Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma da wane ko wance Me-Lambu suke amfani.Ibrahim Me-Lambu ya samu sunan Me-Lambu ne saboda sana'arshi ta saida kayan lambun kamarsu:-tumatur,tattasai, albasa, alaiyaho,yalo,latas, karas,lafsir da sauransu da sauransu.

Asalinsu yan k'aramar hukumar Tsanyawa ne ta Jahar Kano.Cirani yakawosu garin Zonkwa Iyaye da kakanni,dad'in garin da kuma k'addarar ALLAH inda ya rubuta maka zama to ba makawa anan d'in zaka zauna kome dad'i ko rashin dad'in waje,da suna zuwa ganin gida daga baya suka daina sai kalilan daga cikinsu dan suna da yawan gaske a Zonkwa,wasuma basu da sauran dangi na jini a Tsanyawa,Unguwa gudace dasu k'atuwa ta musamman da ake kira"Lungun Kanawa.Sukayi zamansu a nan suka hayayyafa.

Alhaji Ibrahim matanshi na aure guda biyune,Mama itace uwargida kuma mahaifiyarsu Musaddiq,Khausar,da sauran kanninsu maza da mata.Sai Umma mahaifiyarsu Aminu,Adnan,Sudaida da tarin kaninsu maza da mata.Kan ya'yansu a had'e yake saboda matan sunada fahimtar juna,mijinsu kuma yana musu adalci dai-dai iyawarshi.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿

Julaibib yana zaune atsak'ar gidansu yana nazarin wani littafi duk da wancan makon suka samu hutu.Musaddiq yashigo da sallama,yad'an daki kafad'ar Julaibib "Haba malam an samu hutu kaima ya kamata ka hutafa"Julaibib yayi kamar ba dashi yake maganaba.Musaddiq ya jijjiga kai"gaskiya na gaisheka"yawuce dak'in Inna, tana zaune a inda ta idar da sallar walha,sai yasaki labulan"to barinje na dawo anjima".Daga ciki ta amsa"shigo ai na idar.Yazauna suna gaisawa,sai yafara mata hirar Safiyya budurwarshi da sak'on data bashi yakawo mata.

Aminu shima yashigo da sallama yana fad'in shi wai D'ansarai baya gajiya da karatune Inna?Yakama ha6arshi da hannun dama"Tabbb ina ruwan Alhuda-huda,koda yake bazai gajiba tunda yafi sha'awar zaman gida, gaskiyar magana wannan da macece da sai ince ALLAH ya kashe ya ba mijinta kakarshi ta yanke saka wallahi.Inna takalleshi"kamar yaya?Yawaiwaya inda Julaibib yake zaune"o Inna aishi ya huta da fitinar mata tayawan tambayar unguwa, zani gidan wance,anyi haihuwa zan shiga barka, zanje dubiya dan gidan wance an mishi shayi, muna da biki agabas,gobe suna a arewa,jibi tarewar yar gidan wance a yamma, zani, zani, zanin mata ai bata k'arewa.Inna tayi dariya.

Julaibib yakalleshi ba laifinka bane, ka ci bashi zan kuma rama.Aminu yagyad'a kai"Nima zan so haka,ina nan ina jira,yashige D'akin-girki yad'auko kunun tsamiyarshi yafito"Inna yau naci aikine kamar ba gobe,tun daga sallar asubahi sai yanzu zan koma gida.Inna takalkeshi da tausayi "Wayyo sannu,a lallai ka aikatu neman kud'i makahon aiki, ALLAH dai yak'aro masu albarka.Amin Inna nagode barinje in kwanta.To ALLAH huta gajiya.

Kasham...da yaransu na Bajju yana nufin abu me kyau.kuma a zahirin gaskiya wannan suna ya dace da ita dan me kyance, matsakaiciyace a tsawo,me k'irar kalangu,gata da yalwataccen gashi me tsawo da santsi,shi yasa ba kasafai take kitso ba, manyan idanunta masu maik'o(Oil eyes)da d'an k'aramin bakin ta su suka k'ara mata kyau na musamman,wankan tarwad'a ce a yanayin kalar fatar jiki,itama dalibace anan Kaduna State College Of Education(KSCOE) Gidan Waya.Aranar farko a kuma kallan farko data ma Julaibib so da k'aunarshi suka mamaye zuciyar ta ba tare data shirya hakan ba, duk tarin samarin dake mata nacin suyi soyayya sai taji ba wanda yamata nan duniya daya wuce Julaibib,ta so k'warai a ranar suyi magana amma hak'anta bata tadda ruwaba, saboda kwarjinin daya mata lokacin data tunkareshi,ashe gaba da gabanta aljani daya taka wuta.To amma me san d'an tsuntsu shi yake binshi da jifa"naci da shishshiginta yasa suka fara gaisawa duk da idan ba ita ta gaishe shiba ko zasu had'u sau dubu a rana bazai nuna yama ta6a ganin taba.

Duk inda tasan zata ganshi to in dai ba tana da lecture ba to tana wajan,yau da gobe sai ya fahimci tana neman wuce makad'i da rawa sai yadad'a kamewa,amma da Musaddiq sun saba dan suna d'an ta6a hira dan shima yana da miskilanci idan baiga dama ba,amma gangaran d'in miskilai sai "Julaibib Abdullahi D'ansarai ".

Musaddiq yana zaune a capteria yana cin abinci tazo tasa meshi tana fad'a mishi "Wallahi Musaddiq na ka sa danne zuciyata,na ka sa yin yak'i da ita,gaskiyar magana ina san Julaibib zan aureshi".

Cikin tsoro da mamaki yace kina san Julaibib?Yagirgiza kai"to gaskiya ki cigaba dayin yak'in wajan ganin kin cireshi a zuciyarki,baza ki samu abinda kike so...ta tareshi da sauri"me yasa za kace haka? Saboda baki dace dashi ba"wai d'an dambe ya d'auki adda"ni nasan Julaibib farin sani wallahi,kinga kuma addininmu ba d'aya bane. Idanunta suka ciko da k'walla,"wai yau ita ake fad'ama namiji ba zai so taba a yadda take d'in nan me kyau...

Tayi jimmm..na wucewar wasu dak'ik'u "Musaddiq kafad'a mishi "ni Kasham tanuna kanta ina sanshi,ina neman goyon bayan shi ya yadda muyi aure,na mishi alk'awari zanyi abinda yakeyi (Sallah)zanbi addininshi (Musulunci) Abincin da bai gama ciba kenan yamik'e dan zata dame shine kawai.Tabishi da kallo dan ALLAH kafad'a mishi.Ya amsa da To.


Rannan tana zaune a d'akin karatu, nazari da bincike(Library) ta ka sa yin abinda yakaita tunanin Julaibib ne kawai yacika kanta,kamar ance ta d'ago kai sai kawai gashi yashigo dak'in,yaja kujera yazauna.

Ganinshi yak'arasa kashe mata jiki, tanajin wani sabon yanayi daya tsirga ilahirin jiki da zuciyarta,gefe guda kuma tana jin takaicin k'in kar6an tayin soyayyar data keta mishi naci duk da kasancewarta k'wararriya data isa da kanta in dai a fagen hilatar d'a namiji yafad'o tarkon tane,ba wanda ta ta6a d'anama tarko bai fad'aba sai Julaibib,ta rasa me zatayi dan shawo kanshi,dan abinda takeji game dashi ba irin abinda takeji game da sauran maza bane,wani irin abune me sark'ak'iya,me zagaye ilahirin gangar jiki da zuciya,ita kanta bata san ya zata fassara shiba wallahi.Tasake kallanshi rubutu yakeyi cikin natsuwa,takad'a kai.

"Julaibib...you're an enigma".

Ahankali ta furta hakan,sannan tabi d'akin da kallo mutane dayawa sun gama abinda yakaisu sun fita,saita samu k'warin gwiwa koda zai wulak'anta ta bazai mata ciwo dayawa ba tunda mutane kad'anne. Tamatsa gaban kujerar dayake zaune,tasunkuyo tana kallan fuskarshi"Sannu da aiki Julaibib...tafurta hakan da wani salo irin na ta na yanga.Bai d'ago ya kalletaba kamar yadda take fa ta,bai kuma amsaba "shiruma amsace"rubutun shi kawai yakeyi.

Tatsareshi da manyan idanunta masu maik'o,ya mata kyau cikin fararan kayan,yau kanshi ba hula,kwantaccen bak'in gashin kanshi yanata sheki da k'amshin irin mayukan gyaran gashi da yake amfani dasu,jikinta ya gama mutuwa murus,ga k'amshin arabian perfumes d'inshi yadad'a jefata a wani irin yanayi,ta lumshe idanunta wani murmushi ya su6uce mata "ALLAH dai yakai damo ga harawa ko baiciba yayi burgima"taja dogon numfashi tana zuk'e k'amshin,ahankali kuma tafara fesar da iskar tabaki ta hanci sannan tabud'e idanunta tacigaba da mishi kallan k'auna me cike da shauk'i har yagama rubutun,yatattara takaddun daya shigo dasu a gefe, yakwashi wad'anda yad'ibo a d'akin yamayar dasu mazauninsu.

Magana take mishi amma yayi kamar ALLAH baiyi ruwan tsiran taba,ganin haka yasa tayi saurin k'arasawa bakin k'ofar da zai fita ta tare hanya sai yaja yatsaya.

Please...Julaibib...
Magana nake so muyi please...tahad'a tafukan hannayenta alamar magiya."please Julaibib, wallahi with all my heart ina sanka,kana burgeni, me zai hana ka aureni?

Yagirgiza kai"Bazan iyaba.Idanun ta suka ciko da k'walla"wai kai wannan amsar ta "Bazan iyaba"bazata bar bakinka bane D'ansarai? Wai me zan yine da zaka so ni Julaibib?Yakalli agogon dake d'aure a hannunshi nadama tana 6ata mishi lokaci fa.

Ki matsa zan wuce.Tasake kallanshi "Julaibib zanyi sallah fa...yad'ago yana mata rikitaccen kallanshi "Ki bani hanya nace ko? Yafurta hakan da 6acin rai a fuskarshi.

Yamata wani irin kwarjini data kasa aiwatar da k'udurin zuciyarta.Sai tagyad'a kai ta kuma matsawa a kofar"shi kenan zo ka wuce.Ya ra6a ta gefenta kamar wanda akace idan ya ta6ata ya gama amfani a doron duniya.

Tabi bayanshi da kallo har ya6ace ma ganinta...sai tayi d'an yak'e mak'alallun k'wallan cikin idanunta suka samu damar d'igowa a kyakkyawar fuskarta, sai kuma wani sanyi-sanyi data faraji, tsigar jikinta yana tashi alamar zazza7i yana so yakawo mata ziyara.

Harshenka zakinka idan kasa keshi yacin yeka"...

11 Rabi'a Thani 1441
8 December 2019

We Ibrahim's Daughters👇


Asdilat KD...2 geda with Ra'ibs.






DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}




Bismillahi wabihi nasta'in.



...GWAJIN DAFI💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)




Shafi na biyu.


Musaddiq yashigo da sallama, yad'auki ya zauna yasha,sannanya kalli Julaibib "sak'o aka bani wajanka...sai kuma yaja yayi shiru. Yad'an d'ago ya kalleshi"Uhun ina jinka sak'on me? Yaciro d'an k'aramin kati launin ruwan k'asa yanata kyal-kyali yamik'a mishi "karanta kagani.Kasham ce take gayyatar su party dan murnar zagayowar ranar da aka haifeta(Birthday) ranar talata a Bigard Hotel.

Yad'ago yana mishi wani rikitaccen kallo "nasha fad'a maka yarinyar nan ta daina aiko ka wajena kana zuwa kana fad'amin ko?Ya jijjiga kai"to ba laifi ka cigaba amma abinda zan maka zaka sha mamakinshi wa...bai bari ya k'arasa ba shima yatareshi"ba laifinka bane nawane ainan d'in tace za tazo tasame ka da kanta, ni kuma sanin da nayi baka san hakan yasa nace mata ka tafi Matsirga amma takawo in ajiye maka da...shima Julaibib ya tare da sauri..."na tafi Matsirga,na tafi Matsirga fa kace?To saboda me zaka min k'arya?Ganin ranshi ya 6aci yace"kayi hak'uri D'ansarai.Baice komai ba yakoma yakwanta,duk sukayi shiru,zuwa can Musaddiq yasake kallanshi."Kasham da gaske tana sanka Julaibib, ko zamu d'an lek'a matane ko na rabin awa dan itama taji dad'i yaba kyauta tukwuici.Yagalla mishi harara"idan zakaje to ni ina ruwana?Musaddiq yayi murmushi"D'ansarai autan Inna me duniya.Inje kuma?To ni asuwa?Kare da gudun laiya?Da dai zakaje dana maka kara na rakaka.

Yamik'e ni ga ka tafiya ta wajan Safiyya,yamik'a mishi hannu sukayi musafaha"Ka gaisheta.Musaddiq yad'an zaro idanu dan mamaki "Wuuu yau wace rana Julaibib yaji zanje wajan masoyiyata yace agaisheta? Julaibib yamik'e zaune da sauri,yana k'ok'arin kai mishi naushi yagoce yana dariya, ah ka ga mugu da 6allallan kafad'a kake so inji hirar"uu tambayata kakeyi?To tsaya yanzu zaka gani ya yunk'ura zai mik'e Musaddiq yafito daga d'akin da gudu yana fad'in "mu had'u a gidan Hajiya bayan sallar la'asar".


Agajiye yashigo gidan,dawowar shi kenan daga Kaduna.Yaya Karima ta tareshi "oyoyo barka da dawowa.Yauwa Yaya Karima.Yacire takalman shi masu rufi,sannan ya zauna a tabarmar tsakar gidan suna gaisawa.Inna tafito daga D'akin-girki"lale D'ansarai autan Innar shi"sukayi dariya to gashi,ruwa tabashi a k'aramin kwanan sha.

Yakar6a"nagode Inna.Da bismillah yafara shan ruwan,ruwan randan Inna me dad'in gaske ga wani irin sanyi,kowa kuma ya san ruwan randa sanyin shi baya cutarwa,ga k'amshin saiwoyin da take sawa a ciki da suke k'arama ruwan armashi wajan sha.Kad'an yarage sannan ya ajiye kwanan cikin hamdala ga ALLAH.Yakalle ta"Inna ruwan randarki gard'i da d'and'anonshi har yafi ruwan roba Swan.Sukayi dariya.

Abdullahi babban d'an Yaya Karima yayi sallama ya shigo yana rik'e da hannun k'anwarshi Kamila da take kuka."Mama ga tanan tak'iyin shiru tunda ta dawo daga makaranta,wai me yasa baki bari an taso suba kikayi tahowarki.?Ya k'arasa wajan Kawunshi cikin murna "Kawu sannu da zuwa,sannan ya gaisheshi.Yarik'o hannunshi "Yauwa Abdul yakaratu?Ya d'ibo Inibi to ga tsarabar ka.Abdul yasa hannu biyu yakar6a"nagode Kawu ALLAH amfana.

Karima takalleshi kwana biyu ka daina zumunci sai Musaddiq kad'ai yake sadar da ita."Baban Abdul dai yagaji shine yace in biyo sawu ko mun maka laifine"?Yayi murmushi yana shafa kai"Yaya Karima ba kumun laifi ba,bana samun lokacine amma Insha-ALLAH wannan Juma'ar zan shigo kin san tsarin karatunmu ba d'aya bane.Ta gyad'a kai"hakane Ubangiji yanuna mana Juma'ar.Ya amsa da amin.

Wata magana zamuyi.Sai ya tattara hankalin shi ga sauraran abinda zata fad'a."Julaibib me zai hana kafito da yarinyar da kake so a had'a bikinka dana Musaddiq?Ina sha'awa k'warai ace yadda kuke kome tare to lokacin aure ma ku angwance tare.Yagirgiza kai"ni bani da budurwa ma, ki tayani addu'a ALLAH yakawo tagari.To amin. Amma duk yan matan Gidan-Waya ba wacce ka k'yasa?Yad'anyi tsaki'ni fa ba tsayawa kallansu nake yiba,abinda yarabani daku,yakaini can d'in shi nakeyi (karatu)

Musaddiq yashigo yatarar da zancen, yace tab shi autan Inna sai a hankali kuma gashi da farin jini a wajan yan matan amma kowacce sai yace bata da kamun kai,bayan shi kanshi ya sani a shari'ance ba haramun bane dan mace ta yaba da kai tafurta maka kalmar k'auna.Musaddiq yaja dogon tsaki yana hararar Julaibib saboda tuno abinda yata 6ama yar course d'insu.....

Atikah Aliyu Kagoro.

Jikar Sarkin Kagoro ce tana da hankali da natsuwa kuma k'wak'walwannar dai Ubangiji ya hore mata shi na fahimtar karatu,Malamai ma ji da ita sukeyi bari d'alibai yan karankad'a miya.Tunda taga Julaibib tace nan duniya ba wanda yamata da aure kamarshi.sai dai kashhh...yawatsa mata k'asa a idanu.Atikah Aliyu Kagoro tayi kukan rashin shi.

Rannan tazo wajan Julaibib d'in amma bata same shiba sai Musaddiq shine take fad'a mishi zata bar makarantar saboda ba zata iya cigaba da ganin Julaibib ba bayan yace baya ra'ayinta,ita tanaso yasota da zuciyarshi ne ba yaso ta dan an tursasa shi an mishi dole ba,amma badan haka ba tana kai maganar nan wajan Me Martaba to anyi angama maye ya auri ramammiya, Julaibib zai zama mijinta dan bai isa Sarki yabashi auren jikarshi yace baya so ba"ai wata fuskar ta fi gaban mari har abadan duniya"tad'ibo wasu damin sababbin kud'i tabashi,ya girgiza kai ki barshi kawai.Sai tad'an harereshi "kai karfa ka 6atamin rai dan ka san kai ba Julaibib bane,dogarai zansa su baka na jaki".Sukayi dariya.Yagyad'a kai"wannan gaskiya ne ranki yadad'e.

Ta sake mik'a mishi"To d'an ALLAH ka kar6a.Yasa hannu biyu ya kar6a yamata godiya, sannan ya d'an kalleta"yanzu Atikah kin bar karatunki kenan?Tagirgiza kai"zan koma wajan Mahaifina a Saudi-arabia,dama tun daga yaye zamana ya d'ore anan,bayan na gama Secondary d'ina yaso k'warai in koma can in cigaba da karatu amma nace nafi san nan,ba dan ya so ba yahak'ura,saboda ni tagaban goshin Me Martaba ce,abinda nake so to dole kowa ma yahak'ura yasoshi indai yana neman zaman lafiya dashi.

Da jami'ar Abuja zan tafi amma nace ni nan nake so,ni kaina kuma ban san dalilin dayasa na za6i nan d'in ba,ashe k'addarar had'uwa ta da wannan miskilin d'an uwan na kane zai zama silar koma wata wajan mahaifina wanda dama ba abinda yake so sama da ya ganni kusa dashi,saboda mahaifiyata lokacin da data haifi k'anina ko ganinshi batayi ba ta rasu,da yammacin ranar shima abinda ta haifa yace ga garinku nan,mutuwarta ta dakeshi sosai saboda suna san juna suna zaman lafiya. Yadad'e baiyi wani aure ba,auran da yasa ke ma Me Martaba ne yagaji da ganinshi haka ya aura mishi matar. Saboda ni duk lokacin daya samu sarari yake zuwa Nigeria kasarmu ta gado.

Musaddiq ya kuma jan dogon tsaki fiye dana d'azu ALLAH yashiryeka.Julaibib yayi murmushi"amin shiriyar da ba ta ALLAH ba shirme da shiririta ce kuwa ,amin nagode".

Shi da Inna suna zaune a tsakar gida,yana 6arar gyad'a Inna kuma tana gyaran tsakin masara, jefi -jefi suke magana, saboda shirin da suke sauraro a gidan rediyo.

Assalamu alaikum.

"Inna tana nan...?

Daga zauren gidan suka jiyota.Cikin murmushi suka amsa sallamar.Inna tarage sautin rediyon "maraba da yar gidan Inna,to shigo mana kya tsaya a zaure kamar wata bak'uwa?Tashigo tana yar dariya"Inna na yi laifi na zaci kinyi fushi ne shi yasa naji tsoron shigowa kai tsaye"Dan ALLAH Inna kiyi hak'uri.Tazauna tana kallanshi"barka da warhaka Yaya Julaibib,Ina kwana.Yad'an shafa kai,tare da dauke kai daga kallan da take mishi.

Sudaida...Lafiya lau, ya karatu'?

Alhamdulillahi gashinan muna tayi ba kama hannun yaro.

Tajuya wajan Inna tana gaisheta. ALLAH Inna jiya dakika aiko mantawa nayi da aka tashi daga makarantar allo ban shigo ba.Inna ta girgiza kai"ba kome nima nayi tunanin haka.Tasa hannu ta d'ibo gyad'ar tana tayashi 6arewa,yau za musha fate kenan?Inna tace wai da dambu zanyi. Tad'an k'aryar da kanta gefen dama"kai Inna gwamma dai faten,kin san Hajiya(Kakarsu)tafi san shi,zaifi armashi ma idan Yaya Julaibib yaje yasiyo mana tantak'washi.Yad'ago kai yana kallanta"ni zanje insiyo miki tantak'washi?Tace to ai da Hajiya da Inna za musha.Baice komai ba yamik'e yashiga dak'inshi, bai dad'e ba yafito yanasa hula,yama Inna sallama yafita... Sudaida tad'an d'aga murya karfa ka manta kaji?Yak'arasa ficewa.Shiruma amsace.

Sai bayan sallar azahar suka shigo shida Musaddiq.Tace yauwa na ma huta dama yanzu nake shirin biyoku shago.Musaddiq yakalleta "ta samu kenan,idan kaji gangami da labari.Yabud'e kwanan data ajiye agabansu,tana murmushi"Yaya Musaddiq chips d'in gwaza namuku tunda baku cika san shan fateba"Yad'auki d'aya yakai baki,kai wannan yarinya da iyayi kike wai zuwa kashin rana da fitila.To Yaya Musaddiq chips lallai sai da dankalin turawa?Gobe ma da dankalin hausa zanyi. Julaibib yamik'e"kici lafiya...kai zo mutafi gidan Hajiya baza a rasa abincin arzik'i acan ba.Haushi yakamata"to wannan na tsiya ne?A ah sai dai shima chips d'in bazan ciba.

Inna tasa baki"kai baza a maka gwaninta ba kenan?Ya waiwaya ya kalli Sudaida da wani irin kallo data kasa fassarawa"ni nasa ki? Tagalla mishi harara dan ba k'aramin haushi yaba taba,shiruma amsace ta shige D'akin-girki dan k'arasa abinda takeyi.Taja tsaki"shi wannan D'ansarai autan Innan ALLAH yasawwak'e mishi".

Yana wankin kayanshi tashigo gidan, Asma'u ce ita yake bi.Takalleshi"manya ba a ganinku sai an cike foam,foam d'inma sai wanda ake buga mishi stamp.Yayi murmushi"Yaya Asma'u ban kai nan ba,wa ne kare da hantar kura?Barin dai k'arasa inzo mugaisa.Tawuce d'akin Inna suka gaisa,sai ta mik'e"barin lek'a d'akin autan na ki ko zan samu abun sawa a bakin salati.Tashige ciki tana mishi bincike. Yagama shanya kayan sannan yabita,baiji dad'in abinda ta mishi ba,gaba d'aya ta hargitsa mishi d'akin,har kayan sawanshi na cikin akwati sai da ta bincike.Yazauna yana kallanta cikin zancen zuci "Yaya Asma'u yar sa'ido ce ta gaban kwatance, da shiga sharo ba shanu,kamar wata yar C I D,kaza dai garin tone-tone wata rana zata tono wuk'ar yanka ta.

Takalleshi"kai d'akin na ka ba wani abu da mutum zai kai bakinshi zuwa uwar hanji sai tarin littafai kala-kala?Yana tattara littafan data hargitsa yace"to dama me zaki samu a d'akin talaka kuma d'an makaranta?Aike zaki taimakamin koda da yar dubu goma in k'ara na Hand-out da 'yan wasu abubuwan,kinga kinyi halin girma,ladanki yana wajan ALLAH.Lallai yaran nan ka ci abinci sauranka ruwan sanyin randan Inna.Yanzu duk cikinmu akwai wanda ke cin kud'in Baba kai harma da Innan kamar ka? "Ni?yanuna kanshi da d'an yatsanshi"sharri dai ba kyau Yaya Asma'u.Tad'an harareshi tana dariya" za ka fad'i haka mana.Yagyad'akai"ALLAH Yaya Asma'u tunda ke hajiya ce kamata yayi ace kin d'auko ma Inna yar aiki,kina biyanta duk k'arshen wata,ni jarin nawa baiyi k'wari bane dani zanyi hakan.

Tamishi wani kallo"ALLAH sarki, Inna ce za a d'auko ma yar aiki?To ina abun yake wai maye ya cinye jariri?Tabbb...kai akwai ka da san kashe kud'i na ba gaira ba dalili,amma fa harda dan baka san yadda ake wahala wajan nemo su bane.Na sani mana tunda nima ina sana'a.Ta tareshi da sauri "A ah ban yadda ba sana'ar taka har wata sana'ace da zaka fad'i wahalhalun cikinta?Kuna komawa Gidan-Waya Baba zai cigaba da kula muku da kome, kaga ai yafiku shan wahala daga kai har Musaddiq d'in,ko zirga-zirgan da yake yi tsakanin nan da Kaduna ai bakwayi.Hun Julaibib arzik'i gashin hancine rabuwa dashi ba dad'i,kabari sai ka gama karatun,ka fara sana'a ka'in da na'in sai muyi zancen. Yace to Ubangiji yanuna mana lokacin.

Dama so yake yaji me za tace, amma ai ya riga yasan halinta na rowa,indai maganar kud'ine kuma itace zata bayar tofa sai anyi tata6urza,sa6anin idan itace zata kar6a yanzu mutum zai sha dogon lissafi da sharhi.Tamike" kai ni barinje wajan Inna baza a rasa abun kaiwa bakin salati ba.Yagirgizai kai"yanzu haka da abinda yakawota gidan,kuma abun tirrrr d'in tana da rufin asirinta dai-dai

Please Login or Register in order to submit comment