Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta takwanta dakyar.

Da safe suna karyawa yazuba mata idanu yana zancen zuci ganin ta tsame hannunta a abincin wai ta k'oshi kuma ba wani cin kirki tayiba "wannan cikin gaba d'aya ya canja mishi Sudaida,ga yawan laulayi,ga rashin samun ishashshen bacci saboda munanan mafarkai,ga wasu k'ananan k'uraje da suka fito mata a duka la66anta ba irin magungunan da bata shaba dan su warke amma abin yaci tura,tayi sanyi sosai.A hankali tajingina bayan ta da jikin kujera tana yamutsa fuska"wash ALLAH!... Zaujiii...bakaji bayana ba kamar zai 6alle.Yafara mata tausa "sannu Sudaida. Tad'an kalleshi kawai.

Aminu yashigo da sallama shima yakalleta cikin tausayi"Sudaida ko asibiti zamu tafi ne? Tad'an yi luuu...da idanunta kamar zata rufe sai kuma takalleshi"Yaya Aminu sai gobe za muje.To ALLAH yaraba lafiya,yamik'a ma Julaibib hannu sukayi musafaha sannan yazauna suka gaisa da Sudaida. Suna hirarsu da Julaibib amma suna sakota,wani abun tayi magana wani kuma ta musu shiru. Aminu yamik'a mishi katin za6enshi(voters card)ni dai wannan karan bazan yi za6e ba,tunda ko ka za6a wanda kakeso to a k'arshen wanda su suke so shine sai lashe za6en da kuri'a mafi rinjaye,magud'i kiri da muzu haka ake yinshi.Bai wani dad'e ba yamusu sallama yatafi.Shima Julaibib yayi shirin tafiya Kaduna.

Yazauna a hannun kujerar da take kwance suna kallan juna na wucewar wasu dak'ik'u, tarik'e hannunshi"ban so tafiyar nan ba har ga ALLAH, ina ji ajikina kamar ba zamu sake had'uwa ba, idanunta suka kawo ruwa.Haba Zaujatiii...me yasa kike wannan furucin? Insha-ALLAH kafin magriba ai na dawo,sharrr...hawayen suka zubo mata,yafara goge mata"kiyi hak'uri Sudaida kome ya kusa zuwa k'arshe,kullum muna tare har sai kin gaji da ganina,yazame hannushi daga cikin nata,yamik'e yana gyara kwalar farar rigarshi"zo muje kawai kiyi zamanki a gidan Inna ko gidan Kawu idan na dawo sai in tsaya in d'auke ki.Uh uh ba kome idan naji bazan iya zaman ba to sai in tafi,tawani marairaice"

Tafiyar za kayi Yaya D'ansarai? Eh Sudaida ina 6ata lokaci gwamma inyi maza in tafi tunda ba kwana zanyi ba.Yasunkuya yabata sumba,tashafa k'asumbarshi sukama juna adabo.Har yakai k'ofa takirashi"Yaya D'ansarai...yatsaya cak sannu yajuyo "na'am Zaujatiii...suka sake zubama juna idanu na wucewar wasu dak'ik'u,tasauke gwauran numfashi a sanyaye tagyad'a kai "shikenan adawo lafiya.

A gidan Inna ma Bilkisu kuka tasa mishi ita bazai tafiba,ta had'a kai da bango tana sheshshek'a,dakyar shi da Inna suka dinga lalla6ata sannan tayi shiru ita da Walida suka rakoshi k'ofar gida tana k'ananan hawaye,yashiga mota ya zauna yana d'aura belt tarufo mishi motar"Baba ALLAH yatsare a dawo lafiya...Walida ta koma Gidan-Waya da gudu ita bata wani damu sosai ba.Tad'aga hannu tana mishi adabo,yaja motar yatafi,zai sha kwana ya leko tana tsaye, tad'aga murya"Baba Qad uhibbbuka... shima yamata adabo sannan yasha kwana yana murmushi furucinta"My dear Bilkisu kenan nima ina k'aunarki.

Tafiya yake yi amma yanaji kamar yajuya wajen Iyalinshi,ranshi ba dad'i har yashiga Kaduna garin gwamna,kiran Sudaida yashigo yad'aga da karsash"Zaujatiii...gani a garin gwamna.Nayi tunanin dama yanzu ka shiga.To ya jikin? Ya tambayeta cikin kulawa.Da sauk'i yanzu bana jin wani ciwo sai dai na yau da gobe kawai irin na mace me juna biyu,yanzu ma na idar da sallah walha,na kuma maka addu'a ALLAH yatsare min kai a duk in da za ka shiga,nima na rok'i ALLAH yarabani da cikin nan lafiya,yabani nak'uda sassauk'a,sannan nace barin kira D'ansarai mijin Sudaida inji muryarshi da kalamanshi su k'aramin nishad'i.

Oh ya rahmanu rahim...nagode ma Ubangiji da yabani ke a matsayin mata,ke macen albarkace,kece uwargidata har a aljanah,yasake yin k'asa da murya yana fad'a mata wasu kalamai wanda sirrin sune,tako kyalkyale da dariya"kai Ustazu...? Shima dariyar yake yi"na rantse miki da girman ALLAH Zaujatiii...Ko baka rantse ba na yadda da kai,ba abinda yake fitowa daga bakin ka game da soyayyarmu sai gaskiya"ALLAH yamaka albarka Abu Bilqisss...sai ka dawo d'in.Ya amsa da to sannan sukayi sallama ya zubama tashi wayar daya cire a kunne idanu,yayi lallausan murmushi yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"Ummu Bilqisss...ya fesar da iska ta baki ta hanci,sannan yasa wayar a aljihu.

Duk yadda yaso ya koma gida a ranar hakanshi bata tadda ruwa ba, sai dai sun gama kome da Manager,ashe daga can Lagos aka samu matsala amma kome ya dai-daita.Washe gari kuma wayewar gari litini yana shirin barin garin gwamma gari yarikice anata k'one-k'onen tayoyi da kisan rayuka na babu dalili,cikin damuwa Sudaida takirashi"ka riga ka taso ne?A ah.Sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u"to ALLAH ya sauwak'e wai meye musabbabin wannan fad'an?Sudaida ai kin san idan guguwar siyasa tafara kad'awa sai dai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"

Tagyad'a kai"hakane,muma nan d'in sai a hankali,wallahi mutane dayawa suna ta kwashe muhimman abubuwansu suna tafiya wai sai angama za6e kome ya dai-daita sannan zasu dawo,Abu me aikin Inna ma yanzu tazo tamin sallama zata tafi k'auyansu, hankalin jama'a da dama yak'i kwanciya tunda sukaji Kaduna ba lafiya,yanzu mu kuma sai yadda hali tayi kenan?Ta tambayeshi.Eh Sudaida amma nan in da nake ba a kome sai dai ansa matakan tsarone ba shiga ba fita, amma Manager yayi waya da babban d'an shi sojane yanzu zai zo yafitar dani tunda dama rigimar a cikin garine.Ta amsa a sanyaye"to ALLAH yasa.

Tana zaune cikin tsananin tsoro da damuwa na rashin mafita Aminu yashigo"ke Sudaida ki d'auki abinda zaki iya d'auka me mahimmanci yanzu zamu bar garin barinje in dawo...ta tari numfashinshi "har dasu Baba?Yakoma ya zauna tun safe nake magiya da rok'onsu su shirya mubar garin"gudun hijira wajibi ne idan kaga ba dama ka tsere...inji Garba Super,sunk'i toh ni dai gaskiyar magana tafiya zanyi dan wuya ko da magani ba dad'i, sunce basu hana duk me tafiya tafiya ba su dai sunanan,barinje ATM ki zama cikin shiri kafin in dawo. A sanyaye ta gyad'a kai sannan tasake kiran Julaibib sai dai tak'i shiga tabi D'akin-shak'atawar da kallo"to me zata d'auka?

To suma da suka ankare mutanan garin suna tafiya sai suka tare hanyoyi ba shiga ba fita dan suna da wani k'uduri a zukatansu amma a zahirance fad'i suke ba kome ba kome,dole Aminu ya hak'ura.Bayan sallar la'asar wata motar roka shak'e da abinci da mutane hanya tabiyo dasu ta garin suma da gani ba tambaya yan gudun hijirane ko da wani gari suka fito? ALLAH masani.

Direban a rikice yake sunata tsayar dashi amma yak'i tsaya"wanda maciji ya sare shi idan yaga tsumma sai gudu...Kawai yayi k'undunbala zai bi takansu sai suka tarwatse daga tsakiyar titin ya wuce cikin tashin hankali suka rufa mishi baya, saboda rikicewa sai sitiyarin yakwace mishi,take ta daki sabon masallacin mak'era da ake kan aikin ginawa, kowa yayi ta kanshi dan sun kusa cin musu,suka fantsama cikin gari gidajen mutane a kid'ime,su kuma ganin wannan ya dad'a tayar ma da mutane hankali musamman mata.Sudaida tashiga D'akin-girki ta sauke abincin data d'aura dan bata da kwanciyar hankalin da zata iya k'arasawa dama tun karin safe bata kuma sa kome a bakin taba.

Takira Julaibib amma yana ganin kiran yak'i d'agawa a k'arshema yasa wayar a yanayin shiru (silent)saboda d'azu ta sake kiranshi akan kar yadawo, yabari ko zuwa gobe ne dan suma garin ya fara rikicewa, sai yace mata bazai iya ba yau d'in zai dawo yana ma hanya ta kwantar da hankalinta ba kome fa,kuma ta dafata mishi shayi,tayi abinci me kyau yana azumi kome dare bazai yi bud'a baki da kome ba bayan dabino sai abincinta ko da bai shigo kafin magriba ba,bai jira amsawar taba yakatse kiran ya kira Musaddiq yana tambayar shi"wai meke faruwane Sudaida ta dameni kar in dawo?

Yayi tsaki"kai rabu da ita,da da wata babbar matsala ai dana fad'a maka,sun d'anyi zage-zagen sune d'azu ko dak'ik'u talatin ba suyiba suka koma k'auyukan su,in dai wannan hatsaniyar ne yau suka fara?Ka san halin mata basa raina abin tsoro,watama cinnaka za kaga tanama ihu da kururuwa a zo a kashe mata kar ya cijeta.Uh uh Musaddiq sharri dai ba kyau...to suwaye suke ta guduwa?Julaibib yasake tambayarshi.Masu guduwa dama yan ciranine amma ni dai a ganin idanuna banga wani zaunanna gari daya tafi ko mutum d'ayaba.To ALLAH yakyauta.Musaddiq ya amsa"Amin D'ansarai ka iso lafiya.Da wannan dalilin yasa yak'i sake d'aga wayarta.

Sai da yashigo cikin gari sannan ya d'auki wayarshi zai tsokani Sudaida,sai dai missed call d'ari da yagani yasa zuciyarshi bugawa da k'arfin gaske kira daga kowa na zuri'arsu lambar Inna yafara kira amma tak'i shiga,fargaba ta kamashi lallai ba lafiya...

A bakin hanya kuma sunyi kaca-kaca da kayan dake cikin rokan sannan suka banka mata wuta.Me neman kuka ne aka jefe shi da kashin a waki,wai saboda yak'i tsayawa suka fara k'ona shagunan bakin hanya...ALLAH Sarki shagon Ashiru Chindo suka fara k'onawa...Mtswww bahaushe me ban haushi na tanko me kan bashi...wai sai a wannan lokacin suka san eh lallai wad'annan mutanan da gaske sukeyi,suka fara neman mafita a sanda lokaci yariga yak'ure musu, dan ba a fafe gora ranar tafiya...kumamar tsanyar da wuri take tila...Dana sani mara amfani...suka cigaba da k'ona tayoyi suna watsa borkonon tsohuwa(tear gas)wallahi abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,garin yayi bak'ink'irin ga har6e-har6en bindigogi ta ko ina.

Yana cikin wannan hali kiran Sudaida yashigo yad'aga da sauri,cikin rawar jiki data murya tafara magana"Yaya D'an Sarai na rok'eka da girman ALLAH karka k'araso garin nan...me yafaru ne?Yak'i a keyi ka koma dan wallahi sun fara kashe mazaje suna k'ona gidajeee...tak'arasa maganar cikin sarewa saboda harbin bindiga shima yaji hakan jin kunnuwan shi.Kina ji? Ta amsa da eh ina...in...inaji...yana d'ago kai yaga gungunsu sun mishi k'awanya...zufa tasake karyo mishi Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yafad'a,a wayar kuma yana jiyo hayaniya da surutai barkatai... wasu suna ihu wasu suna kabbara,anan kuma suna jiran fitowar shi"gaba kura baya siyaki.

Sudaida tafi gidan Inna Insha-ALLAH zan zo in sameku a can yayi jarumtar fad'a mata haka. Tarintse idanunta saboda a zaba wai...wash...uhhh... bazan iya tafiya ba wallahi!wai...ALLAH na!Tafara nishin azaba Zaujiii...nak'uda nake yi haihuwa zan yi...wai...Wayyo!Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un dan ALLAH ka yafe min Yaya Julaibib mutuwa zan yi!A ah Sudaida ba nak'uda bane cikin naki fa watanni biyar ne...wallahi shine bakaji marataba!Tayarfe hannu. Yasake d'ago kai yakalleshi basu k'araso in da yake ba dan sun san ba ta in da zai gudu,yaga abinda bai gani ba d'azu bindigogi AK47,pistol, shar6a-shar6an wuk'ak'e gayama jini na wuce,adduna,tayoyi da jarka wanda ya tabbatar fetur ne a ciki,ga nishin da Sudaida takeyi cikin tsananin ciwon daya had'u da tashin hankali,sai yaji wasu zafafan hawaye sharrr... sun zubo mishi"yanaji yana gani amma ba shi da damar da zaije ya taimaketa...

Sudaida kiyi hak'uri kiyi addu'a ALLAH yana tare dake,bata amsaba nishin azaba kawai take yi tana kiran sunayen ALLAH wai...ALLAH ka taima... bata k'arasa wasu suka shigo gidan.Wayyo! Yaya D'ansarai ga sunan...wani yad'auki wayar dama a k'asa take ta bud'e maganar"me D'ansarai ya isa ya hanamu yi?Zuciyar Julaibib tafara lugude...malam karka ta6a min mata yafad'a cikin k'araji.Yakyalkyale da dariya "matsoracin banza matsoracin wofi kaje ka 6uya kana magana ta waya,to idan ka isa kazo gidan na ka muyi gaba da gaba mana,I swear a gabanka zan zamu mata yankan rago kai ma mu maka,wawa kawai"filthy bastard...

"Wallahi ALLAH ya fiku...yasake kyalkyalewa da wata irin dariya"eh ALLAH ya fimu mu kuma munfiku kaga dai mune zamuci gari,kabimu a hankali dan zakara a rataye baya caara.Bazan biku ba wallahi.Yajijjiga kai"that's very good,mun shigo gidan ka dan muyi bincike ance kuma kunada bindigogi to amma tunda kace bazaka bimuba za muyi maganin taurin kanka, kuma duk inda ka6uya a fad'in garin nan sai an binciko ka an kawo min kai gabana na maka yankan rago kamar yadda muka fara yima sauran tsinannun yan'uwanka.

Yakalli Sudaida da take durk'ushe tana matagugu dafe da ciki,yayi murmushin mugunta"sai nayi abinda naga dama da wannan banziyar matar taka, ya kyalkyale da dariya.Kalamanshi suka soke Julaibib da Sudaida suk'ar wuk'a a k'ahon zuciya. Ambaton ALLAH takeyi a galabaice dan zuwa wannan lokacin k'arfinta ya riga ya k'are,d'an cikinta ya dunk'ule waje d'aya,wucewar wasu dak'ik'u kawai sai jini ya 6alle mata,tana kwance ko motsin kirki ba tayi,idanunta sun fara canja kala kad'an kad'an bak'in ciki yake 6acewa.

Yayi jimmm...yana kallanta,yayi d'as d'as d'as da yan yatsunshi sannan yagyad'a kai bayan ya kalli sauran da suma shi d'in suke kallo"tunda kin min buk'ulun abinda nayi niyya to kema baki da sauran amfani a doron duniya,yad'aga bindiga yana gyara kunamar jiki(trigger)zan fasa k'ok'on kan matarka D'ansarai...Julaibib yafara karaji karka kasheta dan girman ALLAH kabari in zo ni ka kasheni a madadinta... yakyalkyale da dariya wannan daga bayane sadaka da karuwa...shege d'an iska ai kowa ya tuba dan wuya ba lada"may her gentle soul rest in hell...suka had'a baki wajen amsawa da"amennn...Dai dai da har6e kanta da yayi tauuu...tauuu...sai biyu jini yayi kaca-kaca a jikin bango rai yayi halinshi,suka zuba fetur sannan suka sake harba bindiga wuuuhhh...wuta ta tashi suka fita da gudu wayar ta katse.

Julaibib yashiga cikin tashin hankali,ya tabbatar sun kashe Sudaida.Yayi Istirja'i yana kiran sunanta,ihun kiran sunan yasa wad'anda suka mishi k'awanya suka bud'e motar suna mazurai suka jawoshi "da uban wa kake magana tun d'azu a waya? Ko kana fad'ama sauran yan'uwanku masu sallah su kawo muku taimakone?To su zo d'in ba abinda zasu iya mana dan munfi k'arfinku har abadan duniya, yabisu da kallo duk fentin da sukama fuskokin su bai hanashi gane suba, wasu mak'otan shine,wasu ma akwai kud'ad'en da suke binsu bashi,bazato yaji an buga mishi bakin bindiga"you're very stupid ka tsaremu da idanu ba tambayarka muke yiba?Yarintse idanunshi dan yaji bugun har k'wak'walwarshi,bai gama dawowa dai-dai ba suka rufeshi da duka, naushi da mangari baji ba gani.

Wasu tarin matasan hausawa suka hango sun samu mafaka,abinda yasa suka bar dukan Julaibib kenan suka rufarma wad'ancan.Julaibib yamik'a hannu yajawo wayarshi data fad'i yasa a aljihu,dakyar yashiga motar yatashe ta yana gani dishi-dishi saboda jinin da yake zuba dan sun farfasa mishi jiki bana wasa ba,yana zuwa k'ofar gidansu yaci burki wani abu mara dad'i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarshi"ina Innarshi? Baba?Walida da Bilkisun shi!?Zuciyarshi tana bugawa da k'arfin gaske saboda ganin gidan ya gama k'onewa har ya rufta,ya tabbatar koma menene a gidan ya k'one bashi da sauran amfani a doron duniya.

Yafito daga motar yana jiri yana bin bango har yak'arasa gidanshi,yana cikin tafiyar ya yanke jiki yafad'i,awanni nawa yayi a kwance a wajen bai sani ba,ya farkane yaji mutane nabi takanshi cikin neman ceton rai, yarik'o k'afar wani"dan ALLAH taimakeni in tashi,yafizge k'afarshi"wannan rana ce ta kowa yayi ta kanshi,kalleni da kyau harsasai guda takwas ne a cinyoyina amma ina tafiya sai kai kana kwance babu alamar rauni me tsanani a tare da kai?Yayi gaba dan ALLAH kayita kwanciya har su zo su same ka a wajen...ai bai san da gaske zai iya tashiba sai da yaji hucin wutar da suka banka ya ta6i jikinshi.

Dakyar da sid'in goshi yak'arasa gidanshi nanma ya gama ci da wuta,wani wajen kuma da sauran hayak'i,yana shiga D'akin-shak'atawar yaji kamar an sa adda an sare mishi k'afafu saboda tashin hankalin abinda idanun shi suka gani. Wayyooo...!!! Sudaida ce ta k'one k'urmus,maik'on jikinta male-male a wajen kamar anyi 6arin mangyad'a,tabbasss da a waje yaga k'onannan gawar nan to ba zai gane Zaujatiii...ce ba! Kuka yak'wace mishi jikinshi da zuciyarshi suka d'auki rawa"yanzu irin kisan gillan da akama sauran zuri'arsu kenan!?da sauran yan'uwanshi al'ummar Manzon ALLAH? Yahad'iye wani abu me zafin gaske kamar garwashin wutan da aka barbad'eshi da dakakken barkono d'an munci wayyo! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!Lahaula wala quuwata illah billahil aliyul azim!!! Idanunshi suka kad'a jawur sai yaji kome yafice mishi a rai... zafafan hawaye suna zubo mishi sharrr...! sharrr...!

kira yashigo wayar daya manta da al'amarinta yacirota a aljihu Musaddiq...yad'aga da sauri yana fad'in Musaddiq sun kashe Sudaida sun k'onata ina sauran Iyayan mune? Suna ina?Kaima kana inane?Musaddiq ya amsa cikin tashin hankali "saurara kaji abinda zan fad'a maka dan tun d'azu nake gwada kiranka bata shiga sai yanzu.Sun kashe su Baba a masallaci, gidajanmu, Iyayanmu, matanmu da Ya'yanmu sun banka musu wuta kafin sufito su gudu!Musaddiq yafara kuka sai dai mu bisu da addu'a kafin wa'adinmu yacika,D'ansarai sunci k'arfinmu, sunyi galaba...!D'ansarai bamu da abinda zamu kare kanmu dan nima haka nafito daga gida hannu rabbana...dakyar furucin nashi yake fita... Musaddiq me yasame kane?Saurareni kawai Julaibib meye ma bai sameniba!?Menene ban gani ba?Yak'ara fashewa da kuka"a gaban idanuna akama Adnan da Sagir yankan rago...!!!

Kaiii ALLAH yatsinema arna...Julaibib k'afafuna a karye suke ga sara ba adadi a jikina,ga harsashin da suka harbeni yana cikin cikina...dakyar yake furucin Julaibib yadad'a manna wayar a kunnanshi dan maganar tashi k'asa take dad'a yi,kaima sunata neman ka ruwa a jallo dan haka ni shawarar da zan baka idan kasamu ma6uya to wallahi ka6uya,tunda ba abinda zaka kare kanka dashi...yafara tari da nishi duk tarin da yayi jinine yake fita ta baki ta hanci,yafara numfarfashi sama-sama, numfashin yana san d'aukewa,yafara magana a fizge D'ansarai mu yafema juna...abinda duk yake tsakaninmu na kud'ad'e da sauran al'amuran rayuwa duk mu yafema junaaa...!rayuwata...ta...k'are ina ji ajikina bazan kuma rayuwa a doron duniya ba!Cikina kamar ana huramin wutahhh...!!! Wai...washhh,Yayi nishi me k'arfi...jini yana zubowa tabaki ta hanci.. Ju...l...lai...bib...kumaaa...ina!yayi iya yinshi furucin yak'i fitowa yana nishi cikin tsananin ciwo...



Kaskon wuta me wuyar tallafa.
Na gaban wuta shi yake jin d'umunshi.


9 Rajab 1441
3 March 2020


We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.





DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}




Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFI💔


Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim ( Ra'ibs)




Shafi na ashirin da biyar.




Cikin tsananin tashin hankali yake fad'in Musaddiq...Musaddiq kana inane!?Shiru ba amsa yacire wayar ya duba har yanzu a had'e suke,wucewar wasu dak'ik'u Julaibib yana cigaba da kiran sunan shi Musaddiq!Dakyar ya amsa.Kana inane? Musaddiq yamirgina kai cikin ciwo"bazaiyi amfanin kome ba,na san mutuwa zan yi tawa ta riga ta k'are,D'ansarai...kab... ka6uya... k...kak... kaw... wai.Zuciyar Julaibib tasake tsinkewa yafara kuka"na rok'eka da girman ALLAH kafad'a min inda kake zan zo in taimake ka...kai kad'ai karage min d'an uwa na jini a doron duniya!yacigaba da magiya har Musaddiq yabud'e baki dakyar yace"ina wajen masallaci.Wani masallacin? Wanne Musaddiq?

Yayi tambayar a gaggauce jin wayar shi tayi k'ara alamar caji saura kad'an yak'are... Musaddiq ya kasa magana sai nishin azaba yakeyi... Wanne daga cikin masallacin Muss...kafin yak'arasa fad'in sunan difff wayar takashe kanta.Yafurzar da wani huci yana kallan k'onannun k'asusuwan Sudaida sai yaji kukan cakkk...Ya tsaya,yamik'e tsaye yana mata addu'ar dacewa da rahamar Ubangiji"Zaujatiii...ya fad'i sunan yana jijjiga kai"sai ALLAH yahad'a mu a lahira... uwargidata ta duniya da lahirahh!...

Koma wani masallaci ne Insha-ALLAH sai ya gano Musaddiq ya bashi taimakon gaggawa iyakar iyawarshi,zuciyarshi tabushe,wallahil-azim shima sai yayi kisa sai dai idan bai had'u da arne ba;koda zasu kashe shi,yana fita kuwa yaga k'aramar bindiga an kashe wani arne ta fad'i a hannunshi, yad'auka ya lalube aljihunshi yakwashe sauran harsashin yaloda a ciki sannan yafara tafiya cikin sand'a yana bin bango,daga nesa yahango gungunsu sun dumfaro inda yake,a hankali yazame yakwanta a cikin gawarwaki kamar shima mataccen ne.

Suka zo suka wuce suna surutai da yaren Bajju,a d'an abinda yake tsitssinta daga yaren ya fahimci harsashin sune yak'are zasu koma gida su k'ara sabon lodi,dan haka yad'aga bindiga yasaita su daga kwancen ALLAH ya taimakeshi ya harbe guda uku nan take suka zube a k'asa matattu,sauran suka fara gudun ceton rai suna zage-zage a cikin gawarwakin nan akwai wanda bai mutu ba, amma dan abu kazan uban mutum yabari muje muk'ara shiryawa wallahi zai gane da gero ake koko...Julaibib yasake harba bindiga yasamu wani a kai shima ya fad'i yana ihu da kururuwa,sai da yak'ara mishi harsashi biyu sannan ya tashi yabar wajen kafin su dawo,zuciyarshi tana tafarfasa da kalaman wanda ya harbe Sudaida"zan fasa k'ok'on kan matarka...bata sauran amfani a doron duniya"may her gentle soul rest in hell... Julaibib a gaban idanuna sukama Adnan da Sagir yankan rago...ank'ona su Inna a gidajansu... sun kashe su Baba a masallaci...kalaman da suka dinga mishi amsa kuuwa a k'wak'walwarshi kenan.Sai yaji wani k'arfi yasake zuwa mishi.

Yana cikin tafiya yaci karo da gawar Abdul d'in Yaya Karima an daddatsashi abun ba kyan gani,bai tsaya ba dan tsayuwar bata da amfani tunda ya riga ya mutu,su da arnan kuma kowa k'ok'arin kashe kowa yakeyi haka yakeya cin karo da gawarwaki kisan wulak'anci!Julaibib yayi yawon bin masallatai amma baiga Musaddiq ba,a wajen masallacin Malam Murtala yaga wasu mutane guda biyu an sa musu taya sun k'one k'urmusss...ba ta yadda za ayi ka gane ko suwaye wallahi,yaciga da tafiya zuciyarshi na tafarfasa daga baya yaji an harbe shi a kafad'a ashe wasu daga cikin su sun hangoshi... yajuya yana harbinsu shima har sai da harsashi yak'are,yatura bindigar a aljihu yakwanta yana a k'asa cikin mawuyacin hali jini yana zuba.

A wannan rana ta litini kwana akayi ana gumurzu tsakanin musulmai da arna,duk da musulmai masu kayan aiki k'alilan ne amma sunyi k'ok'ari da k'arfin zuciya suma sun kashe arna ba wanda yayi galaba akan wani,kare

Please Login or Register in order to submit comment