Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigowa sabuwar shekarar musulunci.Me maka fatan alheri a rayuwa.Musha ruwa lafiya...

Sumayya Kantiok Donatus(Kasham)

Dammm...zuciyar shi tabuga da k'arfin gaske.Sumayya...Sumayya yafad'a ya maimaita cikin san tantance wai wace Sumayyar?Yad'auki wasik'ar yakaranta yasake karantawa,kenan ita ce Amira Sumayya da ta musu lecture akan"Media Influence?(Tasirin kafofin sadarwa)Kasham dai daya sani wacce sukayi College of Education ita ce ta musulun ta?ALLAH buwayi gagara misali,ko shekaran jiya sun samu sak'o ta k'ark'ashin k'ungiyar da take jagoran ta akan Islamic Vacation Conference(IVC)yayi zuru cikin tunano wasu kalamanta da suka ta6a had'uwa da ita a wata seminar da akayi a"National Teachers Institute Kaduna akan"Post Primary Institution Programmed"(PPIP)alokacin ta d'aga hannu aka bata damar yin magana"Tace a gajeran tunani na a kirashi da Propaganda zai fi armashi fiye da Program... bata gama rufe baki ba d'akin yad'auki kabbara kowa yayi na'am da hakan,wallahi shi yasha jin wannan sunan Sumayya Kantiok Donatus to sai dai ko sau d'aya bai ta6a tunanin wai Kasham ce ba...Yatuna ranar farko da daddare a wajan seminar abincin alfarma me rai da motsi aka aiko mishi dashi wai inji Amira Sumayya to ganin sauran ma an basu sai bai kawo kome ba"ashe albarkacin kaza k'adangare kan sha ruwan kasko

"Amira... Sumayya Kantiok Donatus...

Yafurta sunan a zuci...sai yaji wani irin yanayi ya ziyarci ilahirin gangar jiki da zuciyar shi game ita na farin ciki.Ashe shine bai gane taba saboda nikabin data sa,har da gilashin data rufe idanunta"Ina mana barka da shigowa sabuwar shekarar musulunci.Musha ruwa lafiya"abinda ta rubuta a k'arshen wasik'arta kenan.Yajijjiga kai "Tabbas yau goma ga watan"Muharram"yau kuma ga duk musulmin daya samu iko yana azumin "Ashura"Itama tana azumin kenan kamar yadda shima yake yi?Yakad'a kai cikin farin ciki.

"Sumayya ina miki fatan alheri a rayuwa,ALLAH yadauwamar dake a musulunci har k'arshen numfashin ki,ALLAH yaba ki mijin da zai rik'eki da amana,mijin da zai ha6aka miki ki cigaba a rayuwa...

Yad'auki jakar ya rataya a kafad'a yana kulle shagon sai ko ya hango wani d'an k'auyan su Kasham daya ke aikin share-share a Fajumali-Hotel yakira shi...yak'ara so da fara'ar shi"idan kaji gangami da labari,wallahi kamar ka san yunwa nake ji.Yakalleshi da natsuwa ai ba abinci na ce zan ba kaba,kuma ai yanzu lokacin cin abincin rana ya wuce k'arfe hud'u da rabi na yammaci fa?Yabuga k'atuwar hamma baki a bud'e kai da kake a k'oshe kenan wallahi rabo na da abinci tun daren jiya sai yan kame-kame dana yi da safe,ka taimaka min da abinda zan sai abinci dan ALLAH.

Yagirgiza kai"K'wandala ta bazan ba kaba tunda na san mashayar D'one za ta tafi...zai fara mishi rantse-rantse yakatse shi da sauri"kaga in dai yunwar da gaske kake ji to jeka katako kace ma Umma tabaka tuwo na yadda zai isheka in jini...Yad'aga hannayen shi sama"Praise the Lord,Thank you God"yajuya da sauri yaje ya kar6o yazauna zai faraci Julaibib yasake kallanshi cikin natsuwa"Kasham tana ina ne yanzu? Kasham...Kasham... yakalli Julaibib wace Kasham d'in?Kasham kanwar su Alhamdu.Yata6e baki "Kasham ai ta dad'e da barin gida wai ta zama me sallah irin ku,ance wai tana Kaduna amma ni"I don't give a damme ko ma a ina take da me take yi fa.Hakane to idan ka gama ka mayar mata da kwanan.Yajuya yayi tafiyar shi...


Sautu a kasuwar wauta jahilci.


14 Jumaada Awwal 1441
9 January 2020

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.




DANGIN NONO WRITERS ASSICIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFIđź’”



Almost true story
Daga alk'alaminđź–Š
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na goma sha uku.



Rana ba ta k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya,ranar juma'ar d'aya ga watan Rabi'a Thani aka d'aura auran Salim da Sumayya,Miqdad da Zainab a ranar kuma ko wacce ta tare a gidan mijinta,sai dai mahaifin Kasham bai samu zuwa ba saboda zazzabin da yake yi.

Sumayya sune zaune lafiya suna da fahimtar juna,suna ma juna uziri shi yasa suke da kwanciyar hankali,suna kuma fatan hakan yad'ore har k'arshen numfashin su.

Yana karya hular k'uben dazai sa tashigo da sallama,ta kar6i hular tak'arasa karyawa tasa mishi. Yad'anyi gyaran murya"Ya dai Sumayya yau fa na ganki wata iri.Me ka gani? Shiru yayi yana mata kallan nazari "banga kome a fuskar kiba amma yana yinki ya nuna akwai wani abu,yadafa kafad'arta "kar kiji kome Sumayya ni mijin kine,ba ki da wanda za ki fad'ama damuwar ki sama dani.

Yamata wani kallo"Sumayya mecece matsalar?Fad'a min in har akwai wannan amincin dake cikin zaman na mu. Tamayar da turaran data gama fesa mishi sannan tajuyo cikin d'an murmushi"Miji na nawa ni kad'ai ko?Yagirgiza kai"ai na fad'a miki Sumayya a yanzu bani da buk'atar sake aure,kuma in dai zaman na mu yad'ore a haka to ai ko kin isheni rayuwar duniya, yakalleta amma fa ba alk'awari na miki daga ke ba wata har abadan duniya ba.Tajijjiga kai"d'aya daga cikin abubuwan da suke k'aramin k'aunar ka a zuciya ta kenan fad'ar gaskiya kome d'acin ta. Sukayi murmushi.

Tasake kallanshi cikin natsuwa"tun daren jiya nayi mafarkin Mama kuma har yanzu mafarkin ya tsaya min a rai sosai,dan haka nake neman alfarma kabarni in je in ganta,ka san Uncle ya hanani zuwa wai sai nayi aure idan miji na ya barni shikenan ban san dalilin shi na hakan ba.A yanzu na san kima da girman da uwa take dashi,lallai ta cancanci a mata kome dan a samu albarkar ta, rayuwa tayi kyau duk da rashin sallar da ba tayi, ina san ganinta kewar ta ta dameni,zan kuma yi k'ok'ari wajan ganin na shawo kanta mun dai-dai ta,wata kila tsawon shekarun da mukayi bamu sa juna a cikin idanu ba yasa idan taganni ta yafe min,ni dai ina ta addu'a ALLAH yasa sanyi a zuciyar ta,na san ba abinda yafi k'arfin Ubangijin mu.Yajijjiga kai"gaskiya ne Sumayya iyaye suna da girma da daraja a wajan Ya'yansu, a addinin mu na musulunci suna da mafificiyar daraja sama da kowa.To yaushe kike so mutafi? Bani da za6i,sa mana lokaci.Yad'auki agogon shi yana d'aurawa "Shikenan za muyi magana da Alhaji idan naje kasuwa.To nagode.Yayi murmushi kawai

Tafiyar Dinatu Kaduna waja taransu na zumuntar mata a babban majami'ar su dake Sabon Tasha"Evangelical Church Winning All" (ECWA)na tsawon makonni biyu yabashi damar gyare-gyaran dayace zai yi, gidan yafito rasss har da sabon fenti ko'ina yanata kyalli.Ranar data dawo ta cika da mad'aukakin mamaki tana ka me da ha6a take tambayar shi"ni dai tun kafin in tafi Kaduna da ma na lura da wasu canje-canje saboda yawan kashe kud'in da kake yi,kai ko a ina ka samu mak'udan kud'ad'en da kayi wannan gyaran?Anya kuwa Baban Alhamdu ba ka daga cikin masu zuwa cikin gari suna fasa shagunan hausawa?Dama kwanakin nan abinda ake ta musu kenan.

Yagalla mata harara"ai kema kin sani ko lokacin dana ke ganiyar k'uruciya banyi sata ba,bare yanzu da girmana da kome ALLAH yasauwake.To me kake siyarwa da bazan yi tunanin haka ba?Ba kome. Tazuba mishi idanu "gaskiyar magana bazan yadda dakai ba in dai ba fad'a min in da kasa mo kud'in nan kayi ba. Yamik'e"ai nima ba so nake yi ki yadda dani d'in ba. Tabishi da kallo har yafita.

Da daddare har ya fara bacci ta tashe shi,fuska a yamutse yake kallan ta dan yanzu shima ya daina d'aukar raini tunda hatimin nasaran nan yana dashi"lafiya kin katsemin bacci kuma baki ce kome ba?"Baban Alhamdu please... kafad'a min in da kake samun kud'i,dan hankali na ya k'i kwanciya.Yasake d'aure fuska"Brother na Shedrak shi ya aiko min da cheque na mak'udan kud'ad'e,kuma ina so ki sani Kasham tabbas tana wajan shi,kuma tana sallah, bayan haka ma tayi auri wancan watan, na so zuwa ma to sai dai zazza6in dana yi yahana ni tafiya kuma suna nan zuwa, ina fata yanzu hankalin ki zai kwanta.


Tadaki k'irji cikin ambaton Yesu alhamisu me ce to(Jesus Christ)tamik'e cikin tafasar zuciya"Kasham tana sallah bayan haka ma ta yi aure ni mahaifiyar ta ba tare da sani na ba?Tayi d'as da yan yatsunta ban ta6a sanin kai munafiki bane sai yau,wato ka tura Kasham taje tayi sallah dan adinga kawo maka kud'i ko?Haba no wonder baka wani nuna damuwar ka lokacin da muka neme ta muka rasa.Wallahi tirrr...da halin ka,kai munafikin addini ne tunda kana supporting masu sallah tacika gidan da hayagaga...

Da abin ya ishe shi shima ya daka mata tsawa kin dameni fa,ki rufe ma mutane baki ke baki san dare bane?Tagirgiza kai, ai idan kaga na yi shiru to kafad'a min in da Shedrak yake a Kaduna gobe in buga sammako in d'auko yarinya ta dan bazan barma wasu tsinannun hausawa ba.Yayi shiru kamar ba dashi take magana ba,zuwan ca kuma ya d'ago ya kalleta"To tunda baza kiyi shiru ba, bari kiji kafin ki tafi Kaduna ni zan rigaki yin sammmakon tafiya,kuma na rantse miki da ALLAH tafiya ta bata dawowa bace,nima na bar gidan nan kenan har abadan duniya muje muci gaba da yin sallah sai in ga wanda zaki dinga wanke ma hannu a ka.Taja dogon tsaki "karka bari sai da safe yanzu ma kahad'a kayan ka dan ka tafi sai me?Mutuwa za a fasa ko hijabi? Tajuya garammm tabugo k'ofar,sai dai fa maimakon bacci yayi awon gaba da ita kamar yadda suka sa ba duk dare sai tane mishi tarasa sai kalaman mijin ta suka dinga dawo mata.

Kusan mako d'aya kenan bataje kasuwa ba wai dan kar yatafi Kaduna bata sani ba,yayi dariya Dinatu kenan idan nayi niyyar tafiya Kaduna zaman ki acikin gidan nan bazai hanani tafiya ba...Dan ALLAH ba wannan nake san jiba,kace kawai ka fasa tafiya,kayi hak'uri da abinda na maka raina ne ya 6aci kayi hak'uri. Yakalleta ai dama kece za ki sani tafiya ba tare dana shirya hakan ba, amma idan muna zaune lafiya ai bazan yi tunanin tafiya wani waje ba tare dake ba"we're together for better for wost till death due part us.

Yana waya tashigo D'akin-shak'atawar ta zauna a hannun kujerar daya ke zaune tana kallan shi, ganin wayar ta k'i k'arewa yasa tamik'e zuwa taga,tad'aga labulan tagar tana kallan mutane na kai kawo a cikin yamma cin.Bataji zuwan shi ba sai maganar shi taji cikin rad'a, tajuyo da sauri tana yar dariya"Kai Salim da girman ka da kome kake irin wannan furucin? Yagalla mata harara "Kaji yar rainin hankali ke kuma...sai ta sunkwui da kai tana murmushi.Toh shi kenan adai bar kaza cikin gashinta kawai.Ta girgiza kai"Uh uh gwamma kawai a yankata a dafata acinye ta kowa ma ya huta.Yamata wani kallo cikin d'an d'age gira,itama tarama irin kallan da manyan idanunta masu maik'o sai ko ya kyalkyale da dariya"Hun Sumayya me duniya...Za ko a yi yadda kika ce da kazar, tad'an motsa kafad'a, sukayi murmushi.

Yakalleta cikin natsuwa"to ya jikin na ki? Abinda yadawo dani daga kasuwa kenan dan na kira wayarki ta ki shiga matsalar sadarwa"naji sauk'i sai dai bani da k'arfi kuma bakina ba d'and'ano.Yagayad'a kai"to Alhamdulillahi, k'arfin jikin sai a hankali za ki da wo dai-dai,ya6are vitamin c guda d'aya yasa mata a baki.

Yakamo hannunta suka zauna a kujera "kuma na zo miki da wani albishir.Albishir?ta tambaye shi"eh albishir.Tayi murmushi fad'i albishir d'inka yanzun nan in wanke ka tasss...da ruwan tukwuici.Yakalleta da natsuwa yana murmushi"d'azu munyi magana da Alhaji akan tafiyar mu Zonkwa ya ce idan mun shirya shima a shirye yake musa rana, to nafad'a mishi jibi idan ALLAH yabamu a ran rai da lafiyar za mutafi,dan haka sai ki fara shiri yau,gobe da sassafe zan tafi kasuwa duk abinda kike so asiyo sai ki fara rubuta shi tun yanzu kin gane ko?Wani dad'i yamamayi zuciyar ta sai ta dad'a jinta garau ba sauran ciwo,ta k'ank'ame shi cikin murna"nagode mijina lallai ka cancanci tukwuici sai ta fara mishi wani irin salo na ta,da sauri ya k'waci kanshi yana dariya har hular shi tana fad'uwa"Ke wannan ne tukwuici?Ni na zaci wasu mak'udan kud'ad'e za ki sa min a asusun ajiya ta ta gidan kud'i?Tagirgiza kai"A ah wannan ai somin ta6i ne"tayi furucin da wani salo irin na shagwa6a. Yagayada kai"ah nima na aga alama to amma jama'a na jira na akasuwa amin afuwa sai na dawo anjima.Tam adawo lafiya suka d'aga hannu suna ma juna adabo🙋

Cikin nishadi suke tafiyar Alhaji Hafiz da Sumayya suna fad'a musu sunayan garuruwa da k'auyaukan da suke ta wucewa,sannu a hankali har suka shiga garin Zonkwa.Alhaji Hafiz yajuya yana kallan Maman Hasan"yanzu zamu shiga shalkwatar k'aramar hukumar Zongon-Kataf sai ku bud'e idanu ku fara kallo "tafiya mabud'in ilmi "Hafsa tace Zongon-Kataf d'in na gaba kenan?Eh Hafsa yana gaba ina gama idan zamu koma tacan zamu biya kuga garin sai mu bi ta Pambegua mu kuma gida.

Jikin Sumayya yayi sanyi tunda matuk'in motar Miqdad yakusa shiga k'auyansu Madauci dan ta san halin Mamanta bata da mutunci "ALLAH kamin maganin abinda bazan iyaba...bani da kowa sai kai...

Sumayya...

A sama taji kiran Alhaji Hafiz"na'am Uncle me kace? Nace na ga an samu cigaba me yawan gaske,kinga wancan asibitin?Takalli asibitin"Eh Uncle.Da nanne wajan da muke buga k'wallon k'afa.Sukayi dariya, Zuhair yace dama Baba kayi wasan k'wallon k'afa?Eh Zuhair amma da ne.Yad'anyi tsallan murna"nima daga yau zan dage in koyi buga k'walan k'afa.Yakalleshi da kulawa "a ah Zuhair bana maka sha'awar k'wallan k'afa,na fiso kayi karatu sosai kazama"Cheif Judge"ko ka fasa zama alkali me adalcin ne? Yakyalkyale da dariya yana bud'e idanun shi"Wallahi ban bafasa ba.Yauwa Zuhair d'ina ALLAH yamaka albarka.

A inuwar barankacin k'ofar gidan Miqdad ya tsaida motar,yabi gidan da kallo an gyara shi gwanin sha'awa,ba kamar zuwan da yayi watan nin baya ba,itama Sumayya abin ya mata dad'i tana rik'e da hannun matar Yaya Miqdad Zainab suka shiga gidan da sallama" Baban na ta kamar ko yaushe yana zaune shi kad'ai a tsakar gidan yayi tagumi da duka hannayen shi"labarin zuciya a tambayi fuska,ranshi a 6ace yake,yasa hannu ya share hawayan da ya zubo mishi sharrr...yana d'ago kai idanun su ya had'u yamik'e da sauri da sauri cikin mad'aukakin mamaki"


Kasham...yanunata Kasham ke ce?

A sanyaye ta amsa"na'am Baba...

"Kasham kece nake gani haka? Halelujah suka rungume juna cikin murna"naji dad'in ganin ki Kasham...


Hankalin ta yad'an kwanta ganin shima ya saki ranshi"Baba ai bamu kad'ai bane...bata gama rufe bakin taba sauran suka shigo.yasake ta ya rungume Miqdad yana shafa kanshi"My son sannnu ku da zuwa.

Miqdad yanuna mishi Alhaji Hafiz"Here is your elder brother sai suka hau kallan kallo na wucewar wasu dak'ik'u aannan suka rungume juna suna ta kyalkyala dariya kamar wasu kananan yara

Awunba wan Shedrak(Shedrak Dan'uwa na)

Alhaji Hafiz ya janye jikin shi yana gabatar mishi da sauran,duk aga gaggaisa sai a k'arshe yasake nuna Salim wannan shine surukinmu mijjn Sumayya. Salim yak'arasa wajan shi cikin girmamawa dan ya gaishe shi,sai kawai ya rungumeshi cikin jin dad'i "Kaine karik'e mana yarinya da amana irin haka? Gaskiya naji dad'i nagode,ALLAH yama auran ku albarka,ALLAH yaba ku zuri'a masu amfani.Salim ya sunkwui da kai yana murmushi a ranshi yake amsawa da amin.

Daga wani d'aki suka fara jin wani irin tari matsanan ci, bayan tarin yad'an lafa cikin galabaitacciyar murya aka fara magana"Baba dan ALLAH kazo kabani ruwa" duk suka bishi da kallo

"Judith...

Abinda zuciyar Sumayya ke fad'a mata kenan. Tasake kallan Baban ranshi a 6ace yakesai kawai tashige d'akin Dammm... zuciyar ta tayi wata rin bugawa da k'arfin gaske tayi mutuwar tsaye,numfashin ta yatafi wucin gadi na wasu yan dak'ik'u Judith ce a kwance marabanta da k'warangwal ya mushashshiyar fatar data rufe kasusuwan jikinta sai kuma numfashin da take yi.

Da rawar murya ta furta Kasham...sai lokacin Sumayya tadawo hayyacin ta, tafara Istirja'i sai ta fashe da kuka ko ba a fad'a mata ba ta sani cutar k'anjamau ce, tunda dama ba abinda take yi sai yawan ta zubar... Judith ta tare ta"Kasham kar ki zubar da hawayen ki a banza ni ai tawa ta riga ta k'are, taimake ni kawai da ruwa yau ban san laifin dana ma Baba ba,gaba d'aya yaki shigowa d'akin nan.Takalleta wa yake jinyar ki?

A hankali tace Baba.Tazuba mata idanu"Kin tafi yawan ta zubar d'inki kin manta da kowa a lokacin dakike cin duniyar ki da tsinki, ko gida bakya zuwa sai lokacin da kika bushi iska kizo zuwan asha ruwan tsuntsaye ki k'ara gaba,sai yanzu da kika ga mutuwa zaki dawo ki d'orama Baba abinda baiji ba bai gani ba?Tasake fashewa da kuka al'amurar rayuwar su ta taci barkatai da suke yi hankali kwance ya dawo mata, itama ba wayo da dabararta ne ya ku6ubtar da ita ba,ALLAH ne kawai yamata wannna gata da suturar da yanzu itama tana nan tana wannan kwamacalar.

Kukan Sumayya daya tsanan ta ne yasa suka shiga d'akin dan gane ma idanun su abinda yake faruwa.Adai-dai lokacin kuma zawo ya 6alle ma Judit tana kwance kamar gawa sai k'arni da wari daya cika d'akin.

Baban yabiyo su"dan ALLAH ku fito kubar wanna yar iskar yarinyar kar ku kwashi cuta,dan Sumaya tana jin k'arnin zuciyar ta ta tashi,tafara kelaya amai.Yakaisu D'akin- shak'atawar gidan kome atsare yake mayan kujeru da carpet ruwan k'asa sai kayan kallo a gefe da nu'urar sanyaya abubuwa(fridge) shima agefe duk sun zauna jungun-jungun saboda ganin Judith, kowa da kalar tunanin shi akan wani irin ciwo ne haka sannan me yasa ba a kaita asibiti ba? Me yasa Baban yake cemata yar iska a irin wannna hali na rai kwakwai mutu kwakwai? amma banda Sumayya da Alhaji Hafiz da suka riga suka san dawan garin.

Baban me fara'a ne shi yadinga jan su da hira har dai suka saki jiki.Suna cin abincin da Hafsa ta girka musu yau an hutashshe da Kawunta.Dinatu tahigo gidan cikin kwala kiran sunan Kasham...Kasham... Kasham..


Sumayya ta cire hannunta a abincin tana Istirja'i kafin tashigo Sumayya ta mik'e, a k'ofar d'akin sukayi kaci6is,takalle ta sama da k'asa sai tayi murmushi"Hail Mary...tarungume ta.Sumayya ta rintse idanun ta tana jiran saukar dundu a gadan bayan ta amma bataji hakan ba, har suka saki juna tana dad'a k'are mata kallo, wani kyau da annuri na musamman tayi"Sannu Kasham tad'an dafa kafad'arta"na ji dad'in ganin ki suka shiga d'akin takalli Alhaji Hafiz"Sannu Shedrak shima ya canja mata gaba d'aya to yaushe raban data sa shi a idanun ta shekara da shekaru yayi kyau mijin ta kuma ya tsufa sai yaza kamar shine gaba da Shedrak.Suka shiga gaggaisawa.Ranar dai suna cikin farin ciki musamma Dinatu ganin duk wanda yazo musu sannu da zuwa sai ya yaba irin kyan da Kasham tayi kamar wacce take zaune a wata k'asa,kowa na so yaga na shi cikin wadata.


"Lallai zaman Kaduna ya miki dad'i.Inji Lidiya.Sumayya tayi lallausan murmushi"kawai kishirya kayan ki mutafi.Tagalla mata harara"ai ko da kikayi wannan kyan banga abinda zai rud'eni in bar addinina ba.Itama ta galla mata harara"a ina kike da addinin?Kina da maraba da pagan ne? Kasham kar fa ki zageni.Sumayya tasake yin murmushi"come on Lidiya ni dake ai mun san gaskiya ko dan kawai d'aci gare ta?Ba fa yau na sanki ba,na sanki farin sani kamar yadda kika sanni farin sani,ranar Lahadi kina zuwa majami'a? Sai ta mik'e cikin borin kunya"bana zuwa kuna bazan je ba sai kiyi abinda za kiyi dani.Tafice fuuuu tana surutai rubbish girl...tabita da kallo haba yarinya ba abinda zanyi dake,za kuma ki dawo ne da k'afafunki.

Sumayya tasa mu Maman a d'aki, ta tazauna akusa da ita sannan tafara rok'on ta "Mama dan ALLAH kiyi hak'uri kiya femin laifin dana yi, na san da ciwon haka azuciyar ki.Cikin fushi ta kauda kai"bazan yafe ba ki tashi ki bani waje.Haba Mama kiyi hak'uri kisa min albarka,ai har kwanan gobe ina sanki ina alfahari dake a matsayin mahaifiya,dan kinyi d'awainiya me yawa akaina tun ina cikin cikinki har kika haifeni, wallahi bani da abinda zan biya ki dashi.Tasake tuno girman hakkin Y'aya akan mahaifansu musamman uwa da addinin musulunci yazo dashi kaico! Wanda ba ya cikin musulunci wallahi yana cikin duhu me girma, inama-inama tana da wani iko!? Da ayau d'in nan kowa na ta sai ya zama musulmi.

Takoma hannun ta Maman ta fizge da sauri"ke sakar min hannu mara jin magana kawai"kiyi hak'uri Mama na miki alk'awari bazan sake 6ata miki rai har kiji ciwon hakan ba Insha-ALLAH matuk'ar bai sa6a ma addinin musulunci ba.Tamata kallan uku ahu"Shari'a law" bata amsa ba tafara kuka haba Mama yanzu bazaki yafe min ba?Duk duniya bani da kamarki

Please Login or Register in order to submit comment