Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kud'i na wajen ganin Son ya aure ki, toh ba dan komae bane se dan saboda wannan ranar da nake ta jiran zuwan ta, kuma gashi Allah ya kawo mu, saboda haka ki bud'e kunnen ki da kyau kiji abinda zance miki.." Da sauri da sauri k'irjin Azrah ke bugawa kamar ze fad'o, bata san sanda ta d'ago ido ta kalli Mami ba tana jiran taji abinda zata furta d'in.........



08124818273



✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION35*




___Mami ta gyara zama sannan ta kamo hannun Azrah ta sanya cikin nata ysannan ta cigaba da fad'in

"Kina ganin dae nima ina d'a koh? Amma komae baban su ya tashi yi toh fa ze mallaka wa Adnan ne, nasan zaki ce Fawaz k'arami ne ba ze iya kula da irin wad'an nan harkokin ba, toh ba gani ba? Se dae amma ya kasa fahimtar hakan, ya kasa fahimtar ni me iya kular masa da companynsa ne, ya k'yale wanda baya so dan kuwa Adnan sam baya son wad'an nan harkokin amma seda yasan yadda ya tursasa shi, toh yanzu ma gashi yana k'ok'arin sake bud'e masa wani companyn mallakin sa, abinda nake so dake indae kin san menene halacci, zaki rama alkhaeri da alkhaeri, kina so ku cigaba da watayawa ke da iyayen ki toh ki bi abinda zance miki idan kikayi hakan zaki cigaba da zama cikin gidan nan hankalin ki kwance.., zan aeko a kawo miki sak'o ki tabbatar kin bashi ya sha, karfa kiyi tunanin wani abin ne, a'ah kawae zamu taemaki kanmu ne kema ki taemaki kanki da iyayen ki dan kuwa dama nasan kema menene ya kawoki gidan nan, nasan kin fahimta ae.." A hankali Azrah ta shiga zame hannun ta dake cikin na Mami ta cigaba da kallan Mamin ido cikin ido, kafatanin jikin ta rawa yake yi sosae kamar mazari, ta riga da ta gama tsorata, kawae kallan Mamin take tana so ta tabbatar shin abinda take ji yana fitowa daga bakin Mamin gaskiya ne? Ko kuwa dae Mamin ta zare ne?, bata ida tunanin da take ba ta sake tsinto maganar Mamin na fad'in

"Ni zan koma, zuwa gobe zaki ga sak'on se kiyi yadda na umarce ki, sannan wannan ya zama sirri tsakanina da ke, muyi komae cikin sirri.." Daga haka Mami ta d'auki jakar ta ta fice daga cikin d'akin, Suman zaune tayi a wajen ta rasa ma wane irin tunani zata yi, kawae seta fashe da kuka ta jinginar da kanta akan kujera ta fara rerashi, haka duniyar ta zama? Inna lillahi wa inna ilaehi raji'un, ita kam ta gama tsorata da lamarin mutanen duniya, yanzu duk yadda Mami ke nuna masa ashe duk yaudara ce, ba k'aunar sa take har cikin zuciyar ta ba?, wannan wace irin rayuwa ce, shin ya kamata ta gasgata abinda Mamin ta fad'a ko dae ta bari taga ko zata farka daga wannan banzan mafarkin da take yi?, se ta sake fashewa da kuka kawae har lokacin jikin ta be bar rawa ba, girkin da bata k'arasa ba kenan dan kuwa bata da wannan k'warin gwuiwar, kae gaba d'aya ma ta manta da wani girki da take yi....




___Sameer ya saci kallan sa a kaekaece yace a hankali

"Ina zamuje?" Ba tare daya kalle shi ba yace

"Kwanar ganduje" Sameer be sake cewa komae ba kawae ya cigaba da driving d'in har suka isa unguwar, Don ke nuna masa inda zasu shiga har suka k'arasa wani madaedaecin layi, Sameer yayi parking k'ofar wani d'an k'aramin gida, Simrah ta kalli inda suka shigo d'in tana mamakin ko ina ne nan d'in?, Don ne ya fara fita daga cikin motar sannan Sameer ya fita, Don ya d'aga waya yayi kiran wani, bansan me suka ce ba naga dae ya maeda wayar cikin aljihun sa, Sameer ya kalle shi yace

"Amma ina ganin kada ka d'auki hukunci da kanka, zefi kyau mu bar hukuma tayi aekin ta, ko mu sanar da Dad nasan baze kasa sanin yadda za'ayi dasu ba.."

"Noo, zan iya yin komae da kaena pls" Sameer ya d'aga kafad'a be sake cewa komae ba. Suna nan tsaye wajen mintuna 10 sega wani ya shigo layin cikin napep, ya k'arasa suka gaesa dasu sannan ya mik'awa Don mukulli kana sukayi sallama ya tafi, Don ya k'arasa ya bud'e k'ofar sannan ya juyo ya kalli cikin motar, ganin haka ya sanya Simrah fitowa tana wani murmushin jin dad'i, tana tunanin ko abinda take buk'ata ne yau ze kasance tsakanin ta da Don d'in, amma daya sani ya fad'a mata ta d'an gyara jikin ta ko yaya ne ( ni kam nace zaki ga gyara dae_dae gwargwado😹 ), Don ne a gaba se Sameer sannan Simrah har suka k'arasa wani d'an madaedaecin d'aki suka shiga, tabi bayan su ta k'arasa taja wata kujera ta zauna tana cire mayafin jikin ta fad'i take

"Washh zafi" ta fad'a tana kallan cikin d'akin, kenan a wannan d'an k'aramin gidan zasu shana? Memakon ya samar musu wani had'ad'd'en gidan ko kuma hotel, koda yake nan d'in ma ta gode, ba wanda ya kalle ta a cikin su, wajen sec30 Don ya kalle ta yace a tak'aece

"Ur phone" seta saki wani fari kana ta d'auki wayar ta mik'a masa, bece komae ba ya fita, Sameer ya kalle ta yana danne dariyar dake cinsa yace

"Bari mu d'an samo wani abinda zaku ci" Simrah tace

"Aekuwa kamar kasan yunwa nake ji, amma gidan babu A.C ne? D'akin akwae zafi" Sameer ya d'auke kan sa daga kanta gudun karya saka dariya yace

"Ehh bari mu dawo se a kunna gen" daga haka ya fice daga d'akin... Yana fitowa Don ya saka mukulli ya kulle k'ofar ruf sannan ya koma cikin mota, Sameer y kalle shi yace

"Meye manufar hakan?" Ba tare daya kalle shi ba yace

"So nake tayi laushi kafin na dawo, yunwa nake ji, zan dawo na tuhume ta anjima" Sameer ya kalle shi yace

"Uhmm uhmm fa, kada ka manta da er mutane fa" Don ya ta6e baki sannan yace

"Noo, ba zan manta ba.."

"Ohk, kabi komae dae a hankali" Sameer ya fad'a na jan motar....




.....Ta shafe fiye da awa d'aya a zaune kan kujerar tun tana kukan harta gaji se sheshshek'a kawae take yi, se dae gaba d'aya hankalin ta yana wani wajen, ta rasa yadda zata yi da wannan al'amari... Yana gama parking d'in motar ya k'arasa shigewa cikin d'akin, tana zaune a takure cikin kujerar tayi lamo se sauke ajiyar zuciya take yi, yayi kamar be ganta ba kawae ya wuce saman yayi wanka ya shirya sannan ya sakko, ga mamakin sa har lokacin tana nan inda ya bar ta, se ya saci kallan inda take d'in sannan ya wuce kan dinning d'in ya zauna, babu komae akae, seya sake kallan inda take sannan ya lumshe idanun sa yana neman waje ya zauna, ta k'ara wajen minti 5 sannan ta mik'e a hankali jiri na d'iban ta ta fara takawa dan hayewa saman, idanun ta suka sauka kan dinning d'in sanda yake kallan ta, jirin da take ji ya k'aru, "yaushe ya shigo kenan?" ta tambayi kanta, tsaki yaja yana d'auke kan sa, sum sum sum ta haye saman ba tare data sake kallan sa ba, mamaki ne ya kamashi ganin gata nan lafiya k'alau amma bata girka komae ba? Ko rashin kunya take tak'ama dashi ne?, ya sake jan tsaki kawae ya koma saman ya d'auki key d'in motar sa ya fice daga gidan, bashi ya dawo gidan ba se can dare gaba d'aya yama manta da wata Simrah, yana dawowa yayi wanka sannan yabi lafiyar gado...




___Wajen k'arfe 10 ya farka daga bacci, ya bud'e idanun sa kana ya tashi zaune, se a lokacin ya tuna da wata Simrah daya ajiye a wani gida, ya sakko daga kan gadon ya fad'a toilet yayi wanka sannan ya fito ya shirya ya d'auki mukullin motar sa ya sauko, ya kalli dinning area yaga akwae abinci akae, bebi ta kansu ba kawae ya fice daga gidan dan kuwa Allah Allah kawae yake yi yaji dalilin Simrah nayi masa haka..... A 6angaren Simrah kuwa data ga sun fita seta tashi ta nemi toilet tayi wanka kana ta fito ta maeda kayan jikin ta, tana tunanin data sani ta taho da kayan baccin ta, se dae tafiyar ce tazo a bagatatan shiyasa, ta nemi waje ta zauna tana jiran dawowar su, tun tana zaune harta mik'e ta lek'a tsakar gidan har lokacin dae shiru, a'ah wasa wasa har gari ya fara duhu amma shiru babu su babu alamun su, seta k'arasa wajen k'ofar ta ta6a, ga mamakin ta seta ji ta a kulle gam gam, kawae seta sake komawa cikin d'akin tayi shiru k'irjin ta na bugawa, kaddae ace yau ma shashanci ta aekata, kodae tarko suka d'ana mata? In kuwa hakane lallae sun shammace ta dan kuwa bata ta6a kawo hakan ba, bata sake gasgata hakan ba seda taga duhu yayi sosae gashi babu haske ga zafi ga kuma wasu sauraye da suka fara dabdala akanta, ga yunwar da take ji, kawae seta fashe da kuka tana fad'in

"Amma Allah ya isa tsakani na daku wallahi" ta fad'a tana kaewa wani sauro daya hau kan k'afar ta duka, tana nan zaune sauro kamar ze kashe ta ga k'arin zafi, ga kuma duhu gaba d'aya tsoro ya cika ta ta kasa bud'e ido ma, ga wata mahaukaciyar yunwa da take ji, ranar dae ba dan bacci 6arawo bane da babu ita babu rintsawa, se dae tana cikin baccin zata farka firgigit, ga dad'in sauraye da aka samu, da sassafe kuwa ta farka ta sake ganin ta cikin gidan seta cigaba da kukan ta kawae, ba tare da ta tashi tayi sallah ba, can ta sake komawa ta ta6a k'ofar gidan ta sake jin ta a kulle se kuwa ta sake fashewa da kuka... Yana zuwa k'ofar gidan ya saka mukulli ya bud'e k'ofar sannan ya shiga yaja k'ofar, tana zaune a tsakar gidan ta mak'ure waje 1 kamar shege a rabon gado, ya bita da wani wawan kallo sannan ya k'arasa ya zauna akan rijiyar dake tsakar gidan, da sauri ta bud'e ido jin alamar motsin mutum tana kallan sa seta sake fashewa da kuka tana girgiza kae take fad'in

"Meyasa kamin haka? Don Allah ka maedani gidan mu.." Babu ko alamar tausayi a fuskar sa yace

"Meyasa kika so 6atamin suna?" Seta girgiza kae tace

"Ni bani bace.."

"Well, seki cigaba da zama a cikin gidan har lokacin da zaki yi laushi" ya fad'a yana mik'ewa ze fice daga gidan, tayi saurin mik'ewa tana fad'in

"A'ah dawo don Allah, wallahi nice, kuma ni ba dan na 6ata maka suna nayi hakan ba, nayi ne dan in sanar dakae abinda baka sani ba saboda ina sonka.." Don ya sake had'e fuska sannan yace bayan ya zauna

"Zaki cigaba da zama a gidan nan har se lokacin da wawiyar zuciyar ki zata sena tunanin sona, har kuma lokacin da zaki fita a rayuwa ta ki dena k'ara tunanin yimin kutse a cikin ta, idan ba haka ba wallahi inyi miki abinda har abada ba zaki manta dani ba, kuma har abada ba za'a sake miki koda makamancin irin wulak'ancin da zan miki ba, kada ki bari in nuna miki other side of me, ki bini a hankali yadda nake k'ok'arin bin ki" ya k'arasa fad'a yana ajje numfashi saboda tsayin maganar da yayi, Simrah ta sake kallan sa sannan tace

"Wallahi kome nake yi soyayyar ka ce ta jawo, ina son ka har abada" Hannu ya d'aga kamar ze kae mata mari se kuma ya fasa ya runtse idanun sa yana jin kamar ya tashi yayi ta bugun ta, wajen sec30 ya bud'e idanun sa yace

"Ba zaki dena ba kenan?" Simrah tace

"Son ka ne ya jamin koma mena aeka ta, kuma ina son na taemake ka ne bawae dan na 6ata maka suna ba"

"Taemako?" Ya fad'a akan la66an sa, se dae saboda shi Simrah take kalla yasa taji abinda yace dan haka tace

"Ehh wallahi taemakon ka zanyi, nasan baka san cewa matar daka aura tsintacciya bace aka rufe aka baka ita a haka, kuma sannan bazawara ce ita aka ninke ka a bae_bae, idan ba dan ina son ka ba ta yaya zan binciko maka wannan abin da baka sani ba?" Dafe kan sa yayi yana jin yadda yake sarawa kamar ze fad'o

"Tsintacciya, bazawara" be san dalilin da yasa ya tsani jin wad'an nan kalmomin ba, kawae seya mik'e ya fice daga gidan ya sake saka mukulli ya hau motar sa ya bar layin a fusace, ita kuwa Simrah ta zube a wajen tana kuka hadda birgima, yau ta shiga 3 ta lalace, meye mafita a wajen ta ita kam?.



....Mami ta k'araso cikin parlourn ta zauna tana kallan Hajja kaltum tace

"Sannun ki da zuwa"

"Yawwah sannu kadae Hajiya, na same ku lafiya?" Mami tace

"Alhamdulillah" Hajja kaltum tace

"Yawwah toh gani dae nazo koh?" Mami tace

"Ehh, kina jin abinda za'ayi ki tafi dashi seki bawa Azrahn, amma kada ki fito daga gidan sekin tabbatar ta bashi shayin sannan seki fito" Hajja kaltum tace

"Kada ki wani damu Hajiya, ni nasan ma ba zata ta6a bijirewa umarnin mu ba, mutuniyar da muka taemakawa? Muka tsamo ta daga cikin halin da take na k'unci zuwa jin dad'i?, zancen tak'i amincewa ma ae be taso ba"

"Dukda haka dae ki jira ta bashin" Hajja kaltum tace

"Toh shikenan karki damu" Daga haka suka mik'e zuwa compound d'in gidan, Mami ta saka driver ya d'auki Hajja kaltum zuwa gidan Azrah, ita kuma ta koma cikin d'akin, tana komawa ta samu wayar ta na ringing, ta k'arasa ta d'auka sannan ta kara ta a kunne, daga can 6angaren Momy tace

"Hadeeza don Allah ina Adnan?" Mami tace cike da mamaki

"Adnan na gidan sa mana" Momy tace

"Gidan sa kuma? Kinga fa tun jiya suka fita da Simrah amma har yanzu basu dawo ba" Mami dae mamaki ya sake kashe ta, toh meye had'in Simrah kuma da Don?, Momy tace

"Hadeeza kina tare dani?" Mami ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Ae na kasa gane abinda kike nufi ne, Adnan, Simrah, meye had'in su?" Momy tace

"Toh duk abinda dae kike k'i seya kasance saboda haka ma ki saka ranki a inuwa dan kuwa jiya har gida yazo ya d'auke ta suka fita.." Mami ta nemi waje ta zauna tana jin abinda Momyn ke fad'a, Momy ta katse mata tunani da fad'in

"Don Allah ki kira min shi, koma wace magana ce mayi daga baya" Mami tace

"Ohk" tana katse wayar ta lalubo number Don ta kira, kira har 2 tayi masa taji wayar tasa a kashe, kawae seta ajje wayar tana zagaye d'akin da mamaki fall cikin ranta.



......Da sallama Hajja kaltum ta shiga parlourn tana bin ko'ina da kallo, Azrah ta fito daga cikin kitchen tana kallan me sallamar haka kawae taji fad'uwar gaba ta same ta haka dae ta daure ta k'arasa tace a hankali

"Sannu da zuwa" Hajja kaltum tace

"Yawwah, ina fatan kin gane wacece?" Ta fad'a tana neman waje ta zauna, Azrah ta girgiza kae kawae, Hajja kaltum tace

"Toh daga wajen Mami ne, sak'o ne daga wajen ta.." A take bugun zuciyar Azrah ya k'aru, Kafin tace komae Hajja kaltum tace

"Kin gama girkin ne?" Seta girgiza kae da sauri, Hajja kaltum tace tana kallan ta sosae

"Meyasa?" Seta lumshe idanun ta sannan ta bud'e tace

"Yace yau ba zeci abinci ba"

"Aou kenan yana cin abincin ki?" Kawae se tayi shiru ta rasa amsar da zata bayar

"Toh ko shayi ne ki dafa masa nasan zeji dad'in sa" Azrah ta d'aga ido ta kalle ta ba tace komae ba ta sake maeda shi k'asa, Hajja kaltum tace

"Tashi muje kitchen d'in, ke se ayi ta magana kiyi shiru" se ta mik'e a hankali tana jin yadda k'walla ke sake tarar mata a cikin idanun ta, haka suka k'arasa kitchen d'in, Hajja kaltum ta d'auko komae na shayin sannan ta kalli Azrah dake tsaye tace

"Ki d'ora mana" kar6a Azrah tayi hannun ta na rawa ta d'ora shayin, suna tsaye a kitchen d'in har ya dahu sannan Hajja kaltum ta k'arasa ta bud'e ta zuba wani abu dake cikin wata er k'aramar kwalba sannan ta kalli Azrah tace

"Ki kwashe koh?" K'arasawa Azrah tayi kanta a k'asa dan lokacin hawayen data ke ta rik'ewa sun riga da sun sauko kan kuncin ta, ta kwashe shayin a cikin wani d'an k'aramin tea flask sannan suka fito daga kitchen d'in, flask d'in na hannun Hajja kaltum ta k'arasa ta ajje kan dinning sannan ta dawo cikin parlourn ta zauna, Azrah dake zaune kan kujera idanun ta da hankalin ta gaba d'aya na kan flask d'in ne, tayi shiru tana jira Hajja kaltum ta mik'e dan tafiya, amma taji shiru har zuwa wani lokaci daya shigo cikin gidan, ya k'araso cikin parlourn, Hajja kaltum na ganinsa ta fad'ad'a fuskar ta da murmushi tace

"Sannu da zuwa d'an gidan Mami" kallo d'aya ya mata ya d'auke kae yana cigaba da tafiya yace

"Kina lafiya?" Tace

"Lafiya k'alau nake, ya aekin?" Shi dae tuni ya wuce abinsa, Azrah ta samu kanta da binsa da kallo cike da tausayawa, suna nan zaune ba wanda ke cewa wani uffan, dan daga farko Hajja kaltum ta fara jan ta da hira da taga dad babu fuska kawae seta kama kanta, bayan minti 25 se gashi ya sauko, kafin ya gama saukowa Hajja kaltum ta mik'e tana yafa mayafin ta tace

"Toh ni bari na tafi.." Ta fad'a dae_dae sanda ya k'arasa yaja kujera ya zauna yana kallan flask k'waya d'aya dake kan dinning d'in, Hajja kaltum ta saci kallan sa sanda yaja flask d'in tace

"Toh ni na tafi se anjiman ku" Ita dae Azrah ba tace komae ba dan gaba d'aya hankalin ta na kan sa ne, seda ta tabbatar ta fita daga d'akin sannan ta maeda duban ta kansa sanda ya tsiyaya tea d'in dake ta tashin wani k'amshi cikin wani k'aramin cup, kawae seta maeda akalar tafiyar ta zuwa dinning area d'in, ta tafi cike da sassarfa jikin ta na rawa ta k'arasa, dae_dae lokacin daya kae cup d'in bakin sa, cikin azama ta sanya hannun ta dake rawa ta tunkud'e cup d'in daga hannun sa, hakan ya bawa cup d'in damar fad'uwa k'asa ya tarwatse, shi kuma tea d'in ciki ya zuba akan dinning d'in da kuma jikin Don..............



08124818273



✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION36*




___Mik'ewa yayi da sauri ya karkad'e rigar sa yana kallan yadda shayin ya zuba a jikin sa, se kuma ya d'aga idanun sa cike da mamaki ya kalli inda take tsaye, cigaba da kallan nata yayi ganin yadda tayi k'asa da kae kamar ba ita ta aekata abinda tayi yanzun ba, ransa ya sake 6aci ya kalle ta da idanun sa da suka fara sauya kala yace

"Are u insane?" Shiru tayi jikin ta babu abinda yake se rawa amma ta gwammace ta jure ko wanne irin magana ko cin mutuncin da ze fad'a mata data, da dae ayi kisa a gaban ta kuma da sanin ta, kafin da gama tunanin da take ta sake jiyo muryar sa yana fad'in har lokacin cikin zafi

"Meye hakan kika aeka ta?, Ko kinyi hauka ne?, Kamar nace miki bansan ganin fuskar ki? ki tabbatar kin kammala duk abinda zakiyi kafin nazo wajen nan? Shine dan ki nuna min baki da kunya kin k'i bin hakan koh?, Saboda ma raenin naki yayi yawa..a'ah toh wae ma meya shiga kanki ne da zaki min wannan haukan?" Ya k'arasa maganar cikin d'aga murya, seta runtse idanun ta kafin a hankali ba tace komae ba ta bar wajen da sassarfa tana jin yadda hawaye ke sintiri akan kuncin ta, yau kam tayi dana sanin abinda ta aekata, data sani ta barshi ya sha shayin ko mene ze faru dashi ya faru, daga yau kam anyi an gama, har abada ta gama shiga harkar sa tunda shi haka yake be san mutuncin ba kullum cikin rashin kirki yake, seya samu kansa da binta da kallo sanda take k'ok'arin wucewa d'in, lumshe idanun sa yayi yana so ya tariyo abinda ya fad'a d'in, haka kawae yaji kamar be kyauta ba, seya bud'e idanun sa yana jan siririn tsaki, "wacece ita dan ya fad'a mata magana zeji kamar be kyauta ba?" Ya fad'a a k'asan ransa, Bin cup d'in daya tarwatse a k'asa yayi ya sake kallan jikin sa yana mamakin dalilin ta na yin hakan "yarinta mana" wata zuciyar ta bashi amsa, se kawae ya haye saman maganar Simrah data kasa barin sa tun d'azun na dawo masa cikin kunnen sa, ya rasa gane dalilin da yasa "er tsintuwa kuma bazawara" ya kasa fice masa a rae, ko yaya yayi shiru se kalmomi biyun nan sun fad'o masa. Yana shiga d'akin wayar sa ta fara k'ara, ya nemi waje ya zauna sannan ya kara wayar a kunnen sa, daga can 6angaren Mami tace

"Barka Son.." yace

"Barka dae Mami"

"Yawwah, ya aekin? Ya matar taka?" Ta fad'a tana mamakin jin ya d'aga wayar, bayan Hajja kaltum ta tabbatar mata ya sha shayin nan, ya d'an lumshe idanun sa kad'an sannan yace

"Mami.." tace

"Na'am Son" shiru yayi kad'an kana yace

"Shikenan?" Tayi murmushi kawae sannan tace

"Ina Simrah ne?" Yayi d'an jim kad'an sannan yace ransa a had'e

"Meye had'i na kuma da me wannan sunan?" Mami tace cike da mamaki

"A'ah, akace kuma tare kuka fita tun jiya?" Ya cije lips d'in sa na k'asa sannan yace

"Kuma kika yarda Mami?, Ban ma gane wace me sunan ba!" Mami ta sauke ajiyar zuciya kafin tace

"Toh shikenan, Nima dama nayi mamaki, kana lafiya dae koh?" Yace

"Ehh Mami" Mami tace

"Toh madallah" daga haka ta katse wayar, kafin ta ajje wayar ta danno number Hajja kaltum ta kira ta tana d'agawa tace

"Kika cemin ya sha shayin nan?" Hajja kaltum tace

"K'warae kuwa, wani abun akace miki ya faru?" Mami tace bayan ta sauke ajiyar zuciya

"Toh be sha ba"

"Inji waye?" Hajja kaltum ta tambaya da mamaki, Mami tace

"Bar wani maganar inji waye, yanzun muka gama waya dashi lafiya k'alau wallahi" Hajja kaltum taja tsaki sannan tace

"Ke kam Hajiya hadeeza ba dae gajen hak'uri ba, ae ya kamata ace kinbi komae a sannu koh?" Mami tace

"Anya kuwa?"

"Wallahi kuwa Hajiya" Mami ta sauke ajiyar zuciya sannan tace a sanyaye

"Toh shikenan"



......Mami na zaune parlour ita da Fawaz suna kallo sega sallamar Momy, dukkan su suka amsa suna kallan Momyn data shigo duk a hargitse, Mami ta mik'e tana kallan ta tace

"Subhanallahi, lafiya kuwa?" Momy tace fuskar ta da alamar alhini

"Ina fa lafiya, don Allah maza kae ni wajen Alh Kabeer" Mami ta cigaba da kallan ta sannan can tace

"Ki zauna ki fad'amin meya faru mana?" Momy tace

"Taemaka ki fara kaeni don Allah, akan rashin ganin Simrah ne tun jiya" Kallan ta Mami ta cigaba dayi kafin daga bisani ta kalli Fawaz dake kallan su tace

"Kayi zaman ka" daga haka suka fice daga d'akin, Mami a gaba yayin da Momy ke bayan ta, a haka har suka k'arasa part d'in Dad, dab da zasu shiga Mami ta dakata tana kallan Momy tace

"Amma kya dakata na fara shiga koh?" Momy bata tanka mata ba amma ta dakata d'in, Mami ta k'arasa cikin parlourn da sallama tana kallan Dad dake kallan labarae a France 24, ya juyo ya amsa sallamar ta ta sannan ya d'auki remote ya rage volume, Mami ta nemi waje ta zauna da murmushi kan fuskar ta tace

"Sannu da hutawa yalla6ae" Dad yace

"Yawwah sannu ka dae"

"Ina fatan dae ba wani abun kake ba, saboda kayi bak'uwa ne" Dad ya kalli Mami sosae kafin yace

"Bak'uwa kuma?" Mami tace

"Wallahi kuwa, Maman Simrah ce tazo wajen ka.." Dad ya sauke ajiyar zuciya kafin yace

"Toh Allah yasa lafiya, fad'a mata ta shigo" Mik'ewa Mami tayi zuwa wajen, bayan wajen minti 1 se gasu sun shigo tare, Mami ta k'arasa ta zauna kan kujera yayin da Momy ta nemi side chair ta zauna suka gaesa da Dad sannan tace

"Wato ranka ya dad'e magana ce akan er waje na, tun jiya Adnan yazo suka fita tare amma har yanzu basu dawo ba, na fad'awa Hadeeza akan ta kiramin shi amma har yanzu shiru, shiyasa kawae nace gwara nazo wajen ka" Da mamaki sosae Dad ke kallan Momyn har ta k'are bayanin ta kafin yakae ga cewa komae ya tsinto muryar Mami na fad'in

"Na kira Son fa, ya fad'a min bema san zancen ba shiyasa kika jini shiru" Momy tace

"Wallahi da idanu na nagan shi, tare suka fita fa don Allah yalla6ae ka

Please Login or Register in order to submit comment