Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai kuma kawai a kashe Sumayya to duk mun ya fe muku bak'ak'en maganganunku, ALLAH ya yafe mana gaba d'aya.Sai dai ku sani shi Ubangijinmu baya ta6a barin wani dan wani, madamar wa'adin barin duniyar ka ya cika to fa ba tsimi ba dabara dole sai ka barta.Kuma ya kamata kufahimci wani abu,shi fa labarin nan idan kuna duba duk shafukan da suka gaba ta,ai muna rubuta"ALMOST TRUE STORY"ba k'irk'irar shi muka yiba,kaso casa'in na cikin shi ya farune,to sai ku gane ba dukkan abinda kake so ne kake samun shi a rayuwa ba,kuma dole ka kar6i rayuwar a yadda tazo maka,canja wani bangare na labarin to yana nufin canja labarin gaba d'ayan shine.

...GWAJIN DAFi💔Labarine me jigo kusan biyar d'unkule cikin d'aya,dan auna fahimtar makaranta.


Your comments is beyond our expectation...
Ibrahim's Daughters really appreciate.
1.Zainab Tijjani Ahmad (Ummu Bilqis)
2.Abdullahi Lawal Abdullahi (D'an Sarai).
3.Me Sunan Manya Khadija Kafanchan.

Ya'yan Ibrahim suna godiya,dan kulawa yabawace.
1.Ummu Ammar.
2.Salima Uba D'an Zainab.
3.Maimunatu Ibrahim.
4.Bilkisu Muhammad (Darling)
5.Zaynerb bello 36
6.عيناء ابرهيم عبد المؤمن
7.Ummul Ameen.
8.Shamsiyya Sani 661
9.Ummee Umar Musa.
10.Samira Garba.
11.A'isha Rabi'u.
12.Zainab A.Sulaiman.
13.Hafsa A.Sulaiman.
14.Khadija Bashir(Ummu Hanan)
15.Ummu aimanal habashiyya(Maman Kinanata)
16.My Sau'ash( Asdilat💋 for real)
17.Nasiba Namadi 'Yar Zonkwa😀
18.Khadija A.Muh'd (Ummu A'isha)
19.+234 813 109 04..I don't really no your name,but you care.
20.A'isha Nura Sani (Dr.Maidiyam)
21.Saudat Ibrahim Yahya.Takwarata wannan sunayen na kifa sune rayuwata💋😀ni Asdilat KD...ina yinki fiye da shurin masaki.

Shafi nagoma sha biyar.



Soyayyarsu ta bazu a dangi,wasu sun yaba sunyi sam barka,yayin dawasu suka koma gefe suna k'unk'uni an rasa gane manufarsu. Suna hirarsu da Hajiya yake fad'a mata"Megado tace a gaishe ki,wannan k'arshen makon baza tazo Islamiyya ba suna jarabawa.Dan haka sai kisa ta a addu'a.Tagyad'a kai"Ubangiji yasa a fara a sa a, yasa asamu kuma abinda ake nema.Amin Hajiya.

Sudaida tana share tsakar gidan tad'an ta6e baki"ni ana fad'in ban iya girki ba sai na iyayi,to su kuma Fulani kona iyayin ma ai basu iyaba,to su da abinda suka iyane banda tatsan nono da tallanshi gidaje da kasuwanni ne?Kai ALLAH yasauwake.Taja dogon tsakin dayasa Julaibib da Hajiya juyawa suna kallanta"lafiyar ki k'alau kuwa Sudaida?

Ta'ajiye tsintsiyar bayan ta kwashe sharan ta zubar.Takauda kai daga kallan da suke mata"kalau d'ina Hajiya gida zan tafi... fuuu tawuce cikin fushi ko sallama bata musu ba.Hajiya tabita da kallo cikin nazari...sai kuma tayi yar dariya"dawalakin goro amiya.


Julaibib yasauke numfashi "Hajiya kwana biyu yarinyar nan sai ta dinga cimin mad'aci,wallahi jiya data shigo wajan Inna tana kallona amma tad'auke kai ba ko gaisuwa kamar bata ganniba.Hajiya tace"yan wasan ne bata jin yi dakai,kaima ba sai ka share ta kaji da hayagagar...su Nasmat ba?Yayi d'an murmushi "Hajiyar mu ALLAH yaja nisan kwana me amfani. Amin Julaibibi amin.

Malam Lamid'o dattijon arzikine yayi karatun addini dana zamani me zurfi a yanzu hakama likitan dabbobine(Veterinary Surgeon) abinda yatarfama garinsu nono kenan Ya'yanshi suke yin karatun boko me zurfi.Bilkisu itace 'yarshi ta biyar,ya barta ta cigaba da karatune kasancewar ta me san karatun,kuma tun data gama Secondary ba wani tsayayye sai Jauro shi kuma yace bazai ba Jauro auran taba,data ce ga abinda takeso ta karanta aikin jinya da unguwar zoma,yaji dad'i ya k'arfafeta dan karatun da za tayi zai amfani mata yan uwanta.Shi da matarshi sunyi tufka me kyau da k'wari wajan tarbiyyar Ya'yansu, sai Ubangiji yadubi niyyarsu sai suka ta so cikin tsoron ALLAH da ganin girmanshi ga kunya da sanin mutuncin mutane.

Nurse Bilkisu Muhammad Lamid'o...

Farace Kyakkyawar matashiyar budurwa,kyau irin na tsurar fulani da bashi da gauraye da kowace kabila dan gaba da bayanta, uwa da uba typical Fulani ne, kome na ta irin na mahaifin tane sai dai bambanci na ita macece shi kuma namiji ne,yanayin maganarta da muryar ta shine kawai irin na mahaifiyar ta.

Bilkisu Megadon zinare...idan tayi murmushi ko dariya kai ko magana tayi sai kaga kamar da san a sanine...takeyi dan kawai tanuna yar lotsar(dimple)dake gefe da gefen fuskar ta da kuma yar siririyar wushiryar ta, abinda yak'ara mata kyau na musamman bak'in gashin kanta me yawa da tsantsi irin na asalin tsurar fulani,sai tattausan jajayan la66anta kamar ta turasu da jan jambaki... Bilkisu me kyauce ga sauk'in hali dan bata rud'u da kyawun halittar da Ubangiji yamata ko ilminta ba,kome na ta a natse take yinshi cikin mutunci da sanin kimar kai(a very meek damsel)Tun tana k'aramar Secondary ta sauke Alqur'ani me girma,har yanzu kuma tana karatun littafan addini.

Sauri take yi tana kuma addu'a ALLAH yasa tasamu abin hawa dan gaba d'aya d'alibai sun gama watsewa a hanyar,Khausar ma ai ta tsufa a gida taimakon ta d'aya da Khausar ta tafi mata da jaka, da harda jakar da littafan ciki da ita kanta ruwan saman da yake shirin sauka zai k'are akansu.

Takad'a kai cikin damuwa"gaskiya wanda duk baiji bari ba zaiji hoho,dama su Nasmat sun fad'a mata kar tasha maganin mura da tsakar ranan nan bacci zai sata,tamusu kunnan uwar shegu tawuce dispensary na makaranta takar6i maganin tasha aiko tun a masallaci suna sallar azahar bacci yafara kawo ma idanun ta ziyara,duk k'ok'arinta na korar baccin abin ya ci tura,ganin haka yasa tama Metron magana dan tasu da Sudaida ta zo d'aya sai ta bud'e mata Hostel"Clerkin's House"har kwanar Kakus d'inta, yar ajin suce amma sunan su d'aya da Hajiya dan haka suke kiranta da Kakus ta haye gadonta ta kwanta aiko bacci yayi awan gaba da ita har aka tashi bata sani ba,bata farka ba sai biyar saura na yammacin amma taji ta garau zazza6in da yake shirin rufe ta ya sauka,sallar la'asar tayi ta d'auki takalmanta tana sawa,lokacin Kakus ta takawo mata jik'ak'k'en k'anzon alkama da madara(corn flakes).

Na ga kina sa takalmi badai tafiya za kiyi ba? Tagyad'a kai tana murmushi"yanzu kuwa"tazauna agefen ta"to amma ai kya tsaya kici abinci na san baza ki iya cin garau-garau d'in dining ba shi yasa na had'a miki wannan me d'an ruwa-ruwa tunda kina fama da mura,tamik'a mata kofin.

Kakus...tasake dubu agogon dake d'aure a hannunta na dama.Uhun Jikalle me kike so kifad'a baza ki sha ba ko me?Tad'an marairaice"ALLAH Kakus...Sai kuma tayi shiru, tasa hannu biyu takar6a,cokali hud'u tasha ta'ajiye "nagode"taharareta"wannan dai dan kar ince baki sha bane kawai.Tadaki kafad'arta'ke yar rainin hankali, to ko akan me zan cika cikina da wanna bayan na san abinci na me rai da motsi yana jirana a gida.Ta tafa hannu cikin salati"Oh ni zamani! yanzu Jikalle ni kike dukar ma kafad'a saboda wuyanki ya isa yanka.Yadda tayi furucin kamar irin Kakar nan ta gaske yasa Sudaida ta kyalkyale da dariya,sai kuma tad'an marairaice itama"come on Kakus don't be upset"kema kin san bana miki haka,to yau d'aya dai ya kamata ki kar6i uzurina, Yaya Khausar ta dad'e da tafiya gida,kuma kinga hadari yana ta had'uwa sai cida akeyi bana so ruwa yatareni.Tadafa kafad'arta"na fahimce ki. Suka mik'e...muje in rakaki.Har gate d'in k'arshe nafita daga makarantar tarakata,dan ALLAH ni dai karki manta gobe ki taho min da soyayyiyar gyad'a,tad'an harareta"to anawa?A neman albarka tad'an zaro mata idanu ko bakya san albarkan manya?Sukayi dariya"so kai"sukayi sallama, sannan suka d'aga hannu suna ma juna adabo.

Iska me k'arfi tafara ta sowa garin yahad'e yayi bak'i sai cida akeyi ba k'ak'k'autawa, abubuwan hawa suka dinga k'ara guda dan tsira daga dukan ruwan watan bakwai,tak'ara sauri akwai gidan yar ajinsu Zamburan agaba sai ta samu tafake,amma ina hak'anta bata tadda ruwa ba,kad'an-kad'an yayyafi yafara sauka tanad'e hannayanta a cikin hijab,sanyi yafara ratsata tarintse idanu"wayyo ALLAH na! Shikenan sabuwar mura zata dawo!

Dagudu motar tazo tawuce ta,wacce yahango tacikin madubi yasa yayi ribas har yak'araso inda take,Caraf idanun su yahad'u yana bud'e motar,wani sanyin dad'i ya mamayeta. Yabud'e mata"to shigo mutafi mana kina ganin ruwan yana k'aruwa...tad'an harareshi sannan tashiga kamar wacce zata zauna a garwashin wuta.


Yaja motar"me kika zauna yi a makaranta? Kamar ba da ita yake magana b.Ba tambayar nake yi ba? Dak'yar kamar me ciwon baki dan haushin shi takeji tace"baccine yad'aukeni a dormitry"bai sake magana ba yacigaba da tuk'inshi cikin natsuwa,sai dai ruwan daya cigaba da zuba kamar da bak'in k'warya yasa shi gangarawa gefen titi yatsaya har sai yad'an tsagaita.

Yaya D'ansarai...

Yad'an kalleta"na'am.Taturo baki gaba"nifa gaskiya in dai ba so kakeyi in k'arasa mutuwa ba to kashe wannan mukayyib d'in(Air Condition) ...kafin tagama rufe baki tafara atishawa,sai da tayi biyar ajere"Yar hamukallah "yace mata bayan ta godema ALLAH."Yahdi kumullahu wayuslih baalakum"tasa hannu tana jan hancin ta daya fara toshewa,k'wallah yacika idanun ta dan wallahi sanyi takeji bana wasa ba gashi kayan jikinta ajik'e suke.Sai da yamaida ita heater sannan tafara dawowa hayyacinta motar ta d'auki d'umi,ruwan yad'an tsaigaita motocin dasuka tsaya kowa yaja yacigaba da tafiya.

Suna shiga gida Mama tace"Masha-ALLAH dama yanzu nake dad'a yima Adnan magana yad'auki mashin yabita makaranta yad'aukota"Yayi d'an murmushi"a hanya muka had'u dawowa ta daga Kaduna kenan.Adnan yafito daga d'akinshi yana mita"Mama banda kece da kanki kin cika min idanu kin shak'emin wuya da wallahi ba inda zani ruwa bai gama d'aukewa ba. Tagyad'a kai"to kayi zaman ka mana.Yak'arasa kulle k'ofar tashi"a haba dai Mama ai wata fuskar tafi gaban mari har abadan duniya.Yana shiga D'akin-shak'atawar yagansu...yauwa yayi yar dariya"kai madallah da autan Inna.Yamik'a mishi hannu sukayi musafaha,yajefama Sudaida mukullin"kai min d'aki".

Khausar tashigo da lemu ta'ajiye agaban shi bismillah fa.Yagirgiza kai"bazan shaba,kirasa abinda za ki kawomin sai lemu me sanyi bayan yanzu aka gama tsuuga ruwan sama har da k'ank'ara?Yamik'e dai-dai da shigowar Mama."Mama na wuce.A ah ka tsaya yanzu nasa Sudaida takawo maka kayan bud'a baki.Yad'an shafa kai"Nagode Mama amma kiyi hak'uri sauri nake yi dan gidan Hajiya zani kafin in wuce gida" To ai ba kome musha ruwa lafiya.Amin Mama.

Hey autan Inna...

Zai shiga mota yaji kiranta yajuya yana kallanta ta canja kayan jikinta da riga da wando kirar Pakistan ruwan k'asa da yarfin k'anana filawoyi ruwan hoda me haske,tad'ora farar rigar sanyi tasak'a da farar hula me harafin M.Gashi inji Mama.Bai kar6i ledar ba yace me wannan harafin M d'in yake nufi?Takai hannu tashafa harafin"Masoyi na Sinan ko da wani masoyi ne bayan shi?Yamata wannan rikitaccen kallan nashi takauda kai "gashi ni sauri nake yi. Yashige mota ya zauna"ki kaimin gida yayi tafiyar shi.Tabi danjojin motar da kallo har ta 6ace ma ganin ta.Takalli ledar taja dogon tsaki"kawai dan kabani wahala,shi dai wannan halin na shi ALLAH yasauwak'e mishi...tashige gida tana k'unk'uni.

A safiyar asabar suna hirarsu da Inna yana shan shayin na'a-na'a da ya'yan algarib tashigo da sallama, tagaishe da Inna sannan tazauna a kusa da ita tana fad'a mata sak'on Hajiya.

Yamaida hankalin shi ga sauraran wak'ar wani balarabe yana wake Habibti d'in shi da irin soyayyar daya ke mata wai"ya kamu da yunwar son ta,kuma ita kad'ai take da irin nau'in abincin da za ta bashi idan yaci sai yadawo hayyacin shi,dan yanzu shi ya zama kamar gawane da rai"yad'auki remote yad'an rage k'ara yana cigaba da sauraran tsadaddun kalmomin da yaketa bayyana irin k'aunar shi gareta me sanya zuciya bugawa a cikin shauk'in so,har baitin k'arshe sannan ya canja tasha.

Kiran daya shigo wayar shi yasa yamik'e yafita,Sudaida tabishi da kallo sai kuma tamik'e itama dan makarantar allo za ta wuce.

Yana tsaye a k'ofar gida yana wayar cikin sakin fuska,yayi k'asa da murya yana gyad'a kai"na sani Megado amma na manta ne,ALLAH yamiki albarka da wannan tunatarwan.Yayi jimmm...yana sauraro"to shikenan karki damu kinji ko?...yauwa to nagode sai na shigo.

Tawuce kamar bata ganshi ba.

"Am Sudaida...

Takalleshi fuska a had'e.Yayi yar dariyar data bata mamaki dan ba kasafai yake hakan ba.Yauma kin shigo gidan nan kin kuma ganni ganin idanun ki amma baki gaisheni ba,wai in tambayeki mana? Kallanshi tayi batace kome ba "Sudaida... wannan cin mad'acin da kike min bana jin dad'in shi kona miki wani laifi ne?Tad'an turo baki gaba sannan ta kauda kai"ni ba kome.Anya zan yadda dake kuwa?Takalli siririn agogon dake d'aure a hannunta sai kawai tajuya "gwamma da kai auran ka da gata kar inje insha dukan makara.Ki tsaya muyi sallama dan baza ki dawo makaranta ki same niba.Jikinta yayi sanyi amma bata tsaya ba tacigaba da tafiya"To ALLAH yakiyaye hanya ai zamuyi waya.Ki tsaya ki kar6i"tasa gudu nifa bana so.Yabita da kallo yana wata kissima a zuci.

Jikokin Hajiya sun cika mata gida sunata sha'anin gabansu.Sudaida takallesu"kun san ALLAH cikin makaranta zan koma(hostel)na gaji da trekking sai randa aka ga dama za a zo a d'aukemu.Nasmat takama ha6a"to makarantar allon kiyi yaya da ita? Idan an ba da hutu na dawo gida sai in d'ora daga in da natsaya.Hajiya tasa musu baki"yanzu ke saboda makarantar boko za ki bar makarantar Mahammadiyya? Bayan shine a hakku akanki?Taturo baki"ai ba cewa nayi na daina ba,kuma ai nafad'a ma Baba ya kuma amince.Hajiya tamata dakuwa"to ni ban amince ba zai kuma zo yasameni bokon banza bokon wofi, bokoko a wuta. Nasmat ta kyalkyake da dariya"Ke Hajiya bokon kike ma wannan zagin kamar bakiyi ba?eh na zaga,dan kayi karatun boko indai ba karatun Muhammadiyy ai shirme kayi...ko ba ga sunan ba marasa addinin k'wararrune a fagage mabambanta na cigaban rayuwa amma sai kika mutum wai yasa abinda zai bautama sai saniya ko rana ko kwad'o...wannan ba 6atan basira bace da rashin sanin tauhidi?Ai ba abinda zai baku rayuwa me inganci sama da Alqur'ani da hadisan Manzon ALLAH dan ya tattara kome shak'undum kenan.

Washe gari kuwa data je gaishe da Baba yake fad'a mata komawarta cikin makaranta an soke shi, Hajiya tazo da magana abar dubawa,yamik'a mata babban envelop foam ne guda biyar a ciki,ki kaima Nasmat na ta gida ko wacce tacike ranar Juma'a zaku fara zuwa makaranta,tasa hannu biyu takar6a"to Baba ta tashi tafita.

"HAYATUDDEEN ISLAMIYYA SAMARUN-KATAF"

yanzu har Samaru zamu dinga zuwa?Wallahi duk Hajiya ce da wannan aikin saboda kawai nace zan koma cikin makaranta shine har ranakun k'arshen makon ma bazata barmu mud'an sarara ba?Taja tsaki tana k'unk'uni,tad'auki biro tana ciccike inda ake so aciken.

Maganar Julaibib da Bilkisu ta kan-kama sun kai kome da a ke kaiwa an kuma tsayar da lokacin biki watanni uku masu zuwa dai-dai da gama karatun ta. Julaibib ya tafi bautar k'asa,jahar Bauchi aka turashi angama basu horan sati biyu a sansaninsu(camp)yakoma inda zaiyi service d'inshi a k'aramar hukumar Azare.


Sai da yayi wata d'aya sannan ya dira a Zonkwa dawani yammacin laraba rana ta tafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai,yatsaya yayi sallar magriba sannan yatafi gida.Inna tayi murnar ganinshi dan bazata ya mata bai fad'a mata ko awaya ba.Baije ko ina ba sunata hirarasu ta yaushe gamo yana cin abinci ita kuma tanata kalan hotunan dasuka d'auka lokacin da a ke basu horo(training)tad'aga wani hoto tana murmushi ashe kunsha wahala?Yagyada kai"Eh Inna akwai wahala dan sojojine suka bamu horon cikin dare zasu kafa su tsare kowa sai yafito su fara bamu horo tayi yar dariya"lallai kun zama k'ananan sojoji.Amma ni ban wani sha wahala ba. Tagyada kai"ai baza kashaba tunda ka saba motsa jiki da manyan k'arafa yanzu har mata sai sunyi wannan?Eh har su sai sunyi masu tsohon ciki ne kawai naga an d'aga musu k'afa.Taja tsaki wannan tsarinne kawai bai min ba.Yad'anyi murmushi"To ya zamuyi Inna tsarin ne yazo da haka amma Insha-ALLAH bama cire rai da wata rana za a samu manya a harkar masu addini da zasu zamantar da abin dai-dai da shari'ar musulunci a raba mata musulmai da irin wannan shigar a bainan-nasi.Inna tad'aga hannu "Allahumma amin Julaibib.

K'arfe shida na safiya sukayi kaci6is akwanar gidansu,dawowar shi kenan daga masallaci sallar asubahi,k'afafunta sanye cikin takalmi sneaker fari igiyoyin d'aurewa ruwan bula,wando ruwan bulu,farar riga sai hijab iya gwiwa ruwan bula sun sha guga tana goye da bakar jaka da Maths-set a hannunta.Tad'an bud'e idanu cikin mamakin ganin shi"Kai Yaya D'ansarai saukar yaushe? Yabita da kallo duk da garin bai gama wayewa ko ina yayi haske ba amma dai tayi kyau"Jiya gab da magriba.Excursion za kuje? Tasake kallan farin agogon dake d'aure a hannunta na dama"ba wani excursion Mr Goje malamin turanci(English)ne yabamu jinga (Assignment) kuma to be submitted before seven O'clock"to shine kike wannan saurin kamar za ki tashi sama?Tagyad'a kai"eh mana wallahi ji nake kamar inyi tsuntsuwa,wai dan ma ba acikin makaranta muke ba shine yad'aga mana k'afa,su yan cikin hostel ai k'arfe shida yabasu,duk wacce tawuce shida koda da dak'ik'a d'aya ne bazai k'ar6a ba,shikenan kuma fa a matsayn C.A test d'in mune,kuma nayita rok'on Yaya Adnan yakaini yace ba abinda zai fitar dashi awannan sanyin,ai dai ALLAH yajik'an Yaya Aminu ba dan yamutu ba dayana gida na san zai kai ni.Tayi gaba da sauri.

A bayan ta taji horn yabud'e mata kofa"ke Sudaida zo ki shiga mutafi.Yad'an kalleta bayan sun hau titi"lallai baku raina Mr Goje ba.Yaya Julaibib wargi waje yake samu,shi wannnan Malamin mugune na gasken-gaske gashi kuma yanzu shine Labour Master,ya yanka ma mutum k'atan fili iya ganinka yace sai ka nome shi wallahi k'aramin abu ne a wajan shi.

Hankalin Sudaida bai kwanta ba har sai da taganta a Staff-Room agaban tebur d'inshi ta'ajiye littafin ta kuma sa hannu,tafito tana sauke numfaahi"wai ALLAH na! nayadda k'wallan mangwaro na huta da kud'a.Takoma wajan Julaibib yanata kallanta ta gilashin motar yana kissima wani abu a zuci,tad'auki jakarta. Yad'ora hannun damar shi a saman sitiyarin motar"kin ko karya?A ah.Yakalli agogon motar ai da sauran lokaci kafin kuyi assebmbly ko muje Staff-Quater gidan abokina Aminu Idris ki karya a can?Tagoya jakar"barshi kawai Yaya Julaibib,ai Yaya Khausar zata kawomin.Sukayi sallama,yad'an lek'o da kai "kuyi hak'uri yau akwai inda zani dana dawo na d'auke ku"tad'aga hannu tana mishi adabo ba matsala nagode,tabi motar da kallo har yafita daga gate d'in farko sannan tajuya zuwa ajinsu tana murmushi.

Kwanci ta tashi asarar me rai,biki saura wata d'aya,awannan lokacin Julaibib baya samun zama saboda zirga-zirga tsakanin Azare da Zonkwa,Yadad'a gyara bangaranshi dan anan zasu zauna tunda bai gama ginin shiba.Dasafe yaje gaishe da Kawunshi sunata hira musamman abinda yashafi kasuwancinsu,sai da zai tafi yamik'a mishi wasu mukallai na gidan kane,na baka d'aya daga cikin gidaje na na Unguwar-Rama daura da masallacin Yarbawa hakak malak. Julaibib yad'ago kai bayan ya duba takardar shaidar mallakar gidan sunan shinei ajiki"Kawu nagode ALLAH yasa da mafificin sakamakon shi, ALLAH yak'ara girma.Amin.wannan ai ba kome bane.

Yad'auki Musaddiq sukaje suka ga gida,sabone dal sai k'ura dayayi tunda bakowa yasa yara suka wanke lungu da sak'o na gidan.Kafin yakoma Azare sun sa kome da ake buk'ata suka kulle sau ranar daza a kawo amarya.

Yajingina da bishiyar mangwaran k'ofar gidan yana kur6an madarar shanun tatsar lokacin,hirarsu sukeyi cikin nishad'i irin ta masoyan juna.Bilkisu har naji kin fara k'amshin amarci fa.Tad'anyi murmushi.Yayi tsai da idanun shi yana kallanta"Megado baki ce kome ba? Takauda kai"Kazo ka tafi bana so kayi dare a hanya daga nan zuwa Azare tafiyace me tsayin gaske"Megadon bana san tafiya yau "Takalleshi cikin kulawa"saboda me?Yanunata da yatsa.

Tad'anyi luuu da idanunta kamar zata rufesu sai kuma ta sunkwui da kai"Julaibib ai kai nawane,ni d'in nan ta kace Insha-ALLAH,amma bazan so ace nice silar ta6ar6arewar al'amuranka masu mahimmanci ba,bautama k'asa a matsayin ka na d'an bautar k'asar dole ne,kome kuma za kayi to kayishi yadda ake buk'ata,kazama me amana; tafiyarka ai ba itace rabuwar muba,koda munyi nesa da juna to amma ai zukatanmu suna tare,kuma ga waya muna gaisawa,muna chatting, har video call duk munayi,tad'ago cikin natsuwa da kulawa tad'an kalleshi"duk basu wadatar ba D'ansarai?

Yanad'e hannayan shi a k'irji yana murmushi "sun wadatar Megado,ke macen alheri ce da bata taya 6era 6ari.Yamik'a mata kofin madarar yashiga mota yazauna yana d'aura belt "ALLAH yamiki albarka Bilkisu "tarufe mishi murfin"Amin D'ansarai nagode,sukayi sallama. Tabi bayan motar da kallo a hankali yake tuk'in har ya6acema ganinta.Tajuya zuwa cikin gida tana mishi addu'ar sauka lafiya.

Inna tabita da kallo"har ya tafi?Sai lokacin tasan Inna tana tsakar gida,ta zauna a gefan tabarmar tana d'an murmushi,kumatun ta suka lotsa ciki"a kunyace tace ya tafi Inna"sai kuma tamik'e da sauri ta shige d'aki.

Tana shan rake tana 'yan wak'ok'inta cikin nishad'i,Khausar kuma tana karanta wani littafi"The secret of occultics powers"su Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu,A'isha tace ya naganku haka?Khausar takalle su "to da ya kike so ki ganmu? Tazauna a gefan gadon"banga kun shirya ba,za muje ganin d'akin amaryane. Khausar ta ajiye littafin"har kin tunamin ance da mahaukaci baya duka.Tabud'e wadrobe tad'auko hijab sannan takalli Sudaida"to mayyar rake badai za kice jiranki za muyi har sai kin gama shaba?

Tamusu kallan uku ahu"kuyi tafiyarku dan ni bana zuwa gayyar sod'i.Suka bita da kallo cikin mad'aukakin mamaki"gayyar sod'i fa kikace? Zuwa gidan Yaya Julaibib d'in?Tayi kamar bataji suba...zuwa can bayan ta shaki iska ta baki ta hanci tafesar tana wani tsuke baki"Eh shi d'in fa wani abu ne?Ni dai wallahi banga abinda zanje gani wanda ban san shiba,ban ta6a ganin shi ba, taja dogon tsaki"gado ne fa da sauran tarkace, tad'ora hannun damar ta a katakon gadan su, wannan ai gadone ko?To gashi na gani akaima nake bacci,sauran tarkacenma muna dasu a D'akin-shak'atawa da D'akin-girki,kuma bama amaryace za tazo da suba,ta kuma jan dogon tsaki cikin tafasar zuciya"kai ALLAH yasauwak'e ma Fulani,wai ace kome mijine zaiyi,ga uban sadaki da suka yanke mai,dubu hamsin sai kace siyar da ita za suyi"ai dai k'arancin sadaki yawan albarkar aure wallahi.

Khausar ta tareta da sauri"ke dakata

Please Login or Register in order to submit comment