Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A'isha tace kaza da kaza game kai,sai dai bazai iya tuno me take fad'a d'inba, dan ba itace a gaban shiba,shi dai bai san tana sanshi ba,dan ko Sudaida bata ta6a fad'a mishi wai A'isha tana san shiba, kila Musaddiq d'inne kawai yake san had'awa.


Sallar a zahar Julaibib yayi yagama azkar d'inshi sannan yafito daga masallacin makarantar,yau ba ayi wani karatun kirkiba saboda Inter-House ya kusa,ga dalibai nan sunyi rukuni rukuni na irin abinda suke so, suke dad'a yin gwaji (practice)yajingina da bishiyar giginya tare da rungume hannayanshi a kirji yana kallan Sudaida yadda take d'aga mulmulallan bak'in k'arfen discus da yadda take jefashi cikin k'warewa da nishad'i a bokan wasanta suna mata tafi wasu suna mata ihu dan tanayi yadda yakamata.Yayi murmushi yatuna lokacin da yake makaranta yayi wasannin kala kala,wasan kwallo ne bai ta6,a burgeshi ba wannan sai Musaddiq,saboda kwazanshi a fannin wasannin shine yarik'e shugaban wasanni na lokacinsu (Game Prefect) yakalli Khausar sune yan Javelin, Nasmat kuma ana bangaran Long jump. Yabar jikin bishiyar yana tafiyarshi cikin natsuwa har yaje Staff-Quater zai kar6i wasu littafai a wajan Mr Julius.

K'arfe uku tanayi yasake komawa filin wasannin da Nasmat yafara cin karo yace"Ke idan ba zaku tafi gida bane ni kunga tafiyata.Dan ALLAH kajiramu barin kirasu tayi cikin filin da dan gudunta.

A mota suka sameshi ya musu wannann rikitaccen kallan nashi Sudaida tabud'e baki za tayi magana yanu nata da yatsa"kul naji bakinki.Tad'an harareshi ta zauna tana turo baki gaba.Yaja tsaki"kunje kun shagala da wasanni ko sallar azahar ma baku yiba ga la'asar ta kusa,kufa kuna da ka'ida da bambanci tsakanin ku da wad'anda dama basu san kome ba sai duniyar, wallahi idan lokacin sallah yayi banga mutum a masallaci ba gobe...yayi kwafa, Nasmat tace"shi fa wannan Game Master muguntar shi har tafi ta Discipline Master.Ke tafi can shi ai ba makaho bane yana ganin k'atan masallaci ai a makarantar,na kuma tabbata da kun fad'a mishi sallah za kuyi bazai hana kuba,ai kowa ya san duk inda musulmi yake ba a rabashi da sallah,sai dai in sallarce bata dame shiba...Yaya D'ansarai... yatari numfashin ta"ke ba nace kar inji bakin kiba?Tasunkwui da kai"wannan mutumin wallahi yanada matsala,tafad'a a zuci,tad'anja tsaki. Nasmat takalleta"ke Sudaida tun d'azu kiketa k'unk'uni abin harda jan tsaki ke da wa? Shiru ma amsace.

A k'ofar gidansu yatsaida motar bai k'arasa dasu gidansu kamar yadda yasaba ba,yakashe motar yafito yashige gida.Sudaida itama tabud'e bangarenta tafito tana masifa"aikin banza sammakon gaida makiyi,aiko ba a motarka zamu dawo gida.


Aminu yana hangota yafara dariya"ke fa Sudaida naga alama raguwa za a yi.Ta turo baki gaba "Yaya Aminu me nayi to? Kinga fuskarki kuwa?Gaskiya yunwar makaranta ba ta dad'i har na tuna lokacin da mukayi makaranta a Bauchi.Yad'an kalleta kinsan yau me su Mama sukayi a gidan? Tagirgiza kai "Tuwon shinkafa miyar shuwaka"Sai kawai tad'ora hannayenta aka"Wayyo ALLAH! ni gaskiya yau ana ta 6ata min rai.Suwaye suketa 6ata miki rai?Takaryar da kai gefen dama ta marairaice "Yaya D'ansarai da su Mama,wallahi gidan Hajiya zan tafi ina canja kaya,dan bazan mutu da yunwaba.Yamik'a mata wasu nannad'ad'd'un carbon paper,Top-bond,babban pensir HB dawasu k'ananan tarkacen zane-zanenshi(Artistry Euipment) to tafi min dasu gida,yanzu haka Bakin Gogi zan tafi wani aikin signboard zanyi.Tasa hannu biyu takar6a "Yaya Aminu ALLAH yatsare.Amin Sudaida suka daga hannayensu suna ma juna adabo,sukayi murmushi sannan kowa yajuya yacigaba da tafiyarshi.


...Dare da rana suna aiki tuk'uru a kanmu,to muma kamata yayi mu zage dantse muyi aiki tuk'uru a cikinsu.Ubangijinmu kabamu rabo me amfani fid-dunya wal aakhirah.


21 Rabi'a Thani 1441
18 December 2019


We Ibrahim' Daughters 👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.




DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}




Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFIđź’”



Almost true story
Daga alk'alaminđź–Š
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)


Shafi na shida.



Da yammacin juma'a jikokin Hajiya sun cika gidan,tun daga zaure za ka fara jiyo hayaniyarsu sun tasata a gaba da shak'iyanci. Sudaida da Nasmat suma suka shigo,suna k'are mata kallo tasha had'ad'd'an leshin auduga ja da k'ananan fararan duwatsu,wuya,hannayenta, da d'an kunnanta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi. Suka kalli juna suka k'yalk'yale da dariya"Hajiya manya wannan irin cakarewar k'uda a gefen gyambo?inji Nasmat. Sudaida tagyad'a kai "Gaskiya kin had'u saura had'uwarki da ALLAH, wannnan k'ure adaka haka?To dawalakin goro a miya,bazawarin tane zai iso da yammacin nan. Gaba d'ayansu suka kuma k'yalk'yalewa da dariya, abinda yahanasu jin abinda Hajiyar take fad'a.

Aminu yashigo sai suka sa ihu da tafi "Yehhh... gashinan, gashinan shine bazawarin data k'urema adaka.Yakama ha6a🤔 wai wai wai, ai kowa ya san Hajiya ba dani take yiba,dan ta san ni bazan juri al'alarta na bani bani kamar mak'ogwaro kullum a bashi ba,bani da wannan hak'urin,kusa idanu anjima kad'an za ku ganshi. Khausar tace Alkasim ne.Aminu yace gajan hak'urine dake koma wanene za ku ganshi. Yamatsa wajan Hajiyar suna maganarsu.

Sudaida tafara shak'o k'amshin turarenshi da iska takad'o mata kafin tayi magana yashigo yana musu wannnan rikitaccen kallan na shi"ku wallahi kun cika hayagaga bud'ar kan karya,sai kusama mutum ciwon kai.Sudaida da dama takejin haushinshi tace"sai dai dama can mutum da ciwon kanshi yashigo,kace kawai a baka magani za kasha. Suka k'yalk'yale da dariya.

Nasmat tace"su autan Inna manya, kace kawai kazo tad'i wajan Hajiya kuma katarar mun tare inda za ka zauna.Sudaida tad'anja tsaki tana mishi kallan sama da k'asa yana cikin fararan kaya yayi shar dashi"Kuma wai haka zai zo hannu rabbana"Yatsareta da idanun shi"ke yarinyar nan wai meye damuwarki da ni ne? Yanunata da yatsa"za fa kisha na jaki,idan baki daina shiga harka ta ba.Ta turo baki gaba"Indai aka k'i jininka ko ruwa kafad'a sai a ce ka tada k'ura,ni kad'ai nayi magana?Ni kamayar marainiyar wayon ka ko?Tahaye gadan Hajiya tana k'unk'uni. Hajiya tace"kai Julaibib yi tafiyar ka anjima sai kadawo muyi hirar mu cikin dad'in rai,lokacin duk sun kama gabansu.Yayi murmushi yana kallan Sudaida data juya musu baya.

Sudaida...

yakirata.Sai tamishi kunnan uwar shegu.Ke Sudaida ba kiranki nake yiba? Hajiya tasa baki"yau na ji yarinya ba dake yake yiba?Shiruma amsace. Hajiya tashiga tafa hannaye da sallallami.Yad'aga mata hannu"kyaleta Hajiya na jaki kawai zata sha.Eh gwamma haka tunda abin nata tsiyane d'inkin ludayi.Yace"ke Asma'u d'auko min bulalan can.Tana jin haka tafara"Ihu sai tajawo k'atan bargon Hajiya ta duk'unk'une aciki.Yayi murmushi "k'aramar mara kunya kawai,fito a cikin bargon kika yadda zan miki walmukalifatu "wallahi bazan fito ba.Yama Hajiya sallama sai bayan sallar Isha'i zai dawo.

Suna hirarsu da Inna tasako mishi maganar A'isha.Yasunkwui da kai tad'anyi murmushi dan ta san halinshi indai yayi haka to zaiyi wuya yayi magana.Kaga kwantar da hankalin ka niba dole zan maka ba,munyi magana ta fahimta da Musaddiq nima banga aibun taba shawara kawai nake ba ka, kanemi auran ta Insha-ALLAH ba kome sai alheri amma fa karka takura kanka idan ba ka so,dan aure ba abin wasa bane zamane da ake fatar yinshi har k'arshen numfashi.Yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi sannan yad'ago cikin natsuwa ya kalleta "nagode Inna ALLAH yak'ara girma na kar6i shawararki da hannu biyu.Tayi murmushin jin dad'i "Ubangiji yamaka albarka ya taimaki rayuwarka. Amin Innarmu.

Wannan makon ya so zuwa wajan A'isha to amma bai samu sarari ba saboda sun gama TP(Teaching Practice)sun koma makaranta. Sai bayan makonni biyu sannan yasamu yashirya ranar juma'a cikin shigarshi ta fararan kaya kanshi da farar hula zita.Yana shiga lungun gidan yahango ya'yan gidan maza suna wasan Hockey.

Nasir abokin Abdul yana hangoshi yak'arasa wajanshi yana dariya yace "Kawu" kamar yadda yaji Abdul yana fad'a "yau kaine a k'ofar gidanmu? Ko kazo gaishe da Mamanmu ne?Yagyad'a kai"eh nazo gaisheta ne amma ba shiga zanyi ba ka gaisheta zamuzo da Musaddiq na musamman mu gaisheta.Yayi tsallan murna"to zan fad'a mata.Aisha tana ciki? Julaibib ya tambayeshi.Eh tana ciki inkira maka itane?yagyad'a kai. Nasir yashige gida da gudunshi yana k'wala kiran sunanta.

Tayi mamaki tare da k'aryata Nasir.Nasir yafara rantse-rantse da gaske ne yana k'ofar gida.Tarik'o hannunshi "To muje ai ba a k'arya kusa da gida,amma na rantse da ALLAH idan ba shi bane?tayi kwafa wallahi ka san sauran"Eh na yadda.Kanshi a k'asa kamar yana k'irga tsakuwan da suke yashe a wajan.Sai tasaki hannun Nasir da yake mata dariya ai dama na fad'a miki,yajuya wajan wasansu.

Yaya Julaibib...

Tafurta sunan kamar tana cikin shakkar shi d'inne ko wani me kama dashine?Yad'ago yad'an kalleta"na'am A'isha... Wani murmushi ya su6uce mata "ALLAH da gaske kaine a k'ofar gidanmu? Lallai yau farar rana ce me kyakkyawar suna "Juma'a.A mutunce ta gaishe shi,sai tayi shiru dan bata san abinda yakawo shiba.Shima shirun yayi na wucewar wasu dak'ik'u.Yad'an sake kallanta "na zo gaishe kine,inafatar banyi laifi ba?Tagirgiza kai"wani irin laifi? Gaskiya nagode da wannan ziyara ALLAH yabar zumunci. Ina Yaya Musaddiq? Ya tafi Kaduna.Hirar tasu jefi-jefi,bai wani dad'e ba yamata sallama yatafi.

Tabi bayanshi da kallo har yasha kwanar lungunsu ya bace ma ganinta tana tsaye a wajan cikin mamakin ganinshi a k'ofar gidan su,kuma wai wajen ta yazo dan sada zumunci, tasake juya kwalban turaren arabian perfume d'in daya bata,tabud'e tashaki k'amshin me wani irin dad'i,bata zata za suyi magana irin na yau ba,dan sunsha had'uwa ta gaisheshi amma sama-sama yake amsawa.Ashe dai Sudaida gaskiya take fad'a mata,Yaya Julaibib fa yana da matuk'ar kirki,shi kawai baya san a dameshine,kuma baya san magana da yawa. Tajuya zuwa cikin gida ba tare data kawo kome a zuciyarta game da zuwan shiba.

Bayan Musaddiq yadawo suka tattauna. Musaddiq yakad'a kai"gaskiya da ka sani kafad'a mata dalilin zuwanka"ai da zafi-zafi a kan daki k'arfe.Yagyad'a kai na fahimceka nagode yamik'a mishi hannu sukayi musafaha.

Ranar juma'a data zagayo yaso kwarai yaje wajan A'isha d'an yafad'a mata kome,to amma hakan shi bai tadda ruwa ba" dan sun fara jarabawa me zafin gaske,ba wanda yakoma gida dan itace jarabawarsu tak'arshe a College Of Education Gidan-Waya,sai kuma a zauna zaman girbe abinda aka shuka.ALLAH yaba me rabo sa a.

Lidiya tabita da kallo ita da d'akin, dan ta had'a k'aramin hazo ne da hayak'in taban da take ta zuk'a, takalli Ash-tray d'in da take karkad'e tokar guntayen taban data zuk'e,sai tazaro idanu da mad'aukakin mamaki,"Eh ta san Kasham tana shan taba amma sai ran ta yayi mugun 6aci,kuma bai wuce tasha kara uku ba,amma yau bata san ko kara nawa bane,tamatsa jikin taga tad'aga labulan tare da bud'e gilasan,hayak'in da gauraye d'akin yafara raguwa.

Kasham...

Lidiya takirata,tad'ago tana kallan ta manyan idanunta masu maik'o sun kad'a jawaur fuskarta har ta kumbura saboda kukan data sha bana wasa bane.

"Inzayadami Kasham?(Kaham me yafaru)

Shar...shar...wasu hawaye masu d'umi suka fara sintiri a kyakkyawar fuskarta"Kasham...dasauri ta d'aga ma Lidiya hannu "Don't dusturb me!

Lidiya tagyad'a kai,tarungume hannayenta a k'irji tana kallanta,Tabud'e dirowa tana dube-dubenta "oh no dammed it"ta dunk'ule hannu ta naushi iska,da alama bata ga abinda take nema ba,takoma ta zauna tasake kunna taba, tabi taban da kallo da tunanin yadda karan zai kare a zuk'a d'aya,takai baki tamata wata irin zuk'a data kusa tafiya da numfashin ta,nan take kuma tari ya sark'afeta.

Tari tadinga yi kamar na shika, abin har yaba Lidiya tsoro ta kamo ta suka fito waje dan tasha iska. K'irjinta yana mata wani irin suya,mak'ogwaranta ya bushe k'amas kamar miyau bai ta6a bi ta wajan ba. Tad'ago a galabaice takalli Lidiya" ruuwa.Lidiya tagyad'a kai"o barin siyo miki,tana k'ok'arin jinginar da ita ajikin bango dan ta fara wata irin shakuwa abinda yadad'a rikitar da Lidiya kenan.

Hey...please come and help meee...!!!

Yadda akayi furucin cikin yanayin tashin hankali da tsoro yasashi waiwayawa inda yajiyo sautin. Tasake yafito shi da hannu... Tabbasss ko su wanene wad'ancan taimako suke nema sai yatafi wajen.Bai gane Kasham da Lidiya bane sai da yakusa k'arasawa inda suke yaji Lidiya nafad'in ban san me yashiga kwakwalwarki da zaki karar da karan taba a zuk'a d"aya ba, gashi nan za kije ki kashe kanki abanza...wani irin abu yaji da yabi ilahirin jiki da zuciyarshi"Kasham kwance wanwar a k'asa,farin wandan legging d'inta yayi dabbare-dabbare da k'asa...

Dan ALLAH ka taimake mu karta mutu,har lokacin tana dafe da k'irji tana wani irin numfashi,gefe da gefen fuskarta busassun hawayen wahala ne,idanunta suna rufewa da bud'ewa bak'i ciki yana 6acewa.

K'amshin arabian perfume d'in data shak'a yasa tad'ago dak'yar takalleshi...sai tamik'a mishi hannunta na dama.Tausayinta yakamashi dan tana cikin wani irin mawuyacin hali,wallahi mutum ba a bakin kome yake ba"Ubangijiđź‘Źkamana kyakkyawan k'arshe.D'azu- d'azun nan yahango su,da yan course d'insu sunci kwalliya mazansu da matansu suna ta hotuna suna hayaniyarsu ta dandazon d'alibai.

Sai da ya durk'usa sannan ya tabbatar lallai tabar tasha dan gaba d'aya warin ta takeyi"me zan baki ne?Dak'yar tayi furucin"ru.rr... ruwa...yabud'e ragowan ruwan swan d'in daya ke hannunshi.Ya waiwaya inda Lidiya take durk'ushe dan ta taimaka mata ta tashi, amma bai ganta ba.Sai kawai yad'agata ta jingina da bango, yamik'a mata ruwan.Saida tashanye shi duka sannan ta sauke gwauran numfash."Sannu...Yace mata da yana yinshi na natsuwa"Kwallah suka cika idanunta,inama inama ace sunyi aure ne yake bata wannan kulawar?Bata ta6a zatan D'ansarai zai taimaketa idan ya ganta a mawuyacin yanayi ba,saboda halin-ko-inkulan da yake nuna mata.

"Kasham...yakira sunan ta.Tad'ago tana mishi kallan k'auna me cike da shauk'i,wallahi kasancewar su a tare,sai ta jita garas...kamar ba ita bace a mawuyacin hali d'azu ba.

Haba Kasham kina mace me kima, amma ace kema kina k'arama sama hazo?(shan taba) abin nan ya bani mamaki fa,ga ki da ilmi kina kuma ganin abinda su masu yin tabar suke rubutawa ajikin kwalin"Mashaya taba suna iya mutuwa da k'uruciyarsu"haba Kasham meye amfanin shan taba sigari ne?Kina sane da "nicotine"gubar dake cikin taba ba karamin jazama hunhu matsala yakeyi ba.Dan ALLAH... yahad'a tafukan hannayen shi 🙏alamar magiya kamar yadda take mishi "Ki daina shan taba sigari dan babu kome a cikinshi sai illah.

Wata irin k'auna da soyayyarshi ta dad'a mamaye zuciyarta"Oh God...ALLAH kamallaka min wannan bawa na ka.Tajijjiga kai "shikenan D'an Sarai nagode,na kuma maka alkawari ko muna tare ko bama tare, na sha taba na k'arshe a rayuwata,daga yau d'in nan na barta har abadan duniya.Yad'an saki fuska"yauwa Kasham.Ungwai bu gangan(Kasham nagode sosai) dakika kar6i nasiha ta.Tad'an zaro idanun ta"kaii dama kana jin yarenmu?Saita kyalkyale da dariya dai dai da dawowar Lidiya da roban ruwa swan.Sai kuma tayi saroro cikin mad'aukakin mamaki "wannan me shegen girman kan dama d'azu takira?Lallai hankali ke gani ba idanu gululuba.Shima mik'ewa yayi bai sake magana ba yajuya yayi tafiyarshi.

Tadinga binshi da idanunta har sai da yayi nisa ya6ace ma ganinta sannan tamik'e tsaye itama tana yar dariya,wallahi wani irin nishadi ta tsinci kanta a ciki, takad'a kai" ALLAH dai yakai damo ga harawa ko bai ciba yayi burgima.Dama duk tunanin rabuwa dashi ne yajaza mata 6acin ran daya sa ta dinga k'arama sama hazo na rashin hayyaci.

Lidiya taja dogon tsaki "mahaukaciya kawai, ya gama zaginki ke kuma kamar wata wawuya kina jin dad'i.Wani murmushin yasake su6uce mata"karki d'auki alhaki dan D'ansarai bai ta6a zagina ba,bare kuma yau da yamin nasiha,na kuma kar6eta da hannu biyu. Lidiya ta jefeta da ruwan swan d'in rubbish girl.Dasauri tacafe ruwan tana dariya"kanki akeji Lidiya...


Haka nafi so an cema makaho je ka ka gani.


23 Rabi'a Thani 1441
20 December 2019


We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.






DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in

...GWAJIN DAFIđź’”

Almost true story
Daga alk'alaminđź–Š
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na bakwai.


Kasan mafarkin danayi daren jiya kuwa? Musaddiq yagirgiza kai.Wai Julaibib ne da Kasham suke kiwon shanu a wani k'aton fili iya ganinka me cike da koren ciyayi.Musaddiq yakyalkyale da dariya"D'ansarai fulani ka koma har matarka take taya ka kiwo saboda tsabar k'auna?Musaddiq da Maimun d'in da yayi mafarkin suka kalleshi yana zuba d'anyan na'a na'a, d'anyan citta da ya'yan algarib a ruwan shayin da yake dafa musu,zuman da suke shan shayi ya k'are,sai yazuba sikari d'an kad'an dan dukkansu basa san zak'i,yamaida murfin tukunyar yarufe,yayi kamar baiji abinda suke fad'a ba.

"Julaibib.

Maimun yakirashi.Yajuyo da saurinshi yana amsawa"na'am.Bakaji abinda nafad'a bane? Shiruma amsace.Yad'auki wasu kud'i a saman tebur yamik'a ma Musaddiq "Malam tashi ka kar6o mana biredi.

Cikin natsuwa yake tafiya dawowar shi kenan daga gidansu A'isha amma cikin rashin sa a yatarar wai sunyi tafiya,ya dai barma Nasir sallahu idan ta dawo yazo yafad'a mishi.Sudaida tana hangoshi tafara murmushi dan ta kwana biyu bata ganshiba,jiya da akace ya zo, taje ta gaisheshi bata jeba.

"Yaya D'ansarai sannu da zuwa...

Iskar data d'ibo tama bai kalla ba bare yasan ALLAH yayi ruwan tsiranta.Ita da Sinan d'in daya ke shirin yimishi sallama suka bishi da kallo har yashige cikin gidan.Sinan yakad'a kai"Julaibib sai a hankali.Suka gama hirar su sukayi sallama.

A D'akin-girki ta tarar da Mama.Mama tace yauwa d'auki abincin nan ki kaima D'ansarai.Haushinshi takeji ta turo baki gaba"Mama shi yace miki yana jin yunwa?Mama tabita da kallan mamaki,sannan tamata dak'uwa gidan ku"Sai yace yana jin yunwa za a bashi abinci a gidan nan?ke wace irin yarinyace?Jiyama danace kiji ki gaisheshi ashe ko bakije ba,saida zai tafi yake tambayar ki sai Sagir ne yace kina d'akinku kin kulle k'ofa.Sa an kine D'ansarai? Tad'auki abincin tabar Mama na mata addu'ar shiriya.Dak'yar tayi sallama dan tasan idan ma bata yiba,sai ya korata ta yishi.Ko kallanta bai yiba har ta ajiye abincin tajuya.

Umma tashigo D'akin- shak'atawar dan lokacin da yashigo tana sallar.Yagaisheta cikin girmamawa.Tayi murmushi"D'an Sarai yaro ne me hankali, yasan ya kamata sosai"Karatu ya k'are sai jiran sakamako ko?To Ubangiji yabada abinda ake nema.Yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi."amin ya rabbi Umma". Tamik'e to bakaci abincin ba?Yakalli kwanon abincin"ai ni ban san ni takawo ma ba,dan a jiyewa tayi tafita.Kai kawai tagyad'a tafita.

Tana cin na ta abincin Umma tasa meta batace kome ba hannunta kawai ta damk'o,rik'on data matane yasa tasan cewa lallai bana wasa bane"Umma me nayi?Bakiyi kome ba ko?Sai tafara tirjewa dan wallahi idan ta yadda Umma takaita d'akinta to na jaki zata sha ba kad'an ba dan Umma ba sauk'i,shi yasama ba ta wani wasa dasu akwaita da zafi,sam ba ta d'aukar rashin kunya shi yasa kowa yake shakkarta a gidan,yana yinsu ba d'aya bane da Mama,da wasu lokutan suke maida ita kamar wata kakarsu,sai tazo ta tsawatar musu suke daina wani abun.

Umma dan girman ALLAH kiyi hak'uri na tuba nabi ALLAH na biki,kiyi ha...saukan marin yasa sauran kalaman suka mak'ale. Idanunta suka ciko da k'wallan wuya, dan marin ya ratsata yadda yakamata.Tasa ihu Mama dan girman ALLANMU zo ki ceceni,wayyo ALLAH! Ke...!Umma tace tana kallanta cikin zaro idanu "rufemin baki ke mara kunya ko?Ai ina jinku da Mama a D'akin-girki..Umma dan darajar Annabi Muhammadu kiyi hak'uri.... Mama wai kina inane?!

Mama tak'araso

Please Login or Register in order to submit comment