Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa(In the whole wide world)


Takalleta cikin fushi"kin san da haka amma nace kar kiyi sallah sai kika gudu wajan Shedrak har kina min k'arya wai an ma Tina Operation?Tagirgiza kai"gaskiya ban yadda ba kin nuna min Shedrak ya fini.Ba haka bane Mama. Tasake galla mata harara"to yaya ne? Tamarairai ce"Mama tafiya ta Kaduna wajan Uncle da duk abubuwan da suka biyo baya"It's a destiny (K'addara ce) suka kalli juna Sumayya tajijjiga kai "Ki yadda dani Mama wannan k'addara tace daban isa in kauce mata ba no matter how,kuma ai gwamma tawa tafiyar sau dubu tunda gashi na dawo a cikin hayyaci, koshin lafiya da kwanciyar hankali kuma kowa ya yaba,yayi sam barka to ai ko Alhamdulillah.


To amma Mama Judith fa...? ran Maman yak'ara 6aci Sumayya tacigaba"Judith ta tafi amma bata dawo a cikin hayyaci, k'oshin lafiya da kwanciyar hankali ba, kuma kowa tirrr... da ALLAh wadarai yakeyi daganin ta, ba kuma wanda yakuma damuwa da ita sai ku.Ba aure tayi ba fornication shine sana'ar ta" which is forbiden"ba addinin daya yadda da hakan Islam ko Christianity sai dai san zuciya kawai,san zuciya kuwa 6acin ta yau ga Judit a ciki kuma Mama...ta tare ta dasauri ya isa haka Kasham jikinta yayi sanyi duk irin alwashin data d'auka ranar duk da sukayi ido hud'u da Kasham sai ta nemi shi tarasa,gaskiya Kasham tafad'a sai ta rungumeta"naya fe miki kome ALLAH ya albarkaci auran ki, wancan d'in shine Julaibib?Tagirgiza kai tana murmushi"ba shi bane.. taba ta labarin duk abinda yafaru da ita bayan barin ta gida.

Tazuba mata idanu"to ni me zance miki Kasham? Sallah ne dai kin riga kin fara kuma ko na ce miki ki daina na san bazaki daina ba, kuma ma ban miki adalci ba,tunda duk a cikin Ya'yana dana haifa daga ke sai Rahab da Bitrus kune kawai masu jin magana, kune kuka maida hankali a karatu gashi nan kuma kune rayuwar ku tayi kyau,yanzu Bitrus shine personal manager a Bajju Community Bank(BCB) Rahab ta gama karatunta har ta fara aikin ta a asibiti, anjima kad'an za ta dawo gida tunda aikin rana wannan makon takeyi,ke kuma gashi kinyi aure hankalin ki akwance kuma kina cigaba da karatu.Rahab d'inma ta kusa yin aure.Sumayya tana ta godema Ubangiji daya sauk'ak'a kome fiye da zatan ta, tasaki jiki sunata hirar yaushe gamo suna kyalkyala dariya "Da da mahaifa sai ALLAH.

A babban D'akin-shak'atawar gidan suka yi jam'in sallar su saboda k'auyan gaba d'aya ba masallaci tunda babu me sallah.Suna jam'in sallar Isha'i Rahab ta shigo da d'okin ganin Kasham dan tun a hanya tasamu labarin zuwan su, d'agowar su daga ruku'u Rahab ta tafi zata rungume ta Maman ta dakatar da ita"Ke Rahab karki ta6a ta baki ga sallah suke yiba?.Taja da baya da sauri"Oh Basakut"ta tuna idan suna sallah ko magana basa yi.Tajingina da bango tana kallansu"yadda suke tsayuwa,suyi ruku'u su d'ago, su tafi sujjada,su d'ago,su sake komawa sujjada suyi zaman tahiya har zuwa sallama kowa yafara karanta azkar d'in bayan kowace sallar farilla.

Cikin murmushi tajuya wajan Rahab. Rahab takama ha6a cikin mad'aukakin mamaki tayi tsalle ta rungumeta tana ihun murna Jesust Christ Halelujah"Kasham kece kika zama wata big madam?What a suprise, ta daki kafad'arta"tell me the secret.Sumayya tashafa wajan"gaskiya fa akwai zafi"suka kyalkyale da dariya.Rahab ai kema kin canja kinyi kud'i fa"mint note"suna shiga asusun ajiyar ki duk k'arshen wata suka saki juna. Rahab tasake binta da kallo daga sama har k'asa gaskiya canjawar da nayi ba irin wacce kika yi bace"wonderful"tashafa kyakkyawar fuskar ta data ke ta hasken musulunci da Imani"wannan irin kumatu da kika fara ajiyewa ga fari, ni dai ko shafa man sa fari kika fara ne?(bleaching)Ba Sumayya ba hatta sauran sai da sukayi dariya dajin yadda Rahab taketa kod'a ta.Tazauna suka gaisa d'aya bayan d'aya take tamabayar Sumayya sunayan su.Salim yabisu da kallo ga dukkan alamu suna san junan su suna da kirki dama Sumayya tafad'a mishi Maman suce kawai sai a hankali to itama bata nuna kome ba banda farin ciki da ganinsu.

Sumayya,Hafsa,Zainab da Rahab su suka gyarama Judith jiki da d'akin dayake ta k'arni kudaje sai budiri sukeyi,tana kwance cikin hawaye"wallahi da ace zan warke babu abinda zai hanani binku Kaduna in zama musulma.Hafsa ta amsa da sauri "ai ba dole sai a Kaduna ba, ko yanzu za ki iya k'ar6an musulunci.Wani dad'i yakama Sumayya.Ki yadda ki amince kina da rabo ne. Judith ko baki warke ba ALLAH zai kar6eki a haka Tagirgiza kai "uh uh ku kyaleni kawai dan bazan iya sallah ba tunda k'arfina ya riga ya k'are.Sumayya takalleta cikin natsuwa"ai addinin musulunci sauk'i gare shi Judit, ba dole sai a tsaye ko kina da k'arfi a gangar jiki za kiyi sallah ba matukar akwai lalura ko a yadda kike akwancen nan akwai yadda za kiyi sallah.

Rahab tagalla musu harara sannnan taja dogon tsaki"addinin ta'addancin kike sha'awa Judith?Tamik'e a zuciye zata bar d'akin Sumayya tarik'o hannunta.Rai a 6ace tace "malama sakarmin hannu kishiga hankalin ki fa.Tagyad'a kai sannan tasake kallan ta ckin natsuwa"to kiyi hak'uri kizauna magana za muyi Takoma ta zauna fuska a yamutse.Shiru ya ratsa d'akin na wucewar wasu dak'ik'u. Tad'ago kai a zuciye"bana san wawanci fa, ke nake sauraro kin kuma yi shiru.To ai naga ranki a6ace yake shi yasa nayi shiru har sai kin d'an huce karr in k'ara miki zafi.Tamik'a mata lemon biyar a raye(five alive)d'an jik'a mak'oshin ki mana.Kasham I'm I your toy to play with?Tayi yar dariya "absolutely no kiyi hak'uri, amma ina so ki sani addinin musulunci ba addinin ta'addanci bane,addinin sauk'i da salama nw ga mabiyanshi.Tawatsa hannaye "ahab...ba cinya ba k'afar baya"ko d'azuma abinda wani musulmin ku Adam yagama fad'a min kenan awajan aiki.Nidai banga dalilin da zai sa inyi sallah ba,ina da yanci bazan koma inda bani da wani yanciba.

Zainab ta tareta da sauri"ai ko addinin musulunci shine yabaki cikakken yanc me lasisi ma, musamman a matsayinki na 'ya mace,kina da yanci kamar yadda namiji yake da yanci,sai dai mu addinin mu, duk da yancin daya k'wato mana ya nuna mana namiji shine a sama da mace,idan banda addinin musulunci wa yake girmama 'ya mace ne?

Rumawa da suke kiran mace"Devil" shaid'aniya? Wai mace shaid'aniyace ana neman tsari da ita kamar yadda ake neman tsari da shaid'an.

Persia su kuma sun d'auki mace wulak'antacciya k'asa da duk wata halitta wulak'antacciya.

Yahudawa su kuma sun d'auki mace kamar baiwa,da zatai tama namiji hidima, ita kuma ba ta da wani hakki akan namiji

Zamanin jahiliyyar larabawa kuma idan aka haifi macen sai ma adinga zuwa maka jaje kai kuma kana 6uya,amata rik'on wulakanci,ko kuma tanaji tana gani da ranta da lafiyar ta a tona k'asa abinneta.

Wanne daga cikin wad'annan suka ba mace yan cinta?
To a duniyar musulunci da gidan musulunci ne kawai mace take yar ga ta,yar lele, sarauniya kome yi mata ake yi,kome kud'in ta k'wandala na ta na k'ashin kan ta sai ta ga dama za ta kashe.Duk masu yeekuwar yan cin mata indai ba wannan da addinin yabasu bane to wallahi k'arya ce,haushi suke ji, suna so ne ku fito ku sha wahala.


Rahab ta ta6e baki"ni kalaman naki duk a matsayin tazo muji ta tawuce ta bayan kunne na d'aukesu. Sumayya tagirgiza kai"ai ko sun wuce tazo muji ta tawuce ta bayan kunne wallahi.A baya dana ke kamar ke ina fad'in haka, amma a yanzu dana san hak'ik'anin musulunci ai na san k'arya ce. Rahab kije kiyi bincike ki ga ne menene addinin musulunci na gaskiya da abinda ya k'unsa,ba abinda kike ganin gama-garin musulmai suke aikatawa ba, ba abinda kike karantawa a mujallu da jaridu ba,ba abinda d'ai-d'ai kun mutane suke fasara musuluncin ba,kije kiyi karatu da bincke a cikin littafan musulunci,ki saurari preaching da luctures d'in malamai,ba abinda wasu gur6atattun musulmai da rashin ilmi ko san zuciya yake musu jagoranci ba.


Musulunci bai yadda da ta'addanci ba ko misqala zarratin,kuma duk wanda yake fakewa da musulunci to gaskiyar magana san zuciyar shi yabi... Rahab ta tari numfashin ta"za ki fad'i haka mana tunda kema kin zama musulma..."Eh zan fad'i haka dan na zama musulma na kuma san d'an abinda ALLAH yanufe ni da sani na daga ilmominshi.

Rahab barin baki misali Christianity bai yadda da shan giya da karuwanci ba,hakane? Rahab tagyada kai.Takalleta cikin natsuwa"to yanzu abinda Alhamdu da Judith suke yi sai ace addinin Christianity ne yace suyi?Sai taki magana. Sumayya ta d'an motsa kafad'a kin gani ko? To kamar haka addinin musulunci yake.Ki yadda kawai Rahab ki kar6i musulunci wallahi sai kinfi jin dad'in rayuwar ki.Ta ta6e baki tana hararar ta.

Sumayya tagyad'a kai tana murmushi "ALLAH kuwa gaskiya nake fad'a miki tabi hotunan d'akin da kallo kin gani,ko Jesus da Mary irin shigar musulunci suke yi a duk irin hotunan da zaki gani an za na su.Tajawo wata mujallar "Jehovah Witness"tana bud'e shafukan ciki Zainab da Hafsa kuzo kutaya ni gani a duk shafukan ciki kunga me"mini skirt da strap top kai ba d'ankwali? Suka kar6i mujallar suna dad'a gani,bayan sun gama dubawa Zainab tagirgiza kai"har shafin k'arshe ba bu,kowacce cikin mayalwacin kaya da lullu6i.Sumayya tace"to mazan fa"?Hafsa tace "suma suna cikin dogayan kaya ga gemu da k'asumba wasu ma har da rawani.Suka zuba ma Rahab idanu.Kingani ko?Wannnan shi yake nuna miki addinin gaskiya mukeyi"ai ko Annabi Isah Alaihissalam Jesus d'in musulmi ne.

Judith cikin hawaye tace"wallahi na yadda daku.Zainab takalleta cikin natsuwa" to ki kar6i musulunci mana.Tagirgiza kai"I seek repent from God and I know he will forgive me.Hafsa takad'a kai cikin damuwa.Sumayya tadafa kafad'arta karki 6ata ranki"dan shiriya ba ta wajan kowa face mahaliccin mu,shi yake shiryar da wanda yaso a lokacin daya so.Tajijjiga kai "wannan gaskiya ne Yaya Sumayya.Haka suka kwanta zuciyoyin su ba dad'i kowacce da irin tunanin ta musamman ganin yadda Judit tazama "k'ashi da rai.Ubangiji kamana kyakkyawar k'arshe.

A sanda hantsi yadubi ludayi tana zaune a inda tayi sallar walha kiran Salim yashigo tad'aga tana dariya"Humm mijina na wa nakai na.Yataya darawa "Sumayya ta tawa ni kad'ai fito waje muyi hira.Yazuba mata idanu har ta zauna a gefen shi,tabi wajan da kallo "wai kana nufin anan zamu zauna?Mushiga gida mana.A ah gwamma muyi zaman mu anan,mu shak'i natural air, ta tacciya me kamshi kinga turawa sun mana wayo sai su tafi "Bar beach"suje su shak'i iska tatacciya dan jikin d'an Adam yana buk'atar hakan,wajan da ba hayaniya kayi refreshing d'in gangar jiki, zuciyar ka da k'wak'walwarka.

Nayi kewarki fa.Tabud'e idanun ta data rufesu tamishi wani kallan k'auna me cike da shauk'i"nima haka"sai sukayi dariya.

Salim...

Takira shi a hankali. Yakalleta... Tagyad'a kai"samun masoyi na gaskiya shine buk'atar kowani d'an Adam,masoyi me amana, masoyi me girmama abinda masoyin shi yake so matuk'ar ba sa6on ALLAH bane,masoyi me k'ok'ari da jikinshi,da kalaman shi, da aljihun shi, da lokacin shi wajan ganin masoyin shi ya samu abinda yake san samu"Godiya ta tabbata ga Ubangijin mu a kowani hali da yanayi. Wallahi ba ka da abokin tarayya a irin k'auna da soyayyar danake maka.Yayi Murmushin jin dad'i"Ina alfahari dake nagode Ubangijin mu daya mallaka min ke a matsayin mata"Sumayya ALLAH yamiki albarka ya lull6emin ke da rahamar shi.Kwanan su hud'u suka musu sallama suka koma Kaduna garin gwamna.


Yau da gobe karyar ALLAH kome gudun ka sai ta ka mo ka.
Tsufa labari...mutuwa k'arar kwana.



18 Jumaada Awwal 1441
13 January 2020

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs



DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFI💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)


Shafi na goma sha hud'u


Zaman su lafiya cikin girmama juna. A yanzu fatansu bai wuce ganin Sumayya ta sauka lafiya ba.Tana kwance a doguwar kujera da yammacin tana ta nazarce-nazarcenta,tsohon cikin bai hana ta yin wasu abubuwan ba,taji muryar Mamanta.Wayyo!zama dak'yar ta shi da dabara kafin ma tayi yunk'urin ta shi ita ta shigo.

"Oyoyo Mama sannu da zuwa...

Da har na cire rai da zuwan ki. Taje ta d'auko ruwa da kanta tasha"Haba Kasham ya za ayi in k'i zuwa, bayan ni nace miki zan zo,kin san yanayin taran na mune yanzu haka ma sun tafi, ni a motar haya zan koma gida.Tabita da kallan tausayi"Sannu Kasham ALLAH yasauke ki lafiya, kwanaki ina ta mafarki wai kin haifi 'yan biyu. Tad'anyi murmushi kawai suka cigaba da hira.

Wannan karan bazan bar Kaduna ba har sai kin kaini gidan Shedrak.Tagyad'a kai"to Mama"takira Salim a waya dan baya gari.

"An ya Sumayya zan barki kifita kuwa? Ba likita ta ce banda yawan zirga-zirga ba?"Na sani kuma ban manta ba,dama Yaya Miqdad zan kira a waya yazo yad'auke mu.To idan baya kusa ko yana wani uzirin na shi baza ki takura mishi ba?"karka damu ai ta mu dashi bata 6aci,zan nemi alfarma na kuma san za a min.To shikenan ALLAH yatsare,kiyi zaman ki acan,nima Insha-ALLAH zuwa bayan Isha'i zan shigo sai inzo in d'auke ki.To nagode"ALLAH yak'ara tsare hanya yadawo mana da kai lafiya.Amin Sumayya nima nagode.

Makonni biyu da tafiyar Maman ta haifi kyakkyawar 'yar ta sunyi murna sosai dan ba a samu tangard'an kome ba,ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Salim d'in da tadad'e da rasuwa Ruqayya suna kiranta da Ummi.Gidan Alhaji Hafiz takoma Maman Hasan tana kula dasu yadda yakama ta,jegon ya kar6esu dan sunyi shar dasu saboda cimar abincin me amfani me gina jiki da k'ara kuzari ai shine jego "Abincin ka lafiyar ka...

Cikin wani dare tana tsaka da bacci kiran Mama yashigo tad'aga cikin fargaban abinda kunnuwan ta za suji dan ta san tabbass ba lafiya ba.Kasham Judith ta mutu tafad'a tana kuka "lallai soyayyar d'a da mahaifa sai ALLAH"kalli irin wahalar data basu amma Maman take wannan kukan?Itama mutuwar tadake ta,duk da sun san k'arshen alewa k'asa.To amma ai ba yadda za suyi dan mutuwa dole ce ko mutum ya yadda ko bai yadda ba idan ajali yazo to fa silke baya tarewa, Kukan mutuwa kuma ba ya dawo da matacce.

Babu addu'a tsakanin musulmi da kafiri dan haka sai tashiga rarrashinta da kalamai masu dad'i har tasa mu tayi shiru"nagode, ALLAH yamiki albarka bawanda yakwantar min da hankali sai ke"To za kuzo funeral service d'in ne?A ah Mama ba wanda zai zo kuyi abinku,amma Insha-ALLAH idan mukayi arba'in za muzo ai.Shikenan sai da safe takatse wayar.Tun daga nan har garin ALLAH j'arasa wayewa Sumayya bata kuma rintsawa ba,sai juye-juye take tayi da tunani barkatai daya cika k'wak'walwarta.

Suna hirar su da Hafsa a D'akin-shak'atawa sukaji sallama tare da k'wank'wasa k'ofa.Hafsa tabud'e k'ofar tana amsa sallamar. Yana tsaye tad'anyi murmushi"au kaine tabashi hanya bismillah shigo "cikin ladabi yadurk'usa har k'asa yana gaishe da Sumayya.Tagirgiza kai" tana nuna mishi kujera"ta shi ka zauna meye na durk'usan? Bai zauna a kujeran ba sai yayi zaman shi a carpet d'in yana d'an murmushi"ai nan d'in ma yayi.Mamana bata nan ne?Hafsa tayi yar dariya "Aikuwa dai Maman Hasan yau tayi nisan kiwo tana can wajan tsoho me ran k'arfe Malam Muhammad Aminu.


Alhassan d'aya daga cikin yaran da suke zama ma Salim a kasuwa ne, yaro ne me hankali da sanin ya kamata,tunda yaji sunan Maman Hassan shikenan yake ce mata Mamanshi, shi kuma Usainar shi ta rasu tun suna k'anana. Itama Maman Hassan tana yi dashi sosai indai yazo tana gida to sai ta san abinda tabashi kome k'ank'antar shi, tun yana jin nauyi baya kar6a har ya saba dan takance"Kai Alhassan anya wannan Mamana da kake kirana ba a fatar baki kawai ya tsaya ba? Uwa ta ta6a ba d'anta abu yaki kar6a? Tun daga nan yaba ta hak'uri idan tabashi sai yasa hannu biyu yakar6a yayi godiya.

Ya ajiye ledar hannun shi a gaban Sumayya"Alhaji ne yace in kawo.Wai ya kira layinki ya k'i shiga,sai bayan la'asar zai shigo.Bakome Alhassan,nima ina ta kiran shi bata shiga akwai matsalar sadarwa yau"kace ina gaisuwa sai ya zo d'in"Yamik'"Zai ji"yad'an kalli Hafsa "idan Mamana ta dawo nima amik'a min sak'on gaisuwa zan dawo ranar Juma'a musamman dan in gaishe ta.Tagyad'a kai" tam za taji"sukayi sallama.

Tana gama wanka suka tafi Zonkwa ita da Hafsa sun sauka lafiya kowa yayi murnan ganin su.Kwanan su biyar da tafiya da yammacin ranar sai kawai ganin Salim suka yi.Takalleshi cikin kulawa da mamaki"ba ranar Alhamis mukayi da kai za kazo ba?Yamayar da kanshi jikin kujerar"ranar alhamis ne amma na ka sa daurewa ne,amma yanzu ai hankali na ya d'an kwanta danazo na ganku"gobe kenan za ka koma? Yabud'e idanun shi daya fara rufewa yakalle ta da sauri"wai kina nufin tafiya zanyi in barku? Tagyad'a kai"haka nake nufi ga waya muna magana da juna.Yad'an harareta"kina wasa ne ko?Wani irin wasa kuma?Ai naga kwana goma kaba mu to yau munyi biyar ba saura biyar ba?

"Sumayya...

Yakirata...suka zubama juna idanu na wucewar wasu dak'ik'u yasauke numfashi yasa hannu yana yata6a kirjinshi dai-dai saitin zuciya "kina so na kuwa? Takalleshi baki a bud'e saboda mamakin furucin shi"haba Baban Ummi me yasa za kamin irin wannan tambayar?Yad'ora hannayan shi a saman tebur "saboda kince gobe zan tafi ma'ana ni kad'ai? Sumayya akwai ayyuka masu yawa agabana amma naturesu gefe duk da mahimman cinsu naza6i zuwa wajanki,sai dai kash...hak'ata baza ta tadda ruwa ba, dan na ga kina so ki watsamin k'asa a cikin idanu.

Tad'an 6ata fuska ni dai gaskiya... Yatari numfashin ta"haba Sumayya ta tawa ni kad'ai yad'an d'age gira"bazan iya hakurin jure rashin ki bane,magana awaya kad'ai ni dai bata gamshe ni ba shi yasama kika ganni ganin idanunki yamata wani kallo"mhm me kika ce ne?

Tasunkwui da kai"haba Sumayya yi magana mana,Salim mijiki ke kad'ai ne fa.Tad'an harareshi bayan kace ba alk'awari kad'auka ba,dan dai dole sai ka k'ara auren nan.Yagyad'a kai"gaskiya banyi wannan alk'awarin ba,kar baki yaci idanu su zo suna jin kunya.Tace"Uhhh madallah to yanzu kake so mutafi?A ah ai yamma ta yi kuma kinga Mama bata dawo daga kasuwa ba dole ai sai mun mata sallama, gobe da sassafe sai muwuce.

Sumayya takoma makaranta dan hutun da aka basu ya k'are,karatu sosai sukeyi ba kama hannun yaro saboda wannan shekarar za su gama.Sumayya ba ta da wata gagarumar matsala a bangaran karatu duk abinda bata gane ba, to tana dawowa gida Salim zai warware mata shi,bata ta6a sanin me tarin ilmi bane sai bayan auransu data shiga wani d'an d'aki dayake yin nazari da bincike wallahi tasha mamakin irin tarin littafan addinin data gani.bai ta6a nuna mata ya san wani abu ba sai da zama yahad'asu. Salim jarumine me damuwa da damuwar iyalinshi.

Suna hirarsu a D'akin-shak'atawa cikin nishad'i yajuyo kukan Ummi daga d'akin baccinsu ta tashi daga bacci kenan, yaje yad'auko ta,yabata ruwan zamzam d'in da suke bata tasha ya mik'a mata ita" ga ta ki bata abincin ta yunwa take ji.Tamarairaice Sumayya a wajan shayarwa ba ta da jarumta"kai ma ka san daga ta shinta a bacci baza tasha ba.Yagalla mata harara"ba yunwa take ji ba amma take ta k'ok'arin kai hannuna bakinta? Kar6eta mana.Tamika hannu ta kar6eta Tad'an 6ata fuska"ai ban san kana harara ba sai na ga idanun a k'asa.Yayi yar dariya"Hunn Sumayya ta ke dai bata abincin ta kawai ba na san neman magana.

Sun gama karatu lafiya kuma sakomako yayi kyau Malam Muhammad Aminu shi yasamo mata gurbin karatu a Jami'ar Madina dan babban d'anshi a can yake da zama shi da iyalinshi Salim shi yanemi wannan alfarmar kuma aka mishi amma ba da san zuciya ba, a ah adadin makin da suke nema to na Sumayya ya kai...anata mata shirin tafiya inda zataje ta yi Masters a kan dai Islamic Studies.Kamar wasa tafara rashin lafiya yau ciwo gobe sauk'i,suka tafi asibiti aka mata gwaje-gwaje har aka gano abinda yake damunta ciwon siga(diabetes) amma sun d'ora ta akan magani da wasu sharud'd'ai da dole sai ta kiyayesu in dai tana san zaman lafiya,kuma sun bata kwanakin da zata sake komawa asibiti dan su tabbatar magungunan suna aikin da ake so ? Idan basa yi sai a canja wasu.

Abokan karatunta kullum suna tafe, basa gajiya da zuwa gaisheta saboda halinta na karamci "masoya da mak'iya ba a guzurin su duk inda kaje halin ka zai ba kasu"abun hannu ta bai ta6a rufe mata idanu ba.Ranan Salim yakalleta "yaushe na baki kud'in da har za kice sun k'are Sumayya?Tad'an marairaice"Baban Ummi ni dai dan ALLAH kataimake ni kawai,akwai wacce mukama alk'awarin ba ta

Please Login or Register in order to submit comment