Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taji wasu zafafan hawaye suna zubo mata sharrr...shar...tasaki labulan takoma ta kwanta cikin kewar masoyiii...

Shekaru goma sha uku kenan cifff...da auren Julaibib Abdullahi D'ansarai da Sudaida Ibrahim Me-Lambu. A wad'annan shekarun ALLAH ya zurta su da Ya'ya sanyin idanu da Bilkisu...kyakkyawar yarinya data d'auko kyan Iyayenta,bak'in gashi me yawa da tsantsi irin na mahaifinta, sannan ALLAH yabata farar fatar da bana Iyayenta bane ganin damar Ubangiji ne kawai.Bilkisu yarinyace data yi farin jini a zuri'arsu kaafatan,gata da natsuwa bata da yawan magana kamar mahaifinta,idan kaji dariyarta toh dashi suke magana, ga ta da k'wak'walwa duk abinda aka koya mata sau d'aya toh ya zauna kenan ba ta buk'atar maimaici,tana da kaifin basira.

Bilkisu Julaibib D'andarai...

Shekarunta biyar a yanzu haka tana primary one a makarantar boko,bangaren Islamiya kuma tana da haddar Izifi goma sha biyar daga Yasin zuwa nasi duk in da kaja mata Insha-ALLAH zata cigaba.

Sai Maimunatu Julaibib D'ansarai... kanwarta takwarar Inna suna kiranta Walida me shekaru uku.Sai kuma wani cikin da take dashi.

Julaibib ya d'auki son duniya ya d'orama Y'ayan nan musamman Bilkisu son ta yake kamar me, saboda dalilai masu yawa,na farko ya sameta a sanda baiyi zato da tsammani ba,na biyu tayi kama da Innarshi,na uku sunan marigayi daya so auren ta kamar me amma ALLAH bai k'addari za suyi aure ba,na hud'u Sudaidan da yake so yake k'auna ita ta haifa mishi,na biyar yarinyar akwai ta da k'wak'walwa da sauransu da sauran...

A gajiye lik'is yashigo gidan da sallama,suka gewaye juna tana mishi tausa a hankali yalumshe idanunshi wata natsuwa ta mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyar shi "Zaujatiii...ta iya biyar dashi da lak'antar abinda yafi kwantar mishi da hankali,yad'an shafa kanta"nagode Zaujatiii...Takawo mishi ruwa yasha,sannan yaje yayi wanka yasa kaya k'ananan wandon chinos ruwan k'asa da shirt mara nauyi fara, yazauna yana hutawa,Sudaida tabishi da kallo.

"Zaujiii...kayi kyau,sai ka zama wani d'an matashin saurayi.

Yayi yar dariya"wani saurayi kina ganin Zaujiii...gemu da k'asumbarshi duk furfura...Ni dai a ah ai bawani tsufa kayi ba gaskiya,kai dai girman kawai kake so.Sudaida ai ko girma ya zo gasu Baba ga ku ga sauran bataliyar daza ki haifamin...Yaran suka shigo da gudu dawowar su daga makaranta kenan,suka haye jikinshi suna mishi surutu.Tace"Oya to muje ku canja kaya...sai suka dad'a mak'alewa a jikin Julaibib "ku tashi mana.Julaibib yad'aga mata hannu"kyalesu sai sunyi wanka zasu canja kaya. Tagyad'a kai tatafi tacigaba da ayyukanta.

Tana aikin abincin dare Bilkisu tashigo D'akin-girkin tasha kwalliya da wata yar rigar turawa mara nauyi ruwan hoda da dogon wando da d'an k'aramin hijab ruwan hoda,tanata k'amshin arabi'an perfume d'in Julaibib fuskarta shar da kwalliya,tayi murmushi kawai dan ta san aikin shine,haka yake zama yamata wannan kwalliyar musamman idan tamata laifi tace baza tayiba,shi kuma zai rarrasheta yamata.

Tafara ta6e-ta6e irin na yara"Mama in dai tuwo za kiyi ni bazan ci ba na fad'ama Baba yace to ki mana doya da kwai da nama,kuma ki had'a mana lemun citta da karas,ni natsani tuwo tana wani yamutsa fuska.Sudaida tajuya takalleta"ALLAH Hajiya Bilkisu?Bilkisu tagyad'a kai tana sake fuska 6ata ALLAH kuwan Mama.Tayi yar dariya"Hummm wato ke dai kullum aci me dad'i ko?Kalleki kamar za ki fashe duk kin fi kowa na gidan nan ki6a,toh yau tuwon dawa miyar kuka nake yi,kuma ba lemu tuwo za a ci asha ruwa.Tad'an buga k'afa cikin shagwa6a "ni dai ALLAH bazanci wannan bak'in tuwon ba,gidan Inna zan ce Baba yakaini ai ita zata bani nama,Baba yace ni ce amaryar shi tana nufin Alhaji Abdullahi,shi kuma zai bani madara da yoghort da biscuit short cake.Tagyad'a kai"toh a sauka lafiya ni dai yau d'an gado nake yi.

Tagama kome tagyara D'akin-girkin sannan tafito tasame su yana koya musu aikin gida da aka had'osu dashi daga makaranta amma Bilkisu tanata ta6ara shi kuma yana wani lalla6ata,suka bata haushi kamar ta dake su.Bata dai kula suba itama ta zauna tana nazarin wani project...Basu gama aikin ba amma da Bilkisu tamatsa a tafi sai kawai yabiye mata taje tad'auko mukullin mota yakalleta"Megado nan da gidan Inna sai munje a mota? Tawani shagwa6e"eh Baba.Yakar6i mukullin to shikenan.

Zaujatiii...Za kije ne?Idanun ta na kan Laptop d'inta ta bashi amsa"uh uh adawo lafiya. Yakalleta na wucewar wasu yan dak'ik'u" Sudaida yakiraya.bata amsaba tad'ago suka kalli juna said yawani kashe mata ido d'aya,takauda da kai kamar bata gane me yake nufi da hakan ba.Yayi d'as da yan yatsunshi"kin ci bashi wallahi.Tagyad'a kai"eh ba kome bashi ai hanji ne yana cikin kowa,kafad'i ko nawane zan biya.Yajuya ba fashi kuwa ina dawowa za ki bani.

Tana jin barar"Allazi wahidin...tabud'e k'ofa takar6i robar almajirin tajuye mishi tuwon tunda d'uminshi dan ta san ko sun dawo shima ba wani ci zaiyi ba,wanda za taci kawai tabari,yakar6a cikin rawar jiki data murya"Iya ALLAH yabiya buk'ata duniya da lahira.

Har bayan sallar Isha'i shiru basu dawo ba, taja tsaki ranta ba dad'i abinda yake ma yaran nan yana neman wuce makad'i da rawa fa,haka Bilkisu take mata wannan iya shegen k'auri da kare in dai tayi tuwo kai bama tuwo ba ko menene in dai bata ga dama ba to baza taci ba,sai tace ita wani abu na daban take so,tana ganin ya dawo zata fara shagwa6a ita yunwa take ji Mama bata ba ta abinda take so ba...

Shi kuma sarki me Bilkisu sai yafara fad'a shifa baya so ta dinga bar mishi Megado da yunwa tunda ba ta son wannan ba sai a bata wanda take so ba? Ai Bilkisu yarinyace sai da rarrashi wata rana za ta daina,wani lokacin su shiga D'akin-girki yadafa mata abinda take so baya wuce soyayyen kwai,ko taliyar yara(indomie)ko yoghort da donut, wasu lokutan kuma yaje yasiyo musu gasassun kaji ko nama,itama mayyar naman ce haka za su zauna suci su k'oshi,shi yasa kumatu a wajenta har da na sai dawa,to ganin haka itama Walida ta ara tayafa in dai tuwo ne to baza su ciba sai dai in baya gari ta musu jan idanu shine zasu d'an tsakura su bar mata..

Ita har ga ALLAH tana ganin wannan abun idan aka d'ore a haka to za a samu matsala fa,ace kome yaro yake so sai an bashi?Haka yake so su taso su basu san babu a rayuwa ba?Wasu lokutan ko fad'a take musu sai yawani 6ata rai alamar baya son hakan duk da bai ta6a furta wa ba to amma ai labarin zuciya a fuska ma ana ganin alama,shi yasa ita kuma in dai Bilkisu ce za tace ayi kaza to baza tayi shi ba,kamar yanzu da tace atafi gidan Inna, tana son zuwa amma tace baza taba,shi dai Bilkisu bata laifi a wajen shi kome tayi,idan tafara mata fad'a sai yayi murmushi"haba Zaujatiii...Bilkisuna guda nawa take ne? Ai za ta bari wata rana.Toh yaushe ne wata ranar bayan kullum k'ara wayau take yi,dad'a sabawa da hakan take yi?Itace dai tun yana d'anye ake tank'warashi idan ya girma bazai tank'waru ba sai dai ya karye.

Dare ya farayi tayi tsayuwar motarshi, yashigo da Walida tayi bacci ya kwantar da ita ya koma yakulle gidan sannan yad'auko Bilkisu,ai yana kwantar da ita tafara mutstsuke idanu sai ta mik'e zaune"Baba ina sauran nama na?Naman ki yana nan kuje kuyi bacci dare yayi sai gobe za kici abinki ko? Tamak'ale kafad'a ni dai a d'akin baccinka yau zan kwana...

Yayi kamar baiji abinda tafad'a ba.Sudaida tayi murmushi a ranta tana fad'in"yayi kyau... Tarik'o hannunshi"Baba a d'akin baccinka zan kwana dan ALLAH.Yagyad'a kai"yashafa kanta na ji Megadona,to maza aje a wanke baki, tatafi dagudu ta d'auko brush da maclean takawo mishi, yamatsa mata taje tayi tanata tsallan murna "yau tare da Baba zata kwana, yarik'e hannunta suka tafi. Sudaida taje takwantar da Walida ta tofeta da azkar d'in kwanciya tagama abinda za tayi tanufi d'akin.

Suna kwance tamak'alk'aleshi tak'i yin bacci tana bashi labarin yan makarantarsu da Inna dasu Kawu Aminu,tabisu da kallo Bilkisu wai lallai sai ya mata tatsuniyar d'an fulani me kiwon shanu dayaje birni.Yayi hamma yasa tafin hannun dama yarufe baki yana Isti'aza"ni dai gaskiya ban iya wannan tatsuniyar ba Megadona,dan ban san abinda yayi a birni ba. Takyalkyale da dariya tana d'an bud'e idanu dan mamaki" Baba ba kace Innace Mamanka ba? Yakalleta da kulawa"eh Bilkisu itace Mamana.Yad'an yamutsa fuska"amma bata baka labari ba?To gobe zan rakaka wajenta sai tabaka labari ai muma ita take take bamu labari,har fa da tatsuniyar gizo da k'ok'i. Sudaida tace"Bilkisu surutun ya isa tashi kije ki kwanta...Julaibib yatari numfashinta"kyale ta bata jin bacci ko Megadona?Tagyad'a kai a shagwa6e"ai haka takeyi idan ba kanan wai muje mukwanta.Haushinsu yakamata kawai sai tajuya"dan ALLAH ku kwana kuna hira.

Sak'onshi yashigo wayarta"Zaujatiii... Kar kiyi bacci fa...ina lalla6atane.Takashe wayar tayi kwanciyarta"kai ka sani.Sai da baccin Bilkisu yayi ni sa sannan yabita...yakunna fitilar wayarshi yana haske mata fuska,tasa hannu takare fuskarta sannan ta bud'e idanu"Zaujatiii baki ga sak'ona bane? Na gani. Tafad'a a taik'aice...Sudaida ta kin fahimce ni amma kika share ni kina ji Bilkisu ta tasani agaba.Tadad'a gyara rufa"uh ai duk a cikin lokacin tane, yaushe ko za a bar ranta ya6aci sarauniya me D'ansarai.Yad'an daki bayanta yana matsa mata hannu a hankali"yau haka kike jin fad'ar sunan nawa D'ansarai gatsau ba ko sakayawa?Tayi shiru kamar ba da ita yake magana ba.

Yagewayeta"to gani na zo a bani bashi na... duk da ranta a 6ace yake amma bata hanashi abinda yake so ba...shima ya fahimci haka shi yasa yake jinta wata ta musamman a sararin zuciyarshi, Sudaida ba dama ne wallahi,ta gama lak'antar shi,a cikin ruwan sanyi take hukunta shi sai yazo yana bata hak'uri da bakin shi dan a zauna lafiya...Yawani narke kamar k'aramin yaro"Zaujatiii... Ina k'aunarki fa I can't do without you.Batace kome ba tacigaba da bashi wasu sak'onni sai shima ya biyema yarima su sha kid'a...

A safiyar asabar yara sun sami hutun makaranta Sudaida tamatsa sai sun tafi Zonkwa dan watanninsu biyu basu je,tagama shirinta tsafff sannan tashiga d'akin...baki bud'e take kallansu da mad'aukakin mamaki baccinsu sukeyi hankali kwance ya lull6esu da bargo,tun d'azu fa tahad'a ruwan wanka za ta musu yace tabari zai musu taje tahad'a musu abinda za suci suna gamawa sai tafiya amma shine bayan fitarta suka koma su kayi kwanciyarsu,wato sune masu idanun jin bacci ko? Tayaye bargon tana tashinsu ya bud'e idanu,ta6ata fuska "haba dan ALLAH Yaya D'ansarai kai bakiyi wankan ba,su baka musu ba?

Yaziro k'afafunshi k'asa"kin san akwai sanyi ban san sanda baccin yasake awon gaba dani ba barinje in yi...tunda yashiga wanka ta san ko ya fito bazai musu ba, dan haka tatashi Walida taje tamata sai da tagama shiryata sannan ta tashi Bilkisu tamata tad'auko shadda getzner ruwan makuba yasha aiki da zare ruwan zinare da wasu k'ananan duwatsu masu d'aukar idanu saboda kyallinsu riga da buje da d'an kwali,tana ganin kayan tawani shagwa6e fuska wai ita baza ta sa kaya irin na Walida ba wanda Baba yasiyo mata dayaje Umrah doguwar rigar larabawa shi za tasa.

Sudaida ta dafa kafad'arta da sigar rarrashi"kisa wannan kinga anko fa za kiyi ke da k'anwarki, yanzu zan miki wannan kwalliyar sai kuyi Selfie da waya ta.Walida tayi tsallan murna"Yehhh...ni ma na iya tsayuwa da shan baki a selfie,Bilkisu ta ta6e baki ita yar gata haihuwar samu sai kawai tafashe da kuka tana bubbuga k'afa ita fa dole rigar larabawan nan za a d'auko mata.Sudaida ta tsare ta da idanu"idan ban d'auko ba fa?Kawai sai ta kwanta a k'asa tana burgima tana k'ara fashewa da kuka dan ta san Julaibib zai shigo...Haushi yakama Sudaida tagyad'a kai "lallai mugun gata asara,rashin shi kwata-kwata illah...

Tanunata da yatsa"ke Bilkisu ki rufe min baki.Bilkisu tacigaba da ihu da burgima tana kiran Julaibib"Baba kazo ka d'auko min doguwar rigar larabawan daka siyo min,Mama wai bazan sa ba. Sudaida ta kifa mata mari ba za a d'auko ba... taduba yar k'aramar dorinar ta take musu barazana da ita tarasa kawai sai ta jawo wayar caja tanad'e ta a hannu"baza kiyi shirun ba ko?Ga mamakinta kawai sai tagyad'a mata kai alamar eh.Ai batayi wata-wata ba shaud'a mata iya k'arfinta caraf a kan idanunshi.

Bilkisu tagigice dan taji dukan yadda yakamata tak'ara fashewa da kuka kamar zata shid'e, ya d'auketa ya zubama wajen data shaud'a mata idanu,cajar ta fito rad'am da kwanciyar jini a wajen toh jikin hutu ko ina lukwui-lukwui da tsoka ga kuma farar fata,yakalleta fuskar shi ba wal-wala"Sudaida baki da hankali kasheta kike so kiyi? Dan tace ga kayan da take so sai yazama laifin da har sai kin mata wannan dukan?An siyo kayan dan ayi meye dasu?Ya rufeta da fad'a kamar zai daketa,Sudaida tayi shiru tana zancen zuci"wai ita ce za ta kashe mishi 'ya saboda ta daketa sau d'aya.

Tashi ki d'auko mata rigar.Takalleshi cikin idanu"na rantse da girman ALLAH ba zan d'auko ba!Yashare ma Bilkisu hawaye"to fad'a min in da take in d'auko...Cikin fushi tace"wannan rigar haramiyar ta har abadan duniya wallahi.Shima cikin fushi yajuya rungume da Bilkisu"kar ki d'auko ki dafa kici...

Sharrr...sharrr wasu hawaye masu d'umi suka zubo mata akan Bilkisu suke wannan ja-in-jar da Yaya D'ansarai?Ranta in yayi dubu ya 6aci wai shi wani irin so yake ma wannna yarinyar da har zai ga laifin ta amma yakasa tsawatar mata?Wannan makauniyar soyayyace wacce daga k'arshe baza ta haifar da d'a me idanu ba wai Zaujiii...Shine yake mata wannan hayagagar...za ta kashe mishi 'ya... tadafa rigar taci tunda baza ta bata ba...taci kukan ta ta k'oshi tayi shiru tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta...yawa-yawan Ya'yan da suke samun matsala a rayuwar su to hakan yana samo asaline daga irin mugun gatan da ake nuna musu tun zamanin k'uruciya.

Sai da hantsi yadubi ludayi sannan Walida tashigo d'akin cikin wata shiga ta daban riga da wando da k'aramin hijab yan kanti...ran Sudaida ya kuma 6aci wato fitan da yayi sababbin kaya yayafi ya siyo musu kenan? Walida takalleta"kingani Baba ya siyo mana wasu kayan?Tagyad'a kai"na gani Walida. Mama kuma na ce mishi ALLAH amfana... tad'an shafa kanta"yauwa Innarmu ALLAH yamiki albarka haka ake so duk wanda yabaki abu kisa hannu biyu ki kar6a kuma kiyi godiya...tayi yar dariya"wanda yagode sai ALLAH yak'ara mishi haka kika fad'a min ko? Eh Innarmu ashe baki manta ba.To nagode da kike rik'e duk abinda nake fad'a miki. Tad'anyi jimmm...sannan ta kalli Sudaida"Mama ita Yaya Bilkisu fa da Baba yakawo sai tace wai basu da wani kyau sai da yahad'a mata lemun tuffa da karas sannan ta yadda tasa...wai ita dai na Umrah nan take so,shine yace sai ya koma wata Umrah,damu zai tafi muje can muza6a irin wanda muke so da kanmu...

Walida... Suka jiyo muryar shi daga D'akin-shak'atawa yana kiranta,sai ta d'an bud'e idanu "Mama...Baba ne yace wai kizo mutafi na manta... tafita da gudu tana amsa kiran na shi.Takoma tayi kwanciyarta"da bata hak'ura ba baza suyi tafiyar ba kenan kome?Tayi k'wafa"wallahi abu d'aya zai sa tabisu dan tafad'a ma su Baba abinda yake yi, da ba in da za taje,gwamma ayi ma tufkar hanci,ai gabama da gabanta aljani ya taka wuta,ita baza ta iya cigaba da ganin kayan takaicin nan ba nama na jan kare.

Ko kallanta bai yiba,to itama a cikin fushi take dan haka ba wanda yakula wani har suka isa Zonkwa. Inna taji dad'in ganinsu sai ina za a saka ina za a aje takeyi da jikokinta haka suka yi wunin farin ciki.Bayan sallar magriba Sagir k'aninta daya yazama matashin saurayi takira yaraka ta wajen gyaran gashi har Julaibib yadawo basu dawo ba shima yazauna ana ta hira,Bilkisu Megadon Zinare an samu abinda ake so dafadukar cus-cus me nama da kayan lambu take ci,ga Baba ya kawo mata yoghurt tana taci tana sha cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.

Sai wajen takwas da rabi suka shigo Sagir yasake gaishe dasu Baba sannan yamusu sai da safe,ita kuma taje tayi sallar Isha'i ta zubo abinci tanaci;yad'an saci kallanta tayi kyau sosai amma ko nahiyar da yake bata kallaba har tagama ci takai farantin D'akin-girki sannan ta dawo ta zauna tad'an kalli yaran"kutafi D'akin-shak'atawa ku kalli wannan shirin na Balarabe da bai iya gaza gurasa ba...Suka mik'e da Sauri"ehhh kuwan Mama...

Tad'an sunkwui da kai cikin ladabi"Baba ina son magana da ku.Yagyad'a kai"to Sudaida... Julaibib yayi wani huci"me wannan yarinyar take nufi? K'arar shi za ta kawo wajen su Baba?Ina jinki Sudaida me yafaru?Muryar ta tafara rawa alamar zuciyarta ta karye"ni dai Dan ALLAH Bilkisu zata dawo gidan nan da zama zan had'o kayanta... Inna tace"ashsha to me yayi zafi idanu za suci wuta har haka Sudaida?Inna kusan kullum sai mun samu sa6ani da Yaya D'ansarai a kan ta,wai d'azu da safe har yana fad'a min zan kashe mishi 'ya saboda na daketa,kuma agaban idanunta ya rufeni da fad'a kamar zai dakeni,Lillahi warasulihi Inna ace kamar Bilkisu sai abinda take so za a dinga yi a cikin gidan nan?Sannan ita ba ta laifi, ba ta kuskure kome tayi dai-dai be a wajen shi, wannnan abinda yake yi ya dace da tsarin ingantacciyar tarbiyya!?

Ni dai ta zauna a wajenku kawai.Inna ta numfasa to me yakawo dukan?Sudaida duka ai baya ba da tarbiyya sai dai yakangarar,ni ma ba na son duka.Wani haushi yamamaye ta wallahi mantawa tayi kuka takawo gidan mutuwa"ai kamar yadda Bilkisu take hantar Yaya D'ansarai to haka abun yake a wajen Inna son ta take kamar me,shi yasa ba gidan da take son zuwa kamar nan dan Inna tana biye mata ne,yanzu ma abincin daren ta daban tadafa mata.

Tasa hannu ta share hawaye"shikenan Insha-ALLAH daga yau ba ruwana da duk abinda Bilkisu za tayi ai ALLAH yagani bani da wani k'arfi ne dan haka zan kyamaci kome a zuciyata.Auna had'a idanu ya gallamata harara"ai dukan yayi yawa ne har ciwo kika ji mata to me zaisa bazanyi fad'a ba.

Baba yayi tsaiii...yana nazarin kalamansu d'aya bayan d'aya,yakad'a kai"Maimunatu wannan hukuncin na ki na adalci ne kuwa?Tsakani da ALLAH Sudaida ta fiku gaskiya;kar k'aunar yarinyar nan tarufe idanunku fa,idan an ciza to yakamata a hura...yanuna Julaibib"Malam D'ansarai da ilminka da girmanka amma kana irin wannan abun?Kiwo aka ba ka game da sha'anin Iyalinka fa,shi itace tun yana d'anye ake tank'warashi...kana nunama Bilkisu tsananin gata amma ba kwa6a to an yi ba ayiba kenan...an 6ata goma biyar bata samu ba,dan me za tayi laifi ba za a hukunta taba?Mahaifiyar tace fa idan ba a nuna mata abinda takeyi kuskure ne tun yanzu ba,to a gaba ma cigaba dayi za tayi,kuma duk fad'an da zaka ma Sudaida to na rok'eka da girman ALLAH kadaina yi a gaban Ya'yanku,hakan yana gur6ata tarbiyyarsu,dan ALLAH Malam D'ansarai idan rai ya 6aci to bai kamata hankali yagusheba kaji ko?

Yanuna ta"ke kuma Sudaida ba ke za ki yanke hukunci na rad'in kan ki ba kome ya miki,tunda shine ubansu shine a hakku a kansu dan shine shugabanku ke da yaran gaba d'aya.Ubangiji ya muku albarka,sannan duk yadda ranki ya6aci kiyi hak'uri dasu kinga banji dad'in furucinki akan Bilkisu ba,ke uwace bakinki amsashshene akan ta,dan haka ki janye wad'annan kalaman na ba babu ruwanki da duk abinda za tayi,ai kece kuwa me ruwa da tsaki yaushe za ki biye ta wani D'ansarai Ya'yanki kadararki su shiga garari,duk abinda ya kumayi ki bugo waya ni dake ki fad'a min zai sha mamakin yadda zanyi wallahi ALLAH kinji na rantse ko?

Kalaman Baba sun tausashi zuciyarta"to Baba nagode ALLAH ya k'ara girma.Inna ma tajijjiga kai toh na gano kuskure na kiyi hak'uri Sudaida ALLAH yamuku albarka,ku tashi kitafi gida dare yana dad'a yi,ta lek'a D'akin-shak'atawa duk sun yi bacci Inna tace suyi tafiyarsu kawai.

Suna zuwa gida taje tayi wanka tayi kwanciyarta shi kuma yatafi D'akin-girki zai dafa shayin na shi na fama taja tsaki sai kaje kayita sha...takwanta cikin tunanin tsohuwar soyayyar su..ita dai ta san da son Julaibib ta girma kuma ba tajin da wani abu dazai rage k'aunarshi a sararin zuciyarta,to amma wannan yawan sa6anin da saka fara samu ita tata k'arfin k'aunar ta zuciyarshi ce ta koma kan Bilkisu da kuma kud'in da yakeji yayi?Ko kuma giyar Ilmi da dukiyace tafara bugar dashi...!?

Tad'auki wayarta takira"Umma kiyi hak'uri na kiraki da daddaren nan wata magana nake so muyi.Ba kome me yafaru ne?Hawaye suka zubo mata"Umma ni da Yaya D'ansarai ne...sai kawai tafara kuka,Umma bata hanata kukan taba sai da taci ta k'oshi tabari dan kan ta...Umma tasauke numfashi "Sudaida kiyi hak'uri ni bazan shiga tsakanin ki da D'ansarai ba ai kunfi kusa,kuma ai ba a ta6a zaman tare ace wani bazai sa6a ma wani ba...fuskantar matsalolin aure irin wannan ai dole ne dan haka ki k'ara hak'uri kuma ki yawaita addu'a kome yayi farko yana da k'arshe...kuma in dai akan Bilkisu ne to fa dole sai kin kawar da kai...ba kome za ki nuna ya dame ki ba...ki dai kiyi k'ok'ari ki jata ajiki kinga ai tafi shak'uwa dashi ko? Eh Umma...to ko ni nan a yanzu nagano wasu kura-kurai danayi game da tarbiyyarku to amma har kwanan gobe ina godema ALLAH ina godema Mama wacce ba dan ita ba da kuma kun samu tasgaro dan haka ki natsu ki san abinda kike yi game da sha'anin tarbiyyarsu...

haba Sudaidan D'ansarai kika juya shi yayi wasu abubuwan da bai so ba sai kuma wannan za ki fara raki? Ki bi dashi ta siyasar rayuwa ko bai daina wasu abubuwan ba to amma ai za ki samu sauk'in wasu,Umma tad'anyi murmushi"taurin kan Bilkisu da kafiya kema fa haka da kike k'arama kinyishi,shi yasa bana miki da wasa...ita kuma sai abun yahad'u mata da gata...

Julaibib yashigo lokacin suna sallama da Umma.Yakar6e wayar"k'arata kika sake kaiwa,me kika fad'a mata?Abinda kunnuwanka sukaji.Yayi murmushi"ALLAH ko?Tajijiga kai"bawai...yashiga rarrashi"kiyi hak'uri Sudaidan D'ansarai ni ma na gane kuskure na,bai kamata ace Bilkisu ce zata shiga tsakanin muba,ai tare tazo ta ganmu,lallai ke macen albarka ce dakika jajirce dan ganin

Please Login or Register in order to submit comment