Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwa ta uba ya kaima k'osan kutifo ya tarwatse a tsakar gidan, hannayenta dafe da kuncinta idanunta sun kad'a jawur suna fitar da hawayen azaba. Hakan bai mishi ba kawai yasa hannu ya zaro belt d'in daya d'aure k'ugunshi yadinga labtarta har sai da ya tsistsinke ya jefar yana huci"ke dan abu kazan uban ki har kin isa kiyi soyayya da wani bayan munyi alk'awarin aure dake?Ina raye da raina da lafiya ta?Bazinzira (na rantse da ALLAH)idan kika kuma zuwa wajanshi abinda zan miki sai yafi wannan stupid,rubbish girl.Yagaji dan kanshi yayi shiru yajuya zai bar gidan.Dak'yar tamik'e dan ma zuciyarta ta bushene amma yadda tasha na jakin nan ai ko d'aga yatsa baza ta iyaba,tasha gabanshi"har ka gama kenan?Tagyada kai tare da had'e tafukan hannayenta.

"Ungwai bu gan gang (Nagode sosai)

Amma ka sani daga yau,yanzu d'in nan na gama soyayya da kai "I jilt"har abadan duniya.Wani kuka ya kufce mata amma bakinta bai mutuba, cikin kukan tanuna mishi d'akin ta shiga ka kwashe kayan sawanka da duk wani abu daka san na kane kabar mana gida.

Jikinshi yayi sanyi"wai an jefi kaza da gishiri"bai ta6a tunanin haka ba"haba Beauty yayi d'an murmushi "It sound phony,to ma me yayi zafi ne da har idanu za suci wuta haka? Me yayi zafi? Ta tambayeshi cikin tashin Hankali. To meye ma bai tafasa har ya k'one ba bare wani zafi? Bana son ka Baranzan, kuma ko ban auri D'an Sarai ba kai dai na gama soyayyah dakai,tad'aga murya cikin kuka haka ake soyayyah?Haka ake nuna soyayyah? Kai baka iya kome ba sai duka? Julaibib ya nuna baya so na kai har yagaji yafad'a min inyi hak'uri shi dai bazai aure ni ba, yana nuna ina damunshi,duk abinda nake mishi baya so d'in amma dai-dai da rana d'aya bai ta6a d'aga hannun shi yace zai mareni ba sai kai,tanuna shi da yatsa sai kai me ik'irarin kana so na, kana so muyi aure in haifa maka Ya'ya,a haka ne zamu zauna zaman auran for better for worst till death due part us?

Dukan da kamin ko Mamana da take da zafi bata ta6a min irin shiba tunda takawo ni doron duniya, tacire rigar ta,ta jefar tana nuna mishi wani k'aton tabo a kafad'arta"wannan ma tabon dukan kane wanda yariga ya zauna kenan har abadan duniya,kalli yadda ka farfasa min jiki?Tasake fashewa da kuka me cin rai,na rantse da ALLAH ta dankwali k'asa a d'an yatsanta ta la sa,na barka har abada kamar yadda na bar nonon uwata.Kai Baka da hankali baka san yadda zaka sace zuciyar mace ba, abinda ka iya shine ka kama mace ka yita duka kamar ka kama 6arawon da yayi fashi da makami da kakin soja a jikinshi da bindiga a hannunshi,wallahi ba ka iya kome ba,kaje ka koyo,sai kuma takoma sambatu Julaibib ya iya tafiya ta natsuwa,baya san hayaniya shi shigar shi kullum ta fararan kayane,ai kaima kasan ba me jure sa fararan kaya sai me tsabta na gaban kwatance"he is a gentle melanin beauty that I have never meet before.

Yarik'o ta kiyi hak'uri Beauty raina ne ya6aci zuciyata tana ta tafarfasa abinda yakaini ga zagi da dukanki kenan, na ka sa danne temper na amma ai kinsan ina sanki, zai rugumeta tayi wani ihu ta k'wace da k'arfin bala'i"tamishi kallan uku ahu"ALLAH sarki ai ban san haka zuciyar ta ka tayi ba,da dai naga tiriri yana fitowa ta kirjin kane to da na yadda, taja dogon tsaki "kai koma menene da menene wallahi ba wajan kuka na bane mutuwar uwar kishiya,ai kome yazo k'arshe.The game is over. sunan wata wak'a.

Yajuya yayi tafiyarshi ai yasan tashi da Beauty bata 6aci sau nawa suna fad'a kuma su dawo su d'inke kamar wani abu bai faruba.Ran tane kawai ya6aci amma da zarar ta huce za su daidaita..

Bai koma gidan ba sai kwanciyar bacci sunje Kasham Hotel Kafanchan sunyi holewarsu da yan mata,yayi tatil da uwar laifi(giya) tamik'e da sauri dan saura kad'an yafad'o a jikinta,Itama ta kasa bacci ne dan gaba d'aya jikinta ya mata tsami dan ma an mata allura tasha magunguna,dak'yar ta canja kayan baccin ta da wando jeans da bakar rigar sanyi me hula tazuba k'ananan abubuwan da zata buk'ata a jaka tabar d'akin tana surutai"ai kin banza talaka ya girmi sarki idan ma kayi aman ka kai zakata gyara d'akin gobe da safe.

Yana tashi yaja doguwar hamma baki a bud'e yana mik'a tare da addu'ar"Our father who is in heaven,I love you thy name...bai k'arasa ba ganin ba Kasham kwance a gefe kamar yadda suka saba,yafito tsakar gida suka gaisawa da Babanta sannan ya tambaye shi " Ina Beauty ne? Baban yace wai ba ta d'akin? Eh bata cikin.To bata kwana a gida ba ko kuma yanzu tafita.Kai yaushe kashigo?Baranzan yasa ke yin hamma"ba a gidan ta kwana ba ke nan, dan a d'akin nakwana yanzu natashi daga bacci,Baba barinje gida in dawo.To Baranzan a dawo lafiya(Oh🤔 mu Ya'yan Ibrahim ALLAH d'aya gari bamban.Abin da mamaki wai talaka da mata hud'u harda k'wark'wara amma me gari gwauro)

Sai yamma lik'is rana ta tafi tana shirin fad'uwa sannan Kasham ta koma gida,tafara masifa ganin bai d'auki ko tsinken sakacen shiba, a fusace tafara watso duk wani abu na shi tsakar gida ai na fad'a maka"I jilt.. Is over,Is totally over...na rantse da ALLAH zan mishi rashin mutuncin da har ya mutu bazai manta dani ba. Babanta yafito daga d'aki yana kallanta da kayan da take watsowa tsakar gida da mad'aukakin mammaki "Kasham me ya ta6a k'wak'walwarki haka?Ya za ki dinga watso mishi kaya tsakar gida?Cikin hayagaga...tad'aga mishi hannu"hey! ba ruwanka ai tun jiya nace ya kwashe kome na shi.Yarik'o hannayenta "Baranzan da za ki aura kayan shine fa kike watsowa? Tak'wace"Baba ka kyaleni a cikin hayyacina nake ban sha giya ba bare kace tafad'a min ba gaskiya ba,soyayyarce kawai bazanyi ba,na fasa auren nashi,kuma na yi alk'awari ko na rasa mijin aure to da in auri Baranzan gwamma in mutu ba aure.Baza ki auri Baranzan ba to saboda me?Wa zaki aura? Saboda bana son shi,kuma D'ansarai zan aura.Yakalleta da sauri yana maimaita sunan D'ansarai? Dansarai? Waye kuma haka?

D'ansarai shine wanda nake so kuma a cikin gari yake,shi zan aura zan kuma yi abinda yake yi,shi musulmi ne,nima wallahi sai na musulunta na yi sallah. Yatafa hannaye cikin kad'a kai"Jesus Christ.Yabita da kallan nazari sai huci takeyi kamar ta ci babu.Yanunata da yatsa"to ban yadda ba.Tagyad'a kai"ni ai na fad'a maka ne dan ka sani,ba wai dan ka yadda ba,tunda dai ai ni zanyi zaman auren ba wani ne zai min b...saukan marin da aka mata yasa sauran kalaman suka mak'ale...

Kasham ai ban san baki da hankali ba sai yau, a duk zuri'ar mu ba me salla sai ke ce za kice za kiyi? Tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta"to baki isaba,ina tagirgiza kai wannan ba za ta sa6uba bindiga a cikin ruwa, dama abinda ki ka dinga yi kenan a makaranta bin mazan hausawa?Tama Maman na ta wani kallo me kama da harara"ni ina ruwa na da rashin sallar zuri'arku?Kuma aike ma kin san mazan hausawa ba k'ashin yarwa,sau dubu nawa ina kawo miki kayayyaki kinaci,kin kuma sani sarai su d'inne suke bani,baki ta6a k'in kar6a ko ki min fad'a akan in rabu dasu ba, sai yanzu dan nace ina san zama irinsu?Ashe kowa yana san wawa haihuwar shice ba a so? Tsamaninki banza kika dinga ci? Takai mata wani mari amma tagoce dasauri yabi iska, tamata dak'uwa kinci uwaki,dan abu kazan ubanki ba za kiyi sallah ba,abinda ba mayi dake sa'in'sa amma gashi daga fara cewa kina san wani tsinannen bahaushe har kina min rashin kunya kina fad'amin maganar dakika ga dama...Tabuga cinye na rantse da ALLAH baki isaba sai dai idan bana numfashi za kiyi sallah.Kasham tagyad'a kai"To maji ma gani ai...an binne tsohuwa da rai.


Lidiya tashigo suka had'u suna ta zagin ta amma ko a jikinta wai anyak'ushi bishiya.Tad'an motsa kafad'a tare da ta6e baki "Kanku ake ji...ta d'auki jakarta"bazan iya wannan bud'ar kan karyan ba, kuci kanku kusha bak'in ruwa.

"Kasham ani yake?(Kasham ina za ki?)

Tajuyo muryar Maman a tsawace.Tayi taku biyu sannan taja ta tsaya"Ani yake?Tasake tambayar ta,ko a jikinta tace.

"Ana kari Julaibib(wajan Julaibib zani)

Dawo ki zauna karki kuskura ki bar gidannan.Tad'anja tsaki sannan tak'arasa ficewa da saurin ta"idan na dawo kar ki barni inshigo"kuma ko ku mutu ko ku rayu wallahi sai na yi sallah kuma ALLAH zai taimakeni in auri D'an Sarai...ALLAH dai yakai damo ga harawa...

Tajuya kan mijinta cikin tafasar zuciya ni dai ka sani gaba d'aya zuri'armu babu wanda yake sallah,sai dai in wancan ne yake yaudare min yarinya,yake so tabi layin shi,to kaji na rantse da girman ALLAH bazan yadda ba, zanje har cikin gidanshi inci mutuncin shi, ba ki yamana ga shi nan yana shirin kama Kasham, dama ya dad'e yana fad'in idan munki sallah to Insha-ALLAH Ya'yanmu sai sunyi.Yagirgiza kai cikin damuwa yasan matarshi bata da mutunci, to shima dai dan uwan na shi Yayanshi uwa d'aya uba d'aya Shedrak,wanda a yanzu yake amsa sunan Alhaji Hafiz ba barin ta kwana yake yiba shima mafad'aci ne wallahi.

Kiyi hak'uri Dinatu mu zauna musan abinyi,nima ba na goyon bayan abinda tazo dashi,kuma da kike fad'in Shedrak ne yake yaudare ta to yaushe rabonshi da zuwa garin Zonkwa bare har yashigo k'auyan Madauci?Tayi shiru.Yawatsa hannaye kingani ko?Ai shekarun da yawa ko Kasham baki haiifa ba a lokacin. Muje wajan Pastor ayi addu'a ko Baptismal idan yaka ma sai a sake mata.Tamik'e cikin gyad'a kai"eh to ka kawo shawara to tasu mutafi ai bamuga ta zama ba da zafi-zafi akan daki k'arfe.

Kasham bata kwana a gidan ba,sai washe gari da hantsi.Lokacin kuma Mamanta ta dad'e da tafiya kasuwa,dama ita take fita ta nemo musu abinda za suci dama sauran buk'atunn rayuwa,yar kasuwa ce sosai da take cin kasuwancin ta gari da k'auyuka na nesa dana kusa,shi kuma mijin kullum yana gida yana aikacen-aikacen yau da kullum da akeyi a gida har girki ma a wasu lokutan idan ba kowa shi yake yi.Yad'ago yana kallanta "Kasham zo mana ganin tana shirin shigewa d'akin ta,tayi kamar ba ta ganshi ba kuma har had'a idanu sukayi lokacin da za ta shigo.


Tazauna a d'aya farar kujerar robar,ko sannu bai samu arzk'in tace mishi ba bare in kwana (Oh mu Ya'yan Ibrahim🤔inda ranka ka sha kallo...sunan wani shiri a Freedom Radio)A ina ki ka kwana Kasham?Tazuba mishi manyan idanunta masu maik'o"wannan wace irin tambaya ce haka Baba? Yagirgiza kai "ai na ga ke a gida kikafi kwana shi yasa na tambayeki kuma Baranzan yazo nemanki na san ba a wajan shi kika kwana ba.Baba ba ruwanka da inda na kwana. Tad'ora k'afa d'aya akan d'aya tana karkad'a kafar dama,tana wata yatsina da hura hanci alamar bala'i takeji da gasken-gaske.Ta sauke gwauran numfashi Ka na ji ko Baba? Eh ina jinki.ALLAH sai na auri Julaibib,ka san yadda nake jin k'aunar shi a zuciya ta kuwa?Takad'a kai"no matter how zan kwatan ta maka ba za ka gane me nake jiba...sai tafashe da kuka duniyar ta cukurkud'e mata wallahi,rana zafi inuwa k'una,to a ina ake so tasamu sassauci ne?Julaibib,Iyayanta,Baranzan, Lidiya, da yan uwan ta kowa yana jin haushinta? To ita tace ma zuciyar ta ta k'aunaci D'ansarai ne???

Tausayi irin na d'a da mahaifi ya mamaye zucyarshi,saboda shi yana da san Ya'ya sai dai abinda tazo dashi me girma ne, amma ga dukkan alamu tana san wannan D'an...menene ma sunan na shi oho ya manta, tunda har ta yadda tabar Baranzan da suka shafe shekaru hud'u suna soyayyar su hankali kwance ba abinda ya ta6a shiga tsakanin su na tashin hankali amma akan shi wannan bahaushen sun fara fad'a,dama duk cikin Ya'yansu ai daga Kasham sai Rahab ne basa canja samari kamar yadda ake canjin kayan sawa,kuma su biyun ne suka maida hankali ka'in da na'in akan karatu, sauran maza da matan suna can suna cin karansu ba babbaka. Matanma sai su shafe watan ni takwas basu lek'o gida ba, suna can wasu garuruwa da jahohi suna zaman kansu suna kuma sheke ayarsu yadda yaka ma ta,galibi ma zuwan su gida sai da dalili me k'arfi kamar lokacin Christmast,New-Year, da Esther,su kanzo a Valentine amma ba kowane Valentine ba.

Kiyi hak'uri Kasham dak'yar ya rarrashe ta tayi shiru,manyan idanunta masu maik'o sun kad'a jawur "Kiyi hak'uri Kasham ni kin san matsala ta ba babba bace,zan iya barin ki kiyi sallah tunda kina sanshi, za kuma cigaba da kasancewa 'ya ta,bazan tauye miki yanciba" you have human right"kuma shekarunki sun kai na duk wani d'an Adam me hankali,babbar matsalar "inda gizo ke sak'ar Dinatu baza ta ta6a amince miki ba,idan kinki ji to na san za ta yafe ki a cikin Ya'yanta, za ta barma hausawa ke forever kinga kuma baki mata a dalci ba, ta so ki ta kula dake ta miki kome na rayuwa...kema ba za kiji dad'i ba.Yakalleta yad'an motsa kafad'a ya cigaba da gyaran waken da yake yi na girkin rana.Itama tamik'e tana k'unk'uni.Yad'anyi murmushi k'uruci dangin hauka,Kasham baki san rayuwa ba.You know nothing but wannan soyayyar data rufe miki idanu." So makaho...

Lidiya tabita da kallo "to wai ke da kike ta wannan hank'oran,kike k'ok'arin 6atawa da kowa akan wannan tsinannan kun dai-dai tane ya yadda zai aureki zai zama miki uwa da uba dasauran danginki da za ki rasa? Dan abu kazan ubanki ina ruwanki?Babbar manufuka kawai,bitch ai na san ke ki ka k'yank'yasa ma Baranzan!

Lidiya ta k'yalk'yale da dariya dan abun bai ba ta haushi ba,ta kuma k'yalk'yakewa da dariya tana tafa hannaye Jesus Christ of Nazareth gaskiya kin fara cin kai (Hauka)

Kasham ta fad'a gado ta rufe idanunta zuciyar ta tana wata irin bugawa,da bata d'auki alk'warin dai na shan taba ba to da yau ALLAH ne kad'ai yasan ko kwali nawa za ta sha,ba ma kara ba,ta dunk'ule hannu ta dinga naushin matashi idanunta na tsiyayar da hawaye masu d'umi " So babbar cuta...

Lidiya ta dafa kafad'arta sai tamik'e da sauri kamar wacce kuna ta harba"get the hell out this house...ta fad'a a haukace.Lidiya tamik'e sai dai in bar miki d'aki amma ba gida ba,dan kema ba na ki bane. Wawuya kawai da har yanzu ta kasa gane san maso wani take yi... Sai kinyi 6atan 6akatatan za ki gane ashe shayi ma ruwa ne madara da bournvita ne ya canja mishi kala.

Mamanta tana dawowa daga kasuwa ko hutawa batayi suka tasata a gaba sai gidan Pastor.Dama yasan da zuwansu dan haka suka zauna zaman jiran fitowarshi Yashigo D'akin-shak'atawar cikin bak'in suit, rigar ciki shirt, takalmanshi da mashak'in wuya (neck-tie)ruwan k'asa,wuyarshi da sark'a rosery.


Yana rik'e da King James Bible.Da fara'arshi yake musu sannu da zuwa shi ma yazauna suka gaisa sannan ya nuna Kasham da kanta ke hayaki ta d'ora kafa d'aya akan d'aya"ke kina so ki bamu matsala me yahad'a ki da bahaushe ne?Tagalla mishi harara tana mishi wani kallan uku ahu "ah kaji k'arfin hali 6arawo da sallama,yanzu kurace za ta cema kare maye? Shi har yana da bakin da zai ma wani fad'a yaushe-yaushe aka gama rigima d'an shi na cikinshi yama wata yarinya yar Kurmin-Bi ciki,yanzu haka yarinyar tana cikin gidanshi sunyi auran leda (auren da ba Pastor ne ya d'aura shi a majami'a ba Church)wai sai ta haihu za a yi auran gaskiya dasa albarkan Iyaye.Yasake kallanta ba magana nake miki ba?To me ko zai had'ani dashi banda soyayyay.Ina son Julaibib zan kuma aureshi ko kamin addu'a bazai kama niba,ai wallahi gwamma ni ba ciki a kamin ba.Maman za ta mareta yahana kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake yi, ki barni da ita kawai Dinatu.

Pastor wannan abun yana cimin tuwo a k'warya,Ya'yanmu da zarar sun girma sun yi soyayyya da hausawa sai kaji suma suna san zama masu sallah, sai su gudu su aure su ko muna so ko bama so,to a kan me za su dinga yaudare mana Ya'ya suna mana d'auki dai-dai suna converting d'insu zuwa musulunci?Sannan su Ya'yan hausawa mata basa ta6a yadda suyi soyayya dana mu Ya'ya mazan,abun yana k'ok'rin shige makad'i da rawa fa,na rantse maka da girnan ALLAH Ya'yanmu mata da suke sallah a cikin gari sunyi yawan da ko mun fara k'irgasu lissafin zai k'wace mana,to gaskiyar magana sai kun k'arae zage dantse da k'wazo wajan preaching ta yadda za Ku dak'ile wannan al'amari suma suji suna k'yamar mazan hausawa kai ba su kad'ai ba da duk wani me sallah kawai(😊Up up up Diniyal-Islam👏).

Yagyad'a kai"Ki kwantar da hankalin ki Dinatu wannan matsalar ita muke tattaunawa a taranmu na Christian Association Of Nigeria(CAN) har yanzu muna kan aikine,ai kowa yaci tuwo damu miya yasha, wannan makon ma a kawai babban taro a Jos har daga kasar waje za muyi bak'i.Wani murmushin mugunta ya su6uce mishi"wallahi za muma duk wasu masu sallah na Southern Kaduna(Kudancin Kaduna)wankin babban bargo a k'aramin k'oko'.Suka gyad'a kai cikin gamsuwa "yauwa Pastor ALLAH yataimake ku. Amin,amin.

Pastor ya dad'e yana jero addu'o'in shi su kuma Iyayan sun durk'usa gwiwa bibbiyu sun rufe idanusu tare da had'e tafukan hannayansu idan yayi addui'ar sai yace In Jesus name we pray sukuma suna amsawa da Amen,amen,amen,ameeennn....

Ita dai kallansu kawai takeyi har zuciyarta ta lula tunanin Enigma man d'inta D'ansarai.Tayi murmushi "Julaibib idan ka aureni za kaji dad'in rayuwar ka,zan saka farin ciki na karanci"Catering & Hotels Management.Na san Food and Nutrition zan dinga shirya maka abinci me rai da motsi, ingantaccen abinci me gina jiki da k'ara kuzari,za kaci har sai ka ture..bata san Pastor ya gama 6aragadar shiba har sai da Babanta ya ta6ata"Kasham tashigo mu tafi gida an gama ganin idanunta a rufe sun zaci ko itama amsawa ta dingayi.

"Gobe ma ku dawo".

Tajuya tama Pastor d'in wani malalacin kallo sannan tajuya,wallahi ba inda zan dawo idan za a ma mutum addu'a lallai dole-dole sai yana wajan? ALLAN ai yana jin kome...


Abinda yafi kome mahimmanci a rayuwar d'an Adam ya fi kome sauk'i,sai Ubangijinmu bai horema kowa mallakan shiba dan kar a k'unta ta ma bayinshi, sannan bai horeshi kaasatan (ake6e) ga bayinshi na gari ba, a ah yabarshi kowa yasamu,Ubangijinmu me rahama da tausayin bayine...

Iskar da muke shaka ta ALLAH ce ba wani me iko da ita.

Ruwa da kusan shine rayuwa duk rintsi duk wuya akwai shi.

Rana kullum sai ta fito itama ta ALLAH ce babu wani me iko da ita.dasauransu...

ALLAH mungode maka da kayi mu musulmai masu bin tafarkin Manzanka,ba dan mun fi wasu girma da daukaka ba a ah ganin da markace kawai.

Ya Ubangijinmu!Kaine me jujjuya zukatan bayinka...ka tabbatar da zukatanmu a kan addinin da ko a wajanka ka kirashi da musulunci.


27 Rabi'a Thani 1441
24 December 2019


We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.







DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFI💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)


Shafi na tara.


A gida Nasir yasamu Julaibib yana fad'a mishi jiya da daddare su Aisha suka dawo.Yauwa Nasir nagode maka ba kad'an ba, yad'ibo dabino me yawa yabashi.Yasa hannu biyu yakar6a cikin murna.Nima nagode Kawu.

Bayan sallar la'asar suna tsaye a k'ofar gidan tafito sanye da farin hijab tana murmushi.Tagaishe su a ladabce.Musaddiq yace to ya gajiyar hanya? Sai kawai kiyi tafiya ba sallama?Tad'anyi murmushi Yaya Musaddiq a min afuwa bazan sake ba.Yagyad'a kai to shikenan. Yayi gyaran murya karmu 6ata lokacin mu tunda lokaci jarin d'an Adam ne,Aisha magana ta gaskiya za muyi.Yad'an kalleta tana tsugune natsuwarta na ga sauraran abinda zai fad'a. Julaibib yana sanki, za ki iya auranshi? Shiru ya ratsa wajan, ta had'a kai da gwiwa dak'ik'u nata tafiya bata ce kome ba.Aisha yi magana mana. Yakalli Julaibib to wata kila ni take jin kunya barin ba ku waje"dama shirun budurwa yaddan ta... bawazara kuma sai ta tanka.

Tad'ago da sauri kwallah

Please Login or Register in order to submit comment