Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anan d'in baze yiwu ba sannan ya d'auke ta gaba d'ayan ta zuwa cikin bedroom d'in, daga nan dae ya cigaba da nuna mata how much he missed her, dama kukan da tayi d'azun be ishe ta ba dan haka yanzun kam ta saki jiki ta dinga zuba kukan shagwa6ar ta ta, shi kam ya rungume ta cikin jikin sa yana rarrashin ta kamar yarinyar goye, wannan shagwa6ar ta ta burge shi take yi sosae, sedae bata san idan tana yi d'in sake shagaltar dashi take yi ba, bashi ya sauke ta daga jikin sa ba se dab da asuba sannan ya janye ta daga jikin sa ya kwantar da ita kana ya bata light kiss a goshin ta ya fad'a toilet ya had'a ruwa sannan ya fito ya kalle ta yace bayan yayi k'asa da kansa yana kallan idanun ta masu kyau

"Zaki iya tashi kona d'auke ki?" seta d'aga idanun ta ta d'an kalle shi a fuzge sannan tace a hankali

"A'ah zan iya"

"Ohk tohm tashi na had'a ruwan wankan" ya fad'a cikin rarrashi, seta lumshe idanun ta sannan ta bud'e bayan ta juya baya tace tana tura baki

"Ni a'ah seka fita zan yi" agogon d'akin ya kalla ganin idan ya cigaba da biye mata ze makara ya sanya shi yin murmushi ya wuce toilet.. Har ya gama shiryawa tana kwancen kamar me bacci ya kalle ta kawae sannan ya fice daga d'akin.. Seda ta k'ara wajen minti 5 bayan fitar tasa sannan ta mik'e ta fad'a toilet d'in tayi wanka ta fito, se a lokacin ta tuna hijab d'in ta na parlour dan haka ta k'arasa k'ofar, tana k'ok'arin fita daga d'akin ya shigo, seta koma baya da sauri ta d'auki kayan ta, tana shirin shiga toilet d'in yace

"Wallahi kika shiga sena biyo ki" ya fad'a yana zube mata narkakkun idanun sa, se tayi rau rau da idanu ba tare data kalle shi ba tace

"Toh ka fita na saka kaya mana" seya k'arasa ya kwanta kan gado yana fito da wayar sa ya kwanta sannan yace

"Ki saka kayan ki ni waya ta nake dannawa" ya fad'a shima ba tare daya kalle ta ba, seda ta tabbatar da gasken wayar yake dannawa sannan ta sanya kayan nata kana ta fita parlour ta d'auki hijab d'in ta ta dawo cikin d'akin tayi sallah, komae take binta yake yi da kallo yana jin kamar ya maeda ta ciki saboda k'aunar ta.... Har wajen k'arfe 7 tana cikin d'akin ta kasa zuwa ko nan da can, gani take kamar tana fita waccan Aleenahn zata shigo ta kawo masa break, dan haka ta cigaba da zama a d'akin duk da yadda yake ta binta da idanu amma haka ta jure tayi zaman ta, shi kansa mamaki ne ya kama shi amma hakan ba k'aramin dad'i ya masa ba, suna nan zaune kiran Aunty Hindu ya shigo wayar sa, ya kalle ta sannan ya mik'e ya fito daga d'akin zuwa parlour, seda suka gaesa sannan Aunty Hindu tace

"Da alama dae matar ka tayi fushi dani koh?" ta fad'a tana er dariya dariya, shima murmushin yayi sannan yace

"A'ah muna jiran dae a kawo mana break ne"

"Waye ze kawo muku?" Aunty Hindu ta fad'a tana rik'e ha6a, se yayi murmushin gefen baki sannan yace

"Ko Aleenah ce.."

"Wa...rufa min asiri don Allah, haka kurum kasa nayi bak'in jini a wajen sirika ta.."

"Bak'in jini kuma?"

"Ehh mana, kaga idan zaka zo ka kar6ar muku toh yanzu zan aeko faruk ya kawo muku k'ofar part d'in seka kar6a, amma babu ruwa na da maganar ku daga yau, dan Aleenah ta fad'a min jiyan nan ko magana bata mata ba" ya d'an yi murmushi kad'an sannan yace

"Oh..k" daga haka ya katse wayar... Tana zaune kan gadon ya turo k'ofa ya shigo d'akin hannun sa d'auke da kayan karin nasu, seta d'aga kae ta kalle shi, haka kurum taji wani abu ya d'arsu a ranta, haka kuma idan ta had'a yadda aka kira shi a waya ya fita yanzu kuma gashi ya dawo da abinci a hannun sa se taga hakan ya bada wata ma'ana daban, seta d'auke kae tana jin wani irin bak'in ciki na tokare ta a mak'oshi, ita gaba d'aya ma wannan k'asar ta ishe ta, ta k'agu taga sun koma k'asar su, ya k'arasa ya ajje k'asan carpet sannan ya mik'e ya matso kusa da ita yace yana kallan ta

"Taso kici abinci!"

"Waye ya kawo?" tambayar data ke mata yawo kenan a cikin k'wak'walwa har bata san sanda ta furta ta a fili ba, ya k'ura mata idanun sa sannan ya lumshe su a kanta yace

"Faruk.."

"Aleenah ce.. Ae dama naga sanda ta kira ka har ka tashi ka fita, nika saka ni ko a mota ne na koma gidan mu.." ta fad'a idanun a rufe tana jin wani kuka na taho mata, seya k'arasa inda take ya rik'o hannayen ta ya kalle ta yace

"Wae ke kam kuka baya miki wuya ne? Baki san bakya kyau ba idan kina kuka ba? Idan kuwa kina murmurshi se naga kinfi kowacce mace kyau a fad'in duniyar nan" ya fad'a yana jin dad'in yadda take nuna kishin sa a fili, amma ita da alama bata san tana yin hakan ba, seta d'aga kae ta kalle shi, ya jinjina mata kae alamar tabbatarwa fuskar sa d'auke da sassanyan murmushi, seta d'an saki murmurshi me had'e da kukan dake taho mata, ya lumshe idanun sa kana yace

"Aunty Hindu ce ta kira ni, idan kuma baki yadda ba ga wayar nan ki duba.." ya fad'a yana mik'a mata wayar, seta bi wayar da kallo sannan ta d'auke kae ta maeda shi k'asa, duk kuma se taji kunya ta kama ta, wae ita kam mene yake shiga kanta ne a kwanan nan, me take aekatawa hakane? Ya karanci tunani take yi dan haka ya cigaba da kallan kyakykyawar fuskar ta, har zuwa sanda ta d'ago idanun ta, se a lokacin ya furta

"Sakko kinji?" babu musu yanzu kam ta sakko, shi yayi serving nasu a plate d'aya, sedae ta kasa ci ita kawae ta cigaba da kallan abincin, ya saka mata cokali sannan yace

"Ci..ko na baki da kaena?" d'aukar cokalin tayi ta fara ci a hankali, seda ya tabbatar taci d'in sannan shima yaci... Ba ita ta bar d'akin ba se wajen 11 se kuma a lokacin taji kunya duk ta kama ta yadda zata ratsa cikin parlourn ta wuce su tunda ae kowa yasan daga inda take, haka dae tayi shahada ta shiga parlourn, cikin sa'a kuwa yaran ne kad'ae a cikin d'akin, seta wuce su zuwa cikin bedroom d'in tana sauke numfashi, d'aga idon da zatayi se taga Aunty Hindu tsaye cikin mayafi da jaka a hannun ta da alama fita zatayi, kanta a k'asa ta k'arasa ta zauna gefen gadon sannan kamar zata saka kuka tace

"Ina kwana?"

"Lafiya k'alau Azrah, kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah" kawae ta iya furtawa tana sake addu'ar Allah yasa karta kuma mata wata tambayar bayan wannan, aekuwa bata sake cewa komae ba harta kammala abinda take cikin d'akin sannan tace

"Toh ni na fita"

"A dawo lafiya" ta fad'a tana sauke numfashi... Tun daga ranar ya kasance tana kula da duk wani motsin Aleenah, sedae ga mamakin ta bata sake ganin Aleenahn na shishishige masa ba, amma duk da haka idan aka gama girki zata tasa d'aya daga cikin yaran zuwa part d'in da yake suje ta tsaya a bakin k'ofa shi kuma yaron ya kae masa sannan su juyo, dan haka kawae take jin kunyar en gidan, ba zata sake kuskuren kwana inda aka sauke shi ba, Aunty Hindu tayi mamakin ganin yadda ta chanja d'in, amma se taji dad'i ko ba komae hakan ya nuna tana k'aunar d'an nata, shima kuma hakan be masa ciwo ba yadda ta dena shigowa sashen da yake ba dan tun daga ranar kullum da safe suke fita shida Aunty Hindu kuma basa dawowa se dab da maghrib, idan suka dawo kuma ze wuce sashen Papi ne su d'an ta6a hira duk da shi ba gwanin ta bane.. Ranar da Dad ya jewa da Papi zancen tafiyar su zuwa gobe ko jibi idan Allah ya kaemu se Papin ya shigar masa da zancen da yake taso yayi masa

"Yanzun kace baka da wata wadda kake ganin zaka aura koh?" Dad yace

"K'warae kuwa yalla6ae" Papi ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Idan na baka auran Hindatu zaka kar6a?" da sauri Dad ya d'aga kae ya kalli Papi wanda shima shi yake kalla, seya jinjina kae sannan yace a nutse

"Yalla6ae waye zek'i d'iyar ka? Amma wani hanzari ba gudu ba, kada ka yanke hukunci ba tare da sanin Hindatun ba" girgiza kae Papi yayi sannan yace yana murmushi

"Kada ka damu in dae wannan ne nasan bani da matsala da ita, amma duk da haka zan tuntu6e ta, idan ta amince toh za'a d'aura auren ne kafin kubar k'asar nan"

"Toh nagode ranka ya dad'e, Allah ya k'ara girma"... Koda Papi ya tuntu6i Aunty Hindu da maganar seta nuna amincewar ta, musamman idan ta tuna yadda zata koma rayuwa kusa da d'an yayar ta ta, haka kuma Dad d'in bashi da wata makusa, aekam babu 6ata lokaci Dad ya gabatar da sadaki aka d'aura auran sa da Aunty Hindun.. Suka gama shirye shiryen komae na komawa Nigeria sannan suka yi sallama da mutanen gida, wasun su harda kuka saboda tafiyar Aunty Hindun amma babu yadda suka iya haka suka hak'ura, Azrah kam da zata tafi taga abubuwa, dan kuwa kowa da abinda yake kawo mata a matsayin tsarabar ta, haka ta dinga kar6a tana godiya, Papi kansa ma ba'a barshi a baya ba seda ya bata tasa kyautar sannan ya dinga sanya musu albarka akan auren su gaba d'aya..... K'arfe 7pm agogon k'asar Nigeria suka sauka a cikin gidan Alhaji Kabeer Tajuddeen, Dad da Aunty Hindu ne suka fara sauka daga motar bayan driver d'in daya kawo su ya sauka sannan ta fara k'ok'arin bud'e motar zata fita, ya sanya hannu ya rik'o ta sannan ya jata cikin jikin sa ya rungume ta yana sakin ajiyar zuciya dan sunfi kwana 5 be sata a jikin sa ba, dan haka sosae yayi kewar komae nata, ita kanta se taji wata nutsuwa na shigar ta dan haka ta kwanta luff a k'irjin nasa, tun d'azun dama yake ta binta da ido musamman da yaga kamar ta sake kyau, idan ma idan sa ba k'arya yayi ba har gani yayi ta sake yin wani acan acan da ita dan kuwa kayan data saka d'in sun zauna mata cas cas a jikin ta sun sake bayyana kyawun surar ta, dan ma dae ta saka babban mayafi ne, idanun su Dad ne kawae ya hana shi rungume tan tun d'azu, yanzu kam ya kasa hak'uri ne yana son jin d'umin matar sa, sun kae wajen minti 1 a haka sannan ya fara magana

"I missed u so much wifey" shiru tayi tana jin yadda muryar tasa ta shiga cikin kunnen ta da kuma hucin maganar tasa har bata san sanda ta lumshe idanu ba, seda taji ya d'ago fuskar ta kuma indae yayi hakan tasan abinda ze faru sannan ta maraeraece fuska tace

"Su Dad fah.." se a lokacin ma ya tuna a inda suke, dan haka ya sake ta yana d'an rufe idanun sa ya bud'e, ya bud'e musu k'ofar suka fita tare zuwa sashen Yakumbon dasu Dad d'in suka shiga suma... Da sallama suka shiga parlourn yana gaba yayin da take a bayan sa, ta k'arasa ta zube kan carpet d'in kanta a k'asa tace

"Barka da wannan lokacin Yakumbo" kallan ta Yakumbo tayi dan yadda taga yarinyar ta girma kamar ba ita ba sannan tace

"Lafiya k'alau Alhamdulillah, kun dawo lafiya?" tace

"Alhamdulillah" se a sannan suka gaesa da Don sannan Yakumbo ta kalli Buhaesa dake zaune gefen ta se cika take tana batsewa tace

"Bud'e fridge d'in nan ki kawowa yarinyar nan fura nasan yanzu haka tayi sanyi, ke dae Hindatu kince ba zaki sha ba" ta k'arasa maganar tana kallan Aunty Hindu dake murmushi, mik'ewa Buhaesa tayi ta bud'e fridge d'in ta d'akko fura da nono dake cikin wani kwanan sha me kyau, ta k'arasa ta ajiye a gaban Azrah sannan ta koma ta zauna tana cigaba da satar kallan Don da duk wani hankalin sa ke kan Azrah, lumshe idanun ta Azrah tayi tana jin yadda k'amshin furar ke shigar mata cikin hanci, seta samu kanta da kallan cikin kwanan shan, da alama tayi sanyi sosae dan yadda take wani irin shek'i, haka kawae taji ta burge ta amma mutanen dake wajen ba zata iya shan wani abu a gaban su ba dan haka ta kama kanta kawae, amma tana jin yadda tsohuwar yunwar da take ji ta dinga taso mata haka tayi ta had'iyar yawu kamar wata tsohuwar mayya, (lolz) muryar Yakumbo ta jiyo tana fad'in

"Ki sha mana kinji?" seta d'aga kae kamar zata fasa ihu tace

"Na k'oshi".. Mik'ewar da Dad yayi ne ya sanya Yakumbo maeda duban ta kansa sanda yake fad'in

"Bari mu bata waje ko zata iya sha, seda safe Yakumbo"

"Toh shikenan, Hindatu seda safe.."

"Allah ya tashe mu lafiya Yakumbo" Aunty Hindu ta fad'a tana mik'ewa bayan sunyi sallama da Don suka fice daga d'akin, cigaba yayi da kallan ta yana lura da yadda take satar kallan furar se yayi murmushi kawae dan yasan tun kafin su taho rabon ta da abinci, duk yadda akayi yunwa take ji se ya kalli Yakumbo yace

"Juye mana a jug, zamu tafi da ita.." Yakumbo ta kalli Buhaesa tace

"Maza d'auki ki juye musu, kinga dare na sake yi" mik'ewa tayi tana jin kamar ta rufe kowa ma da duka ta huta da wannan takaecin data keji, haka dae ta d'auko jug d'in tazo ta juye sannan ta ajje, se a lokacin ya mik'e yace

"Toh mu mun wuce.."

"Toh Adnan ku gaeda gida, can sabon zaku wuce ko kuwa za'a yi taro ne?" ya d'an yamutsa fuska sannan yace bayan ya d'auki jug d'in

"No, can zamu wuce"

"Toh madallah, Allah ya sanya alkhaeri ya kad'e fitina.. Ku gaeda gida kinji en nan" Yakumbo ta had'e maganar tayi ta lokaci guda sanda Azrah ta mik'e itama

"Ameen Yakumbo seda safe" ta fad'a tana bin bayan sa, Yakumbo ta bisu da kallo har suka fice, kukan da taji daga gefen tane ya sanya ta saurin juyawa cikin mamaki tace

"Ke meye haka? Wani akace miki ya rasu?" ta fad'a tana kallan Buhaesa dake kuka bilhak'k'i

"Ni wallahi Yakumbo ki yiwa Yah Adnan magana, ni shi nake so wallahi"

"Iyeee, ji min wani iya shege" Yakumbo ta fad'a tana rik'e ha6ar ta sannan ta d'ora da fad'in

"Wato Adnan kike so, kuma dan rashin ta ido ma ni zan masa magana" kukan ta sake fashewa dashi tana fad'in

"Ehh wallahi, ki masa magana ko kuma na bar gidan nan na koma gidan mu tunda bakya son farin ciki na" Kallan ta Yakumbo take yi tana tunanin anya yarinyar nan ba aljanu ke gare ta ba idan kuwa basu bane yau take ganin iya shege

"Toh ba dani ba, wato dan kina jika ta kawae se in saka a yiwa er tahalikar nan kishiya, baewar Allah ba abinda tamin, toh kin dad'e baki tafi ba kinji?" Buhaesa ta share hawayen ta sannan ta mik'e buguzun buguzun ta wuce d'akin ta ta bud'e wardrobe ta fara hautsino kayan ta tana yi tana kuka, daga inda Yakumbo take zaune tace cike da mamaki

"Lallae yarinyar nan mahaukaciya ce, ke kiji min jaraba fa?, toh gama had'a kayan kizo ki same ni ja'irar yarinya"





✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION58_59*

( _Second to the Last Page_)



___Yakumbo na zaune Buhaesa ta fito d'auke da akwatin ta tana goge hawayen idanun ta, tana shirin gota ta Yakumbon ta janyo ta dama ga d'an jiki be kae ya kawo ba aekuwa se gata a k'asa, Yakumbo ta had'e rae tace

"Wato ke wani lokacin duk yadda kika nuna kinyi hankali se kin 6ata hakan koh? Ina zaki je a irin wannan yanayin? A cikin daren nan? Ko so kike ki d'agawa bayin Allah hankali suna zaman zaman su lafiya?" Buhaesa ta sake kwa6e baki sannan ta d'ora kanta akan cinyar Yakumbo tace

"Toh Yakumbo ya zanyi, kince baza ki masa magana ba, ni kuma Allah da gaske nake son shi"

"Oh ni yau nake ganin ikon Allah" Yakumbo ta fad'a akan la66an ta, a fili kuma seta sassauta murya ta fara cewa tana shafa kan Buhaesan

"Kiyi hak'uri kinji shalele na, kinsan dae Adnan ba sonki yake yi ba koh? Ki k'yale wanda baya sonki ki jira me sonki, ke ni bama zan ta6a yadda ki auri wanda baya sonki ba saboda muguwar wahala matan suke sha wanda daga k'arshe ma saki ne yake biyo baya" bud'e idon ta Buhaesa tayi sannan tace tana turo baki

"Saki kuma Yakumbo?"

"Ehh mana, toh ta yaya mutum ze zauna da wanda baya so? Ae shiyasa nace miki ni bazan yadda ki auri wanda baya sonki ba, kuma ba kiga yanzu karatu kike yi ba?" Yakumbo ta fad'a cikin rarrashi

"Toh idan kuma Yah Adnan d'in ne da kansa yazo yace muku yana sona fa?" Buhaesan ta fad'a tana sake turo baki

"Wa salam wa kitabihi, se munfi kowa farin ciki, kinga shikenan se a wanke ki akae masa ke" seta tashi zaune tana murmushi tace

"Yanzu kenan zaku yadda indae shine yace yana sona?" Yakumbo tayi murmushi tana sake kallan yarintar Buhaesan amma se cewa tayi

"Ehh mana amma daga yau bana so ki sake nuna kina son shi, idan ba haka ba raeni ne ze shiga tsakanin ku, kinji koh?"

"Ehh" ta fad'a tana murmushi sannan ta mik'e ta wuce d'aki da akwatin ta, Yakumbo ta bita da kallo tana girgiza kae.


... Yana gama parking ta mik'a hannun ta baya ta d'auko jug d'in da furar ke ciki, ya kalle ta yace

"Ba zaki bari se munje gida ba?" girgiza kae tayi kafin a hankali ta furta

"Yunwa nake ji" be sake cewa komae ba harta fice daga motar da sauri zuwa cikin gidan, shima seya k'arasa gyara motar sannan yabi bayan ta zuwa cikin gidan, da sallama ta shiga d'akin, Meemarh data fara ganin ta ta mik'e da sauri ta rungume ta tana fad'in

"Oyoyo sister.." itama rungume tan tayi sannan suka k'arasa suka zauna, Meemee tace

"Sannu da zuwa" dan ita har yanzu kunyar Azrah take ji, Azrah dake k'ok'arin wucewa kitchen tace

"Yawwah Meemee" Tana shiga kitchen d'in ta juye furar cikin wani bowl ta d'auko cokalin sa ta fito, Ammi da fitowar ta daga d'aki kenan ta bita da kallan mamaki dan gaba d'aya d'iyar ta ta ta chanja ta sake haske da murjewa, kafin ta k'arasa tunanin Azrah ta taho da sauri ta ajje bowl d'in gefe sannan ta rungume Ammi tana fad'in

"Nayi kewar ki sosae Ammi na" murmushi Ammi tayi tana maeda duban ta kan Don da yake shigowa cikin parlourn, Azrah ta sake ta ta koma gefe ta d'auki furar ta ta fara kaewa cikin ta, Ammi suka gaesa da Don sannan Twins ma suka gaesa dashi, Ammi ta maeda duban ta kan Azrah dake shan furar hannu baka hannu k'warya, seta kalli Don d'in tace

"Daga ina kuke ne haka?"

"Daga can gida kawae muka je, shima bamu dad'e ba mukayo nan" seta maeda duban ta kan Azrah tace

"Yunwa kike jine?" seta yamutsa fuska kafin tace

"Ehh Ammi" murmushi Ammin tayi tana karanto abubuwa da dama a tattare da Azrahn, Meemarh ce ta katse su da fad'in

"Ko dae kin yi missing abincin k'asar nan ne?" Ehh toh da wannan d'in ma dan tabbas tayi missing abincin qasar nan duk da can d'in ma suna iya k'ok'arin su wajen samar musu abincin da zasu iya ci, ko kalar nasu wanda suka saba ci amma ba kamar a gida Nigeria ba

"Ehh Meemarh" Meemee ce ta mik'e ta kalli Azrah tace

"Ko akawo miki fankaso?" seta girgiza kae da sauri tace tana yamutsa fuska

"A'ah fa wannan ya ishe ni" komawa Meemee tayi ta zauna, ita kuma Azrah ta cigaba da shan furar ta yayin da Ammi ke d'an jan Don da hira, har zuwa lokacin da Azrah ta shanye furar tass ta mik'e ta kae kitchen ta wanko bakin ta sannan ta fito tana lumshe idanu dan ba k'arya cikin ta ya cika sosae, ita kanta tayi mamakin yadda ta shanye furar kasancewar ta ba ma'abociyar cin abinci me yawa ba, ta 6angaren sa ma yayi mamaki amma seya ta'allak'a hakan da missing d'in abincin nan d'in, dan sau da dama acan d'in sedae tasha fruit kawae ta tashi.. Mik'ewa yayi yana kallan Azrah da take shirin zama yace

"Ammi zamu wuce"

"Toh, ku gaeda gida..Allah ya tsare" kallan sa Azrah tayi kamar zata saka kuka amma taga shi har yayi gaba ma, Ammi ta kalli yadda take wani had'e rae tayi murmushi sannan tace

"Toh ae seki tashi ki wuce.." Twins suka mik'e dan taka mata, ita kuma ta kalli Ammi tace

"Ammi semun dawo, ae dae yau ba zuwa mukayi ba"

"Ehh hakane, toh se kunzo" Ammi ta fad'a tana bin bayan su Azrahn har suka fice daga d'akin ita da Twins sannan ta dawo ta zauna kan kujera tana sake tuna sauyin data gani tattare da d'iyar ta ta, da alama su dukan su basu lura da abinda ita take zargi ba, koda yake ba abin mamaki bane idan tayi duba da duk cikin su babu wanda ze d'orar da yadda shigar ciki yake, dukan su basu da wani experience akan abin, se tayi murmushi tana sake fatan Allah ya d'orar da zaman lafiya a garesu.. Har mota Twins suka raka ta suna sanar da ita zuwan da zasuyi cikin satin nan, seda ya tashi motar suka bar cikin gidan sannan suka koma ciki... Kwantar da kanta tayi jikin kujerar da take kae dan wani bacci bacci take ji, yana lura da ita ji yake kamar ya jawo ta jikin sa ya cigaba da tuk'in, sedae yana tunanin kada a samu matsala dan haka ya cigaba da driving d'in jefi jefi yana juyawa ya kalle ta har zuwa sanda ya hau titin sabuwar unguwar da yayi gini, bud'e idanu tayi tana kallan titin da suka hau, ita kam bacci take ji a yanzu babu inda take so ta bud'e idanu ta ganta se gida amma kuma shi da alama wani wajen yake k'ok'arin kaesu, dan haka ta d'aga kae bayan ta maraeraece fuska tace

"Bacci fa nake ji" murmushi yayi a ransa yana raya ae dole taji bacci wannan uwar fura data tashe ta, amma a fili se yace

"Uhmm, matso ki kwanta kafin mu k'arasa.." shiru tayi kawae ta cigaba da bin inda suke wucewa da kallo har sanda ya shiga wani k'aramin titi sannan yayi parking k'ofar wani k'atan gida, ba tace komae ba har ya fita ya bud'e ya dawo ya tashi motar zuwa cikin gidan, seta samu kanta da bin cikin gidan da kallo dan babu k'arya ko harabar gidan kad'ae abin kallo ce.. Seda ya gama duk abinda zeyi sannan ya zagayo ya bud'e inda take zaune beyi wata wata ba ya d'auke ta gaba d'ayan ta, ta bud'e ido cikin mamakin dalilin da yasa yayi mata hakan amma tana kallan fuskar sa seya lumshe mata idanu yana girgiza kae, ya bud'e parlourn suka shiga, light d'in d'akin a kashe yake dan haka bata iya ganin yadda parlourn yake ba, ya cigaba da tafiya da ita har ya bud'e wani d'aki, se a lokacin ya sanya hannun sa ya kunna light d'in d'akin, take haske ya gauraye ilahirin bedroom d'in, seta rufe idanun ta kana ta bud'e su dae_dae lokacin da yake sauke ta, seta tsaya tana k'arewa kyakykyawan d'akin daya gaji da had'uwa kamar a turae kallo, yayi mugun kyau seta lumshe idanun ta kana ta bud'e su se kuwa suka sauka akan wasu tarin akwatina dake ajje gefe guda, seta juya ta kalle shi yana tsaye yana cigaba da kallan ta hannayen sa duka biyun hard'e a k'irjin sa, k'arin bayani take nema akan gidan, d'akin da kuma akwatinan dake ajje, kamar yasan me take tunani d'in seya k'arasa ya rik'o hannayen ta cikin nasa sannan ya saka idanun sa cikin nata yace

"Sabon gidan ki ne nan d'in, wad'annan kuma lefen ki ne da ban samu na miki ba..se kuma waccan ledar.."

Please Login or Register in order to submit comment