Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baccin da ake so mutum yayi duk dare,gobe kowa sai ya tashi a watstsake katafi Katsina,ni kuma in shiga makaranta ba shikenan ba?

Takauda kai daga kallan dayake mata, tafara jero azkar d'in kwanciya.Ai ko ba shikenan ba,ki sallameni.Tagyad'a kai"toh jeka na sallame ka, ALLAH ya lullu6eka da rahamarshi da albarkarshi, asubah tagari.Yayi murmushi sannan yasa hannu yana mata wani salo...salon data kasa daurewa tamik'e zauna tana dariya"Yaya D'ansar...sauran kalaman suka mak'ale sakamakon wani sak'o d'aya bata me girman ban mamaki me sa a fita a hayyaci.

Da safe yagama shirin shi tsab natafiya cikin shigar farar shadda yana zaune a D'akin-shak'atawa, yayi shiru cikin nazarin kalaman Sudaida dan ko da asubahi sai da tadad'a tabbatar mishi tana nan akan bakanta,ta kuma bashi sarari tana zaman jiran shi.Yadda yake juya zuman da yasa a shayi haka yake juya kalaman;tafito daga d'akin baccin su cikin shigar mutunci da mutunta kai kamar ko yaushe za ta shiga makaranta.Tazauna a hannun kujerar "Yaya D'ansarai wai har yanzu shayin ne baka shaba?Tun kafin in shiga wanka fa nakawo maka.Yasunkwui da kai.Sai kawai tamik'e tad'an kalleshi nawucewar wasu dak'ik'u

"Yaya D'ansarai ALLAH yakiyaye hanya...

Tad'an sunkuya tabashi sumba sannan tayi furucin da wani salon shagwa6a"sai munyi waya ko?...tajuya tayi tafiyarta dan tasan ba magana zaiyi ba in dai yayi wannan sunkuyar da kan"sanin hali ai yafi sanin kama.

Yabita da kallo yana lallausan murmushi yayi d'as da yan yatsunshi"hak'ata zata tadda ruwa Insha-ALLAH ai ni dake mutu karaba yarinya.Yakalli agogon dake d'aure a hannunshi na dama,lokaci yaja a gurguje yagama karyawa,yad'auki jakar shi ta matafiya ya rataya a kafad'a da mukullin mota yakulle gidan yana addu'ar fita daga gida"bismillah tawakkaltu alallahi walahaula walaquuwata illah billah.Yashiga mota ya zauna yana d'aura belt yana kuma amsa wayar wani abokinshi na koyarwa da za suyi tafiyar tare.Tun daga ranar Julaibib yacanja taku tunda abin iya ruwa ne...

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar litini (Monday)ranar aiki ko nasara na tsoron ki tana kwance cikin bargo tana baccinta na tofan gira dan yau sai yammaci zata shiga makaranta kiran wayar Inna yashigo tad'aga da fara'a"Innarmu Sudaida takirata tana yar dariya"na'am yar gidan Inna,suka gaisa Inna tace"na ji autana shiru ni da Alhaji har mun gaji min kira layinshi sau shurin masak'i,da tana shiga baya d'agawa amma daga baya kuma ta daina shiga kwata-kwata.

Dasauri cikin d'an bud'e idanu dan mamaki tace"shi Yaya D'ansarai d'in Inna?Eh shi d'in,ko baya jin dad'i ne kuke 6oyewa?Fargaba takamata dan kwana biyun nan itama fa bata gane mishi wallahi"a ah Inna lafiyar shi k'alau,yanzu ma yana cikin makaranta bari ya shigo inji abinda yafaru.Toh ALLAH yadawo dashi lafiya,ALLAH ya jishshemu alheri sukayi sallama Sudaida tana amsa addu'ar Inna da amin,amin Inna.

Tafito D'akin-shak'atawa kawai taganshi kwance a doguwar kujera.Yaya Julaibib takira sunan shi. A hankali yabud'e idanun shi yana kallanta"har ka dawo ne amma baka nemi ni ba? Ni banji shigowar kaba.Yauwa sai tajuya ta d'auko wayarta"munyi waya da Inna d'azu barin kirata,yafizge wayar ta bishi da kallo yakasheta gaba d'aya sannan yatura a aljihun gefen rigarshi ta dama"rabu da ita Sudaida.Tazauna a k'asa gefen k'afafunshi tana bud'e idanu da mad'aukakin mamakin furucinshi"Innarce za a rabu da ita? Bai bata amsa ba yamaida idanun shi yarufe.

Tasake bin shi da kallo cikin tsoro da shakka"to ko dai Yayi Julaibib ya fara k'arama sama hazo ne?data isheshi da tambaya sai kawai yamik'e yashige d'akin baccin su har yanasa mukulli,bai fito ba sai da za shi masallaci sallar azahar.Tamik'e ta tare k'ofar.Yad'an yamutsa fuska "ke bani hanya yanzu za tada sallah.Tagyad'a kai"ba in da za ka har sai ka fad'amin abinda yake damunka da har za kace a rabu da Inna..

"Adai-daita sahu a had'a kafad'a...


Suka fara jiyowa daga masallaci yad'an kalleta cikin natsuwa"barin dawo daga sallah sai muyi maganar ko?

Daga masallaci makaranta yawuce bai koma gidan ba,tagaji da jiranshi,itama tatashi tabishi,yana jin an kwankwasa k'ofar ya amsa daga ciki"na'am bismillah shigo,bai zaci itace ba.Takulle k'ofar tazare mukullin"Yaya D'ansarai ni fa ka sani a rud'ani wallahi, wai me yake damunka ne Inna za tayi magana dakai kace wai a rabu da ita sannan ka k'wace waya ta ka kashe,ta kama ka kashe me yafarune?Ni ma kwana biyun nan kwata-kwata bana gane maka.Yamaida kanshi jikin kujerar"to Inna me za tamin?Inna bata da maganin damuwata fa.

Da rawar murya tafara nuna shi da yatsa"Kai Yaya D'ansarai Innarce..ba..ta da maganin... damuwarka?To duk fad'in duniyar nan ma kana da kamar tane?Takalleshi cikin takaici"to wa yake da maganin damuwarka?!

Yajanye kanshi daga jikin kujerar yad'ora duka hannayenshi a saman tebur d'in sannan yakalleta cikin natsuwa"Zaujatiii...ke ce maganin damuwata,ina k'aunar ki, ina jin takaicin ace wai ni Julaibib yanuna kanshi da yatsanshi wai ni zan rabu dake dan kawai ba kya haihuwa, ni ina son ki a kowani irin hali da yanayi na rayuwa,Sudaida ko baki haifa min Ya'ya ba ba na nadamar aurenki.

Ni yanzu abinda yake damuna yahanani rawar gaban hantsi shine na kasa samo mana mafita ta yadda zamu rabu salin-alin ba tare da Inna ko Kawu ran wani daga cikin su ya sosuba, kema kuma na san kin k'osa amma kina min biyayyane kawai saboda na rok'i alfarma kar kice kome...Dammm... Zuciyarya tabuga...tanajin wani irin yanayi mara dad'i yana bin ilahirin gangar jiki da zuciyarta,gaskiya idan tarabu da Yaya Julaibib...kai anya? Sai tabar wannan ayyane-ayyanen na zuci.

Yawani marairaice"ALLAH yamiki albarka Zaujatiii...yarik'ota da wani salo"ko ke zan d'aurama wannan aikin na lalubo mana mafita danni dai har yanzu na ka sa, amma ko bama tare Zaujatiii...ki rik'e wannan a zuciyarki "ke ce mace ta farko dana fara k'auna,k'auna irin wannan ta aure zan kuma cigaba da k'aunarki ko da bama taren.Jikinta yadad'a yin sanyi da jin kalmar nan ta rabuwa...ganin hakan da tayi sai yacigaba da zugata ta hanyar kambama halayenta na kwarai,da kuma mamakin da yakeyi wai ita da kanta take ikirarin saki bayan ta san hadisin Manzon ALLAH da yace duk macen data nemi mijinta yasake ta batare da wata hujja ta shari'aba toh k'amshin aljannah ma bazata shak'aba,kuma shi k'amshin aljannah ana fara shak'arshine tun daga tafiyar shekara d'ari biyar,haba Zaujatiii...da ilminki da wayonki da kome na ki,tayaya wasu dangin miji can za su rabamu,bayan basu suka had'amu ba,ni fa nake auren nan ba wani ne yakemin ba,ai nine zan miki gorin haihuwa kece kin d'anji haushi ko?Karki kuma d'aga hankalinki a kan duk maganar masu magana,sau nawa muna zuwa ganin likita akan rashin haihuwa ana kuma bamu tabbacin dukkanmu lafiyar mu k'alau lokacine kawai baiyi ba,ba da bakinki kikace ke kin daina shan wata k'waya dan neman haihuwa kin barma ALLAH ba?Me Yaya Asma'u za tayi ta6ata miki rai?Yau kika san halinta?Ai tun kafin mu zama ma'aurata kin sani dan ko gidanku taje sai tanuna wannan halin na ta,kin gani ganin idanunki ke ganauce kuma jiyau..

Rashin haihuwa ba k'ask'anci bane wallahi,Idan kika duba gidan Manzon ALLAH a duk matanshi ba wacce ya keso sama da Nana A'isha kuma har ta koma ga ALLAH bata haihu ba,bayan ita a kwai wash matayen na shi da basu haihu ba,to me garage darajarsu?Annabawan ALLAH nawane da basu haihuba?

Ganin damar ALLAH me idan yaga dama yabaka Ya'ya maza zallah,ko yabaka mata zallah,ko yahad'a maka maza da mata,haka kuma ganin damarshice yabarka bakarare(Mara haihuwa) kinga da...

Bai k'arasa furucin shiba ta k'ank'ameshi tana kuka,yayi lallausan murmushi dan hak'anshi ta tadda ruwa,yacigaba da rarrashinta"Zaujatiii...ni D'ansarai ni ne me auren nan kuma na ce mutu ka raba,ko kin haifa min Ya'ya ko baki haifa min Ya'ya ba,kuma na miki alk'awari zan yima tufkar hanci,ba me kuma samun ke a damuwa a dangina,su suje su rungumi mazajensu cikin annashuwa ni kuma su dagulama Zaujatiii...nah lissafi?Toh karki damu kinji ko?Tad'ago takalleshi"Ya'ya D'ansarai nagode maka da wannan tunatarwar ta ka"idan rai ya 6aci to bai kamata hankali ya gushe ba...kai mijin alheri ne;tasauke gwauran numfashi

"Rayuwata idan babu kai a cikinta za a samu tasgaro me tarin yawa,tadad'a k'ank'ameshi tana shak'ar k'amshin deodorant da arabi'an perfume d'inshi,yad'ago fuskarta suka kalli juna yad'an dage kira yana mata wani kallan k'auna yana murmushi "mun zama k'arfe da mayen k'arfe ko? Tajijjaga kai"eh wallahi autan Inna,D'ansaran Baba,Zaujiii... Ustazun Sudaida yar Ibrahim,jikar Ibrahim Me-Lambu.Suka sumbanci juna yace kuma"mayyar rake abin ma yasamu shiga wai d'an wake a hotel har da injin d'in matse ruwan ko da ta zama tsohuwa ba hak'ora ko?


Tad'an daki k'irjinshi,shi kuma yabata marin soyayya suna dariya.Tad'auki wayarta a saman tebur d'in ta kunna"toh kira Inna gaskiya dan ta damu da rashin jinka tunda har takirani.Yagirgiza kai "gwamma mutafi Zonkwa ayi kome idanu na ganin idanu"zan fad'a mata kece kika hanani.Tad'auki jakarshi taraya a kafad'a suka fito daga office d'in, suka jera suna tafiya zuwa inda ake ajiye motoci da mashinan malamai tana fad'a mishi"Inna baza ta ta6a yadda ni na hanaka kiran taba,tunda ni kullum sai mun gaisa ko ta kirani ko in kirata.

Watannin Sudaida bakwai kenan da tafiyarta Gidan-Waya,duk wannan watannin zuwanta Zonkwa sau hud'u,yanzuma tanata mishi magiya yabarta taje tunda sun samu hutu amma ya hana,wai tayi zamanta a in da mijinta yake ai shine zai fi mata kwanciyar hankali,tagyad'a kai"ni ma na sani ai bawani dad'e wa zanyi ba mak'o d'aya dan ALLAH, amma ya hana,haka dole ta hak'ura,dangin Julaibib kuma sun barta tana rawar gaban hantsi bata san me yafaru ba,amma tabbasss...ta dad'a yadda da kalaman shi kamar yadda yace ba me sa mishi mata a cikin damuwa.

Da safe tana kwance tak'i tashi tahad'a mishi shayin shi ko ruwan wanka,shi yamusu kome,yagama shiryawa sannan ya zauna a gefen gado"Sudaida yakira sunanta.Tad'ago tana kallanshi yana sanye da babbar riga yar ciki da wando na farin yadi yana karya hular zita"har yanzu baza ki tashi daga kwanciyar k'asan nan ba?Tasauke idanunta k'asa"ni dai nafi jin dad'in nan.Yagyad'a kai"sauri nake yi damunje asibiti.Tamik'e zaune dakyar"ba sai munje asibiti ba,naji sauk'i Yaya D'ansaarai.Yagirgiza kai"za dai kiji sauk'i,tun yaushe nakai miki ruwan wanka amma har yanzu baki tashi kinje kin yiba?Yamik'a mata hannayen shi"ta so muje in cud'a ki.Tayi yar dariya"bayan ka shirya?Ai zaka 6ata adon ka,yi tafiyarka yanzu zan yi.Yad'an motsa kafad'a"uh to menene a ciki,ba sai in canja wasu kayan ba? Tamik'e tana mishi rakiya,kad'an ta taka mishi ta dawo tayi kwanciyar ta dan dama bata so tayi wankan,idan tafad'a mishi to sai ya tilasta ta yin wankan ko ta so ko tak'i.

Har yadawo tana kwance yayi tsaiii...yana kallanta yana bin d'akin da kallo,ba abinda tayi yakad'a kai cikin damuwa"wannan ba halin Zaujatiii...bane tabbasss bata da lafiya.Dakyar yatashe ta sai wani narkewa takeyi, amma tanayin wanka sai tajita garau...yana kallon tashar larabawa suna nuna yanayin al'adunsu yana cin gasashshiyar kaza me kayan lambu tashigo yabita da kallo tana sanye da material bak'i me yarfin filawoyi ruwan k'asa, d'an kunne,sarka da warawarenta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi saboda kyallinsu,fuskarta shar da kwalliya, bakinta yana kyallin jambaki ja.

Tazauna suna kallan juna "Zaujatiii...kinyi kyau dame kike son tukwuici?Tad'ora ha6arta a kafad'arshi tayi furucin da wani salon shagwa6a "agada(plantain) yajuyo yakalleta"kin cinye wannan agadan dana siyo miki ne?Ta amsa kai tsaye"wallahi tun jiya.Yabud'e baki dan mamaki saboda ada shi yake matsa mata tasoya musu dan ba wani dad'ata da k'asa yayi ba,amma a yan kwanakin nan cin agada takeyi kamar ta samu abincin gado,d'an kullum, ranshi yadad'e me martaba tuwo miyar kuka abincin hausawa.Kai shifa bai yadda ba sai da yaje yaduba in da suke ajiyewa yaga ba kome sannan yadawo yana cemata lallai kinyi k'ok'ari,yad'auki waya yana kiran wani mak'ocin shi da yau yatafi Jos kuma anjima zai dawo dan ALLAH yasiyo mishi agada.

Yasake kallanta bayan yagama wayar amma fa na d'auka bakya jin dad'i danaga tun safe kina ta bacci har shabiyun rana.Ai na fad'a maka lafiyata k'alau kawai ni dai nafiso in kwanta in yi baccine.Ya mata nuni da kazar.Tagirgaza kai dan ko sha'awar ci batayi,tad'auko lemun peach tana sha suna hira jefi-jefi suna kallansu har suka gama shirin,sannan yamik'e zai koma makaranta "adawo lafiya.Takashe kallan tad'auki wayarta ta kunna data zuwa duniyar yanar gizo...

Da daddare kafin yadawo daga sallar Isha'i Sudaida tayi baccinta a inda ta idar da nata sallar. Yatasheta"Zaujatiii...ga agadan an kawo.Dakyar tad'an bud'e idanunta da yanayin bacci takalleshi sai ta mayar ta rufe,tayi wani juyi tana dad'a shemewa a dadduma"barshi sai da safe ni bacci nake ji,tacigaba da baccinta sai kuma tamik'e zuwa d'akin bacci.

Yabita da kallo har tashige.Shi kad'ai yayi zaman D'akin-shak'atawa yaci abinci kad'an, yaje yahad'a shayin shi da baya gajiya dasha.Yagama yan rubuce-rubucen shi har zuwa sanda bacci yafara kawoma idanun shi ziyara,yashiga d'akin ta kashe wuta,yakunna fitilar wayar shi yana hasketa" tana kwance a k'asa kuma yau tsabar jin bacci ko kayan bacci bata tsaya sawaba,yad'anyi murmushi yana cigaba da kallanta numfashi na shiga da fita cikin kwanciyar hankali,sai tamishi wani irin kyau na musamman, ya dad'a gyara mata rufa dan yasan ko ya maida ita gadon to sai ta sauko wai ita k'asa yafi mata dad'i,yakashe fitilar yakwanta yana musu azkar d'in bacci.

Abinda yaketa maimaituwa kenan,kullum bata da kuzuri,bata san yin kome sai kwanciya,yau dai abin ya isheshi,dan haka yana dawowa daga Kaduna jakarshi kawai ajiye,yatasata agaba sai tashirya sun tafi asibiti dan daren jiya kusan kwana sukayi tana mishi wash...wash...mararta tana mata ciwo amma abin mamaki baturiya da suna manga gari na wayewa sai tamik'e wai ta warke,yanzu kuma yadawo ya ganta lamooo bata da wani kuzari sai bacci-dai bacci dai bata gajiya...Yabita d'akin tanata nuk'u-nuk'unta"Zaujatiii...hijab d'in ne baki gane ba kome?Tabud'e wardrobe tad'auko.

A k'ofar gida sukayi kaci6is da motar Musaddiq tsayuwar shi kenan suka fito shi da Hajiya. Sudaida tarungume ta tana murna"oyoyo Hajiyarmu sannu da zuwa,suka koma ciki.Julaibib yayi murmushi"yau farar ranace agaremu me kyakkyawar suna.Hajiya ta ajiye kofin lemun"to ance ka gaida me gaisheka,kunzo nan kun share waje kun manta da kowa kuna sha'anin gabanku.Julaibib yasa hannu yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi "munata fama dai da ayyuka da d'alibai Hajiya.

Ganin Hajiya yasa Sudaida ta nemi kasalar data rufeta tarasa,tashige D'akin-girki tana k'ok'arin shirya musu abincin data cema Julaibib ita yau baza tayi wani girki ba,yad'an motsa kafad'a" duk d'aya 6arin manshanu a miya, dan shima ba kullum yake cin abinci me nauyi da daddare ba.Musaddiq dai bai tsaya cin wani abinci ba Sudaida tafito suka gaisa yamusu sallama suka fita da Julaibib.Har suka gama cin abinci bai dawo ba, takwanta suna hirarsu me dad'i da Hajiya,bacci yafara d'aukanta sama-sama, sannan taji sallamarshi yashigo musu da gashashshiyar kaza,bata tsaya ciba tamusu sai da safe taje tayi kwanciyar ta tana jinsu sunata hirarsu, ita kuma baccinta rabi-da rabi tayishi saboda ciwon maran d'aya matsa mata daren jiya to yauma daren yayi shine yace bari ya motsa.

Yadawo daga masallaci sallar asubahi yaganta tsugune a bakin famfo tana ta yunk'urin amai amma yak'i zuwa,Hajiya tana mata sannu,tarik'ota suka koma D'akin-shak'atawa takwanta a doguwar kujera jikinta a mace yake murusss"sannu ALLAH yasauwak'e"Hajiya ta zauna tana mata fifita ganin yadda tajik'e sharkaf da zufa kamar wacce tafita motsa jiki da sanyin safiya.

Yazuba mata idanu zuciyarshi ba dad'i saboda yadda take dad'a rintse idanunta tana mirgina kai gefen hagu zuwa dama tana yarfe hannuwa,tana ta6a mararta da take mata wata irin d'aurewa tamauuu...ita kad'ai tasan azabar da take ji, wucewar wasu dak'ik'u cikin ta ya dad'a yamutsewa ciwon yana k'aruwa,mararta kamar zata 6alle,Hajiya itama ta shiga cikin damuwa"Sudaida wai meke damunkine?wai!Wash...wayyohALLAHnan...uhhh...washhh.. tasake yarfe hannun hagu na dama na saman mararta,da kyar tayi furucin"Wayyoh! Hajiya marata ce take ciwo. Julaibib yajuya dan tsayuwar ba amfani, motarshi kuma ba ishashshen mai"Hajiya barin samu mai yanzu mutafi asibiti.Tagyad'a kai"to hanzarta dan naga abun yana dad'a k'amari.

Wayyo ALLAH! tafad'a a galabaice tayi nishin wahala...uhhh...Hajiya marata!"sannu Sudaida yanzun nan Julaibibi zai zo mutafi asibiti.Ta cije le6enta na kasa ta yunk'ura zata mik'e zaune amma ta kasa;Hajiya ta taimaka mata,tad'ora kanta a kafad'ar Hajiya idanunta na rufewa da bud'ewa cikin azabar ciwo,cikinta na cigaba da hautsinewa ciwo na k'aruwa,da marar tayi wata irin murd'ewa sai ta k'ank'ame Hajiya tana Istirja'i da salati, tasake k'ank'ame Hajiya iya k'arfinta tayi wani nishi sai kawai taji wani ruwa me d'umi ya 6alle mata da kyar taduba sai taga jinine,cikin yan dak'ik'u zanin jikinta ya jik'e sharkaf,zata tashi jiri luuu...yayi awon gaba da ita ta zube a jikin Hajiya cikin d'aukewar numfashi.

Hajiya ta rikice tashiga jijjigata amma ko motsi ga jini na cigaba da zuba, saboda rikicewa sai tarasa me ma za ta matane?Tana cikin wannan halin Julaibib ya turo k'ofar yashigo.Cikin tsinkewar zuciya yake kallansu saboda ganin Sudaida da yayi kwance cikin jini male-male,k'wak'walwarshi bangaren tunani da adana bayanai yafara tariyo mishi shud'add'en abinda yafaru a shekarun baya lokacin da Bilkisu take kwance sam6al cikin jini fuj'atan.Dammm...yaji ruguzowar wani abu a k'ahon zuciyar shi"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...baiyi wata-wata ba yasa hannayenshi ya cicci6eta cikin tashin hankali yayi mota da ita,Hajiya tabiyo shi.

Sun 6ata lokaci suna dubata sannan wata ma'aikaciyar jinya takirasu"kaine mijinta? Yajijjaga kai kawai.Tad'an kalli Hajiya sannan tamaida kallanta gareshi"yarinyar nan gaskiya tana mugun jin jiki kuma matsalar ta fi k'arfin mu,tunda sai an mata aiki kuma likita baya nan,to sai ku gaggauta kaita wani asibitin,irin wannnan zubar jinin idan yazo da k'arar kwana sai a rasa mutum."ALLAH yabata lafiya yasa kaffarace.

Tajuya tayi tafiyarta.Hajiya ta kalli Sudaida bata san wanda yake kanta ba.Julaibibi mu san abinyi mana.Idanun shi sun kad'a jawur,yayi wani huci cikin tashin hankali sannan yaba motar wuta,a guje yafito daga harabar asibitin suka fad'a kwalta zuwa wani asibitin.

Dasauri suka d'auketa zuwa d'akin agaji da taimakon gaggawa suma sun 6ata lokaci sannan likita tafito suka bi bayan ta zuwa office suna tambayarta me yafaru?Yajikin na ta?Ku kwantar da hankalinku.Tadanyi rubuce-rubucenta a katin data shigo dashi tagama taturashi a aljihun Labcoat d'in ta, sannan tad'ago cikin natsuwa ta kalli Julaibib"ka gane ko,matsalar matarka sai an mata aikin gaggawa, idan ba haka ba za ta iya rasa ranta,saboda ciki tasamu amma ya zauna a bayan mahaifa.

Shi da Hajiya suka kalli juna sannan suka kalleta cikin murna da mad'aukakin mamaki.Yayi yar dariya"ciki likita?Tajijjiga kai"eh ciki.Suka shiga tasbihi ga buwayi gagara koya dan furucin likita ya zo musu a bazata."Julaibib yayi sujudush-shukri.Likitar ta cigaba to amma an samu matsala dan cikin har ya fashe, abinda yasa take wannan serious bleeding d'in kenan (rupture ectopic pregnancy)kuma wannan aikin dole sai Gynea Doctor(likitar dake mu'amala da abinda yashafi lalurorin mata)kana...Julaibib yatari numfashinta"to ke fa?

Ni nan da dak'ik'u talatin zan shiga wani aikinne(operation) amma karku damu dan nayi waya da Doctor Kagarko itama kwararriyace yanzu haka tana kan hanya.Tabud'e dirowa tad'auki wani fallen littafi tayi rubuta sannan ta fad'a mishi adadin kud'in da zai biya,tamik'a mishi wannnan fallen littafin kaje kabiya kud'in sannnan kaje a d'auki sample d'in jininka idan yazo d'aya danata basai an siyaba. Yamik'e yaje yabiya kud'in,kuma yasa hannu sannnan yawuce aka d'auki jinin shi ana dubawa akaga yazo d'aya sai aka wuce dashi laboratory dan tantance sahihancinshi kafin ak'ara mata.

Doctor Khadija Aminu Kagarko tak'araso, matar me hankali da natsuwa ga tarin ilmi da ya ratsata,ta gaishe da Hajiya cikin girmamawa"ki mana addu'a Ubangiji yasa a dace.Hajiya tagyad'a kai"ALLAH ya amsa yar nan.Hajiya da Julaibib sunata kai-kawo bakunansu d'auke da addu'o'i tunda aka shiga da ita d'akin theatre,har akayi aikin aka gama aka fito da ita agadon marasa lafiya ana turata a hankali dan zuwa d'akin hutu,idanunta a rufe bata san in da takeba,ta d'ashe saboda rashin ishashshen jini,yasauke gwauran numfashi"Alhamdulillahi an tsallake tsirad'i d'aya na yin aikin cikin nasara,saura na farfad'owarta,ALLAH yasa tafarfad'o cikin hayyaci da lafiya.

A sanda rana tatafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai Sudaida tad'an motsa da alama maganin da suka ba ta na anaesthetic ya fara sakinta...wucewar wasu dak'ik'u kuma tayi motsi da fatar idanunta sai kuma tad'an bud'e idanun tana bin Julaibib da Hajiya da suke rige-rigen yi mata sannu,a hankali bakinta yamotsa tana salati, sai kuma ta yunk'ura zata tashi,yarik'eta da sauri "Zaujatiii... kiyi hak'uri kinga aiki aka miki kar a samu matsala,takoma takwanta ta damk'i hannunshi tamau tafara kuka mara sauti saboda jikinta ba k'wari"ni dai ku yafemin mutuwa zanyi furucin a hankali yake fita muryar kamar bana taba, sai kuma tafara sambatu

"Dan ban haihuba sai a dinga min cin kashi? Ni zan ba kaina haihuwa? Shima autan Inna ai ina jin haushin shi dan bai kawo min agada ba,har madidi nace yasiyo min amma yak'i...Hajiya cikina ciwo yakeyi marata... wai...wayyoh Zaujiii...ni fa ba na san wannnan kallan na ka dan haushi yake bani...kai fa ran...da sauri yasa tafin hannun damarshi yatoshe mata baki dan kartayi kato6arar da zai sa shi jin kunyar Hajiya tunda ba a hayyacinta take ba kome ya d'arsu a zuciyarta fad'arshi za tayi.Ganin tak'i sakin hannun Julaibib dan yakira likita yasa Hajiya ta tafi kiranta"to fa tashin hankali gobarar gemu...

Magani a shaka badan yunwa ba.

Kome tsawon giginya daga k'wallo tafara.



2 Rajab 1441
25 February 2020


We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.





DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in.



...GWAJIN DAFIđź’”




Please Login or Register in order to submit comment