Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun cika idanunta"a ah ka tsaya kawai hawaye masu d'umi suka zubo mata sharrr...Lafiya kike kuka kuma? Tagirgiza kai inafa lafiya Yaya Musaddiq na shiga rud'ani,zuciya ta tana min zafi, tunani na yana shirin rikicewa.Saboda me? Musaddiq ya tambaya cikin mamakin kalaman ta.Saboda soyayyar mutane biyu"wa zan za6a?Takad'a kai cikin takaici"Kaiyah...Yaya Julaibib bakamin adalci ba,kaci amanar k'auna.Yakalli Julaibib sannan yakalleta"banga ne ba kamar yaya Aisha?Ta share hawayan da suke gudu a fuskar ta sannan tamik'e tsaye"Na so Julaibib amma dole tasa na hak'ura saboda banga fuska ba,kwatsam kuma sai ga ku da tayin soyayya a lokacin da yariga yak'ure. Musaddiq yad'an kalleta kin daina san na shine? Ko d'aya har yanzu ina san shi to amma ya zanyi?Akwai alk'awarin wani a kaina.

Yaya julaibib ka ci amanar k'auna, kwarai na so ka,kai ka k'i bani goyon baya. Aisha ki taimake mu.Takalli Musaddiq da mammaki kamar yaya?Eh ni a ganina lokaci bai k'ureba tunda ba auran aka d'aura ba, gashi kin tabbatar da bakin ki kina san shi,amince mana kawai kome zaizo gidan sauk'i,su Baba zasu shiga cikin lamarin.Julaibib yana sanki,za kuyi zama cikin amana...ta tareshi da sauri"haba Yaya Musaddiq wannan san kai da yawa yake, me yasa kake aran bakinshi wajan cin albasa? Kai ni nama game ba wani so na da yake yi.A ah Aisha karki fad'i haka dan Julaibib ya zo wajanki ba sau d'aya ba ba sau biyu ba to a tunaninki zuwan me yake yi? Sada zumunci,ziyarace ta sada zumunci,kullum haka yake fad'a kuma haka na da'uki zuwan na shi.To Aisha....

Julaibib ya katse shi"kar muyaudari kanmu Musaddiq,neman aure akan neman aure haramun ne a musulunci,ni na yadda da hukuncin Ubangiji duk abinda ba ka samu ba to dama can rubutacce ne tun daga lauhul-mahfus ba na ka bane.Yad'an kalleta Aisha ina miki fatan alheri da dacewa a gidan aurenki.Yarik'o hannnun Musaddiq yamata sallama sukayi tafiyarsu.Tabisu da kallo har suka 6ace ma ganinta.wata sabuwar soyayyar shi ta dad'a mamayar zucyarta.Hashim ma yafad'o mata, shima tana kaunarshi da wata irin soyayya ta daban. Tagyad'a kai"lalalai wannan muk'addari ne"rabon kwad'o baya hawa sama... Tad'an cije le6enta na k'asa sannnan ta juya zuwa gida..

Da daddare bayan sun gama cin abincin dare ya fad'a ma Iyayanshi kome game da Aisha.Sukace ba kome sai a nemi wata.Ya amsa cikin ladabi Insha-ALLAH.


Danbarwa me yawan gaske akayi tsakanin Kasham da Baranzan kafin ya yadda ya tattara kome na shi yabar gidansu tare da alk'awarin tunda tak'ishi saboda wani tsinanne to ko ba jima ko ba dad'e shine nan yanuna kanshi da yatsanshi shine zai zama ajalin Julaibib. Yanunata da yatsa"ni nake fad'a miki wannan maganar ki rubuta ki ajiye.Idan ka kashe shi ba tare da ya maka kome ba shari'a ai ba kyaleka za tayiba,kaima zakabi bayanshi ne.

Tabi k'ofar da ake ta kwankwan sawa da wani malalacin tsaki tadad'a d'ora kanta ajikin matashin "Yes come in"suka shigo sama da k'asa take musu wani kallan uku ahu.Sisters ne su biyu "menene?Cikin d'oki me rik'e da madaidaicin kofin silver tabud'e murfin sannan ta mik'a mata"Shekaran jiya Reverend Father yadawo daga Jerussalam(Darussalam)to jiya Pastor yaje mishi ban gajiya shine yabashi Holy Water(Ruwan Zamzam)me yawa anba kowa ya sha,ke kuma bakije majami'a ba shine aka d'iban miki ta ajiye kofin a gaban ta.Tamik'e zaune da sauri daga kwanciyar da tayi,tasa k'afa ta ture kofin.Kafin suyi wani yunk'uri ruwan yabi carpert d'in d'akin.Suka bita da kallo cikin mad'aukakin mamaki"Kasham Holy Water ne fa?Tawatsa hannaye cikin halin-ko-in kula"dan Holy Water ne sai me?Suka 6ata fuska gaskiya baki kyauta ba.Tagyad'a kai "to sai a yanke min hukunci.Suka juya har sun kai k'ofa d'aya ta juyo"mun manta Pastor yace mu fad'a miki anjima ki shirya za ku tafi a miki baptismal.

Taja dogon tsaki"Allah suturi bukwui inji kishirya k'onanniya" Ku fad'a mishi bana so dan haka ba inda zani wallahi.Takalleta na wasu dak'ik'u Kasham da kinyi hak'uri an miki kinga ran...Cikin hayagaga da tafasar zuciya tamik'e tsaye"na ce bana so,to a kyaleni ko ana dole a rayuwane? Daku dashi kuje kuyi baptismal d'in ko ba daku suke fornication d'in ba?"Get lost dan abu kazan ubanku,get the hell out of my room tanuna musu k'ofa yan iska kawai kuje kuji dana ku zunubin"dan nace ina san D'an Sarai shi kenan sai yazama zunubin da har sai anyi baptismal (wankan tsarki)?Ko wani abune yazama zunubi? Za su sake magana tayi wani ihu ta buga tebur d'in tsakar d'akin sai da littafin kai suka zubo k'asa"now get out dan abu kazan uban ko wace shegiya!.Suka fita ka me da ha6a🤔lallai Kasham ta ci kai(hauka)dole ko a mata wankan tsarki ko za ta samu lafiya.

Tafad'o gado cikin takaici da damuwa da kuma matakin d'auka.Ba zato wani tunani yazo mata.Tamik'e da sauri har tana bugewa da katakon gefen gadan,tayi tsalle tana wani ihun jin dad'i"Halelujah...Diary d'inta ta d'auka tayi waje da gudu hurrayyy.

Babanta tasamu yana zaune a inuwar barankaci yana sauraran rediyo a cikin shirin tambayoyin addinin kirista.Tazauna a gefen shi cikin walwala,yabita da kallo ba Pastor yana kiranki bane?Tayi yar dariya "Ba kirana yake yiba ya dai cene a fad'amin gobe da yamma inshirya za a min baptismal d'in.Yagyad'a kai Ohooo. Yacigaba da sauraran rediyonshi ita kuma tana bud'e diary d'inta tana karantawa.Wacewar wasu dak'ik'u tad'ago tana kallanshi"ni ko Baba in tambayeka mana. Uhun tambaye ni ina jinki.Tad'anyi rubutu a diary sannan ta kalleshi "wai brother d'inka daka ta6a bamu labarin shi har ka nuna mana hotonshi tun da dad'ewa yana nan kuwa?Yad'aure fuska"me yadameki da Shedrak? Ina ruwanki da jin labarinshi kuma?Yayi d'ad d'as d'as da yan yatsunshi ki karkad'e kunnuwanki ki jini da kyau "Shedrak is no more in our family,mun dad'e da yafeshi mun barma musulmai shi,kamar yadda shima yazabi zama musulmai da addininsu. Ta ta6e baki

"Basakut Baba(Kayi hak'uri Baba)

Dan na ga kamar ranka ya 6aci,ni abinda yasa na tambayeka a cikin wani littafi d'azu dana ke karantawa naci karo da sunanshi shine na tuno da wannan d'an uwan na ka,ai kaima ka san tunda muke dakai ban ta6a maka zancen shiba.Yakashe rediyon dan sun gama shirin.To woo na d'auka kina san jin labarin shine.Tad'an motsa kafad'a ko d'aya Baba dan labarinshi ba zai amfane ni da kome ba.Tamik'e Baba barinje unguwa amma ba dad'ewa zan yiba.Yad'aga mata hannnu yana mata adabo.

"Sai aburak" ( Sai kin dawo).

Sakamokon jarabawar su na fitowa Water Fall Hotel matsirg suka d'auke ta aiki amma k'ememe tace ba ta so duk da albashinta me tsokane.Mamanta takalleta cikin takaici to saboda me ba kya so?Saboda Baranzan yana da hannun jari a hotel d'in ni kuma na gama amfanuwa da duk wani abu indai a kwai Baranzan a ciki wallahi bazan yiba.Suka had'u suka dinga zagin ta amma tayi kunnan uwar shegu dasu ko a jikinta an yak'ushi bishiya.

A sanda rana tatafi tana shirin fad'uwa Kasham tashigo gidan da kaya nik'i nik'i ta zauna tana hutawa.Rahab da Mamanta suka bita da kallo daga ina kike ne?Tabud'e manyan idanunta masu maik'o da suka d'an canja kala kamar me jin bacci"daga kasuwa nake tamik'a musu tsire da lemun kwali Don Simon tashige d'aki.

Rahab tabiyota wai kashe-kashen kud'in nan da kikeyi ko dai kin yi sabon saurayine? Tamata wani malalacin kallo kamar za tayi magana sai kuma tayi shiru tad'auko diary d'inta tana rubutu.Tagama abinda takeyi takwanta da tunanin wanda zai zo yasiye aladunta gaba d'aya dan kud'i sosai take buk'ata,dama ita da Rahab kiwon aladu sukeyi da shi suke rufama kansu asiri shi yasama basa harkar tara samari barkatai,mazan ma ba sa, ba su na jaki kamar yadda suke ma yan matan bariki dan sun san ba da kud'insu suka dogara ba,a dating zata watse. Yauma aladu biyar takama tasiyar dan ba ta da kud'i.

Dasafe tasamu Babanta a d'aki yana kallo tazauna tana tayashi suna hira. Baba ka san abinda yake bani mamaki?Yagirgiza kai"to wai shi Shedrak da aka yafeshi a cikin dangi yana jin dad'i?Yatsaida idanunshi a kanta tsawon lokaci, nazarin ta yake yi"Kin dameni da maganar Shedrak a yan kwanakin nan me ki ke so kiyi ne? Me ki ke shirya wane? Banza bata kai uwar akuya kasuwa,Meye a zuciyar kine Kasham?Cikin dariya tace kai Baba ALLAH ba abinda nake shiryawa,ni abinda yake bani mamaki ace mutum ba shi da yan uwa blood relatives saboda zai yi sallah kuma shi ya yadda da haka? Ni fa shi yasa nafara canja tunani a kan Julaibib saboda zo mu zauna zo mu sa6ane,to idan munyi fad'a wajan wa zani inji dad'i ku kun yafeni? Yagyad'a kai "Ehem yanzu kika zo inda muke so kizo, yanzu kin gane abinda muke k'ok'arin nuna miki kenan amma ki ka k'i sauraran mu gashi daga fara addu'a kin fara dawowa hayyacinki.

Yayi yar dariya"God bless you my daughter. Wani murmushi ya su6uce mata amin Baba.Tagyara zama"gaskiya Baba ni yanzu na amince gobe muje a min baptismal.Yayi kyau Kasham,Yakad'a kai cikin damuwa "Hum Shedrak? Kar kiyi tunani irin na shi fa.Tagyad'a kai"haka fa.Ko yanzu yana ina ne oho mishi.Yace wa? Shedrak ai nasan inda yake da Dinatu ma tana zuwa gidanshi a shekarun baya...bai k'arasa ba tad'an ta6e baki tare da mik'ewa cikin halin-ko-in kula da maganar,Baba barinje inyi wanka dan yau zanje a min nail fixes.Tana shiga d'aki tayi tsalle tafad'o gado Hak'anta za ta tadda ruwa Halelujahhhhh...

Ranar lahadi duk suna ta shirin tafiya majami'a(Church)ita kuma tana zaune tana shafama faratanta da taje aka sa mata na roba jan farce.Mamanta ta kalleta ke baza ki shirya ba sai kin makara? Ta yamutsa fuska"ni fa yau ba inda zani"baki da lafiya ne?Rahab data fito daga d'aki take tambayarta.Lafiya ta k'alau zuwan ne kawai bazan yiba.Shikenan sai ki mana abincin rana.Tagyad'a kai To Mama.Tad'aga hannu tana musu adabo sai kun dawo.


Tamaida k'ofar gidan ta kulle sannan tashige d'akin Baban wajan daya ke ajiye muhimman takaddunshi tanufa,d'aya bayan d'aya take dubawa cikin tsanaki,wasu takardun ma tun na makarantar Primary suna nan saboda ya iya ajiya,anan taci karo da wani tsohon hoto Baban ne da Maman suna ganiyar k'uruciya, tamayar da hoton tana dariya,kakaf binciken ta bata ga abinda take nema ba.Rai a6ace taja dogon tsaki"Ohhh no damme,ta dunk'ule hannu ta naushi iska.Tayi jifa da wani tsohon wallet k'ananan katunan ciki suka tarwatse a tsakar d'akin.Tadafe kanta dake barazanar ciwo.

Wucewar wasu dak'ik'u tana zaune cikin tafasar zuciya,ta tsuke bakinta kamar za ta rufeshi amma bata rufe ba tana zuk'ar iska, ta zuk'eshi da yawa sannan tafara fesar da iskar ta baki ta hanci ta sauke gwauran numfashi tamik'e ranta in yayi dubu ya baci ta tura hannunta acikin gashin kanta,tasake dunkule hannu ta naushi iska"Damme...a kasalance tamayar da takaddun, sannan ta tsuguna tana kwashe tarwatsastsun k'ananan katunan a cikin ma'ajiyarsu,idanunta suka kai wajan guda d'aya daya kusa shigewa k'ark'ashin kujera,tad'auko shi tana dubawa.


Complementary card ne me d'auke da sunan Alhaji Hafiz Donatus,sunan unguwar da yakeyi,sai lambar waya na gida dana wajan aiki.Tayi tsalle cikin dariyar murna,ta k'ank'ame katin a kirji"Hallelujah...wallahi wani karfi da karsashi ne ya mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta.Batayi niyyar yin abincin ba amma farin cikin data tsinci kanta a ciki yasa ta zauna ta shirya musu abinci da abun sha me rai da motsi(Yummy).


A sanda hantsi ya dubi ludayi na safiyar talata tagama shirya kayanta a yar madaidaiciyar jaka trolley,tana zuge zip d'in Mamanta tashigo tana mata kallan nazari

"Ani yake ?(Ina za ki)


Kamar da gaske tajuyo cikin damuwa suna kallan juna,tad'an sosa kunnen ta na dama"Ramai zani wajan Tina tun jiya da rana nasamu labarin an mata Operation,tun ajiyan naso tafiya to bani da kud'ine.Wayyo! takad'a kai cikin damuwa ALLAH yabata lafiya, kigaishe ta,tasa hannu a mata sun gane(Lalita)taciro kud'i to kenan ko na mashin baki dashi? A ah ai na samu Mama ina da wanda zai kaini.To gashi kya kara wannan zai miki amfani, dan na san zaki tarar da ita da wata buk'atar,kin san majinyaci.Takar6a tana d'an murmushi "Nagode Mama. Maman tarakata har sai da ta hau mashin tana dad'a jadda dama me mashin d'in Ramai za ka kaita kayi tafiya da ita a hankali,dan jiya na hau mashin d'in wani wawan yaro saura kad'an yazubar damu.To Mama zan tafi a hankali kar in zubar miki da wannan kyakkyawar yarinyar ni da zaki bani ita wallahi ina so.Shi da Maman sukayi dariya ita kuma ta d'aure fuska"Kai malam ina da abinyi dallah ja mutafi. Mama sai na dawo.Yauwa Kasham ALLAH yakaiku lafiya.

Suna zuwa kwanar da zata sadasu da cikin gari tace shiga nan yad'an juyo ya kalleta ba Ramai a kace zan kai kiba? Eh can ne amma na fasa mushiga cikin gari idan nagama abinda nake yi ka kaini tasha.Yaja mashin"to amma kin san kud'inki ya k'aru da yawa tunda har sai na jiraki kin gama abinda za kiyi a cikin garin ko? Tagyad'a kai "Indai kud'i ne to ka kwantar da hankalinka kamar ka mari uwar soja,wallahi abinda ka yanke da bakin ka shi zan ba ka.Yayi yar dariya "godiya nake yi me kyau, wallahi irinku nake so.


Tanata mishi kwatance har suka zo gidansu Julaibib amma k'atan kwad'an da suka gani a k'ofar gidan yabata tabbacin mutan gidan ba sa nan tace su wuce shigon shi sai dai kash...nan d'in ma a kulle. Tasauko tana waige-waigenta ta hangota.

"Hey Sudaida Ibrahim Me-Lambu...

Sudaida tajuyo,idanusu yahad'u tak'araso wajan tana murmushi"Malama Kasham ke ce?Ina kwana. Takamo hannunta"Lafiya lau Sudaida,ya karatu? Alhamdulillah. Sukayi d'an shiru na wuce war wasu dak'ik'u.Kasham tasake kallanta"yanzu ajin ki nawa?Aji uku zamu shiga idan aka koma hutun nan.Tagyad'a kai"yayi kyau,kidage sosai kinji ko? Ina Ya'yanku na ga shagon a kulle? Sudaida tabi kofar shagon da kallo"Yaya D'ansarai ai baya gari,watanni biyar kenan har yanzu bai zo gida ba,Shida Yaya Musaddiq zuwan shi uku.Suna ina? Tad'an kalleta "Suna Zari'a k'aro karatu.Tad'anyi murmushi "Julaibib ya tafi Jami'a zai d'ora degree a Islamic Studies kenan,tun a Gidan-Waya taso canja course,da ace shima Special Education yake yi irin karatun Musaddiq wallahi da sai ta koma irin karatun,da yanzu itama ta nemi addmision ta bishi can.

"Hummm my enigma man wish you all the best"...

Takalli Sudaida to me zan bakine? Tazuge zip d'in jakarta taciro yar k'aramar "Damask rose-flower"ta rabo me kyan gaske tashak'i k'amshin sannan ta mik'a mata"gashi ba yawa.takar6a da godiya.Kasham ta sake ciro wani rufaffen envelop tamik'a mata"wannan ki ba Yayanki D'ansarai duk lokacin da ya dawo dan ALLAH ki adana shi dakyau,kar kuma kimanta, tahad'a tafukan hannayenta please... Sudaida tayi yar dariya ganin yadda tawani marairaice mata tagyad'a kai"Malama Kasham Insha-ALLAH I will do as you say"tadafa kafad'arta"Yauwa Sudaida thank you very much,I really appreciate sukayi dariya.

Tabud'e wallet d'in hannunta kud'ine sababbi yan naira d'ari tad'ibo su dayawa bata tsaya k'irgawaba tamik'a mata, amma Sudaida bata kar6a ba. Tamata kallan nazari"Me yasa?Ba kome kawai ki barshi.Ba zato Sudaida taji ta rungumeta "Kar kimin haka Sudaida,ni kaina ban san dalilin da yasa nake k'aunar duk wanda yake da alak'a da Julaibib ba,ban san dalilin ba, hakanan nake jinku a jinina,tanannad'e kud'in tasa mata a tafin hannu, ai ni naba ki ba rok'ona kika yiba,sai ta sake ta a hankali.


Kiyi karatu Sudaida,dan shine hasken rayuwa,shine abinda baya k'arewa kullum kina tare da abinki ba a fashin shi duk rintsi duk wuya yana cikin kwakwalwarki,Ina miki fatan alheri,ki gaishemin da D'an Sarai,Julaibib my enigma man dakyau da kyau.Me mashin d'in yatayar tahau,Sannan suka d'aga hannu suna ma juna adabo🙋Sudaida tad'an d'aga murya dan har sun kusa shan kwana"Malama Kasham kema ina miki fatan alheri nagode.Kasham tamata murmushi"Toh nagode suka sha kwana. Suka 6ace ma Sudaida.


Cikin sa a suna zuwa tasha motar saura mutane biyu ta cika tabiya kud'in mutum biyun sannan ta sallami me mashin da kud'in da baiyi zatoba dan ta ninka mishi abinda yace tabayar,yatafi yana mata godiya.Tana shiga tazauna ta d'aura belt direba yaja motar sai...

KADUNA garin gwamnahhh...cibiyar ilmi,wayewa da iya d'aukar wankan dake bin jiki.Oh yessss...mune the KD's mune nan,kowa kagani da wanka rainan mune,a wajan mu ya koya...😎



Me neman ruwa yatafi randa.
Me neman jini yatafi kwata.
Me neman labarin wuta ya tambayi tsire.
Masu mura suke da majina.
Masu ruwa suke da kifi.
Masu abin fad'a ba sa fad'a.


3 Jumaada Awwal 1441
29 December 2019

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.






DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFI💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A. Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na goma.



Motarsu na tsayawa a kawo tad'auki shatar taxi,dak'ik'u kad'an suka iso unguwar saboda ba cunkoson abubuwan hawa, tabi wajan da kallo bayan tasallami me taxi,tasake kallon wajan da tunanin ina za tabi dan hanyoyin sun karkasu.

Yan makarantar Islamiyyar rana sun fara tafiya,wasu yara guda biyu maza za su wuce ta tsayar dasu "Sannunku yan makaranta. Suka amsa da yauwa sannu.Dan ALLAH tambaya nake yi gidan

"Alhaji Hafiz Donatus"

Tamik'ama babban katin hannunta, yad'an kalleta da mamaki bayan ya duba katin, sanin Alhaji Hafiz da yayi mutumin kirki me rik'o da addini,dan babban d'an Alhaji Hafiz abokin Kawun sune, to ita kuma wannnan me zak'o-zak'on faratan rumfar shaid'an fa?Kuma ko mayafi babu haka take tafiya kamar wata namiji,a gidan Alhaji Hafiz ma basa mu'amala da kome sai hijab,to kuma meye darin gamanka da ita? Tamabayarka tayi idan ka sani fad'a mata,idan baka sani ba fad'a mata.Zuciyarshi tafad'a mishi haka.sai yagyad'a kai.


Yamik'a mata katin,gidan wanda nasani nake kuma kyautata zatan shine to kinga wancan titin yanuna mata titin da d'an yatsan shi tagyad'a kai tana kallan titin, to kimik'e shi,kwana tafarko zaki shiga,gida na hudu nan ne gidan ai zama kigani idan kika duba katin. Tahad'a tafukan hannayanta"nagode.A ah ba kome yarik'o hannun k'aninshi suka tafi.

Tacigaba da tafiya har tazo gidan me k'atuwar k'ofa ruwan zinare,tayi tsai...na wucewar wasu dak'ik'u,ta kai hannu zata fara rank'washin k'ofar kenan sai gata a bud'e wata farar mota kirar marsandi tana fitowa, yabita da kallo ta cikin madubi,itama shi take kallo, yashiga tunanin a ina yasan wannnan fuskar ne? "Mahaifiyarshi"abinda yafad'omishi kenan daya ga manyan idanunta masu maik'o da yanayin k'irar jikinta,sai yayi ribas tabbas wannan yar'shice,yar d'an uwanshi Kantiok ga kamanni nan,yafito daga motar suna kallan juna,itama tagyad'a kai cikin gamsuwa tabbas wannan dan uwan Baban tane sai dai shi bak'i ne,Babanta kuma fari,yana sanye da dogayan fararan kaya,bak'ar hular dara akanshi da bak'in takalmi,yanata k'amshin turare me sanyin dad'i wajan shak'a.

Tayi yar dariyar murna"Uncle.Yayi murmushi"na'am.Rahab ce ko Kasham ko Judith? Uncle Kasham ce.Masha-ALLAH sannu da zuwa, yakulle motar yazare makullin"to bismillah yanuna mata hanya mushiga ciki,yakar6i trolley d'in har suka shiga wani babban D'akin-shak'atawa me cike da ni'ima,wani sassanyar iska da k'amshin turaran d'aki ya mamaye ko'ina,kome agyara tsab a muhallinshi,tazauna a kujera tare da lumshe idanun ta tana zuk'e k'amshin tana zancen zuci "Lallai Uncle yana jin dad'in shi,tasauke numfashi sannan ta bud'e idanunta, suka kalli juna sai ta d'anji kunya ta kauda kanta gefe.

Yayi murmushi kinsha hanya ai na san kin gaji,yad'auko abinci da ruwa da lemun kwali na biyar a raye (five alive) yamik'a mata kofi,tazuba ruwa tafara sha sannan taci abincin ya kuma mata dad'i taci to k'oshi dan bata wani tsaya bak'unta ba,kad'an tasha lemun ta godema Jesus Christ,Yesu almasihu me ce to.

Saida da tagama suka fara hirar yaushe gamo?Shi dama bai san taba dan tun kafin a haife ta rabonshi da kauyansu Madauci.Ikon ALLAH banyi zaton wani a cikin ku zai zo inda nake ba,wai Kantiok ne da kanshi yafad'a miki inda nake?Tagirgiza kai"a ah ba shi bane,ni nayi ta bincike har naga complementary card d'inka, ni ba ma wanda yasan wajan ka na zo dan na fad'a ma Mama wajan k'awata Tina za ni.

Yayi yar dariya"Dinatu kenan,wato me hali baya fasa halinshi,amma ba abinda yafaru ko?Eh Uncle ba abinda yafaru kowa lafiya.suka cigaba da hirar yan uwa ya tambayeta

Please Login or Register in order to submit comment