Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'i irin wanda nake so,idan an kawo naga kalar bai min ba dole yakoma yaza6o wani, ko kuma in ce yad'ibo su da yawa in za6i wanda suka kwanta min a rai...Habiba ta tari numfashinta"tabbb ai ko baki isa ba,tamata wani kallan uku ahu kai... ALLAH ko ya isa da wannan iko sai kace ke kika kawo shi duniya.

Sudaida ta kalleta cikin kukawa"Habiba kenan kisa ranki a inuwa dan ko ba iko dama ALLAH ai ya isa da kome,shine dama me kowa da kome na doron duniyar nan. Asma'u tamik'e"ke fa yarinyar nan wato salan mulkin ki kenan ki hana mutum rawar gaban hantsi ko? Batayi niyyar maida martani ba to amma Yaya Asma'u ta dad'e tana shiga mata hanci da k'udundune ya kamata ta fyaceta,kuma kunyar mara kunya ai asarace,idan babba ya yadda girman shi to ai ba laifi bane dan an taka.


Sai tagyad'a kai"ai kuwa dai Yaya Asma'u na zama kuturwar uwa zama dani dole,kuma duk wanda zai zauna dani d'in to d'aurin gwarmai nake mishi.Habiba da take ji kamar ta shak'e Sudaida dan haushi tace"to ai barewa baza tayi gudu yar ta tayi rarrafeba.Sudaida ta kyalkyale da dariya"ai dama kyan rawa da makar6i,kyan d'an yagaji ubanshi. Asma'u tafara tafiya "to Sudaida na yi gida amma dai kiyi a hankali dan ni bazan mulku ba, idan kuma kika matsa da yawa to abu ne me sauk'in gaske cire wando taka inyi waje dake.tak'arasa fita ba dan bata da sauran abin fad'a ba,a ah sai dan kar k'ilu taja bauuu...ga Hauwa'u nan itama munafuka ce idan anzo maida magana Sudaida za ta goya ma baya sai a d'ora mata sata da maitar,amma lallai sai tasa Dannarai ya k'ara aure, itama Sudaida ta so data tsaya ta ba ta amsa dan haka duk sunji ciwon kalaman juna.

Tacire hannun Hauwa'u da tayi tagumi dashi tana kallan su kawai,ta kashe ta da lallausan murmushi tunda ance iya ruwa fidda kai."kiyi hak'uri ba kud'i a hannuna amma idan bafade na autan Inna yadawo ranar jumma'a to zan turo miki shi wallahi har gida yazo yabaki kud'in d'inki dana takalmi da hijab,dan kin san ni a gidan nan k'arfine dani na gaban shari'a kum...Hauwa'u tasa tafin hannun ta rufe mata baki"dan girman ALLAH ya isa haka Sudaida.

D'akin-shak'atawar ya d'auki shiru na wucewar wasu yan dak'ik'u.Habiba tayunk'ura tamik'e cikin fushi bata musu magana ba tayi hanyar fita.Sudaida tad'an d'aga murya"toh uwar biyu sauka lafiya sai kin kiramu,ALLAH yaraba lafiya.A ciki ta amsa da"uhun.Tana fita Hauwa'u ta kyalkyale da dariya"matar D'an Sarai yau kin burgeni.Takad'a kai"ni har ga ALLAH banyi niyyar kula suba to amma naga abun na su yana neman wuce gona da iri ne,shiru-shiru kuma ai ba tsoro bane gudun magana ne"dodo d'aya akema tsafi,ba su suke aure na ba Yaya D'ansarai ne dan'uwan ku,duk fad'in mutanan doron duniya idan za suce yarabu dani idan yana so na,yana san zama dani to ba wanda ya isa ya rabamu,tunda ba wanda yake mishi auran nan,shi d'in da kanshi yake abinshi,haka kuma idan yace ba yayi ba wanda zai tilasta mishi zama dani.Hauwa'u tajijjiga kai "tabbsss zancen ki dutse"ALLAH yashirye su da sauran dangin miji masu mugun hali na mugunta "abun wani banza na su dukiya.

Tana kallan shirin Akhbar-Al'an tana cin awarar madarar shanu Khadija yar Khausar tashigo da gudunta cikin d'oki tafad'a jikinta"Inna Mamace tace in zo in tambayeki wai anjima za tayi tuwon shinkafa miyar shuwaka,shine tace wai a k'aton kwano guda nawa za a zuba miki? Sudaida tayi murmushi ta san wayau aka mata, kafin tayi magana kiran Khausar yashigo"Nana Khadija ta k'araso kuwa?Eh gatanan ta kuma fad'a min sak'on,ina za ki?Asibiti zan kai Misbahu ta kuma na ce dole sai munje da ita.Wayyo! har yanzu jikin ne?Shine Sudaida daren jiya kusan kwana mukayi bamuyi bacci ba saboda kukan shi. Toh ALLAH yasauwake zan shigo anjima idan kun dawo. Sukayi sallama.

Inna me zan fad'a mata?Takalleta da kulawa"bari sai anjima idan nayi wanka sai muje can muci ko?Toh Inna amma kamar kinyi wanka ga shi kina ta k'amshin irin turaren Baba D'an Sarai,ina son k'amshin. ALLAH Khadija?Khadija tayi d'an tsallan murna kamar yadda yara keyi"ALLAH Inna,to maza shiga d'aki ki d'auko kema in fesa miki,da gudunta ta d'auko Sudaida tafesa mata.Nagode Inna.Tad'an kama ha6arta"yauwa Khadija ga yoghort can kije ki d'auka,tad'an mak'ale kafad'a"Inna ni dai nafi son Caprisonne.Tamik'e shikenan muje in baki.

Sudaida tazuba mata idanu cikin tasbihi ga Ubangiji,k'udurar ALLAH dayawa take,wai yaushe-yaushe akayi auren su amma gashi har an haifi yar da za a aikota daga wani gida zuwa wani gida da k'afafunta da bakinta"oh ALLAH kaine ALLAH.Sharrr...sharrr...hawaye masu d'umi suka zubo mata"anya za taga gudan jininta a doron duniya kuwa?Ta rungumeshi a k'irjinta yaji d'uminta na uwa itama taji d'uminshi na d'a?Ta tuno da bak'ar magana habaici da dangin Julaibib suke mata,wanda in dai da mutum shi yake da ikon ba kanshi haihuwa to kuwa da tayi zuciya ta haifo musu yan hud'u a haihuwar farko,to ina ALLAH ne,ba kuma a mishi dole...tasake tuno kalaman Inna,Mama,kai rannan har Umma sai da tadinga kwantar mata da hankali akan dai tayi hak'uri tayi hak'uri,kullum haka suke fad'a mata musamman idan sun ganta cikin damuwa ko da ba wannnan ne abinda yake damunta ba "kiyi hak'uri Sudaida hak'uri kan tadda rabo,wata rana sai labari..

Khadija tamatsa wajenta"kukan me kikeyi Inna?Waya dake ki?Tarungumeta kawai tacigaba da kuka Khadija na tayata,sai da sukaci suka k'oshi dan kansu sannan sukayi shiru a hankali kuma bacci yayi awon gaba dasu.

Kiran wayar Julaibib yatashe ta daga bacci"wash ALLAH Zaujiii...yatare ta da sauri"me yafaru ne Sudaida?Tayo k'asa da murya"ba kai bane ina cikin baccina me dad'i ka tashe niba.Yayi murmushi"to fa tawa tasameni kenan malami da tallan jigida,kiyi hak'uri ki koma baccin anjima mayi magana.Uh uh ai kuma ko na koma baccin ba lallaine yazo ba sai dai in ta juyi"goben zaka dawo?Na so haka to amma bazai yiwuba dan gobe muna da serminar a jahar Katsina idan na dawo kuma akwai jarabawar da zan ma d'alibai,nima na so zuwa dan zan ba Inna wasu kud'i,amma barin miki transfer idan kika ciro sai ki kai mata,yanzu zan kira ta in mata bayani.Ranta bai mata dad'i ba amma ta daure ta amsa da to tare da addu'ar ALLAH yakiyaye hanya,sukayi hirarsu ta kewar juna sukayi sallama.

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba tabawa ranar sa a,Nasmat tazo gidan,suka rungume juna"oyoyo Nasmat...Sudaida ta d'auki Ahmad tana mishi wasa shi kuma ya bud'e wawulan bakinshi yana kyalkyala dariya.Nasmat taje tad'auko lemun sprite tabud'e tana mita "Sudaida kin zama abinda kika zama wallahi,abinda yasa meki ALLAH yasa kar yasamu sauran dangi.Tamata kallan k'arin bayani...Nasmat tagyad'a kai"in dai na zo gidan nan ni zan ba kaina ruwa ko abinci?Haka ake ma bak'o?Taja tsaki"na d'auka wani laifin nayi to kar kisha ruwan mana cikin wa zai shiga?

Takama ha6a"kar dai zama da mad'aukin kanwa Yaya Asma'u ya sa kema kin zama abinda kika zama? Haushi yasa Sudaida tak'i magana tanama Ahmad wasa yana cigaba da dariya.Itama tamik'e zuwa wajan taga tana amsa waya,tagama wayar tad'an kalli dai-dai kun mutanen da suke kai-kawo a safiyar sannan tacema Sudaida"na biyo miki ne muje duba yar gidan Yaya Asma'u da jiki.Hu'un tafad'a ba tare tadata bud'e bakintaba.Menene kuma hu'un?Nasmat ta tambayeta.Tamik'e zaune daga kwanciyar da tayi tad'ora Ahmad a cinya"ke ni fa bazani in da raina zai dinga 6aci a banza ba,dan na riga na k'una bana tsoron wuta.A ah Sudaida kiyi hak'uri kawai idan an miki kan kara karkice za kiyi na itace.Tayi wani huci cikin kad'ai"ai na rantse da girman ALLAH ni yanzu har na gungume zan iyayi yadda zai shekara yanaci,kawai sai tarufe idanu tana zazzaga fad'a,Nasmat bata kar zomo ba amma an bata rataya.

Tazuba mata idanu har tayi tagaji dan kanta tayi shiru,sai kuma tayi kwafa"banda ina duba darajar yan'uwantaka da dangantaka kinaga zan bar Yaya Asma'u tacigaba da cin dunduniyata tana min hawan k'awara yadda taga dama?Nasmat tagirgiza kai sannan ta amsa cikin natsuwa"a ah baza kiyiba, to amma karki manta hak'uri kan tadda rabo...idan ka gaida wada da tsawonka zaka mik'e...Sudaida ALLAH yana son masu hak'uri masu had'iye fushi,da dama su rama abinda aka musu amma sai suyi hak'uri ba saboda kowa da kome ba sai saboda zatin ALLAH... tacigaba da rarrashinta har fushin daya mamaye zuciyarta yalafa,ta kuma yi nasarar janta suka tafi dubiyan...



Da kunu da miya har abadan duniya ba za su had'uba sai dai a cikin ciki.


27 Jumaada Thani 1441
21 February 2020

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.




DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}




Bismillahi wabihi nasta'in




...GWAJIN DAFI💔




Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na ashirin da biyu.




A wulak'ance da halin-ko-inkula kamar yadda tasaba haka yauma ta amsa gaisuwar Sudaida, amma tanata jan Nasmat da hira suna shirin tafiya sai ga Hauwa'u itama ta zo dubiya,suka tsaya ana gaisawa, Hauwa'u tamatsa kusa da Sudaida "yar'uwa yayane jikin ne ko garin ne,ko wannnan bak'in mijin na kine dayaje yashare waje a Gidan-Waya?Takai mata duka a kafad'a,tagoce da sauri yabi iska.Kin sama mijina rabin raina idanu fa,meye darin gamarki dashine wai?Asma'u da wata k'awarta yar duniya me irin halinta sukayi dariya suka tafa"haka fa kullum ana nuna ana k'aunar miji amma an k'i nuna mishi k'aunar a zahirance,ta hanyar barin Ya'yanshi suzo su shak'i iskar duniya,takad'a kai cikin ta6e baki"kullum ana ba mutum amma har yanzu ya kasa yin zuciya yak'ar6a ko da sau d'aya ne,sai dai ayi ta asara,a wanke abun yabi rariya.

Hauwa'u takalleta"ke wai Asma'u kullum ba ki da abinyi sai gori?Sannan ma dake ake magana me ko ko ita tace miki ba tajin dad'i?!Nasmat ma ranta ba dad'i tace"haba Yaya Asma'u wannan ba girmanki bane wallahi,kin san duk me gori matuk'ar bai tuba ba to yana haramtama kanshi rabon alheri ne a lahira, sannan wannnan gorin ma d'an Adam d'in doron duniya ba shi da iko akanshi,wannan ba huruminki bane Yaya As...kafin tak'arasa sai ga Hajiya tashigo d'akin tana d'agama Nasmat hannu "dakata Nasmat in dai gori ne ta tara ta samu, Hajiya tanuna kanta"ni d'in nan yau har goruba zan mata, zanyi maganin iya shegen nan k'auri da kare.

Tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta"ki bud'e kunnuwanki da kyau ki saurareni,na rantse miki da girman ALLAH in har Sudaida bata haihuba to ba itace ba ta haihuwaba,k'aninkine Julaibibi,matan kakanku ai su biyune uwargidan shice mahaifiyar ubanki,su uku tahaifa,amma amaryar shi sai da ta haifa mishi Ya'ya goma shabiyu, ubanki gashinan shima Ya'ya uku yahaifa,d'aya kanin na shi yahaifi Ya'ya biyu, d'ayan kuma ai har yakoma ga ALLAH bai haihuba,matar shi data gama takaba tayi wani auren bagata can da Ya'ya bakwai ba?

Karima Yayarki Ya'yanta biyu,ke kuma yarki d'aya jallin-jal kamar rai,sai 6ari da kika ta6a yi sau d'aya duk shekarun da kukayi a gidan miji,mata nawane ta dangin kakar ta ku ga sunan a gidajen miji ba haihuwa sai dai suci su k'oshi suje masai su juye kayansu?Ai suna da yawa saboda ku ba irin haihuwa bane,toh Sudaida fa?Su goma sha takwas ne a gidansu,kuma duk cikin Ya'yana ba uwarki ce kawai me Ya'ya uku ba?Tanuna ta da yatsa"to dan haka ahir d'inki hawainiyarki takiyayi ramar Sudaida, kuma ko yanzu da k'anin na ki zai rabu da ita,toh idan ma na rantse ba kaffara a kaina bazata rufe shekara a wani gidan auren dazata yiba za ta haifo gudan jininta takuma sa zani tagoye abunta,ai ga sa'o'in auren na ta nan kina ganinsu ganin idanunki kowaccensu ta fara kafa na ta Iyalin...

Tambayar me jikin da batayiba kenan ta ajiye ledar ayaba da lemun tajuya cikin fushi"jahilar addini kawai wacce bata yadda kome muk'addari ne tun daga lauhul-mahfus ba,na rasa a ina kika d'auko wannan bak'in halin na ki,banda ma ke shimmeruwa uku ce(sha-sha-sha)Sudaida ba yar'uwarki bace da zaki iya tare mata fad'a a inda kikaga za a wukak'anta taba?Toh karki daina abinda kikeyi ai hassada ga me rabo ta kice...Nasmat da Hauwa'u sukayi lallausan murmushi suna shima Hajiya albarka"ALLAH yak'ara girma me amfani Hajjaju makkatan...kaza dai garin tuno-tone take tono wuk'ar yanka kanta...baki shi ke yanka wuya.Sai da Hajiya tabar gidan sannan Asma'u tafara nad'e tabarmar kunyarta da hauka.

Da wannnan 6acin ran Sudaida tawuce ATM taciro kud'in da za ta kaima Inna,sukayi kaci6is da Aminu shima ya zo ciren kud'i yabud'e mata murfin motar"shigo ki jirani tunda yau na ga ba layi.Dak'ik'u basu wuce goma ba yadawo.Yaya Aminu gida za ka koma? Yana tayar da mortar yake amsawa "Jos zani,amma ke zan mayar gida wani abune?Tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata sharrr... "mutafi kawai sai ka saukeni a Gidan-Waya.

Sun d'auki hanya sosai sannan yajuyo cikin kulawa yakalleta"wai yau waya ta6a kanwata rabin raina ne?Tad'anyi murmushi"share kawai Yaya Aminu ni da Yaya Asma'u ce.Yakama ha6a wuuu... Asma'u ciwon idanu sai hak'uri,ai ko jiya danaje dubiya nima sai da muka hau sama muka fad'o,wai nayi kud'i bana son zuwa gaisheta,kinji sai kace wata Yayata.

Sudaida takawar da zancen ta hanyar tambayar Siddiqa nan da nan ko yayi lallausan murmushi suka shiga hirar arziki har suka iso Gidan-Waya,har k'ofar gidan da Julaibib yake yakaita anan rukunin gidajen malamai,yasake kallanta cikin kulawa"Sudaida kiyi hak'uri na san kinayi amma ki k'ara wata rana sai labari,ai duk abinda yayi farko to tabbasss yana da k'arshe,wallah-azim da ana siyan haihuwa da kud'i toh dana sai miki kome tsadarshi,toh ina abin na ALLAH ne "ance da kare me sunan maza.Tajijjiga kai"na sani Yaya Aminu na kuma gode, duk cikin Yayyina kaine taurarona"Ina sonka sosai.Sukayi murmishi"nima nagode kanwata rabin raina data za6eni sama da kowa a matsayin tauraronta,toh me kike so in siyo miki a matsayin tsaraban mutan Jasawa?Tagirgiza kai"bani da za6i kasiyo min ko menene nagode.

Yayi yar dariya"tunda kin bani wuk'a da nama Insha-ALLAH za6in nawa zai burgeki,idan nadawo zan shigo in baki tsaraban,sai in kar6i kud'in da kikace zan kaima Inna,kiyi hak'uri ko?Nagode Yaya Aminu tabud'e motar tafito,tarufe mishi"adawo lafiya ALLAH yatsare,suka d'aga hannu suna ma juna adabo.Tabi danjojin motar da kallo har ya6ace ma ganinta.Tarik'e k'ugu tana fesar da iska ta baki ta hanci sannan tasa hannu a jaka ta d'auko mukullin gidan tabud'e tashiga.

Wani k'amshin turaren d'aki da sassanyar iskar da take shigowa ta tagogin da suke bud'e yamamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta,sai taji ta samu natsuwa ta lumshe idanunta tana jan numfashi"Yaya D'ansarai wallahi me tsabtane,ji yadda yazauna yagyara gidan kamar mace. Tashige d'akin bacci,tazauna a gefen gadon tad'auki wani d'an k'aramin hotonta da ya ajiye a dirowar gefen gadon,ta d'auki hotonne a wani excursion da sukaje a Wadom akan harkar gona tun tana aji biyu a k'aramar secondary,tak'arema hoton kallo tana tuno irin kyan da Julaibib d'in yace wai tayi...Wanda ita dan haushin irin munin da tayi ta turo baki gaba zata yaga sai gashi ya shigo gidan shine yakar6a,tamaida hoton ta ajiye tana murmushi ita tama manta ta ta6ayin hoton.

Taje tayi wanka tabud'e wardrobe tad'auko riga da zani na shadda ruwan makuba dan dama akwai kayanta a gidan,wasu lokutan idan tazo makaranta ba ta komawa Zonkwa sai tayi zamanta koda ba Julaibib a garin tunda baya samun zama yau yana Zari'a gobe yana Katsina, jibi yana Kaduna,haka dai haka dai ake ta gwagwarmaya da zirga-zirga a cikin rayuwar.

Tana azkar d'in yammaci bayan ta idar da sallar la'asar Aminu yashigo ya ajiye mata injin d'in matse ruwan rake tagama azkar d'in sannan takalleshi cikin murna da shakka tanuna injin d'in tana kallanshi"Yaya Aminu da gaske?Yajijjaga kai "Sudaida ko da nake da raha ai na san irin rahan da nake yi da kowa,bazanji dad'i ni akaran kaina amin irin wannan kyautar bayan na sa hannu na k'ar6a,sai kuma a kar6e wai wasa akeyi,dan haka bazan ma wani ba, bare ke kanwata da nake ji da ita a cikin k'annina,yad'an kalleta a kwai rake a gidan nan? Tamik'e ai ba a rasa nono a riga sai dai idan rigar ba ta tsurar fulanin asali bane,a na'urar sanyaya abubuwa(fridge)tad'ibo ferarrun rake guda biyar takawo mishi,yauwa d'auko wuka kigani.

Yakar6i wuk'ar yak'ara yankasu k'anana sannan yasa a ciki,yan dak'ik'u kad'an yad'auki Kofi yajuye mata tataccen tsurar ruwan rake, yamik'a mata tasa hannu biyu takar6a takai tsakanin la66anta da bismilla takur6a,sai kawai tacigaba da sha har sai da tashanye duka.Suka kalli juna,yad'an dage gira"toh ya?Takyalkyale da dariya tana jijjiga kai "Alqur'an yayi ba k'arya,nagode Yaya Aminu ALLAH yasaka maka da mafificin sakamakon shi.Amin Sudaida"ke ma muk'amuk'inki sa huta da tauna,to kai baka shaba?Yagirgiza kai"sanda za a nuna min sahihancin injin d'in an matsa min na sha. Yamik'e yana gyara zaman hular shi"to barin kama hanya,taje ta d'auko mishi kud'in da zai kaima Inna sukayi sallama.

Tana wanke d'anyen na'ana'a yashigo D'akin-girkin a d'okance"Zaujatiii...saboda ALLAH dama kinzo garin amma baki fad'a min ba?Yazuba mata idanu"to yanzu dana wuce Zonkwa ne fa? Tad'an motsa kafad'a"duk d'aya 6arin manshanu a miya.Yarik'ota cikin kewa sai kuma yasake ta barinje in sallami d'aliban da suke jira a waje yawuce D'akin-shak'atawa yad'ibo wasu takaddu yafita.

Sai da yayi sallar Isha'i sannan yashigo yazauna a kusa da ita yana ganin rubutun da takeyi a na'ura me kwakwalwa"barka da shigowa Yaya D'ansarai.Yagyad'a kai"barkanmu kema kinzo lafiya?Tayi shiru kamar bataji shiba,wucewar wasu dak'ik'u kuma tad'an kalleshi"yayi murmushi kina k'ok'ari fa ALLAH yak'ara basira.A tak'aice ta amsa da "amin.Sai kuma tarufe Laptop d'in tamayar ma'ajiyarta.

Ta dawo tazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna,zama nesa dashi da tayi yabashi tabbacin akwai maganar da zata fad'a mishi me mahimmaci dan haka take yi,dan haka shima yadad'a gyara zama dan yaji yau kuma dame tazo?

"Yaya D'ansarai kana k'aunata kuwa? Baiyi tunanin abinda za ta fad'a kenan ba,amma sai ya 6oye mamakinshi ya amsa mata kai tsaye"eh Sudaida ina k'aunarki.To na rok'eka da girman ALLAH karabani da damuwa,kome yanada iyaka to tsakani da ALLAH abinda zuciyata za ta iya d'auka kenan,idan ba haka ba to ba abinda zai hanata kumbura ta fashe k'arshen rayuwata a doron duniya ya zo kenan,tanuna kanta da yatsa,ni na san ba autar mata bace dan haka zan tayaka addu'a ALLAH yabaka wacce tafini, wacce zata haifa maka sanyin idanu tunda ni na kasa, nima ALLAH yabani dai-dai ni.

Yakalleta cikin natsuwa"me aka miki da kike zancen rabuwa?Da mamaki takalleshi"au yanzu baka gani ba?Saboda bakai ake ma ba?Tayi wani huci cikin kad'a kai"toh madalla,amma Yaya Julaibib gaskiya ni dai bazan iya wannan zaman ba,duk lokacin daka shirya nima a shirye nake zan ba ka sarari.Tamik'e.Jinan Sudaida koma ki zauna. Bata zauna ba sai kawai ta durk'usa a gabanshi tafara kuka

"Yaya D'ansarai kaji tausayina mana bazan iya jure wani wulak'anci da bak'ak'en maganganu ba dan kawai ban haihuba,bana so zumunci ya6aci ne amma na rantse maka da girman ALLAH da da kaina zan d'auki mataki.Tasake fashewa da matsanancin kuka,kukan abu biyu take yi,gana rashin haihuwar akaran kanshi,gana wulak'anci da tozarcin da ake mata akan dai rashin haihuwar me makon ma abarta taji da abinda yake damunta.Haka ta dinga fad'ar duk maganar data fito daga bakinta ba tare data tauna ba.

Yad'ago ta fuskarta sharkaf da hawaye da majina yazuba mata idanu na wucewar wasu dak'ik'u saboda ya rasa abinda zai fad'a mata,sunyi waya da Hajiya kuma tafed'e mishi bire har bindi "tabbasss an dad'e ana mata wannan cin k'ashin, amma shi da ita bata ta6a fad'a mishi ba,ko ya ganta cikin damuwa idan ya tambaya za ta girgiza kai"tace ba kome ko tace wani abu kazane ba gorin rashin haihuwaba,yayi tsaiii...har yasamo bakin zaren,sai yayi murmushi"kinga Sudaida share hawayenki tabbasss ni D'ansarai ina k'aunarki dan haka zan rabaki da bak'in ciki da damuwa.Takalleshi kallan k'arin bayani"Yajijjiga kai"kiyi hak'uri kibani lokaci zanyi tunanin yadda al'amuran za su kasance ba tare da an 6ata zumunci kamar yadda kika hango haka ko?

"Zaujatiii...ina so kimin alk'awari zaki bani lokacin ba tare da kin sake tambaya taba har sai na zo miki da zancen,lokacin na samu mafita...za tayi magana yatari numfashinta"dan ALLAH kar kice kome,ai kin san ba zanyi abinda zai cutar dake ba. Tayi shiru kawai tana share hawaye tamik'e zuwa d'akin bacci takwanta tare da d'ora kanta a saman matashi.

Kad'an yaci abincin daren sannan yaje yayi wanka yasa kaya marasa nauyi na shan iska,yazauna a doguwar kujera ya barbaza wasu takaddu yana aikin cikesu d'aya bayan d'aya sai dai ya kasa jure rashin Sudaida,kewarta ta dame shi dan haka yamik'e zuwa d'akin.Suka kalli juna tana kwance da wani littafin lissafi tana nazarin shi,tamaida kanta cikin littafin amma ta gagara cigaba da nazarin,yazauna a gefen gadan sannan yasa hannu yakar6i littafin.

Tawani 6ata fuska"Yaya D'ansarai gobe fa muna da jarabawa shi yasa nake nazarin nan.Yamata wannan kallan da yake ba ta haushi yagyad'a kai"uh na sani...ni ma gobe zan tafi Katsina yaya kenan? Tad'an turo baki gaba tana dad'a gyara bargon data rufa"toh kowa sai yakwanta yayi ishashshen

Please Login or Register in order to submit comment