Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)




Shafi na ashirin da uku.




Kwanakin su uku Doctor Khadija Aminu kagarko tabasu sallama dan Alhamdulillahi ta samu sauk'i, wata ma'aikaciyar jinya tana tsokanar Julaibib saboda yadda yadamu da Sudaida,lokacin ba da magani (medication)nayi idan basu zo ba da kanshi za shi yakira su"ALLAH dai yasa d'an daza'a haifa yamaka kara yayi kama da kai dan ba k'aramar hidima kayi ba.Yayi murmushi kawai yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi.Mutan Zonkwa ma d'ai-d'ai kune wad'anda basu zo dubiya ba a cikin yan'uwa da abokan arzik'i.

Doctor Kagarko takalli Sudaida cikin kulawa"ki kula da kyau kinga aikine a jikinki,banda aiki bare d'aukar abu me nauyi okey?Sudaida tagyad'a.Tarakasu har wajen mota, Sudaida tashiga tazauna sannan ta rufe musu motar, tad'an sunkuyo ta taga"Hajiya ALLAH yakiyaye hanya. Madam adinga kula da dressing d'in wajen yadda yakamata, kidawo akan lokaci kar fa kiyi sakaci.Tad'aga hannu tana musu adabo,suma godiya sosai suke mata.Doctor Khadija Aminu Kagarko ta san ya kamata.

Julaibib da Hajiya su suka cigaba da kula da ita da ayyukan gida.Watannin Hajiya hud'u tafara musu zancen tafiya.Sudaida tawani marairaice"Lillahi warasulihi Hajiya yanzu sai ki tafi kibarni?Tagalla mata harara"to da ni zan tayaki zaman auren?Taware yatsunta hud'u watannina haka a gidan nan,ai ko na yi iya abinda zan iya.Julaibib yagama abinci yazubo musu a faranti"sannu da aiki Zaujiii...Yayi murmushi kawai,yashige bayi yahad'a mata ruwan wanka

"Sudaida ga ruwan can kije kiyi wanka.Hajiya takama fad'a"kai Julaibibi bana ce kadaina kai mata ruwan wanka ba?Ruwan kawai da za ta bud'e famfo ta tara sai an mata kai haba,tanuna shi da yatsa "kazama jarumi dan a haka nasanka.Sudaida tamik'e kaji matar nan da wata magana to ko wankan ma idan takama ba shi zai min ba?Tamata dakuwa"ungo nan,zancen banza kawai dan an miki aiki shikenan kuma ke bazaki dinga motsa jikin kiba? Sudaida tawuce batayi magana.

Ita kuma Hajiya tana dad'a jaddada mishi gobe Insha-ALLAH zan koma in da nafi wayau Zonkwa.Yagyad'a kai sannan cikin girmamawa yace"ALLAH ya nuna mana goben da ran mu da lafiya...mungode kwarai Hajiya ALLAH yak'ara nisan kwana me amfani.To amin kaga ai kai ka san yakamata,ita wancan matar taka ai bata gode min, niko ba in da zan fara azumin watan ramadana sai a d'akina. Kiyi hak'uri Hajiya bari tafito ai dole kuwa tagode miki.

Suka cigaba da hirar su har Sudaida tafito,yad'ago yana kallan surarta a cikin hasken farin watan daya haskesu"kinyi kyau Zaujatiii...Hajiya tagalla musu harara musamman Julaibib daya kasa daina kallanta,takad'a kai"ba shakka ai kinji sauk'i tunda kika iya zama kiyi wannan kwalliyar abin ma bai tsaya anan ba kikabi jiki kika shafeshi da wannnan shu'umin humran me k'amshin fita a hayyaci,to ni kuwa zaman me zan kumayi?

Sudaida tayi lallausan murmushi"haba Hajiyarmu ban fa sanki da halin sa'idawa ba,yanzu har wani kwalliya nayi?Ko unguwa ai zan iya fita a haka.Eh to in dai kai kikaci(hauka)ai bazan musa ba.Suka kalli juna ita da Julaibib tamishi wani kallo ta kashe mishi ido...Yakai hannu yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi a hankali ya motsa la66anshi,Sudaida ta matsa kusa dashi"ni dai Yaya D'ansarai ban gane me kake fad'a da la66a ba gaskiya.Hajiya tamik'e"abin nayi ne to ALLAH ya tashemu lafiya.Sudaida tace kai Hajiyarmu yau da wuri haka zaki kwanta?Eh dan gobe sammako zanyi Julaibibi sai da safe.To Hajiya ALLAH ya tashemu lafiya.

Washe gari tun daga sallar asubahi bai shigo gidan ba sai da hantsi yadubi ludayi da kaya nk'i-nik'i,duk suka bishi da kallo har yagama shigo dasu sannnan yazauna suka gaisa.Hajiya tace"ai na zaci guduwa kayi saboda kar in tafi dama nace anjima kad'an tafiya ta zan yi ko kadawo ko baka dawo ba tunda duk wayoyinka a guda kabarsu. Mantawa dasu nayi sai da nayi nisa da tafiya sannan na tuna.Jos natafi na miki siyayyan tsaraba dana azumi.Hajiya tabi manyan ledojin da kallo tana jinjina k'ok'arinshi tare dasa mishi albarka"Ubangiji yayi albarka, yabaku masu muku madallah nagode nagode Julaibibi. Yayi murmushi"ai ba kome Hajiya, yad'an kalleta cikin natsuwa "na so kwarai da dakaina zan kaiki to amma hakan bazai yiwuba saboda yanayin aiki,yanzu ma Kafanchan zan tafi amma na ma wani direba magana k'arfe d'aya na rana zai zo kutafi,yasake bata wasu kud'ade sannnan yamik'e dan shirin tafiya Kafanchan.

Sabo turken wawa...kowa yayi fushi da bak'o ya ji kunya,da Hajiya tatafi sai taji gidan ya mata girma gashi shima Julaibib ba ya nan tagaji da nazarin da takeyi a cikin na'ura me k'wak'walwa ta rufe, tasa bayan tafin hannunta na hagu tana Isti'aza tare da rufe bakinta saboda hamman da tayi.Julaibib yashigo da sallama, yazauna a kujera a gajiye lik'is yacire riga yabar farar singlet. Sannu da zuwa Yaya D'ansarai.Ya aikin? Yafurzar da iska tabaki ta hanci"aiki ba dad'i kuma ba dama a bari.Wayyo! neman halali da wuya,kowa ga ganshi a inuwa tabbasss ya sha rana sannu Zaujiii...nah,tad'an shafa kwantacciyar gargasarshi"ubangiji yak'aro lafiya ta gangar jiki da natsuwar zuciya,tad'ora ha6arta a kafad'arshi,tagewaye hannayenta tana mishi tausa. Yasauke numfashi yana jin gajiyar data lullu6eshi tana tafiya a hankali a hankali"Shukran jazilan Zaujatiii...Yad'an bud'e idanun shi daya rufe yakalleta "kin cinye agadan?A ah ai yanzu kad'an nake ci dan yafara fita kaina.Yayi murmushi.

Kafin tagama abinci takawo mishi bawan ALLAH har yafara bacci sai da ta tashe shi tana mishi dariya"yau baza ayi nazarin karatu anjima ba kenan?Yayi mik'a yana salati"gaskiya yau ba nazarin karatun dazanyi,kin san tun a office nake gyangyad'i saboda baccin da kika hanani daren jiya.Takama ha6a tana yar dariya"Kai Yaya D'ansarai nice na hanaka baccin?Yagyad'a kai.Tayi yar dariya"au to shikenan ta kwana gidan sauk'i daga yau bazan kuma hanaka bacci ba shikenan ko?Yamata wannan kallan da bata so yayi bismillah yafara cin abincin data zuba mishi.Takauda kai tana k'unk'uni dan wallahi haushi kallan yake bata.

Ramadan wata me albarka,wata me alfarma.Tana kwance ta kifa fuskarta a cikin matashin,ya san ba bacci take yiba tsabar jin jikine kawai,tunda ko da da take ita kad'ai azumi wahala yake bata bare yanzu ga ciki,bataji shigowar shiba sai da yazauna a gefen gadon yadafa bayanta "Zaujatiii... Tamik'e zaune dakyar tana kallan shi bata da kuzari kona sisin kwabo.

yakalli cikinta yayi girma yanayinta ya canja gaba d'aya,tausayinta da k'aunarta suka mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarshi "Zaujatiii... Ki hak'ura da azumin nan mana,kinga wahala kike sha,barin had'o miki shayi kawai.Tawani marairaice "haba Yaya D'ansarai kalli agogo kagani k'arfe uku saura kwata na rana sai in karya azumi? Uh to menene ai kina da lalurane.A ah kayi hak'uri ai azumin ma ya kusa k'arewa tunda nayi ashirin to ai ko tara ko goman dasuka rage bazasu gagara ba Insha-ALLAH za k'arasa dani,nima ina kwad'ayin dacewa da daren"lailatul qadri".Yagyad'a kai"Toh ALLAH yasa mudace da wannan dare daya bambanta da darare dubu a daraja,ALLAH yabaki nak'uda kafiifan(me sauki) Tayi murmushi"amin Yaya Julaibib.

Yarik'o hannunta tamik'e suka fito waje suna d'an tattaki har zuwa bayan gidan in da sukayi yan shuke-shuken su kamar su alaiyahu,ganyan ogu, timatir,attarugu,zogale,d'ad'd'oya(scent leave)da sauran su, dakyar ta zauna a d'an k'aramin dakalin wajen tasa hannu tana tsinkar lemar kwad'i/naman k'asa(mushroom)ya tsuguna yana tayata tare da tambayar ta"yau kuma me za kiyi dashi?

Tun safe natashi da sha'awar shan romon shi(mushroom sauce) yad'an kalleta"ni fa yau a tsarin abincin mu ba shinkafa.Toh Yaya Julaibib,ni ma ba da wani abu zan had'a ba haka kawai zanyi romonshi in sha. Suka gama tsinka sannan suka wuce D'akin-girki yakar6a yawanke ya yayyanka mata, yad'uko kaskon suya yazuba magyad'a kad'an yad'ora a wuta sannan yakalleta"to na miki me wuyan zo kibashi tsoro. Tad'an kalleshi a marairaice nagode,to amma Yaya D'ansarai...sai kuma tayi shiru"uhun menene kuma?

Tanuna mishi abinda take so yayi.Yad'auki wuk'a da albasar yana mita"ni fa a duk aikin gida ba abinda yake bani haushi irin yankan albasa,tagyad'a amma kuma kafi kowa san albasa me yawa a girki,jiyama ai miyar albasar kasani nayi dayake ba kai kake yankawa bako? Eh mana...sukayi dariya yana fara yankawa idanun shi suka fara ruwa, yarintse su"Zaujiii...Karfa kayanke"eh ai kin san zan iya yankewa amma kika sani,da sauri yayi yagama yana fad'in"kai gaskiyar bahaushe da yace albasa batai halin ruwa ba, yawanke hannayen shi da omo,yanad'e hannu riga toh aikin dai aikine an ba kuturu tallan jakai"yad'auko abin markad'e(blender)ina karas d'in dana gyara d'azu?Ai na had'a maka lemun,yana cikin fridge.Yawarware hannun rigar"yauwa Zaujatiii...Kin kyauta nagode ALLAH yamiki albarka.

Yanzu barinje in yi alwala lokacin tafsir ya kusa,kuma yau d'in nan Insha-ALLAH nake tunanin zamu rufe sai ALLAH ya kaimu ramadan me zuwa ga masu tsawon rai.Toh Yaya Julaibib adawo lafiya, kuma dan ALLAH ana idar da sallar magriba ka dawo gida da wuri kasha ruwa,tazuba mishi dabinon ajwa a aljihu daya manta bai d'iba ba kaji Yaya D'ansarai?Yad'an dafa kafad'arta"Insha-ALLAH nagode Sudaida.Tabi bayan shi da kallo cikin yaba k'ok'arinshi da wata irin k'aunarshi da take dad'a narkewa a sararin cikin zuciyarta.

Safiyar sallah garin yayi lullumi a sanda hantsi yadubi ludayi ta yi k'ok'ari tagyara gidan da taimakon shi,ko ina yana k'amshin turaren d'aki, sassanyar iska tana kad'a fararen lubayen da ratsin ruwan hoda saboda rashin nauyin su.Tana sanye da voil-lace ruwan sararin samaniya(sky blue)doguwar riga dan d'aura zani wahala yake mata yanzu,d'an kunne,sark'a da warawaran hannayenta da zobe na zinare,suna ta d'aukar idanu saboda kyallinsu,ga jan lallanta me yarfin bak'i da tayi k'afafu da hannaye sun k'ara haskata,bata d'aura dankwalin kayan ba sai tayafa k'aramin mayafi ruwan sararin samaniya me shara-shara,gashin kanta yasha gyara daren jiya a wajen gyaran gashi da Julaibib yarakata.

Takoma D'akin-shak'atawa tazauna tana kallan shirye-shiryen wasannin sallah a tashoshi mabambanta aranta kuma tana mita"Yaya D'ansarai ya hanata tafiya gida taje tayi sallah a cikin Iyaye, yan'uwa da abokan arziki,sannan tun d'azu aka sakko daga masallacin Idi ya aiko a kar6a musu tuwon sallah shi da abokanshi kusan awa d'aya kenan,taja tsaki ai ko danko sukeci yaci ace zuwa yamzu sun gama ya shigo,a hankali tazame takwanta a doguwar kujera tacigaba da kallan amma ranta sam ba dad'i.

Taji ana sallama tare da k'wank'wasa k'ofa, taja malalacin tsaki a yadda taji dad'in kwanciyar nan data sani tabar k'ofar a bud'e koma waye tad'aga murya tace a shigo,tamik'e dakyar taje tabud'e, bakinta yak'i rufuwa saboda mamaki sai bin yaran takeyi da idanu,suma sunata tsallen murna sunzo gidan Inna Sudaida,za suci dad'i,yarik'o hannun wasu daga cikin yaran"kai kuzo kawai in maidaku wajen Iyayenku dama daga masallacin Idi natarkato miki su,ban tsaya tambayar kowa ba,yad'aure fuska ganin sunk'i motsawa"mitafi nace ko? Wasu suka mak'ale kafad'a, wasu har idanun su yaciko da kwallah.

Tarik'o hannushi"haba Yaya Aminu talek'o ta koma kenan,yagyad'a kai" eh mana tunda baza ki bamu hanya mushiga ba basai mu koma in da mukafi wayau ba?Oh dan ALLAH kayi hak'uri murna da mamakin ganinku ne yamantar dani abinda zan yi tun farko,tamatsa yaran sunata rige-rigen shiga,suka zazzauna suna tsallan murna wasu suna fad'in su sun dawo nan gidan Inna baza su wani koma Zonkwa ba.

Yaya Aminu naji dad'i wallahi,tazauna suna gaisawa tare yima juna barka da sallah ALLAH yamaimaita mana na bad'in bad'in bad'ad'a...tana tambayarshi mutan gida.Kowa lafiya k'alau Sudaida, mutuniyarki Nasmat ta bani sak'o yana mota,yakalli yaran sun baje suna cin abinci, hakanan zuciyata taraya min dama kaje wajen Sudaida, nace musu nan zanzo shine suka dinga rok'ona ALLAH annabi wai suma za suzo.Tayi yar dariya"ai kuwa nagode daka zo min dasu ALLAH yabar zumunci,dama kad'aici ya dameni.Yakalleta cikin tausayi dan cikinta ya girma"sai hak'uri kanwata,kafin mu shigo na ga Julaibib d'in mutane sun mishi yawa,na san haka kawai bazai kyaleki ke d'aya ba.

To Yaya Aminu kaci abincin mana. Yad'auki wayarshi yana duba sak'on karta kwana da aka turo mishi"ke ni dama kunu kika kawo min. Takalleshi wani iri "kai dan ALLAH wani irin kunu yau take sallah fa.Yamaida wayar aljihu"uhun ba a shan kunu ranar sallah ne kome? Yayi bismilah loma biyar yayi a tuwon sannan yad'auki cinyar kaza yad'an gutsira yamayar ya ajiye dan baya wani jin yunwa,ai kin san halina ni nama ba d'ad'ani da k'asa yayi ba, wannan sai su autan Inna kura kyaci da gashi,tad'an yamutsa fuska"to ai bashi kad'ai bane har da Yaya Musaddiq, yakama ha6a wuuu...au haka ne?Babbar magana ance da mak'asau bawa,barin kama bakina.Tayi yar dariya.

Julaibib yashigo aka cigaba da hirar dashi, ranar wunin farin ciki sukayi,sai bayan sallar la'asar Aminu ya kwashi yaran dayazo dasu cikin mota,Sudaida takawo musu cin-cin,nama da goron sallarsu,kowa ta bashi a hannunshi,sunata murna da rige-rigen fad'in" Inna Sudaida nagode,ALLAH amfana. Takalli Aminu"na rasa me zan baka rabin raina. Julaibib yadafa kafad'arta"juye mishi ragowar kunun safen nan yatafi yayi farau-farau dashi.Tagalla mishi harara,yad'an d'age gira yana mata wannan rikitaccen kallan na shi"eyehhh...ni kike harara?Kinga Sudaida Aminu yakirata,tabishi da kallo daina hararshi haka,yad'auko sak'on Nasmat data rufeshi da wrapping sheet me zanen zuciya da rafar kud'i yan naira ashirin guda d'aya"nawa goron sallar.Julaibib yasa hannu biyu yakar6a"toh Yaya Aminu mungode ALLAH yak'ara bud'i,ALLAH yabarka da Siddiqa tazama tauraruwarka har gaban abada.Yadda yayi furucin yasa sukayi dariya.

Sudaida tarufe musu motar itama tana godiya,Julaibib yasunkuyo"toh kagaishe mana da Hajiyarmu kace mata munanan zuwa mata yawon sallah ta ajiyemin dambun nama,tasa amin kilishi me tsomen aya,yanzu ma zan kirata in fad'a mata. Yad'aura belt yana dariya"toh kura duk kai kad'ai? Yaran sunata tsalle daga cikin motar suna d'aga hannu sunama su Julaibib adabo,a hankali yaja motar suka bi danjojin motar da kallo har tayi nisa tasha kwana ta6acema ganinsu.

K'arfe hud'u na yammacin asabar motar Julaibib ta tsaya a k'ofar gidan Hajiya.A D'akin-shak'atawa suka sameta tana waya,tagama tasauke wayar a kunnanta tana murmushi"lale marhabun,yau ina da manyan baki. Takalli Sudaida cikin tausayi dan ta kasa zama a kujera, zama tayi ak'asa tana matsa k'afafunta da suka fara kumbura alamar ciki ya tsufa wash...tafad'a tana yamutsa fuska"sannu Sudaida ALLAH yaraba lafiya.

Kai Julaibibi Sudaida tadawo kenan sai ta haihu ko?A ah jibi zamu koma ni bazan tafi in bartaba. Hajiya tagyad'a kai"madallah,to idan haihuwar tazo sai kuyi yaya?Hala ka ta6a kar6an haihuwa ne? Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"wannan karan dai zanyi,Hajiya bar wannan maganar kinji,ai haihuwar ma da saura,yad'an kalleta kuma ni gaskiyar magana"I can't do without Zaujatiii... besides me.

Bashakka Julaibibi zama da mad'aukin kanwa...ni dai na sanka me kawaici amma wannan matar taka me suffar takand'a ta fara koya maka rashin ta'ido ko?To kaji dakyau baza tabikaba,to me zata maka da wannan tsohon cikin?Sudaida tayi murmushi tana zancen zuci"lallaima Hajiya ni ce na koya ma Julaibib d'in rashin ta'ido?Yaya D'ansarai wallahi gwani na gwanaye ne bar ganinshi haka Ustazu-Ustazu baya san magana hummm... takyalkyale da dariya tuno abinda yagama fad'a mata daren jiya data keta wani sha mishi k'amshi dan ta karance tsabbb...da abinda yake so.

Tad'an turo baki gaba"Hajiya ai gwamma in zauna a suffar takand'a da dai in zama tashi da nishi...bakiji kirarin muba?Bena bakya tsufa sai dai kiyi girgiza ki sake sabon gashi,kuma waya jazamin wannnan k'aramin jikin idan ba ke ba?Takalli Julaibib"Yaya D'ansarai...Kasha kuruminka k'afata k'afarka ai tare ta gammu.

Yauwa Zaujatiii...tabashi hannu suka tafa, tad'an yafito shi zo kaji,yamatsa kusa da ita tasaita bakinta a kunnanshi tana rad'a mishi wata magana, suka kalli juna,yad'age gira yana nunata da yatsa cikin yar dariya"da gaske Zaujatiii...? Ta amsa kai tsaye"na rantse maka da girman ALLAH.Hajiya takama ha6a ba shakka"wato ana nuna miki ma'aiki kina rintse idanu,da wannan tsohon cikin kike wannan iya shegen k'auri da kare? Tawatsa hannu"to ai shikenan jiki magayi baki kuma mafad'i.Yamik'e barinje shago wajen su Baba"ke sai na dawo zamu tafi gidan Kawu ko? Toh adawo lafiya.

Yana fita Sudaida tamatsa kusa da Hajiya takalleta cikin natsuwa"Hajiya na rantse miki da girman ALLAH nima na fiso in zauna a nan sai bayan na haihu,toh kin san halin Yaya D'ansarai da banyi haka ba ni zai rufe da fad'a,kilama yace nina kira a waya na fad'a miki,saboda ni ma ina ta damunshi ya dawo dani gida,shi kuma yana cemin a ah acan zan haihu,dana fara nak'uda wai asibiti za mutafi, mutumin da a wasu lokutanma har na fara bacci bai shigoba.

Kin san halin miskilancinshi idan suka motsa, maganar duniyar nan za ki mishi,sai dai yamiki kunnan uwar shegu,yasunkwui da kai bazai yi magana ba ko da me za kiyi,yamaida mutum kamar wanda yaci kai(hauka)to Hajiya me zuwa fada ga banza bare kuma Sarki na kira?Hajiya tajijjiga kai"eh lallai kinyi hikima da siyasar rayuwa a nan, dama idan kasan mutum to sai kaci maganin zama dashi, barni dashi zai zo zamu sake tattaunawa.

Suna cin abincin dare kiranshi yashigo tad'aga da sallama,ya amsa muryarshi a dake"har yanzu kina gidan Hajiya ne?Eh Zaujiii... dama yanzu zan kiraka dan na jika shiru...yatari numfashinta"kin jini shiru,ke makauniya ce dabaza ki iya tafiyaba dole sai da d'an jagora ko?Tad'anyi murmushi wannan fad'an dawalakin goro a miya,ba mamaki taran dangi aka mishi akan dole yabarta anan,sai ta fad'a a tausashe duk shi d'in yace ta zauna idan yadawo za suje gidansu"Esbeer Yaya D'ansarai nahhh...ganinan zuwa.Hajiya takalleta"karki nuna mishi kin fahimci abinda yasa shi a damuwa,tarataya jakarta"toh Hajiyarmu mukwana lafiya. ALLAH yasa Sudaida.

Da sallama tashiga D'akin-shak'atawar, yakalleta a d'age yakauda kai.Bismillah,wash...ALLAH! tafad'a sanda ta zauna a k'asa dirshan tana maida numfashi kamar wacce gudun famfalak'i"Yaya D'ansarai na dawo. Yayi kamar ba dashi take magana ba,ganin haka tasama ma kanta lafiya ta hanyar kunna data tana turama A'isha sak'o,wucewar dak'ik'u kusan arba'in sannan yamik'e zaune daga kwanciyar da yayi yakira sunan ta.

Takashe data tana amsawa da na'am.Kishirya gobe da sassafe zamu koma. Gobe kuma?To saboda me?Hummm...ki bari kawai wai har da Baba a fad'a min ya kamata a barki,ni kuma bazan iya ba, Sudaida ko baza kimin kome ba to ni dai ina san zamanki kusa dani,yabud'e idanun shi daya fara rufewa gaba d'aya a kanta"Zaujatiii... ina k'aunarki ba tare da wani dalili ba,zan cigaba da k'aunarki a kowani hali da yanayi na rayuwa kingane ko?Tajijjiha kai"na'am na gane Zaujiii...ALLAH yabarmu tare,mutu karaba takalmin kaza.

Ta sauke numfashi to amma Yaya Dansarai... wani hanzari ba gudu ba,Baba da duk wanda yace kabarni anan umarni suka ba ka ko shawara?Yad'ago yakalleta"shawarace ba umarni ba.Tawani marairaice"to in ko hakane bai kamata kawatsa musu k'asa a cikin idanu ba "Yaya D'ansarai tsakani da ALLAH ba wanda zai so ya haifi d'a a cikinshi bayan fad'i tashin da yayi a rayuwar d'an nan har yazama abinda yazama a doron duniya,sannan wani abun yata so,su bashi shawara a matsayinsu na masoyin shi da suka fi kowa k'aunar shi bayan ALLAH da manzon ALLAH amma yawatsa musu k'asa a cikin idanu ta hanyar kin kar6an shawarar da suka ba shi ace ransu bazai sosu ba?Duk fad'in duniya duk wani me da'awar yana k'aunar mu toh daga bayane sadaka da karuwa,dan da Iyayen na mu basu maidamu mutane a sanda bamu da kome baza mu iya amfana ma kanmu kome ba to da bamu girman da duk wani me son mu ya so muba.

Tasake tausasa murya"Zaujiii...gyara kayan ka baya ta6a zama sauke mu raba,nima yanzu d'an mune a cikin cikina,to ai baza muji dad'i mu bashi shawara bayan mun maida shi mutum yak'i kar6a,bayan kuma shawarar bawai ta sa6ama shari'a bane"Yaya D'ansarai kayi hak'uri kabarni anan d'in,na tabbatar dan haihuwar farice,amma da baza su d'aga idanu su kalli rayuwarmu da abinda yake gaban muba, in dai bamu muka fad'a musu dan neman shawara ko kuma addu'a ba.Zaujiii...Aljannarka a k'ark'ashin Iyayanka take sai ka bisu ka kyautata musu zaka sameta fa.Tayi murmushi kasha kuruminka mijin Sudaida ni zan dinga zuwa maka hutun k'arshen mako(weekend)a 6oye,wallahi ba wanda zai sani sai Yaya Aminu dan na san ba zai k'i kawo ni ba.

Kalaman Sudaida gaskiyace wacce daga k'inta sai 6ata,zuciyarshi tayi wasai,d'aya daga cikin jin dad'in doron duniya samun mace tagari "Zaujatiii...Ke macen alheri ce,ALLAH yamiki albarka. Kiyi zamanki ba sai kin dinga zirga-zirga tsakanin Zonkwa da Gidan-Waya ba ni duk lokacin dana samu sarari zan zo ko a k'arshen mako ko a ranakun mako(weekdays)ALLAH yamiki albarka yabaki nak'uda kafiifan.

Yana had'a kaya a jakar da zaiyi tafiya da ita yana dad'a jaddada mata"Zaujatiii...kullum fa kisha ruwan zamzam d'in nan,kici dabino,ki yawaita addu'a ba dare ba rana,gobe Insha-ALLAH zan ai ko miki da hulba ki fara tafasashi kina shiga,da kinji alamun nak'uda ki d'ibeshi ki had'a da zuma ki cakud'a kidaure kishanyeshi kinji ko?Jikinta yayi sanyi sai take ji kamar kar yatafi,ko kuma su tafi tare tana lumshe idanunta mak'alallun kwallan da suka cika su,suka samu damar zubowa sharrr...yayi kamar bai gani ba,yagama shirya kome a jakar ya rufe yatafi yayi wanka yashirya cikin shigarshi ta dogaye fararan kaya kanshi da hular dara bak'a.

Yagama d'aure bak'in agogo a hannun damarshi,sannan yagewayeta yana magana cikin tausayi da k'auna"haba Zautajiii...kuka kuma! yafara share mata hawayen ai ke macen albarkace Sudaida,ban ta6a nadamar zama dake ba ko na sisin kwabo...haba Sudaidan D'ansarai...Ki k'arfafamin gwiwa kamar yadda ki kayi jiya mana,wannan hawayen na ki sai su sa autan Inna a uku fa...yacikata da kalaman k'auna da kambamawa... Itama ta gewaye shi tare da d'ora ha6arta a kafad'arshi

"Zaujiii... na yi shiru...ALLAH yamaka albarka. Yayi murmushi"amin.ALLAH yatsare min kai, yakiyaye ka da kiyayewarshi,tasa hannu tad'an shafa k'asumbarshi...wucewar wasu dak'ik'u sunata kallan juna, a hankali suka saki juna yad'auki jakar shi sannan yad'aga hannu yana mata adabo...Yajuya yatafi sai ta d'aga labulan taga tana cigaba da kallan shi yashiga mota yad'aura belt yayi azkar yasa mukulli yatashi motar...har yabar haraban gidan tana cigaba da kallan danjojin motar yayi nisa ya6ace ma ganinta sai

Please Login or Register in order to submit comment