Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ba ta kulashi sai dai tayita kallanshi.Tamaida kanta jikin kujera ta lumshe idanunta tana wata kisima a zuci "Julaibib kyakkyawane"Melanin beauty"tayi nazarin shi dakyau baya san hayani,wani abun ba wulak'anci yake mataba haka halinshi yake bashi da yawan magana,tana so ta aureshi tahaifi yarinya me irin kwantaccen gashinshi, tana san Julaibib ta rasa ya zatayi da rayuwarta"Ciwon so" data san inda zata nemo maganin shi tasha ta warke daga san D'an Sarai ne?


"Oh my God!, ta dunk'ule hannu ta naushi iska"


Dasauri tamik'e zuwa wajanshi D'ansarai takira sunanshi.Yad'ago yakalleta yacigaba da abinda yake yi,sai ta rasa me zatace...Dan ALLAH bani aran correction pen. Yaciroshi a aljihun gaban rigarshi daya soke yamik'a mata.Tashafi hannunshi sannan ta kar6a "nagode idan nagama zan kawo maka.Yagirgiza kai "Kirik'e kawai.To nagode,tasa ajaka dama neman magana ne itama tanada nata fa.


Duk ranar alhamis suke House Assembly, wani ikon ALLAH sai akasa Kasham da Julaibib a house d'aya,Sudaida ma anan take. Kasham a matsayinta na sabuwar malama ita tafara musu bayanin kanta da yar nasiha,sai malamai biyu duk yan TP sai Julaibib cik'on na hud'unsu.Cikin natsuwa yake musu bayani sannan yad'ora da nasiha a kan su dage da karatu ba kawai sai lokacin jarabawa ko za ai wata kaci-kaci da muhawaraba, kullum Ku zama masu nazari da bincike da tambayar duk abinda baku ganeba, da wanda baku saniba da hakane ake samun ilmi me yawa,ita k'wak'walwa d'an Adam ne yake cikata da aiki,idan kuma baiyi hakan ba to ita zata cika mishi da abubuwa na shirme wanda bazai amfaneshi akaran kanshiba,bare har al'umma ta amfana,ina fata zaku dad'a sa k'wazo duk da nasan kunayi amma Ku k'ara, ina kuma fata zaku zama masu amana kamar yadda sunan gidan na ku yake "Amana House.

D'alibai suka d'auki tafi.A'isha da take bayan Sudaida tace"Amma gaskiya ina san Yayanki Sudaida,yanayinshi me sanyine,sukayi murmushi.Mr Julius shugaban house d'in shima yatafa mishi,yau bani da abin fad'a.Yanuna Julaibib da yatsa"This great teacher of ours has said all".Yad'an bubbuga kafad'arshi sukayi murmushi,sannan yakalli d'aliban yad'an motsa kafad'arshi"shikenan you can go back to your classes" duk suka watse.


Maimun yakawo musu ziyarar bazata ranar juma'a da yamma,sun kuma ji dad'in haka sunata ba juna labarin makarantun da aka turasu har Maimun yasako mishi maganar Kasham...Yayi kamar badashi yakeyi ba.Zuwacan kuma yagirgiza kai"ni fa ba zanyi abinda zai zama min matsala ba,aure ba abin wasa bane, ba kuma yin auran ne yadameni ba,a ah samun matar data dace dani me mutunci da mutunta kai.Kasan ALLAH Julaibib Kasham tana sanka,wannan soyayyar da take maka zaisa tamaka biyayya tabi umarninka.Yagirgiza kai"Kyaleta kawai Maimun. Maimun bai kuma maganarba suka cigaba da hirar data shafesu har Musaddiq yafito suka tafi k'wadago neman halali.


Baranzan yajuya yana kallanta"Ke wai meye damuwarki ne?Wani haushin shi takeji gwamma tabar mishi d'akin dan batayi maraba da zuwan shiba,idan tazauna za ayi d'anyan aikine dan shima bashi da mutunci idan yana 6acin rai.A fusace tajuya zata fita,caraf taji yarik'o dantsen hannunta kamar zai k'aryata.


Tarinse idanu dan azaba. Yasunkuya akan fuskarta"sai kin fad'a min da uban wa kika fara soyayya da har kike guduna? Sake min hannu.Yasake rik'eta tamau.Sai fa kin fad'amin da uban wa kika fara soyayyah? Haushinshi yadad'a ninkuwa a zuciyarta Kawai sai tace da"Ubanka...bata gama rufe baki ba taji saukan mari hagu da dama,idanunshi suka kad'a jawur"za kimin rashin mutuncine?Uba na sa'ankine?Yafad'a da karfi cikin tashin hankali da alama allurar soja ta motsa.Uba na ko? Tagyad'a kai duk da a zabar rik'on data keji.Kikace eh? Yashak'eta,manyan idanunta suka fir-firto numfashinta yazo wuya,yasake kifa mata mari hagu da dama,sai da taga wasu k'ananan taurari sun tarwatse, gefen bakinta ya fashe,ji da ganinta suka d'auke na wucin gadi..


Wannene abin so?... A tari fitsari a wanke zawo?


18 Rabi'a Thani 1441
15 December 2019


We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs



DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFIđź’”



Almost true story
Daga alk'alamin đź–Š
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na biyar.



Dak'yar aka 6an6areta a hannunshi bayan tasha wahalar duniya.Yarafff... tafad'a gado tana wani irin tarin wahala tana fuzgo numfashin ta dayake k'ok'arin kufcewa.Shima ya fuzge daga rik'eshin da akayi ana ta bashi hak'uri,yayi kanta,aka sake rik'eshi


Lidiya tashigo da gudunta dan bata san abinda ke faruwa ba yanzu aka kai mata rahoto"haba Baranzan kazama namiji mana, jarumin namiji me kwanan daji irinka me zai sa katsaya fad'a da mace?Kasham fa kwana biyu bata da lafiya ya kamata kamata uzuri.Anki a mata uzurin wa tafad'a ma bata da lafiya? Yabita da kallo tana kwance sambal,gashin kanta a hargitse kuma ta rame ba haka yasan Beauty d'inshi yar gayu ba.To kitashi muje asibiti. Shiruma amsace.Yad'ibo wasu damin kud'i yaba Lidiya wai tarakata asibiti ta tabbata an dubata ankuma bata magani me kyau.Tagyad'a kai tare da sara mishi "Yes sir tabuga k'afar damanta a k'asa.

Tarakashi da adawo lafiya sannan ta rufo k'ofar ta zauna a bakin gadon,tasa hannu tashare mata jinin da yake gefen bakin ta,tabud'e idanunta suka kalli juna.Lidiya tad'an d'age gira"wallahi kashin kare baya taki" Baranzan shine yadace dake ba wancan tsinannan bahaushen ba,danni bazan fasa fad'a miki gaskiya ba,kome naku d'aya da Baranzan"Hun wai saboda wani bare da bai san ALLAH yayi ruwan tsiran kiba kike ga ba dani,indai bani namiki magana ba ke bazaki minba. Tamaida idanunta tarufesu"ita abinda yadami zuciyarta shi d'in ne yadameta"daga ita har Baranzan basu d'ad'ata da k'asaba"kowa da kiwon daya kar6e shi mak'ocin me akuya ya sai kura".

A'isha tabiyo Sudaida dad'an gudunta da aka buga tara"Ke malama jirani"Tatsaya tana kalllanta har ta k'araso"Kefa kika ce ba inda zaki".Aisha tagyad'a kai"Eh nafa sane naga gaba d'aya ajin an watse an barni kamar mayya,me zaki siyane?Ta tambayi Sudaida"Ba abinda zan siya dan bana jin cin kome na makarantar nan yau.Wajan Nasmat zani.Tarik'o hannunta"Dalla shareta zo muje wajan Yayanku tad'an turo baki me zanje in mishi?Ke shifa Yaya D'ansarai ba yaso a dameshi.Ke dai zo muje mana ni wallahi ina sanshi.Sudaida tamata wani kallo sannan ta ta6e baki"Lallai kinji jiki, Yaya Julaibib d'in kike so?.Eh wallahi"Yanayin shi me sanyi ne,baya san hayaniya.

Wa alaikumussalam.Ya amsa sallamar su. A'isha tamata nuni wai su zauna,ita kuma tana nok'e kafad'a.Yad'an d'ago yakalle su,sai yacigaba da nazarin d'aya daga cikin tarin littafan dake gefan shi,hannunshi rik'e da jan biro da alama hannu yake sawa akan aikin daya basu.Yasake d'agowa yakallesu ganin sun zauna sunata kallanshi"yaya wani Abu ne?Aisha tayi tsagal "Yaya Julaibib dama... da... sauran kalaman suka mak'ale saboda wani rikitaccen kallo da yake mata,sai ta mik'e "bakome Sudaida taso mutafi.Har sun jiya Sudaida taji kiranshi.Ta tsaya sannan tajuyo tana kallanshi ya yafitota da hannu.Tak'arasa wajan"Yaya Julaibib gani "Yad'anyi murmushi"hala kud'in taran na ku ba yawane yau?A ah wallahi muna da kud'inmu. Yamik'a mata wasu kud'in"duk da haka sai Ku k'ara,tasa hannu biyu takar6a"Mungode ALLAH yak'ara bud'i.Yad'an bita da kallo yana murmushi.

A'isha taja tsaki kawai anzo wajanka amma saika wulakanta mutane. Sudaida tad'aga mata hannu"a ah wallahi Yaya D'an Sarai bashi da wulakanci, kuma baki ga abinda yakeyi bane?Ai dama nafad'a miki shi fa baya so adameshi...Nasmat tak'araso wajan tatarar da Aisha tana k'unk'uni "Ke da wa kuma?Da Yayanku d'an wulak'ancin can mana tanu mata Julaibib d'in da d'an yatsa.Nasmat ta kyalkyale da dariya miskili kafi mahaukaci ban haushi"to amma shi da baya shiga shirgin mutane to me yahad'o ki dashi? Tawatsa hannu"shareshi kawai suka cigaba da tafiyarsu suna hira.

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar lahadi suna hirarsu da Inna Khalifa d'an mak'otansu yashigo da gudunshi"Yaya Julaibib ana sallama dakai"To kace ina zuwa. Suka cigaba da hirarsu,ganin bashi da niyyar tashi Inna tace"Tashi katafi mana.Yamik'e To Inna yad'auki rigarshi daya cire yana sawa,a zaure yak'arasa sawa,yana fitowa caraf idanunsu yahad'u,yamata wani irin kallo data kasa fassarawa.Tayi yar dariya"Malam D'ansarai kenan wato ganina yasa ka canjawa kamar kaga me tagayyara rayuwarka har abadan duniya ko?To ni dai nazo gaisheka ne,wancan makon ko sau d'aya ban samu nazo makarantaba dan bani da lafiya kuma a dalilin sanka nashiga halin dana shiga amma ko katambaya"Lafiya kuwa Kasham bata zuwa makaranta?To koma dai yayane Thank God naji sauk'i,ina kuma so kamin jagora zan shiga gaishe da Mama."Bata nan"Yabata amsa a takaice. Takama ha6a🤔D'ansarai wallahi bakayi kama da masu zabga k'arya a kalaman suba,nafa tambayi yaran yacemin tananan,inaso muyi kome cikin mutunci da girmama junane shi yasa ban shigo kai tsaye ba,amma kai naga kamar ba hakama kake so ba,idan natsaya rarrashinka kuma raina ne kawai zai 6aci a banza,tunda har yanzu baka d'aukeni wata tsiya ba,ko albarkacin k'aunar da nake maka ban ta6a ciba.


Koma inda kika fito,tunda ba gayyatoki nayi ba.Tagirgiza kai idan kamin haka tsakani da Allah baka min adalci ba,tanuna mishi Bible d'in hannunta daga majami'a (Church) nake,ana tashi nashigo cikin gari ko gida ban koma na ajiye Bible d'in ba,duk dan d'okin ganinka.Yau d'aya dai kamin adalci a matsayina na yar Adam bama masoyiyar kaba.

Inna tafara jiyo hayaniya."Na rantse da girman ALLAH idan kika tako inda nake sai na 6allaki.Inna tajuyo furucinshi cikin fad'a.Kai dawaye Julaibib?Inna ta tambayeshi bayan tashigo zauren.Cikin tafasar zuciya yajuya yakalli Inna idanunshi jawur"ni da wancan mara kamun kance.Zuciyar ta tabuga Dammm...Kasham wato kwana biyu da bataji d'uriyar taba ta zaci ta hak'urane kamar yadda taita zuwar mata kwanakin baya. Inna dai hakuri take bata tunda maigayyar yace baya so, zuwan ta nak'arshe da Inna tafad'i haka yar dariya kawai tayi tamata sallama tatafi .To yau kuma kwatsam ba zato sai gashi tadawo.

Kasham daga waje tace"Mama kice yabarni in shigo dan ba wajanshi shi kad'ai nazo ba har dake,idan kuma ba haka ba zan mishi abinda har abadan duniya bazai manta dani ba.Wata jijiya tafito rad'am agoshin shi kamar shatin bulala"ni kuma sai dai baki k'araso wajan nan ba amma wallahi sai na 6allaki"ke! yafad'a a tsawace idan kin fasamin abinda bazan mantaba har abadan duniya ke ba...Inna tatareshi"Kai Julaibib dakata! Inna wallahi...tad'aga mishi hannu na dai ce ya isako?Yasunkwui da kai.."haba Julaibib idan rai ya6aci bai kamata hankali ya gushe ba,wai kamanta da sharrin mace har yafi na shaid'an kaifi?.Bai sake magana yasa kai yafita.

Kasham tashigo zauran suna gaisawa,Inna tabita da kallan tausayi"Iska na wahalar da me kayan kara.Takai gwiwoyinta k'asa tahad'a tafukan hannayenta alamar magiya idanunta sun ciko da k'wallah "Mama ki taimakeni mana".

Inna tajijjiga kai"Zanso k'warai Julaibib ya aureki ko dan matsananciyar k'aunar dakike mishi,kuma ya tsamoki daga duhu zuwa haske amma hak'ata bata tadda ruwaba,to kema me zai sa bazaki hak'uraba? Sharrr...hawayen masu d'umi suka zubo a kyakkyawar fuskarta "saboda ina san shi Mama,Julaibib d'an kine na san zaiji maganarki,idan kikace dole ya aureni ai bazai k'i miki biyayya ba.Inna tadafa kafad'arta "Kasham kenan, kasancewar Julaibib d'a na ne ba yana nufin in tilas tashi yin abinda baya so bane,Julaibib yana da hakki akaina, kamar yadda nake da hakki akanshi,shi aure ba abin wasa bane,zaman aure kuma ana yin shine bana wucin gadi ba,a ah zaman din din din ne da ba a san rabuwa sai dai idan k'addarar hakan ta kasance ba yadda za ayi,kinga shi yasa ma ake so mutum yaza6i abokin rayuwar daya kwanta mishi arai, kowa yanajin k'auna da soyayyar d'an uwanshi da gasken-gaske,tayadda idan an samu sa6ani za ayi fad'a, idan an huce za ana juna uzuri,za a yafema juna, amma idan d'aya a dole yake zaune da d'aya to abu kad'an d'in da bai ta ka kara ya karya ba sai rigima ta 6alle wanda daga nan auran zai lalace an rabu, to ina amfanin 6ata goma biyar bata gyaruba?

Suna cikin haka saiga Alhaji Abdullahi yashigo shima da nasiha yabita me ratsa jiki.Tagyad'a kai"Eh tabbas duk abinda suka fad'a gaskiyace wacce daga k'inta sai 6ata. To amma fa ita har kwannan gobe tana san D'an Sarai bata kuma cire rai da auran shiba.

Bayan sun gama cin abincin dare.Alhaji Abdullahi yakalli Julaibib "D'ansarai na san ba abinda ke tsakaninka da wancan yarinyar amma duk da haka sai ka k'ara yin taka tsantsan,dan shaidan baya raina k'ofa,kai kace bazaka aure taba,ita kuma bata hak'ura ta daina bibiyarka ba.Kanemo mata kayi aure dan shine kwanciyar hankalinka damu kanmu,bana so kad'auki wani dogon lokaci ba tare da iyali ba.Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi "Sannan ya amsa cikin ladabi.Amma cikin zuciyar shi inda kizo ke sak'ar wacece yake jin santa? Dammm...Zuciyar shi tabuga,yayi maza yakawar da tunaninta a,Yasauke gwauran numfashi " Yau ake yin ta wai anyi da mutum ya ji"...

Hajiya takalli Sudaida da 6acin rai"Kai wannan yarinya da kafirin taurin kai take kamar mutanan farko,za ki d'auka kisha ko sai na sa6a miki? Ta turo baki gaba"ni fa wallahi na ji sauk'i"ke tafi can kinji sauk'i amma kwana biyu kina kwance?Ni na ta6a jin inda akayi haka? Baka da lafiya bazaka sha magani ba,baza a maka alluraba?To ko duk tsiyarki gobe sai kin tafi makaranta dan naga abun na ki "Tsiya ne d'inkin ludayi.

Ya shigo da sallama.Tabishi da kallo "Yaya Julaibib ina atilan dana ce kasiyo min"?Yayi kamar ba dashi take magana ba, yazauna a kujera suna gaisawa da Hajiya.Tad'anyi tsaki"ALLAH yasauwak'e maka wannan halin... takauda kai daga kallan da take mishi tafara k'unk'uni saiga Sinan shima ya shigo"Tace yauwa Sinan kamar kasan ina mararin ganinka.Yagaishe da Hajiya tare da tambayar ya akaji da me jiki? A Alhamdulillahi ai taji sauk'i tunda har tana k'in shan magani, shekaran jiya da bata san inda kanta yake ba ai ina bata take kar6a tashanye ba musu ba gaddama.Sudaida ta turo baki gaba ni fa kaina ba inda yatafi yabarni muna tare har a k'abari.

Sinan yamatsa kusa da gadan da take kwance ta lullu6e jikinta da bargon Hajiya fuskarta kawai ta bari a bud'e.Yamata wani kallo"Sannu sarauniyar Sinan" tagyad'a kai cikin murmushi.Yafara mata magana k'asa-k'asa. Takyalkyale da dariya tad'an zaro idanunta"Kaiiii Sinan wallahi ba ruwana.Sai yamik'e tsaye daga sunkuyan da yayi a kusa da ita"Me zan kawo miki anjima"?Tad'an harari Julaibib caraf idanunsu yahad'u tadauke kai,sannan tad'an marairaice "atile"dame kuma?Sai kuma yaba kanshi amsa"da masoyin sarauniyar Sinan rake.Tayi murmushi" Wallahi nagode maka ba kad'an ba Sinan.Tad'aga hannu tana mishi adabo"adawo lafiya.

Filin wajan da malamai suke ajiye mashina da motoci taje,tad'are mashin d'in Shunkut dan yayi saiti da inda Julaibib yazauna a barandar d'akin malamai,tana kare mishi kallo...Tayi murmushi cikin sauke numfashi "Julaibib da ka san matsanan cin son danake maka wata kila daka ceci zuciya ta da take shirin yin gobara.

Holy ghost fire!

Lidiya tafad'a dan Kasham batama san tazo wajan ba.Akan wancan tsinannan bahaushen kina neman zama mahaukaciya"For Christ sake wai me yashiga k'wak'walwarkine? Lidiya kome zaki fad'a min indai akan son wancan bahaushen ne tamata nuni da inda yake zaune, to ina maraba dashi,kin sani tun ganin Julaibib a kuma kallanshi farko so da k'aunarshi suka mamaye zuciya ta,shi kanshi ya fad'a min uncountable times bazai aure niba and I don't know why har yanzu nake jin kaunar shi deep down my heart".

Tadafa kafad'arta ki tayani addu'a duk ranar da ALLAH yabani sa'a yashiga nan ta nuna tsakiyar tafin hannunta,yad'and'ani zak'i da gardin zuma ta,to wallahi na mishi katttt...kisan mummuk'e.Lidiya ta kyalkyale da dariya"gaskiya iska tana wahalar da me kayan kara,malama dame kama ake yin k'ota.Wancan me shegen girman kanne kike tunanin za ki yaudare shi?To yaushe ma yatsayi kulaki bare har hilarki tayi aiki akanshi? Wallahi kinga dai bana san shi amma na jinjina mishi đź‘Ťzan kuma iya bada shaidarshi harkar mata baya yinta, dan da yanayi wallahi ko sau d'aya ne tun zuwanshi Gidan-Waya da mun sani,kema ai kin san mune idon gari a makarantar nan,wannan harkar sai sojanki Namamajo,ke dai kawai ALLAH yaganar dake,amma banda 6atan basira mutum yace baya sona to nima banga abinda zai sa ya kuma d'ad'ani da k'asaba tunda shi d'in ai ba mahad'in numfashi na bane,ko yaranmu d'aya dashi zan hak'ura in kyaleshi,bare wani hausawa me girman kan tsiya,shiba kowan kowaba dillalin kashi,kin sani ni nak'i jinin hausawa, ke ba hausawa kad'ai ba duk wani me sallah bana sanshi da inda k'arfin iko na rantse miki da ALLAH ba wasu tsinannun masu sallah dazasu zauna mana a gari.Taja tsaki fuskar nan tarine da 6acin rai ruwan kafircine zallah babu gauraye da haske da tausayi da Imani ko na sisin kwabo, jikar kajawace (Bajju) gaba da baya"bana san ma su sallah.Kuma ba yadda za kiyi dasu "sun zama kuturwar uwa dole a zauna dake.Kasham tabata amsa,sannan tasauko akan mashin d'in tawuce bayan aju-juwa da aka k'awata wajan da shuke-shuken filawowi masu ban sha'awa,tadinga bi tana tsinkosu kaloli mabambanta masu k'amshi tacika hannunta sannan tasa zaran ulu,ruwan hoda tadaure tawuce d'akin malamai zaman jiranshi.Dak'ik'a biyar da buga k'ararrawar canjin darasi sai ga shi yashigo,saida tabari ya zauna a kujerarshi yana hutawa ba ajin dazai kuma shiga sai gobe.Yakwantar da kanshi a jikin kujerar, idanunshi a rufe wani bacci me dad'i yafara shirin saceshi sai kawai yaji an shafa mishi wani abu a daidai hancinshi me wani irin k'amshin dad'i, yabud'e idanunshi da yanayin bacci har sun d'anyi ja.

Tamishi lallausan murmushinta "perceive the natural fragrance of this bounch of flowers.Tafurta hakan da wani salo irin na ta nayanga sannan tacire daga hancinshi ta d'ora mishi a saman tebur.Yakauda kai daga kallan da take mishi kamar kura taga nama.Wallahi yama rasa abinda zai ce mata.

Tayi k'asa da murya ganin wasu malaman sun fara sa musu na mujiya"ai nasan ban kyauta maka ba ko?Kai dai ba a maka gwaninta,d'an motsa kafada tayi "karka damu dani,kar kayi la'akari dacewa nice nakawo maka,tagirgiza kai kayi la'akari kawai da tarin amfanin da k'amshin furen filawa yake dashi ga d'an Adam.How I wish Jualiabib ka bani dama na nuna maka irin kaunar danake maka, tagirgiza kai cikin damuwa "How I wish ka tallafi zuciyata ka magance min damuwar cikinta...sai dai kash!Ban samu hakan ba,saboda baka san illar kaso a k'ikaba,tabbas daka san haka da baza kabari zuciyata tayi gobara ba.Tahad'a tafukan hannayenta alamar magiya "Don't let the love that I have for you to go in vain please...!

Yad'ago yakalle ta,sai yaji wani abu ya tsirga ilahirin jiki da zuciyar shi,har ya bud'e baki zayi magana sai kuma yagirgiza kai"a ah Julaibib daure kawai, maganin kar ayi to tun farko kar a fara"kawai sai yamik'e yabar d'akin.

Shunkut ya sunkuyo a fuskarta yana murmushi"Ke ki hak'ura dashi mana ai ba a soyayyah dole, yanuna kanshi da yatsarshi"ni d'in nan namiji ne duk abinda yake dashi namazan taka nima ina dashi,kiyadda kawai muyi soyayyah.A fusace ta tureshi"you fool! dawa za kayi soyayyah Shunkut?Tayi d'as da yan yatsunta over my dead body.Tagalla mishi harara sannan taja mummunan tsaki"ruwa ai ba sa'an kwando bane"sai yajuya yana tafiya "Amma kuwa za kiyi 6atan 6akatantan...

A gajiye lik'is yashigo,gidan shiru dan Inna tana gidan Hajiya,yazauna yana hutawa, ya6alle botiren gaban farar rigarshi,yamaida kanshi jikin kujera tare da lumshe idanunshi sassanyar iskar bayan la'asar tana ratsashi. Mafarkan da kwana biyu nan yakeyi sun tsaya mishi a rai"Kasham yake gani cikin kyakkyawan kirar kalangunta,sanye da kayan fulani,gashinta yasha gyara ta tufkeshi a baya,amma kuma idan tayi magana muryar Sudaida yakeji"ya rasa kan wannan mafarki.

Hayaniyar shigowarsu Kamila yasashi bud'e idanunshi,aiko suka shigo sunata zuba surutunsu, sunata mishi tambaye- tambaye.Shigowar Musaddiq yasa suka koma tsakar gida suna wasannin su,yadaki kafad'ar shi"kai malam tashi da ALLAH magana nazo muyi. Uhun ina jinka.Musaddiq yabishi da kallo"Julaibib ka nemi A'isha kawarsu Sudaida mana tunda dama ta nuna tana sanka kaine baka bada goyon baya,tana da hankali kuma ko su Baba idan sukaji ita kake so za suji da...yatari numfashinshi a hasale "bata min a matsayin matar aure ba,dan haka akai kasuwa".Yakalle shi da mad'aukakin mamaki"To me yayi zafi da har idanu za suci wuta haka? Tagyada kai "To yayi,indai har A'isha bata maka a matsayin matar aure ba to ashe gulmace da kai,kana kuma kallan mata za kuma ka iya za6a,amma da zarar magana ta tashi sai kace ba sa gabanka,to kuma harsu Baba sai sunji zancen nan.

Yanunashi da yatsa"Idan kai zaka min zaman auran ai sai in aureta.Yamaida idanun shi ya rufe, shi wai ma wacece wata A'isha?Wasu lokutan dai Sudaida tana fad'a mishi"A'isha tace tana gaisuwa"ko kuma

Please Login or Register in order to submit comment