Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takewar auran ku to baza su yadda dashi amatsayin surikiba,kiyita addu'a kina kuma nusarshe shi illar zama da irin wad'annan mutanan.To Yaya Aminu nagode. ALLAH yaba ka Siddika.Yayi murmushi.

Tana gidan Hajiya taji sallamar Julaibib.Yanad'e hannayen shi ak'irji yana kallan ta"kina kwance anan gashi can anata karatu a makaranta.Tad'an harare shi"uh na gajine yau da gobe ai sai ALLAH,dan dai rana d'aya mutum ya huta sai afara binshi da k'orafi? Yatsuguna yana duba wasu tsofaffin littafai adirowan Hajiya"hutun jaki da kaya aka ba.Tad'auki man zafi asaman kujerar"kai baka san k'afafuna ciwo suke yiba "me zai hana su ciwo tunda jiya kinsha rawar samba" daga baya suka jiyo muryar shi, Musaddiq ne.

Yagalla mata harara,sai ta sunkwui da kai"tashi ki wuce makaranta, tamarairaice"dan ALLAH Yaya Musaddiq...yatari numfashin ta shhh...yad'ora yatsan shi abaki,in dai ba so kike yi ki kwashi kashin ki a hannu ba to tashi kawai "tafara matso kwalla aranta tana addu'ar ALLAH yakawo Hajiya ita kad'aice zata ta ka mishi burki,itama d'in idan ta ga dama.Julaibib yasa musu baki"amata hak'uri mana tunda tana da lalura"wa zan ma hak'urin?Wannan yarinyar? Yanuna ta da yatsa"ai da lalurar arzikice da har pain-relief zan k'arama ta dashi,ai ka san jiya anyi Inter-School a Saint-Francis College to nan suka tafi tun safe har biyar da rabi ba makarantar da suka je ta allo data Islamiyya,ashe yauma basuje ba da safe suka kwanta bacci wai sun gaji,to d'azu ina gidan Umma takorasu kasan sun maida Mama kamar sa'ar wasan su koda tayi magana basu jiba,to su sauran sunji maganar Umma sun tafi ta yamma sai ita shafaffiya da mai tazo nan tayi kwanciyarta?Tafara kuka"ni dai ALLAH yanaji yana kuma gani banyi rawar samba ba.Yakalleta cikin fushi" karya zan miki ko?Me zai za k'afufunki suyi ciwo bayan wasan discuss kike yi indai ba rawan kika yiba?

Hajiya tashigo"yayane Sudaida kike kuka kuma?Musaddiq yayi kwafa"kyale ni da ita kawai Hajiya samun waje ne kuturu da gad'a a rama.Julaibib yadafa kafad'arshi"ka kyaleta mana wata kila bayan ciwon k'afafun akwai hujjar datasa tak'i zuwa,ka san hali da dabi'ar mata Iyayanmu, yan'uwanmu,k'anninmu sai hak'uri, sai ana kawar dakai awasu lokutan idan ba haka ba,sai su maida kai wani iri,yazame hannun Julaibib daga kafad'ar shi, yajuya yayi tafiyar shi;tasauke numfashi sai a lokacin tashak'i iskar yanci"kai Yaya Musaadiq barkono ne,yanzu haka yakema Safiyya wannan halin?Hajiya tace"barin kira miki shi yaba ki amsa dan wak'a abakin me ita ta fi dad'i.Takama ha6a"wuuu...Tabbb Hajiya rufa min asiri kar k'ilu taja bauuu...

Ya tashi sahur azumin nafila na ranar alhamis yana juya zuman dayasa a shayin na'a na'a da 'ya'yan algarib yayi tsai...cikin tunano mafarkin dayayi da daddare...

"Kasham yake gani da kayan fulani tayi kyau k'irar kalangunta ya fito rad'am,amma idan tayi magana muryar Sudaida yake ji.

Shekarun baya yayi wannan mafarkin to yanzu ma mafarkin ya dawo shi ya rasa gane kan wannan mafarkin.Yayi bismillah yafara kur6a amma ko kwata bai sha ba kome ya gundire shi,shayin yamishi wani irin d'and'ano mara dad'i,ya ajiye kofin a saman tebur.Yad'auki farar hular zita yasa yad'auki Alqur'ani me girma yana karantawa har aka kira assalatu daga mabambantan masallatai na unguwar,yayi raka'atal fajri sannan yafito suka tafi masallaci shi da Baba.

Tana fitowa daga asibiti motar shi tana tsayawa,yabita da kallo tayi kyau a cikin fararan kayan riga da wando da d'an madaidaicin farin hijab,suka kalli juna sai yamik'a mata hannu ta san me yake so dan haka tamik'a mishi ragowan Schweppes d'in da yake hannun ta"ya ajiye a mota dashi zan yi bud'a baki "Megado kinga kyan da kike k'arawa kuwa tun bamu fara cin Shahrul-Asal (Honey Moon) ba?Ya d'aga kai sama alamar tunani"Bilkisu k'wak'walwata 6angaren nazari da tunani ta gaza gano yadda zan fasalta irin kyan da kike tayi,wai meye sirrin ne?Yazubama tattausan jajayan la66anta idanu;tayi dariyar da tun had'uwar su bata ta6a irinta agabanshi ba, kumatunta suka lotsa ciki sosai yar siririyar wushiryar ta,ta dad'a k'awata fuskar ta,Ya ilahi... shi da kanshi ya kauda kai yana jin wani irin yanayi a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar shi game da ita.

Wai kai kwana biyun nan me yake damun kane sai kadinga wasu maganganu kamar lokacin kafara gani na?Yamata wani kallo"yunwar so ke damun zuciya ta. Matsirga zan tafi,takawar da wannan maganar.Yakalleta cikin makaki"wani irin Matsirga kuma da safen nan?Haba kibari kid'an samu bacci koda awa uku ne,kinga aikin dare kika yi na san baki yi bacci ba,idan kika d'an huta bayan azahar ba sai ki tafi ba?"ni dai dan ALLAH yanzu nake san tafiya kar inyi hutun jaki da kaya aka,agida sai in huta gaba d'aya.A ah Megado ban yadda ba,ba ranar lahadi da yamma kika dawo daga Matsirgan ba?Tagyad'a kai"Inna nake san gani, tayi yar dariya"wallahi gobe da safe zan dawo Insha-ALLAH.Ba ga waya ba kikara ta mana.Tad'an marairaice"ni dai nafi so inganta ganin idanu na.Yad'an harareta"shikenan tunda kin na ce sai kin tafi to muje in kaiki,idan muka kwana sai mubugo sammako da sassafe dan nima Zari'a zani a goben.

Tad'an bud'e idanu dan mamaki"ka kwana a ina?Bai bata amsa ba yashiga mota yazauna sannan yakalle ta"shigo mutafi mun... kiran wayar Baba takatse shi yad'aga da sallama "kazo yanzu na yi baki suna jiran ka a shago.Ya amsa cikin ladabi"to Baba gani nan zuwa.Yad'anyi jimmm...D'ansarai lafiya kuwa?Kiyi hak'uri Megado na so kwarai mutafi tare to sai dai hak'ata bata tadda ruwa ba,akwai bak'in da suke jirana a shago.A ah ba kome" tashiga ta zauna yaja motar.

Tasha yakaita yasata a motar haya, gidan gaba yabiya kud'in mutum biyun dan ta zauna ba takura,suna ta hirarsu yana fad'a mata wasu kalamai masu nauyi,tad'an harareshi sannan ta sunkwui da kai "ka san ALLAH idan baka daina fad'a min wad'annan kalaman ba zan daina sauraranka,kuma ko waya ka kira bazan d'aga ba, yayi yar dariya"ni kuma ban san inda kike bako? kaji yar rainin hankali kamar wata k'aramar yarinya, ba aikin asibiti kikeyi ba? Wancan makon ba d'akin yan hatsari kuma maza aka kaiku ku musu dressing ba?Wani dare ne jemage bai gani ba?

Tasa hannun damar ta tashafa dogon karan hancin ta,tayi kamar bata gane me yake nufi ba.Akwai dararan da jemage bai gani ba fa.To wani dare ne kuwa?Shima yatambaye ta. Tamishi wani kallo daya sa zuciyar shi bugawa Dammm...bai kuma san dalili ba.Daren da aka haife shi da daran mutuwar shi ko ya gani? Yagirgiza kai.Kiran Adnan yashigo wayar shi, yad'aga da sallama.Adnan ya amsa sannan ya tambaye shi"kana ina ne D'ansaarai?Ina tashar mota.Tashar mota kuma?Me kakeyi a tasha? Bilkisu zan sa a motar Matsirga.Tam dama Hajiya zan kai unguwa Yaya Aminu yafita da motar gida. Shikenan zo ka kar6i mukullin.Suka cigaba da hirar su har Adnan d'in yak'araso suka gaisa da Bilkisu a mutunce yakar6i mukullin motar yatafi.

Shafff...ya manta da kiran Baba sai da kiran shi yasake shigowa sannan ya tuna"Baba ayi hak'uri gani nan zuwa"yamayar da wayar aljihu "Bilkisu barin je in dawo.Takalleshi cikin natsuwa "bak'i fa kukayi kafin kugama abinda za kuyi ka dawo ai na tsufa a gida,sai dai munyi waya. Yagyad'a kai"shike nan nagode ALLAH yamiki albarka.Amin.

"Sai munyi waya...suka fad'a atare.

Sannan suka kalli juna sukayi murmushi yad'aga hannu yana mata adabo yajuya da d'an sauri dan kar Baba yasake kiran shi,tabi bayan shi da kallo har ya tsallaka titi ya6ace ma ganinta,tamaida kanta jikin kujera tana sake kiran lambar Inna dan ta kira sau shurin masak'i amma bata shigaba,saboda matsalar na'urar sadarwa. Motar su ta cika suna shirin tashi ta tura ma Julaibib sak'on murya(voice note).

"Julaibib yanzu motar mu ta tashi... Ina sauka kai zan fara kira,ta mishi sautin sumba muahhh... 💋"

Abinda yaketa rok'on ta ayan kwanakin nan tamishi kenan,amma k'ememe tace wai ita bata iya ba,rannan data bashi haushi yace"kar ALLAH yasa ki iya d'in za ki zo hannu duk sai kin biyani bashi dalla-dalla.

Yadawo daga sallar azahar zai shiga d'aki kiran Bilkisu yashigo,yayi murmushi "haba Nurse Megado ko dak'ik'u talatin bakuyi da tashi bare kice har kin sauka, yad'aga da sallama "hayaniya da kururuwane ya cika kunnuwan shi "Bilkisu lafiya kuwa?Wata murya ta amsa"ba Bilkisu bace kazo Wadom yanzu-yanzu sunyi hatsari ne"Innalillahi Wa'inna'ilahi raji'un" Istirja'in shi Inna taji fito daga D'akin-girki da sauri. Yajingina kanshi da bango jikin shi a sanyaye "lafiya kuwa D'ansarai? Sai ga Musaddiq ya shigo duk suka zuba mishi idanu su. Musaddiq yace"me yafarune?Inna tawatsa hannu"abinda nake tambayar shi kenan kashigo.Yadafa kafad'arshi"yi magana mana Julaibaib..."Megado ce sukayi hatsari.Inna da Musaddiq suka yi Istirja'i suma, yaja hannunshi"to tsayuwar me muke yi?Inna sai mun dawo.Tabisu har zaure bakin ta d'auke da addu'ar Ubangiji yatsare musu hanya.

Gudu sosai Musaddiq yayi.Wajan ya cika dank'am da mutane da jerin motoci,wani hukuncin Ubangiji kuma daga Bikkisu sai wani dake gidan baya sune sukaji mummunan ciwuka, sauran dai k'uk'k'urjewa kawai sukayi, shi dama d'an Wadom d'in ne yan'uwan shi sun zo sun d'auke shi zuwa asibiti.

Ruguzowar wani abu yaji a k'ahon zuciyar shi lokacin daya ga Bilkisu a kwance sambal cikin jini fuj'atan, zuciyar shi tafara wata irin bugawa da k'arfin gaske kanshi yasara, yahad'iye wani abu me zafi,yasa hannayenshi biyu ya cicci6eta zai sa a mota sai kawai wajan ya kaure da salati, masu ihu na yi,masu fad'in Jesus Christ,Holy Mary nayi,masu d'ora hannaye aka suna sambatu da yarukan su na yi, bai fahimci kome ba sai da yaga Musaddiq ya d'auki farin hijab d'inta da yarine da jini ya koma ja,yad'aure mata kai,ashe kan tsagewa yayi ana hango ciki, yashimfid'eta a bayan mota.

Jama'ar wajan na musu fatan su sauka lafiya, ita kuma ALLAH yata shi kafad'a yasa kaffarace.Shi kanshi Musaddiq ta maza yayi yake tuk'in saboda ya shiga rud'u da damuwa,a haka har suka koma Zonkwa.

"Saint Louis Hospital 6angaren hatsari da taimakon agaji na gaggawa(Accident and Emergency) aka wuce da ita,Julaibib ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai-kawo yake yi a barandar wajan.Musaddiq yarik'o hannun shi suka zauna"kayi hak'uri Julaibib na kira Malam Lamid'o a waya yanzu haka suna hanya.

Suna zaune jingum-jingum har su Baba da Malam Lamid'o da Yayyin Bilkisu Maude da Tukur sukazo, zaman awanni biyu sannan zugan likitocin da ma'aikatan jinya suka fito daga d'akin.Gaba d'aya suma suka mik'e kowanne hankali a tashe,Babban likitan yace ku biyoni office.

Cikin natsuwa yad'ago yana kallansu bayan ya gama yan rubuce-rubucen shi a wani fallan takadda me sunan asibitin"kuyi hak'uri Insha-ALLAH kome zai zo da sauk'i,yanzu dai mun bata taimakon gaggawa wanda za mu iya amma gaskiya abin ya fi k'arfin mu dan ya shafi k'wak'walwarta sai dai kuwuce da ita Shika, Ahmadu Bello Teaching Hospital Ubangiji yaba ta lafiya,yanad'e takaddan yamik'a ma Malam Lamid'o"Idan kunje ku ne mi...

"Doctor Garga Ibrahim Manogi...

Maude yagyad'a kai"Alhamdulilahi Doctor Manogi k'wararren ne akan abinda yashafi k'wak'walwa (Neurology) kuma k'anwar Innar su yake aure, dan haka fad'uwa ce tazo dai-dai da zama.Suka koma d'akin da Bilkisi take kwance, jikinsu yayi mugun sanyi,wallahi mutum ba a bakin kome yake ba, Ubangiji kamana kyakkyawan k'arshe👏Tukur yace muna 6ata lokaci ai gwamma muyi harama.

Malam Lamid'o da Tukur agaban motar sai Julaibib da Bilkisu a baya,su Baba dasu Musaddiq suka lek'o to Ubangiji yakaiku lafiya. Maude yace gobe sammako za muyi da Inna, Malam Lamid'o yagyad'a ka.Tukur yaja motar, suka bisu da kallo har suka fita daga asibitin suka hau kwalta.

Julaibib yazuba mata idanu zuciyar shi na bugawa da k'arfin gaske d'ik d'ik d'ikkk...wuyan ta ya karye an sa mata stiffness collar,kanta yana cinyar shi har lokacin jini bai daina zuba ba,bandejin da aka nannad'e kanta dashi saura kad'an yajik'e,hannunta nadama akwai karaya guda biyu,idonta na dama ya zurma ciki sosai alamar ya fashe ruwan ciki ya gama tsiyayewa,idonta na hagu kuma ya kumbura suntum har wani kyalli yakeyi,gaba d'aya kamanninta ya canja saboda kumburin da fuskarta tayi. Idanun shi sun kad'a jawur kanshi yana wani irin sara mishi,yakad'a kai cikin maimaita Istirja'i yana tallafe da kanta... motar tsittt kowa da yadda abin yadake shi,wucewar wasu dak'ik'u hannun hagunta da yarik'e yaji ya saki tayi wata ajiyar zuciya Dammm...zuciyar shi tabuga!Yasake zuba mata idanu yana ta6a wuyan ta,harbawan da yake yi ya tsaya cakkk...Tukur yana kalkanshi ta madubi a hankali yagangara gefen titi yatsaya.Malam Lamid'o tun shigar shi motar kanshi ak'asa yad'ago"Tukur lafiya?duk suka juya baya,Tukur yabud'e motar yakoma baya yana tatta6a ta,da rawar murya yace"Malam kamar fa bata numfashi.Sukayi shiru nawasu yan dak'ik'u.Malam Lamid'o ya tabbatar Bilkisu ta mutu!

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!...KULLU NAFSIN ZAA'IK'ATIL MAUT!kowace rai sai ta d'and'ani mutuwa😭Ubangiji mun tuba,dama kowane d'an Adam me kuskure ne,sai dai mafi kyawun masu kuskure sune masu tuba.Ubangijin mu kamana gam da katar da kyakkyawan k'arshe,mu mutu cikin da'a da dokokin ka😭👏...

"Julaibib yace Malam Bilkisu fa bata mutu ba,dogon suma tayi.Tukur ma yagyad'a kai"nima haka nake tunani yakoma gidan gaba yazauna yana k'ok'arin tayar da motar"Malam inaga jinin da take ta zubarwa ne yahaifar da haka.Juya da motar nan mukoma gida a mata wanka akaita d'akin ta na gaskiya Ubangiji yasa k'arshen wahalar kenan Bilkisu,kwallah suka cika idanun shi,yasa gefen babbar rigar shi yagoge. Julaibib da Tukur sukace "a ah Malam Bikkisu bata mutu ba,Insha-ALLAH kuma za ta warke. Malam Lamid'o yadafa kafad'ar Julaibib"kar muyi haka daku mana, ni tunda naga Bilkisu dama na san indai ba wani hukunci na Ubangiji ba to baza ta rayu ba,idan ma ta rayu to za ta samu tasgaro me yawa arayuwar ta,kuyi hak'uri Bikkisu ta riga ta tafi ni naga mutuwa ba d'aya ba ba biyu ba.

A asibiti ma likita yabasu tabbacin ta rasu,dukkansu hawayene yake zubo musu sharrr... sharrr... Wayyo ALLAH!Duniya gidan ci rani,duniya gidan azo a wuce! kowa sai ya koma gidan shi na asali (Lahira)

Gidansu Julaibib suka wuce da gawar Bilkisu dan Malam Lamid'o ya ce ba sai sun tafi Matsirga ba,duk inda musulmi yamutu ai za a iya yi mishi wanka a mishi sallah akwaishi makwancin shi.

Inna da Musaddiq da Hajiya suna zaune cikin jimami sai ga Julaibib yashigo cikin tashin hankali "Lafiya kuwa Hajiya ta tare shi,me yadawo da kai? Ya zauna a kujera idanun shi sun kad'a jawur,wata jijiya ta fito rad'am a gefen goshin shi kamar shatin bulala, yabisu da kallo sai kuma yamik'e, jikinsu ya basu dan haka cikin zafin nama Musaddiq yarik'o shi"Hajiya tace kayi hak'uri... mutuwa ba ta jira ALLAH baya barin wani dan wani, ALLAH shi yayi Bilkisu, dama aran ta aka ba mu,to lokacin tafiyarta ta yi dan haka bamu isa mu hana ba,suka cigaba da rarrashin shi da kalamai masu taushi,Musaddiq yafita wajan su Malam Lamid'o dan har an shiga da ita D'akin-shak'atawar Inna.

Maude ne yazo da Inna,tana ganin ta a kwance sambal fararan kayan aikinta sun rine da jini sun koma kalar ja,tayi fari fattt...ta d'ashe alamar babu sauran jini ajikinta.Inna ta zuba mata idanu cikin hawaye"Bilkisu ke ce kika zama haka? takad'a kai cikin sarewa da al'amarin rayuwa, kamanninta sun canja ta zama wata irin halitta,a fuskarta ba irin halittar d'an Adam ba amma wai hukuncin Ubangiji sauran gangar jikin ta lafiya lau ko k'warzone ba bu na ciwo,in banda hannun damar ta "Bilkisu kece mace d'aya acikin 'ya'yana na so ganin auran ki sai dai kash... Kana na ka ALLAH na na shi kuma na ALLAH shine dai-dai,ALLAH yamiki rahama yasa k'arshen wahalar kenan,Bilkisu kin dace Insha-ALLAH dan kin mutu a d'aya daga cikin ranakun da babu tambayar kabari akan mamaci,kin mutu ranar alhamis, tasa hannu tashare hawaya ta fuskanci su Innan Julaibib "mu mata abinda aka fiso ama mamaci da gaggawa,su uku suka mata wanka suka samata likkafani suka sata a makara Innan tad'auko fallan zani aka lullu6eta,Maude da Julaibib suka fita da ita aka mata sallah sai makabarta! Sun dad'e suna ne ma mata gafara musamman mahaifinta da masoyin ta Julaibib da Yayyinta su Maude da sauran yan'uwa da abokan arziki.

"YA ALLAH!KA GAFARTA MATA!YA ALLAH KABA TA TABBATA!

Suka juya zuwa cikin gari jikinsu a sanyaye,zuciyoyin su cike da alhini da d'acin mutuwa.

Malama Lamid'o da iyalinshi suka fito za su tafi.Julaibib yana tsugune a gabansu ya sunkwui da kai,kukan shar6e yake yi hawayen suna ambaliya a fuskar shi, ganin haka yasa Tukur yarik'o hannun Inna da take matsar kwallah zuwa mota"Inna zauna.Cikin dauriya Malam Lamid'o shima yatsuguna yadafa kafad'arshi"kayi hak'uri Julaibib hak'ik'a wannan mutuwar babu wanda ta dake su kamarmu iyayanta da kai,to duk mu d'auki hak'uri kowa zaman jiranta yake yi,tabbasss da ina da wata 'yar bayan Bilkisu to dana ba ka, amma zan cigaba da maka addu'a"ALLAH yaba ka wacce tafi Bilkisu,yayita rarrashin shi sannan sukayi sallama dasu Baba.Tukur yaja mota suka tafi. Julaibib yabi bayan motar da kallo har tasha kwana ta6ace ma ganin shi sharrr...sharrr...wasu zafafan hawaye suka zubo mishi. Yakad'a kai cikin maimaita Istirja'i.

Bayan sallar magriba Inna ta kawo mishi kunun tsamiya da kosai.Julaibib daga dawowa daga masallaci sai kuma ka kwanta? Tashi kayi bud'a baki mana.Yamik'e zaune dak'yar dan kanshi na wani sarawa "Inna bana jin yunwa cikina ya cunkushe kamar na ci abinci"Tajijjiga kai"na sani D'ansarai to amma dai ai ka san an umarce mu da gaggauta bud'a baki,azumi fa kayi daure kaci dabino kaji... yakar6i guda d'aya haka dai yaci amma wallahi baiji d'and'anon shi ba dakyar ya had'iye.

Malam Abdullahi yashigo shima yazauna yadafa kafad'ar shi"Malam D'ansarai ai wannan lokacin yana d'aya daga cikin lokutan amsa addu'a,to ba sai kayi amfani da wannan damar wajan rok'ama Magado gafara dama kai kanka ba?Duk da yana cikin damuwa amma sai da yad'anyi yake ganin yadda suke ta rarrashin shi Inna wai ita sai ta bashi kunnun ma abaki wallahi kuma yau a d'akin baccin ta za su kwana tare "Karki damu Inna zan sha amma sai zuwa anjima kin san ba sosai nake cin abinci daga shan ruwa ba.Eh haka ne ,tamik'e ta barshi da Baba.

Washe gari su Julaibib da iyayan su motoci guda uku sukayi dan zuwa Matsirga ta'aziyya sun tafi da manyan kololin shake tam da abinci ,kullum sai sunje har sai da akayi addu'ar uku.

Yana rik'e da agogon da aka cire a hannun Bilkisu lokacin da za'a mata wanka sai jujjuya shi yakeyi,tunaninta da irin hirarra kinsu ya cika k'wak'walwar shi"Bilkisu a very meek damsel ta tafi ta barshi,burin su na zama ma'aurata bai cika ba.

"Sai na kira...

kalmar da suka fad'a ma juna ta k'arshe shi da ita kenan,sai sak'on muryar data turo mishi,yasake kunna sak'on muryar yana sauraro a karo na barkatai sau shurin masaki,ya kad'a kai"uh uhun mutuwa rigar kowa...

Sudaida tashigo tana kallanshi cikin zancen zuci"shi ko wani irin so yakema wannan Bilkisun?Kullum taganshi sai taga ya dad'a ramewa,tausayinshi yamamayeta dan ba ta jin dadin ganin shi a haka,itama tayi nadamar abinda tadinga ma Bilkisu wanda ita Bilkisun ko a fuska bata ta6a nuna ta ji haushi ba"Yaya Julaibib dan Allah kayi hak'uri,kaga yadda kake ta ramewa? Yad'an kalleta"to nagode.Ta ajiye rediyon tafita. Inna tafio daga D'akin-girki tana kallanta tana sa takalmi"ba dai tafiya za kiyi ba?Tafiya zan yi Inna dan zanyi rubutun allo yau akwai darasu,amma idan nagama zan dawo in sha fate na.To shikenan, ALLAH yamuku albarka"Amin Innarmu.

Malam Lamid'o yana zaune a d'akin zaure yajiyo sallamar Julaibib.Yafito da sauri kaine haka?To maraba yashiga suka gaisa.Malam Lamid'o yace ikon ALLAH dama Tukur nake jira yadawo anjima za muzo wajan na ku.Ya amsa cikin girmamawa"Malam shi yasa ma nazo dan Baba yafad'a min yadda kukayi ta waya"Indai za kuzo ne dan kawo wani abu game da kayan auran Megado to kubari.

Malam Lamid'o yagirgiza kai"sam-sam baza ayi haka ba.Ya amsa cikin ladabi"wallahi Malam kome da aka kawo saboda Bilkisu na bar muku har abadan duniya arabama yan'uwa da abokan arziki bazan kar6a ba.Malam Lamid'o yayi shiru cikin jinjina wannan al'amari,sai kawai yad'auki wayar shi yakira Alhaji Abdullahi yafad'a mishi abinda Julaibib yace"Baba yayi murmushi "haba Malam dan D'ansarai ya ce haka har sai ka kira?Tunda yace ya bari to ya bari d'in ne,kutaya mu addu'a kawai Allah yabashi macen alheri.Ya ajiye wayar cikin sanyin jiki.Karka damu Malam Julaibib yafad'a."Julaibib ALLAH yamaka albarka,ALLAH yasa kagama da duniya lafiya, ALLAH yaba ka wacce tafi Bilkisu.

Yamishi jagora zuwa cikin gidan. Innan Bilkisu tana ganin shi tafara kuka,ya sunkwui da kai cikin wani irin yanayi,ga tausayin ganin yadda Innar Bilkisu ta zabge,tayi bak'i, idanun ta sun k'ank'ance saboda yawan kuka"Inna kiyi hak'uri Bikkisu ba kuka take buk'ata a wajan muba,addu'a tafi buk'ata.Inna takad'a kai cikin hawaye "kaiya d'an nan ba kukan rabuwa da Bilkisu nake yi har yanzu ba,ina kuka ne saboda wata rana za a manta da Bilkisu wajan yi mata addu'a kaasatan(a ke6e) saboda bata bar baya ba,dama Ya'ya sune duk rintsi baza su gaji dama mahaifa addu'a ba,har sai ranar da suma suka koma ga Ubangiji.Yajijjiga kai haka ne,to amma Inna ya zamuyi da hukuncin Ubanguji?ALLAH bai k'addari za tayi aure ba, bare har ta haifi Ya'ya,Inna duk hukuncin Ubangiji akan bawan shi adalcine,duk da bata haihu ba to ai akwai sadakatul-jariya,sadaka me gudana kamar mutum yana raye adoron duniya ni zan je cikin k'auye inda duke wuyar ruwa zan gina mata rijiya...Malam Lamid'o yatari numfashin shi"a ah basai ka sake kashe kud'in kaba kabari kawai tunda kabar mana kome to zan gina mata da kud'in sadakinta...Inna tafashe da kuka ALLAH yabaka wacce tafi Bilkisu d'an nan, hakika kai masoyin Bilkisu na gaskene dan ka nuna mana haka duk da

Please Login or Register in order to submit comment