Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zama ciwo...ciwon da mutum zai zo yashiga wani mawuyacin hali na ni ya su.. Yakalle ta cikin natsuwa"ahab ba cinyaba k'afar baya...

Ni dai na fada'a miki ki dinga cin abinci"toh Yaya D'ansarai nahhh...tayi furucin da wani salo na yanga da shagwa6a.Suka kalli juna sukayi murmushi,bata gama shan raken ba ta ajiye dan yau tayi d'amarar hana karatun daren nan,shi dai kullum cikin bincike da nazari,a makaranta karatu a gida karatu?Rai ai dangin goro ne yana buk'atar ban iska...batayi magana ba kawai zama tayi a gefenshi ta gewayeshi,a hankali tafara mishi wani salo...salon daya tilas tashi ajiye littafin nazarin yafara bin yarima dan su sha kid'a.

Hantsi yadubi ludayi na alhamis bataje makaranta dan basu da lacca,tana kwance a doguwar kujera Hajiya tashigo da sallama, tamik'e zaune"lale marhabun Hajiyar mu,sannu da zuwa.Tasa hannu tad'auki ledar da Hajiya tad'ora a saman tebur"me nasamu haka? Tabud'e talek'a sai tasa hannu tad'auki guda d'aya awarar madarar shanu ce,tagutsira sannan takalli Hajiya "nagode ALLAH amfana.

Tanaci suna hira,Hajiya kuma tana ta kallanta cikin nazari dan yar shimice ruwan madara ajikinta,ta yi kyau sosai amma ta rame"ni wai ramar nan dakike dad'ayi to ko dai ciki ne dake?Sudaida takama ha6a"wuuu..ciki?Tad'an ta6e baki"uhun rufani ki saya.Hajiya takad'a kai"eh lallai ba shakka k'uruci dangin hauka,cikin ne kike neman tsari dashi?Ke ba a haihuwar aka haifoki? Ya'ya da kike ganin su ai rahamane jin dad'in rayuwa ne,su Khausar ba gashi har sun fara zuwa asibiti awon cikin ba.Tamaida bayanta jikin kujerar tana cin awararta"hu'un to ni dai Hajiya bani da wani ciki.Ai ban musaba"ALLAH na tuba shi ciki ai d'an dumane a hankali yake yad'o.

Julaibib yashigo da sallama yazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna da Hajiya"Hajiyarmu kin shigo?Ta amsa da eh Julaibibi.Yakalli Sudaida"lallai yarinyar nan,wasa tare ci bamban ko?Zanga me siyo miki rake anjima.Tad'auki ledar ta zauna a k'asa kusa da k'afafunshi"duba kagani,kaifa kake fad'in awarar madara bata dameka ba.Yad'auki guda d'aya"ai ba cewa nayi kwata-kwata bana ci ba.Tamishi wani kallo a marairaice"to afwan Zaujiii...yayi murmushi koma dai toshiyar baki kika bani yau dai baza ki sha rake ba,kema muk'amuk'inki su huta.Haba Zaujiii...kaima kasan"I can't do without sugarcane" tayi furucin da salon shagwa6a.Yamata wani kallo "au bama ni ba?Tasake wani narkewa"na rantse da girman ALLAH har da kai Yaya D'ansarai nahhh...Hajiya tagalla musu harara"oh Ya'yan zamani.Sudaida takalleta"da mukayi me kuma? Hajiya wai kin manta gidan amare kika zone?Hala kin manta hud'ubar dakika dinga manane a gidanki?

Takalleshi"Yaya D'ansarai kome tace mu muku indai bai sha6ama shari'a ba,ko menene shi bata togance ko abu d'aya ba.Hajiya tayunk'ura tamik'e"toh barin barku kuci karen ku ba babbaka.Shima yamik'e"Hajiya kiyi zaman ki,ni dama wayata dana sa a caji nashigo d'auka. Yacireta dan ta cika.Tagyara zaman hijab d'in ta"ai ba ganin ka yasani tafiya ba dama nayi niyya ne. Yasa wayar a aljihu"ALLAH huta gajiya Hajiyarmu sai nazo.Inji Sudaida.Tagyad'a kai"sai na ganki. Suka fita da Julaibib.

Bai dawo gidan ba sai da yamma tana D'akin-girki yamik'a mata raken"karki isheni da mita anjima.Tasa hannu biyu takar6a"shukran jazilan Ustazu. Yakalleta da sauri"au har dake? Yagyad'a kai tana yar dariya"har dani.Toh bar d'aura girkin nan kizo muje unguwa.Yaya Julaibib da wannan yammacin?Yad'aure fuska"ko da sulusin dare ne bazaki bane?Ta tsame hannunta daga cikin kayan miyar da take gyarawa"ALLAH yabaka hak'uri"ya amsa da amin.Kiyi sauri ki shirya ina jiranki a waje.Tabi bayanshi da kallo "zuciyar ta na raya mata wasu al'amura game dashi, takad'a kai"ALLAH yakyauta maka wannan halin wallahi.

Yana kallanta tafito amma sai da wasu dak'ik'u suka wuce sannan yabud'e mata motar tashiga tazauna tana d'aura belt.Ganin sun bar cikin gari yasa ta tambayeshi inda za su,amma yayi kamar bai ji taba.Itama sai taja bakin ta ta d'inke,tamaida bayanta jikin kujerar tare da lumshe idanun ta,tana sauraran wa'azin daya kunna na Ahmad Ibrahim(Bamba)sai da yatsai da motar sannan tabud'e idanun ta tana kallan wajen,nan kuma ina ne?Ta tambayi kanta"fito muje mana..taji maganar shi a sama,tafito suka jera zuwa gidan.

Inna tayi murna da ganin su kwarai, irin kambamawar data musu yasa jikin Sudaida yayi sanyi, wato su wasu irin mutane ne masu karamci da girmama d'an Adam,suna da shiga ran da ciresu a sararin zuciya bazai zama abu me sauk'i ba wai cire wando taka,shi yasa Julaibib yakasa mantawa dasu duk da babu wacce tazama sanadin had'uwar ta su a doron duniya.Inna tad'an kalli Julaibib"ai munyi waya da Bongel take fad'amin gobe zaka koma lallai abaka madara katafi musu da ita wai wanda suka tafi da ita sun tsaya a Gama-gira wajen wata k'awarta shine tabata duka,dama Maude nake sauraron shigowar shi in bashi yakawo maka ikon ALLAH kuma sai ga Ku.Ya amsa da ladabi"eh Inna nima ta kirani ta fad'a min,sammako zanyi a goben shi yasa nace barin zo in k'ar6a daga nan kuma Sudaida ta gaishe ki.Ai kuwa naji dad'i ALLAH yamuku albarka.Suka sake sabuwar gaisuwa da Sudaida tamata sannu da jiki.Jiki ai Alhamdulillahi naji sauk'i sosai.

Da zasu tafi Sudaida tace gashi ni dai nazo banga Bello ba.Inna tad'anyi murmushi"ai da ya san da zuwanki da bazai raka Malam Zango ba.To agaishe shi. Zai ji.Julaibib yamata alheri me yawa,ada tana damuwa da irin hidimar da yake musu har tazo ta daina,tun ranar daya kalleta cikin natsuwa da girmamawa"Inna ki d'auke ni matsayin d'a,idan kika d'auke ni a haka toh na san duk abinda zan baki zaki kar6ane da dad'in rai kina kuma shimin albarka tare da min addu'ar dacewa a doron duniya da lahira.

Megado ita tahad'a mu,koda ba ta, bazamu rabu ba dan kuma baku k'ini ba.Inna tajijjiga kai tasa gefen hijab d'in ta tana share kwallah"gaskiya ne d'an nan,toh ALLAH yamaka albarka,ALLAH yabaka zuri'a d'ayyiba,ALLAH yasaka maka da mafificin sakamakon shi, yasa hakan a mizanin kyawawan ayyukanka.Yanzuma irin addu'o'in data dinga musu kenan shi da Sudaida.Suna ta amsawa da amin,amin.

Gidansu Sudaida suka wuce...Sauran k'anninta suka dinga murnar ganinta,itama taji dad'i sosai dan basa wani zuwa gidan ta,to yaushe ma suke da lokacin yawo?Daga andawo makarantar boko za a tafi ta allo,ko ta Islamiyya da daddarene kawai suke da lokacin kansu,idan ma ranar ba a had'o mutum da aikin gida ba (home work)Tasaki hannnunsu,taje ta rungume Mama kawai sai tasa kuka,Umma,Julaibib dasu Asma'u suka bita da kallan mamaki yanzun nan fa tagama kyalkyala dariyar shirmen gwarancin da Nana take mata...

Mama tace ashsha"to me yayi zafi haka da idanu za suci wuta?Tana k'ok'arin d'ago ta Sudaida tadad'a k'ank'ameta.Umma ta fusata"ke menene haka yau naji shashanci rok'o a gidan bebe.Mama tad'aga mata hannu"na ki idanu 6arin mai a yashi.Umma takyalesu suna magana da Julaibib.

Mama tayi k'asa da murya"to d'agani tunda bazaki daina kukan ba.Tayi shiru tana share hawayen sannan tad'an marairaice "Dan ALLAH har yanzu baki zo na ganki ba,ai dama na san ke kad'aice za ki zo,ko Umma ce tazuga ki?Mama tayi murmushi"au dalilin kukan kenan?Eh mana Mama.To karki damu inanan zuwa ni ba wacce ta isa ta hanani zuwa inda kike.Yauwa Mama ALLAH yabar mana ke,suna ta hira sai da Baba yafito yace su tafi gida haka dare yayi gashi sammako Julaibib zai yi.Sudaida tabi Umma d'aki tafito daga bayi alwala tayi tanasa hijab Sudaida tashigo.Suka kalli juna sai Umma tad'anyi murmushi"za ku tafi ne?Ta amsa cikin ladabi"eh Umma.Kun san Umma Boss ce bata d'aukar raini.Tabata wasu humrah masu k'amshin fita hayyaci"gashi nan dama ke kad'aice ba a kai miki ba.Tasa hannu biyu takar6a tana godiya. Umma to yaushe za kizo? Ke! Umma tafad'a cikin d'an bud'e idanu.Sudaida tasunkwui da kai.Sai kuma ta sassauta murya"Sudaida me zanzo in miki ne?Duk abinda kike so kima Mama waya ko ni,ko ki turo mana ta sak'o a rubuce ba shikenan ba?A sanyaye tagyad'a kai sannan sukayi sallama.

Tafiyar Julaibib da yammacin ranar tadawo makaranta tana so tayi girki tatafi gidan Inna sai ga Asma'u tashigo.Tataro ta cikin murna 'oyoyo Yaya Asma'u sannu da zuwa.Ta amsa da yauwa tashige D'akin-shak'atawa,ganin haka yasa Sudaida tayi sauri tagama markad'a kayan miya taje suka gaisa,kamar kullum yau ma haka ta amsa gaisuwar cikin halin-ko-inkula tun bayan auren ta da Julaibib Asma'u take mata wani gani-gani data kasa gane manufarta.Tabi d'akin da kallo sannan ta sauke idanun ta akan Sudaida, tana sanye da riga da zani da dankwali na kamfala, ta ta6e baki"ina D'ansarai?Baya nan yatafi.Yatafi fa kikace?Tajijjiga kai"eh ya tafi.Toh yayi kyau... bani sak'ona sauri nake yi.Sudaida tagirgiza kai "bai bani kome in ajiye miki ba.Bata sake magana ba wayar ta taciro ta kirashi.Yana d'agawa ko sallamar daya mata bata amsaba tafara hayagaga...

kai D'ansarai haka mukayi dakai? Tayi shiru tana sauraranshi...wucewar wasu dak'ik'u sai kawai taja dogon tsaki"kai malami wallahi daga bayane sadaka da karuwa...eh to naji sai ta mik'a ma Sudaida wayar "Zaujatiii... kud'in dana baki kin kai gidan kud'in ne?(bank)A ah sai gobe Litini...Yauwa toh kiba Yaya Asma'u dubu goma a ciki,ki bar sauran idan nadawo nabaki duka sai ki kai kinji ko?To Yaya Julaibib, ALLAH yadawo dakai lafiya.Tamik'a mata wayar sannan take ta d'auko takawo mata,a wulak'ance takar6a kamar wacce aka bata najasa.

Sudaida takawo mata meatpie da lemu dan bata gama abinci ba.Tagirgiza kai"bani dankalin turawa da kwai zanje in soya a gida, tamik'e bani leda,inda suke ajiyewa ta nufa, Sudaida tabiyo ta da ledar tana fad'a mata amma fa kwan ya k'are.Sai tabi d'akin da kallo gwangwanayen madarar Nido tagari guda biyu dana Ovaltine guda d'aya sai siga me y'aya na kwali(cube sugar)sai tasa hannu ta d'auki gwangwanin madara d'aya da siga kwali biyu a ranta tana mita"ni nasan D'ansarai baya shan shayi da madara,yanzu nan ita za taita shansu? To aiko bazata shanyesu ita kad'aiba dan nima wannan ai yafi min dankalin.Sudaida tabita da kallo itama tana jiinjina k'arfin hali fin me kora shafawa irin na Yaya Asma'u.Toh sata za a kira wannan abun kome?Tunda bata tambayi wanda yasiyo ba.

Abinda Yaya Karima bata dashi kenan ganin gari da san na Bello-badin,ko wajen Inna taje haka take mata d'auki d'ai-d'ai d'in duk wani abu daya bata sha'awa,abin mamaki kuma Baturiya da suna manga,kamar ba Inna da Baba ne Iyayen taba dan su sun san mutumci da karamci wallahi.Idan an mata magana ta ta6e baki tana fad'in to menene a ciki? Sata a gida ai rance ne...bare ita ai bama sata tayi ba tunda a gaban idanu take d'aukar abu.To amma dai ai ba ace an ba taba kai ALLAH yasauwake. Takar6i ledar tasa a cikin sannan tajuya"sai anjima.To Yaya Asma'u ki gaida gida.

Kwana biyar bayan nan da yammacin la'asar tadawo daga makaranta kawai tawuce gidan Inna. Asma'u tana zaune tana cin dafaffiyar masara takalli Sudaida sama da k'asa bata amsa gaisuwar da take mataba,sai tambayar ta tayi"hala daga awo kike? Fuska a d'an yamutse dan tafara gajiya da irin abubuwan da Asma'un take mata tace"awon me? Asma'u tamata wani kallo me kama da harara "awon me mata suke zuwa yi a asibiti? Tamotsa kafad'a tare da watsa hannu"oho nima ban sani ba tunda ba ta6a zuwa nayi ba.Tawuce randar Inna tad'ibo ruwan sanyi,tashiga D'akin-girki tazuba abinci, tayi bismillah ta faraci.

Inna ta idar da sallar la'asar tajuyo tana shima Sudaida albarka"kin kyauta dakika bata wannan amsar.Ke Asma'u tanuna ta da yatsa"me yasa kike san zama babbar kwabo ne?Asma'u tamik'e"to yanzu Inna me nayi?Ni fa dama kullum a gidan nan a ban iyaba aka d'auke ni.Eh ai halinki yake ja miki.ALLAH yabaki hak'uri Inna ni tafiya ma zanyi,me zaki bani?Inna ta d'aure fuska"ba abinda zan ba ki sai dai in omon wanke-wanken da kika kawo min za ki koma dashi.Kai Inna haba-haba dai,tashige d'akin bacci tana fad'in"ni ai na ga abinda nake so,sink'in sabulu da man shafawa guda d'aya ta d'auko. Inna takalle ta"Asma'u na ba ki ne?Tayi yar dariya tana turawa a jaka"Inna kayan ALLAH ai na annabine,ba sid'i ba sad'ad'a ma kinyi kyauta ga wasu bare kuma ni?Tajuya na tafi Inna,idan Baba ya dawo a gaishe shi.Suka bita da kallo kowacce da abinda zuciyar ta ke rayawa.

Kwanci tashi a sarar me rai...Shekara d'aya da auren su A'isha,Khausar da Nasmat ne suka fara haihuwa,A'isha da Nasmat rana d'aya,ranar suna Sudaida tarasa inda za tayi ga makaranta,ana tashi Kafanchan tawuce gidan A'isha aka sha suna,ba ita taje gidan Nasmat ba sai da akaci aka kusa cinyewa dan ma na ka na kane...a yadda tagaji lik'is d'in nan,gida za ta tabi lafiyar gado.

Tak'arema jaririyar kallo tad'ago cikin murmushi "ALLAH na rasa da wanda tayi kama,ranar da aka haife ta sak babanta yau kuma ta canja batayi kama da ku ba, tamaida ita k'irji ta rungume ta lumshe idanun ta"ina son yarinyar nan ki bani ita mana.Nasmat tayi murmushi"ai dama ta kice na kuma bar miki.Tabud'e idanun ta suka kalli juna sukayi dariya.Nasmat ta kalle ta"d'azu dangin mijin ki bakiji irin habaicin da suke yi ba wai wasu sai dai suci su juye shi a masai,wani abin mamaki kuma Yaya Asma'u itace shugaba,sai da Hajiya ta musu wankin babban bargo sannan sukayi shiru.Sudaida ta d'auki kunun aya tana sha"kar ki wani ce abin mamaki,yau kika san Yaya Asma'u da halinta?A ah ai ni abinda yabani mamakin shin ke d'in ba matsayin kanwar ta kike ba? Tad'anyi murmushi"da ne nake kanwarta lokacin ina gidan mu,toh yanzu kuma ai k'aninta nake aure ina zaune a gidan shi,ita kuma dangin miji ce,wasu dangin mijin kuma ba mutunci suka sani ba.

Asma'un ce tashigo ma da Nasmat farantai takalli Sudaida sama da k'asa cikin ta6e baki "hamshak'iya,maduga ke sai yanzu kika ga damar zuwa? Komu da muke tare da Iyali ai hidimar su bata hana mu zuwa anyi kome damu ba,bare kuma ke da kike zaune ke d'aya ba wata hidima a kanki.Sudaida tayi lallausan murmushi"toh Yaya Asma'u dan ALLAH ina ruwan maza da wankan jego?Abinda tafad'a mata kenan tajuya suka cigaba da hirarsu dasu Nasmat.

Ta koma gida tayi wanka tana so tatafi gidan Inna,kiran Julaibib yashigo tad'aga da sallama"Zaujiii...afwan yanzu nake shirin kiranka "kasha ruwa lafiya?Yau banyi azumi ba Zaujatiii... bana jin dad'i.Wayyo! Sannu ai naji muryar ka wata iri,sannu kasha magani sai ka kwanta,dan ALLAH yau dai karka tsaya yin wani nazarin karatu,lafiya ai tafi kome.Toh nagode,kin tafi gidan Inna ne?A ah sai nayi sallar Isha'i.Kiyi zamanki ina hanya.ALLAH yatsare, yakawo ka lafiya.Amin,nagode Zaujatiii...Sai kuma tad'an turo baki kamar yana ganin ta"ni dai ALLAH na tsani dawowar cikin daren nan.Yayi murmushi"sai nazo kawai.

Jakar Magori take ji a k'aramar rediyo taji kwankwasa k'ofa,talek'a ta taga sai tagan shi a tsaye. Tabud'e ta k'ar6i jakar shi"sannu da zuwa Yaya Julaibib ina motar?Bazan iya tuk'i ba shi yasa nashiga tahaya.Har ta ajiye jakar bai shigo ba tasake fita sai taga a hankali yake tafiya,yashigo D'akin-shak'atawa yazauna tare da maida kanshi saman kujerar ya rufe idanun shi.Tazauna a hannun kujerar"sannu...ALLAH yasauwake.Bai amsa ba yamik'e wani jiri yakwashe shi luuu...sai ya durk'usa a gaban ta,yadafa gwiwoyin ta dan saura k'iris yasha k'asa. Sannu Yaya Julaibib. Yagyad'a kai ya yamik'e da sauri yafita,tabi bayan shi"Yaya D'ansarai ina za ka?

Abakin famfo yatsuguna yana amai,itama ta tsuguna tana ta jera mishi sannu, yagama aman yabud'e famfo yana taro ruwan da tafukan hannayen shi yana wanke kanshi zuwa fuskar shi.Yad'an kalleta yamik'e dakyar jikinshi a mace kamar yayi awanni yana aikin dabai huta ba,yasake kallanta...yayi magana amma bataji me yafad'a ba,tamatsa kusa dashi "me kake fad'a Yaya D'ansarai?Idanun shi sun k'ank'ance, luuu kawai taga ya tafi zai sha k'asa,a tsorace tarik'o shi wani abu mara dad'i ratsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta,nauyin shi ya rinjaye na ta, gaba d'aya sukayi jikin bango,dakyar yasa hannunshi nadama yadafe bangon, kome yana hautsine mishi,kanshi na mishi matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu,cikin dukan zuciya tafara kiran sunan shi"Yaya D'ansarai... Yaya D'ansarai... zuciyarta tayi rauni sharrr... sharrr...hawaye suka fara sintiri a fuskarta,jikinta yafara rawa"Yaya Julaibib ta fara jijjigashi sai tana Istirja'i dan wallahi a tsorace take,tana sake shi ko shakka babu zai zube mata a wajen,gashi baza ta iya rik'eshi gaba d'aya ba, k'arfin namiji da mace bambancin a bayyane yake.

Dak'yar tazame suka zauna a k'asa ta jingina bayanta da bango...tazuba mishi idanu a cikin hasken farin watan tana zancen zuci"gashi bata fito da waya ba bare takira wani daga cikin Yayyinta su zo su taimaka mata,takai hannu tana d'an ta6ashi"Yaya D'ansarai kata shi,Yaya D'ansarai dan ALLAH kabud'e idanun ka ka ji?Bazan iya bane dana kaika d'aki,a hankali yabud'e idanu yad'an kalleta sai kuma yamayar rufe...Tanata kallanshi tana ayyane-ayyane a zuci tana kukan shar6e, wucewar wasu dak'ik'u masu yawa sannan taji hucin numfashin shi me zafin gaske "Sudaida ki daina kuka naji sauk'i.Tahad'iye kukan tana kallan shi ta san fad'a kawai yayi dan hankalin ta yakwanta amma ko wannan hucin numfashin me zafi ai bana lafiya bane"Yaya Julaibib to za ka iya tafiya mutafi d'aki?Yagyad'a kai tamik'e tarik'o hannayenshi duka biyun sannan shima yamik'e suka tafi yakwanta, dan yak'i cin abincin data kawo mishi,shayin ma bai shaba...


Yi dai-dai dan dai-dai,dai-dai ne ba dan wasu sunyi dai-dai ba.


Facebook:سودة ا.باب
Facebook:Bilkisu Ibrahim Bilkisu Ibrahim
Email:Saudatibrahim333@gmail.com

23 Jumaada Thani 1441
17 February 2020

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.




DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}




Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJI DAFI💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba ( Aadilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na ashirin da d'aya.



Dasafe yayi wanka yana sanye da yadi ruwan madara mara nauyi,yayi lamooo a cikin kujera.Tashigo da sallama tabi kayan abincin da kallo yana nan yadda ta ajiye"Yaya Julaibib har yanzu baka karya ba? Yagyara zama"na d'an sha kunun gyad'an, ina jin bakina ba d'and'ano ne.Tad'ago tana mishi kallan tuhuma bayan ta bud'e kofin"na ce bakaji sauk'iba ka ce ba haka ba,yanzu wannan kunnun an sha shi kenan?Kur6a d'aya kayi ko? Yad'anyi murmushi"afwan Zaujatiii...zan sha anjima.A hankali yamik'e"barin je gidan Inna ko za kimin rakiya?Uh uh adawo lafiya.ALLAH yasa.Ta amsa da amin tabi bayanshi da kallo wata irin k'auna da tausayin shi suka tsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarta,bata ta6a ganinshi a irin wannan yanayin na daren jiya ba.Tasauke gwauran numfashi"Ubangiji yasa kaffarace Yaya D'ansarai nah... Takoma D'akin-girki tak'arasa ayyukanta sannan taje tayi wanka ta shirya cikin shigar mutunci da sanin kimar kai kamar ko yaushe tatafi makaranta.

Bayan sallar Isha'i yashigo yana kallanta, itama ta idar da sallah tana azkar,tagama ta mishi sannu da zuwa zata cire hijab yarik'o ta"bar hijab d'in ki muje kimin rakiya gidan Hajiya d'azu ban samu na shiga ba, muna ta hidimar jama'a a shago.Tad'an turo baki gaba"a hakan da ba ka da lafiya me makon kadawo gida kayi kwanciyar ka,kaima kahuta ma ranka?Ai naji sauk'i. Tazuba mishi idanu nawasu yan dak'ik'u sannan tace"tun safe har zuwa yanzu me kaci?Na sha shayi a gidan Inna. Tad'an harareshi"shayi dai shayi dai ai sai kaje kayi ta sha, toh yanzu ga abincin dare na jiranka muje kaci sai mutafi gidan Hajiyan.Yagirgiza kai"bari mu dawo sai in ci yanzu banajin yunwa.

Hajiya tana shan dabgen bindin sa suka shigo da sallama.Sudaida tasa hannu wai wai wai gaskiya matar nan kina sha'aninki wallahi,tagalla mata harara"kema wa yahanaki na ki sha'anin? Sakarya kanki kawai kika sani,toh maza d'auki faranti ki zubama mijin naki mana.Yad'aga hannu"a ah barshi kawai Sudaida bazan iya ciba.Suka zuba mishi idanu"har yanzu jikin ne Julaibibi? Hajiya ta tambaye shi.A ah naji sauk'i Alhamdulillahi.

Ganin ya sake anata hira yasa suka saki ransu.Hajiya ta ajiye tsinken data gama sakacen naman daya mak'ale mata a hak'ori"to ko wannan zirga-zirga da kukeyi ai dole yakarar daku daga kai har matar taka,duk da yanzu na ga tafara sabawa, tana maida jikinta a hankali.Yad'anyi murmushi yana kallan Sudaida"ai Insha-ALLAH zirga-zirgan zai ragu dan an d'aukeni koyarwa a Gidan-Waya, farkon wata me kamawa zan fara zuwa.Hajiya tafad'ad'a murmushinta zuwa dariya"kai Masha-ALLAH...Wow Congratulations.

Suka kyalkyale da dariya"Hajjaju makkatan ashe dai baki manta karatun ba?Inji Sudaida.Tamata dakuwa"ungo nan,mu turancin muma gangariya turawa yan misionaries su suka koya mana baki da baki.Toh Hajiya kingama aji bakwai d'in danaji ance anayi a zamanin da amma bakiyi aikin gwamnati ba?Oh oh k'arya ciwo aji hud'u nayi Baba ALLAH yajik'anshi da rahama yamin aure.Sudaida takalleta cikin natsuwa"toh kema nan kunyi soyayya ke da mijin naki?Hajiya tafara tafa hannaye cikin salati da sallallami.

Sudaida tad'an yamutsa fuska "daga tambaya sai ki fara salati.Hajiya tajawo carbi zata shaud'a mata tamik'e dasauri tafita da kwanan da tagama cin dabgen tawanko hannunta sannan tadawo tana kallan Julaibib daya tsaida gwiwoyinshi yasa duka hannayen shi ya rungumesu,tazauna kusa dashi tad'an marairaice" Yaya D'ansarai anya kaji dad'in zaman nan?Yakalleta me kika gani?Kamar kana jin sanyi...Tabbasss sanyin ne yafara ratsashi amma bai nuna ba,sai yamik'ar da k'afafun na shi yasa hannu yana shafa kwantaccen bakin gashin kanshi "ba kome fa.Tagyad'a kai.Hajiya kuma tagalla mata harara "to iyayin yace me?Julaibib yakalli Hajiya "Sudaida fa amaryace kin kuma san amarya bata laifi,idan kina matsa mata to abu me sauk'i ne tayi yajin zuwa gidan nan.

Takad'a

Please Login or Register in order to submit comment