Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Compiled By Umar Dalha Funtua.


✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




*innama amruhu iza arada shai'an an yaqula lahu kun faya kun*



0⃣1⃣



          

Falo ne mai matsakaicin girma wanda ke dauke da set din kujeru labulaye carfet wanda dukkansu kalolin ash ne turarre da kuma mai haske,daga bangare daya t.v plasma ce 'yar matsakaiciya reciever da kuma D.V.D  wadanda aka qawata jeransu.

     Can daga kowacce kusurwa ta falon flower ce cikin plower vase dake a tsaye masu matsakaicin kudi,sosai falon ya bada sha'awa duk da ba wani uban kudi aka narka masa ba sakamakon yadda komai yake tsare a muhallinsa,bugu da qari kuma yadda ya wadatu da tsafta yake bada qamshin turaren wuta mai sanyi

    Mamallakiyar falon ce zaune kan daya daga cikin kujerun falon,matashiya ce wadda ba zata wuce shekara sha takwas ba,fara ce ba irin qal din nan ba,tana da matsakaicin kyau wanda kwalliyar da tayi cikin shadda orange dinkin bubu ya sake fidda kyanta,dan kwalin shaddar na ajjiye gefanta wanda ya zamo sanadiyyar bayyanar kitson dake kanta qananu wadanda aqalla sun doshi guda dari da hamsin,yadda falonta ke qamshi hakama jikinta yake yi.

    A hankali ta daga kanta karo na barkatai ta sake aza su kan agogon bangon dake manne saman t.v plasma din dake gabanta maqale jikin bango.

     Sauke idanun nata tayi kana ta maida kan dan madaidaicin centre table din dake gabanta,ta miqa hannunta ta dauki wayarta samfurin tecno w3 ta sake lalubo lambar da tun dazun take ta nacin kira,duk da cewa amsa daya ake bata tun dazun cewa lambar da take nema din a kashe take amma hakan bai sanyata ta daina kira ba.

   Yanzu ma amsar duka daya ce,bai saba kaiwa war haka bai dawo gida ba,yawancin baya gota qarfe takwas indai ya dade da yawa bai dawo din ba,sau tari idan taga hakan kuma ta tabbatar ba zaya wuce gidan babbar yayarsu ba hajiya yahanasu,saidai yau duk sai taji gidan shiru babu dadi,saboda baki daya 'yan tayata zaman sun tafi gida saura ita daya.

    Sauke ajiyar zuciya tayi tare da lumshe idanunta,ta dan zame kadan ta kwanta saman kujerar tana jin kewa na ratsata,kewar yara take sosai,mutum ce ita mai bala'in son yara,saidai Allah bai azurta ta da samun nata na kanta ba tsahon shekara shida da aurenta,kasancewar tayi aure tun tana da shekara goma sha biyu kacal a duniya.

     Tayi zurfi kadan cikin tunanin nata taji ana yunqurin bude qofar gidan da muqulli,ta bude idanunta tana duban agogo,qarfe tara har da mintina arba'in da biyar goma saura kenan,zumbur ta miqe ta janyo dankwalinta ta daura kana ta fito a hankali ziwa tsakar gidan nasu wanda yake da yalwa babu laifi,bayan nata dakin ciki da falo akwai dakuna biyu masu ciki dai dai wanda guda daya mallakin mai gidan ne,dayan kuma 'yan karikicen da ba'a rasa ba take ajjiyewa ciki,sai kuma bandaki daga bangare daya gefensa rijiya ce,sai kuma yalwataccen kitchen dake kallon dakuna biyu masu ciki dai dai din wanda yayi girman dakunan nasu,fes tsakar gidan shima yake kamar yadda ilahirin gidan yake,sumuntin tamkar ka zuba abinci a qasa kaci saboda wadatar tsafta.

   
    Tana tsayen har ya kammala bude gidan ya turo babur dinsa(lifan)samfurin companion,a tsakar gidan ya masa matsugunni gefe daya lokacin da take qarasowa gareshi tana ambaton "sannu da zuwa" fuskarta qunshe da murmushi wanda lokaci guda ya soma qoqarin gushewa daga fuskarsa sakamakon ganin fuskarsa sam babu annuri lokacin da yake amsa mata da "yauwa sannu da gida,na barki ke daya na tsaya gidan yaaya yahanasu"
"Eh nayi zaton hakan" ta fada tana sanya hannunta ta amshi jaka da ledar hannunsa jikinta a sanyaye tana qara cika da mamakinsa saboda sam ba haka ya sabar mata ba idan ya shigo gidan.

      Tana gaba yana biye da ita a baya tare da qare mata kallo,komai na sumayyarsa na burgeshi,har yau baya manta lokacin da ya aureta da qananun shekarunta wanda za'a iya kiranta qwaila,amma a ayanzun sai ka rantse ba sumayyar nan bace wadda ya aureta shekara shida baya da suka wuce.

   A falon ta barshi ta dawo tsakar gida tana hada mishi ruwan wanka zuciyarta na sake gaya mata akwai abinda yau ke damun mukhtar dinta,mutumin da ita ke tayashi shigowa da babur dinsa ta hanyar bude masa qofa da rufewa,da ya shigo zai rungume ta yana yaba kwalliyarta,a haka zasu qarasa falo,ko da ruwan wanka wani lokaci tare suke hadawa,bai barin bakinta ya huta idan ya dawo,gwanin tsokana ne da son sanyata dariya.

   Falon ta sake dawowa tana tsane ruwan hannunta,yadda ta barshi zaune haka tazo ta tarad da shi,bata ce uffan ba ta qarasa gareshi ta rage masa kayan jikinsa,shima bai tanka ba illa kallo da yake binta da shi har ta kammala ta miqa masa towel,karba yayi ya rataya a wuyansa sannan ya fice.

   Kafin ya fito har ta kammala jera abinci zuwa ruwan wanke hannu,dakinsa ya wuce kansa tsaye ya sanya jallabiya kana ya dawo cikin falon.

    Dukkaninsu jagula abincin kawai suke da cokulansu,damuwar data lura yana ciki ita ta hana mata sakewa taci abincin,duk da yunwar da take ji saboda bata iya cin abinci sai tare da shi,hakan ya sanya ko da rana ba don albarkacin yaran dake shigo mata ba wanda ta maida tamkar qannenta da ba zata dinga cin abincin rana ba,tana son tambayarsa amma bata son masa katsalandan,saboda shi da kansa yake sanar mata damuwarsa ba tare da ta kai ga tambayarsa ba,kasancewar ya maidata tamkar abokiyar shawara gareshi,sosai zuciyarta tayi ta kasa sukuni.

   A hankali ya daga idanunsa ya dora akanta sakamakon tuna a inda yake,sai yaji tausayinta ya kamashi,baiji dadin sanyata a damuwa ba,ga uwa uba yana hasashen nan gaba kadan zata iya shiga damuwar data linka wannan.

   Ajjiyr cokalin yayi yana qirqirar murmushi tare da kamo hannayenta ya riqe
"Lafiya qalau kuwa yau kike my sumy?" Cikin raunanniyar murya tana qoqarin maida qwallar data taru a idonta kasancewarta mace marason damuwa,kanta ta langabe cike da rauni
"Kai zan tambaya yaya mukhtar" ta qarashe fada muryarta na rawa,girarsa ya dage
"Me ya faru?" Qoqarin daidaita muryarta tayi
"Ban taba ganinka cikin damuwa yaa mukhtar irin haka ba,me ya faru da kai" kai ya girgiza yana sake qirqirar murmushi yana qoqarin azawa fuskarsa,don baisan ta ina zai fara sanar mata damuwarsa ba,ya tabbatar za tayi nauyi a qirjinta fiye da yadda tayi nauyi a nasa qirjin,bai da buqatar fadawarta damuwa ko kusa,sai gashi yaya yahanasu nason jefasu damuwa duka su biyun,sonta da tausayinta wani bangare ne mai girma a rayuwarsa
"Sumayyaaaaah" ya dan ja sunan nata yana kallonta
"Babu wani abu da yake damu na,gajiya ce kawai,matso maza kici abinci don na tabbata babu abinda kika ci" ya fada yana janyo plate din gabansa tare da zare nata cokalin ya fara juya abincin da iya nasa cokalin da alamu yana nufin ciyar da ita da kansa kamar yadda yake mata wasu lokuta.

   Kan ta ta girgiza idanunta cike da qwalla"ya mukhtar kayi haquri amma wlh ban yarda cewa baka da damuwa ba,bazan ci abincin nan ba har sai ka gayamin meke damunka"cokalin ya ajjiye kana ya sauke ajiyar zuciya,baya da nufin fada mata komai amma ya fuskanci idan baiyi wani abu ba zata qi cin abincin ne kuma ta kwana cikin damuwa saboda haka yace da ita
"Naji,zan gaya miki amma ba yanzu ba,kinga dare yayi sai gobe idan Allah ya kaimu,yanzun ki matso kici abinci tukun"
"Kayi alqawari?" Dariya ta bashi saboda yadda quruciyarta ta fito muraran sanda tayi maganar
"Eh nayi" ya fada shima.

    Ko da suka zo kwanciya haka ya dinga qoqarin boye damuwarsa,ya dinga qarfin halin aiwatar da duk wani abu da ya saba yi mata su don cire zargi daga zuciyarta da kuma son ganin ta sake,zamu iya cewa barcinsa kadan ne a daren ranar,cikin duhun dakin ya dinga juyi yana sake bitar maganganun da sukayi da yaaya yahanasu a wannin da suka shude dazu,yana cikin wannan tufka da warwarar bacci yayi awon gaba da shi.

    Washegarin ranar duk da maganar da sukayi daren jiya na maqale a zuciyarta tana mata yawo wanda ya haddasa mata wata kasala hakanan da mutuwar jiki saboda har wayewar garin damuwar dake fuskar sa bata bace ba,hakan bai mata tasiri ya hanata yin duka wata hidima ta gidan ta ba,wanda ya kama da tsaftace gidan kafin tashin mukhtar daga bacci,shirya abun kari da tanadar masa ruwan wanka.

     Yana tsaye bakin gado yana sanya links din hannun rigar shaddarsa,yayin da take gaban madubi tana shirya masa ragowar kudadensa da ya taho da su daga kasuwa da zai fita da su ya kaisu banki,hira suke jefi jefi duk da ba kamar yadda suka saba bane.

     Bayan ya kammala ya tako gaban madubin yana gyara zaman hularsa a kanshi,sumayya ta dubeshi cikin zuciyarta tana yaba kyawun da yayi,ya kula da ita saboda haka cikin salon tsokana yace
"Ki fito kawai kice na fiki kyau yarinya,sai wani satar kallona kike" sau tari idan ya fadi haka kunya da dariya yake bata,har ma wani lokacin musu ya dan kaure tsakaninsu,yau din ma dariyar tayi,maimakon ta biye masa auyi musun su na ta fishi kyau da iya kwalliya yadda suka saba sai tace
"Yaa mukhtar,yau ne fa sunan fiddausin" yanayin fuskarsa taga ya dan sauya,bai ce komai ba yana daura agogon hannunsa,har ta fidda rai tayi zaton ba zaya ce komai din ba sai taji yace
"Zaki je dinne?" Murmushi tayi saboda mamaki tambayar ta bata,fiddausi ai kamar diyarsa ce saboda 'yar yaya yahanasu ce,kuma shi da kansa ya bada kudin ankon sunan harda kudin dinkin ma
"Me zai hana yaa mukhtar,saidai idan kai ka hana" shiru ya sake yi har ya kammala ya dauki jakarsa ya rataya sannan ya sanya hannu cikin aljihun rigarsa ya fiddo da dari biyar ya miqa mata kudin cefane,sannan ya sake fitar da dubu daya daban yace mata kudin mota,ya sake bata wata dubu biyun yace ta baiwa mai jego barka,hannu biyu ta saka ta amsa tana jera godiya kamar yadda ya zame mata al'ada duk qanqantar alkhairin da zaya yi mata,tako masa tayi ta rakoshi har ya fidda babur dinsa waje tayi masa a dawo lafiya.

    Tana shirin mayar da qofar gidan ta rufe taga ya juyo
"Idan kika je kada ki dade,ki dawo gida da wuri,kuma bana son ki shiga cikinsu kuyita faman surutu" dan jim tayi saboda bai taba cewa hakan ba idan zata shiga cikinsu sai yau,amma sai ta share ta gyada kai kawai tace
"Insha Allahu".

    Qarfe sha biyu da arba'in ta kammala shirinta tsaf,tayi kyau cikin ankon sunan duk da cewa qaramar atamfa ce 'yar leda wadda kudinta bai wuce dubu da dari biyar ba,mayafinta takalmi da jakarta har sarqarta duka sun dace da atamfar,yau cikin yaranta ba wanda ya leqo,hakan baya rasa nasaba da ce musu da tayi zata unguwa ne gobe,yaran kusan tarbiyyarta ce,suna da hankali da nutsuwa,tsahon shekara shida suna tare suke debe mata kewa,sanda aka kawota unguwar ita din ma tana qwailarta,yaran basu wuce shekara biyu ba harda masu daya da rabi,ita ta dinga rainonsu,don karbo su take su wuni gurinta,iyayensu sun riqeta tamkar 'yarsu,don haka sabo da shaquwa ne tsakaninsu sosai.

   Gidan maman sadiya ta shiga saboda tahowa da nana yarinyar maman sadiya wadda zata rakata,duk cikin yaran yarinyar tafi shiga ranta,a kitchen ta samu maman sadiyan na dora girkin rana,nana anci kwalliya ana tsaye bakin qofar daki,hatta da takalminta na qafarta,cikin barkwanci suka gaisa da maman sadiya kana tac" ga mutuniyar nan,tun dazun ta addaba sai taje taga kin shirya,ni na hanata"dariya sumayya tayi
"Ai na gama sai tafiya" fatan dawowa lafiya maman sadiyan tayi musu kana suka fice.

     Qarfe daya da wasu mintina ta isa gidan,tuni har ya fara cika da jama'a kasancewar haihuwar fari fiddausin tayi,gaisawa ta dinga yi da duk wanda taci karo har ta dangana da dakin mai jegon,'yan uwan mukhatar ne cike da falo zuwa uwar dakan fiddausin,bata gajiya ba sai data bi ta gaida kowa,yayin da kowa ke amsa mata cikin mabanbantan yanayi,wani ya amsa mata ba yabo ba fallasa,wani ya amsa mata cikin shakulaton bangaro,yayin da wani bai amsawa ma sai an tabo shi ance ana gaidaka,duk hakan bai dameta ba saboda shekaru biyu kenan da fara fuskantar irin hakan daga garesu,mutum ce ita mai qaranta zargi qwarai a kan mutum,babu wani abu da suka taba ce mata face sauyin fuska kawai da take gani daga garesu.

    Cikin uwar dakan ta cimma fiddausi tare da yaya bara'atu wadda ita ke bin muktar sai mai bi mata fadima sai kubra 'yar yayan mukhtar,sai babbar 'yar yaaya yahanasu mansura,jaririyar ta dauka fuskarta qunshe da murmushi tana fadin
"Kai masha Allah,jariri akwai abun sha'awa"
"Hmmm,ku kam ba ruwanku da ita ko?"cewar fadima kafin tace wani abu yaaya bara'atu ta karbe zancen
"Nan da wata goma idan Allah yaso gidan mutari zamu suna,wannan karon kam shima Allah ya kusa kawo masa"
"Allah yasa"inji fadiman.

    Hakanan ta samu kanta da fargaba hadi da faduwar gaba,bata fita daga wannan yanayin ba maganar fiddausi ta katse mata zaren tunanin da ta fara qullawa
" au,ciki ne da sumayyan?"tabe baki yaya bara'atu tayi tana fadin
"Hmm,ina fa,yaaya yahanasu ke nema masa auren fa'iza" wata matsananciyar faduwar gaba ta saukar mata,jikinta yayi sanyi qalau,ta dinga jin zuciyarta na bugawa da sauri
"Alla ya sanya alkhairi" fiddausi ta fada tana kwashe rigunan barka na jaririyar daga kan gadonta tana lodawa cikin sif,hakanan take,baka fiya gane alqiblarta kan lamura ba.

    A hankali ta zame yarinyar daga cinyarta cikin kasala sakamakon shigowar 'yan suna cikin dakin,ta budr jakarta ta fito da dubu biyun da mukhtar ya bata ta miqawa fiddausin tana cewa
"Gashi,a siyawa baby turare" karba tayi tana fadin
"An gode".

     Duk yadda zancan ya daketa haka ta dinga dakewa tana yaqe,sam hankalinta ba'a kwance yake ba,qarfe hudu da rabi ta musu sallama don komawa gidan,ba wanda ya damu da tafiyar tata ballantana ya tambaya,sai data miqa nana gida sannan ta bude gidanta ta shigr.

    Kan kujerar falonta ta zube tana kiran sunan Allab,tayi a qalla awa guda tana saqa tana warwarewa,tabbas sauyin fuska da ta samu daga garesu yana da nasaba da rashin haihuwarta?,aure kenan mukhtar zai qara?,eh mana,dole mukhtar ya qara aure,'yana da buqatar ganin jininsa kamar yadda danginsa ke da irin wannan buqatar',abinda zuciyarta ta tunasar da ita kenan,ambaton sunan Allah tayi ta runtse idanunta,babu shakka don so tana son mukhtar,amma bata jin zata yarda ta zama silar batawarsa da yayarsa wadda take tamkar mahaifiya a wajensu,tasan halin yaaya yahanasu sarai,duk abinda ta quduri aniya sai ta aiwatar da shi,hana na nufin bashi da amfani tace zatayi adawa da abinda ta umarceshi.

    Cikin mutuwar jiki ta miqe don yin sallar la'asar tana istigfari,saboda lokacin ta da ya kusa qwace mata ba tare da ta yita ba,ko da ta idar ta jima zaune saman abun sallar tana addu'o'i sannan ta samu ta miqe,kitchen ta shiga,ta riga da tasan yau ta makara don haka bata da buqatar dora girki mai wuya saboda bata son mukhtar din ya dawo ya buqaci abinci bata kammala ba.

    Tana girkin tana saqe saqe,tana ta faman hada daya da daya,sai yanzu ta tabbatar cewa damuwar jiya da mukhtar ya shigo da ita bata rasa nasaba da wannan zancan kenan?,da gaske ne kenan auren mukhtar zai qara?,sai tasa tafin hannunta ta share qwallar da take zubo mata tana addu'ar neman agajin ubangiji,babu shakka qauna ce ta sanya mukhtar ya kasa gaya mata komai.

    Jallope din shinkafa tayi da kayan lambu saboda haka ana kiraye kirayen sallar magariba ta kammala,tuni dama tana da lemonta cikin dan qaramim fridge dinta wanda zobo ne da lemon tsamiya saboda mukhtar na sonsu musamman lemon tsamiya saboda maiqo.

    A gurguje tayi wanka ta hada da alwala,bayan ta kammala sallah ta shirya tsaf cikin qananun kaya wanda take siya cikin gumama da ake budewa bayan layinsu,sosai kayan suka yi mata kyau,sai ka rantse babu wani abu dake damun zuciyarta.

    Tana cikin yin turaren wuta taji bugun qofa,ta ajjiue kaskon ta zira hijabinta kana taje ta bude,Amrah ce 'yar maqotansu daya daga cikin yaran gidanta kenan riqe da kwanon samira a hannunta
"Anty yau duk bamu ganki ba,baki dawo daga unguwar da wuri bane?" Yarinyar ta tambaya tana murmushi,murmushin itama sumayya tayi
"Da wuri na dawo amrah,banajin dadi ne sosai yau"
"Allah sarki anty sannu" yarinyar ta fada cikin nuna alhini,sumayyan ta amsa mata tana karbar kwanon da amrahn ke miqo mata
"Gashi,dama mama ce tace na kawo miki dambu ne" murmushi ta sake yi tana cewa
"Ayyah ki cewa mama na gode,ashe bata manta da ni ba,jirani ina zuwa" ta fada tana shiga da kwanon ciki,alewa ta ciro guda biyu cikin jakar alawar 'yar dari da hamsin da take badawa ana siyo mata saboda yaran
"Ungo ki gaida mama da kyau" hannu biyu tasa ta amsa tana cewa an gode ta juya ta tafi.

    Tana shirin maida qofar ta rufe horn din mashin din mukhtar ya dakatar da ita,sai ta zare sakatar gami da bude masa qofar ta raabe daga can bakin qofar tana jiran shigowarsa.



*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

_bismilla hir rahmanir rahim_

*_qul ya ibadiyal lazina asrafu ala anfusihim la taqnad'u minr rahmatillah_*

_____________________


0⃣2⃣







Shi din ma a yau kallo daya yayi mata ya tabbar akwai abinda ya mata kutse cikin farinciki da walwalarta,sosai fuska da jikinta baki daya suka nuna gazawa da kasawarta,gabansa ya fadi saboda wani tunani da ya darsu cikin zuciyarsa,a hankali qirjinsa ya dinga bugawa.

Yarinya ce amma a dabi'unta sam ba zaka kirata haka ba,tana da halin manya da dattako da sanin ya kamata,sai tayi qoqarin cilla duk wata damuwarta gefe guda ta garbeshi yadda suka saba,a yau din ya sake sosai har ma yana tsokanarta,amma ta nan fannin sai ta samu kanta da gaza amsa masa,duk da murmushin yaqen da take ta qoqarin binsa da shi,wani abu ne cunkushe a qirjinta.

Tana ta kai kawon shirya masa abinci yana ta binta da kallo,babu shakka iya kula da miji ba wai mace mai karatun boko kawai ta iya ba,shi ya yadda da wannan,komai na sumayya a nutse yake,ba zaka taba tunanin bata taba shiga aji ba face ajinsa,shi ya koya mata yadda zata yi karatu da rubutu,rainonsa ce shi ya raini abarsa,ko motsi sumayya tayi yasan me yake nufi,hakan ya sanya a yanzu kallon da yake binta da shi karantarta yake,duk wani motsi nata na gaya masa akwai damuwa mai yawa cikin zuciyarta.

Hannunsa ya sanya ya ruqota lokacin da take duqe tana shirin zuba mishi abinci,sai ta dago idonta take idanunsu suka gamu,ko baiyi magana ba tasan meke yawo cikin idanunsa,sai ta narke qwalla ta cika idanunta,janyota yayi ta fada jikinsa ya rungumeta da dukka hannayensa,kuka ne ya qwace mata ba tare data shiryawa hakan ba,baice mata komai ba har sai da tayi mai isarta,ya fuskanci zuciyarta ta soma sanyi sannan yace da ita cikin murya mai sanyi
"Me ya faru my sumy,me ya sameki?" Cikin muryar kuka maganar na kakkatse mata saboda shishshiqar kukan dake kawo wa muryarta caffa
"Yaa mukhtar,yanzu saboda zakayi aure kake boyemin?,me yasa baka gayan ba ya mukhtar saidai na tsincin zancan a waje?" Shiru yayi wuta ta dauke masa lokaci guda,zancan da yake ta faman boye mata kenan,shi kansa cikin awanni kadan maganar ta dagulamasa dukka wata nutsuwa tasa,ina ga sumayyar tasa,ajiyar zuciya ya saki sannan yace
"Sumayya,bana son ki tada hankalinki kan wannan maganar,ni mukhtar a yanzu bana sha'awar qara wani aure,ke daya sumayya kin isheni,kuma babu wanda ya isa ya sani dole tunda ni zan zauna da ita".

Da sauri ta daga kanta daga qirjinsa tana dubansa tana kada kanta.

"Ko ba jima ko ba dade dole ya mukhtar sai ka qara aure,koda baka da muradi 'yan uwanka zasu tursasa ka,tunda na kasa samar musu da abinda suke da buqata,na kasa haihuwa....." Ta qarasa maganar kuka na sake qwace mata.

Da sauri ya sanya hannunshi ya rufe bakinta.

"Subhanallah,sumayya!,ina ilimin addininki ya tafi?,Allah kadai ke bada haihuwa kin sani na sani kowa ma ya sani saidai klwa ya take saninsa,to saboda haka babu wani sake auren da zanyi,mu barwa Allah lamuranshi har zuwa lokacin da yaga damar bamu".

Ta lura da gaske mukhtar yake ba zaya karbi auren da aka bashi ba,wanda hakan dai dai yake ya debo baqin fenti ya yaba mata a idanun 'yan uwanshi,a yanzun ma tana rakawa ne kawai da yanayin dangantaka da alaqarsu,ba zata iya tuna yaushe rabon da ta ga wani da ya jibanceshi a gidansu da zummar ziyara ba,kawaici kara da yakanarta ne kawai yasa bata dauki lamarin a bakin komai ba,ta riga ta sani ta kuma yi imani da shi shine dukkan tsanani yana tare da sauqi.

Ji take a jikinta wannan ce kadai dama ta qarshe a gareta da zata dawo da kyakkyawar alaqar da a da can baya take tsakaninsu

" ya mukhtar"ta kira sunansa,bata tsumayi jin amsarsa ba ta dora

"Don Allah da annabinsa kada ka yimin haka,kada kace ba zaka karbi auren nan ba"

"Sumayya,bana so kuma bazan karba ba,bana da buqatar qarin aure a yanzu haka,domin babu abinda na nema na rasa ga mata ta" ya fadi yana dubanta kansa tsaye,rasa me zata ce masa tayi

Please Login or Register in order to submit comment