Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tallafi a k'ungiyarmu ni wallahi na manta,anjima za tazo k'ar6a ai da bazan kashe wadan can ba aciki zan bata" haba nijina duk abinda kaba wani shine na ka,wanda kaci kashi yake zama,wanda kake ajiyewa ba lallai kai d'in ne za kayi amfani dashi ba, wata kila sai dai magada su gada.Alheri dank'one da baya fad'uwa k'asa banza.

Yak'irgo adadin data fad'a yabata"ina sanki Sumayya ta tawa ni kad'ai"Tasa hannu biyu takar6a nima haka mungode madallah Ubangiji yak'aro bud'i. Yad'an d'age gira yana mata wani kallo. Tagyad'a kai"Eh mana you're a good samaritan"Yad'an bata marin soyayya suka kyalkyale da dariya.

Abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,ciwo ya tasa Sumayya a gaba, kullum magani akeyi ciwo yana dad'a k'aruwa, watan ta d'aya cur tana kwance a gadan asibiti sannan tad'an dawo hayyacin ta,ita tamatsa aka sallame ta tare da k'arin wasu sharud'd'ai da zata kuma kiyayewa dan ta zauna lafiya.

Yazuba mata idanu bacci take yi, tayi bak'i ta fita hayyacin ta,shima wallahi jinshi yake kamar mara lafiya.Yadad'a rungume Ummi da take bacci bayan ta gama rigimar a bata abincin ta kuma an yaye ta,ya had'a mata shayi amma tak'i sha,dak'yar dai ya rarrashe ta takoma bacci sai ajiyar zuciya take yi.Ya sauke gwauran numfashi "ALLAH yabaki lafiya Sumayya,ALLAH yasa kaffara ce".

A hankali tabud'e idanun ta takai hannu tana d'an shafa kan Ummi sannan ta kalleshi "sannu Baban Ummi wai har yanzu baka fita ba?Yakad'a kai"Kayyah... Sumayya duk inda naje tunanin halin da na barki bazai barni inyi wani sukuni ba. Amma ai yau naga jikin na ki da sauk'i ko?To me za ta ce? Ita kad'ai tasan azabar ciwon da take ji,ba tasan yawan k'orafi tunda yana matuk'ar k'ok'ari da jikinshi,aljihunshi,kalamanshi da kuma lokacin shi, duk tsadar magana bai ta6a nuna gazawarshi wajan siyo mata shi ba, haka irin kalar abincin da akace shi zata dinga ci dayawa yasiyo mata ya ajiye. Tad'an yi yak'e dayafi kuka ciwo"Alhamdulillahi ala kulli halin".

Ummi tasa hannu a baki tana tsotsa cikin dabara yazare hannu sannan ya kwantar da ita yana tambayar Sumayya abinda za taci da rana duk da a yanzu cin abincin na ta,ba wani na azo a gani bane,wasu lokutan ma sai yanuna 6acin rai sannan take d'an tsakura.

Salim...tabishi da kallo yazauna a gefen gadan yana kallanta shima ya d'anji mamakin kiran sunan shi da tayi yanzu kai tsaye.Yarik'o hannayan ta yana kallan yadda tafin ciki ya d'ashe kamar mara jini amma ko d'azu da safe Doctor Zainab ta tabbatar mishi tana da jini dai-dai yadda ake so baiyi kad'an ba"Uhun me kike so kifad'a min ne?Sharrr...sharrr...wasu hawaye masu d'umi suke zubo mata"muryar ta tafara rawa"ni dai nagode ma Ubangijin mu daya min gata da samun ka a matsayin miji. Ina san ka Baban Ummi...tamishi wani irin kallo da yasa zuciyar shi bugawa da k'arfin gaske.Yakauda kai "Sumayya me za kici?Yasake tambayar ta.Kar ka damu zan sha shayi.Yasa hannu yana share mata hawayen"ki daina kuka ALLAH zai ba ki lafiya mukoma cin had'ad'd'an abincin ki me rai da motsi.Tabishi da kallo cikin kissima wani irin yanayi a zuciyarta.Hawayen suka sake zubo mata sharrr...idan tafad'a mishi yadda take ji a cikin jikinta tayar me da hankali za tayi zai rasa sukuni dan haka taja bakinta tayi shiru.

Ranar da taje gidan Alhaji Hafiz suka wuni suna hira sai bayan isha'i yazo ya d'auke su.Sun kwanta lafiya lau cikin farin ciki sun dad'e suna hirar su kafin bacci yayi awan gaba dasu, amma cikin dare nishinta metsananin k'arfine yafarkar dashi daga bacci, yakunna wutar d'akin tana kwance cikin mawuyacin hali. Sumayya...!ko kallanshi ba tayiba, dan ba ta cikin hayyacin ta ne, idanunta sai rufewa da bud'ewa suke yi kamar wacce tasha kayan maye ta bugu sosai,bakin ta a bud'e ya bushe k'amas,ta rasa inda za ta tsoma ranta taji dad'i sai tafara wata irin shak'uwa,a gigice ya d'auko ruwa yana bata amma bata iya had'iya ba haka yake biyo gefen bakinta yana zubewa tana wata irin jijjiga... Sumayya...! Yafara girgiza ta Sumayya kalleni...!Ina hankalin ta baya jikinta tana gargara..."Laahaula wala quuwata illa billah "kome na ta ya saki a hankali tafara jan numfashi me tsawo sai ta sauke shi a hankali,sai takuma janshi sai yayi kamar ya tafi bazai dawo ba zuwa can sai ta sauke shi a hankali, haka tadingayi,yakwantar da ita yafara neman makullin motarshi amma tsabar rud'ewa wallahi sai yarasa a inda ya ajiyeshi,a fizge tafara kalmar shahada abinda yadad'a gigitashi kenan...zuwa can kuma kamar anyi ruwa an d'auke sai yaji d'ifff...

Sumayya...!yakira sunanta da k'arfi yata6a kirjinta difff...Numfashi baya shiga da fita...Sumayya! Yad'aga hannun ta na dama yarafff...yafad'i a kan katifa.Abubuwa da yawa suka yamutsa k'wak'walwar shi bangaran tunani sai yaji ruguzowar wani abu a k'ahon zuciyar shi da k'arfin gaske Dammm...!!!

Ta mutu...!Sumayya ta mutu...?!!!

Sai yafara k'arya ta zuciyar shi dan idanun sun fara mishi gizo sun nuna mishi ga tanan tana numfashin ta"Sumayya au dama baki mutu ba? Yasake kallanta idanun ta a k'ak'k'afe ruwan ciki yak'ame k'amas suna kallan sama tayi tsawo da wani irin kyau na ban mamaki shi bai ta6a ganin wannan kyan ba ko lokacin da take ganiyar lafiyar ta take kwalliya da gayu...bai san awani yanayi yake ba har sai da aka kirashi a waya.

Miqdad ne yake tambayar shi lafiya kuwa ban ganka a masallaci sallar asubahi ba,ko jikin Sumayyan ne?Asanyaye yace"Sumayya ta mutu.Cikin k'araji Miqdad ya sake tambayar shi"ta mutu? Yaushe?Wasu irin hawaye masu d'umi suka zubo mishi sharrr...sai kawai ya katse wayar yakifa kanshi a kusa da fuskar ta, ya rasa abinda yake mishi dad'i sai yafara Istirja'i...Miqdad shi yaje gida yad'auko su Alhaji Hafiz suka d'unguma gaba d'ayansu zuwa gidan hankali a tashe.Amma Salim yayi dauriya dan shi yamata wanka yashirya ta tsab aka mata sallah aka d'auketa a makara sai makwancinta na gaskiya kabari d'aki a cikin kasa"Uh uhun duniya rumfar kara...Wata rana zai fad'i.ALLAH yajikanki Sumayya yasa k'arshen wahalar kenan!

Lokaci d'aya Salim yayi wata rin rama kamar wanda ya shekara yana jinya.A ranar Iyayanta suka zo.Maman tana kuka ta rungume Ummi tana sambatu "Holy Jesus why? Why? Me yasa Kasham za ta mutu yanzu? Me yasa za ka bari a kashe min yarinya...To wallahi bazan ta6a yafewa ba...me Kasham ta tare muku ne?

Alhaji Hafiz ya k'araso wajan da sauri "haba Dinatu ya kike irin wannna kalaman ne? Mutane fa za suyi zatan kasheta akayi.To dama ba kasheta akayi ba? Kaima ai ka sani ko har ka manta tunda ba 'yar ka bace? Yakad'a kai cikin damuwa"ko na sani a yanzu dai na manta,mudai a addininmu na musulunci duk wanda yamutu to tabbaci hak'ik'a kwananshine kawai yak'are, amma ba mayune suka kashe shiba "ai sara da sassak'a basa hana gamji toho...a ah Shedrak wallahi Kasham dai kashe min ita akayi, ba ta zo sun ganta cikin rufin asiri ba?Takuma yin kururuwa cikin tafasar zuciya"Wai...Wayyoh...ALLAH!!! Kasham ta mutu...Judith ta mutu...oh Jesus Christ of Nazareth!

Shedrak!

Tazuba mishi jajayan idanun ta da suka rine da 6acin rai tadad'a rungume Ummi"bazan yafe ba. Yagyad'a kai"to naji amma dan ALLAH kiyi hak'uri da kukan nan muje ga abincin ku can kije ki k'arya.Bana ci, tasa gefen zaninta tana share hawaye da majina an kashe min Kasham an bar min grandchild cikin maraici... for God sake Shedrak Ummi guda nawa take da zata iya d'aukar wannan tashin hankalin?

Yakalli Ummin"tabbass Ummi ba ta san kome ba,bata ma san me ake kira da mutuwa ba bare har yatashi hankalin ta,guda nawa take?Ko shekara uku batayi ba to amma ya za suyi da hukuncin ALLAH?Yadda duk yaso haka yake zartar da hukuncin shi"idan yaso yafitar da rayayye daga jikin matacce,idan yaso yafitar da matacce daga cikin rayayye"Qaadiran alaa manyasha'u.Dak'yar yasamu ta yi shiru da wannan sambatun da take tayi cikin kuka da d'aga murya.

Makon su d'aya sukayi shirin komawa k'auyansu Madauci,Maman ta so k'warai abata Ummi ta tafi da ita amma Salim da Alhaji Hafiz suka bata hak'uri akan hakan bazai yiwuba kasancewar addini ba d'aya ba.Salim ma yasake ba ta hak'uri tare da alk'awarin kawo musu Ummi lokaci zuwa lokaci suna ganin juna.

"Mutuwa ba ta zama masifa ga mumini,mutuwa hutuce ga wanda yadace da kyakkyawar makoma...ALLAH ba yana nufin 6atama bawa bane dan ya d'auki wani bangare najin dad'in shi Iyaye, mata, miji,Ya'ya da yan'uwa.. Alhaji Hafiz yadafa kafad'arshi "Salim...na san kai namiji jarumi ne,to na rok'eka da girman ALLAH kayi hak'uri kaga yadda kazama kuwa a yan kwana kin nan? Sumayya ta riga ta tafi rayuwarta ta doron duniya ta riga ta k'are,ba abinda take buk'ata awajan mu yanzu sama da addu'a...Addu'a itace abincin mumini...to mu yawaita aika mata dashi.Kaima ka natsuwa kacigaba da zuwa kasuwa ALLAH yabaka macen albarka.Yahad'iye wani abu me d'aci dak'yar yayi furucin" nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma...

Ummi tana gidan Alhaji Hafiz dan shi yanemi wannan alfarmar,amma Salim ya dai basu ita dan kawai sun cika mishi idanu ne,saboda yadda yake sintiri ba dare ba rana.Suna hira a D'akin-shak'atawa zuwan shi gidan a aranar karo na uku kenan.Alhaji Hafiz yakalleshi cikin natsuwa "Salim kayi aure mana.Yad'an yi murmushi kawai. Kayi shiru bakace kome ba?Alhaji ba auran ne bana so ba, tunani nakeyi anya zan samu mace kamar Sumayya?Wani irin zama mukayi me cike da amana, me cike da girmama juna,zan samu macen daza ta rik'e min Ummi da amana? Yagyad'a kai"me zai hana Salim?Kai da can abaya ka san za kuyi irin wannan zaman da Sumayya?To karka cire tsammani daga al'amarin Ubangiji mana.jikinshi yayi sanyi wannan gaskiya"nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma.

Ummi ta shigo da gudunta dan taji muryarshi"Abba na baka tafi ba?Uh ban tafi ba.Tayi dariya"to muje ka kaini Galaxy...in kira Yaya Zuhair mutafi tare?Yakalleta da kulawa "Ummi baza muje Galaxy ba, lokacin makaranta ya kusa,baza mu sake zuwaba sai an bada hutu kinji ko?Ta6ata fuska sai kawai tajuya tayi tafiyar ta, kwallah sun cika idanun ta.Suka bita da kallo har tafice.

Me yasa kayi haka Salim?Dama taku da Ummi zata 6aci?Lallai yau na ganku a rana.Yad'an yi murmushi"ai ba duk abinda take so nake biye mata ba,wani lokacin ko akwai abin ina hanata saboda ta taso cikin sanin ba ko me da mutum yake so a rayuwa yake samu ba, ko da kuwa yana ganin abin baifi karfin shiba, kauna da soyayyar dana ke ma Ummi ba makauniya bace...

Lokaci k'ank'ani Salim suka dai-daita da 'yar limamin unguwarsu aka daura musu aure,shima sai ya samu sauk'in zirga-zirga tsakanin gidanshi dana Alhaji Hafiz saboda Ummi.Mariya tana kula mishi da Ummi gwargwadan ikon ta, shima ya yaba da hakan sai suka samu kwanciyar hankali dan kowa yana yaba k'ok'arin dan'uwanshi,sai tak'ara bada himma tana mata rik'on tsakani da ALLAH kamar yadda zata rik'e Ya'yan cikinta"yaba kyauta tukwuici.

Yana sanye da wandon chinos ruwan zinare sai riga me dogon hannu da ratsin ruwan zinari da bak'i,kwantaccen bak'in gashin kanshi yanata k'yallin hair fruits,k'amshin Arabian perfume d'inshi ya cika d'akin. Alk'asim da suke abokan wasa tawajan uba yashigo yana kallanshi "Lallai mutumin nan kana jin dad'in ka, kaga yadda kazama wani d'an matashin bak'in bature kuwa? Yabashi hannu suka yi musafaha.To ya karatun? Alhamdulillahi ai ya zo k'arshe tunda na gama rubuta Project d'ina.Ah lallai sai shirin tafiya bautar k'asa to Ubangiji yasa aje a sa a.Amin nagode. Yad'auki remote yana canja tasha baya san labaran CNN d'in nan,yan kanzagin Amurka (America)kanwa uwar gami ce,da yad'a propagandar k'arya akan addinin musulunci da musulmai.Yacire wayar shi da yasa a caji ta cika,suka fita zuwa gidan Hajiya sai dai gidan na ta da kwado sai sukayi zamansu a dakalin k'ofar gidan suna hira.

Aminu yak'araso yana kallan Julaibib cikin raha yace"hey dude what's up?Yagalla mishi harara "Amincin ALAH zaka rok'amana ba wannan ba..yatare shi cikin dariya"kar ka wani harareni kai kayi shiga irin ta su ai dole in maka irin al'adarsu,shima yazauna sannan yamik'a musu hannu sukayi musafaha.

Suna ta hira amma ya dai na jin abinda suka fad'a tunda ya hangota"indai yana gari to ranakun k'arshen mako irin haka yana ganinta.A natse take tafiya irin ta 'ya macen data san abinda take yi wato gefen hanya, yanata kallanta har tasha kwana.Wani murmushi yasu6uce mishi"Yarinyar can ya yaba da hankali da natsuwar ta.Aminu yayi yar dariya"Dan Sarai kenan biri yayi kama da mutum fa...na rantse maka ALLAH da zafi-zafi ake dukan k'arfe idan katsaya kallan ruwa...irin na Aisha to ko ba abinda zai hana kwad'o yamaka k'afa. Yajijjiga kai "tabbass zancen ka dutse...

Washe gari lahadi yakafa ya tsare sha d'aya da rabi yabar Musaddiq a shago yaje dakalin wajan yazauna yana fatan ganinta,dai-dai lokacin aka ta shi daga Islamiyar su,wucewar wasu yan dak'ik'u sai ko gata ta zo zata wuce,yabita da kallo tana sanye da dogon hijab me hannu ruwan sararin samaniya kafad'arta rataye da bak'ar jaka.

"Assalamu alaikum...

Karo na biyu kenan yamata sallamar.Dafarko tayi tsammanin ba da ita yake yiba shi yasa tayi shiru, sai da yasake maimaitawa,a hankali tad'an juyo ta kalleshi sannan ta amsa.Da sauri yamik'e daga dakalin ganin ta juya taciga da tafiyarta... "am... Dan ALLAH...Jimana.Tatsaya ba tare data juyo ba tana jiran abinda zai fad'a.Yayi k'asa da murya "kinga yanzu sauran d'aliban za su firfito kuma kamar zamu takura musu idan muka tsaya anan, ko zamu d'an matsa daga can bakin Library? Batace kome ba suka k'arasa wajan yad'an jingina da k'arfen allan bayani(signboard)d'in yana kallanta ta sunkwui da kai.

Ya Ilahi...sai yarasa abinda zai fad'a ta mishi arwa.Wucewar wasu dakk'ik'u tad'ago kai ta kalleshi cikin natsuwa dan shirun yayi yawa "Malam lafiya?Yad'an sosa kunne"Kiyi hak'uri da na san gidan da kike bazan tsaida ke a hanya ba,can d'in zan biyo ki dan kambamawar data dace dake kenan"Dan ALLAH ina ne gidan ku?Tagirgiza kai"ni ba yar garin nan bace karatu nake yi a Nursing School a cikin makaranta nake zama.

Ayyah...to ya muka ji da shan geron Sunday?(garin kwaki/rogo)yadda yayi furucin cikin jimami yasa tad'anyi murmushi"har da kai? Yagyad'a kai"eh ai duk kanwar ja ce,nima d'alibi ne gobe war haka ai na tsufa a makaranta.Atakaice yamata bayanin kanshi itama haka da garin data fito.

Adai-dai lokacin suka shawo kwana dawowar su daga makarantar allo kenan.Juyowar dazaiyi dan sunyi sallama da Bilkisu caraf idanun su yahad'u dana Sudaida"wani irin yanayi mara dad'i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta, tagalla mishi harara sannna takauda kai,cikin fushi tayi gaba su Khausar suka tsaya gaisawa suna d'an tsokanar shi"a k'ofar gidansu Nasmat tatsaya dan allanta yana hannun Nasmat d'inne kuma rubutu za tayi da wallahi bata tsaya ba"Khausar takalleta "to ke wai saurin meye haka kike yi?Sauri kuma ba wajan zuwa ba tunda gashi dole ta tsaya jiranmu.Tamusu wani malalacin kallo"shiru ma amsace.Nasmat tacigaba"anya waccan ba budurwar D'ansarai bace?Cikin tafasar zuciya ta fizge allanta"kya tambayi kaza hanyar rafi...?Fuuu tayi gaba tana k'unk'uni.Suka bita da kallan mamaki cikin tunanin abinda ya caza mata k'wak'walwa haka.Nasmat tad'an motsa kafad'a "wallahi can da yawarki yarinya.

Tun daga ranar D'ansarai bai kuma yadda sun had'u da Bilkisu a kwanakin k'arshen mako ba. Ranar wata Juma'a yayi shigarshi ta fararan kaya yad'auki motarshi sai Matsirga anan yayi sallar Juma'a.Yana fitowa daga masallaci yadinga bin kwatancen Bilkisu kasancewar shi ba bak'o bane a garin sai ko gashi a k'ofar gidan.Wani dogon dattijo kyakkyawan farin Bafulani yahango, shi da wani da bai k'arasa shi a tsufa ba suna magana, sun dad'e suna maganganunsu sannan sukayi sallama.

Julaibib yatare shi cikin sallama...

Malam Lamid'o ya amsa sallamar yana mik'a ma Julaibib hannu dan suyi musafaha amma ya nok'e a haka ya gaishe shi cikin girmamawa.Malam Lamid'o sai ya yaba da natsuwarshi yayi murmushi"samari daga ina? Cikin ladabi ya amsa"Baba ni bak'on kune. Yagyad'a kai yana kara nazarinshi"af to,to madallah sannu da zuwa to bismillah shigo ciki,yabud'e mishi d'akin zauran suka shiga yanuna mishi wajan zama"zauna ina zuwa"yajuya zuwa cikin gidan sai gashi ya dawo da damammiyar fura da nono tasha zuma da ruwan sha "bismillah samari"to Baba nagode"yajuya yasake fita dan yabashi waje. wucewar dak'ik'u talatin yasake shigowa lokacin Julaibib yad'an sha fura dan baya wani jin yunwa.

"Samari daga ina kake?

Julaibib Abdullahi D'ansarai...

Shine cikakken sunana daga Zonkwa nake.

Yabashi labarin kome game da had'uwarsu da Bilkisu...Ita kanta ba ta san zanzo nan ba.Ni nazo wajan kane Baba indai bakama Bilkisu miji ba to idan ka amince zan turo maka manyana.Yamishi kallan nazari" yanzu misali idan na amince ita kuma Bilkisu bata amince dakai amatsayin miji ba fa?Yad'anyi jimmm...sannan yad'ago cikin natsuwa yakalleshi "bazanji dad'i ba amma bazan ji haushi ba ,dan na san kome na rayuwar bawa yana rubuce ne,yana kuma tafiya daki-dakine kamar yadda numfashi yake shiga da fita ajikin d'an Adam,zan mana addu'a ni da ita Ubangiji yahad'amu da abokan zama na arzik'i.

Malam Lamid'o yabishi da kallo cikin zancen zuci"wannan d'an matashin tun yanzu yana da halin dattako to inaga ya dad'a girma,ilmi yadad'a cika k'wak'walwarshi? Julaibib idan har Bilkisu ta amince da kai to nima na amince dakai dan ni bazan ma Bilkisu auran dole ba sai wanda ta yadda tana so dan haka,kaje na yadda ka nemi soyayyar ta. Irinka nake ma Bilkisu sha'awa kasancewar ta me d'an ilmi duk da bai taka kara ya karya ba,to amma na san idan tazama matarka za ka ciyar da ita gaba,ta inda taka sa zaka taimaka mata har itama ta tsaya da kafafunta wata rana.

Nayi karatun addini dana zamani dai-dai gwargwado,shi yasa na hana Jauro auran ta saboda ba abinda ya iya ba abinda yasani sai kiwon shanu,ni na san illar zama da jahili dan bazai amfanar da ita da kome ba,d'an abinda tasani d'in ma idan ba tsananin raboba a haka zai k'are.Katuro min manyanka za muyi magana gemu da gemu.Ubangiji yasa Bilkisu rabonka ce.Yasunkwui da kai yana murmushi labarin zuciya a tambayi fuska.

Tana goge kayan sawanta abokiyar karatunta tazo mata da sak'on daya bata mamaki"Julaibib kikace yana nema na?Eh ai kibar wani mamaki dan ga kai ga k'afa ai ba tambayar me aka yanka, jeki wajan da ake ajiye abubuwan hawa za ki ganshi ganin idanunki.

Dogon hijab me hannu ruwan k'asa tasa, yana hangota yafito daga cikin motar.

"Bilkisu me gadon zinare...

Tagaishe shi cikin natsuwa.Ya amsa yana murmushi"Yau dai gani ALLAH ya nufeni da zuwa a wannan yammacin,da zan bari sai gobe to amma dana tuna yaufa Juma'atu babbar rana ce sai kawai nace barin dai k'araso in k'ar6i goron juma'a ta kawai.Tad'anyi murmushi "goron juma'a kake so? Ai ko ka tara ka samu sai ta mik'a mishi lemon Schweppes d'in hannun ta.Yasa hannu biyu yakar6a "wannan kyautar goron juma'ar ta faranta min rai naji dad'i na kuma gode dashi zanci tuwon dawar Inna miyar kuka.

"Bello yace a gaisheki"

Takalleshi tabbass ya je Matsirga tunda basuyi maganar yan'uwan taba, Bello kuma shine autansu. Yaushe kaje?Duk suna nan lafiya? A lafiyarsu kalau,suma suna gaishe ki dakyau. Yad'auko bak'ar leda yaba ta "Malam ne yace in kawo miki.Tarungume ledar cikin farin ciki "nagode.Yad'an kalleta sannan yasanar da ita abinda yake tafe dashi.Tasunkwui da kai"bazance kome ba sai abinda Malam yace"fad'uwa ta zo dai-dai da zama kenan"Malam ai ya amince dani Bilkisu.A kunyace tace to ai shikenan.Sukayi sallama dan rana ta tafi za ta fad'i magriba na shirin kunno kai.




Ana bikin duniya ake na k'iyama.
Akwai lauje cikin nad'i...


20 Jumaada Awwal 1441
15 January 2020

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.






DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in




...GWAJIN DAFI💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)

Masu k'orafin dan me Sumayya bata auri D'ansarai ba,da masu zaginmu wai labari ya d'auko dad'i

Please Login or Register in order to submit comment