Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunanin me kikeyi?Tun d'azu kin tasa kofi a gaba kin kasa san shayin.Yatsareta da idanu cikin d'aurewar fuska,ganin haka yasa ta sunkwui da kanta tayi shiru.

Kina sane da maganar danace za muyi?Eh Uncle.Yanunata da yatsa"Ina sane da abinda ke faruwa, banyi niyyar magana ba,to sai dai naga abin yana k'ok'arin shige makad'i da rawa,mutane uku suna zuwa da niyyar auranki amma kina korarsu,wannan kuma ba dai-dai bane tunda ba haka zaki dauwama ba dole za kiyi aure,dan haka akwai abokin kasuwanci na dayace yana sanki to nayi na'am da shi dan mutumin kirki ne,kuma ban 6oye mishi kome game da keba, shima ya amince yana sanki a haka.To jiya yasame ni dan niman izini yana so zai zo ku gaisa.

Sumayya karki 6oye min kome idan ya zo baku dai-dai ba,dan ba auran dole zan miki ba kin gane ko? Me zatace?Tagyad'a kai"Uncle zan zama me biyayya zan kar6i duk hukuncin daka zartai,dan haka ko wanene shi na yadda zan aureshi dan na san baza kamin za6en tumun dare ba.Yayi murmushi kin amince kenan?Tajijjjiga kai"eh Uncle na amince.To ALLAH yamiki albarka,yasa ki gama da duniya lafiya,ki kuma yi hak'uri da kome akan Julaibib, Sumayya wani hanin ga ALLAH baiwa ne.To Uncle nagode. Yamik'e shikenan ki daure kisha shayin.Takai kofin tsakanin la66anta kamar tana sha,suna fita shi da Maman Hasan da take mishi rakiya tadire kofin a k'asa tawuce d'akin baccin su takwanta tare da lumshe idanunta, kwallan da suka cika idanun suka samu damar zubowa sharrr...ranta ba dad'i sai ta fara karanta"ALLAHU-ALLAHU Rabbi laa'ushrika bihi shai'an.Tana ta maimaitawa har bacci yayi a won gaba da ita,sai da lokacin makarantar yakusa Maman Hasan tashiga ta tasheta.

...Aiki ke koran bak'o d'an gida ya dad'e da sabawa.
...Nagaji sai rago😊



10 Jumaada Awwal 1441
5 January 2020

We Ibrahim's Daughters 👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.




DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFI💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)




Shafi nagoma sha biyu.



Tana yankema Khadija faratan ta Hafsa tashigo da sallama,tazauna a hannun kujerar tana kallansu cikin murmushi sun sha wanka da kwalliya kayan su iri d'aya,doguwar riga k'irar Bahrain ruwan makuba, k'amshin turen ta ya mamaye d'akin.

Tad'an kalli Hafsa"bakin ki da magana. Tayi yar dariya"Yaya Sumayya ba wata magana,amma fa kina da bak'o a waje.Tayi luuu da idanun ta kamar zata rufesu,sai kuma tabud'e su gaba d'aya a fuskar Hafsa "bak'o?Ta tambayi Hafsa itama."Eh bak'o ne a wajan ki amma wasu lokutan nakan ganshi tare da Baba.Tad'aga idanu takalli agogon da ke manne a jikin bangon d'akin k'arfe uku saura minti goma na yammacin. Tagyad'a kai "fad'a mishi ina zuwa.Ta amsa da to.Sumayya tabita da kallo da tunanin irin mutumin da idanun ta za su gane mata wani daban,ba D'ansarai ba.Tayi wani d'an huci cikin kad'a kai,sai da tagama yanke mata faratan duka sannan ta d'auki farin dogon hijab d'inta a saman kujera tasa.

Miqdad yana zaune a D'akin-shak'atawar yana cin abincin rana yad'an kalleta ganin ta nemi waje ta zauna"Sumayya ba jiranki ake yiba?Tamishi nuni da Maman Hasan data basu baya tana kallan taga,waya takeyi.Ya watsa hannu"kije kawai ai ta san da zuwan shi ita ta aiki Tawaje nah(Hafsa)tafad'a miki,kema ai kin san gama wayar Maman Hasan ba yanzu ba,idan suka fara hira da tsoho me ran k'arfe Malam Muhammad Aminu sai kin sike ko kuma kud'in wayar ya kare an katse sadarwar tasu.Tarik'o hannun Khadija Miqdad ya girgiza kai "saketa kiyi tafiyar ki,ke Khadija zo nan ya yafito ta da hannu.Bata so ba sai dai ba yadda za tayi ne,yanuna mata kujera zauna anan kijira ta,ba dad'ewa za tayi ba kinji ko? Tagyad'a kai idanun ta sun cika da kwallah,yayi kamar bai gani ba yacigaba da cin abincin shi.

Yana zaune a dakalin dake harabar gida yana duba wani d'an k'aramin littafi Dammm...taji ruguzowar wani abu me k'arfin gaske a k'ahon zuciyar ta, ta dafe kirji cikin Istirja'i dak'yar tak'arasa wajan da sallama.Yamayar da littafin aljihun gaban rigar shi yana amsa sallar. Yana d'ago kai zai kalleta caraf idanun su ya had'u,shi dama ya san ta,dan d'ai-d'ai kun ranane baya ganin ta lokacin da take zuwa Sanawiyya, itace dai yau tafara ganinshi.

Takauda kai ba wani babba bane dan ita tayi zatan sa'an Uncle za ta gani tunda yace abokin kasuwanci shine,dogo ne kuma shima yana da nashi kyau da fasalin, yana sanye da shadda me maik'o ruwan siminti, hularshi k'ube ruwan siminti da ratsin bak'i, sai bak'in takalmi sawu waje.Yakatse shirun"ranki yadad'e barka da fitowa.Sai lokacin ta gaishe shi,yamik'e tsaye yana nuna mata wajan Bismillah ga waje ki zauna "tagirgiza kai "bak'on ka annabin ka"kai yafi cancanta daka zauna. Nagode amma ki barni a tsayen,ni namiji ne zan jure tsayuwar koda awanni biyu ne.Bata ce kome ba tazauna "Yad'anyi gyaran murya "Malama Sumayya kin san abinda yake tafe dani ko?Fuska a d'an yamutse ta amsa"Uhhh" ba tare data bud'e bakin taba.Yabita da kallan nazari dama Alhaji Hafiz ya sanar dashi kome shi yasa take amsa mishi a d'ad'd'age kenan,sai yayi murmushi cikin kad'a kai.Sai fa ya yi hak'uri dan ya san jin kan mata sarai bare kuma ga matsalar k'auna.Wayyo!Sumayya kema sai kinyi hak'uri,ni da shi ba d'aya bane koda kuwa uwar mu d'aya uban mu d'aya ne.

"Sumayya kin san wani abu kuwa? Yadda yayi furucin kamar irin sun dad'e d'in nan ya zo da saurin shi yana so yabata labrin wani abu da d'umi-d'umin shi.Sai tayi saurin d'ago kai tad'an kalleshi amma bata ce kome ba.Idan mukayi aure,ALLAH yabamu haihuwa d'anmu na farko indai namiji ne to ni d'in nan yanuna kanshi da dan yatsa, na miki alk'awari ki rubuta ki ajiye,da bakinki me albarka zaki mishi hud'uba da sunan Julaibib... dan ki tabbatar ni masoyinkine na gaskiya me san abinda kike so.Cikin mamaki da dariyar data kasa dannewa na jin dad'i ta kalleshi kai tsaye ta d'an bud'e idanunta"to ya akayi kasan sunan shi? Yanunata da yatsa"an ta6o inda yake miki k'aik'ayi ko?

Shi Salim wani irin mutum ne da duk abinda yake so yana yin k'ok'ari wajan sanin wasu muhimman abubuwa game dashi,ta yadda bazai sha wahala wajan mu'amala dashi ba.Ya gane soyayyar da take mishi wata jarabtace daga Ubangiji,tunda ya fad'a mata bazai aure taba,kuma ta yi hak'uri ta fauwalama ALLAH duk da yana ranta,to yanzu ga shi,shi ya zo zai maye gurbin shi da gyara harda alakoro Insha-ALLAH sai tayi alfahari dashi a matsayin mijin sunnah.

Kayi alk'awarin sama d'anka sunan shi?Yajijjiga kai"Eh wallahil-azim na yi alk'awari. Tamishi wani lallausan murmushi sannan ta kauda kai daga kallan juna da sukayi nawasu dak'ik'u.Daga nan hira ta6alle...

Zuhair ne yakatse musu hirar ta hanyar kawo ma Salim ruwan alwala a buta dan mukhtarin la'asar yayi.Tanata kallanshi yana alwalar cikin nutsuwa kuma cikakkiya har yagama yamaida hular shi kanshi sannan yamik'a mata butar,sukayi sallama dan an fara kiraye-kirayen sallah daga mabambantan masallatai,Miqdad ma yafito shi da Zuhair sun tafi masallaci dan sauke farali.Tabi bayanshi da kallo har yafita daga harabar gidan "Yanada saurin shiga rai.

Fuska a sake tashiga gida. Maman Hasan tace"Yaya dai Sumayya?Sai ta zauna a kujera tana yar dariya wallahi haka kawai take jin nishad'i,rabon data tsinci kanta a irin wannan yanayin tun ranar da D'an Sarai yamata nasiha data daina k'arama sama hazo(shan taba) Maman Hasan ta tayata da murmushi"a Alhamdulilla labarin zuciya a tambayi fuska.

Da safe tana shan shayin na'ana'a, kalla,kanumfari,da ya'yan algarib sai tiriri yake yi da k'amshi me dad'in dake k'ara mishi armashin da ko bakayi niyyar sha ba idan aka baka sai ka sha.Hafsa tashigo da waya d'akin baccin su dan yau bata fita D'akin-shak'atawa ba,anan ta zauna tana karyawa tana nazarce-nazarcenta.

Tamik'a mata wayar"ga shi ana magana"takar6a takai kunnan ta da sallama,ya amsa sallamar yana tambayar ta ya gida ya karatu?A takaice ta amsa"Lafiya...Alhamdulillah. Sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u"wake magana?Takatse shirun.

"Salim ne.

Salim... Salim...

Tafad'a ta maimaita cikin tunanin ga no wa ye haka?Sai yatari numfashin ta,a d'an marairaice"Innalillahi...Ina zan sa kaina...? Mummuna ya ga mata.Kar dai ace baki gane Salim d'in ba?Haba Sumayya to Salim d'in kine fa. Ta d'an bud'e idanu"Oh...Ya Rahman afwan Salim ka san bani da lambar ka.Yayi yar dariya"na sani nima jiya ne na kar6i ta ki lambar a wajan Alhaji,yana nufin Alhaji Hafiz.Kin san ranar dana zo k'aunar ki ta mamaye k'wak'walwa ta har natafi ban baki ba,nima ban kar6i ta kiba.Suka gaisa a mutunce"Sumayya da yammacin yau nake san zuwa wajen ki shin kina da lokacina?

Tad'anyi murmushi"haba Salim girman ka ya wuce haka,ai ko ba lokacin ka to dole a k'irk'iroshi bare ma a kwai,amma I'm really sorry to say...ka san yanayin karatu,yau k'arfe goma na safiyar nan zan tafi makaranta kuma gaskiya sai biyar da rabi za mu gama lectures sai dai gobe.Yagyada kai"ba damuwa da yau da goben duk d'aya ne.Kad'an suka ta6a hira sukayi sallama.

Sumayya da Salim k'ank'anin lokaci suka aminta da juna.Sumayya har ranta take jin ta samu abokin rayuwa,saboda Salim mutum ne me sauk'in kai,bai cika d'aukar al'amura da zafi ba.Dariya takeyi saboda kalaman shi,yabita da kallo cikin zancan zuci,wallahi kome na ta akwai tsabta,hak'oranta farare tas kamar ba dasu take tauna duk abinda yake shiga cikin cikin taba.

"Sumayya dawani man goge baki kike amfani ne?Takatse dariyar"man goge baki kuma?Yajijjiga kai eh dan na ga hak'oranki sun bambanta dana mutane da yawa cikinsu kuwa har da ni d'in nan yanuna kanshi,kamar bakya 6a tasu da abinci sai d'aukar idanu suke yi.

Kana so kasan sirrin?Sosai kuwa.To ka zama me yawan aswaki ba sai lokacin alwala kad'ai ba, kuma musamman kasa mu aswakin al'araq,wannan shine sirrin ga shi kuma sunnane.Kuma ka san ko masana a harkar bincike na yanzu da suke ganin sune tushen ilimin kome,to sunyi bincike kuma sun ga no sun kuma tabbatar yin aswaki goge hak'ora da chewing-stick magogi,ba brush ba yana k'ara k'arfin dasashi. ALLAU-AKBAR tsarki ya tabbata ga ALLAH. Manzan ALLAH sai da yace ba dan kar ya takura ma al'umma ba da ya farlanta mana yin aswaki. Salim ya jijjiga kai gaskiya kin tunatar dani abinda na manta,nagode miki Sumayya lallai tunatarwa tana amfanar da mumini.

Sumayya ki bani dama in tura Iyayena,ai mun d'an fahimci juna,yanzu mun san wasu daga cikin halayan junan mu ko? Duk da dai ba a sanin maci tuwo dole sai miya ta k'are. Takalleshi cikin natsuwa"Salim a da zuciya ta, tana rayamin inyi musulunci saboda Julaibib ne, kuma koda na kar6i musulunci na kar6a ne saboda shi,amma cikin k'udirar Ubangiji sai zuciya ta,tacanja daga wancan tunanani da niyar.A yanzu na yadda saboda zatin ALLAH nake musulunci,da taimakon su Uncle ta fuskar nasiha da zuwa Islamiyya da sauraran wa'azi daga bakunan manyan malamai mabambanta duk su suka cusa min yin abu saboda ALLAH,na san na rasa D'an Sarai amma zuciya ta bata aminta da barin musulunci ba,dan na gamsu addinin musulunci shine addinin gaskiya,ina zaune kwatsam sai Uncle yazo min da maganar ka,a lokacin na amsa mishi ne saboda kawai tsakani na da Uncle ba musu har abadan duniya,wallahi kome rashin jin dad'in abu in dai yabani umarni inyi ko in bari zan yi,dan na san soyayya ce a tsakanin mu,har fa zuciyata ta fara min sak'a da mugun zare amma ban biye mata ba,nayi ta addu'a ina neman rok'on Ubangijin mu yakawo min agaji kar in biye ma sharrin ta.

Amma a ranar da idanuna suka fara yin tozali da kai,kalamanka da kome naka sai suka burgeni, zuciya ta tayi wasai...A ranar na kar6e ka kamaye gurbin Julaibib,tad'an sake kallanshi cikin natsuwa Salim har yanzu ina jin wani abu game da D'ansarai amma ba soyayya ba,saboda sanadiyar shi nabar kowa da kome, harkar da nake yi nabin maza da tara abinda duniya daga garesu yabar zuciya ta,fatana kawai in mallake shi,to sai nagane a yadda yake me natsuwa da kamewa hak'ata bazata tadda ruwa ba, sai na bijiro mishi da maganar aure, na sadak'ar zanyi sallah ba dan kome ba sai dan kawai na k'wallafa rai shi d'in kawai nake san mallaka,manyan idanunta masu maik'o suka cika da kwalla.Ubangijin mu alhakimu ne,sai gashi ya canja min da wani daban kuma zuciya ta ta aminta da shi,dan haka Salim kai nake so soyayyar da ba ka da abokin tarayya.Julaibib dai yana da lada a wajan ALlAH saboda halayan shi masu kyau da tsabta wanda addinin musuluncine yazo dasu da kuma karatun addinin da yayi shine ya siffantu da siffofin,nima sai yanzu nagane wasu halayanshi da, a da nake mugun mamakin me yasa shi baya kaza?Me yasa yake kaza? Tad'aga hannayen ta sama ALLAH kahad'ashi da macen albarka,kamilalliya me addini.ALLAH kasamu daga cikin wad'anda ta sanadiyyar mu wasu za su samu haske irin na addinin ka.Ubangiji ka kara mana lafiya ka kara inganta mana Imanin mu.Yanata kallanta cikin so da k'auna,sai yadad'a aminta da ita dan Alhaji Hafiz ya mishi bayanin kome dalla-dalla ba jibge.

Sumayya...

Bata amsa ba tad'ago a hankali suka kalli juna"Sumayya yau rana ce ta musamman a wajan mu ko?Tasunkwui da kai daga kallan da yake mata tana murmushi.

Sai da a ka tsaida ranar auran Salim da Sumayya,Miqdad da budurwar shi Zainab sannan Alhaji Hafiz yatashi Miqdad d'in musamman dan zuwa k'auyan su Madauci wajan d'an uwanshi,bai ta6a zuwa garin ba amma da tambaya sai gashi a k'ofar gidan.Yanata sallama yaji shiru ba a amsaba,zuwa can sai yatuna to su ina ruwansu da wata sallama?Sai yakai hannu yafara rank'washin k'ofar.Yana gyangyad'i kamar a sama yaji ana buga k'ofar yamik'e dasauri yana fad'in"kai wanene haka daba zai shigo ba,bayan k'ofar ba kulle ta akayi ba amma yatsaya awaje?Sukayi kallan kallo na wucewar wasu dak'ik'u sannan ya matsa mishi yashigo,suka zauna a fararan kujerun robar tsakar gidan har yanzu kallan juna sukeyi "daga ina haka d'an Samari?Kantiok ya tambaye shi.Miqdad yayi murmushi daga Kaduna nake.Ai yana jin haka sai yamik'e ya rungumeshi yana dariyar murna"haba no wonder naji a jikina kamar na san ka to sai dai a ina?

Kai yaran Shedrak ne ko?Ina Kasham? Ya baku zo tare ba?Su ma suna nan zuwa.Yasaki Miqdad yafita dasauri,lemun kwali Don Simon,ruwa da kofi yakawo mishi gashi nan kasha barin kar6o maka abinci... ya tareshi da saurin"a ah kabar shi kawai.Yaja yatsaya yana kallanshi"Kazo gidana amma baza ka ci abincin mu ba saboda me?Yad'an shafa fuskar shi"Kayi hak'uri Kawu ina azumi ne amma da ba abinda zai hana ni ci.Yadawo yazauna to kai saboda ALLAH za kayi tafiya ba sai kabar azumin ba?Ya amsa mishi cikin girmamawa"Kawu azumin yana da muhimmancine.

Suna ta hira kamar sun saba. Miqdad yabashi sak'on da aka aiko shi wasik'a ce Alhaji Hafiz d'in yake sanar dashi"Kasham tana wajan shi tana kuma sallah,yanzu kuma ta samu mijin aure,dan haka zai aurar da ita,amma bayan bikinza suzo Insha-ALLAH,sai takardan kud'i (cheque)an rubuta mak'udan kaud'ad'e an sa hannu sai zuwa gidan kud'in(Bank)a Kar6a "Hallelujah..yafad'a saboda mamakin adadin kud'in daya gani a rubuce,gaskiya shi har yagama aiki bai ta6a kar6an rabin-rabin wannan ba,yana ta dariyar murna,shi kuma Miqdad tasbihi yakeyi a zuciyar shi"ALLAH buwayi gagara misali hatta wushiryar shi irin ta mahaifin shine,sunyi kama sosai sai dai wannan fari ne, mahaifanshi kuma baki ne.

Kiran wayar ta tashigo yad'aga da sallama"Yaya Miqdad ya hanya ka sauka lafiya ko? Yagyad'a kai"na sauka lafiya Sumayya gani ga Kawu na ganshi ganin idanuna.Tayi yar dariya."to masha-ALLAH ba shi wayar.Yamik'a mishi.Yana jin muryarta yayi dariyar jin dad'i "Kasham sai kuma yajuya harshe zuwa yarensu na Bajju,sun dad'e suna hira sannan yafara gyad'a kai da alama wata magana me mahimmanci take fad'a mishi yake gyad'a kan cikin gamsuwa"amin Kasham nagode ALLAH yamiki albarka.Miqdad yakad'a kai"wato kowa dai ya san akwai ALLAH yadda da shine dai ba kowa yayi ba.

Yana shirin tafiya yace ni har zan tafi banga Maman Sumayya baWai Kasham ce ta koma Sumayya?Eh kawu"Yayi murmushi kawai, Maman Kasham ta tafi kasuwa gashi kuma sai yamma za ta dawo,to ka kwana mana.Yayi yar dariya"Kawu ina da ayyukan da zanyi da yawa amma zan zo na musammma idan nasamu sarari zan kwana in ga sauran yan uwan mu.To shikenan ALLAH yakaimu"yarakoshi har inda ya ajiye motar shi yana bashin tabbacin zaizo ayi d'aurin auran su dashi.To Kawu aiko za muji dad'i ba kad'an ba,yad'auko rafar kud'i yan naira ashirin guda d'aya yabashi,sai yagirgiza kai,haba My Son ni ban ba ka kome ba ai kuma bazan kar6e na kaba, kabarshi kawai nagode,ga cheque na kud'i me yawa da zan kar6a.Miqdad yakalleshi cikin natsuwa"Kawu ai wancan d'an uwan kane yabaka,wannan kuma d'an kane yabaka,tashi kyautar daban,tawa ma daban,sai dai ban sani ba d'an uwa ya fi d'ane a wajanka?Yasake mik'a mishi sai yakar6a yanata mishi godiya,sukayi sallama cikin farin ciki.Yad'aga hannu yana mishi adabo tare da addu'ar ALLAH yatsare ya kiyaye mishi hanya,har motar tasha kwana ta6ace ma ganin shi, sannan ya juya,yak'are ma gidan kallo lallai gyara yazo tunda kud'i sun samu.

Lokacin daya k'arasa cikin gari har an idar da sallar azahar dan haka yayi alwala yayi sallarshi raka'a biyu ta k'asaru yayi azkar d'inshi sannan yakoma mota yana bin shagunan bakin titin da kallo yana kuma tunano kalaman Sumayya "Idan kaje Rahama Store to ka tambayi shagon Julaibib za a kai ka,yana tambaya kuwa aka nuna shi shagon sai dai kash...Musaddiq ne a shagon, daya tambayi Julaibhib yace yana gida sai bayan sallar la'asar zai fito.Yamik'a mishi wata yar madaidaiciyar jaka ruwan k'asa"Idan ya fito abashi "Miqdad yasake mik'a mishi hannu sukayi musafaha yajuya ya fita daga shagon.

Shima ya so ganin wannan D'ansarai d'in da Sumayya take bala'in so,yayi murmushi ganin yadda tayi da yace bazai kar6i sak'on wani Julaibib ba dan shi ba d'an aiken ta bane, wallahi idanunta har sun cika da kwallah ta sunkwui da kai k'asa bata kuma magana ba,sai tabashi tausayi.Sumayya yakira sunan ta,tana d'ago kai sharrr...hawayan masu d'umi suka zubo a kyakkyawar fuskar ta,tasa hannu ta share su sannan ta amsa a raunane"na'am...Yad'an harareta ke fa raguwa ce daga wasa sai hawaye? Tagirgiza kai"ni ma ban so hakan ba, ban kuma san ya akayi suka zubo ba,ni da Julaibib ai ba wata alak'a kuma sai ta yan uwan takan musulunci,sak'on dazan ba ka wallahi tun a Makka nasiyo mishi,da kuma na san zan had'u dashi a taron MSSN d'in nan na Katsina dana tafi dashi na bashi...ni a yanzu ina san D'ansarai ne saboda shi mutumin kirki ne me addini,amma karka manta ina da jan gwarzo na,dubu jiran mutum d'aya tad'an d'age gira tana wani lallausan murmushi sannan tafurta sunan Salim.Yayi yar dariya "Sumayya kenan so gamon jini.yashige mota yazauna ya d'aura belt sannnan yatayar cikin ambatan sunan ALLAH yad'auki hanyar Kaduna garin gwamna.

Musaddiq yana lissafin wasu kud'ad'e bayan sallar la'asar Julaibib yashigo da sallama yazauna yana kallanshi har yagama yayi rubuce-rubucen shi a littafin da suke rubuta kome na kud'ad'en kasuwan cinsu yamayar cikin dirowa sannan ya ajiye mishi jakar a gaban shi "dazu aka kawo maka.Inji wa?Musaddiq ya dauki mukullin motar julaibib d'in zai fita sannan yabashi amsa "Wallahi ban san shiba bak'o ne"ni nafi. Yagyad'a kai " To Allah yatsare.

Yabud'e jakar dabinon ajwa yagani, ruwan zamzam da farin miski sai envelop da sunan shi yake jiki 6aro-6aro da manyan bak'ak'e

"JULAIBIB ABDULLAHI D'ANSARAI...

Yabud'e da tunanin wa ya aiko mishi da wannan sak'on?

Assalamu alaikum warahmatulla. Julaibib ina gaisheka gaisuwa irin ta addinin musulunci.Ya su Mama?Ya karatu?ALLAH yamaka jagora.Julaibib kasance wata yau raye a cikin musulunci ba wayau da dabara ta bace,a ah ganin damar Ubangijinmune"Alhamdulillahi bi ni'imatil Islam.Wallahi a duk inda naje babu rauni da tsoro zan bayyana identity d'ina saboda addini na yafi kowane addini tunda ALLAH mahaliccin muma yafad'i hakan a Alqur'ani cewa"Addinin musulunci shine addini ko awajan shi "Subhanallahi addinin mu kome anyi programming d'inshi an ba mu.

"Julaibib na san kai mutumin kirkine me k'ok'arin bin dokokin ALLAH gwargwadan iko, dafatar baza ka canja daga yadda na sanka ba. Dan ALLAH kar kabari shaid'an ya rud'eka, rayuwar jami'a ta canja ka.
Daga k'arshe nake mana barka da

Please Login or Register in order to submit comment