Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata cikin doron duniya.

Idanun shi suka kad'a jawur"ni gobe zan koma wajan bautar k'asa dama sallama nazo muyi sai an kwana biyu,suna sallama Bello yashigo da gudu yana haki yana dariya"Yaya D'ansarai ina dabinon ajwa na da inibi na?Suka zuba mishi idanu ba abinda yadame shi sai tsallan shi yakeyi"k'uruci dangin hauka.Yamik'a mishi ledar daya shigo da ita a hannunshi.Yakar6a cikin tsallan murna"Yaya D'ansarai nagode ya k'ank'ame ledar akirjin shi"to yaushe zaka dawo? Yakalleshi da kulawa"zan dad'e ban dawo ba. Bello yad'an zaro idanu"kaiii kaima irin tafiyar da Adda tayi za kayi?Inna fa tafad'a min wai ita baza ta sake dawo wa ba sai dai muje mu same ta,ni fa shi yasa baza ni ba,kai ai za ka dawo ko?Insha-ALLAH Bello... Idanun Julaibib suka sake kad'awa jawur ya tuno da Bilkisu da take cewa gobe fa zan dawo Insh-ALLAH... Cikin wani irin yanayi suka yi sallama yaja motar shi yatafi,ya dad'e a Water-fall d'in Matsirga yana kallan ruwan yadda yake gudu cikin Qudirar Ubangiji ba dare ba rana shekara aru-aru.

Sagir yafito da gudu yana kiran shi" Yaya Julaibib wai katsaya.Inji wa?Yana hakin gudun da yayi yace"inji Yaya Sudaida.To ya shiga mota ya zauna yad'aura belt,k'afarshi d'aya tana waje.Tak'arsso wajan yana waya,wucewar wasu dak'ik'u sannan yagama wayar ya ajiye a gafenshi sannan yad'an kalleta kince in tsaya me zaki bani? Tabud'e gidan baya ta ajiye mishi wata madaidaiciyar leda ruwan hoda"Donut na maka, tarufe murfin tadawo wajanshi,wallahi tausayi yake ba ta duk yayi sanyi dama shi bame san hayani bane"sai yaushe zaka dawo?Ba rana sai dai kun ganni.Idanun ta suka cika da kwallah"dan ALLAH Yaya D'ansarai ka dinga cin abinci kaga yadda kazama kuwa?Ina cin abinci mana Sudaida ai d'an Adam bazai rayu ba abinci ba.Tad'an marariraice"to amma dai d'an tsakura ka keyi, kadinga ci dayawa,yamaida k'afarshi cikin motar tarufe murfin.Nagode Sudaida.kadinga cin abinci kaji?Tasake fad'a.To ya fad'a a tak'aice. Tasunkuyo"Allah ya kaika lafiya.amin Sudaida yaja motar tabi bayan motar da kallo har yayi nisa ya6ace ma ganinta,wani abu na mata kai-kawo a zuci,tasauke numfashi tabaki ta hanci sannan tajiya zuwa cikin gida ran ta ba dad'i.

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar alhamis suna cikin hutun makarantar boko na ranar yara(Children's day)kuma yau ba makarantar allo ba Islamiyya kowa yana abinda yake so ne, dan duk sun gama ayyukan gida.Tana kwance ranta ba dad'i tunda Julaibib yatafi sau uku kawai sukayi waya yauma takira shi sama-sama suka gaisa yakatse,tasake kira yad'aga da sallama"Yaya Julaibib na maka laifine? A ah baki min kome ba.To me yasa kike min wani iri? Yad'anyi murmushi"Sudaida kenan ni ban miki wani iri ba fa zan shiga aji ya katse wayar...Tayi lamooo a gadan,tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta ta rasa na za6a tayi.

Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu kamar yadda suka sa ba,suka kalleta suka kwashe da dariya"Sudaida uwar tafakkuri (tunani)me kuma yafaru?Khausar ta ta6e baki tabud'e wadrobe ta d'auki kayan da zata goge a D'akin-shak'atawa tafita...Bata basu amsar tambayar su ba,takalli Zainab"ya maganar bikin saukar mu?Ta zauna a gefan gadan"ai Malam yayi tafiya sai ranar asabar zai dawo.A'isha tamik'e "barinje muk'arasa kallan mu dan yau bazan dad'e ba,angona Hashim anjima yana hanya.Nasmat tad'an daki kafad'arta"to gaggawa hannu hagu a romo mutumin da ko tasowa bai yiba.suka mik'e ita da Zainab.Nasmat tabi da Sudaida da kallo "dan ALLAH me yake damun kine?Tamaida kanta saman matashi"na fad'a miki ba abinda yake damuna to ki rabu dani mana.Sudaida na damu dake shi yasa nadamu da halin dakike ciki. Tamaida idanun ta tarufe...Nasmat ki kyaleni bana san hayaniya fa.Tamik'e ALLAH yabaki hak'uri, amma ina zargin wani abu koda yake...sai tad'an motsa kafad'a shikenan can da yawarki yarinya.

Sai da aka cinye zangon karatu d'aya sannan Julaibib yazo gida.Yau alhamis ranar da ake bikin saukar Alqur'ani me girma nasu Sudaida,kome an shirya shi cikin mutunci, bangaran maza daban na mata daban Liman yabud'e taran da addu'a yama daliban addu'a Allah yasa suyi amfani da abinda aka koya musu a kowani irin hali da yanayi suka shiga na rayuwa...aka biyama d'aliban allunan su sannan aka cigaba da wa'azi da fad'akarwa akan neman ilmi dan shine yake sanya rayuwa tayi kyau tayi albarka.

Bayan angama kome sannan aka shiga yin hotuna da rabama d'alibai kyaututtuka aka rufe taro da addu'a,Sudaida tasunkwui da kai abinda yaba mak'alallun k'wallan cikin idanun ta damar zubowa k'asa sharrr... wannan taran me tarin albarka mutane da yawa sun halacceshi amma banda Sinan,to me ya hanashi zuwa tunda ya sani?Tayi kwafa wallahi za mu had'u ne.

Tana d'ago kai,caraf idanun su yahad'u, wani sanyi dad'i taji a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar ta. Alk'asim yak'araso wajan "gaskiya yan matan nan kun had'u,zai mik'a ma Sudaida rufaffen envelop A'isha takai hannu za ta kar6e,yajanye hannunshi da sauri"a ah ya haka? Tagyad'a kai"eh haka nake nufi,kai kaga hakan zata sa6u bindiga acikin ruwa? Wasa tare ci bamban?Khausar tace ko muma abamu ko itama tarasa. Yayi yar dariya "mata problem kunga fa ba wani abu bane a ciki,rubutune kawai akayi da biro bulu.Eh koma dai menene to abamu na mu. Nasmat ta katseshi"to wai ma yahaka?Ana zatan wuta a mak'era sai ga ta kuma a masak'a?Wallahi wanda nayi hasashen zai bata kyautar kaasatan bai yiba sai kai?Yamaida envelop d'in aljihu "shikenan karku samu damuwa za kuji a salansa, Sudaida sun hana in baki hannu da hannu zan aiko miki dashi gida,yajuya yayi tafiyarshi bai saurari hayagagar da suke mishi ba.Suka jera suna tafiya zuwa gidan Hajiya"Aisha tace wai me yahana Sinan zuwa wajan saukar mu,naga har Hashim daba d'an gari ba ya zo?Tawatsa hannu"nima ban sani ba amma ina ga kamar ba k'alau ba.

Dayammacin ranar sai ga shi da kaya nik'i-nik'i lemukan gwangawani dana kwali, yana zaune a dakalin k'ofar gidan tafito cikin fushi Sagir na biye da ita da kayan,takar6a ta ajiye mishi "Sinan ba wad'annan nafi buk'ata ba,zuwanka wajan ya fi duk abinda za ka bani. Tajuya...Yasha gabanta da sauri yahad'a tafukan hannayen shi da sigar rarrashi"Sarauniyar Sinan kiyi hak'uri "Tagirgiza kai"ban hak'ura ba sai ka fad'a min abinda yahana ka zuwa.Yad'anyi jimmm... na wucewar wasu dak'ik'u"za ki yadda dani?Tayi shiru sai yacigaba"to ni dai na san na miki laifin da ban ta6a miki irin shi ba,Sudaida baccine yayi awan gaba dani,to ya zanyi?To wayar ka amfanin me takeyi na kira ka sau shurin masak'i baka d'aga ba,sai kace me baccin mutuwa? Yakad'a kai cikin damuwa"lallai na cancanci abani horo,itama fa wayar a yanayin shiru nasa ta,kiyi hak'uri Sudaida "ALLAH yana san masu hak'uri,masu had'iye fushi, suna da dama su rama abinda aka musu amma sai suke hak'ura su yafe,su maida kome ba kome ba saboda ganin girman ALLAH...yacika da dad'ad'an kalamai har sai da yashawo kanta. ALLAH da gaske ke nake so Sudaida alk'awari ba karyawa ni da ke sai mun zama abin kwatance mutu ka raba takalmin kaza. Da haka yaba Sagir kayan yamayar dasu cikin gida..

Kwana biyu da fara azumin watan ramadan yashirya shi da Musaddiq sai Matsirga. Inna tana zaune a d'aki taga ana shigo da kayayyaki tasa hijab tafito tsakar gida tana tambayarsu daga ina wad'annnan kayan? Sai ga Bello yashigo da murnar shi yana fad'a mata su Yaya Julaibib ne.Jikinta yayi sanyi tabi kayayyakin da kallo cikin zancen zuci"wato k'auna ta gaskiya tana d'orewa koda ba wanda ake k'aunar a doron duniya. Bello yarik'o hannunta "Inna na shigo dasu. Tayi murmushi"lale maraba,sannunku da zuwa bismillah tajuya zuwa cikin d'aki suka bita,cikin girmamawa suka gaisheta"Iyayan na ku k'alau ko? A lafiya k'alau Inna suna gaishe ku.To madalla ALLAH yamuku albarka,ku bakwa gajiya da hadima?Musaddiq yace"haba Inna ai bakome... yiwa kaine.To Ubangiji yasa ka muku da mafificin sakamakon shi;ALLAH yasa hakan amizaninku na kyawawan aiyuka. Amin,amin Inna.

Inna su Malam basa nan ne?Eh d'azu shi da Maude suka tafi Zango wajan k'annin mahaifanshi,Tukur kuma jiya yakoma makaranta. Suka d'an ta6a hira sannan suka mata sallama taciko musu jarkoki da kindirmo da manshanu, Bello yasa kuka shi dole sai sun tafi dashi Inna tayi-tayi ya zauna amma ya kafe ya nata ihu shi dai zai bi su,duk yamak'alk'ale Julaibib ya 6ata mishi farar shaddar da yasa da majina da ruwan hawaye,yarik'o hannun shi.

Inna bari muje waje muyi magana tabisu da kallo,a mota suka dinga rarrashin shi "kaga idan muka tafi dakai Malam bai sani ba idan ya dawo zaima Inna fad'a muma zai mana fad'a, yamak'ale kafad'a"uh uh ai idan tace kaine bazai yi fad'an ba,kuma kana da waya kafad'a mishi na san zai yadda,ni dai kawai ALLAH mutafi"to naji na kuma maka alk'awari idan aka samu hutu Insha-ALLAH zan zo in tafi dakai Zonkwa.Yad'ibo dabinon ajwa da yawa a aljihunshi idan ka yadda sai in bar maka wannan dabinon,yakalleshi sannan yakalli dabinon" to duka zaka barmin?Yayi murmushi"eh mana sa hannunka ka kwashe ma, yana ta d'auka da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai yana sawa a aljihunshi har ya kwashe duka sannan yayi dariya aina kwashe, to sai ka zo d'in barinje in nuna ma Inna,yauwa Bello mutumin kirki barin rakaka,har ciki ya kaishi ya kuma fad'a mata yadda sukayi tayi murmushi kawai sannan suka sake yin sallama sunama juna asha ruwa lafiya.

Rana ta tafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai,an kusa shan ruwa takashe rediyon da take sauraran tafsirin Alqur'ani me girma a gidan rediyon jahar Kaduna(FRCN)farin gida kafin Sardauna.Tayi doguwar hamma tasa tafin hannun dama tarufe bakin ta, tana Isti'aza yau ba laifi tana jin azumin nan ajika dan ma yau Khausar ce da aiki da wallahi bata san yadda za tayi ba kanta har barazanar ciwo yake yi,daga can D'akin-girki tajiyo kiran Umma tamik'e da sauri tafita.

Umma gani.Umma tamata wani kallo "ba tun d'azu nace ki d'auki dabgen Hajiya ki kai mata ba?Baki ji bane ko zuwan ne baza kiyi ba? Tad'an sosa kai Umma fa boss ce,bata d'aukar raini ko na sisin kwabo"Yi hak'uri Umma barin d'auko hijab,tasa hijab ta d'auki kwanan samiran sannan tad'an kalketa cikin shakka"Umma dan ALLAH daga nan zan biya gidan Inna.Tayi shiru kamar bata jiba sai da tagama zuba wani dabgen a wani samiran ta rufe sannan takalleta"adawo lafiya suma ki tafi musu da wannan.Wani murmushi yasu6uce mata dan ba k'aramin aikin Umma bane tahana"nagode Umma tarik'o hannun Hanifa'yar Musaddiq ta fari suka tafi.

Tana shiga sai ga Nasmat itama takawo ma Inna hadaddan kunun aya kafin a kira sallar magriba sunyi alwala,ana kiran sallah sukaci dabino da lemun 6awo da ruwa me rangwamen sanyi sannan suka tada kabbarar sallah.

Julaibib da Baba suka shigo da sallama sukama juna barka da shan ruwa sannan ya ajiye ledan hannunshi a gaban Inna.Nasmat tajawo ledan gabanta tafara shan abarban da yake ciki da kankana yankakku tana fadin"kyan rawa da makar6i.Sudaida ma tasa hannu ta d'auki kankana tana cema Hanifa sa hannu ki d'auka...Baba yayi murmushi ganin irin kallan da yake musu,yayi k'wafa yajuya zuwa d'akin shi Inna tana mishi dariya itama.Sudaida ta ka sa cigaba da sha, ranta ba dad'i har yanzu bai dawo yadda tasan shiba, ba wani kyan gani da yayi,yabar k'asumba ba wani gyara,kana mishi magana zai bika da wannan rikitaccen kallan,ya ya6a maka bak'ar maganar da ko barinje (mahauci) iya karta kenan.

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba yana nazarin wani littafin tafsirin Alqur'ani me girma Hajiya tashigo da sallama,yamik'e da sauri yataro ta"maraba da zuwa Hajiyar mu,ta ture shi"kai tafi can matsa kabani waje,ta zauna a kujera tana murza k'afafunta,ya d'auko man zafi zai shafa mata tajanye k'afafunta da sauri"bana so.Yayi murmushi"haba Hajjaju makkatu wal madinatu gwiwata a k'asa,kaina bisa wuyana.Oho ashe kaima ka san kayi laifi,saboda ALLAH Julaibibi tunda kazo garin nan sau d'aya rakkin rak kazo gidana,ba fad'a to me yakawo wannan gabar? Kiyi hak'uri Hajiya bana jin dad'i ne.Tajijjiga kai tana mishi kallan nazari"kai Julaibibi tunanin Bilkisun ce yake susuta ka haka?Yagirgiza kai "haba dai Hajiya ba wannan bane.

Yamik'e da sauri ya d'auko madara da maltina da kofi.Hajiya tabishi da kallo cikin mad'aukakin mamaki"ciwon har yakai ba ka iya yin azumi ne Julaibibi?Yadafe kai "Innalillahi.Ina yi, wai dama ke zan kawo ma na man tane.Tamik'e wa?Ni kaga tafiya ta.Yarufo gidan"barin taka miki suna tafiya suna hira"anjima da daddare zan zo miki hira sai ki tanadar min garwashi zan zo da d'anyan masara in gasa mana"To ALLAH ya kaimu har gidan Kawun shi yakaita.

A D'akin-shak'atawa Sudaida ce kawai tana kwance a doguwar kujera tana waya,tamik'e zaune saboda shigowar su,kusan dak'ik'u goma sannan tagama wayar,tad'ago tana kallan Julaibib bayan ta d'ora ha6arta a kafad'ar Hajiya"Hajiyarmu you're welcome.Kin san abinda bature me jan kunne yake nufi da haka?Tajijjaga kai"tun kafin in haifi uban ki ya haifeki kuwa.Tad'an turo baki, Julaibib yayi murmushi yana shafa k'wantaccen bak'in gashin kanshi"Yo kya 6ata fuska ba tambaya kikayi nabaki amsa ba?

Mu turancin mu ma gangariya masu abu da abun su kura da kallabin kitse, turanwan ne fa suka koya mana baki da baki,To me yasa bakya yi?Tad'an kalleta kaji wata magana to yaran turanci yarena ne?Ni yarene hausa idan takama ayi turan cin inayi mana"do you get me? Sudaida takyalkyale da dariya saboda yadda Hajiya tayi furucin tagyad'a kai"yes grandam.Su Mama suka shigo suna gaishe da surukar ta su cikin girma da mutuntawa.

Da daddare yana gidan Hajiya suna hirarsu takalleshi"tunda katafi Azare kayi zaman ka shiru ba amo ba labari ko wata bafulatanarce takuma rik'e mana kai?Ya jujjjuya masarar sannan yad'ago yakalleta"ko d'aya Hajiya.To in dai haka ne ya kamata ka nemi wata,ga yan mata nan burjik a cikin dangi sai ka za6a ka darje,kana gani ganin idanun ka Musaddiq Ya'yan shi biyu ga cikin na uku nan.Cikin wasa yace"Hajiya banga wacce nake so ba ko za ki tayani nema?Tagyada kai"anyi an gama maye ya auri makauniya.Bai wani dad'e ba yamata sai da safe, saboda akwai tashi cikin dare domin yin munajaati ga ALLAH buwayi gagara koyo ga kuma tashi yin sahur.


K'arfe-k'arfene sai dai a cikin k'arafan akwai zinare da azurfa.

Idan baka san gari ba...saurari daka.

Abdullahi Lawal Abdullahi (D'ansarai)
Saudat Ibrahim Yahya (Takwara ta)
Mungode da tunatarwan ku bisa wani kuskure da mukayi a shafi na goma sha biyar..

Falmata Maiduguri mungode da kulawa.

28 Jumaada Awwal 1441
23 January 2020

We Ibrahim's Daughters 👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.



DANGIN NONO WRITERS ASAOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}




Bismillahi wabihi nasta'in




...GWAJIN DAFI💔




Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'iba)



Shafi nagoma sha bakwai.


Bayan sallar asham Julaibib yawuce gidan Hajiya anan yatarar dawasu daga cikin jikokinta maza anata hira da ciye-ciye.Yajawo kaskon data cika da garwashi gaban shi, Musadduq yaja tsaki"Lillahi warasulihi yauma karasa abinda za ka kawo mana sai bushashshen masara?Kai ALLAH yasauwake.Ya amsa da amin "dan ka kawo mata bushasshen nama wai shi kilishi ba shi zai hanata cin gashashshiyar masara ba.Musaddiq yagirgiza kai"kai Malam ai yanzu ba lokacin cin kilishi bane,watan ramadan muke gasassun yan shila nakawo mata me ruwa-ruwa da yajin tafarnuwa ya ji kayan lambu.Yaturama Julaibib k'unshin duba kagani.Yayi kamar ba dashi yake magana ba yafara gasa masararshi yana tambayar Hajiya ta saurari tafsir na karfe uku da yammacin yau?

Kwanci tashi har anyi azumi takwas, agida tasame shi yana shirin komawa Azare "tazauna tana kallan shi"Yaya D'an Sarai tafiya ba sallama?Yacigaba da shirya kayan shi a jaka ba tare daya d'ago ya kalle taba"ai naje gidan akace kin tafi Hayin-Dogo"haka ne to yaushe za ka dawo? Yarufe jakar yad'auki agogo yana d'aurawa a hannun damar shi"sai ALLAH ya kaimu sallah idan muna raye,ta taya shi kwashe kaya zuwa mota yayi sallama da Inna suka fito,tajingina da motar tana kallan shi cikin kissima wani abu a zuci yana zuba ruwa a lagireto har yagama yashiga mota yazauna yana d'aura belt.

Yad'anyi murmushi"duk kinyi wata iri ko za ki bini ne?Ta turo baki gaba"da inada wannan damar ai da ba haka ba wallahi.Baiyi magana ba,yabata wasu kud'i"bayawa.Tasa hannu biyu takar6a"nagode Yaya D'ansarai ALLAH yak'ara bud'i,suka d'aga hannu suna ma juna adabo.

Sun dawo makaranta suka tarar da Asma'u kanwar Sudaida ta ci kuka ta gode ALLAH idanun ta sun kumbura sun kad'a jawur"lafiya Asma'u? A tare suka tambaye ta,sai tasake jin wani sabon kukan ya kufce mata tafi minti goma sannan tafara rage sauti tana ta jera ajiyar zuciya"ke wai kukan me kike yi ana tambayar ki kin ma mutane shiru wacece sa'ar ki anan? Khausar ta tambaye ta.Taja majina tana hura iskar bakin ta"labarin zuciya a tamabayi fuska ranta in yayi dubu ya 6aci,cikin hawaye tafara magana"wai arasa wanda za a bani a matsayin mijin aure sai Yaya D'ansarai...wasu hawaye masu d'umi suka sake zubowa sharrr...sharrr...Sudaida tamik'e zaune da sauri kamar za ta hantsila,duk suka bita da kallo ganin yadda tayi sai kuma ta koma ta kwanta batayi magana ba dan ta ma rasa abinda za ta fad'a wallahi.

Asma'u tacigaba bayan kowa ya san Alk'asim nake so amma ance a ah wai shi yaro ne ko Secondary bai gama ba,takad'a kai cikin takaici"saboda ALLAH wai Yaya D'ansarai. Khausar takalleta cikin natsuwa"bakya san shine? Dasauri tace"eh mana me zanyi dashi bak'ink'irin dashi kamar bak'in gashin kanshi...bata gama rufe baki ba taji saukar mari hagu da dama"Yaya D'ansarai kike za gi?To dame kwad'o yafi gaya?Ba gwamma shi bak'i kyakkyawa bane.Asma'u tamik'e cikin hawaye"amma wannan rashin 'yanci da yawa yake,ga mari ga tsinka jaka?Takalle ta "wallahi Yaya Sudaida bana san shi,tafita a d'akin da gudu cikin shashshekan kuka.

Tadunk'ule hannu ta naushi iska"da kin tsaya k'aramar mara kunya da kinga yadda zan yi dake.Khausar takalle ta"ai baki isa ki kuma dukan taba akan me? Dan tace ba ta san shi shine ya zama laifi?Yaya Julaibib d'in?Kwarai kuwa shi wanene da kowa sai ya so shi so?Wa kika ta6a gani ko jin labari kowa na doron duniya ya so shi? Ko wanda yayi mu an samu wanda basa san shi ta hanyar k'in yadda da duk abinda yace ayi,da wanda yace abari,bare wani Julaibib ordinary human being,ai dama na dad'e ina zargin wani abu bani da tabbasss shiyasa naja bakina nayi shiru; to amma yau na samu yak'ini san Julaibib d'in nan ki keyi,to dake dashi d'in duk sai kuje kuji da manufurcin ku,ai shima ina lura da takunshi akanki.Yaya Khausar daza kice haka shi kuma Sinan d'in ina zan kai shi?Tawatsa hannu"ke kika sani...

Cikin bugun zuciya tafara harhad'a littafan data barbaza a kan gado da niyyar yin nazarin su,ta tsuke baki tana yamutsa fuska Khausar tayi yar dariya tana rage kayan jikinta za ta shiga wanka Asma'u ta D'ansarai bak'ak'e biyu kila za su iya samar da wankan tarwad'a ko fari ko sarauniyar Sinan?Bata kula taba tamak'alama wayar ta earphone tana k'ok'arin toshe kunnuwan ta dashi. Khausar ta fizge"ke malama kirufa mana asiri karki zama kanwar kurma,so nawa ni da ke munajin bayanan da likitoci k'wararru a bangaran kunne,mak'ogwara da hanci(E N T) sukeyi,yawan amfani da earphone yana kawo matsala a bangaran ji"tagyad'a kai "naji bani wayata.Tamik'a mata, kita shi kisan abinda za ki d'ora tunda su Mama basa nan ko miyar shuwaka za ki mana mun kwana biyu bamu ciba wallahi,ta san Sudaida bata so dan tayi tsokana tafad'a. Yaya Khausar"ai bazan hana kiyi idan kina so ba"kuturu da kud'in shi alkaki ba sai na k'asan kwano ba?Gaskiya ne to d'anje kifara wanke min shuwakar kafin in fito wanka.

Kwana biyu da maganar ranan Asma'u ce da aiki tasame ta a D'akin-girki tana kad'a miya sai ta kar6i maburgin barin taya ki,Asma'u tad'anyi murmushi "Yaya Sudaida saboda ALLAH ko kuma cin tuwon kishiya...?Duka biyun.Sukayi dariya, Asma'u tana zuba mata garin kuka tana cigaba da burgawa har suka gama, tad'an jefa kanwa kad'an wucewar wasu yan dak'ik'u tasauke to d'orama Yaya Aminu ruwan da zata dama mishi custard aranta tana mita"gaskiya Siddika ta shiga uku da shan kunu,ga fa kunun tsamiya can Inna ta aiko mai dashi amma duk da haka wai dole-dole sai ta dama mishi custard,ruwan yana tafasa ta dama tajuye mishi a flask.

Tamatsa gefe tana cema Asma'u ai dai na taya ki,dan haka zo ki dora ruwan tuwon ki. Takalli Asma'u da natsuwa bayan tad'ora ruwan "waye yace za a ba ki Julaibib a matsayin mijin aure?Tayi d'an tsaki"na manta.Kin manta?Eh,to ban sa a ka ba inji 6arawon tagiya,sai kuma tayi kwafa"ba Hajiya ce da wannan neman maganar ba,haka kawai ga wanda zuciyata take marari... Tad'auki flask batace kome ba tajuya tafita. Asma'u tabita da kallo"yauma kinji haushi dan na ce ba shi nake so ba ko?Tad'an motsa kafad'a,sai dai kiyita jin haushin me zanyi dashi?Tad'auko garin dawa za tayi talge dan har ruwan ya tafasa.

Littafan tane a saman tebur ta barbaza, nazarin su take so tayi d'aya bayan d'aya saboda ranar Litini za su fara jarabawa,tad'auki littafin lissafi tana dad'ayin nazari akan

Please Login or Register in order to submit comment