Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so suke yi a samar musu jika a cikin gidan nan ba" Aekuwa dama a kusa take ta sake fashewa da wani kukan cike da jin haushin Zarahn, idan kuma ta tuna abinda mutumin nan ya mata seta sake sakin wani kukan, Zarah kuwa ta sanya ta a gaba ita kuwa se kunnuwa take ta maeda ta kamar wata sabon kamu........


✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION49*



___Seda Zarah ta gaji dan kanta sannan ta tashi tana rik'e da cikin ta ta bar mata d'akin, har lokacin kuka take yi, seda tayi me isar ta har muryar ta ta fara dashewa sannan ta mik'e idanun ta sunyi jawur ta k'arasa wardrobe ta ciro kaya ta saka a jikin ta sannan ta koma ta zauna, wunin ranar gaba d'aya a cikin d'akin tayi shi ita kad'ae ranta duk a matuk'ar jagule, kuma duk sanda ta tuna abinda ya farun In Sha Allah se hawaye ya zubo mata, sam ta rasa gane wane iri ne wannan mutumin, shi abin ma ya masa yawa, kuma yace baya son ta amma har yanzun yak'i sakin ta, shin ma wae me yake nufi ne? Tana nan zaune Ummu ta shigo d'akin, tayi maza ta d'auke kae dan tasan d'azun da yazo zataga sanda yake fitowa daga d'akin nasu, haka kawae zesa Ummu ta mata kallan er iska, Ummu ta kalli Azrah da keta kaucewa had'a ido da ita tace

"Azrah, lafiya kuwa? Naga idanun ki sunyi jawur, kin ma ci abinci kuwa?"

"Ummu kaena ke ciwo" ta fad'a dae har lokacin bata kalli Ummun ba

"Subhanallahi, shine baki fad'a min zaki zauna kina kuka?"

"Ae nasha magani" ta fad'a tana jin dad'in da alama bata ganshi ba, toh amma ta yaya ya shigo cikin gidan har cikin d'akin nan?

"Toh tashi zaune yanzu zan kawo miki abinci kici, yau baza muje gyaran ba se zuwa gobe idan Allah y kaemu" wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana jin dad'in hakan, dan dama ita kam ta gaji da wannan abubuwan da ake mata dan haka ta amsa da "toh" Ummu ta d'an bita da kallo na sakanni sannan ta fice daga d'akin.




__Sake hargitso kayan da suke cikin akwatin tayi tana sake dubawa cike da tashin hankali akan fuskar ta, Hajja Kaltum dake gefe ta sake ta6e baki tana cigaba da cin yalon dake hannun ta tana danna waya, se a lokacin Mami ta kalle ta ganin duk abinda take yi bata tanka mata ba tace

"Don Allah baki ga sark'ok'i na ba?" Hajja Kaltum ta bud'e baki

"Kamar yaya? Nama san kinzo dasu ne ballantana in san inda suke? Ae tun farko da kin bani na ajiye miki da ba haka ba" Mami tace

"Amma dae fisabilillahi kinsani na sani mu biyu ne a cikin gidan nan, toh kenan ina abubuwana suke?" da matuk'ar mamaki Hajja Kaltum ke kallan Mami kafin tayi k'arfin halin fad'in bayan ta had'iye wani yawu muk'ut

"Ae ban fahimci abinda kike fad'a bane, ki min da yaren da zan gane mana"

"Don Allah ki bani sark'ok'i na wallahi nayi alk'awarin zan baki d'aya daga ciki" tashi tsaye Hajja Kaltum tayi cikin kumfar baki tace

"Ahh toh lallae yanzu na sake sanin wacece ke, in d'auke ki ki zauna min cikin gida sannan ki rasa da abinda zaki jefe ni dashi se sata, toh wallahi baki isa ba, nima na gaji ki tattara kayan ki ki k'ara gaba, ae nama yi k'ok'ari" sosae Mami ke kallan Hajja Kaltum d'in wato tana nufin tayi biyu babu kenan, sark'ok'i dae ta riga tasan sun tafi yanzu kuma tabar mata gida? Meyasa ma tun farko bata yi shawarar ta siyar ta siyi gida ba, Se tace fuskar ta a maraeraece

"Kiyi hak'uri k'awata, inaga na jefa su wani wajen ne bansani ba, amma zan sake dubawa"

"Ahh toh ya daefi miki" Hajja Kaltum ta fad'a tana ficewa daga d'akin, Mami ta bita da kallo wasu hawaye masu zafi suna sauka akan kuncin ta, wae yau itace haka, itace gidan k'awar ta wadda dan rayuwa ta juya mata baya take mata wulak'anci, lallae duniya juyi juyi.


.. Washe_gari wajen k'arfe 7:30 Zarah ta gama shiryawa cikin uniform ta zauna kan gadon tana saka socks, tunda take shiryawar Azrah dake zaune gefen gadon ke kallan ta, seda ta mik'e sannan tace

"Wae kyau nayi haka ne naga kina bina da kallo?" D'auke kae Azrah kawae tayi tana d'auke k'wallar data tarar mata a idanu, haka kawae an hana mutum zuwa makaranta, wannan ma ae zalunci ne, Zarah ta kalle ta tace

"Toh nidae na tafi sena dawo" gyad'a kae kawae tayi sannan tabi Zarahn da kallo har ta fice. Anan d'in ta cigaba da zama har zuwa k'arfe 11 da wani abun aka turo k'ofar, ta d'aga kae ta kalli me shigowar, Ummu ce shirye cikin atamfa da hijab hannun ta d'auke da jaka tace tana kallan Azrah

"Maza ki tashi mu tafi, so nake yau mu dawo da wuri" mik'ewa Azrah tayi kamar zata fasa ihu saboda tasan inda zasu je d'in amma haka kawae ta mik'e ta janyo hijab ta saka ta rufawa Ummu baya.. Dab da azahar suka dawo bayan an sake k'alk'ale Azrah d'in kyawun ta da hasken ya sake fitowa, haka zalika farar fatar ta tayi acan acan cikin ja da bak'in lalle, seta fito tamkar wata amarya kuma tauraruwa tayi wani shahararren kyau.. Sanda suka dawo a lokacin itama Zarah ta dawo tana parlour tana cire takalmin k'afar ta, ganin su ya sanya ta mik'ewa tana kallan Azrah da taga ta sake yin wani kyau tace

"Wowww" ta k'arasa fad'a idanun ta na sauka kan farar k'afar Azrahn data fito tayi d'ass da jan lalle, ta sake fiddo idanu

"Wayyo Azrah wallahi Yah Adnan yaga lallen nan bansan irin rud'ewar da zeyi ba" ta fad'a sam tama manta Ummun na wajen, seda taga Azrah ta d'aga ido ta kalli Ummu, sannan ta rufe bakin ta tayi wuri wuri da idanu ta kasa ko motsi daga inda take, Ummu tace

"A'ah k'arasa mana rasa kunya" ta fad'a fuskar ta a had'e, Zarah ta sake yin shiru tana kallan Ummun, Ummu ta d'auki cup d'in data gani gefen ta tace lokaci guda

"Bar nan wajen kafin na raunata mara kunyar bakin kin nan" da sauri Zarah ta mik'e tayi cikin d'aki tana dariya, Ummu ta kalli Azrah

"Kiyi sallah kici abinci akwae wani abu da zan baki" da "toh" kawae ta amsa sannan ta wuce cikin d'akin tana sake bin jikin ta da kallo, ita kanta tasan tayi kyau, zata iya cewa tunda take ba'a ta6a mata fulawa ba, har gwara ma lalle wani lokacin idan Hauwa'u ta kwa6a lalle takan bata itama ta saka a yatsun ta, amma yau taga hannun ta da k'afar ta reras cikin wani kyawawan zane, seta lumshe idanu kawae.. A cikin d'akin suka ci abinci ita da Zarah bayan sunyi sallah, Ummu ta shigo rik'e da wani plate a hannun ta da kuma wata jarka, ta k'arasa ta zauna tana kallan Azrah tace bayan ta ajje mata plate d'in hannun ta

"Ga nan maza ki cinye shi" bin abinda Ummun ta bata tayi da kallo, ganin wani abu kamar nama amma ba normal suyan nama bane, seta d'aga idanun ta ta sauke su kan Ummun dake kallan ta

"D'auka kici mana, se ki kora da zuma gata nan" Ummu ta fad'a tana matso da jarkar dake hannun ta, d'aukar plate d'in tayi ta matso dashi kusa da ita, Zarah dae binta da kallo kawae take ba tace komae ba dan gudun kada ta sake su6utar baki ta fad'i wata maganar, a hankali ta saka hannu ta gutsuri naman dako k'amshin sa be mata ba, Allah ya gani ta gaji da wannan sabbin abubuwan da Ummun ke had'a ta dasu, ta gaji wallahi, kwae se hawaye sharr ya zuba akan kuncin ta dae_dae lokacin data kae naman bakin ta, ae kuwa ta 6ata rae tana taunawa saboda yadda taji ko a baki ma babu dad'i, ta ajje plate d'in gefe tana matse k'walla, Ummu ta had'e rae

"D'auki ki ci mana, ko sena miki d'ura?" d'auka ta sake yi a hankali ta dinga dannawa tana goge hawayen idanun ta lokaci zuwa lokaci, kamar wadda kecin kashi haka take ta6e baki, tana kuka kamar k'aramar yarinyar goye, Zarah na gefe tana dariya k'asa k'asa, dududu ko rabi bata ci ba ta ajje ta d'aga kae tana kallan Ummu tace cikin kuka

"Wallahi Ummu zanyi amae, ba dad'i don Allah ki barshi haka" murmushi Ummu tayi sannan tace

"Toh shikenan, d'auki zumar ki sha" wannan kam babu musu ta d'auka ta kae bakin ta, se dae itama taji sauyi daga aenahin d'and'anon zumar, amma a haka ta maaze kawae ta sha sannan ta ajje tana sake goge k'wallar idanun ta

"Yawwah ko kefa" Ummu ta fad'a sannan ta maeda duban ta kan Zarah

"Tashi ki shirya zan aeke ki gidan Hajiya Nafisa" da "toh" Zarah ta amsa sannan ta mik'e dan dama ta gama cin abincin, ta shiga toilet ta wanke hannun ta sannan ta fito ta d'auki dogon hijab d'in ta dake kan gado ta zura, Azrah tayi rau rau da idanu tana kallan Ummu tace

"Don Allah Ummu zan je" Ummu ta girgiza kae

"A'ah base kin je ba"

"Ummu don Allah tunda a cikin mota ne kinga" Wannan karon Zarah ce tayi magana, Ummu ta mik'e tana fad'in

"Naji, kada ku dad'e, ke kuma idan da dama ma kiyi zaman ki cikin mota, tunda dae yawon kike so bayan yanzu muka dawo" Murmushi Azrah tayi kana ta mik'e ta isa wardrobe ta fiddo wani jalbab hijab ta zura sannan suka fita ita da Zarahn, a parlour suka tadda Ummu, nan ta fad'a musu aeken kana suka fice daga d'akin.



.. Yana sauka daga motar tasa shima Fawaz yana sauka daga motar, ya k'araso yana kallan Don yace

"Barka da zuwa" murmushin ya maeda masa sannan yace

"Barkan ka dae, ya karatu?"

"Alhamdulillah" Fawaz ya fad'a da murmushin nan nasa, wanda hakan ya farantawa Don, da alama damuwar daya sanya wa kansa yanzun ya rage ta.. Tare suka jera zuwa parlourn Dad, da sallama suka shiga, Dad ya dube su yana murmushi yace

"A'ah tare kuke kenan?" kusan tare suka zauna kan kujerar sannan Don yace

"Ehh anan muka had'u, barka da wannan lokaci" yayi maganar a lokaci guda

"Barka dae Son" Fawaz yace

"Dad ya aeki?"

"Aeki Alhamdulillah, ina fatan dae babu wata matsala koh?" gyad'a kae Fawaz yayi, Dad yayi shiru na d'an wani lokaci, yana so yayi wa Don d'in magana akan dangin mahaefiyar sa dake Sudan, amma yafi so yaji ya fara zancen da kansa, dan haka ya bar zancen kawae a ransa yana sake addu'ar Allah ya k'ara daedaeta al'amarin..

"Kun shiga wajen Yakumbo ne?" Fawaz ne ya amsa da

"A'ah Dad, ae naga shima Bhai kamar yanzun ya shigo gidan"

"Toh ya kamata kuje ku gaesa d'in" Don ne ya fara tashi yace yana kallan Dad

"Ni inaga daga can zan wuce kawae"

"Toh shikenan, Allah ya tsare" da "Ameen" dukkan su suka amsa sannan suka fice tare zuwa sashen Yakumbon suna tafe suna hira jefi jefi.. Kallan su Yakumbo tayi sanda suke neman zama tace

"Sannun ku da zuwa" Fawaz ya amsa da

"Yawwah Yakumbo, yau babu fura ne" ta d'an kalle shi sannan tace

"Aekin kenan, abinda ya kawo ka kenan ko gaeshe ni kazo yi" yace

"Wallahi gaeshe ki nazo yi Yakumbo"

"Toh madallah, sannu da zuwa"

"Barka da wannan lokaci" ta jiyo muryar Don yana fad'a, seta d'aga kae ta kalle shi, ko babu komae an samu cigaba akan da, dan da da ne sedae yace "kina lafiya?" toh In Sha Allah zasu cigaba da masa addu'a, Allah ya shirya shi gaba d'aya

"Lafiya lau, ya matar taka?" yayi d'an jim kad'an yana tuna moment d'in jiya daya kasa barin kwanya da k'wak'walwar sa yace a nutse

"Tana lafiya" murmushi Yakumbo tayi tana sake jin dad'i kafin tace

"Toh madallah, a gaeshe ta" bece komae ba ya mik'e yace yana kallan ta

"Mun koma"

"Toh ka gaeda gida kaaji" Fawaz ya kalli Yakumbo

"Nifa banji motsin Buhaesa ba, ko har yanzu bata dawo ba?"

"Uhmm, ya zanyi mata ne Fawaz, wallahi har yanzu bata dawo ba, ae inaga sakawa zanyi aje a d'akko min abata, daga zuwa gida hutu kuma?" dariya Fawaz yayi sannan yace

"Aekam dae Yakumbo, ya kamata shalelen ki ta dawo haka nan dan ko muma munyi missing nata gaba d'aya" ya fad'a yana bin bayan Don daya dad'e da ficewa, a harabar gidan Don ya kalli Fawaz yace

"Ka tabbatar babu matsala?" Fawaz yace

"Ehh Bhai, idan ma akwae zan fad'a maka"

"Yayi kyau" Don ya fad'a yana k'arasawa motar sa, Fawaz ne ya bud'e masa k'ofar, ya shiga da murmushi akan fuskar sa, sannan ya tashi motar Fawaz na d'aga masa hannu ya fice daga gidan... Sanda ya fito daga gidan yayi dae_dae da lokacin da suma tasu motar ta fito daga cikin gidan, seya samu kansa da bin motar da kallo kamar wanda wani maganad'iso ke fuzga, aekuwa cikin sa'a idanun sa suka sauka a kanta sanda take d'age glass d'in motar ya zama ta rufe shi gaba d'aya kenan, da alama basu ganshi ba dan kuwa ta gefen motar sa suka wuce, seya lumshe idanun sa yana juya kan motar tasa yabi bayan su, sannu a hankali yake bin su har zuwa sanda suka hau kan titi, se a lokacin Zarah ta samu damar fad'ar abinda tayi niyyar fad'a d'azun babu dama

"Hmm wae kin ganki kuwa Azrah?, na fad'a miki wallahi se kin rud'ar da Yah Adnan, kinga yadda fulawar nan ta zauna akan fatar ki kamar an d'ora kuwa?" ta6e baki Azrah tayi ba tace komae ba, ita bata san meke damun Zarahn ba da zancen ta kullum na Yah Adnan a kanta, mutumin da ba sonta yake ba? Mutumin ma da take neman saki a wajen sa? Murd'awar da marar Azrah tayi ne ya sanya ta yin k'asa sa kae tana rik'o cikin ta, Zarah ta kalle ta tace

"Lafiya?" jinjina mata kae kawae tayi amma ba dan tana nufin hakan ba, dan yadda taji cikin ya sake murd'a mata, nan da nan k'walla ta taru a idanun ta tana tuna shikenan lokacin yazo, bata manta wahalar da take sha duk lokacin da bak'on watan zezo mata, fata take Allah yasa kar ciwon ya turnuk'e ta har se sun koma gida, dan tasan zuwan sa kam ba yanzu ba seta gama shan wahalar sannan yake zuwa, addu'ar ta ta ta kar6u dan kuwa ya d'an lafa be sake murd'awa ba, Haka Zarah ta cigaba da yiwa Azrah maganar Don d'in, da dae ta fahimci sam Azrah bata son zancen seta bashshi kawae ta d'akko wata hirar har zuwa sanda suka isa dae_dae layin da zasu shiga, Zarah tace

"Yawwah, sauke mu anan kawae, ba dad'ewa ae zamu yi ba" babu musu ya gangara gefen titi ya kashe motar sannan su kuma suka sauka, Azrah na mazewa kawae dan a lokacin da k'yar ta iya mik'ewa. shima tsayar da motar sa yayi se dae be kashe ta ba, yabi kyakykyawar matar tasa da kallo, wadda yau yayi na'am da sunan da mafi yawan mutane kan kira ta dashi a wajen sa, dukkan ta yabi da kallo, sanye cikin hijab d'in daya rufe gaba d'aya jikin ta, baka ganin komae se fuskar ta, ya d'an ji dad'i da ganin hakan, se dae kuma fuskar ta ae a bud'e take, seya samu kansa da juyawa ko akwae maza a wajen, bega kowa ba se wata mota data zo ta wuce zuwa cikin layin da suka shiga, zuciyar sa ta d'an sosu kad'an, ya zama dole ya shatawa yarinyar layi akan fita ba tare da izinin sa ba, idan kuwa hakan ta kasance toh ya zama dole ta sanya wani abun daze rufe fuskar ta, a hankali ya lumshe idanun sa yana tuna kyakykyawar fuskar ta ta daya hango dukda ba'a kusa dashi take ba.. A hankali suke takawa zuwa cikin layin hannun su cikin na juna, tafiyar tasu ta sake yin slow saboda yadda Azrah ke tafiya kamar mara laka har seda Zarah tace

"Anya kuwa lafiya kike?" girgiza kae Azrah tayi tana d'an sake rank'wafawa tace

"Wallahi mara ta ke ciwo kamar zata 6alle"

"Kae subhanallahi, Allah ya tsare toh dae har muje mu dawo koh?" jinjina kae Azrah tayi ba tare da tace komae ba suka cigaba da tafiya, shiru layin yake babu kowa, dae_dae lokacin da suke k'ok'arin shiga wani babban layi, d'aya daga cikin wad'anda ke cikin motar data shigo layin ya fito da sauri yana kalle kalle, sannan beyi wata wata ba ya kalli inda suke, wanda yake cikin motar yace

"Malam kayi sauri, wadda tafi hasken itace.." kafin ya gama jin maganar na cikin motar ya k'arasa inda suke babu 6ata lokaci yaja Azrah wadda saboda rud'ewa ta sanya ta sakin k'ara, ya toshe mata baki da safar hannun sa, Zarah ta d'ora hannu aka ta saki wata k'ara, se dae da alama babu kowa a layin, gashi kuma sunyi nisa da titi dan haka ta matsa kusa da mutumin tana kuka kamar zata rik'o Azrah, wanda ke cikin motar ne ya matso da motar kana wanda ke rik'e da Azrah ya jefa ta ciki shima ya shiga, mutumin yaja motar yana sakin wani shu'umin murmushi yace

"Yess, yau kam komae ze tafi yadda na tsara, da alama ma jinkirin da nayi yayi dan naga kamar an k'ara mata kyau ne" wanda ya d'auko Azrah ne yace

"Kae mutumi na kasan takan tsiya wallahi" Murmushi yayi yana cigaba da gudu sosae kafin yace

"Naga ma su biyu ne, da mun sani dukkan su muka d'auko kaema seka d'an rage zafi, dan ni dama buri na akan wannan ne kuma yau zan cika shi".. Zubewa Zarah tayi a wajen tana fashewa da wani irin kuka tana fad'in

"Na shiga 3 na lalace" se kuma ta mik'e da gudu fara takawa dan barin layin tana kuka kamar sabon kamu.. Yana cikin motar yaga sanda motar data shiga layin d'azun ta fito da wani irin mahaukacin gudu, be iya ganin wanda ke driving d'in ba dan ba damuwar sa bace wannan, haka kuma be kawo komae a ransa ba ya cigaba da kallan cikin layin dan ganin sanda zasu fito d'in, kamar an jefo ta haka ta fito daga layin idanun ta sunyi jawur tana kuka sha6e-sha6e, haka kawae yaji gaban sa ya fad'i, a hankali ya lumshe idanun sa, yana sake duba gefen ta dan ganin daga inda zata 6illo, haka nan kawae shi da ba kasafae tsoro ya cika shigar sa ba amma wannan karon se yaji kamar wani abu me kama da tsoro na shirin shigar sa, kawae seya kashe motar gaba d'aya ya fita daga ciki da sassarfa ya k'arasa inda Zarahn take......

✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION50*


___Zarah ta kalli inda motar data kawo su ke tsaye har lokacin drivern na ciki a zaune bema san abinda ke faruwa ba, d'aga idon da zatayi seta hangi Don se taji kamar an k'ara mata k'warin gwuiwa ne amma kuma zuciyar ta ta sake karyewa, da k'yar ya bud'e bakin sa ya iya furta

"Ina take?" haka kawae yaji yana jin shakkar amsar da zata fito daga bakin Zarahn, Zarah ta girgiza kae wasu hawayen na zubo mata tace

"Yanzun nan wasu suka d'auke ta a mota, yanzun nan motar ta fita daga cikin layin nan bansan ko su waye ba" ta fad'a tana nuna hanya, dafe motar dake gefen sa yayi ya lumshe idanun sa yana jin yadda lokaci d'aya kansa ya sara haka zuciyar sa ma ta buga da wani k'arfin gaske, ya kae second 10 a hakan sannan ya bud'e ba tare daya sake kallan inda Zarah take ba ko dan ta kuma k'ara bashi wani hasken ba ya juya cike da sassarfa ya k'arasa inda motar sa take ya shige ya fizge ta da wani irin gudu wanda ya wuce wanda yake yi ada, binsa da kallo Zarah tayi tana maemaeta kalmar "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" anya kuwa zata iya komawa gida? Toh ta koma gida tace musu ina Azrah? Kawae seta sake fashewa da kuka duk da mutanen da jefi jefi kan juya su kalle ta su k'ara gaba, ita kam hakan be dame ta ba, bama tasan suna yi ba, se kuma a hankali ta k'arasa ta bud'e motar ta shige har lokacin tana kuka, toh idan sun zauna anan d'in me zata yi? Cire earpiece d'in kunnen sa yayi ya juya ya kalle ta ganin yadda take kuka kamar wadda akama mutuwa yace

"Hajiya lafiya kuwa?" share hawayen tayi sannan tace

"Muje gida don Allah" be sake cewa komae ba ya tashi motar yana tunanin ko meye ya faru?, duk da haka dae be sake cewa komae ba kawae yaja motar a haka har suka isa gida Zarah bata dena kuka ba haka k'irjin ta be bar bugawa ba tana tunanin me zata cewa mutanen gida.. A parlourn ta tadda Ummu har lokacin, se dae yanzu ita da Abunnas ne suna kallo, ta shiga d'akin tana kallan su su duka, haka nan kawae Ummu taji tsoro ya kamata ta mik'e da sauri tana kallan Zarahn da idanun ta suka yi jawur alamar kuka take, yanzu ne ya tsaya

"Ina Azrah?" shine abinda Ummu ta fara tambaya, aekuwa Zarah ta fashe da kuka, abinda ya sake d'aga hankalin Ummu kenan taji bugun zuciyar ta ya k'aru, se tayi k'arfin halin sake fad'in

"Zarah ina take?" ta fad'a tana rik'o Zarahn

"Ummu an sace ta!"

"Ke bansan shashanci, sace ta kamar yaya?" Ummu ta fad'a kamar zata rufe Zarahn da duka, Zarah ta girgiza kae tace cikin kuka

"Wallahi Ummu, wasu mutane ne suka d'auke ta a cikin motar su, Ummu bansan su ba wallahi, bansan me muka musu ba" komawa Ummu tayi tayi zaman dirshan kan kujerar tana fad'in

"Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" seda ta maemaeta fiye da sau 3 sannan ta iya d'agowa ta kalli Zarah wadda yanzu Abunnas ke kusa da ita yana mata magana tace

"Garin yaya akayi haka Zarah?" Ummu ta fad'a k'walla fall idanun ta tana tunanin me zata cewa iyayen Azrah d'in? Uwa uba kuma mijin ta shi kansa? Kasa cewa komae Zarah tayi har seda taga Ummu ta mik'e ta zari mayafin dake gefen ta ta yafa sannan ta jiyo muryar Abunnas na fad'in

"Ummu ina zaki je?" se a lokacin Zarah ta d'ago ta kalli Ummu tace

"Kar kije ko'ina Ummu, Yah Adnan ya bisu.."

"Adnan kuma? Ya akayi yasan da maganar?" ta fad'a bayan ta dawo tana kallan Zarah

"Nima bansan yadda akayi yazo wajen ba, kawae ganin sa nayi shine na fad'a masa abinda ke faruwa kuma naga yaja motar sa da gudu" Komawa Ummu tayi ta zauna tana sake karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, bata so ta tayar wa da iyayen Azrah hankali, yadda ita kanta hankalin ta ya tashi tasan nasu seya ninka natan, Saboda haka ba taga alfanun fad'a musu d'in ba gwara ta zauna suyi ta addu'a Allah ya bawa Adnan d'in sa'a ya samo inda take.. A 6angaren Don kuwa sosae yake gudu akan titin kamar ze tashi sama, abinda ya sake bashi mamaki har lokacin bugun zuciyar sa be saetu ba, duk motocin dake gaban sa seya kalle su, yana so yaga waccan motar amma be gani ba har zuwa sanda suka zo dae_dae wani round about, traffic jam ya rik'e su seya tsaeda motar kawae ya kifa kansa akan steering motar, idanun sa ya lumshe yana sake fuzgar numfashin sa dake chanja yanayin fitar sa, hango motar ya cigaba dayi cikin idanun sa seya bud'e idanun da sauri dae_dae lokacin da aka bada hannu, ya juya gefe da gefe har lokacin dae bega motar ba, ya sake kallan gefe da gefen, cikin Ikon Allah ya hango motar dake sharara gudu ta hau kan wani titi, babu 6ata lokaci yabi bayan motar ya cigaba da binta, a haka har suka sauka zuwa cikin wani layi wanda bashi da zurfi, dan haka ya tsaeda tasa motar a bakin layin yana hangen su, suka tsaya a k'ofar wani gida, d'ayan ne ya sauka ya saka mukulli ya bud'e gidan sannan Irfan yaja motar zuwa ciki kana suka kulle k'ofar, a compound d'in gidan yayi parking sannan ya bud'e k'ofar inda yake zaune ya fito yana kallan cikin motar da Azrah ke ciki tana kuka kamar ranta ze fita, yana tsaye mutumin ya bud'e back seat yace

Please Login or Register in order to submit comment