hakama Alhaji Ali. cikin amincin ALLAH suka fara fiddo ayyuka na cigaban ƙasa wanda ina ɗaya daga mashawartan na cikin gida. Ƴan ƙasa nata murna da nuna jin daɗinsu, sai dai kuma ga Abdul-aziz abubuwa sun fara canjawa, walwalarsa da kuzari duk sun fara raguwa, idan ya zauna sai kagansa zugum tamkar wani wanda abin duniya ya addaba. Abotarsa da Sadi kokino kamar ta fara ja baya, dan yawan zuwa da ya keyi gidan sai naga ya rage daga shi har Ali. A koda yaushe ya dawo gida yana manne da Jawaad kamar wani wanda za'a ƙwace masa shi. Idan na tam

bayesa mike damunsa kuma sai yace dani babu komai, ko yace, “Harka mulkin ƙasarnan sai addu'a Bilkisu, babu komai cikinsa sai baƙin tashin hankali, a zahiri kawai shugaban ƙasa yake amsa sunansa, amma a baɗini ɗaure yake tamau agun waɗanda ke zagaye da shi”. Nakan nema fashin baƙi akan wannan magana a duk sanda ya yita, amma sai dai yay murmushi kawai baya cewa komai. Tun ina ƙoƙarin tambayarsa ma harna daina, sai dai inata masa addu'a. Yana wata na goma da hawa mulki nakasa haƙuri nai masa tambaya akan Sadi da Ali, amsar daya bani itace kawai babu komai. Hakan yasa naji babu daɗi gaskiya. dan harna nuna masa. Mutum ne shi mai matuƙar sauƙin kai ga iyalansa. sai ya zauna ya dinga bani haƙuri damin nasiha akan wani abun barinsa a yanda yake yafi muhimmanci fiye da tonasa. Nanma dai haƙura nai na barsa badan naso hakanba, sai daga bayane na samu Mama maryam da maganar dan abin ya kasa barin zuciyata. A ranar yazo nan gidan, sai dai bansan mi suka tattauna ba, da ya koma gida kuma ban tambayesa komaiba”. Umm-Anum ta sauke numfashi da share hawayen dake gangaro mata, wanda su Bilkisu ma kukan suke a hankali. Ƙafarta mai ciwo taɗan miƙe da cigaba da faɗin,
   
            “A daren wata juma'a dake dai-dai da cikar Abdul-aziz shekara ɗaya da wata ɗaya akan kujerar mulki sai yay baƙi bayan sallar isha'i, tunda naga har ya yarda zaiga baƙin na tabbata masu muhimmanci ne, dan a ƙa'ida shugaban ƙasa baya irin wannan zaman musamman ma da daddare, kuma a cikin gida, gidanma a falonsa. Inason tashi na bisa naga wanene Jawaad dake fama da zazzaɓi ya hanani tashi dan yanata faman kuka, haka na haƙura nai amfani da telephone nai kiran su Wasila dake ɗakinsu, dan suna a tare damune kowa ya sani. Rahma ce ta ɗaga wayan, a cewarta Wasila tayi barci. Umarni na bata akan tasaka akaima baƙin Abdul-aziz abin sha, idan kuma suna buƙatar wani abu sai a haɗa da shi. Ta amsamin da to na katse kiran. Kusan mintuna arba'in da yin haka harma na manta ina jiran shigowarsa ne kawai sai ga Rahma ta shigomin a wani iri. Faɗa na fara mata, dan basa shigowa ɗakinsa inba da wani babban daliliba. Cikin rudin da take ciki tace, Kiyi haƙuri Yayah, wlhy wani abune ya sakani a ruɗani, zomuje ɗakinki kiji dan ALLAH kada Yah Abdul ya shigo. Ban musa mataba nabi bayanta muka fita, ina goye da Jawaad da yay barci a bayana”.
       (Yayah wai dan ALLAH mi su Alhaji Sadi keson Yah Abdull yayi ne yaƙi?). Ban ganemba Rahmah miya faru?. (Ruwan da kikace na saka a kaimusu saina iske ma'aikatan sunata faman aiki, kinsan kuma Yaya bason kowa yay masa aiki yake ba wani lokacin, shinefa na ɗauka da kaina nakai ruwan, to saina iske Yaya Nasir, Alhaji Ali da Alhaji Kokino tare da shi, sai dai kafin nai sallama naji wani furuci na Yaya Nasir daya saka bayan na gaishesu na ajiye ruwan na sake laɓewa, dan tundafa na shiga falon kan Yah Abdull a ƙasa alamun ransa a ɓace yake. Kinsan minaji kuwa?) kaina na jinjina mata a lokacin. (Ta cigaba da faɗin Yaya Nasir naji yana faɗin, “Amma dai Abdul-aziz kasan baka isa sanin sirrinmu ba sannan ka bijire mana, bafa wai dan bama sonka bane muke jawoka jikinmu, duk yanda kake tunanin mulkin ƙasarnan yafi ƙarfinka saika ɗaura ɗammarar da muke nuna maka, dan mulkin ƙasarnar baya buƙatar GASKIYARKA ko ƘWAZONKA balle son TALAKAWANKA”.  Murmushi Yaya Abdull yayi yana girgiza kansa, cike da ladabi yace, “Yaya dan ALLAH mu ajiye maganarnan, indai nine kusa a ranku abinda naji na gani a can wajen na barsa wlhy, kuma har abada bazan taɓa furtashi ga waniba koda kuwa ace Bilkisu ce ko Mama ko Jawaad. Amma hakan bawai yana nufin zan barku kucigaba da zama akan wannan hakalarba, kuji tsoron ALLAH, karku.........” da sauri Yaya Nasir ya ɗaga masa hannu, “Bama buƙatar ji”. Murmushi Yaya Abdull yay kawai yaɗan girgiza kansa, “Shikenan Yaya na bari, ALLAH ya ganar daku gaskiya idan kunada rabonta. Sai dai gaskiya koda zan haɗe wannan maganar a cikina bazan iya barin Sadi ya cigaba da sarrafa mugan ƙwayoyi ana cutar talakawa naba, dolene kodai ka rufe kamfaninka na sararafa magunguna, kokuma ni nasaka kwamitin bincike a kansa ƙarƙashin hukumar lafiya.......”

a fusace Alhaji Ali (Dad) yace, “Mi kake nufi Abdul!? Kenan zaka iya mana SARAN ƁOYE (littafina na zafafa 2021🤗😋) kenan bayan kasan mu duka nan munada hannun jari a wannan kamfanin hatta da kai kanka ka sakama ɗanka hannun jari zaka aikata hakan kuma?”. “Babu wani maganar Saran Ɓoye Alhaji Ali, inda Saran Ɓoye zan muku da bazan fito na faɗa muku ba ai, sannan da kake maganar na sakama Jay hanun Jari a ciki ALLAH shine shaidata bansan abinda kukeyi a ɓoyeba kenan ai, nidai ABINDA KE CIKIN ZUCIYA ta (Littafin Rano a Zafafa 2021🤗😋) na fito na faɗa muku, dan ALLAH ya kukeson nayi? Ku kune garkuwata, a wannan tafiyar, amma kundawo kuna meman sakani cikin SIRAƊIN RAYUWA (Littafin Huguma a zafafa 2021🤗😋) kuma? Dama kun dafamin bayane domin kuyi amfani dani wajen cimma burinku ko mi? To wlhy! Wlhy! Wlhy!! Kunji sau uku, bazan taɓa cutar da talakawana danna faranta mukuba, bakuma zan taɓa nisanta kaina da UBANGIJINA saboda ku ba, sirrinku kuwa zan riƙe, domin wanda ya halicceku na kallonku, nayi imani da KIBIYAR AJALI.....(Littafin Miss Xoxo na zafafa 2021🤗😋)  sulke baya tareta saita gitta wataran, duk abinda yay farko zaiyi ƙarshe. Karku sake zuwamin gida akan wanan maganar daga yau na rufeta, kuma har gaban abada bazata sake tashiba insha ALLAH”. Kallon tsoro suke masa sosai, Alhaji Kokino zaiyi magana Alhaji Ali ya hanashi, shinefa na taho ganin Yaya zai fito). Ajiyar zuciya na sauke da cigaba da kallon Rahmah tamkar a jikinta zan samu amsoshina, fassara maganganunta nake amma babu wadda na iya samawa fassarar data dace, haka na haƙura na barta ta tafi ɗakinsu saboda farkawar da Jawaad yayi baban yaji kukansa ya shigo. Ban tambayesaba a ranar sai bayan sati kusan ɗaya, sai dai ko uffan baice daniba balle na samu amsa, haka na cigaba da masa naci daga ƙarshe yace karna sake damunsa akan abinda bai shafeniba. Ranar haka muka yini ran kowa a ɓace ni da shi”.
      Ta sake share hawayenta tana shaƙar numfashi da ƙyar, saida Gambiya ta bata ruwa tasha sannan ta cigaba.
        Tun daga wannan lokacin na fahinci abubuwa sun ɗauki zafi tsakanin Abdul-aziz da su Sadi, sai dai yaƙi faɗa min komai duk yanda naso ji, kamar yanda yay alƙawari ya saka kwamitin bincike akan kamfanin magunguna na Sadi, wanda abin bai nisaba aka ƙwace kamfanin batare da am bayyanama duniya mi aka gano a cikiba, sai dai abin mamaki ko sati biyu ba'ai da amsarba aka maida masa abinsa. daga wannan lokacin kuma yanayin yanda Abdul-aziz ke gudanar da mulki ya fara canja taku, baya iyayin komai sai abinda su Sadi sukace, ikon ALLAH dai talakawan ƙasa basu fahimci hakanba sai mu dake a kusa da shi sosai. Hankalina ya tashi sosai, dan ko shawara na bashi akan abu ko Baba da Mama maryam suka bashi sai yace ba hakaba, ga abinda Sadi da Ali sukace, ma'ana dai yafi yarda da nasu. Cikin wata guda duk ya susuce komansa ya koma ƙarƙashin ikonsu, mulkinma dai tamkar sune suke yinsa bashi ba, dan komai akan ikonsu yake gudana, sai sunce yayi yakeyi, wanda kuma sukace kar yayi komai muhimmancin abun bazai yisaba. Tun yana ciwo a tsaitsaye harta kaisa ga kwanciya, da ƙyar ya amince Doctor yazo ya dubashi a wata ranar laraba, a gwajin farko aka gano ciwon hawan jini tattare da shi, sannan zuciyarsa na barazanar kamuwa da ciwo kuma. Hankalina ya tashi, na dinga masa kuka da roƙon ya sanarmin abinda ke damunsa ko shawara na bashi, amma yaƙi. Bayan kwana biyu ya cigaba da ƴan harkokinsa yana nunamin ya warke, amma ni nasan akwai wata a ƙasa tunda nasha ritsashi yana hawaye, sannan idan ya zauna shi kaɗai zaka samesa yayi jigum yana tunani. Sai kuma rama da ya ketayi a tsaye wadda Baba da Mama maryam suka kasa haƙuri suma sai da suka tambayeni ko lafiya?. gudun karsu tashi hankalinsu nace babu komai kai kawone kawai irin na shugabanci da kuma ɗan zazzaɓi da yay na kwana biyu. Sun masa addu'a daga haka muka bar maganar.
         Bayan kamar sati shida da tashinsa daga wannan ciwo sai ya ƙara kwanciya, wannan itace kwanciyar data zama ajalinsa, a ranar bai fita office ba duk da kasancewar ranar aikice, yanama da meeting da gwamnoni, amma hakan ya gagara. Wajen yamma sai ga Sa

di Kokino da Ali sunzo sun dubashi, ban kawo komai a rainaba na barsu daga su sai shi, ina ɗakina inama Jawaad shirin islamiyya sai ga Rahma da gudunta, sai dai tama kasa magana, hannuna kawai taja muka fito zuwa ɗakin da Abdul-aziz yake kwance. Sai dai muna kawo ƙofar ɗakin su Sadi na fitowa. Kallon Rahmah suka dingayi cikin wani yanayi daya sakani faɗin, “Lafiya kuwa? Miya faru?”. Cikin shashantar da zancen suka shiga gaisheni da tambayar jikinsa, tare da ɗorawa da faɗin ya kamata a sanar dan a fita dashi ƙasar U.S yaga likitan daya san aikinsa. Ban musa musu hakanba, dan nima ina buƙatar lafiyar mijina, na raɓasu na shige ɗakin sai na tadda Abdul-aziz a lulluɓe har fuskarsa, nai saurin matsawa na janye bargon. Ajiyar zuciya na sauke ganin idanunsa biyu, sai dai da alama hawaye yakeyi, amma jin motsina yay saurin sharewa ya maye fuskarsa da murmushi. Zama nai kusa dashi ina jera masa sannu, na shiga karanto addu'a kuma ina tofa masa kamar yanda ya buƙata, dan ya faɗamin jikinsa na masa zafi kamar ana hura wuta.
         Indai taƙaice muku a wanan dare  bamuyi barciba sam, washe gari muka wayi gari jikinsa ya rikice, da yayi tari sai jini, tun yanayi a ɓoye harna farga da hakan, sai dai ya hanani na faɗama kowa, a cewarsa zasu tafi asibiti gobe idan ALLAH ya kaimu zai samu sauƙi insha ALLAH. Badan hankalina ya kwantaba na yarda.
      Zuwa bayan sallar la'asar baba yaje gida ƴaɗan watsa ruwa dan tare damu ya yini sai ga Alhaji Ali (Dad) Alhaji Sadi Kokino, Alhaji Nasir (Uncle Nasir) da wasu mutane biyu daban saniba sunzo dubashi wai. Da yake muna falon ɗakin da yake kwance sai nace su shiga yana ciki, caraf Rahma ta riƙemin hannu tan girgizamin kai hawaye cike da idanunta amma ban fahimtaba, duk zatona damuwar ciwon nasane kawai, dan ita da Wasila tunda gari ya waye suke kuka, amma da yake Rahma tafi Wasila wayo a lokacin sai nata yafi yawa. Suna shigewa ta miƙe zaram ta kama hannuna tana nunamin ɗakin, mamaki abin ya bani na hau mata faɗa akan bata da bakine?. Har sannan bata tankaminba, kanta dai taketa faman jujjuyamin da fusgar hannuna muka zagaya ta Window.
        Ban taɓa ganin tashin hankali mai muni irin na wannan ranaba, dan kuwa zagaye muka hangi su Alhaji Kokino akan Abdul-aziz, sun lulluɓa masa wani jan ƙyalle suna wani kalar yare da su kaɗai suka san mi suke faɗa, duk yanda naso ɗaga ƙafa naje cikin ɗakin dagani har Rahma mun gagara hakan, a gaban idanunmu Nasir ya shiga zubama Abdul-aziz wani ruwa yana surkulle, sannan ya hau kansa yay....ya ya...yay fasiƙanci mafi muni da shi”. Umm-Anum ta ƙare maganar da fashewa da wani irin matsanancin kuka mai cin rai da zuciya, numfashin ta sai sama da ƙasa yake tamkar zata shiɗe.
      Tsitt falon yayi babu maiyin koda ƙwaƙwaran motsi, da alama dukansu sunyi suman zaune ne.
     Umm-Anum dake kuka tamkar ranta zai fita ta cigaba da faɗin, “Yana kuka da roƙonsa karya aikata masa wannan aiki maimuni, ga aman jini yanayi amma sam Nasir bai sauraresaba, sai da ya biya buƙatar zuciyarsa Ali ma yayi, Kokino ma Yayi. Duk muna kallonsu ni da Rahma, sai dai ko motsin kirki mun gazayi balle wani yunƙuri har suka fito suna kuka. Fitowarsu tayi dai-dai da dawowar baba tare da Mama Maryam. Sai ji kawai mukai suna faɗin Abdul-aziz ya rasu. Iya abinda naji kenan ban sake sanin mi nake cikiba sai a Saudia, shima ban tuna komaiba makamancin hakan sai shekaran jiya dana farka tamkar mai barci naga Anuwar da Abbunsu tare dani............✍
     

______________
ZAFAFA 2021
___________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS

BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Kwace wannan kodai itama su Dad sun ƙwamusheta ne🤣, na barku a gidan Alhaji babba kunata jira, yo sakawa sukai nimafa akai kidnapping ɗina, da ƙyar na fito a inda suka ɓoyeni😪🚶🏻🚴🏼.

Ku fara da waɗanan kafin na ƙara editing sauran na turo muku da safe idan ALLAH ya kaimu💃🏻. Yanzu kam mankaina ya tsiyaye sai an ɗura wani😣😪😫🚶🏻🚶🏻.
[2/17, 9:22 AM] HASNA: Page 63

....................Su Jawaad basu san wainar da ake toyawaba a gari, sai iface-iface suka dingaji da tashin hayaniya, sai kuma hayaƙi daketa turnuƙe sararin samaniya a hankali. Sai sukaga kuma mutane nata fita daga asibitin.
    Gaban Jay ya faɗi, ya zaro waya daga aljihu yay kiran Jabeer dan yaji ko lafiya?. “Boss wlhy akwai matsala, an fito da mutanen nan daga prison za'a kaisu kotu jama'ar gari sun tare motar sun banka mata fetur sun saka wuta. Wlhy duk yanda jami'an tsaro sukaso tsaidawa al'amarin ya gagara, harma an raunata mana ɗan sanda guda daketa ƙoƙarin basu kariya da roƙon mutane su kwantar da hankalinsu kotu za'a kaisu, kuma a yau za'a yanke musu hukunci. Amma sam basu sauraresaba, saima suka nema haɗawa dashi shima, dan acewarua shima nasune”. Innalillahi Jawaad keta ambata zufa na keto masa a duka sassan jikinsa. Dole yabar asibitin ya nufi inda al'amarin ke faruwa..

        Wuta taci su Alhaji kokino sosai kafin ƴan kwana-kwana suzo da masu bada taimakon gaggawa na jami'an tsaro, da ƙyar aka iya samun hanyama motar ta ƙarasa, police kuma suka fara jefa barkonon tsohuwa, da wannan damar aka samu mutane suka fara darewa har aka ƙarasa gasu Dad aka basu taimakon, sai dai kuma ina komai ya gama ƙurewa, dan wutar ta cisu sosai, sunta ihu da neman taimako basu samuba. Waɗanda basu mutunba ma da wahala ace zasu rayu, dan su Dad ko iya gane fuskokinsuma ba'ayi sam. A haka dai aka kwasosu zuwa General hospital inda su Bilkisu suke.
           Faruwar hakan yasa aka baza jami'an tsaron sintiri a kowane titi, tare da kafa dokar hana shiga da fita gaba ɗaya, kasuwanni da kowacce ma'aikata an rufesu ruf an kora mutane gidajensu. Garin yayi tsit, sai gidajen redio dana tv kawai ke aiki, anan mutane kejin halin da ake ciki.
         Kafin a ƙarasa dasu Dad asibiti wasunsu suka sake mutuwa, ciki harda Uncle Nasir kuwa. Suma dai an shiga da sune kawai, amma likitoci sunma rasa ta ina ya kamata su fara basu taimakon daya dace, gaba ɗaya jikinsu ya sale tas, yay jazur tamkar naman dake kusa da wuta ana masa gashi😭.
      Ba ƙaramin tashin hankali su Umm-Anum suka sake shigaba da ganin su Dad, duk da zalincin da sukaima rayuwarsu har hawaye sukai musu. Bama suba duk mai hankali yaga wannan bahagon al'amari dolene ya shiga ruɗani mai tsanani, ya kumaji tsoron wannan mummunar rayuwa da waɗanan mutane suka ƙirƙirar ma kawunansu. Gadai duniyar an tara, kuɗi, mulki, zuri'a, da komai amma an ƙare da tafiya a barsu cikin tozarci da wulaƙanci. Basu karesu daga faruwar kowanne irin bala'iba ko masifa ba, abinda suka tara da wanda suka shuka bai hanasu mutuwaba, bai hana ƙarshensu muniba, wannan shinefa ake kira da BA FARKON BA ƘARSHEN, yakai ɗan uwa bari murna akan aikata mummunan aiki kuma babu abinda ya sameka, bari tinƙaho da taƙama akan kai haƙƙin wani bai sakaka komai sai ƙiba da kwanciyar hankali, bari farin ciki kaine sama dakowa saboda kasancewarka azzalumi, bari taƙama da tinƙahon ka tara kai babu yanda aka iya da kai. Rage buri da hangen haramun domin kawai burge duniya ko morarta dayin bishasha a cikinta. Daure ka nema halak komai wahalarta da ƙaracinta, nisanta kanka daga haramun komai sauƙinta da zaƙinta. Ji tsoron UBANGIJI koda ace baka ganinsa to shifa yana kallonka. Kiyaye ruɗin duniya dana abokan banza ka kama ALLAH da abokan ƙwarai masu nuna maka muhimmancin tsoronsa. Ya ALLAH ka gafarta mana, kasa muyi ƙyaƙyƙyawan ƙarshe. ya rabbi ka ɗauki rayukanmu muna masu cike da ɗunbin tsoronka da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W)🙏🏻😭.

__________________________________

           Al'amura sun sake ƙwaɓewa, a gaba ɗaya kwanakin satin da suka biyo baya, babu wani farin ciki daga jama'ama balle su Jawaad da iyalan waɗanan mutane. An samo gawar Aunty Mah-Mah (Rahmah) a gidan Dad cikin wani akwatin tsafinsu, ashe lokacin da suka halakata wata gawar daban suka kawo a zuwan itace, shiyyasa Dad ya hana kowa yimata wanka shine yay mata a lokacin. To ashema ba gawarta baceba, gawarta na nan cikin ɗakin sirrinsa da ko Mom ta rantse bai taɓa barinta ta shigaba, ita kuma duk tunaninta bai taɓa kaiwa ga hakanba.
     Abin sha'awa da tsarkake sunan UBANGIJI gawar Rahma fes aka sameta dukda sheɗancin da Dad ya ɗauki tsahon shekaru yanayi da ita. Fuskarta fayau tamkar a yaune ALLAH ya ɗauki ranta. Bilkisu ta rungume gawar tana kuka abin tausayi. Da ƙyar Jawaad ya ɗagata akan gawar shima yana nasa hawayen da baisan suna zirarowaba. Alhaji babba kam yayi dauriya matuƙa, sai dai haɗiyar zuciya kawai yakeyi da kukan zuci. Umm-Anum tai mata wanka aka suturtata. Ɗunbin al'umma daga ɓangarori da dama suka sake sallatar gawar Rahama a karo na biyu, ta kuma samu rakkiyar ɗunbin jama'a zuwa makwancinta na gaskiya.
       An samo zunzurutun kuɗaɗe da kayan tsafi kala-kala da wasu abubuwan a gidan Dad, hakama Uncle Nasir da sauran abokan sheɗancinsu irinsu Kokino. Kamfanoninsu ma an samo abubuwa masu yawan gaske masu matuƙar tada hankali, ciki harda kayan shaye-shaye kala-kala da tabar wuwu buhu-buhu da adadinsa ya tasarma dubu goma. Sai wasu gurɓatattun abubuwan da bama zasu lissafuba gamai sauraro.
     Ƙasa tayi tsitt, manyan dake huɗar kasuwanci dasu data abokantaka sun fito sunata ALLAH wadai da nisanta kansu da ɓoyayyun ayyukan su Dad ɗin, komai dai ya fito fili, anyi walƙiya ijiya taga kowa da komai. Inda aka bar iyalansu da waɗanda aka zalunta irinsu Jay da jiyyar zukata.
     Idan kaga Bilkisu a irin wannan lokacin dole ka tausaya mata, ga laulayin ciki ga tashin hankali da damuwa, sauƙintama ƴan uwanta da mijinta kowa tattalinta yake da burin ganin farin cikinta. Takanyi kukan jin daɗi da ganin ƴan uwanta zagaye da ita, waɗanda ada ta rasa samu.

★★★★★★

         Ɓangaren Shahudah kam ba'a cewa komai, ita babban kukanta da tashin hankali bawai ya ta'allaƙa da halin da Dad yake ciki na halin rayuwa da mutuwa bane, babban tashin hankalinta shine ance babu aure tsakaninta da Jay sai dai idan sakin Bilkisu yayi kota mutu, amma bazai yuwu suyi zaman aure a ƙarƙashin miji guda ba ita da ƴar uwarta da suke Uban ɗaya.
      Hakan ba ƙaramin tada hankalinta yayiba, babu kunya babu tsoron ALLAH ta dinga tsinema Dad da jera masa ALLAH ya isa cikin hausarta da koma fitar kirki batayi. Ƙiri-ƙiri ta nema haukata kanta. Mom ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi itama, da abinda ya dameta zataji kokuwa da haukar Shahudah, ko ciwon mama atika, ko kuma nisantarsu da Qaseem yayi?. Dan tun bayan lafawar komai Qaseem ya ajiye aiki yabar ƙasar gaba ɗaya batare da kowa ya saniba sai daga baya sukeji ta hanyar saƙon daya bar musu.

       A yanzu kam kowa burinsa Jawaad da mahaifiyarsa da ɗan uwansa su yafe musu a wannan family, musamman ma waɗanda sukasan sun muzguna masa bisa jagorancin makircin mama Atika da ƴaƴanta.
             Dan samun lafiyar Mama Badiyya ta sake bayyana abinda ta gani Uncle Nasir nayi a wani dare bayan ɗakunansu shinefa ya banka mata baƙin asiri itama ya tauye rayuwarta ta koma ita ba'a duniyaba ba kuma a lahira ba😪.
      Jay dai bai samu zaman sauraren kowaba, dan shi a yanzu ta matarsa ma yakeyi da fatan samun nutsuwarta da abinda ke cikinta.

★★★★★

          A kwanakin da aka cika kwana goma da sakama su Dad wuta shima ya mutu da safe yana ihu da kururuwa kamar yanda su Uncle Nasir sukayi lokacin da suma zasu mutu, ga wani irin kakari maiban tashin hankali, jikinsa kuma ya koma fari fat tamkar babu jini a jiki, gashi dama wuta ta gama ɗaye fatar gaba ɗaya. Da yamma Alhaji Kokino yabi bayansa da Abban Zuhrah, kamar yanda aka binne su Uncle Nasir babu wanka saboda ƙunar jikinsu haka shima Dad dasu Abban Zuhrah aka haɗasu akai musu salla aka biznesu da halinsu. Wata shari'ar dai kam lallai tafi ƙarfin alƙalan duniya, sai dai a jiraceta daga sarkin alƙalai kuma😭🙏🏻.

     Haka rayuwa take su Dad sun tafi tamkar ba'ayusuba a duniyar dagasu har ayyukan da suka shuka, a hankali hankulan jama'a sun fara dawowa jikinsu daga abinda ya faru, sai kuma labarai da maida yanda akayi da har yanzun sun gaza ƙarewa. Yayinda akebin gidajen da suka bari ɗaya bayan ɗaya ana rushewa, wanda suke ciki kuwa ana barinma iyalansu dan su sami matsugunnin rufama kansu asiri. Masu ƙarfin imani a cikinsu kuwa sun tsame kansu daga komai na dukiyar acewarsu basa buƙata, dan dukiyace ta tsafi, sun gwammaci su ƙare rayuwarsu a talauci da su zauna a ƙarƙashin ikon dukiyar jinin al'umma.

BAYAN WATANNI BIYAR.

        Abubuwa sun sake lafawa, harma wasu da yawa sun faffaru, ciki kuwa harda komawar Umm-Anum Saudia tare da ƴan uwanta suka sauke faralin miƙama ALLAH godiya daya kawo musu ƙarshen komai cikin rahamarsa da hikimarsa. Bayan kammala aikin hajji su suka dawo ita kuma aka barta a can tare da mijinta da Anum, Anuwar dai kam yayi uwa yayi maɗaukiya a ƙasarsa

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment