Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajan da saurinta"a ah to me tamiki kuma?Ni tama laifi dama jira nake Musaddiq yashigo in fad'a mishi.Sudaida kuka takeyi da gaskiyar ta ita dai aba Umma hak'uri dan idan ba itace da bakin ta,tace ta hak'ura ba to lallai sai tayi dukan nan ko kuma ta had'a ka da Adnan shima kwallan shege a wajan iya ba da na jaki.Mama takan cemishi "Sarki zalimu dan dai ba ya'yanka bane,baka san zafin suba shi yasa kake musu wannan dukan na rashin tausayi.Sai yayi dariya "ai ko su d'in ne haka zan musu indai sukace baza su bi abinda zan fad'a musu ba wallahi.Dak'yar takwace Sudaida a hannun Umma.Sudaida tace" nagode"to amma Mama kibata hak'uri.Tagyad'a kai"ai zata hak'ura ne.Umma tace"na rantse da girman ALLAH zan hak'ura ne kawai idan taje takaima D'ansarai ruwan sha,tamatsa da abincin gabanshi, takuma gaisheshi tabashi hak'urin dangwarar da abincin da akace takai mishi.Idan ba haka ba tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta ta shige d'aki.


Duk yadda taso dakewa idan zata shiga d'akin abin yaci tura.Cikin kuka tayi sallama.Yad'ago yana kallanta ta ajiye ruwan ta d'auko abincin,wani haushinshi yacika mata zuciya saboda shi aka so a bata na jaki,da Mama ba tanan a yadda ran Umma ya6aci ba k'aramar wahala zata shaba,shi ba a ganin abinda yakema mutane na halin-ko-inkula sai ita?Dak'yar tace"Ina wuni...wani sabon kuka ya kufce mata wai har hak'uri sai tabashi? Yaya...kayi hak'uri... tausayinta yaka mashi koma menene yasan Umma ce ta sata wannan ban hak'urin.Nayi hak'uri Sudaida ai dama baki min kome ba,to zuba min abincin kad'an, tadauki faranti tazuba ta mik'a mishi.Yayi bismillah yafara ci.

Kafanchan ne garin dasu A'isha suka tafi. Babban gidane a Magiya Street me sassa guda bakwai sai dai a kulle suke da kwad'o saboda mutanan ciki ma'aikatane a garuruwa mabambanta,idan ana sha'ani ko sun samu hutun aikine za kaga gidan ya cika da jama'a. Sashin Kaka dana kusa da itane kawai koda yaushe a bud'e jama'a na kai kawo.

Gidan yayi shiru saboda sauran yaran gidan sun tafi makaranta sai kukan tsuntsaye da suke ta shawaginsu."Hantsi ya dubi ludayi rana ta haska ko'ina. Hashim bacci yake so yayi amma wani nishad'd'd'an al'amari ya hanashi sak'at bare yabarshi yarintsa.

"Aishahhh...

Yafurta sunan a zuci sannan yabud'e idanunshi cikin agogon dake manne a bangon d'akin "goma da rabi na safiya.

Sai yamik'e, sashin Kaka yanufa Alhamdulillahi"yafad'a daya fara jiyo dariyar ta, hira sukeyi da Kaka.Yayi sallama sannan yad'aga labulan dak'in,caraf idanunsu yahad'u tace"Hum manya gatan wasa,akwana a hantse... Kaka ta 6alli goronta tajefa a baki sannan ta d'an harareshi"to kar dai kanka yayi girma dan tace haka. Yak'arasa shiga yazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna da A'isha.Shi dai A'isha tana burgeshi baya gajiya da kallanta da duk wani abu data keyi.Yamaida kallanshi ga Kaka saboda me kikace kar kaina yayi girma?Tace naga dai wannan kirarin kyawawa akema. Aisha tasa baki "yanzu Hashim yana da makusa neKaka?Aiko makaho yashafa wannan k'ayatacciyar fuskar zaice me kyauce. Yad'an motsa kafad'a"Ah to gane min hanya...wai yaushane tafiyar taki?Tawatsa hannaye"ganinan dai, amma ba wani dad'ewa zanyi ba, tare dasu Mama zamu tafi,kasan har yanzu bamuyi hutu ba, amma da zamana zanyi wallahi garin bai ishe niba.

Yagyara zama"Shikenan sai a miki babban gida kawai yadda zai dad'a burgeki,kidinga jin dad'in zama.Cikin rashin fahimta tayi yar dariya "Kaji Hashim fa babban gida sai kace wacce zata dawo da zamanta gaba d'aya? Yagyada kai"To menene A'isha dan kin dawo gaba d'aya? Ai kamar ba matsala bace garin da kike so ne,ga kuma mutanan da kike so.

Yakalli Kaka da take ta cin goronta "Ke dai kamar mayya haka kike da goro.Eh koma dai mecece ni ba daina ci zanyi ba ko kai kake siyomin?Ya yamutsa fuska"To da wacce hujjar nasara zaiyi hawan k'aho? Tamishi dak'uwa idan baka siyo ba ai ubanka zai siyo.Shi da Aisha suka d'aure fuska wai su an ta6a musu Iyaye. Hashim yace"a ah Kaka wasa kar yayi wasa a tsikari uwar miji fa.A'isha tagyad'a kai"gaskiya ne dan uba baifi uba ba "Kaka tafara tafa hannaye cikin sallallami.Sai suka kyalkyale da dariya.Ba shakka wuyanku ya isa yanka. Tad'auko carbi zata shaud'ama A'isha ALLAH yabata sa a tayi tsalle gefe"Tabbb yanzu dan ALLAH sai ki shaud'amin wannan k'irgin carbin na ki me siffar rodi?To dawo ki gani mana.Tagirgiza kai"a ah wallahi ai sai in kwanta jinya, suka gama mata shak'iyanci san ransu sannan suka fara hirar arzik'i.

Hashim yadad'a gyara zama sannan yakalli Kaka cikin natsuwa"Kaka gaskiyar magana nifa A'isha nake so ba wani 6oye-6oye dama karatune yahanani sak'at to yanzu kam sai dai godiyar Ubangiji an gama har kuma an samu abun yi basai maganar iyaliba? Kaka tad'aga hannayenta sama tanama ALLAH godiya"Ashe tuntuni dakake fad'in Aisha ce matarka na d'auka na k'uruciyane nan gaba idan aka maka zance za kayi tawaye?To masha-ALLAH,ALLAH yasanya alheri,naji dad'in wannan al'amari,dakan d'aka shik'an d'aka tankad'en bakin gado.

Hashim yayi yar dariya"Aiko dai ba wani tawaye da zanyi yakalli Aisha ta sunkwui da kai amma labarin zuciya a tambayi fuska murmushi takeyi.Kaka tamik'e zata shaud'a mata carbin"Munafuka ana zance auranta ta nemi waje ta zauna saboda rashin kunya irin na ya'yan yau.Tashige d'akin baccin Kaka da gudu dan wallahi bata manta dukan carbin Kaka ba akwai mugun zafi.

Hashim yayi murmushi Kakarmu ta kanmu ALLAH dai yabamu i taku.tsufa me amfani acikin hayyaci da tunani.To Amin Hashimu,amma ba abinda yake kawo tsufa me kyau me amfani sai aikin k'warai lokacin k'uruciya"tsohon banza daga yaran banza yafara"kurik'e karatun"Alqur'ani da sauran kyawawan dabi'u da halaye, kuyi gaskiya da adalci a kome,idan kuka d'ore a haka Insha-ALLAH babu ta6ewa a rayuwarku.


IImi shine jigon rayuwa,shine abinda yake gyara d'an Adam,yagayara tunaninshi dan haka ku kara zage dantse da kwazo wajan nemanshi,Ilmi ko wani irine to yanada amfaninshi. ALLAH yama rayuwarku albarka. Amin Kaka.

Hashim da A'sha sai rawar kai sukeyi kamar k'adangaran gobara,daga ranar yakoma cin abincin darenshi a d'akin Kaka abinda da ba yayi sai can nisan dare sannan yake tafiya na shi d'akin wani lokacinma Kaka ce take korarshi yatafi yabasu waje za su kwanta. Kafin su A'isha subar garin Kafanchan sai da aka tsaida magana tana gama makarantar secondary za ayi bikinsu ba wata matsala da aka samu kasancewar su Ya'ya mazane kuma duk Kakace ta haifi Iyayan nasu. Shi kuma nan da nan yafara aikin ginin gidanshi a Zaria Street.

Kasham tana shafa ma faratanta jan farce (nail polish)ruwan k'asa,Baranzan yashigo cikin kakin soja. Suka kalli juna na wucewar wasu dak'ik'u."Beauty ina kikaje tun d'azu nake ta jiranki?Kamar ba da ita yake magana ba,zuwan can kuma bayan ta shak'i iska ta baki ta hanci sannan tace kasuwa naje siyo wannnan tanuna mishi nail polish d'in.Yazauna"anjima zani Jos amma kwanaki uku zanyi,to na baki time kafin indawo ki shirya kayanki zamu wuce barrack.

Barrack kuma?Ta tambayeshi cikin mamaki"Eh barrack kin gama makaranta to zaman me za kiyi?Mutafi kafin lokacin auran mu yayi nafa gaji da zama ni kad'ai kingane ko?Bai jira amsawarta yajuya yayi tafiyarshi.Tabi bayanshi da harara lallai za ayita dan wallahi tayi rantsuwa ba wanda zata sake bi har takwana dashi indai ba D'ansarai ba,bata ga kuma wanda ya isa sata canja wannan ra'ayi na taba har abadan duniya.Ita ya ma sosa mata inda yake mata k'aik'ayine,cikin gari za taje wajan Julaibib ta kwana biyu bata ganshi azahiran ceba amma kullum dashi take kwana dashi take tashi a cikin zuciyarta.


Tacanja kayan jikinta da dogon buje na velvet bak'i sai rigar shirt checker me d'amewa ta yafa siririn bak'in mayafi a gyararren gashinta data mishi ponytail style,jaka da takalmanta masu tudu bak'ak'e,tasa wasu manyan d'ankunne masu kama da awarwaro suma bakak'e sai siririyar sark'ar rosery a wuyanta.


Kai tsaye tashiga shagon.Abdul yana zaune yana aikin gida da aka had'osu dashi daga makaranta a darasin tattali (Economics) tak'arema shagon kallo ya dad'a cika ba kamar kwanakin baya ba, za taso taga irin canjawar da D'ansarai yayi.Tadawo da kallanta ga Abdul "Kai d'an samari ina Julaibib d'in? Fuska a had'e ya amsa "Baya nan.Haushi take bashi ita ba wani abu za ta siyaba amma sai tazo tana damun mutane yad'anyi k'unk'uninshi.

Taja kujera tazauna tana mishi kallan nazari,wani murmushi ya su6uce mata "wai shima k'arami dashi ya iya had'e girar sama data k'asa,tana so ta mishi wasu tambayoyi game da Julaibib amma ta san ko tayi a banza talaka ya girmi sarki bazai bata amsaba"Kai k'aninshine? Uhh yace batare daya bud'e bakiba. "Ina Sudaida?Ya yamutsa fuska shifa baya san adameshi, dak'yar kamar me ciwon baki yace "Ta tafi makarantar allo.Bata sake tambayar shi kome ba ta dai gane wannan halin nasu na rashin san magana a jinin sune.Itama sai ta bud'e Ovation d'in hannunta tana dubawa amma rabin tunaninta na ga Julaibib da inda yatafi.

Da d'an hanzarin shi yashigo shagon tare da sallama dan ya san lokacin makarantar allo yayi ba ya so Abdul ya makara.Caraf idanunsu yahad'u"La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin"tabbas da bata ganshi ba komawa zaiyi.Tamik'e tsaye tana mishi kallan k'auna me ciki da shauk'i " Yayi shar dashi cikin fararan kaya kanshi da bakar hula dara takalmanshi sau ciki farare,k'amshin arabi'an perfume d'inshi ya mamaye shagon,D'ansarai d'an gayu ne,me tsabta na gaban kwatance dan ba wanda zai juri sa fararan kaya sai ma'abocin tsabta.Idanunsu yakuma had'uwa...sai sukaji wani irin yanayi a ilahirin gangar jiki da zuciyarsu,da sauri yakauda kai yana Isti'aza.

"My enigma ma You're wellcome.. Julaibib bazan gaji ba ga shi na sake biyo ka,wallahi ba saboda kowa nashigo cikin gari da safen nan ba sai dan kai.Abdul yad'auki allanshi "Kawu na tafi.To Abdul ALLAH yabada sa a. Yara6a ta gefensu yawuce yana amsawa da"amin ya rabbi.


"Julai...yatari numfashinta"Kiyi hak'uri bazan ta6a miki k'arya wai dan kiji dad'i ba,bazan iya auran kiba, kiyi hak'uri dan girman...k''iris ya rage ta rungumeshi yayi taku biyu baya da sauri sai ta biyoshi har yafita a shagon yajuya da sauri yacigaba da tafiya.Tabishi da kallo har yasha kwana ya6ace ma ganinta.

Damme what an enigma man.Tafurta tana furzar da hucin takaicin,ta rik'e k'ugu tana kallan shagon"Ya tafi yabar mata shagon duk da kayan mak'udan kud'in da suke dank'are a ciki amma ko a jikin shi, wai an yak'ushi bishiya"shi D'an Sarai ta rasa me yasa yakeyi kamar yana jin tsoronta a wasu lokutan? Ba saurayin data ta6a yi da baiyi kwad'ayinta ya nuna maitarshi a fili ba sai shi, To me yasa!!!???

Yanzu duk abinda yamata za ta iya d'auka ko? Sai kuma ta girgiza kai"Aiko ba kayan Julaibib bane baza ta iya d'aukaba tunda ba na ta bane,idan tayi haka ai tazama 6arauniya"which is forbiden".Taja kujera tazauna dan bazata tafi tabar mishi shago a bud'e ba tunda ita tasashi tafiya,da batayi yunk'urin rungume shiba ta san zai tsaya.

Aminu ne yashawo kwanar yana rik'e da bokitin fenti da roller daga wajan neman halali yafito. Tamik'e da sauri tana fad'in"yauwa dan ALLAH Aminu ka taimakeni kajirama D'ansarai shago yaje gidane ni kuma sauri nake yi ban san abinda ya tsaya yiba.Ya ajiye kayan aikinshi aciki yajawo buta ba matsala.Sukayi sallama.Yayi alwala ya gabatar da sallar walha da aiki yanashi yi a dai-dai lokacin daya sabayi da zarar rana ta 6ullo.Shima gajiya yayi da jiran dawowarshi yaduba mukulli ya kulle shagon, a gajiye yake yaci aikine kamar ba gobe,yanzu zai je gida ya huta,gaskiya neman halali da wuya kowa kagani a inuwa to ba shakka ya sha rana.

Tunda yakoma gida yarasa sukuni wani abu a can k'ark'ashi zuciyarshi yana damunshi,shi dai yasan Kasham tana san shi da gaske, to amma ya rasa gane fargabar da take mamaye zuciyarshi game da ita.Ga wasu irin rikitattun mafarkai da yakeyi,ya rasa gane ma'anarsu,sai dai shi har kullum yana mik'a al'amuranshi a wajan ALLAH,yana yawaita sadaka.

Da daddare suna zaune a tsakar gida ita kanta Inna ta lura dashi, abincin ma k'adan yaci dan yasan Inna tana saurin gane yanayin shi da bazai ci ba dan cikinshi a cunkushe yake."Autana yau dai ko baka jin dad'ine?Yabud'e idanun shi daya rufesu kamar me bacci sun d'an canja kala"Inna kai nane naji yana d'an saramin.Tamishi kallan tausayi me cike da soyayya irin ta d'a da mahaifi"wayyo! Sannu...ai na ganka yau ba wata walwala,ya kamata kasha magani,ALLAH yasauwak'e. Yagyad'a kai "Amin Inna, ai nasha magani".

Alhaji Abdullahi ne yashigo da sallama Julaibib yakar6i kayan hannunshi "Sannu da zuwa Baba" Yauwa D'ansarai mun wuni lafiya? Yau ka rigani dawowa. Yazauna yana hutawa.Inna tad'auko mishi abinci tana mishi nata sannu da zuwan.Ya amsa da kulawa.Yafito da kaya d'inkakku kala biyar dukkansu farare yana nuna ma Inna.To har anyi d'inkin ne? Amma sunyi kyau madalla Ubangiji yasa rai aka yiwa.Ya amsa da amin yana kallan Julaibib"Ina alfahari dakai D'an Sarai tunda kana san ganin tsohonka ya fi na kowa,amma ni gaskiya nan gaba kar a sake d'in kamin kaya duka kala d'aya yo wannan idan hira nake zuwa ai sai budurwar tawa tace min d'an anace,wanke kamayar,itafa bazata gane cewa kullum wani sabo nake sawaba.Julaibib Yad'an shafa kwantaccen bakin gashin kanshi "kai Baba wani irin zuwa hira kuma,yanzu sai kama Inna kishiya?A ah kaji D'ansarai da wata magana fa, ba a aurowa aka auro ta?Inna tana yunk'urawa za ta tashi yafara dariya"Dakata mana ina za ki?Ko sauraran shi bata yiba"kanka akeji...yad'an daga murya"zo mana Maimunatu...tashige d'aki.Alhaji Abdullahi yakad'a kai "Uh uh uh mata duk haka suke da kishi ba babba ba yarinya,ka ganta nan tunda k'uruciya indai zanyi maganar k'arin aure to zata tashi tabarmin wajen.Julaibib ya sunkwui da kai dan maganar ta mishi nauyi.


Yasake kallan Julaibaib sannan yanuna shi da yatsa "Ita mace dad'in mu'amala ne da ita amma sai ka fahimci halinta,ka kuma sauke duk wani nauyi na ta daya ke kanka,to sai kaga ALLAH yahore maka ita kaji dad'in zama da ita,ai ka sani dai-dai da tsinken da zatayi sakacen naman da ka siyo mata idan tagama ci kai zaka kawoshi ko?Yagyada kai "Eh Baba na sani".

Yace to mace yar gatace gaba da bayanta, kar kayi la'akari da kome yayin da zaka mata kome face cewa aure bautar Ubangijine, shid'in ne yace haka za a mata bad'an kome na taba.Kuma babban jigon zaman aure shine HAK'URI za kayi hak'uri da ita a wajan gazawar ta irinta yar Adam,kaima za tayi hak'uri dakai a wajan gazawar ka irin na d'an Adam,dan babu wani mutum a doron duniya da yake cikakken da bashi da nak'asu sai Annabinmu Muhammad sallallahu alaihi wa ahlihi wasallam.Dan haka sai ana kauda kai ana yafiya,dan wasu lokutan idan suka kwafsa maka sai kaji kamar ka karairayasu,kashafe su a doron duniya,to amma hakan bazai yiwuba dan namiji ne yake cika mace,macece take cika namiji,taimakeke niyace atsakanin juna.

Kadinga tuna cewa tunaninka da nata ba d'aya bane,ko a gidan fiyayyan halitta za6abban za6abbuma sun nuna irin halin nasu,kuma hakan shine cikar macen taka,haka ALLAH yaga damar halittarsu. Yagyad'a kai cikin ladabi" To Baba nagode.


Maza dangin gurjiya sai an fasa ake sanin me k'waya.


25 Rabi'a Thani 1441
22 December 2019

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs






DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFI💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na takwas.


Baranzan yashigo gidan da d'okin ganinta, yanata k'wala mata kira amma shiru bata amsaba. Yashiga d'akin da niyyar tashinta dan ya san bacci ne kawai zai hanata amsa kiranshi da kuma fitowa ta mishi Oyoyo cikin d'okin ganinshi itama.Yaja yatsaya da mad'aukakin mamaki yana kallanta,tana zaune kwalliya take fuskarta,yanuna ta da yatsa"au dama kina jina amma kika ki amsawa?Wai lafiya kuwa?Yabita da kallan nazari cike da shakka.

"Beauty wai lafiya kuwa?

Tafurzar da hucin takaici sannan tace"da wannan kiran irin na yan farauta zan amsa maka?Tacigaba da zizara ma girarta jagira"ni gaskiya bana san rashin natsuwa.Yayi saroro kawai yana kallanta tagama kwalliyarta tajawo kayanta tana sawa bujen jeans ruwan bula da d'amammiyar riga mara hannu ruwan madara, yau tayi k'ananan kitson kalaba ta tubkeshi da ribbon ruwan madara sai d'an kunnan beads ruwan bula data sa,wallahi tayi kyau k'irar kalangunta ya fito rad'am,ta sunkuya tana sa takalmi ruwan madara sau ciki me tudu,tagama sawa tamik'e tsaye tana saba jakarta a kafad'a kalar takalmanta ruwan madara,tana shirin fita yakirata "Beauty...Taja ta tsaya sannan tajuyo fuska a yamutse take mishi wani kallan uku ahu"wani abune?Kamar yaya wani abune?Tad'aga misho hannu"kaga malam ya za muyi canjan tambaya ba amsa?Ni fa wallahi sauri nake yi idan ba ka da abin cewa...Yayi murmshi dan wannan kwalliyar ta tsumashi.

"Kurum Ishshi Bazinzira(Akwai kud'i sosai, na rantse miki da ALLAH)

Yanuna mata aljihunshi yaushe kike so muje Kasham Hotel muci ubansu?Da kud'i da maciji maganinsu kisa"sai yamik'a mata abinda ya nannad'e a warraping sheet.kallanshi tayi kamar bata gane abinda yake nufi.Yagyada kai "yes take it's yours...ta d'auke kai daga kallan da yake mata,ta san Champagne ne,to ita da ne zai bata Champagne taji ya burgeta ya mata gwaninta, cikin jin fushi tace" baa na so.Kamar ya bakya so? Mutumin na ki nefa?Tagalla mishi harara"so bloody what?To hell with it.Ba na sha,bazan k'ara sha ba,dan haka karka k'ara kawo min.Beauty... tad'auki agogonta na fata tana d'aurawa kana da lokacin 6atawa amma ba da Kasham ba,tayi tafiyarta.Yayi murmushi yakai d'aki ya ajiye mata, ya san za ta sha yanzu dai ranta a 6ace ne, ko me yasame ta haka oho yad'an motsa kafad'a shima yajuya.

A waje suka had'u da Lidiya yake fad'a mata abubuwan da Beauty take mishi sunyi yawa fa,she bai gane me yashiga k'wak'walwar taba.Takad'a kai cikin takaici "Ranar wanka ba a 6oye cibi...dan haka ta k'yank'yasa mishi abinda ke faruwa. Yajijjiga kai "lallai biri yayi kama da mutum"To yanzu kina nufin cikin gari ta tafi wajan shi?Ko shakka babu,abin takaicin kuma nama na jan kare sai shishshigi da k'wala kai a faranti amma ba kwarjini.


Oh damme.Yadunk'ule hannu ya naushi iska ran maza ya 6aci, allurar soja ta motsa.Ya kalli Lidiya za muyi magana anjima? Tagyad'a kai "shikenan.

Yashiga mota ya zauna yana sauraran wakar"Who let the dogs out..ya kunna taba yana zuk'a, amma zuciyarshi k'ara tafarfasa take yi idan ya tuna duk abinda Beauty take mishi wai saboda wani filthy stupid bahaushe d'an cikin gari ne.Yadinga tuna beautiful life d'in da sukayi,suna matukar son juna,kuma Beauty kome na ta daban ne,musamman shi da take son shi tana bashi kome da yake so cikin dad'in rai,bayan alakoro har gyara take k'ara mishi.Wata soyayyarta ta dad'a tsumashi sai kawai yaja motar dama cikin gari za shi yabiya kud'in k'ofafin da yace a mishi na dank'areren gidan da yake gina ma Beauty ita da kids d'in da za ta haifa mishi.

Yana tsaye a Mak'era suna magana da me aikin k'ofofin kawai ya hango ta goye a bayan wani me mashin sunata dariya. Ranshi in yayi dubi ya 6aci zuciyar shi ta raya mishi wannan ne tsinannan bahaushen da take bi cikin gari,sun gama abinda za suyi yanzu kuma zai maida ita gida.Lallai yau za a yi ta sai yashige mota yabi bayansu sai dai kash... Kafin yak'arasa har me mashin d'in ya sauketa ya k'ara gaba dan Samaru zai wuce shi yasa Baranzan bai ganshi ba.

A tsakar gida yasame ta, ta d'ora k'afa d'aya akan d'aya tana cin k'osan rogo tana wata yatsina kamar dole a ka mata sai ta ci.

Beauty daga ina kike?Yayi tambayar cikin d'aga murya da tashin hankali.Itafa Baranzan ko k'aunar ganinshi ba tayi dan haka tajuyo cikin jin haushin tambayar da wanda yayi ta"daga Inda ka aikeni mana. yanuna ta da yatsa"ke! kar ki min rashin kunya fa, manufuka kawai,ba daga wajan tsinannan bahaushen nan kike ba?Tayi lallausan murmushin tura haushi "Thank God tunda ma ka sani,wani abu ne? Tamishi tambayar cikin wani malalacin kallo sannan tacigaba da cin k'osan rogon ta hankali kwance tana wakar "Hail Mary mother of Jesus.

Bazato taji saukan mari hagu da dama yafara zaginta ta

Please Login or Register in order to submit comment