Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gwargwado dan tafi Yaya Karima ne sa ba kusa ba, amma Yaya Karima ta fita wadatar zuci.

Da safe kafin Inna tafito ya gama had'a karin kumallo,yashare tsakar gidan,ya wanke bayi,tafito tana shi mishi albarka kamar yadda tasaba "Ubangiji yamaka albarka, yarufa maka asiri duniya da lahira.

Yayi murmus"Amin Innar mu ALLAH yabar manake, yad'an kalleta"nifa yar aiki zan d'auko miki Insha-ALLAH kafin mukoma makaranta, ayyukan suna miki yawa,ni kuma a yanzu ina san ganinki cikin jin dad'i da hutu.Tayi yar dariya"to banda abinka Julaibib ina aikin yake da har za a d'auko maiyi?Dagani sai Alhaji,idan kana garine muke mu uku fa.Tagirgiza kai "ni kam nagode,da duk ya'ya haka suke jin tausayi da soyayyar mahaifansu to da al'umma ta kasance cikin tsabta da kwanciyar hankali mara yankewa,nagode maka gaya amma kabar zancen yar aiki,kai baka san 'yan aikace-aikacen ma motsa jiki bane?Na sani Inna"to kibari asamo miki koda wacce zata dinga miki hidimar tsakar gida,ke kuma kicigaba da yin abinci.

Ga kayan motsa jikina nan ba sai ki dinga amfani dasuba.Inna takama ha6a🤔tana dariya"Wuuu rabani da wuyu"kashin k'ota"kayan motsa jiki na zamani ai sai ku,ni ina zan iya da wad'annan k'arafa da na'urori? ALLAH dai yamaka albarka autana.Yayi murmushi yana shafa kwantaccen bak'i gashin kanshi me shek'i da kyallin irin mayukan gyaran gashin da yake amfani dasu. Suna gama karyawa yamata sallama yatafi shagonsu dan neman na halali,dansu an d'orasu a kan dogara da kai a hakan kuma suka taso,ba dogara da kud'in mahaifa ba...


Yana sanye da farar shadda,kanshi da farar hula zita,sai bak'in takalmi sau ciki,kafad'arshi ta dama rataye da dudduma,dawo warshi kenan daga sallar juma'a.A tsaye yake a k'ofar gidan yana tunanin kawun nashi jarumin mutum ne me kamanta adalci a komai nashi,ga shi yanaji da mahaifiyarshi da gasken-gaske,yana mata wata irin k'auna ta ban mamaki,kafin asamu me halinshi sai an tona,dan yafifitata sama da mata da ya'ayanshi,yar gatan tsohuwa kenan data kerema duk tsofaffin k'arninta, kai ita Hajiya ALLAH yamata gyad'ar dogo sama ya'ya,k'asa ya'ya tsakiya ma ya'ya,gaba d'aya ya'yanta takwas babu k'ashin yarwa.

Kai Julaibib ka tsaya awaje kamar wani bak'o me jiran abashi izinin shiga?Hajiyace, yakalleta da murmushi"to ai dama ke nake jira "bismillah muje...Suna tafiya suna hira har suka shiga cikin gidan.Musaddiq yafito daga d'akinshi, kaga ban tsaya jiran kaba, wallahi a sahun makararru natsaya,idan su Baba suka fito suka hangoni a haraban masallaci kasan zan sha fadane.Kamar ba dashi yake magana ba yashige d'akin yad'ebi wasu takaddu zai fita,Musaddiq yakalleshi bari akawo mana abinci mana dama kai nake jira. "Bazanciba" Ah bazaka ciba kamar yaya? "Azumi nakeyi" yabashi amsa atakaice. Azumi yau juma'a? Yagyad'a kai "Eh azumin tsakiyan wata sha uku,sha hud'u,sha biyar,to yau sha uku ga wata.Yagyad'a kai"ALLAH yabada lada"yafara kiran Sudaida,Sudaida,shiru Khausar nan ma shiru sai yamik'e to ina jin basanan barin d'auko da kaina,suka fito tare shi yawuce wajan Hajiya, Musaddiq kuma yatafi D'akin-girki d'auko abincinshi.

Sha d'aya da rabi a sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar asabar aka taso su daga makarantar allo, tana sanye da bak'ar abaya da farin hijab,da wasu littafan addini a jakar data rataya a kafad'a,allanta kuma ta rik'e a hannu.Suna zaune a dogon dakalin tazo tawuce kamar bata ganshi ba. Yamik'e da sauri yabita"haba ranki yadad'e Sudaida Sarauniyar Sinan,me yayi zafi haka idanu suke cin wuta?Takalleshi da 6acin rai"wai dan ALLAH kai baka da wajan zamane sai a cikin yan maro (Wiwi)? Zama da mad'aukin kanwa fa yana kawo farin kai. Yagirgiza kai cikin damuwa "Sudaida ba yadda zanyi da sune,ina zaune zaman jiranki suma sukazo suka zauna,wajene na kowa to ya zan musu?Khausar tazo tawucesu da takaicin Sudaida,ta rasa abinda yaja hankalinta wajan soyayyar Sinan.

Bakice kome ba.Sinan yakatse shirun. Tad'an harareshi"ALLAH yaso ka na na huce.Yayi dariya tare da shafa k'irjinshi bangaren da zuciya take.Yauwa ko kefa,kinga yanzu hankalin masoyi ya kwanta.Sukayi hirarsu sannan yataka mata kad'an sukayi sallama,yaso yarakata har k'ofar gida amma tace nan ya isa, dan tasan su Yaya Musaddiq suna wajan da autan Inna,kuma ba tasan wannan rikitaccen kallannashi me ban haushi dan ba magana zai yiba..Taja tsaki"ALLAH yasauwak'e mishi wannan halin...

Nagari ake so ba d'an gariba.


13 Rabi'a Thani 1441
10 December 2019


We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD... 2geda with Ra'ibs.




DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in.



...GWAJIN DAFI💔


Almost true story
Daga alk'alamin 🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)


Shafi na uku.


Kasham tabaro k'auyansu Madauci da yammacin ranar talata,bayan taji sauk'i daga jinyar da tayi na tsawon awanni ashirin da hud'u.Tashiga cikin makaranta da d'okin ganin Julaibib ta kuma hango shi a inda suke zama.Tak'arasa da saurinta "Barkanku da yammaci"Maimun abokin karatunshi ya amsa"Yauwa barka dai.Tatsare Julaibib da manyan idanunta masu maik'o cikin kallan k'auna me cike da shauk'i "kai bazaka amsaba kenan?Iskar data d'ibo tama bata isheshi kalloba.Tayi jimmm...na wucewar wasu dak'ik'u tana kissima wani abu a zuciyar ta,sai tad'an motsa kafad'a any way...sai anjima. Tajuya tayi tafiyarta tana murmushi.

Julaibib my enigma man...Salonka yana k'ayatar dani wallahi"...


Maimun yakalleshi"Kai nifa bangane ma wannan bita da kulli"dukan kabarin kishiyan ba"Meye had'inka da itane duk inda taganka sai tazo wajan?... Julaibib yafad'a mishi kome.Maimun Yagyad'a kai "to ka yadda mana tunda har ta amince za tayi sallah ba kuma wanine ya tilasta mataba,ai inaga ba wata matsala,kuma kayi jihadi ne,gata kuma Masha-ALLAH kyakkyawace.Yamik'e yana mishi wannan rikitaccen kallan nashi"bazan iyaba.Maimun zai sake magana yad'aga mishi hannu"dakata haka malam, taso mu tafi.Maimun yagirgiza kai "ba d'akin da zan tafi yanzu gwamma in d'anyi shawagina.Yajuya yayi tafiyarshi to shikenan.

Yana shiga d'aki ya ajiye Hand-out, yasa hannu yana 6alle botiren gaban rigarshi tare da lumshe idanunshi a kasalance,yacireta rigar yajefa a saman kujera,ya gaji lik'is ga rashin bacci,dan baiyi wani baccin kirki a daren jiya ba saboda karatu da binciken wasu littafai da yake yi na tafsirin Alqur'ani me girma,idanunshi har wani yaji-yaji sukeyi,a a hankali yafurta"yau da wuri zan kwanta...

"Zanzo tayaka kwana...

Bazato yaji an mishi wata irin runguma ta baya,zuciyarshi tabuga dammm...dan wallahi yaji tsoro...

"Zanzo tayaka kwana tunda Musaddiq baya nan.Tafad'a cikin rad'a

Kasham...zuciyarshi taraya mishi, tabbasss ita d'ince danga k'amshin turaranta nan... Yayi k'ok'arin raba ta da jikinshi amma ya kasa,dan ruk'on kura taga nama ta mishi...

Kanshi yayi wani irin sarawa.

Tafara mishi wani salo da hannayen ta a cikin gargasarshi dake kwance lufff bak'ink'irin da sheki...kar...kar...kar...Jikinshi yad'auki rawa"baah...ba... bahh..banasooo!...dak'yar yafuzgo furucin.Tayi lallausan murmushi tad'ago kanta tana kallan kwantaccen bak'in gashin kanshi...

Meye baka so din...???

Yayi shiru.Tagyad'a kai"tayaka kwannanne baka so ko wannan din?tacigaba da mishi wani salo da hannayenta a dai-dai saitin zuciya... Jikinshi ya mutu murusss...

My enigma say something hun"

Tasake fad'a cikin rad'a da wani irin salo na ta nayanga.Yadaddage ya hankad'eta...tafad'i tabaya akan katifarsu.Hanyar fita yayi sai dai abin mamaki "talaka da mata hud'u har da k'wark'wara me gari gwauro"ta kulle k'ofar dan dama baiji shigowarta ba.

Daga kwancen take kallanshi, yasunkwui da kai,gaba d'aya ya jike sharkaf da zufa kamar wanda yad'auki awanni yana matso jiki.Wata jijiya tafito asaman goshin shi rad'am kamar shatin bulala ranshi in yayi dubu ya 6aci...Amma jikinshi ba k'arfi kona sisin kwabo kamar wanda aka zarema laka.

Sai kuma jikinta yayi sanyi, tasan itace tasashi a damuwa tamik'e tsaye"Kayi hak'uri Julaibib "tahad'a tafukan hannayenta"Dan ALLAH kayi hak'uri ba naso ace ta dalilina kashiga damuwa,danni me k'aunar kace,farincikin ka shi nake so ba damuwa ba.k'walla yacika idanunta... muryarta tafara rawa

Bazaka hak'ura bane D'ansarai?

Yadda tayi furucin a hankali da wani irin salo,yasa yad'ago zai kalleta,itama shi take kallo caraf idanunsu yahad'u,yakauda kai dasauri yanajin wani irin abu yana zagaye ilahirin jiki da zuciyarshi,shi yasa baya san kallan wannan manyan idanun na ta masu maik'o.Kawai sai ta fashe da kuka,tsoro da mamaki suka baibayeshi to me aka mata wai???

"Kasham...

Yafurta sunan dak'yar.Tad'ago da sauri tana kallanshi.Sai kuma yayi shiru kamar me koyan had'a kalmomi da yadda ake furtasu.Idanunshi sun kad'a jawur.


Julaibib kayi hak'uri dan ALLAH".


"Bakomai...Tayi murmushi yau wace rana ya mata wata magana ta daban ba amsar daya saba fad'aba na "Bazan iyaba"saita kalleshi "to za ka aureni?Yayi shiru kanshi ak'asa.Tad'an motsa kafad'a. Tana zuwa kusa da k'ofar ya matsa da sauri kamar zai hantsila.Tayi yar dariya"Matsoraci kawai "ni ba abinda zan maka yanzu amma duk ranar daka shigo nan tanuna tsakiyar tafin hannunta na maka kattt...kisan mummuk'e,sai tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta wani murmushi ya su6uce mata. Tamishi wani kallan k'auna me cike da shauk'i...Tabud'e k'ofar tayi tafiyarta.Yasauke gwauran numfashi "wallahi da basu da lecture gobe da sassafe da yau yayi tafiyar shi gida kamar yadda Musaddiq yatafi.Yamaida k'ofar yarufe da sak'ata yasa mukulli sannan ya kwanta cikin wani irin yanayi.

Tana zuwa d'aki tafasa ihu tafad'a gado.Lidiya da suke yan'uwa kuma d'akinsu d'aya sai dai kowa da abinda yake karanta kamar dai Julaibib da Musaddiq tabita da kallo sai juyi take cikin wani irin yanayi,tabar yanka ganyen Ogu da take yi na abincin darensu,tazauna agefen gadan.

"Inzayadami Kasham?(Meyafaru Kasham)


Kasham tacigaba da juye-juyenta cikin wani irin yanayi,zuwa can kuma tamik'e zaune, tajingina kanta ajikin gadan cikin sanyin murya tace " Julaibib ne"

"Jesus Christ! Holy ghost fire!!!

Lidiya tafad'a tare da dafe kirji da duka hannayenta,tabita da kallan takaici taja dogon tsaki, wallahi kinji kunya,wai dan ALLAH me kika ganine ajikinshi daya tafi da hankalinki haka? Dogone k'akk'arfa,kar kuma kimanta Baranzan wanda kukayi alkawarin aure dashi,shima haka yake,ke ya mafi Julaibib tunda shi Sojane training d'in da yakeyi shi ko rabin-rabinshi ba ya yi, sunansu kuma d'aya"Maza"ko akwai wani abu bayan haka?Tayi lallausan murmushi"taja dogon numfashi a hankali take fitar da iskar tabaki ta hanci.Sannan tace"Hummm...Lidiya kenan ai maza kama suka tara amma halinsu ya bambanta. Tagalla mata harara"kin gama asara,ni dai banga abin so a wajen me shegen girman kai ba,shi ba kowan kowa ba dillalin kashi.Sannu wannan dazai amsa miki da yauwa sai yaga dama amma ke kina neman haukacewa saboda shi...kai tirrr...wallahi tayi d'as da yan yantsunta takoma kan girkinta tana mita Rubbish girl...

Kasham tazame takwanta"duk abinda zaki fad'a indai akan san D'ansarai ne bazai ta6a tasiri a zuciyata ba har abadan duniya, ina san shi koda shi aka tarama munanan halayen jama'ar duniya,ni na san ko waye Julaibib,ba shi da wani girman kai"so hana ganin laifi...


Suna zaune a shago jadawalin bikin Musaddiq d'in suke dad'a dubawa,dan saura kwanaki goma sha biyu.Tayi sallama daga waje tana sanye da riga da zani da dankwali na atamfa ruwan goro da ratsin k'ananan filawoyi ruwan madara da Bak'i,tayafa bak'in mayafi takalmanta bak'ak'e abinci takawo musu.


Wa alaikumussalam shigo.Tana shiga idanunsu yahad'u,yad'an saki fuska"yau Baba yayi tafiya sai zuwa yammaci zai dawo, ni kuma ban san irin garar da yake had'a muku ba idan kun kawo abinci"rake zan sha"sai Maths text book da Graph-book da za a sai mana ni da Yaya Khausar.


Banza yar k'auye,tafi kibamu waje, ba dama a tambayeta me take so sai tace"rake"to ba za a sai rakenba.Julaibib yad'aga mishi hannu "a ah malam shan koko fa kwanciyar rai,to me yamaka zafi?Yamaida kallanshi wajanta"koda yakema idan fitsari abin banzane kaza ma tayi mana.Ta sunkwui da kai"kowa yayi zagi a kasuwa ya san da wanda yakeyi,shine ko nama a wasu lokutan baya iyaci duk san shi da nama kamar kura sai gani sai hange idan ciwon hak'orinshi ya motsa.


Me kace? Musaddiq yatambaye shi fuska a yamutse.Abinda kaji na fad'a"ke Sudaida jeki ki...sai kuma yamik'e ina zuwa.Dakanshi yasiyo musu Maths da graph d'in yakuma kar6o musu gasassun kaji guda biyar,d'aya ki kaima Inna,biyu nasu Mama,ku kuma dukkanku kuyi hak'uri ku raba biyun.Tasa hannu biyu takar6i ledojin"mungode Yaya Julaibib".Yakauda kai daga kallan da take mishi.Jeki kinji karki daka ta wannan da hidimar aure tasa kanshi yake shirin yin gobara... mutum bai kar zomo ba sai kiga yana shirin ba shi rataya.Tawaiwaya inda Musaddiq d'in yake,shima su yake kallo.Sai ta toshe bakinta da sauri kar dariyar da take 6oyewa ta su6uce mata tashiga uku,idan yakoma gida da daddare zai iya bata na jaki...tajuya dasauri tabar shagon.Julaibib yabita da kallo fuskarshi da murmushi.


Yauma Musaddiq ya rigashi komawa gida tun ranar laraba yatafi,Maimun ma an aiko mahaifiyarshi bata da lafiya shima yatafi.Yana fitowa daga masallaci yanufi d'akinsu dan yanajin yunwa shi kuma yafi gane yadafa abinda zaici fiye da yaje capteria,yana da miya dan haka yadora farar shinkafa yazauna yana yayyanka kabeji, tumatir albasa da gurji.Tana jingine da bishiyar barankaci tana hangoshi dan abaranda ya zauna saboda cikin akwai zafi kuma ba wuta,tana mishi kallan k'auna me cike da shauk'i,shi ko baima san tanayi ba kunu a mak'ota.Tasauke numfashi tana kiran sunan shi a saman la66anta wani murmushi yasu6uce mata ranar da duk ALLAH yabani sa a akanka?....Hummm tagyad'a kai"d'aurin gwarmai za kasha amma na k'auna... tajuya tafiyarta.


Hajiya tashigo da sallama.Ya amsa cikin murmushi"Sannu da zuwa Hajiyarmu, yashimfid'a mata tabarma.Tace a ah mutanan Gidan-Waya saukar yaushe?Ai tun safe ina garin nan,wajejen k'arfe sha d'aya naje gida ba kyanan.Tagyada kai"Tabbas anyi haka,naje asibiti gaishe da Liman na masallacin juma'a ne.Yace "ALLAHU-AKBAR"ashe har yanzu ba a sallameshi ba?Ubangiji yabashi lafiya,zaman jinyar kuma yasa kaffarace. Ta amsa da amin,amin.Anjima ya kamata kuje kugaishe shi Yagyada kai "Insha-ALLAH.

Kai kadaine agidan?A ah Inna tana wankane"Tamishi kallan nazari"ni wannan zuwan sam baka min kyan ganiba,duk kayi wani firgai-firgai sai kace angon da hidima tasha kanshi kud'ad'en aljihu sun k'are,ko dai bakaji dad'i kwana biyu bane?Cikin yar dariya yace "to da Musaddiq kike wannan gugar zanan.Kai tafi can Musaddiq d'in wa?Shi da za a mishi auran gata,dakai nake yi.Yagirgiza kai"Hajiya ni dai lafiya ta k'alau.Cikin kad'a kai tace"amma dai sanin hali ai yafi sanin kama,idan ta kumbura tafashe tayi wari zamuji.


Bismillahi tamik'e"ni bazan zauna zaman jiran uwarka ba wannan halin nata tun na k'uruciya ashe bata barshi ba,taja tsaki haka takeyi idan tashiga bayi kamar tasamu gadon bacci da daddare,wani lokacin sai na bita da bulala take fitowa,shiga bayi ai lalurace da kake sauri ka kawar da ita kafito.Julaibib yad'an yamutsa fuska"Kai Hajiya"takalleshi saboda uwarkace sai ink'i fad'an halinta?Yagirgiza kai. Tace"to wooo ashe dai kowa yana san wawa haihuwarshi ce ba a so,dama wajanta nazo kwana biyu bangan taba"To kijirata mana.Wa?Ai tunda na mik'e sai dai kuma tabiyoni nawa gidan,tunda na ganka ai shi kenan ko baka gode bane? Aiko nagode miki ba kad'anba Hajiyarmu.Barin taka miki. Suna tafiya a hankali suna hirarsu,har gida yarakata sannan yawuce gidan Yaya Karima.Yaya Karima tadabance wallahi saboda halin dattakonta.

Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya,ranar juma'a aka d'aura auran Musaddiq da Safiyyah,abokan karatunsu sunzo d'aurin auran nan Motoci har hud'u cike tam da jama'a.Maimun yace gaskiya garin Zonkwa yamin ba zata yadda nake tunanin garin ashe yawuce haka.Aminu yagyad'a kai"k'warai kuwa muna yin addininmu da komai namu kamar yadda hausawa,musulmai sukeyi a k'asar Hausa tunda akwai malamai masana addini a fannoni mabambanta,ga makarantu sai wanda kaza6a.


Maimun yakalli Julaibib cikin tsokana "Yah D'ansarai inane k'auyan mutuniyar takane?Na ta6a tambayarta tace min Mabushi ko Madakiya?Ko mene?Ni na manta.Shiruma amsace. Yagyad'a kai "To da alama yan miskilancin sun motsa kenan.Aminu yamik'e"Maimun zo muje muyi shawagi kaji,zama waje d'aya tsautsayi.Suka bar Julaibib a d'akin,sunyi yawo sosai har Fadar Sarkin hausawan garin saida yakai Maimun yakwashi gaisuwa,Sarki me kirki da karamci yayita sa musu albarka yamusu addu'ar sumu ALLAH yabasu mata nagari,sai bayan la'asar suka koma gida dan shirin tafiya wa'azin maza da za ayi agidan Bak'i,bayan sallar magriba aka rufe taro da addu'a abokansu suka dauki hanyar Gidan-Waya, Aminu dai yarik'e Maimun wai dole sai ya kwana.A kwana d'aya da sukayi sunyi sabo naban mamaki kasancewar duk su biyun baki abin magana ne, sukayi sallama da alk'awarin kaima juna ziyara a duk lokacin da suka samu sarari.

Yafito daga cikin dalleliyar motarshi kirar Toyota bak'a wuluk sai walainiya takeyi a cikin hasken rana.Yana sanye da kakin soja,tafiya yakeyi cikin isa da gadara dajin cewa eh ya ne kayi hattara,ka kuma kiyaye ni ko kasha na jaki.Kwan kwan kwan...ahankali yake rank'washin k'ofar kwan kwan kwan...Just come in... yajiyo muryarta daga ciki.Yasa hannu a marik'in k'ofar yamurd'a yashiga.


Yabita da kallo tana kwance ruf da ciki da kayan bacci,dasauri yak'arasa gadon ya d'agota...suka kalli juna na wucewar wasu dak'iku, sai ta kauda kai a maimakon tabashi sumba kamar yadda tasaba.Yajuyo da fuskarta yana k'ok'arin sumbantar ta amma ta fuzge da sauri. Takoma ta kwanta "Beauty...tashi muje asibiti me ke damunki ne haka? Nace maka bani da lafiya ne? Hey don't fool me,idan ba ciwo ba me zai ramar dake haka?Idanun ta suka ciko da kwallah sai kawai tafad'a kirjinshi tafashe da wani irin kuka.

Lidiya tashigo da murnan ta sai kuma tayi saroro tana kallansu,Ya juya yana kallanta. Lidiya me yasamu Beauty haka?Tad'an motsa kafad'a"Ga kai ga k'afa ka tambayi me aka yanka? Ai ita zata fad'i meke damunta.Baranzan yayita rarrashinta dak'yar yasamu tayi shiru.Ya gewaye hannayenshi ajikinta,yana mata magana a hankali "na fa shirya mana party na Birthday d'inki da akayi bana nan.Lidiya tabashi hannu suka tafa. "Good Baranzan a ina za a yi?Yakalli Kasham yana murmushi"Kasham Hotel Kafanchan"Lidiya tayi d'an tsalke tana ihu "Hallelujah".

Tad'an daki kafad'arshi ta hagu,suka kyalkyale da dariya.Tad'auki jakarta"to yah ne? Bani kud'i zanje inyi nail fixes da gyaran gashi.Ya zarosu da yawa baiko tsaya k'irgawa ba ya bata.Tak'arba tare da sara mishi"Yes Sir ta buga kafarta da dama a k'asa"Thank you Sir.Tafita da sauri.Yasaki Kasham ya kunna taba sigari, yamata kyakkyawan zuk'a sannan yafara fesar da hayak'in tabaki ta hanci cikin shakara yana mata wani kallo.


I miss you deadly Beauty...

Yamik'a mata karan taban,tagirgiza kai "No I'm not in the mood"yakalleta nifa gaskiya yunwa nakeji saboda d'okin ganinki ko karyawa ban tsaya na yiba dan nasan zaki dafamin abinci me rai da motsi amma gashi baki da lafiya "Tashi muje in nemi abinda zanci".

Tacanja kayan baccin jikinta da wando legging ruwan zinare da wata shirt checker,tana sa ma6allan gaban rigar shi kuma ya d'auko katon ribbon ruwan zinare ya tattara gashinta daya hargitse yad'aure, yana kallan d'an k'aramin bakinta daya d'an bushe dan bata shafa mishi mai ba"ni fa da yunwan kome na zo, kema kuma kin sani,amma na ga kamar hak'ata bazata tadda ruwa yadda nake so ba ko?Tayi kamar bataji abinda yake fad'aba.Tarik'o hannunshi"dan ALLAH mutafi dan idan nakoma na kwanta wallahi ba inda zani".


Yana sanye da fararan kaya, bak'ar hula da bak'in takalmi sau ciki yayi sharrr dashi,ya rataya bak'ar jaka a kafad'arshi.Daga bayanshi yaji k'arar mota, sai ya kauce gefe.Tasauke gilashin bangaran da take zaune.

"Barka da safiya D'ansarai...

Yayi kamar ba dashi take yiba, yacigaba da tafiyarshi har yasha kwanar lecture hall d'insu ya6ace ma ganinta.Baranzan yaja motar yana tambayarta"waye wannnan ana mishi magana yayi banza da mutane?Tamaida kanta jikin kujerar motar"Ina ga baiji bane dan naga da headphone a kunnuwanshi.Jikinta yayi sanyi bata so yaganta da Baranzan ba wallahi,duk maganar da yake mata tamishi shiru kamar me bacci.


Wannnan party baiyi wani armashi kamar yadda suka saba yin chasu da rawar mak'osa ayi shaye-shaye yadda a kaga dama,dan gaba d'aya bata da walwala banda ma ya takura mata da ba inda zataje, kwananshi uku awajanta

Please Login or Register in order to submit comment