Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abadan duniya bazan ta6a mantawa da karamcinku kai da marigayi Musaddiq ba,duk in da zan ba da tarihin rayuwata to tabbasss sai kun fito a ciki.A lokacin da muke karatu a Gidan-Waya na baka wannan labarin yanzu ma zan sake ba ka"tun ina ciki mahaifina yakwanta dama,a haka mahaifiyata ta haifeni tacigaba da kula dani da sauran Yayyina su hud'u duk dani mu biyar,bata samu wani tallafi daga dangin mahaifinmu ko na ta dangin ba,kasancewar suma babu ta musu katutu,duk da haka munfi wasu daga cikinsu duk da mahaifinmu shima ba shi dashi,to amma ALLAH yatarfama garinmu nono gidan da muke ciki na shine ba haya muke yiba,wasu da yawa daga cikinsu kuma haya sukeyi,wasu kuma suna zaune a gidan da aka musu alfarma su zauna har zuwa lokacin da ALLAH ya yassare musu sukayi na su.

Mahaifiyar mu tunda jajayen sawunta take sana'o'i mabambanta ta ajiye maganar aure a gefe ta kuma toshe kunnuwanta ga duk abinda zaije ya dawo na zamanta a haka ga k'uruciya ga rashin aure ba irin sharrin da ba a mataba,ita dai kawai burinta ta inganta rayuwarmu,a haka da taimakon ALLAH dana yan'uwa d'an abinda ba a rasaba ta gangand'a ta aurar da Yayyina matan,muka cigaba da gara rayuwar a yadda tazo ba a yadda muka so tazo mana ba,rannan dai ganin wahalar tayi yawa nace mata ni kawai zan fara bin mota in zama kwandasta idan na iya in samu mota in zama direba.Idanunta suka kawo ruwa tana kallona cikin jarumtacciyar zuciyarta me k'arama mutum juriya da hangen wata rana sai labari.

Maimun ni da mahaifinka ba irin rayuwar da muke so kayi ba kenan,kullum burinmu ace Ya'yanmu sunyi zarra wajen ilmin addini,dan haka kayi d'amara kabani goyon baya dan girman ALLAH karka watsa min k'asa a cikin idanuna,tanuna kanta da yatsanta"madamar ina numfashi a doron duniya to Insha-ALLAH sai ka zama abin kwatance sai anyi alfahari an mori tarin ilminka...


Idanun Maimun suka kad'a yanajin kamar a lokacin ta zaunar dashi tana fad'ama mishi kalaman.Julaibib mun sha wahalar rayuwa,har k'anzon abincin gidajan mak'ota take kankaro mana muzo muci.Kullum kalamanta na k'arfafa gwiwane "Maimun kayi hak'uri wata rana sai labari ba wani yanayi da yake din din din a doron duniya,a haka dakyar da sid'in goshi muka gangand'a na gama secondary,sai da nayi k'wadagon shekara uku sannan na had'a kud'in registration nafara karatu a Gidan-Waya.

wasu lokutan inji kamar in gudu dan bak'ar wuya amma idan natuno da kalaman mahaifiyata sai inji k'warin gwiwa dan na san tanacan tanata k'ok'arin tara min wasu kud'ad'e kafin buk'atarsu ta taso,har zuwa lokacin da kuka shigo makarantar,tamu tazo d'aya kuka fahimci halin da nake ciki kuka taimakeni tun kafin in furta hakan,kuka yadda na dawo d'akinku gaba d'aya da zama inci abincinku,in sa kayan sawanku...da sauransu da sauransu,kun d'auke min abubuwa masu yawa game da karatuna, kuma kuna bani girma a matsayina na d'an Adam bakuyi duba da cewa k'asa nake da kuba.

Mun gama karatu lafiya har na samu koyarwa,D'ansarai kazo ka d'aukeni muka tafi Jami'ar Ahmadu Bello wai ka samo min gurbin karatu...Yakalli Julaibib ban ta6a ganin mutum me irin zuciyar kaba,kai ka biyamin kud'in registration.Da taimakon ALLAH dana mahaifiyata da kai nakai matsayin da nake,toh ta yaya zan manta wannan d'imbun alheran Malam D'ansarai?

Ya share hawayen da yazubo mishi sai dai shi ALLAH baya barin wani dan wani...ina matakin Senior lecturer mahaifiyata itama takwanta dama an gama cin mad'aci za a fara cin zak'in....ALLAH ya jik'anki mahaifiyata da sauran Iyayenmu kaafatan.

Yakalli Julaibib"to dan na baka d'an wannan kud'in da bai wuce kacika matorka da mai ba (full tank)kawanice bazaka kar6a ba?Julaibib yayi yar dariya"D'ansarai ko tayar keke bai dashi bare mota. Babu damuwa motar ma tananan tafe Insha-ALLAH,ka kuma fara shiri dan Umrah na bana da kai zamu tafi muyi azumin ramadana a can.Julaibib yayi godiya sosai sannan yarakoshi wajen mota,anan ma sun 6ata wasu dak'ik'u kafin sukayi musafaha yashiga motar ya zauna direban yaja motar,shi da Maimun suka d'aga hannu suna ma juna adabo.

Miliyoyin kud'ad'e Julaibib ya samu daga abokan arziki da gwammati,dan haka yasai fili babba yasake gina makarantar da tafi ta garin Zonkwa kome da kome gefen makarantar ya gina d'an madaidaicin gida.Ya ajiye aikin koyarwa na duk makarantun da yake zuwa, yadawo makarantarshi daya gina,suna cigaba da koyarwa da wasu malaman daya d'auka.

Alhaji Salim yakalleshi cikin natsuwa bayan sun dawo daga masallaci sallar Isha'i"Julaibib na so kwarai da da matarka ta aure ka tare a gidan ka. Yad'an bud'e idanu dan mamaki"Alhaji aure kuma?Sai yagirgiza kai"zanyi zamana a haka har zuwa lokacin da nima zan daina numfashi a doron duniya.Alhaji Salim yakad'a kai dan shima ya d'an d'and'ana irin abinda Julaibib yake d'and'ana amma ba kamar na Julaibib ba.

Lallai zasu tattauna cikin tsanaki,ai yana da ilmi zai kuma fahimci zama da auren zai fi mishi fiye da yak'arasa rayuwar a haka,tsananin martaba aure irin na bahaushe yasa kome tsufan mutum sai kaga yayi auren koda kuwa irin na butane kamar yadda suke fad'a.

Wata d'aya bayan nan Julaibib yana zaune a D'akin-shakatawar gidan shi yana kallan kwanukan abincin da Misbahu ya ajiye,duk da yabar gidan amma kullum ta ALLAH basa gajiya sau ukun nan sai an kawo mishi abinci, yanzu idan yace a daina kawo mishi bai san yadda zasu fassara al'amarin ba, abu d'aya zaisa a daina kawo mishi wannan abincin shine suga macen aure a gidan,shi kuma bayajin wani aure a ranshi,jiya ma abinda Maimun yagama fad'a mishi kenan wai da yana da 'ya mace da tuni ya aura mishi ita"Julaibib yayi murmushi"haba farfesa gwamma da ALLAH ma yasa baka da ita 'yar tawa zan aura?Ya jijjiga kai"ai hakan shine dai-dai taci karanta ba babbaka.

Ranar Juma'a bayan an sakko daga masallaci Julaibib ya tsaya suna gaisawa da Alhaji Salim,yakalleshi maganar Iyali har yanzu dai shiru bakace kome ba,yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"zan duba...ko kuma ma dai Alhaji kasamo min yar mutunci a unguwar nan tunda ka dad'e a unguwar ka san yar babban gida.

Alhaji Salim yayi murmushi"fad'uwa tazo dai-dai da zama,yakalli Julaibib "ka bani wuk'a da nama nagode,amma wani hanzari ba guduba idan kuma kaga yarinyar kaji bata kwanta maka ba fa?Ya amsa kai tsaye"zata kwanta min ko yaya take dan na san baza kamin za6en tumin dare ba, zan aureta zan kuma girmamata.

Alhaji Salim yasake kallanshi"yanzu me zakayi a gida?Yad'an motsa kafad'a"bakome.To zo muje gidana akwai maganar da zan fad'a maka suka shiga mota suka tafi.

Sai da suka gama cin abincin rana sannan Alhaji Salim yakalleshi cikin natsuwa"Julaibib zan baka auren 'ya ta Ummi kana son ta?Julaibib yaji wani irin yanayi na girma da nauyin Alhaji Salim,ai wata fuskar ta fi gaban mari har abadan duniya wallahi,Ummi a yadda ya karanceta ai bata da wani aibu tana da natsuwa da hankali,gata da ilmi,kai ko da ace ballagazace a dai irin karamcin da Alhaji Salim yamishi to wallahi ba abinda zai hanashi auren ta "Insha-ALLAH kuma sai ya d'orata a kan hanyar dai-dai bare kuma a kauwamen ta take.Ya amsa cikin girmamawa"to Alhaji nagode ALLAH yasaka da alheri.

Yagyad'a kai"Julaibib ya kamata kasan wacece Ummi da kuma mahaifiyarta.Yayi shiru yana sauraro...Alhaji Salim yabashi labarin aurenshi da Sumayya,'yar data haifa mishi da kuma rasuwarta...Ni tun ranar daka farfad'o na tambayi sunan ka kace min Julaibib na gane ko wanene kai,da irin k'aunar da marigayiya take maka,dan haka Ummi yar wajen Sumayya(Kasham) ce,ita zan baka idan kaga kana sonta.Julaibib yabud'e idanu dan mamaki...zuciya da k'wak'walwarshi bangaren adana bayanai ta koma baya da gudu tana tariyo mishi kome daki-daki tun had'uwarsu ta farko da Kasham a Gidan-Waya ranar da sukaje yin registration... har zuwa ranar data aiko mishi da wasik'a,ruwan zamzam,farin miski da dabinon ajwa da abinda tarubuta mishi"Musha ruwa lafiya...ranar azumin ashura tara ga watan farko na musulunci Muharram...Da abinda ta rubuta a k'arshen wasik'arta

Sumayya Kantiok Donatus(Kasham)

Yayi shiru yana tasbihi a cikin zuciyarshi"ALLAH Alhakimu gwanin iya hakima, ALLAH buwayi gagara misali...Qudirarka da yawa take"ni Julaibib Abdullahi D'ansarai ni zan auri 'yar da Sumayya ta haifa?Lallai ba wanda yasan abinda gobe zata haifar sai ALLAH,dan shi wallahi har ya manta da wata Kasham da Sumayya a rayuwarshi...A hankali mafarkan da ya dinga yi na shekara da shekaru suka dawo mishi wannan mafarki me ban mamaki da yarasa gane ma'anarshi

"Kasham da yake gani cikin shigar kayan fulani idan tayi magana sai kuma yaji muryar Sudaida.

Wannan yana nuna Sudaida matar shice,haka kuma zai auri wata kenan me alak'a da Kasham d'in?Gashi kuwa ya tabbata 'yar data haifa a cikinta...kayan fulanin kuma yana nufin kenan Bafulatana ce?Yajijjiga kai"ko shakka babu tunda Alhaji Salim Iyayenshi Fulanine amma girman birni dan ko Iyayensu basuyi kiwon shanu ba bare kuma su... La'ilaha'illallah.

Sai yasake tuno ranar da Maimun yake fad'a ma Musaddiq mafarkin da yayi"Wai shi da Kasham ne suke kiwon shanu a wani k'aton fili iya ganinka me cike da koren ciyayi"Musaddiq yakyalkyale da dariya"D'ansarai fulani ka koma har matarka take tayaka kiwo saboda tsabar k'auna?A lokacin bai kula suba.Yayi ma Alhaji Salim godiya sosai,amma har yabar gidan bai daina mamakin wannan al'amarin ba.

Bayan tafiyarshi Ummi tashigo d'akin da sallama,ta zauna tana kallanshi"Abbana kace za muyi wata magana idan ka dawo daga masallaci, yana murmushi yace ban manta ba Ummi,ya san yana da yak'ini zata amince,sai yafara mata nasiha akan biyayya ga Ya'ya a wajen Iyayensu wajibine matuk'ar abinda suka zo dashi bai sa6ama shari'ar musulunciba,a hankali kuma yafara kambama halayenta na k'warai, ganin tana ta murmushin jin dad'i,sai ya maida abun zuga"ai na san baza ki bani kunya ba;baza ki watsa min k'asa a cikin idanu ba,ni a duniyar nan ban ta6a ganin yarinya me tsananin biyayya ga mahaifanta ba irinki,nima kinga shi yasa nake miki wata irin k'auna mumaiyiza(ta musamman)

Tagyad'a kai"tabbasss ta yadda Abbanta yana mata k'auna ta musamman d'in dan kome nata na musamman ne wallahi a wajen shi. Cikin d'oki tace"me kake so in maka ne Abbana? Yakalleta cikin kulawa"aure zan miki Ummi,kuma ni da kaina na za6ar miki mijin.Da sauri ta sunkwui da kai dan batayi tsammanin abinda zai fad'a kenan,tanajin wata irin kunya na lull6eta.

Yacigaba da magana "shekaru da yawa da suka wuce ina da labarin shi, mutumin kirkine... kuma nima a yanzu nayi nazarin shi tsafff...naga hakan ganin idanuna,hasashena yana bani zai rik'eki da aminci da amana,burina kullum a kanki Ummi shine kiyi aure,kiyi bautar cikin aure tunda ibadane, ranar alk'iyama ki samu sakamako mafi kyau da daraja,kisamu shiga darul-karamah (aljannah) aljannarma ina miki kwad'ayin samun mad'aukakiya (firdausss)

Yayi shiru yana kallanta"Ummi kiyi magana mana ai ba auren dole zan miki ba,idan kina da za6inki na kuma bincika naga shima mutumin kirkine,toh shi zan aura miki,zan kuma ba wancan hak'uri na san zai fahimceni,tayi k'asa da murya cikin jin nauyinshi"Abbana ina fata in biku in muku biyayya a duk abinda kuka umarceni ko da bana so,zan tilastama kaina so,dan na san baza ku cuceniba,dan nima inaso agaba a bini,na san kuma sai na biku na samu albarkanku,nima zanga da kyau a rayuwata ta gaba.

Yayi lallausan murmushi yana yaba hangen nesan ta"toh kin yadda da za6in Abban naki koda mutumin me gemu da k'asumba cike da furfura kamar na Abbanki?Tasake sunkwui da kai"shi wallahi haka Abba yake magana wasu lokutan sai yaba ka kunya.

Haka rannan yace ma Mamansu wai tana ta wani shashshare shi,to shi gaskiya ya gaji da wannan shariyar,aure zai k'ara kuma sa'ar Ummi zai auro.Ita kuma ta galla mishi harara"dan ALLAH ka auro wacce bata kai Ummi bama.Sai yafara dariya yakalleta"ke Ummi ki zama shaida ai kinji abinda tace ko?Batayi magana ba,sai guduwa d'aki tayi ta barsu,yanzu ma tashi tayi yana kiranta amma bata dawo ba.Alhaji Salim yana da shak'uwa sosai tsakanin shi da Ya'yanshi,dan haka zaiyi wuya yafad'a musu abinda yake so na ayi ko abari kaga basubi umarnin na shiba.

Haiya Bara'atu tak'arasa shigowa"to ai Alhaji wannan al'amari yayi dan shirun budurwa yaddan ta,bazawara kuma sai ta tanka.Tamishi wannan kallan nata dasu biyu suka san ma'anar ta"ko kuwa?Yana dariya ya amsa"ai zancenki ba ja kare ya mutu a juji.

Ranar wata alhamis ba makarantar Islamiyya kuma dama ta gama secondary ana zaman jiran sakamako kafin a d'ora zuwa Jami'a,suna D'akin-girki Alhaji Salim yabisu yana musu sannu da aiki.Suka amsa mishi cikin sakin fuska.Yakalli Ummi "bar kwa6in nan ana sallama dake a waje.Tad'anyi jimmm...Hajiya Bara'atu ta kalleta cikin kulawa"jeki mana Ummi.

Tajuya jikinta a sanyaye tana sanye da riga da zani na atamfar classic,tasa bak'in silifas da hijab tafita,sai dai bata ga kowa ba sai Julaibib,tasha jinin jikinta,ta gaishe shi duk da d'azu tagan shi a hanya da take dawowa daga gidan Alhaji Hafiz kuma ta gaisheshi.Yak'araso in da take tsaye"ai ni nake sallama.

Sai tasunkwui da kai k'asa batace kome ba tana wasa da gefen hijab d'inta"to yaya na miki?nan ma shiru tayi sai yacigaba kinga karfa kiga dan na kwana biyu gemu da k'asumba sun cika fuskata toh na iya soyayya sai na zama tauraronki.Sai kuma yayi shiru yana kallanta ganin har lokacin batace kome ba.Sai yakad'a kai cikim jimamai"Oh D'ansarai marayan ALLAH ba uwa da uba ba sauran dangi da alama baka samu kar6uwa ba dan haka sai ka d'au na Annabawa kawai.Yadda yayi furucin cikin tsananin tausayin kai yasa tad'an d'ago tana murmushi,amma ba shi take kallo kai tsaye ba"Yaya Julaib...ba haka bane ai tunda Abbana ya gamsu da kai bani da ja...shima kallan fuskarta yayi..ALLAH buwayi sai lokacin yake ganin kamanninta da Sumayya har jerarrun hak'oranta farare, da manyan idanunta masu maik'o,wad'annnan sune abinda ta d'auko na ta kai tsaye da kowa zai iya ganewa.Kad'an sukayi hira yamata sallama dan ya lura a takure take.

Watanni uku bayan nan aka d'aura aurensu Alhaji Hafiz yatsaya a matsayin waliyinshi, aka kai amarya gidan mijinta ana musu fatan zaman lafiya. Ummi tashiga bautar gidan aure da duka k'arfi da kuma iyawarta,zaman nasu ba yabo ba fallasa, suna mutunta juna,tana bashi girma a matsayinshi na babba kuma mijinta sama yake da ita,shima yana jin tausayinta amatsayinta na k'arama kuma mace me rauni...

Yasauke gwauron numfashi a sanda k'wak'walwarshi bangaren tunani da adana bayanai tagama tariyo mishi kakaf rayuwarshi daki-daki.

Yauma abinda yasa yamata haka jiya yatafi Gidan-Waya yakwaso kayansu anan yaci karo da kayayyakin Iyalinshi...abinda ya famo mishi wani miki kenan haka ya kwana ranshi ba dad'i... Ummi bata kar zomo ba sai ya bata rataya...yayi huce haushin kaza a kan dami.Yajijjiga kai"gaskiya Ummi bata cancanci haka ba,ai idan d'an kaciya baici kazaba toh tsakani da ALLAH bai kamata kuma yayi baraba...Har lokacin yana jiyo sautin kukanta dan haka ya mik'e dakyar duk da har lokacin kan nashi bai daina ciwo ba.

Ruqayya...tanaji amma tak'i amsawa "haba Ruqayya...sai ya zauna ya gewayeta"Ruqayya Esbeer...ni me laifi ne,laifina kuma babbane...amma na gane kuskurena gani a gabanki na zo ki yafemin...d'ago kanki ki gani na san ke macen albarka ce,baki furta kalamanki ba har sai da kika rasa hanyar bi wajen shawo kan matsalar gidanki,ni d'innan nina tunzira zuciyarki,amma Insha-ALLAH zan kiyaye furucina...ni dai ki taimakeni ki yafemin...ta tari numfashin shi tamik'e zaune tana kallanshi da idanunta da suka kad'a jawur"na yafe maka.

sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u sannan ta cigaba da magana"Julaib...ina tabbatar maka kana d'aya daga cikin bayin da ALLAH yake so Insha-ALLAH idan katuno da jarabawar Annabi Ayuba Alaihissalam"ya kamu da ciwo tsawon lokaci, Ya'yanshi suka dinga mutuwa,duk jama'a suka k'aurace mishi to amma da yayi hak'uri ya mik'a al'amura a wajen Ubangijin mufa?ALLAH mahaliccin mu yace mishi "madallah da wannann bawa nawa me yawan hak'uri da juriya.

Julaib...karage tunanin nan,ka sani wanda duk ya mutu toh ya mutu kenan abadan,babu sauran soyayya da k'auna da zaka nuna mishi face ka yawaita aika mishi da abincin shi(addu'a)idan kana da hali ka mishi sadaka me gudana,toh Julaib...ka musu anata aika musu da ladan kullum ta ALLAH, kaima kullum kana musu addu'a,nima ina musu, Abbana...Mamanmu, kai da d'aukacin al'ummar Manzon ALLAH ga wad'anda suka ga kisan gillan da aka musu,da wad'anda sukaji labari da sauran yan'uwanmu musulmai na garin Jos da Maiduguri da sauran arewacin k'asarnan.

Duk masu ta'addancin nan tun daga duniya zasu fara ganin sakamakonsu,da izinin ALLAH fashewar kwai a saman kwalta za suyi,mutuwar kare a saura.Tad'an kalleshi"dan ALLAH kayi hak'uri ka saki ranki muyi rayuwar aure kamar yadda sauran ma'aurata suke yi cikin nishad'i da karsashi.Yasauke numfashi"Ruqayya ke macen alherice...ALLAH yamiki albarka.Tagyad'a kai"amin,shukran jazilan...Qad uhibbuka...yatari numfashinta kafin ta k'arasa furucinta"hubban jammahhh...sukayi murmushi"to yanzu muje ki bani abincin yunwa nake ji cikina ba kome sai yan hanji.

Bayan ya gama cin abincin yasha magani yad'an huta,sannan tafara mishi bayani a kan gidauniyar"D'ansarai da Me-Lambu Foundation"da suka kafa musamman dan taimakon marayu da zawarawa yan gudun hijirar Zonkwa da ta samar da kud'i me tarin yawa,d'azu bayan tafiyarka masallaci Maman Hasan ta kirani tafad'a min.Baba Alhaji ma (Alhaji Hafiz) ya sake bamu gudummawa kamar yadda yasaba,sai dai wannan karan kayan masarufi muka samu kasancewar watan ramadana yanata matsowa.

Abbana ma zakkarshi ta bana daya fitar d'ungurungum yabamu kud'in,shi tun jiya bayan tafiyarka Gidan-Waya yakira yafad'a min idan ka samu lokaci kaje ka kar6o dan ya kira lambarka bata shiga.Jikinshi yai sanyi "Ruqayya Ubangijine kawai zai saka muku,ina kuma rok'onshi yasaka muku da mafificin sakamakon shi. Yaciro wasu kud'ad'e masu yawa yana mata bayani "wad'annan farfesa Maimun AbdulQadir ne ya aiko dasu.Tagyad'a kai"mungode kwarai ALLAH yasaka mishi.Amin.Bayan la'asar sai inji in kar6o na wajen Alhaji zuwa jibi sai mutafi Mando mu raba musu,tunda kowa kika gani a wajen yana cikin halin ha'ula'i ne.

"Julaib...wai har yanzu gwamnatin jahar nan ba wani tallafi da zata bayar ne? A yanzu dai kam babu amma bamu san a gwamnatin gaba ba tunda wannan ai kinga saura shekara d'aya tak'are tenure,ke dai Ummi Ubangiji yacigaba da rufa mana asiri duniya da lahira wanda yasamu kud'i ko yaya sai yafara sana'a kome k'ank'antarta yacigaba da addu'a ALLAH yasa mishi albarka sai kiga kome ya wuce,ai da rarrafe yaro yake tashi.

Rannan naji a labarai agwam Bajju yana dad'a ba musulman Zonkwa hak'uri akan abinda yafaru wai ba a san ranshi hakan yafaru ba.Julaibib yakad'a kai"rabu dashi ai bakinsu d'aya,in banda haka a ina suka samu wad'annan mugayen makaman? Kud'in baikon da suke bayarwa duk ranar lahadi a majami'unsu bai isa yasiye suba...Gari ne dai an bar musu,ai k'asar ALLAH fad'i gareta,masu murnar sunyi kud'i da kud'in hausawa to yanzu baki gansuba"garin banza dama a farau-farau d'in bamza yake k'arewa.

Ringtone d'in Ummi"This is my hijab...I will never remove.yafara tashi.Rahab ce dan haka ba tare da tayi sallama ba tad'aga.Rahab ta fashe da kuka"Ummi Bobby ne...Me yasa meshi ne haka Aunt? Tayi tambayar da kulawa.Cikin kukan take mata bayani"wai sun tafi Fadan Karshi d'auko akwatin gawa (coffin)na wani abokin su daya mutu, to a hanyarsu ta dawowa motar takama da wuta sun k'one k'urmusss. Ummi tayi jimmm...to me zata cene? Idan batace kome ba tabbasss Aunt Rahab baza taji dad'i ba,Bobby shine babban d'anta,kuma tana son ta,dan ko bata kira taba to ita tana yawan kiranta kusan rabin yaren Bajju ita ta koya mata a cewarta dole ne tayi haka tunda da Kasham tana raye zata koya mata, toh tunda ta mutu ita meye amfanin ta idan bata koya mata ba? Sauran kuma ta koyeshi a gidan Alhaji Hafiz da take zuwa.

Ta tausasa murya"Aunt basakut (kiyi hak'uri)Kuka bazai dawo da Bobby ba"I know it's hurt, but you've to bear it,since you already know that sooner or later each and every one we will go back to our creator...tacigaba da rarrashinta har tayi shiru amma bata yadda ta mishi addu'a ba dan musulunci ya haramta hakan ga duk wanda ya mutu bai yadda da manzancin Manzon ALLAH Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam ba.Rahab taji dad'in kalaman Ummi sosai "Thank you very much my dear Ummi for this condolence.Sukayi sallama.

Sunyi shirin tafiya Umrah a can zasuyi azumin ramadana,d'aya ga wata kuwa jirginsu ya d'aga zuwa k'asa me tsark'i,garin Manzon ALLAH me safa me marwa,garin dabino da ruwan zamzam... ruwan zamzam me tarin albarka da duk buk'atar da kashashi zata biya Insha-ALLAH.

Dabinon ajwa sukaci da tataccen ruwan inibi da tuffa,bayan angama kiran sallar magriba, shi da Ummi suka kalli juna suna murmushi yad'aga hannayenshi sama dan wannan lokacin amsa addu'a ne kafin a tada sallah"Ya ALLAH bayinka da aka kashe bada hakkin suba a ko ina suke a doron duniya al'ummar Manzon ALLAH! Ubangijinmu albarka wannan rana,albarkan wannan d'aki na ka me alfarma ka yafe musu!Ya Ubangijinmu mahaliccin kowa da kome jinin nan nasu daya zuba a doron k'asa,kasa yazama sanadi na samun d'aukaka da darajarsu!Ya Ubangijinmu kasa hakan yazama sandin shigarsu darul-karamah (Aljannah) Jannatul firdausss al'a'ala.

"Ya Ubangiji!Miyagun da suke ma al'ummar manzonka kisan gillan nan idan wad'anda za su shiryune to ALLAH na rok'ek'a kashiryar dasu, idan kuma 6atattune abadan Ila yaumil k'iyamah... ALLAH! Kai ka haliccemu gaba d'aya, kuma gareka zamu koma gaba d'aya mun bar kome a hannunka

Please Login or Register in order to submit comment