Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan,ya tambayeta wancan, wata amsar ta bashi dariya, wata kuma tabashi tausayi, wata tambayar kuma tace bata gane ko suwa yake nufi ba,dan tun kan a haife ta fa,har suka gangaro kan yan uwanta.

Alhamdu Ya'yanshi nawa yanzu? Tad'an ta6e baki ita kanta tana dad'ewa bata ganshi ba"ai duk cikinsu Bitrus ne kawai yayi auran majami'a,amma Alhamdu ai gaba d'aya ya koma D one(D'orawa one)yana tsiran naman kare,baka ga yadda ya lalace ba saboda shaye-shayen miyagun k'wayoyi,amma watannin baya budurwar shi ta haihu ta kawo mana yarinyar data haifa mun gani.Yakad'a kai cikin damuwa,wannan irin rayuwa dame tayi kama?

Yakalleta ke kuma na ki Y'ayan guda nawane?Bazaice kaso nawa bisa d'ari ba dan ba shi da k'ididdiga amma dai ya san samun cikakkun 'yan mata(Virgin)a cikinsu,ba masu yawa bane saboda wata irin rayuwar san zuciya,taci barkatai da suka za6a suke yinta cikin kwanciyar hankali.Tagirgiza kai"Uncle ban ta6a haihuwa ba,kuma duk abinda muka yi da Baranzan"I repent"Ya yadda da ita,yajijjiga kai"toh ya karatu kin gama secondary ko anan zaki k'arasa?Ta ajiye kofin lemun a saman tebur sannan ta bud'e jakar hannunta taciro wani babban envelop ruwan k'asa ta mik'a mishi.

Yad'ago cikin mamaki da murmushin jin dad'in ganin sakamokon jarabawar ta na College of Education.Kinyi k'ok'ari kuma na yadda lallai baki tsaya shashanci ba"wai rok'o a gidan bebe"suka cigaba da tattauna al'amura mabambanta har Kasham tafad'a mishi gaba d'aya abinda yakawota.

Yakalleta lallai kin yadda za ki musulunta Kasham?"Eh Uncle na yadda zan musulunta.Yagyad'a kai"To ki sani musulunci yana da sharud'd'a guda biyar duk wanda kika ganshi a cikin musulunci to tabbaci hak'ik'a sai da ya yadda da wad'annan sharud'd'an, Sharad'in farko kuma mafi girma a cikin su shine kalmar shahada.

Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, bisa cancanta sai ALLAH,kuma Annabi Muhammad bawan shine kuma manzan shine.

Ma'anar kalmar {لاإله} tana kore duk wani abin bauta ne koma bayan ALLAH{إلاالله}wannan kuma tana tabbatar da bauta ne ga ALLAH shi kad'ai ba tare da abokin tarayya ba.

Sharud'd'an kalmar shahada kuma sune:
1.Ilimi wanda yake kawar da jahilci.
2.Yak'ini wanda yake kawar da kokwanto.
3.Ikhlasi wanda yake kawar da shirka.
4.Gaskiya wacce take kawar da k'arya.
5.Soyayya wacce take kawar da k'iyayya.
6.Janyuwa wajan yin aiki wacce ke kawar da k'in yin aiki.
7.Yadda wacce ke kawar da juyarwa.
8.Kafircewa da kin yadda da duk wani abin bauta koma bayan ALLAH.

Tare da sanin cikakken bayani danga ne da"Shahdatu anna Muhammadan rasulullah.

Ma'anar kuwa:Gasgata Manzon ALLAH a duk abinda yaba da labari,da yin biyayya ga abinda yayi umarni dashi,da nisantar abin da yaja kunne ko yayi hani dashi,da kuma bautawa ALLAH dai-dai da koyarwarshi.

Bayan wannan sai sauran sharud'd'an musulunci sune Sallah,Azumin watan Ramadan, Zakka ga wanda yake da dukiyar data kai nisabin yin Zakkar,Aikin Hajji ga wanda yasamu iko. Kingane ko?Naga ne Uncle, kuma na yadda da duk abinda kafad'a to yanzun nan za ki kar6i musulunci.

Ashhadu anla'ila ha'illallahu wahdahu laashari kalah...Wa ashhadu anna muhammadan abduhu wara suluhu.Yana fad'a tana fad'a har suka zo k'arshe. Yayi murmushi Alhamdulillahi yanzu kin zama musulma, ALLAH yamiki albarka. Acikin sunayan musulunci da kike ji wanne kike so a dinga kiranki dashi?Tad'anyi jimmm...na wucewar wasu dak'ik'u sannan tace"Uncle Sumayya nake so...Yayi murmushi ALLAHU-AKBAR kin za6i suna me daraja a tarihin addinin musulunci,Sumayya mace ta farko data kar6i addinin musulunci.


Tunda kin zama musulma to akwai wankan shiga musulunci dan haka nake so ki natsu kiga yadda zan kwatanta miki.Yadinga mata bayani dalla-dalla sannan yace ta mishi bayanin yagani inda tayi kuskure ya gyara mata.

"Dafarko tsarki zan fara sau uku,sai in wanke hannayena zuwa mad'aurin agogo sau uku,kurkure baki,shak'a ruwa a hanci da fyacewa sau uku,wanke fuska daga matsirar gashin kai zuwa k'arshen ha6a,daga gefen kunnan dama zuwa gefen kunnan hagu sau uku,wanke hannun dama zuwa gwiwar hannu sai uku,wanke hannun hagu zuwa gwiwar hannu sau uku,shafan kai daga matsirar gashin kai zuwa keya,a kuma dawo dashi da duka tafukan hannaye sau d'aya, sai shafan kunnuwa ciki da waje sau d'aya,wanke k'afar dama saman k'afa da tafin k'afar ko ina ya jike da ruwa zuwa k'wauri ko idan sawu sai an tabbatar ta wanku,ta hagu ma haka za a mata, wannan itace cikakkiyar alwala.

Sannan sai in zuba ruwa a kaina da duka tafukan hannayena in cuccud'a in tabbatar gashin kaina ya jik'e da ruwa,zanyi hakan har sau uku,sai in wanke barin jikina na dama har zuwa tafin k'afar dama,sai in wanke 6arin hagu har zuwa tafin k'afa,sai ingame jikina da ruwan in tabbatar ko ina ya jik'e da ruwa,lungu da sak'on jikina.

Idan kuma na so bayan nayi tsarki sai kawai ingame jikina tun daga kai har zuwa tafin k'afafuna da ruwa in cuccud'a ko ina nanma wanka yayi.Tad'an kalleshi amma Uncle wannan wanka zaifi dad'i a shower(shaya)ko?Yayi murmushi wannan sharhin kine amma ko ba shaya mutum idan yaso zaiyi abinshi.Kin burgeni yadda kika kowa kome dalla-dalla kamar yadda na fad'a miki,da alama zaki fahimci kome a d'an k'ank'anin lokaci.

Wannan wankan shi za kiyi duk lokacin da jinin al'adarki tad'auke,shi za kiyi idan janaba tasa meki, shi za kiyi idan jinin biki yadauke,bambancin dake tsakaninsu kawai wajan niyya ne.

Cikin d'an shakku takalleshi "to Uncle kana ganin Julaibib zai aure ni?Sumayya sanin gaibu sai ALLAH, tunda yafad'a miki ko zakiyi sallah shifa bazai iya auran kiba,amma babban abinda za ki fara yanzu shine addu'a"Allah ai maji rok'on bawane,ba kuma abinda ya gagara a wajan ubangiji".

Yanzu kinga za kiyi wankan tsarki amma dole fa sai kin cire wannan faratan roban(nail fixes)dan a addinin musulunci sa shi haramun ne,tad'auki abin yanke farce tafara k'ok'arin ciresu,data gama yakaita wani d'aki, kishiga kiyi wanka,d'akin yar uwan kice,kome yana zaune a muhallinshi Dammm...Zuciyar ta tabuga saboda irin wannan k'amshin a d'akinsu Julaibib ta ta6a jinshi wallahi ranar data mamayeshi tashiga.Ta tsuke baki kamar zata rufeshi tana zuk'e sassanyar k'amshin tabaki ta hanci tare da lumshe idanunta,tana wata kissima a zuci,wani murmushi ya su6uce mata wucewar dak'ik'u masu yawa, tasauke gwauran numfashi sannan tarage kayan jikinta tashiga wanka.

Yakoma D'akin-shakatawa yazauna, tunanin ya cika k'wak'walwarshi har baiji fitowar taba.Uncle na gama tafad'a lokacin da take k'ok'arin zama,ya kalli agogon dake d:aure a hannunshi lokacin sallar la'asar ya gabato.Yamik'e "zani masallaci,daga nan zan wuce in d'auko mutan gidan,ko kin jini shiru karki damu dan wata kila zamu had'u da cunkuson abubuwan hawa.Ta amsa da"to Uncle a dawo lafiya.Tad'auki wani littafi data gani a saman kujera"Islamic Perspectives On Reproduction, Health ChildBirth Spacing In Nigeria.Tafara karantawa.

Miqdad ne yafara dawowa a sanda rana ta tafi za ta fad'i magriba na shirin kunno kai,ya san ba kowa a gidan shi yasama yatafi da mukulli amma yana ta6a kofar yajita a bud'e,yasa kai cikin murmushi tare da sallama bak'uwar fuskar yagani a kwance tana karanta littafin da ya ajiye a saman kujera jiya da daddare, tamik'e zaune daga kwanciyar da tayi,tajuya inda taji sallamar Dammmm...Zuciyarshi ta buga da suka had'a idanu,Hafsa yake gani a fuskar ta,hatta manyan idanunta masu maik'o irin na Hafsa ne.

Tad'anyi murmushi"Sannu da zuwa. Yagyad'a kai"yauwa.Tanuna mishi kujera"kazauna mana, mutan gidan ba sa nann ne Uncle ya tafi d'auko su.Yasake kallanta jin tace Uncle wannan yar uwarsu ce ta Zonkwa yayi yar dariya sannnan ya zauna"kema sannunki da zuwa,daga Madauci ko?Tagyad'a kai.

Fara kiraye-kirayen sallar magriba daga mabambantan masallatai na nesa dana kusa yasa shi mik'ewa barinje masallaci? Bai jira amsar taba yajuya yafita.

Bayan sallar Isha'i suka shigo gaba d'ayansu dama Alhaji Hafiz ya fad'a musu kome tun a hanya.Hafsa ta rungumeta tana dariya "Yaya Sumayya ina tayaki murna da shiga addinin gaskiya.itama tasa hannayenta ta rungumeta tana murmushin jin dad'i suka saki juna suna kallan kallo.

Alhaji Hafiz ya kalleta"Sumayya wad'annan sune iyalina.Yanuna ta wannan Maman Hasan kenan kasancewar haihuwarta uku duk yan biyu take haifa kuma maza amma ba sa dad'ewa suke komawa ga Ubangijinmu,akan wannan yanuna Miqdad haihuwar tafara tsayawa daga shi sai Hafsa, Zuhair da Khadija.Takalli Miqdad"Ashe babban Bros d'inmu ne shine baka fad'a min ba?

Tamatsa wajan Maman Hasan tana gaishe ta"gaskiya Mama nima ina san yan biyu,kimin addu'a ALLAH yaba ni.Sukayi dariya dan bata wani nuna bak'unta ba kamar ta ta6a zama dasu.Maman Hasan ta jijjaga kai "ALLAH buwayi gagara koyo,duk wanda yakalli Sumayya ya kalli Hafsa yasan Yaya da kanwa ne,lallai jini abune me k'arfin gaske ko Khadija batayi kama da Hafsa ba kamar yadda Hafsa tayi kama da Sumayya.

Hafsa ta d'auko abinci amma ba wanda yaci dan a k'oshe suke sai Miqdad kawai yaci,yana gama ci Maman Hasan takalleshi d'auki abincin nan ka kaima almajirai tun kafin ya lalace.Yad'an 6ata fuska dan baiso fitaba"Maman Hasan yanzu a ina za a ga almijiri?Dare fa yayi.Tad'an harareshi"kai malami ba kasan gidan almajiran kasan layin nan bane? Yad'an shafa kai"na sani. To can za ka kai musu suma suci da d'uminshi.

Zuhair ya mik'e"Yaya Miqdad barin d'auka muje in rakaka.Yauwa Zuhair nagode.Suka fita Zuhair yana bashi labarin abinda yafaru d'azu a gidan Malam Muhammad Aminu (Kakansu).

Sunyi hira sosai suna dad'a wayar mata da kai,ita kuma duk abinda bata gane ba kai tsaye zata tambaya karfe goma Alhaji Hafiz yakallesu to ya kamata kowa yaje yakwanta haka, Sumayya sai ALLAH ya kaimu gobe zamu fara karatu.Hafsa tamik'e"Baba Insha-ALLAH yanzu kafin muyi bacci zamu fara.Yagyad'a kai cikin gamsuwa"yauwa Hafsa ALLAH yamiki albarka.Su kayima juna saida safe.

Hafsa matashiyar budurwa me ji da ilimin addini dana zamani,ajinta biyar Secondary a fanni kimiyya (Science)Suka shige d'akin baccinsu suna jin k'aunar junansu a zuciya.Taje tayi alwala tafito sannan takalleta "Yaya Sumayya kema kije kiyi alwala ganin tana shirin kwanciya.Alwala kuma Hafsa?Ba d'azu nayi alwala nayi sallar...tayi shiru sallar me ma?Ta tambayi Hafsa.Sallar Isha'i.Hafsa tabata amsa tana murmushi.Tagyad'a kai Yauwa shi.Hafsa ta zauna a gefen gadon "wannan alwalar idan za a kwanta bacci a keyin ta dan ita kariyace daga shaid'anu,shifa zama da alwala yana ba mutum kariya sosai a rayuwa amma ba kowa yake iya jure yiba,shi yasa Baba da Yaya Miqdad suke burgeni saboda sun rike wannan,wallahi basa zama ba alwala,nima dai wasu lukutan nakan kwatanta.

Mako d'aya,biyu,uku shiru makatau balaguro a lahira,ba Kasham ba labarinta.Rahab taja dogon tsaki saboda gajiya dajin mitan da Maman take yi a kan rashin dawowar Kasham. Tadago takalleta"To wai menene abin damuwa dan har yanzu bata dawo ba? Kasham fa ba k'aramar yarinya bace.Yakike irin wannan maganar Rahab?Kasham ba 'ya ta bace, ya bazan damu ba.Yar kice amma kin san lafiya ita kesa aji mutum shiru, tad'anyi murmushi amma Mama kema sometimes bakya ganewa...ta tari numfashin ta kamar ya bana ganewa? Rahab tamik'e zaune daga kwanciyar da tayi ta d'an ta6e baki"ni wallahi na san ba yadda za ayi Kasham tayi wad'annan makonnin a Ramai,ni nafi kyautata zatan tana cikin gari wajan saurayin nan data nace tana so.Tadaki kirjinta da karfi"Jesus christ...ta jijjaga kai lallai biri yayi kama da mutum ni banyi wannan tunanin ba,yanzu barin shirya intafi Ramai d'in ga kai ga k'afa ai ba tambayar me aka yanka.

Matina tana zaune a shagon kitson attachment d'inta ta hagonta Tamik'e dasauri ta tarota "oyoyo Mama sannu da zuwa"tabata wajen zama sannan ta kar6o mata ruwa da lemon mirinda da manyan cincin guda biyar a faranti. Tazauna suka gaisa.Mama kwana biyu ni da Kasham ba wanda yakawo ma wani ziyara,ni dama wannan Sunday d'in zanzo. Tafara girgiza kai tana tafa hannaye"Jesus Christ"Kina nufin Kasham bata wajanki makonni uku da suka wuce?Tace an miki Operation za tazo gaisheki? Matina ta kama ha6a"kaji muguwa zata jazamin masifa to ni Mama lafiya ta kalau ba abinda akamin.Takad'a kai"wato gaskiya ne abinda Rahab tafad'a Kasham tana cikin gari wajan wannan tsinannan bahaushen?Anya Mama Kasham tana wajan Julabib?Kin san yace bazai aureta ba...Ke tafi can idan takai mishi kanta yana ganin ta fad'i gasassa zai yi wani yunk'urin korarta ne?Matina tagirgiza kai"Kin san ALLAH Kasham bata wajan D'an Sarai dan bata ta6a 6oye min kome game dashi ba, kinga ko a makaranta bai tsaya kulata ba dan bata gabanshi,lokacin nema yake zaune zaman yanci da aikata abinda yake so dan ba idanun wani babba na shi,bare kuma yanzu dayake cikin iyaye da yan uwa?

Tina nifa ban yadda ba idan kin san gidansu kawai ta shi mutafi ki rakani,tasan gidan har shagonshi sun ta6a zuwa da Kasham, to amma ta san halin Mama bata da kirki,yanzu zataje ta tada hayaniya bayan ta san wallahi Kasham bata wajanshi,to sai dai itama ta fara tunani ina Kasham za ta tafi tayi wannan dad'ewar?Bata saba haka ba dole kuwa Mama ta damu, amma dayake Judith da halin tane haka ai bata ma maganar ta sai ranar da aka ganta kawai.

Shiru na nucewar wasu dak'ik'u zuwa can Tina ta numfasa"Mama na fi tunanin Kasham tana Kaduna?Cikin rashin fahimta tace Kaduna kuma?To wajan wa?Ko tayi sabon saurayine a can?Kasham bata da wani saurayi acan,sai dai kwanaki tafad'a min matuk'ar za ku takura mata,ku hanata auran Julaibub to lallai zata koma wajan Uncle d'inta dayake sallah.Tadafe kirjinta dan taji kamar ruguzowar wani abu a zuciyarta,ranta in yayi dubu ya 6aci.Takalli Tina "nagode,gobe dole zan tafi Kaduna na rantse da ALLAH ban haifi yarinyar da zatayi sallah ina numfashi a doron k'asa da raina da lafiya ta ba, Kasham taci k'arya ta kwana da yunwa ta tashi a rame.To maji magani an binne tsohuwa da rai.

Cikin rashin sa a ta isa Kaduna,sai dai almajirai ta tarar agidan bayan sun gaisa da malamin take tambayarshi Alhaji Hafiz yad'an kama baki "Wai wai wai ai Alhaji Hafiz yafi shekara goma sha biyar da barin gidan nan,danshi yabani yace halak malak acigaba da koyarwa, kuma yanzu hakama basa k'asarnan shida Iyalinshi sun tafi aikin hajji.To ko kasan unguwar daya koma? Ban rik'e sunan ba,saboda shi lokaci zuwa lokaci yana zuwa mu gaisa,amma Lado ya sani.

Kai Lado...Lado dayake biyama wasu almajirai karatu yad'ago yakalli Malam,Malam ya yafito shi da hannu zo mana.Yak'araso cikin ladabi.Ya sunan unguwar da Alhaji Hafiz yakoma? Ya amsa da ladabi unguwan Kanawa,amma Malam kafin tafiyarsu aikin hajjinnan mun had'u da Miqdad yace sun tashi sun koma Unguwan Rimi G.R.A inzo muje inga gidan,ni kuma ranar baka nan ni zanma yara darasu shi yasa ban bishi ba, amma na san idan sun dawo zaizo har nan ya daukeni muje.Malam yace"to kinji ko?Tayad'a kai tamusu godiya.

Tadawo gida agajiye lik'is ga mugun 6acin rai,tadinga zagin Shedrak zagin tsamen nama tun mijinta yana tayata har abin ya isheshi yayi shiru dan abun na ta ya wuce makad'i da rawa,zagin shi takeyi kamar cin kwan makauniya, yadda take mishi tofin alatsine sai yaji ba dad'i "Lallai na ka na kane ko ya cinyeka bazai tauna k'ashin ba"ai koda suka yafeshi suka barma musulmai shi amma dai ai still blood brother d'in shine.

Dakarfi yabuga sandar hannunshi a k'asa"Wannan zagin da kike ma Shedrak ya isa haka for what?Tanunashi da yatsa Shedrak d'inne baka so a zaga?To an zageshi matsiyaci kawai,ai dama yadad'e yana mana wannan mugun baki "Dinatu ya ishe kifa" yafad'a a tsawace dan banga abinda yamiki ba,shine yazo yatasa k'eyar Kasham sai sun tafi koko itace ta saci jiki tafi har inda yake?

Ta tafa hannaye cikin bala'i"Holy Mary mother of christ yanzu saboda Shedrak kake min wannan hayagagar...Ashe kai munafiki ne, tunda har kake fad'a dani akan masu sallah?To kasani tayi d'as d'as d'as dayan yatsunta"as from today an daina dafa abinci a gidan nan kowa yazage yanemi kud'i yaciyar da kanshi,idan Kasham tadawo shikenan everything will be normal.

Jikinshi yayi sanyi,fushin daya taso dashi yane mishi yarasa,sai yakoma rarrashi madadin shi da za a rarrasa"hun kud'i k'are magana.Yaro da kud'i abokin tafiyar manya.Hajiya naira Zainabu-Abu me maganin surukan zamani... Inji Sadi Sidi Sharifai.ALLAH ka azurtamu da arzik'i na halali.ALLAH muna niman tsarinka daga masifar talauci👏.Idan tahana shi abinci ai ya kad'e har ganyanshi, baya aikin kome,tunda aka sallameshi daga leburancin daya keyi na titin jirgin k'asa,to dama aikin ba wani na azo a gani bane,sai dai motsi yafi la6ewa indai ba niman ka a keyi ba...


Dabara ba ta d'aure kaya dole sai da igiya.


6 Jumaada Awwal 1441
1 January 2020


We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.




DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFI💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na goma sha d'aya.



Hajiya Sumayya Kantiok Donatus...

Ta canja tayi kyau na ban mamaki, kome na musulunci ya fara ratsa ta,sai dai ko a d'awafi baiwar ALLAN nan bata manta da Julaibib ba.Kullum addu'arta ALLAH yamallaka mata shi yazama mijinta,dan ita har kwanan gobe bata ga wani namiji kamar Julaibib ba.

Makonsu biyu da dawowa tafara zuwa makaranta Sanawiyya kansancewar ta me k'wak'wa da san karatun kullum iliminta k'aruwa yake yi,dan addu'o'in cikin Hisnul-Muslim wallahi kad'an ne bata haddace ba,a kwaita da tambaya sai kuma akayi sa a mutan gidan suna da ilimi dai-dai gwargwado suna mata bayanin kome dalla-dalla ba jibge.

Maman Hasan tabita da kallan tausayi"Iska na wahalar da me kayan kara"ta tsuniyar gizo ba ta wuce k'ok'i"Julaibib,D'an Sarai ko Enigma Man,wad'annan sunayan dai duk wayewar garin ALLAH sai ta kira d'aya daga cikin su,sun san labarin Julaibib a baki duk da basu ta6a ganin shiba.

Rannan dai Miqdad ya galla mata harara"Ke malama kar ki damume da maganar wani D'ansarai mutumin da ko hoton shi baki dashi.Wani lallausan murmushi yasu6uce mata"na rantse maka da ALLAH inada hotunanshi,ni ban san yadda akayi da nazo nan ban gansuba ina tunanin Lidiya ce ta bincike min jaka ta kwashe su amma da hannuna na sakasu.Bros karka damu duk ranar danaje Zonkwa bazan dawoba sai da hotunan shi"za kaga kyakkyawan bak'in mutumi na,me tsabta,ma'abocin sa fararan kaya.

Sumayya...a d'an firgice tad'ago sannan ta amsa"Na'am.Lafiya kika zabga wannan tagumin?Takad'a kai kwallah sun cika idanunta tamaida kanta jikin kujeran dan ba ta so su zubo "Maman Hasan Julaibib ne na kasa yin yak'i da zuciyata wajan cireshi a cikinta, kullum sai na yi mafarkin shi sai dai ban kwanta bacci ba me yasa?Saboda abinda kika sa a zuciyarki kenan tunanin shi,duk abinda ka kwallafa rai da shi to a mafi yawan lokaci sai kayi mafarkin shi"sa rai a ci shi ke kawo jin yunwa"

Takamo hannayenta,Sumayya ki fahimci wani abu"D'an Adam da kike ganinshi to shi yake saima kanshi mutunci da daraja,shi zai kame kanshi sannan mutane su d'aukeshi da mutunci su girmama shi"Haja ita takema kanta kud'i.kin damu dashi da yawa,sannan abin takaicin bai san kina yi ba harara a duhu..kilama ya manta ya ta6a ganinki,shi yana can hankalin shi a kwance yana gudanar da al'amuran rayuwar shi,ke kina nan kin takure kanki cikin tunanin shi"wannan fa kamar aikin banza ne sammakon gaida mak'iyi.

...Julaibib yana da matar aure makaranta ake jira tagama musha biki,kuma k'anwata ce...kalaman matar Musaddiq kenan ranar dataje musu murnar aure...

Tasauke numfashi"to amma ai banyi laifi ba ko a addinance.Maman Hasan tajijjiga kai"kwarai kuwa bakiyi laifi ba,hakan ya halatta sai dai a yadda muka saba a al'adance namijine yake furta hakan ga 'ya mace,saboda kawaici irin na Hausa-Fulani,sai dai ban san sauran al'ummatai ba,ba kasafai matan suke yin haka ba.Kiyita addu'a ALLAH alhakimune ba yadda ba ya shirya al'amura. Jikinta yayi sanyi ba wata gaskiya bayan wannan"a hankali tayi furucin nagode Maman Hasan da wannan tunatarwa.

Miqdad yafito daga d'akinshi yana karya hula.Sumayya tabishi da kallo yanayi da d'abi'unshi suna mata shige dana D'ansarai shima ma'abocin sa fararan kayane.Yayi murmushi ganin kallan

Please Login or Register in order to submit comment