Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na dawo kan hanya nagode Zaujatiii...ALLAH yamiki albarka ya saukeki lafiya.Sai taji zuciyarta ta yi wasai"ta marairaice Zaujiii..to idan banyi hak'uri ba me zanyi bayan mun zama k'arfe da mayen k'arfe,mutu karaba takalmin kaza...?Hummm fushin masoya hutuhhh...


Rawa da k'afa d'aya sai gwani.
Da ba 'yan koyo da gwanaye sun k'are...



5 Rajab 1441
28 February 2020


We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.




DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION

{Da Inganci Mukayi Fintinkau}




Bismillahi wabihi nasta'in




...GWAJIN DAFI💔




Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na ashirin da hud'u.




Gobe zan tafi Sudan fa...takalleshi wani iri" haba dan ALLAH shine baka fad'amin ba sai da daddaren nan?Yagyad'a kai"ai dan ma mun shiryane da sai na tafi zan turo miki sak'o ni nawuce sai ALLAH yamin dawowa. Tad'an harareshi"gaskiya banji dad'i ba,ba fa abinda na shirya maka.Uh bakome kibani abinda yasauwak'a,kin san ni bana raina kad'an"da hanau ai gwamma mannau. Tare suka shirya kayan tafiyar.Washe gari jirginsu yad'aga.

A wad'annan shekaru goma sha ukun Julaibib Abdullahi D'an Sarai ya taka matakai da yawa a bangaren ilmi har ya zama shehin malami ferfesa gangaran(Professor)Yasai k'aton fili yana gina had'ad'd'iyar makaranta ta zamani bangare biyu bangaren addini da bangaren boko,aiki tuk'uru ake yi k'asa tanata cin kud'i,makarantace tun daga matakin prenursery,nursery,primary da secondary,abubuwa k'alilan suka rage mishi a bud'e makarantar,yana kuma da buri nan gaba yad'ora makarantar zuwa Jami'a me zaman kanta, yana kuma fatan makarantar tacigaba har bayan rayuwarsu,Ya'yansu su cigaba har jikoki...ta shahara har zuwa sauran k'ananan hukumomi da jahar Kaduna da d'aukacin sauran jahohin dake tarayyar Nigeria.

Abubuwan rashin jin dad'in da suka faru kuma shine tun bayan yak'in Zongon-Kataf da yak'in da akayi a k'waryar cikin Kaduna na k'addamar da shari'ar musulunci wani hargitsi da kisan rayuka bai kuma faruwa a k'aramar hukumar Zangon-Kataf ba,to amma a 'yan kwanakin nan manyan kabilun yankin Bajju da Atyap da sauran kabilu da basa sallah sun fara neman hana musulmai rawar gaban hantsi,takalan fad'a ba irin wanda ba sayi to amma bai damu hausawa ba,saboda duk fad'in doron duniya kowa ya shaida duk in da kaga musulmi kuma bahaushen mutum to ba wani abu yakai shiba face neman ilmi ta yadda zai bautama Ubangiji ba tare da jahilciba,sai kuma neman kud'i,kuma musulmi na da sauk'in halin da basa son tarzoma,wannan dalilin yasa suka d'an sararama hausawa amma ba hak'ura sukayi gaba d'aya ba,aka cigaba da zama cikin aminci da amana kamar yadda zuciyar bahaushe take a ko ina.

Tana kwance a d'akin baccinsu lullu6e da bargo tana chat da Nasmat,video call d'inshi yashigo ta d'aga da sallama,ya amsa da wani salo irin nashi yana murmushi"eyehhh... kaga Hajiya baki da wata matsala.Tayi yar dariya"godiyar Ubangiji a kowani hali da yanayi Zaujiii...Yagyad'a kai"ina yaran?Suna gidan Inna wai a can zasu kwana,yad'auki kofin gabanshi ya kur6i abinda yake ciki yamayar ya ajiye. Me kake shane?Shayi tad'an yamutsa fuska"asha lafiya.

Zaujatiii...Yakirata.Na'am.Nayi kewarki, bakya barina inyi ayyukan dake gabana,gangar jikina ne kawai a Sudan amma tunanina da zuciyata suna gida wajenki,gashi kwanakin basa sauri,anya ba visa za kiyi ki taho ba?Tawani marairaice"ni ma nayi kewarka,Yaya D'ansarai...Esbeer kaji?Kamai da hankali akan aikin da kaje yi,ai kamar yaune zaka dawo gida katarar da zuri'a da Iyalinka cikin k'oshin lafiya Insha-ALLAH,ka yi kwanaki goma sha shidda,saura kwana hud'u kacal ai...

Zaujatiii...na rantse miki da ALLAH daga shi ba wani kece duniyata,ina k'aunarki fa.Tagyad'a kai cikin gamsuwa da kalamanshi bawai shaci fad'i bane"ni ma haka Zaujiii...Ina k'aunarka a kowani hali da yanayi, baka da abokin tarayya a irin k'auna da soyayyar da nake maka"in poor and in rich,in sickness and in health...till death due part us''Yaja numfashi yafesar da iskar ta baki ta hanci"oh ya rahman...wani shauk'i da d'okin ganinta yamamaye shi...sun dad'e suna musayar kalaman k'auna sannan suka fara magana akan kud'in daya turo aka sai wasu kayan aiki na ginin makaranta.

Hantsi yadubi ludayi tashirya cikin doguwar riga kamfala,tatafi gidan Inna suna tattauna wasu al'amura daya shafesu,Abu me aikin da Julaibib ya d'auko ma Innar tashi tashigo da sallama ta ajiye farantin hannunta a gaban Sudaida tana tsokanarta "uwar biyu tashi kici kwad'on zogale na miki naga kwanaki biyu in dai kinzo abinda kike tambaya kenan, yau kuma naji baki tambaya"tamik'e zaune dakyar tana murmushi"nako gode miki Abu ba kad'an ba,sannu da aiki,tad'iba da bismillah takai bakinta, tafara taunawa cikin gyad'a kai "gaskiyar magana wannan k'uli-k'uli akwai d'ankaren dad'i da d'and'ano, tasa hannu a jaka taciro dubu biyu tabata"yaba kyauta tukwuici Abu.Abu takar6a tana godiya "madallah ALLAH yak'ara bud'i,yasaukeki lafiya... tad'anyi murmushi kawai,sai Innace ta amsa da" amin. Abu tajuya takoma D'akin-girki tana yaba halin kirkin zuri'ar Hajiya.

Bilkisu tashigo cikin shagwa6a ta rungume Sudaida tabaya"Mama kince za ki kira min Baba mu gaisa.Tad'an harareta"kin fa dameni idan nace na fasa sai ayi yaya dani?Asma'u da shigowarta kenan ta amsa dama me hali baya fasawa"wallahi abu me sauk'ine muyi k'uli-k'ulin kubura dake.Bata kula Asma'u ba tafara kiranshi,cikin d'oki Bilkisu ta manna wayar a kunne"Baba afqadtuka(nayi kewarka) Yayi dariya ALLAH Megadona?ALLAH kuwan Baba jiya ma nayi mafarki wai ka dafa mana naman talo-talo naci nak'oshi...tanata mishi shirme yana dariya... toh ni dai gaskiya idan bazaka dawo ba zan sa Kawu Aminu yakawoni in da kake ai yasan wajen ko Baba?Eh yasani.Ina Walida?Tatafi da Kawu Aminu siyo kindirmo a riga ni dai nace baza niba,shine wai yace idan suka dawo suma bazasu sammin ba,Baba kace Mama yau ta soya min dankalin turawa da kwai. Yagyad'a kai"to Bilkisu na har da lemun kwakwa ko?

Tajijjiga kai tana tsallan murna"zan rage maka har kadawo,yaushe zaka dawo d'in?Insha-ALLAH gadan bil-lail.Tawani fasa ihun murna Sudaida takwace wayar ta buge mata baki"ban hanaki wannan ihun murnan ba?Kawai ki cika mana dodon kunne.Inna tafara fad'a"nifa Sudaida ban san sanda kika 6aci da saurin hannu ba,tad'anja tsaki"haba ina amfanin irin wannan?Tayafito Bilkisu da hannu"zo nan muga bakin...yauwa kingani ko har ya fara kumbura.Sudaida tace"kiyi hak'uri Inna,Inna bata kulataba sai da tagama lalla6a Bilkisu ta daina kuka sannan ta kalli Sudaida"ya wuce amma a dinga kulawa... tayi murmushi"to Inna a ranta tana fad'in "wuuu na manta ashe hantar Inna nata6a a gaban idanunta.

Dawowar shi da kwana biyu ya tasata a gaba wai dole sai ta raka shi wata seminar,sun gama abinda za suyi suka wuce kasuwa yasai kayan wuta na mak'udan kud'ad'e da za a sasu a makaranta.Sudaida tayi tsaiii...cikin tafakkurin abinda za ta sai ma Yaya Aminu wanda zai burgeshi har yayi amfani dashi,saboda abubuwa da yawa basu d'ad'ashi da k'asa ba.Zaujatiii...tunanin me kike yi haka?Takalleshi"Yaya Aminu na rasa me zan sai mishi bani shawara"yayi murmushi"turare da kayayyakin da yake ayyukanshi dasu(artistry equipment) sune kawai zai yaba ko?Yauwa Yaya Julaibib wannan shawara taka ta samu kar6uwa nagode.

Bayan sallar Isha'i taje gida tasame shi a D'akin-shak'atawa yana shan fura da nono,ya maida ludayin cikin kofin yana amsa sallamarta"Sudaida kece haka da daddaren nan,ina autan Innan?Ta zauna a k'asa tana maida numfashi kamar wacce tayi gudun famfalak'i saboda nauyin da cikin ta yayi"su Bilkisu yatafi d'aukowa a gidan Inna,ni kuma nagaji da jiranshi shine nayi tahowata.Da sauri ya d'auko ruwa ya zuba a kofi ya mik'a mata,har ta kai tsakanin la66anta da bismillah yasa hannu yakar6i kofin"yi hak'uri ina zuwa,bulkodi(glucose D) yad'auko yazuba mata babban cokalin cin abinci d'aya a cikin ruwan yajujjuya sannan yabata,ta shanye duka,suka kalli juna suna murmushi"yaya a k'aro?A ah Yaya Aminu nagode kwarai taurarona.

Yazauna"da kinyi zamanki, kina kirana a waya ai kin san bazank'i zuwa ba.Yaya Aminu ba kome ai nima ina motsa jiki ne.Ya kalli k'afafunta da suka kumbura,har ranshi yaji tausayin ta"mata suna shan wahala da ciki fa,duk mace me ciki ai kana ganin yanayin ta ka san abin ba a cewa kome"lallai biyayya ga mahaifa dolen-dole ne ga duk mai son gamawa a doron duniya lafiya".Sannu kanwata to baza kije asibiti su baki magani ba? Tayi yar dariya ganin yadda yadamu dama haka yake nuna mata tausayi duk sanda suka had'u,tasa hannu tana murza k'afafun"wannan ba kome bane,ba shi da wani magani wasu suna yi yayin da cikin su ya tsufa wasu kuma ba sayi,duk cikina bai wani girma amma gashi na fara wancan makon ma naje an dubani kome nawa lafiya lau.

Yakad'a kai"toh Ubangiji yaraba lafiya.Amin Yaya Aminu nagode"ga wannan.Yakar6i ledan, yad'ago yana murmushin jin dad'i bayan yaga abubuwan da suke ciki "yanunata da yatsa duka na Aminu ne shi kad'ai?Tajijjga kai.Toh nagode ba kad'an ba"ALLAH yamiki albarka Sudaidan D'an Sarai. Sukayi dariya.Sun d'an ta6a hira har zuwa takwas da rabi sannan yace ta tashi yarakata gida dare ya farayi,suka jera suna tafiya a hankali suna magana har suka zo k'ofar gidan"shige gida kinji dare na dad'ayi ga hasken farin wata kar yasa miki mura.Sai da safe ko?Tagyad'a kai"ALLAH ya tashemu lafiya tabi bayanshi da kallo har yasha kwana ya6ace ma ganinta.

Ranar wata laraba a watan Rabi'u Awwal kabilun garin suka tashi da neman rigima ba wanda yataka ko ya zubar musu suka fito suka dinga zage-zage da k'one-k'onan tayoyi nan da nan gari yafara rikicewa kowa yatashi a wajen sana'arshi sai gida hankali a tashe, basu suka daina wannan abun ba sai wajen k'arfe d'aya na dare.

Sudaida ta sauke gwauron numfashi "Zaujiii...garin nan yafara bani tsoro,sallolin yau gaba d'aya kowa a gidanshi yayi bayan ga masallatai nan, amma saboda tsoron wasu marasa sallah an rasa wanda zai fita?To wai me aka musu? Yayi murmushi "kome zai wuce Insha-ALLAH gobe za a tattauna da Agwam Bajju (Sarkin Bajju) kin san shi mutumne me san zaman lafiya na san kuma zai ja musu kunne Kwanta muyi bacci kinji"gobe asubanci zanyi zuwa Gidan-Waya, har Sudaida tayi bacci amma shi idanun shi biyu yana tunanin al'umara mabambanta, lokuta da dama shima yanaji kamar yatattara yabar garin,to amma idan ya bar garin ai anyi gudu ba a tsira bane"gudun da ba a tsira ba kuwa kwanciya ta fishi".

Gaba d'aya zuri'arsu a garin suke Iyaye da kakanni,ai duk in da za shi dole dai sai ya dinga zuwa duba Iyaye da yan'uwa dan ya san mahaifanshi ba yadda za suyi su bishi ba,yasauke numfashi "zaman su a garin Zonkwa cikin wad'annan kabilu muk'addari ne tun daga Lauhul-mahfuz, k'addara ta riga fata,sai dai ya kamata suyi ho66asa dan suna so su fara musu cin kashi, shekaru kusan goma da suka wuce haka suka zauna cikin fargaba saboda fad'an d'aya 6arke sakamak'on k'addamar da shari'ar musulunci da akayi a Kaduna, a cewar su wai an kashe musu mutane da yawa a Kaduna dan haka suma za su d'auka fansa a kan musulman da suke zaune anan,tsawon lokaci haka suka zauna cikin tashin hankali,har dai kuma Ubangiji ya kawo k'arshen abun ba tare da sunyi kome ba...da wannan tunane-tunanen bacci yayi a won gaba dashi.

Sai dai cikin baccin na shi yayi mafarkin daya dinga na shud'ad'd'en shekaru"Kasham dai yau ma yasake gani cikin shigar Fulani kirar kalangunta ya fito rad'am kamar dai wancan lokacin amma idan tayi magana sai yaji muryar Sudaida...ya farka yanata nazarin wannan mafarki"toh me yak'un sane?...baccin da bai kuma komawa ba kenan har aka fara kiraye-kirayen sallar asubahin farko...

Hausa/Fulani Community Development Association(HAFCODA)Taza6i manya daga cikin su, suka tafi fadar sarkin Bajju,ya kuma kar6esu cikin mutuntawa, sun gabatar da abinda yakawo su,nasan zaman lafiya,da hak'uri da juna,shima Agwam Bajju a zahirance dai ya nuna 6acin ranshi"dan sanin asirin ciki sai hanji,ya kuma tabbatar musu su kwantar da hankalinsu lallai zai tsawatar musu ta hanyar yin gargad'i a dukkan majami'u(churches)ga wad'annan samari yan zauna gari banza masu son tada hargitsi,idan kuma basuji ba to lallai zai buga musu sandar shi(a al'adarsu idan har agwam Bajju yace zai buga sandarshi to duk abinda mutum zaiyi to ba zaiyi nasara ba)

Wad'anda ba son zaman lafiyar suke yiba suka had'a taron su.Shugaban nasu yabisu da kallo d'aya bayan d'aya"kunji abinda yake faruwa, dama hausawa masu san zaman lafiya ne tunda duk abinda muke musu basu ta6a mai da martani ba...toh ni dai kawai bana son ganinsu a garin mune,kome sune suke dashi sama damu sannan hakan bai wadatar dasu ba kullum aure mana Ya'ya suke k'arayi,wani abin takaicin ko da wasa baza kaga wata yarsu kace kana sonta zaka aureta ta yadda da kaiba,sai tace bata yadda ba tunda baka yadda da addinin taba,kunaji suna fad'a kakar za6e me zuwa zasu za6i mutum biyu daga cikinsu su tsaya takarar Chairman to kuna gani za su yadda su sake dangalama wani na mu k'uri'arsune?Yaja dogon tsaki"infact I'm sick and tired of seeing all those masu sallah bounch of idiot,we've to do something,something seriously againts them.

Wani daga cikinsu me rangwamen kafircin yace"da munyi hak'uri kawai ai mun riga mun zama d'aya,ga Ya'yanmu a cikinsu idan munyi yak'i mun kashe mazaje to yaya zamuyi da tarin mata da Ya'yansu?Nifa Ya'yana guda uku ne masu sallah.Cikin fushi shugaban nasu ya daka mishi tsawa"enough of this stupidity,so bloody what da Ya'yanka uku ne a cikinsu? Ko akwai 'yata a cikinsu na rantse muku zan iya kasheta, ba sune shegu masu kwad'ayin abin hannun hausawa ba? To da irin suma zan fara kisa,so dubu nawa suna wulak'antasu? Yanuna mishi k'ofa yana mazurai"now get out! Kai baka cikinmu.

Yasake bin sauran da kallo,suma shi suke kallo suna jijjiga kai alamar gamsuwa da matakin daya d'auka,fuskokin nan babu rahama da tausayi kona sisin kwabo,idanuwa jawur saboda shan burkutu da hayakin maro."nayi dai-dai?Suka had'a baki wajen amsawa"kayi dai-dai.Yakyalkyale da wata irin gur6atacciyar dariya da bata da dadin ji saboda giya da hayaki sun gama lalata hunhunshi"that's very good of you... Suka rufe k'ofa suna cigaba da k'usk'us d'insu na yadda zasu canja salon takunsu akan hausawa, d'akin ya kaure da dariyarsu dan sun gamsu d'ari bisa d'ari da matakin da suka d'auka...

Hankulan jama'a ya kwanta an cigaba da harkoki kamar yadda aka saba,sai dai kuma watanni kad'an a hankali abubuwa suka fara rinca6ewa za a koma yar gidan jiya,aka sake komawa cikin zaman d'ar-d'ar,basu da wani kwanciyar hankali, harbin bindigogi daga daji haka yake shigowa cikin gari ba dare ba rana alamar suna koyan harbi amma abun duka ba sanda da yake kuma dama bahaushen me ban haushinne na tanko me kan bashi,hakan bai d'ad'asu da k'asa ba,su dai neman halalinsu kawai. Mtswww ALLAH yakyauta.

Gidan shiru saboda yaran yanzu a gidan Inna suke kwana a duk ranakun k'arshen mako,Julaibib ya d'auko musu abinci,tamik'e zaune dakyar suka faraci da bismillah yana kuma mata bayanin aikin kafa ma'adanar littafai(bookshelves)da aka fara a d'akin nazari da bincike na makarantar (library)Tayi lallausan murmushi"Ubangiji yacigaba da rufa mana asiri duniya da lahira,gaskiya naji dad'i wallahi.Amin Zaujatiii...

Cikin firgici ta farka daga bacci a sulusin daren,wasu irin munanan mafarkai takeyi duk dare,har fargaba duk lokacin da rana tatafi zata fad'i magriba ta kunno kai,saboda da zarar ta kwanta baccin dare zata fara wannan mafarkan masu tashin hankali da sanya damuwa a zuciya.Julaibib yana zaune yana cike wasu bayanai a na'ura me kwakwalwa yaji motsinta,yajuya yana kallanta,tana zaune a tsakiyar gadon ta kama kanta da duka hannayenta cikin maimaita Istirja'i,rigar shimin dake jikinta ta jik'e sharkaf da zufa"Sudaida lafiya?Zafi kikeji haka?

Yamik'e barin kunna miki mukayyib. Takalleshi a rikice"Yaya D'ansarai ba zafi nake jiba,jikinta yakama rawa"kasan abinda nake gani kuwa?Wai...yatari numfashinta ta hanyar sa tafin hannun damarshi ya rufe mata baki sannan yakalleta cikin kulawa"ba wai bana so inji abinda zaki fad'a bane a ah ina miki kwad'ayin samun lada saboda bin umarnin Manzon ALLAH dan yayi hani da bayyana mummunan mafarki,duk abinda kike gani to ki nemi tsarin ALLAH akan abinda kike ganin,kiyi tofi a gefen hagunki sau uku"A'uzu billahi minashshaid'anir rajim "sai ki juya daga gefen da kika kwanta zuwa d'aya gefen.Wannan shine abinda yadace.Ta rungumeshi tana sauke numfashi"nagode da wannan tunatarwan.

Ranar wata Litini aka bud'e makarantar Julaibib a zangon karatu na farko me suna...

"Alfurqan Science Academy.

Musulman Zonkwa sunyi murna da farin ciki da samuwar wannan makaranta,Ya'ya dayawa an ciresu daga wasu makarantu an dawo dasu nan.Julaibib ya so kwarai ya zauna da Iyalinshi dan bata jin dad'i,sai dai hakanshi bata tadda ruwa ba dan da yammacin ranar ya mata sallama yakama hanyar Gidan-Waya washe gari da sassafe zasu tafi Jos asibitin k'ashi na Bima abokin karatunsune yayi hatsari a hanyar shi takomawa garin na su na Jos yakakkarye.

Sai k'arshen mako yazo,gidan Hajiya yafara zuwa kamar yadda yasaba,su Hajiya an dad'a tsufa sai dai Alhamdulillah tsufa me amfani tayi dan bata rikice ba,tana gane kome da kowa,sun dad'e suna hairarsu kamar yadda suka saba.Bilkisu kuma tagaji da jiranshi kamar yadda Sudaida tace mata ta zauna ta jirashi ba sai ta bishi ba ai zo.Tanata k'unk'uni tana turo baki gaba,Sudaida tana shiga D'akin-girki Bilkisu tasa dogon hijab d'inta har yana jan k'asa,wai haka sabuwar malamarsu ta Alfurqan take sawa,shine tace lallai itama haka zata dinga sawa Julaibib kuwa yad'inka musu ita da Walida kala-kala,tayi sand'a tafice da sauri.

Hajiya tana ganinta tace kai wannan yarinya da gaggawa kike hannun hagu a romo"sarauniya me D'ansarai ai ban ce zan rik'e miki uba ba.Julaibib yayi yar dariya ya tuno da Sudaida itace me fad'a mata haka musamman idan tana jin haushin su.Bata kula Hajiya ba tarungumeshi tawani shagwa6e"Baba tun d'azu kazo kayi zamanka anan.Yashafa kanta "Esbeeer Megadona yanzu zamu tafi.

Takalleshi cikin farin ciki"Baba yau Mama ta barni ni na had'a maka lemun karas,kashu da citta"kaji d'and'anon kuwa?Yagirgiza kai.Wallahi sooo luciousss...yadda tayi furucin yabasu dariya. Shima yace"thank you sooo very much my dear Bilkisu. Yarik'o hannunta suka mik'e"Hajiya barinje in sha lemun nan tunda sanyin shi. Bilkisu tad'an zaro idanu tana kallan Hajiya"ALLAH na mantane amma yanzu zan kawo miki naki dama Mama bata san nafito ba.Hajiya tace"tafi can sai yanzu kika tuna dani to bana sha.Tabi Julaibib da sauri da yasa takalmanshi yafara tafiya"ALLAH kuwan sai kin sha idan ba haka ba nima bazan kuma shan dabgenkiba.

Da daddare Julaibib yatafi kai Bilkisu da Walida hutun k'arshen mako gidan Inna,Sudaida tana shan rake taji tauuu...tauuu...tauuu...!k'arar harbin bindiga har tana hango kyallinshi ta tagar da take bud'e,raken hannunta ya su6uce, tarintse idanunta cikin matsanancin tsoro duk da abin ya zame musu jiki to amma na yanzu ya firgitata wallahi, tana Istirja'i yashigo da sallama yazauna yana kallanta"lafiya kuwa?Tad'ago tana kallan shi cikin mad'aukakin mamaki"kai bakaji harbin bindigar da akayi yanzu a jere har sau uku ba?

Yaya D'ansarai anya garin nan za a samu kwanciyar hankali a cikin shi? Yamaida kai da bayanshi jikin kujerar yana murmushi"matsoraciya kawai...Ta tsare shi da idanu. Yad'an kalleta" ke ba kome fa na...Ta girgiza kai"ba kome fa kace?Haka shekaran jiya danaje gida muna magana da Baba shima yace wai ba kome,to ni abinda bangane ba,a ba kome d'in me yakawo wannan harbe-harben ba dare ba rana?Anya ba koyan harbin suke yi ba? Baza kusa yan lek'en asiri su binciko muku me ake ciki ba Yaya Julaibib? Yaciro wata takadda daga aljihun gaban rigarshi da biro yafara lissafe-lissafenshi a ciki"to me kika ga anyi?Koma me sukeyi bata shafe muba...tayi shiru tana kallan shi aranta tanata maimaita Kalmar"kome sukeyi bata shafe muba... Yagama ya bud'e Laptop d'inshi yayi yan rubuce-rubuce a ciki ya rufe sannan ya kalleta"gobe Insha-ALLAH zani Kaduna mun tura kud'in kayayyaki amma har yanzu shiru tun wancan makon muke waya da manager na wajen amma sai wani hanya-hanya yake mana toh zani inga koma meye ganin idanuna.

Takalleshi wani iri ranta ba dad'i"nifa tafiye-tafiyen nan naka ya fara shigar min hanci da k'udundune wallahi,yana hanani rawar gaban hantsi, jiya fa yakamata kazo garin nan baka zo ba,na kauda kai banyi magana ba,yau kazo sai kuma gobe kace Kaduna za ka tafi washe gari da sassafe ka koma Gidan-Waya?A k'arshen makon ma baka hutaba?Ni gaskiya ban yadda ba shi Yaya Musaddiq d'in yatafi mana.Yayi yar dariya"Zaujatiii...uwar gidata anan duniya har a aljannah;ai ko Musaddiq yaci ya huta ko da yaushe shi yake tafiya,rabona da inje Kaduna saro kaya na kusa shekara fa,ko wannan karon bashi yace inje ba nine naga dacewar hakan shima yad'an huta...Kyan rawa da makar6i,amma kisha kurumunki Sudaidan D'ansarai ai na kusa ajiye koyarwar da nakeyi in dawo kan wannan makarantar gaba d'aya, kinga tafi-tafiye ya k'are sai mu manne kamar k'arfe da mayen k'arfe kullum muna tare mutu ka raba takalmin kaza ko?Yad'age gira yana mata wani kallon k'auna.Tayi shiru ta kyaleshi,dan wannan tafiyar da zaiyi ta 6ata mata rai sosai wallahi.

Shi kuma yacigaba da maganar shi duk da bata kulashiba,ai ya san tanaji tunda ba kurma bace,ranar litini d'inma bazan bar garin nan ba har sai munje an sake miki scanning ni wannan girman cikin yana bani mamaki a watanni biyar kacal.Hummm kawai tace tazame

Please Login or Register in order to submit comment