Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take mishi"Sumayya ya akayi ne? Tayi yar dariya"wallahi Bros kayi kyau ba k'arya wannan shigar sunnan ta k'ayar dani fa. To nagode,yau ba Islamiyya ne?Akwai sai zuwa anjima.

Hafsa tafito daga D'akin-girki tana kallanshi "Yaya Miqdad baza ka tsaya kaci abincin bane?Yad'an sosa kunne"fita zanyi.Tad'an marairaice"ALLAH sarki Yaya Miqdad inata sauri ne fa,wallahi na kusa gamawa. Yakalli agogon dake d'aure a hannun shi na dama"Ina bazan tsaya ci ba gaskiya.Ta turo baki gaba gaskiya ni dai banji dad'iba.Sai kawai tajuya tana k'unk'uni. Yarik'o hannunta"baba tawaje nah,kiyi hak'uri kiran gaggawa aka min a wajan aiki,yadafa kafad'arta yad'an d'age gira cikin murmushi"Yaya Miqdad ne fa?Tad'an harareshi tana dad'a turo baki ni dai...yatari numfashin ta"kinga kwantar da hankalin ki"bayan sallar azahar zan aiko a kar6a sai inci acan shikenan ko?Tad'anyi tsallan murna"yauwa Yayanmu to adawo lafiya"tabashi hannu sukayi musafaha suna dariya.ALLAH yasa tawaje nah...suka d'aga hannu suna ma juna adabo.


Julaibib tunda yatafi sau d'aya yazo sai yanzu da suka samu hutun Semester, haka yadinga zaga gidajan yan'uwa yana gaishesu.Suna zaune shi da Musaddiq suna tattauna al'amuran daya shafesu Safiyya tayi sallama tashigo D'akin-shak'atawar sanye da dogon hijab suka gaisa cikin mutunta juna ta tashi tafita,bata sake shigowaba sai da tagama abincin rana tahad'a duk ahinda za su buk'ata a babban tire takai musu.Musaddiq yakar6eta da saurin shi"yauwa Safiyya,ALLAH dai yak'ara miki albarka da lafiya.Shida ita suka kalli juna suna murmushi,ta tsuguna da niyyar zuba musu yace"a ah wallahi amaryata ai kinyi me wuyar jeki kawai tuzuru zaiyi kome.

Julaibib yayi kamar bai gane shagu6en ba,yad'auki kofi yazuba lemun kashu da abarba,yayi hismillah yafara kur6a.Musaddiq yace kai ni bangane bane anyi yamma da kare ni baza ka zuba min bane?Ya ajiye kofin yana nuna kanshi da yatsa"ni kace zanyi kome ko tuzuru? Ni sunana Julaibib ban san wani tuzuru kake nufi ba, ka san dama ni ban saba da sai anyi service d'ina ba, yazuba abincin a faranti yafara ci.Musaddiq yagalla mishi harara"wa za ka raina ma hankali? malam kayi aure kaji dad'in rayuwar ka,dawani tuzuru ne bayan kai?Yayi kamar ba dashi yake magana ba.Musaddiq yad'auki cokali to ajiye abincin muci mana. Yajanye farantin da sauri"a ah yau bazan ci abinci dakai ba,tashi katafi wajan matarka taba ka abincin abaki ma wannan ba damuwata bace.Au haka za kace?Yad'an d'age gira yana mishi wannan rikitaccen kallan nashi"Eh haka nace da magana ne?A ah ba ni da tacewa...wai ankama 6arawo da kayan sa ta.

A sanda hantsi ya dubi ludayi na safiyar alhamis Sudaida da d'an d'okinta na san ganinshi ta tafi gidan Inna,amma irin amsa gaisuwar daya mata yasa jikinta yayi sanyi"wai an jefi kaza da gishiri,baiko d'ago kai ya kalleta daga tarin littafan daya barbaza a saman tebur ba,a dak'ile yake amsa gaisuwar da take mishi da lafiya...Tazuba mishi idanu na wucewar wasu dak'ik'u sannan ta d'ora envelop d'in hannunta a saman tebur d'in gabanshi.Yakalli envelop d'in a gajarce yacigaba da rubutun shi ba tare kuma daya d'ago kanshi ba yake tambayar ta"na meye? Haushinshi yakamata,ta galla mishi harara tajuya"nima ban sani ba.garammm tabugo k'ofar da k'arfi.Sai lokacin yad'ago yakalli k'ofar,yad'an motsa kafad'a yacigaba da abinda yakeyi har aka fara kiraye-kirayen sallar azahar bai gama ba, turesu kawai yayi gefe yayi alwala yatafi masallaci.

Bai samu damar bud'e envelop d'in ba sai daya zo kwanciyar bacci"D'an k'aramin frame ne me hoton ayatul Qursiyu,a kasanshi wani tsibiri ne me ban sha'awa ruwa yana gudu...sai d'an takadda anyi rubutu sad'ara hud'u.

...Julaibib...na san kome zan ba ka a banza zaga ganshi,amma wannan na tabbatar ma kaina koda ba ka so na,na san za ka alkinta shi ko???
I dore you my Enigma...
Kasham Kantiok Donatus.

Yakaranta yasake karantawa,yakai hancinshi yana shinshina frame d'in daya ke k'amshin irin turaran ta.Yayi lallausan murmushi dan yaji dad'i har ranshi yajijjiga kai"Tabbas kin bani abinda zan alkin ta Kasham...na kuma gode. Sai ya d'orashi agefen gado yakwanta yana azkar d'in bacci, yanata kallan frame d'in yana tuna had'uwarsu da Kasham tun ranar farko da kallan farko da sukama juna a haka har bacci yayi awan gaba dashi.

Azaure sukayi kaci6is taja baya da sauri jakar hannunta ta su6uce zata fad'i a k'asa,cikin zafi nama yacafe,yamik'a mata, takar6a tana gaishe shi. Idanunshi akanta"wa yabaki envelop d'in nan?Tamishi wani irin kallo fuska a d'an yamutse"Malama Kasham.Tun yaushe?Baku dad'e da tafiya Zaria ba.Yad'anyi murmushi cikin gyad'a kai"To nagode,Kawu yana ciki?Eh yana ciki.Yajuya zuwa cikin gidan tabishi da kallan mamaki D'ansarai kamar kuli-kuli yake da ba a gane gabanshi wallahi,Jiya fa shine yamata halin-ko-inkula amma yanzu har da wani murmushi taja dogon tsaki "Kai ALLAH yasauwake maka.

Sumayya ta zage dantse tana kwankwad'ar madarar ilimi,gaba d'aya ta canja ta zama wata ta musamman"Unique charisma"fatar jikinta ma ta canja saboda canjin cima,a gidan Alhaji Hafiz za a ci abincin safe me kyau me gina jiki,da ranama haka a mafi yawan lokuta ba sa kasafai suke yin girki da daddare ba,sai dai asha su gwanda,Inibi,tuffa,dabino a kora da madara idan kuma abincin za ayi to mara nauyi za a dafa.

Tana zaune a D'akin-shakatawa sanye cikin bak'ar doguwar riga kirar Saudiya,tayi rolling da mayafin tana nazarin"Dealing with Depression Islamically na Dr.Bilal Philips.Ta gaji lik'is a gangar jiki,amma zuciyar ta, tana k'ara k'arfafarta tad'aure ta k'arasa.Karo na uku kenan tana kallan d'an siririn bak'in agogon dake d'aure a hannunta ta k'osalokacin dawowar Hafsa yayi daga makaranta ta tambayeta wani abu.Tatsiyaya ruwa a k'aramin kofi daga babban tambulan takai bakinta da bismillah kad'an kad'an take kur6a tana jujjuya kofin kamar tana nazarin ruwan har ta shanye,ta ajiye kofin tana fad'in Alhamdulillah...

Ahankali ta d'ora kanta ajikin kujerar tare da lumshe idanunta tana addu'a "Yahaiyu Yaqaiyumu birahmatika astagis,aslihli fi sha'ani kulluh,wala takilni ila nafsika d'arfata ainin" wato "Ya Rayayye dauwamamme,da rahamarka nake niman taimako ka gyara min al'amurana gaba d'aya,ALLAH karka barni da kaina koda da k'iftawar idanu ne".

Miqdad daya shigo yatarar tana wannan addu'ar ya amsa da amin Sumayya. Tabud'e manyan idanunta masu maik'o da suka d'an canja kala saboda baccin da yake shirin kamasu.

Abrugo? (Ka dawo)

Yagyad'a kai dan shima yanajin yaran,Alhaji Hafiz ya koya musu kuma duk sun iya ko Maman Hasan tanaji.

Umburak (Na dawo)

Wannan addu'ar muhimmiyace daya kamata ace kowani musulmi yana yinta kullum ta ALLAH.Yad'auki littafi d'aya daga cikin tarin littafan data barbaza a saman tebur yana dubawa, yaciro biron daya soke a aljihun gaban rigarshi yana gyara mata wata kalma data rubuta ba dai-dai ba,yanuna mata kinga yadda ake rubutata, wancan wata ma'ana ta daban tabayar ba wacce aka tambaya ba.Tagyad'a kai "na gane,nagode Babban Yaya.

Yamik'e zai shige d'akinshi, danshi ba ma'abocin zaman D'akin-shak'atawar bane. Tad'an kalleshi"afwan Yaya Miqdad ga wata tambaya,yakoma yazauna"Uhun ina jinki"Tace yau Malam nasiha yamana da muke rik'e sunanil rawatib kar muyi sakaci dasu,to ni kuma gaskiya ban san meye su d'in ba,to kuma dana tambaye shi shima bai fad'a min wai ya bani jinga (Assignment)in tambayo gobe yana jiran amsa. Yayi murmushi gaskiya Sumayya kina burgeni nan gaba da alama babbar malama za ki zama. Tajijjiga kai"Insha-ALLAH nima sai na ba al'umar manzon ALLAH gudummawa daga d'an abinda Ubangijinmu yanufeni da sani na ilimi,ka san fatana Yaya Miqdad?Yagirgiza kai.Fatana ALLAH yabani miji me ilimi wanda zai dad'a d'orani akan tafarkin dai-dai, wanda zai sa in zama productive akaran kaina,how I wish Julaibib ya aure ni...

Yanunata da yatsa"ke dai da Julaibib d'in nan?Enigma man ko?Tayi yar dariya ai kuwa, yana da wuyar fahimta sai dai ni na fahimce shi, baya so adame shi,baya san hayaniya,baya shiga abinda ba da shi akeyi ba,amma ni har yanzu ina san shi"so gamon jini"yakad'a kai"ga shi kuma so ba samu ba,sai dai fatanmu har kullum ALLAH yaji6anci al'amuran mu.Amin big Bros.Sukayi murmushi.

Mukoma kan tambayarki abinda ake nufi da sunanil rawatib sune sallolin da akeyi na nafila kafin sallar farilla ko bayan sallar farilla kamar :-

Sallah raka'a hudu kafin sallar azahar da kuma rak'a biyu bayanta.

Sallah raka'a biyu bayan la'asar.

Sallah raka'a biyu bayan magriba.

Sallah raka'a biyu kafin sallar asubahi.

Babu wani musulmi dazaiyi wad'annan sallolin (Nafila) raka'a goma sha biyu(12) a kowace rana yana me d'a a da ganin girman ALLAH da k'ank'antar da kai a gareshi ba tare da ALLAH ya gina mishi gida a Darul-karamah (Aljannah) ba.

Sumayya ba ki da burin samun gida a aljannah?Tayi dariya so kai.Yagyad'a kai "To ki d'auki sahawarar da annabin mu,annabin rahama daya bamu, kidinga yin wad'annan sallolin.Tad'an kalleshi"Bros bayan sallolin farilla dasu shafa'i da wutri,raka'atal fajri da sallar walha ne zan dinga yin wad'annan sunanil rawatib d'in.Eh Sumayya. Tagyad'a kai"na gane Bros I'm very glad, Godwilling daga yau zan fara ina kuma neman taimakon ALLAH da d'orewar shi har k'arshen numfashi na kataya ni addu'a. Ya amsa da To Sumayya Ubangiji yayi jagora.

Suna kwance da Khadija tana duba Hadisin Annawawis Collection a cikin littafin Islamic Studies na B.A'isha Lemu(ALLAH Yajik'an ta.ALLAH yakyautata makwanciđź‘Ź)baturiyar Ingila (England) data musulunta ta auri babban alkali d'an jahar Niger (Minna) Sheikh Ahmad Lemu tayi karatun addini me yasa take bada gudummawa da tarin iliminta ga al'umar manzan ALLAH shekaru masu yawa.


Dawowar Alhaji Hafiz daga masallaci sallar la'asar yasa takalli Khadija data ke kwance a gefenta,ta gaji da wasanta tayi bacci,sai ta gyara mata kwanciya sannan ta tafi D'akin shak'atawa.

"Yauwa Sumayya.ya amsa barka da dawowan data mishi.Takalleshi cikin natsuwa "Uncle na ji wa'azi sosai daga bakunan malamai mabambanta game da girman zumunci da irin matsayinshi a addinin musulunci da hukuncin me yanke shi dame sadar dashi, Uncle ni da kai a jinsi yaran Bajju ne,amma a addini mu musulmai ne, kuma addininmu na musulunci bai hana mu sadar da zumunci ga yan'uwanmu wad'anda ba musulmai ba, to amma kai me yasa ba ka sadar da zumuncin ka da sauran yan'uwanka na jinsi Bajju?

Yakad'a kai"Sumayya ban k'i sadar da zumunci dasu ba har sai da naga suna niman kasheni... bari kiji abinda yafaru tun kafin a haifeki.

"Wata rana hanya tabiyo dani ta Zonkwa sai kawai na k'arasa K'auyan mu Madauci dan mu gaisa tunda na kwana biyu ban jeba, wallahi kamar jira ta sukeyi sai ganin Kantiok, Dinatu da wasu daga cikin yan'uwanmu matasa a bayansu d'auke da kokara da adduna, nafito daga cikin motar ina kallansu da mamaki "Kantiok ina za kuje da tsakar rana haka?...ban gama rufe baki ba naji an sakar min adda a tsakar ka,aiko nan take jini ya 6alle,wani ne daga cikin yan'uwan mune da wannan aikin, danaga da gaske k'ara saramin yake shirin yi aida gudu nakoma motata amma kafin inyi wani yunk'urin tayar da ita sun fara dukar motar,gilasanta sun farfashe,banyi aune ba naga sun fincikoni wasu suna ba da umarnin a samin taya in babbake kawai kowa ya huta,wallahi na ci na jaki da gasken-gaske.

Dak'yar Kantiok ya ceceni bayan ya samu nashi rabon,suka haushi da zagi ai ba haka suka shirya ba dan me zai 6ata musu shiri?Yana hawaye yake basu hak'uri,dak'yar suka hak'ura suna cigaba da zagina idan ban daina zuwa inda suke ba sai sun kasheni tunda sun riga sun yafeni,sun barma musulmai to inje in k'arata can dai gasu gada zomo ya ji kid'an farauta.

Kantiok shi yakaini asibiti kwanana uku nad'anji sauk'i nace mishi ni zan tafi yadinga bani hak'uri wai ba laifinshi bane,ba yadda zaiyi ne "Naka na kane ko ya cinyeka bazai tauna k'ashin ba,nace mishi ba kome,nabashi complementary card d'ina,dama na zo in fad'a musu na yi sabon gida,wanda muka tashi a ciki na ba wani malami halak-malak acigaba da koyar da karatun alqur'ani da sauran littafan addini ina fatar ya zamar min sadakatul-jariya bayan numfashina ya k'are a doran duniya.

Yakar6a yana tayani murna da kuma bani tabbacin duk lokacin daya samu dama zai kawo min ziyara bazai bari Dinatu tasan sabon gidan na ba,namishi ihsani kamar yadda nasaba mishi mukayi bankwana.Sai dai har yau d'in nan bai zoba,amma lokaci zuwa lokaci muna magana dashi tawaya daga baya kuma na daina jinshi ko na kira lambar ta shi ba ta shiga,amma yanzu Insha-ALLAH za muje gaba d'ayanmu.

"Uncle to ya akayi ka musulunta? Yayi yar dariya"shekarun dayawa Sumayya,ina secondary aka kawo mana yan bautar k'asa (corpers) anan na had'u da Corper Muhammad Aminu,shi yake koya mana lissafi (Mathematics) kin san ko wani malami yana san d'alibin daya ke gane darasin shi,to haka abin yakasance tsakani na da shi,har mukayi sabo na ban mamaki har aikena yakeyi wasu lokutan in siyo mishi kayayyakin buk'ata na yau da kullum idan baya jin zuwa cikin gari,sai washe gari in taho mishi dasu.

Har Staff-Quarter ina binshi idan yana da abun bani naci ko nasha yaba ni,idan babu muyi hira,wasu lokutan kuma yak'ara min haske akan lissafi.Yakan dafa kafad'ata yayi murmushi "Shedrak kwakwalwarka tana ja sosai akan lissafi,kaje ka karanci Accounting nan gaba kazama Accountant General Of The Federation. "Malam bani dame tsaya min inyi karatu iyayena sun mutu.Yayi murmushi dan Iyayenka sun mutu ba shine zai dakatar dakai daga san abinda kake san zama a rayuwa ba,kai namiji ne gwagwarmaya da rayuwar za kayi"babu maraya sai rago"zan taimake ka kayi karatu idan ka gama secondary ka kawo min takaddun ka zan samo maka addimision a jami'ar Ahmadu Bello(ABU)ga tallafin karatu da za a dinga ba ka,kuma ai sana'a zaka fara yi sai kaga kome yana tafiya.

Corper Muhammad Aminu me sauk'in kaine da bai d'auki rayuwar duniya kayan gabas me k'amshin turaren d'an goma ba, a hankali dabi'un shi suka fara burgeni banyi aune ba sai kawai najini rannan ina karanta"Innas safa wal marwata min sha'a'irillah.Ni ban san kome ye ba amma nasan a irin karatun dayake yawan sawa ne,dama su bismillahi na iya saboda indai zaici abinci ko abinsha sai yafad'a dan wasu lokutan ma yana zubawa a faranti d'aya yace muci,tun ina jin nauyi da kunya har nasaba.

Gab da zasu tafi sun gama hidimar k'asa nasame shi a d'aki yana karatun Qur'an sai da yakai aya,sannan nazauna ina gaisheshi dan ranar bai shigo makaranta ba"Malam yau baka shigo ba.Yagyad'a kai "Bana jin dad'i,ban dad'e da dawowa daga asibiti ba"Yadai? Yatambaye ni. Nad'anyi murmushi"ni dai malam ina sha'awar addininka sai dai baza a barni a gida ba.Yamik'e zaune daga kwanciyar da yayi yana fad'in Shedrak kai namiji ne,ka kuma fara mallakar hankalin kanka dan haka kanada damar yin musulunci tunda shi kake so.Da wannan nasamu k'warin gwiwa.

Ranar da zasu yatafi nasha kuka shi ya rarrasheni"haba Accountant General Of The Federation wannan ba girman ka bane,share hawayenka maza basa kukan hawaye,wannan ai d'abi'ar yarane.Da haka mukayi bankwana. Direbansu yaja motar ni da sauran dalibai dawasu daga cikin Malamanmu muka d'aga hannu muna musu adabo🙋har motar tayi nisa ta 6acema ganinmu."We may or may not see each other again.

Gaba d'aya sai makarantar ta gundireni kamar akan k'aya nake,a dadddafe nak'arasa.Muna gamawa nafara zuwa kasuwa, dako nake yi dan bani da kud'in da zan yi sana'a, nasha wahala amma na tara kud'i masu yawan danake ganin intayi ruwa rijiya idan bata yiba Masai,sannan natara yan uwanmu nafad'a musu k'udiri na nasan zama musulmi.Sai sukayi tsalle suka dire ALLAH yakashe su ban isaba, bazan yiba meye yata6i kwakwalwata haka?Nima naja tunga nakafe sai nayi sallah.Da suka rasa yadda za za suyi dani sai suka dinga zagina suna fad'in sun yafeni acikin zuri'a da jinsinsu na Bajju,har abadan duniya basu ba ni,ban bi takan suba na d'auki jakata sai cikin gari.

Agidan Liman tsoho anan na zama cikakken musulmi na za6i sunan Hafiz nacigaba da harkokina da musulmai,ina kuma zuwa kasuwa ina yin dako dan incigaba da rufa ma kaina asiri duk da kome ana bani amma ban yadda na zama cima zaune ba.

Rannan kamar wasa ina gwada lambar Corper Muhammad daya bani sai kawai naji ta shiga dan ban ta6a samun shiba sai ranar.Yad'aga da sallama nima ina murmushin jin dad'i dan nasan ma'anar sallamar dakuma muhimman cinta a musulunci"Malam ina wuni. Yad'anyi Jimmm...nawuce war wasu dak'ik'u cikin tunanin a ina yasan wannan muryar? Zuwa can naji ya amsa tare da fad'in "I'm I talking with the Accountant General of the Federation?Na kyalkyale da dariya ina gyada kai dan sunan fa yana sa ina jin kaina a duniyar wata"Yes Malam you're...mukayi dariya.Bayan mun gaisa nake fad'a mishi na gwada layin shi sau shurin masak'i ba ta shiga.Yace matsalar network d'in k'auyen kune,kuma ai laifin kane kadaure kawai Accountant kasamar muku na'urar sadarwa me k'arfin zango...nayi dariya kawai dan na san zolayata yake yi.

Nafad'a mishi kome.Yaji dad'i sosai yadinga ambaton ALLAH cikin shauk'in murna,tundaga ranar sai muke yawan yin waya danma wasu lokutan ni ina samun tangard'an sadarwa sai dai shi yakirani,muna haka ALLAH yama Liman tsoho rasuwa.Iyalinshi basu kore niba amma sai naji gidan ba dad'i, rannan muna waya sai na fad'a mishi damuwa ta yace ba kome inzo Kaduna insa meshi,aiko washegari dasassafe nayi sallama da mutan gidan Liman tsoho nad'auki hanyar KD.

Malam Muhammad yana aiki da ma'aikatar Ilimi ta jahar Kaduna(Ministry of Education)Ina zuwa yad'orani akan kasuwanci dan ya tambayeni zan tafi jami'a karatun ne? Nace mishi a ah nafi san kasuwanci d'an tunda nafara dako a Zonkwa naji dad'in kudi,yasani a makarantar addini,da daddare ma ba barni na zauna ba,ina makarantar Islamiyya ta maza,ina karatu ina sana'a, k'ank'anin lokaci kuma ALLAH yasama kasuwan cin nawa albarka,wallahi duk abinda nata6a sai yazama bud'i daga Indallahi.

Shekaru na biyu a Kaduna muka had'u da wata Atika muna soyayya har an kai kud'in aure da sadaki amma Iyayanta suka dawo da shi wai su baza su ba tubabbe auran yar su da a ka haifeta musulma iyaye da kakannin kakanniba,Ina ai wannan ganganci ne zagin uba ranar sallah.

Ran Malam Muhammad in yayi dubu ya 6aci yadinga fad'a wannan ma ai jahilcine to ko musuluncima ai da tubabbun yafara yacigaba da bunk'asa har zagaye ko ina lungu da sak'o nafad'in duniya gaba d'ayanta.

A ranar bayan munyi sallar la'asar a masallacin unguwarmu yatsaida mutane dan su shaida.Yad'aura min aure da yarshi mace guda d'aya da ALLAH yabashi daga cikin Ya'ya maza guda bakwai Ummulkhair me kimanin shekara goma sha uku dan lokacin ajinta hud'u a secondary.Yakalli Sumayya yana murmushi kin san abinda yace min? Tagirgiza kai.Bayan an kaita gidana yadafa kafad'ata "Hafiz ga Ummulkhairi nan kaji tsoron ALLAH karik'e ta da amana,Idan tayi ba dai-dai ba ka nuna mata kuskurenta nan take,ka kuma muna mata yadda za tayi dai-dai,shi icce tun yana d'anye ake tank'warashi...Kome daza ka d'orata akai to a yau d'innan za ka fara k'ok'arin gina matashi a cikin zuciyarta,ko ba ta so to kai kajajirce karka karaya Insha-ALLAH sai kayi nasara.Ubangiji ya albarkaci auranku...abinda yafad'a min kenan yajuya yayi tafiyarshi. Sumayya tajijjiga kai"Malam Muhammad Aminu yacika jarumin maza Ubangijinmu kasa ka mishi da mafificin sakamakon ka.Amin,Amin Sumayya.

Shigowar Maman Hasan yasa yanuna ta da yatsa"kin gan ta nan Sumayya har yanzu muna zaman lafiya.Tazauna a kujera tana kallansu"Eh gani nan,to me namaka kake ta nunani da yatsa?Tayi furucin da wani salo irin na shagwa6a.Sumayya tayi murmushi ganin wani irin kallon k'auna me cike da shauk'i datake mishi.Tsam tamik'e za ta shige d'aki "Sumayya dawo kiyi zamanki mana...dasauri tak'arasa shigewa ta rufo k'ofar tana girgiza kai "wanan kallan da abinda zai biyo bayan shi ba dani ba gaskiya"ga d'a da fatalwa.


Bayan shekara d'aya Sumayya ta gama karatunta,har tasamu gurbin karatu a jami'ar Kaduna (KASU) tad'ora degree a Islamic Studies ta kuma k'ara zage dantse tana kwankwad'ar madarar ilimin addinin musulunci, dama can a goge take ga Ilminta na Catering &Hotel Managements,gashi kuma yanzu wani fannin na daban take karanta,yanzu larabci kamar dama can dashi ta taso sai dai me zurfi daya wane ba ta ganewa har sai ta duba k'amus d'in larabci...


Sai dai weak point d'inta Julaibib musamman da sukaje taran Muslim Student Society Of Nigeria(MSSN)a jahar Katsina ta ganshi ganin idanun ta yayi kyau,yadad'a zama d'an gayu,shigarshi kamar ko yaushe ta fararan kaya.Shine shugaban kungiyarsu ta ABU,har tagaban shi tawuce suna tsaye shi da Maimun amma ba ta ga Musaddiq ba,wallahi daurewa kawai tayi ba ta musu magana ba amma ta dad'e a tsaye a gefensu tana k'are mishi kallo tana wata kissima a zuciya,har had'a idanu sunyi amma bai gane taba saboda tasa nik'abi ta kuma rufe k'wayar idanunta da gilas.Tunda taganshi d'aliban da suke k'ark'ashin kulawarta suka ka sa gane kan Amirarsu Sumayya...Da akace tazo zasu yi magana da yan Jami'ar Ahmadu Bello kasancewar su yan Jaha d'aya ne,kwanciya tayi wai bata jin dad'i,dan wallahi idan taga Julaibib har kuma sukayi magana to tsohon mikin k'auna ne zai 6alle gwamma daga nesa-nesa kallan kura...

Yafito yana sa links d'in hannun riga Maman Hasan tanuna mishi Sumayya.Sai yazauna yana kallanta"Tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i,abu d'aya yahana shi zuwa yasamu Julaibib suyi magana akan Sumayya shine yace baya son ta,to ko dabara kad'ai bazata d'aure kaya ba dole sai da igiya.Yakira ta da kakkausar murya

Please Login or Register in order to submit comment