Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan yayi shirin komawa Jaji Barrack bakin aiki amma yayita rok'onta idan ta samu sarari tabiyoshi,ta amsa da to,amma tayi alk'awari ba wanda zata sake bi har ta kwana dashi indai ba Julaibib ba.


Ranar talata Musaddiq baije ko ina ba yana zaune a D'akin-shak'atawa yaji ana k'wank'wasa k'ofar,yace shigo dan yasan kila Asma'u ce amma sai ta fad'a mishi dalilin ta na k'inyi sallama,amma me?Kasham yagani a tsaye. Kasham? Yafad'a da mamaki kece?Dama kinsan gidana ne?Takasheshi da lallausan murmushinta "Kabar mamaki,dan matambayi ai baya 6ata.


Naji kayi aure shine nazo tayaka murna, I'm I not wellcome? Bata jira amsar shiba tama kanta mazauni a d'aya daga cikin kujerun d'akin,tad'anbi D'akin-shak'atawar da kallo, sannan takalleshi "To ina amaryar taka?Yamike bari akirata yashige d'aya d'akin sannan ya kullo k'ofa"Safiyya takalleshi lafiya?Yarungume hannayen shi a k'irji lafiya lau,tashi kije ku gaisa wata yar makarantar muce tazo mana ALLAH yasanya alheri.Tamishi kallan tuhuma"Oh wanda tamaka a makaranta bai gamsar da itaba har sai ta biyoka gida?Yayi murmushi"Haba amaryata yaushe akai daren da gari zai waye? Kasham...she mean nothing,ai kece komai na, yafara Istirja'i, shaid'anne yake so yasak'a miki mummuna,kinji amaryata?Tayi murmushi suka fito tare.


Wani Ovation take dubawa tad'ago tana murmushi"Amarya barka da fitowa,tanuna Musaddiq kinga mijin kin nan kirkinshi ragaggene a wajena tunda har zaiyi aure amma bai fad'a minba,ni kuma ai naga abin farin cikine to meye na 6oyewa,?To koma dai yayane ba a gayyace niba amma danaji labari gashi na zo" Musaddiq ina tayaku murnar aure,kuyi hak'uri Ku zauna lafiya for better for worst.Suka mata godiya, tace haba ba komai fa,wata kilama mutumin nakane yace karka fad'amin. Kamar bai gane wanda take nufiba yace"Wa kenan? Tad'an kalleshi "Wa kake dashi a Gidan-Waya daya wuce D'ansarai?Yayi murmushi"au shi kike nufi?To ba ruwanshi,Julaibib bai ta6amin maganar kiba.


ALLAH da gaske!???

Ta tambayeshi cikin mamaki zata cigaba yatari numfashinta"Indai maganar D'ansarai zakiyi tona rok'eki kiyi shiru kawai tunda bashi da wani amfani.Yafad'a miki gaskiya... Takatseshi da sauri "Karkasa jinina ya hau,danni nayi alk'awari ko ana ha maza ha mata sai na auri Julaibib dan ina sanshi,takalli Safiyya" Madam ku taimakeni dan na san za ku iya wallahi,sallah ne dai da banayi yasa kuke k'ok'arin nisantani daku ko?To nace zan iya, ai ko bai kamata a k'wacemin gatarin danace zan iya had'iyaba...

Safiyya ta jijjiga kai kenan a yadda take magiyar nan ta dad'e tana yak'in neman soyayyarshi ALLAH ne kawai yatsare shi daga fad'awatarkonta,tasake kallanta masha-ALLAH tanada kyau najan hankali,d'an k'aramin bakin ta da manyan idanunta masu maik'o su suka k'ara mata kyau na musamman ga ta da yalwan gashin kai,gashi kuma da alama ma'abociyar kwaliyar jan hankalice,dabara tazo mata dan haka ta kalli Musaddiq cikin tashin hankali"Dama baka fad'a mataba?To bari kiji Kasham kike kowa?Ki bud'e kunnnuwanki ki saurareni dakyau"Julaibib yana da matar aure karatu ake jira tagama musha biki kuma kanwata ce,dan haka kitashi kibar min gida.Tamik'e rai a 6ace ta wuce cikin.

Takalli Musaddiq shi kuma yayi saurin kau da kai"Shin da gaske ne abinda tafad'a? Yagyad'a kai "Aishi yasa tun farko nafad'a miki Julaibib bazai aureki ba danna sanshi farin sani.Tamik'e tana sa6a jakarta akafad'a" Shikenan amma ba hakan yana nufin na hak'ura da shi bane,ku ai musulmai mata hud'u kuke iya aura,dan haka ban damu ako tanawa zanzo ba,ni dai burina in mallaki Julaibib a kowani irin hali da yanayi,zanje inyi tunanin abinda zai fishsheni.

Tana fita Safiyya tadawo.Yayi murmushi yana mik'o mata hannayenshi "Amma gaskiyar magana kin burgeni"bata mika nata hannayenba,tagalla mishi harara"Shi me gayyarma ba shiga shirginta yakeyiba sai kai,ba kamar kid'iba sai kayan ganguna? Yafuzgota da k'arfi" Haba Safiyyahhh... Kina ganin wani abu zai shiga tsakanin mune?Kasham bata gabana. Tashagwabe murya"ai ba anan takeba an danne bodari aka,ni dai kawai ko?Tad'ago tana kallanshi.Yagyad'a kai" Uhun ke me? Ni dai kawai maganin kar ayi to tun wuri kar a fara..Yayi yar dariya yana d'an jan karan hancinta"To ranki yadad'e zan kiyaye"Yakamata kuwa hakan.Sai yad'an bata marin soyayya suka k'yalk'yale da dariya.


Kwanakin Julaibib uku a Kaduna sannan yadawo ranar laraba da yammaci,wata yar Seminar sukayi da k'ungiyar"Ansaruddeen"yana rataye da bak'ar jakar matafiya,godiya yakeyi ga ALLAH daya kaishi lafiya yadawo dashi lafiya sannan yashige gidan da sallama.Inna ta amsa sallamar da murnan ganinshi "Maraba da autana "Yazauna agefen tabarmar cikin murmushi,Iyaye dad'in ganine dasu,musamman idan kayi dace da masu ilmi da sanin yakamata. Fatanshi har kullum ALLAH yabashi ikon jiyar dasu dad'in rayuwa kamar yadda suka jiyar dashi,musamman ilmin addini dana boko da tarbiyar Al'Isamiyya da suka bashi.

Yacire takalmanshi masu rufi da safa sannan yagaisheta"Inna ya zafi"?Tagyada kai "Zafi kam akwaishi,sai dai yakusa k'arewa tunda damuna nagab da sauka.Yadi6o ruwan randa yanasha yaji dad'i har ranshi saboda k'amshin saiwoyin datake zubawa aciki dan k'arama ruwan armashi wajan sha yana zancen zuci"Inna duk lokacin da bana gida ruwan randan nan naki nake fara kewa,ya ajiye kofin.To Ubangiji yabamu damuna me albarka.Inna ta amsa da Amin.Yaciro mata tsarabarta sannan yamik'e yasa takalmanshi"barinje gidan Hajiyar mu"To ka gaisheta.



Daga gidan Hajiya yawuce gidan Kawunshi,yaran gidan suna zaune a D'akin-shak'atawa suna kallo,k'ananan suka taso aguje suna murnan ganinshi"oyoyo Yaya Julaibib,oyoyo Yaya Julaibib duk suka mak'alk'aleshi dan D'ansarai indai wajan kyautane to ba daganan ba,sam abin hannunshi baya rufe mishi idanuba, suna ganin ya bud'e jaka suka fara tsalle kowa yana fad'in "Yaya Julaibib bani, a ah ni zaka ba,nima ai na iya rabo Yaya Julaibib....yace a ah bari aba babba Sagir maza kaima Khausar taraba muku, yanunata da yatsa"banda ke a ciki,rabo irin na adalci kawai za kiyi a tsakaninsu.Tayi yar dariya"To shikenan Sagir kawo ledan."waisu Mama basa nan ne? Eh sunje gidan suna. Yajuya shikenan na dawo anjima.


A zaure sukayi kaci6is,taja baya da sauri"Sannu da zuwa"ya amsa da yauwa.Daga ina kike? "Gidansu Nasmat.Ka siyo min tsaraba?Yad'an kalleta "Haba dai, babba dake acin tsaraba?Tayi yar dariya "Yanzu dan ALLAH Yaya D'ansarai wani girmane dani?Ina abin yake wai maye yacinye jariri?Ai duk girmana ban kai Hajiya ba,daga gidansu Nasmat naje gidanta na kuma tarar da ita tana cin tuffa kuma tace tsabarar dama kai matane.


To dake da Hajiya dayane?

Daga baya suka jiyo muryarshi.Tad'an karyar da kai gefen dama"Kai Yaya Aminu yanzu ni banfi Hajiya ba?

Ke dalla tafi kabamu waje, irinki goma baza su kama k'afar Hajiyarmu ba bare su fita,to ke asuwa?Karankad'a miya dake. Julaibib yace"ah to kin daiji ko?Ya tambayi Aminu"akwai ragowar kunun tsamiya a d'akinka? Kaima ka san ba a rasa nono a riga sai dai idan rigar bata Fulani bace.Yace yauwa to kije ki d'auka kiyi farau-farau dashi.Tajuya zata shige gida"ai ni kunu koda d'uminshi ba d'ad'ani da k'asa yayi ba bare ragowa, zanzo har gida in kar6a,sai kaba Innarmu ta ajiyemin koda na zo baka nan...


...Kome na rayuwa naci dana sha an halicceshine dan d'an Adam,shakeru aru-aru tun kafuwar doron duniya,za kuma kaci har kagaji,basa k'arewa sai dai kagama rayuwarka katafi kabarsu...

...Rabo na me rabo ko kura tagani haramiyarta.


15Rabi'a Thani 1441
12 December 2019

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.



DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in



...GWAJIN DAFI 💔



Daga alk'alamin 🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)



Shafi na hud'u.



Monday ranar aiki ko nasara na tsoronki.Ranar litini aka koma makarantun boko a zangon karatu na farko.Sudaida da Khausar sunfi kowa farin ciki saboda shigarsu aji d'aya a k'aramar Secondary,kuma a wannan lokacin aka turo yan TP(Teaching Practice) Julaibib na d'aya daga cikin wadanda aka turo makarantar su,to kamar yadda su Sudaida ke murna haka Kasham ma tayi murna dan makarantarsu d'aya.

Dasafe yashiga gidan cikin shigarshi ta fararan kaya.Yagaishe da su Mama, sannan yakalli Sudaida da take karyawa"idan kika bari nafito daga d'akin Kawu baki gamaba to ni tafiyata zanyi.Tamik'e tsaye tana addu'ar gama cin abinci nama gama barin kira Yaya Khausar sai mujiraka a mota.Gaisawa kawai sukayi da Kawun nashi yafito suka tafi.

Kasham tana zaune a farar kujerar roba a inuwar dalbejiya kullum tana ganin irin zirga-zirgan da Sudaida takeyi idan an tashi tara(break) tsak'anin wajan saida kayyakin da wajan da Julaibib yake yawan zama,da alama ita yake aika tasiyo mishi abinda yake buk'ata. Tasauke gwauran numfashi wato dai yana magana,kalli yadda Sudaida take dariya, duk yadda akayi shi yayi furucin daya sata darawa.

Bayan an koma aji yamik'e yashiga d'akin malamai(Staff Room)sai ganinta yayi zaune a tebur d'inshi magana zamuyi tafad'a cikin murmushi.Ranshi a 6ace yama rasa abinda zai fad'a sai kawai yajuya dama alli(chalk)zai d'auka to gwamma yatafi Principal Office yad'auki wani acan.Tabiyoshi da sauri"ji mana Julaibib,ka tsaya kaji abinda zan fad'a maka,idan kuma kaki to ina biye da kai duk inda kasa kafafunka.Bai saurareta ba yayi tafiyar shi,sauri yake yi har yana tuntu6e, abin yabata dariya"To wai shi Julaibib tsoronta yakeji da bayaso ya tsaya kusa da ita ko me?Ta tuno ranar data mamayeshi ta rungumeshi a Gidan-Waya yadda ilahirin jikinshi yakama rawa.Toh ni dai bana gane ma wannan tsoron naka wallahi.

Lidiya tak'araso wajan tana mata kallan takaici nama na jan kare"ai ke dai kin gama a sara Kasham,namiji yana gudunki amma ke kina ta shige mishi sai kace shine mahad'in numfashinki?Taja dogon tsaki"to kidai yi a hankali kafin dalibai su farga,dan kin san ba dad'i zaki jiba idan suka tasaki a gaba da wak'ok'in shak'iyanci.Tagyad'a kai"zan so hakan indai zasu danganta ni da Julaibib a cikin baitocinsu.Ke Lidiya bazaki gane kome ba dan baki fad'a tarkon so ba. Ai ko na fad'a tarkon so bazanyi hauka da wawanci da rashin aji a wajan da nasan ba a maraba dani ba.tawuce tabata waje."Iska dai na wahalar da me kayan kara.


A sanda hantsi ya dubi ludayi na ranar a sabar,yana zaune a shagonsu yana lissafin mutanan da suke bi bashi kuma su kai shiru mak'atau balaguro a lahira"kamar sun sha nonon uwarsu,d'ago kan da zaiyi caraf idanunsu yahad'u.Yafara ambatan ALLAH a zuci.

Tana tsaye a barandar shagon cikin shigar shadda me maik'o ruwan makuba riga da zani bata d'aura d'ankwalin shaddar ba sai ta yafa k'aramin mayafi ruwan madara a saman gyararren gashinta data d'aureshi da k'atan ribbon ruwan makuba jaka da takalmanta ruwan madara,fuskarta,ta d'auki kwalliya,ta rungume hannayenta a k'irji tana k'are mishi kallo,yana sanye cikin yadi ruwan madara kanshi ba hula saisayan dayayima gashin kanshi da k'asumbarshi sun mishi kyau,ya fito sharrr dashi k'amshin arabian perfume d'inshi ya mamaye har inda take tsaye.

Yamaida kallanshi cikin littafin amma ya kasa cigaba da abinda yakeyi. A hankali tafara taku d'ai-d'ai har tashiga shagon.Hucin numfashinta kawai yaji a gefen fuskarshi"Dan Sarai barka da hutun k'arshe mako".

Ke malama na fad'a miki kifita harkata ko ana soyayyah dole ne!?Tamishi fari da idanun ta sannan tafara magana da wani salo irin nata na yanga "Kana ganin ba a soyayyah dole?Tagyad'a kai "To ko ba ayi za a fara hakan akan mu,kaga zamu shiga kund'in tarihin duniya"Julaibib da Kasham"what a perfect match.. Wai kai sai dubu nawa kake so in fad'a maka ina sanka, zanyi sallah koda zan 6ata da kowa nawane sannan za ka yadda dani? Haba Julaibib lokaci fa yayi da zan tunkari iyayena da maganar ka,kabani goyon baya,kaga mun kusa gama karatunmu sai kawai muyi aure hankalin mu zai kwanta"kanwa ta kar tsami k'wannafi ya kwanta.Tayi taku biyu tad'auki ragowar ruwa da yasha,tafara kur6a tana kallan shi danjin abinda zai fad'a,amma har ta shanye baiyi wani motsi ba.

"Jesus christ"!

tafad'a cikin kad'a kai,miskilancin ka yawane dashi wallahi,wanda bai sanka ba zaiyi zatan kai kurma ne awasu lokutan fa.


Bai kalletaba yace nima sau dubu nawa kike so in fad'a miki bazan iya auren kiba kafin ki yadda dani?!

No No No tad'aga mishi hannu ni ba irin wannan banziyar amsar zaka bani ba.

Musaddiq yashigo da fara'arshi ganinta yasa shi d'aure fuska.Suka gaisa a tak'aice tana tambayarshi ya d'aliban makarantar da yake TP?Ya amsa da lafiya lau a tak'aice.Yamik'ama Julaibib hannu sukayi musafaha. suka cigaba da maganganun su zuwa can Musaddiq ya kalleymta"Wai lafiya kuwa? Tamishi wani kallo"Kaima ai kasan tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i "Musaddiq ban sanka da irin wannan halin ba.Yadauke kai daga kallan datake mishi "Eh ai kinsan kamawa takeyi a d'aure me d'aurewa,Zama da mad'aukin kanwa kuma shi ke kawo farin kai.

Musadd...yatareta da sauri "A ah kiyi hak'uri kawai matata tace bata yadda magana tadinga shiga tsakanin muba. Matarka?Ta tamabaye da mamaki Eh haka nace matata.Tad'an ta6e baki"to kenan tsoronta kakaji? A ah Ba tsoronta nake ji ba,sai dai bana san 6acin ranta kona sisin k'wabo.Ahaf,tawatsa hannaye "ba cinya ba k'afar baya.tama Julaibib lallausan murmushin ta"ni zan wuce sai mun had'u ranar litini a makaranta"tajuya tayi tafiyarta.


Ranar litini itace da darasin farko a ajinsu Sudaida tana shiga ta tarar dasu a tsaitsaye suna caccar baki.Tabisu da kallo "Lafiya kuka cika ajin da hayagaga bud'ar kan karya?Linda tafara mata bayani "ranar juma'a Sudaida tana cikin yan weekend-sanitation na wancan makon, amma takama hanya tayi tafiyarta ba tare da tayi kome ba,shine yanzu muke fad'a mata wannan juma'ar dole ta tsaya suyi ita da Dinatu,shine tafara masifa wai ba wanda ya isa yasata tayi sai idan taga damar tsayawa tayine kawai zata tsaya,wancan makon ne take da aiki batayi ba kuma ai yariga ya wuce. Kasham tace"baki kyautaba maimakon ki bada hak'uri kome yawuce shine sai ki rufesu da masifa?Sudaida ta turo baki gaba"to ai bani kad'ai bace Dinatu ma tafito indai gaskiyane abun.Tatsareta da manyan idanunta masu maik'o"Idan kuma karya ne fa?Sudaida tad'an motsa kafad'a"shikenan sai tayi zamanta dama idan aka tsaneka ko ruwa ka fad'a sai ace ka ta da k'ura"tafara k'unk'uni.

Kasham tajijjiga kai"ban ta6a dukan kowa ba tunda nazo makarantar nan,amma yau za kisha na jaki,jeki Staff-Room ki jirani.Yan ajin suka zaro idanu, wasu suka d'ora hannayensu aka"Yau Sudaida zata kad'e har ganyanta a wajan malamai.Har ta kusa fita daga ajin sai kuma takirata"Hey come back"Sudaida tadawo tana kumburi"Kneel down here"takai gwiwoyinta k'asa tana k'unk'uni.Kasham tanunata da yatsa ke"If you dare say something again...I will deal with you.

Takira Dinatu tana tambayarta me yasa baki tsaya an gyara ko in dake ba? Cikin rawar murya"Tace bani da lafiya ina kwance a hostel ranarma ban shigo ajiba". Hakane? Ta tambayi sauran d'aliban suka amsa da eh.sai tadan dafa kafad'rta"Amma yanzu kinji sauk'i?Eh malama naji sauk'i.To jeki zauna ko.Tajuya gaban allo tafara rubutu,tagama rubutawa tajuyo tana fuskantar d'aliban tana musu bayanin sabon darasin da suka shiga.


Sudaida tasake kallan siririn farin agogon fatar dake daure ahannunta na dama,lokacin tama ya kusa k'arewa amma dan wulak'anci ta barta a durk'ushe, gwiwoyinta har sunyi tsami dan rashin tausayi da imani,tabi k'eyarta har zuwan gashin kanta da harara, wannan uban gashin k'aryane ba na ta bane wig ne,ga wani d'inkin rashin mutunci da tayi da atamfar jikinta,koya tayi tasa oho?Taja dogon tsakin dayasa duk yan ajin suka kalleta da mad'aukak'nn mamaki.

Kasham tasake jijjiga kai"ni keki jama tsaki ko?Wallahi yau sai nayi maganin bakin rashin kunya.Tashi kafad'a min abinda yasa kikaki tsayawa ranar juma'a.Taturo baki gaba"to ai Yaya D'ansarai ne yace shi bazai zauna jirana yarasa sallar juma'a ba,ni kuma shine na bishi. Wani lallausan murmushi yasu6uce mata har kyawawan fararan hak'oranta suka bayyana,jin ta ambaci D'ansarai wato dama k'anwarshice wannan? Kawai sai ta rik'o hannunta suka fita.


Ajin yakaure da hayaniya,wasu suna mata ALLAH yak'ara gwamma ayi maganin bakin tsiwan, wasu masu raunin zuciya har idanunsu sun cika da kwalla na tausayin halin da zata tsinci kanta aciki indai tashiga dak'in malamai,musamman kuma da Kasham tayi wannan murmushin sai suke ganin lallai na tanadin wuyane da ALLAH ne kad'ai zai ceci Sudaida.

Sun d'anyi nisa da ajin sannan suka tsaya.Kasham tadafa kafad'arta "Kidaina irin wannan halin bashi dakyau,masoya da mak'iya ba a guzurinsu halinka zai baka su a duk inda kaje"Next time karki sake binshi sai kinyi aikinki kingane ko? Tagyad'a kai.Nima kiyi hak'uri da abinda namiki.Tayi mirmishi "bakome jeki aji ga malamin lissafinku can zai shiga"Always be a good student.


Takoma aji tana wata tafiya irin ta eh yane naci dubu sai ceto.D'aliban suka zaro idanuna suna binta da kallan sama da k'asa alamar"a ah abin mamaki wai Baturiya da suna manga.Dan ba hawaye ba wata alama ta an bata na jaki,amma ba damar tambayarta ya akayi aka haihu a ragaya?Danga Malamin lissafi nan yahad'e girar sama da k'asa,dan shima k'wallan shegene shi yasa ko d'an k'us k'us k'us d'in nan na d'alibai basuyiba sai an tashi tara za a baje kome a fai-fai.Sudaida tamusu fari tana wani lallausan murmushi sannan tazauna awajan zamanta,Suna had'a idanu dashi itama tashiga taitaiyinta.

Suna ciye-ciyensu dasu A'isha a sanda aka buga tara,sauran yan ajin sun zagayesu ana tambayarta an daketa kuwa?ya akayi tabarta tadawo aji da sauri?Sun dauka har a buga tara basu gama horata ba,bulala nawa aka mata?Tawani hura hanci cikin kuri kamar gaske "tama isa ta dakeni ne?Ai wallahi ko kura ta san gidan me babban sanda.Suka kyalkyale da dariya suna ihu;shegiya yar gidan Ibrahim-Mai Lambu, tad'aga musu hannu"a ah kar wasa yayi wasa a tsikari uwar miji fa.Ni yar sunna ce dan haka kar wacce takuma shegan tani ehemmm.


Kasham dasuke zaune a benci ita da wasu malaman suna hirarsu ta k'walamamata kira tayafito ta da hannu.Sudaida tadanja tsaki"nifa wannan malamar tana neman shigarmin hanci da k'udundune. Suka sake kyalkyale da dariya"kila yanzu ne zata hukunta ki a bainan-nasi.Dammm...zuciyarta tabuga tsoro ya baibaye ta, kuma kila hakane,ba mamaki tajuyo maganganun sune tunda dama ba a hankali sakayi taba.Bata kulasuba tamik'e tana Istirja'i.


Ga ni tafad'a cikin ladabi "dole gyad'a tai mai idan tak'i tasha matsa"Kasham tabita da kallo,haka kawai taji tana santa,tunda k'anwar masoyin tane.Lidiya tace"meye haka kuma?Kin kira yarinya kin tasata a gaba da kallo kamar wata magiji.Tasauke gwauran numfashi, tasa hannu a jaka ta zaro kud'in dabata k'irgaba tamik'a mata"ungo kije kisai abinda kike so. Sudaida tabita da kallan tsoro da mamaki kamar yadda sauran malaman sukayi "to da wace hujjar nasara zaiyi hawan k'aho?

"Kar6a mana Sudaida.

Tajuya ba tare data kar6a ba"bar abinki nima ina da nawa.Lidiya tadaka mata tsawa"ke k'aramar mara kunya dawo.Sai kawai tasa gudu.Tayi kwafa zamu had'u dake gobe aji.Kasham tahad'a tafukan hannayenta"Dan ALLAH Lidiya karki daketa dan bata miki kome ba.How dare you Kasham kice bata min kome ba ni sa'ar wasan tace dazan kirata tak'i zuwa?Saboda ita kanwar wancan me shegen girman kan tsiyan?To niba ruwana abu kazan uban ta zanci.Haushi yakama Kasham sai kawai tace"ai ko abu kazan uban ta yafi k'arfinki har abadan duniya.Cikin tafasar zuciya Lidiya tanuna kanta da yatsanta"Kasham ni kikema wannan rashin mutuncin saboda wasu tsinannun hausawa?Ban miki wani rashin mutunci ba, magana kikayi ni kuma na baki amsa.Banda shiga sharo ba shanu ina ruwanki da ita?Ko ke kika kirata? Kome tamin ni naja,idan naga dama in mata hukunci,idan naga dama in k'yaleta bai shafeki ba"wannan sa kai a uku ne takaban siriki.

Suka farar cacar baki malamai suka shiga tsakani daga nan taran yawatse dan an koma aji. Takoma Staff-Room dan bata da darasi a kowani aji har a tashi sai kuma gobe.Tabishi da kallo cikin harara dan kwana biyu taje yajin aiki akanshi, duk yadda takejin san

Please Login or Register in order to submit comment