Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa magana da yau kam seta kalli cikin k'wayar idanun sa ta fad'a masa wata maganar da shima se yaji zafin ta, se dae ina ba zata iya ba dan haka seta sake lumshe idanun ta tana bari k'wallar data taru a cikin idanun ta ta zubo, shin wae wannan wane irin mutum ne? A hankali taja k'afafun ta zuwa d'akin ta tana sake tuna irin maganganun daya fad'a mata.....



______Ya k'arasa ya zauna kan kujerar parlourn, Fawaz ma ya nemi waje ya zauna kusa da Don d'in yana kallan sa yace

"Wallahi Bhai nayi missing naka sosae, gashi idan na cewa Mami zanzo se tace wae god'e god'e dani inyi ta zuwa gidan mutane, Bhai wae ku ne mutanen.." ya k'arasa maganar yana turo baki, Don yayi murmushi yana kallan Fawaz yace

"Noo..idan ma so kake ka dawo gidan da zama u're welcome boy" Mami ta wulla musu harara su duka sannan tace

"Toh bari a tattara masa komae seya koma.." Fawaz yace

"Yawwah Mami na" Mami tayi dariya kana tace

"Boy, boy, kae fa ka d'auka da gaske koh?" Ya sake tura baki yana kallan Mamin yace

"Aou wae Mami gatse kike min?" Tace

"Toh Allah ya shirye ka"

"Amm, Son ka duba jikin Yakumbo kuwa?" Ta fad'a bayan ta maeda duban ta kan Don, Ya d'aga kae a hankali yana kallan Mamin sannan ya girgiza kae yace

"No babu buk'ata" Mami tace

"A'ah pls kaje ka duba ta bata ji dad'i ba sosae.."

"Ohk" kawae yace, ya cigaba da biyewa hirar da Fawaz yake masa.. Seda yazo tafiya sannan ya wuce part d'in Yakumbo. Da sallama d'auke akan la66an sa ya shiga parlourn, Buhaesa da ke zaune kan side chair tana rubutu a littafi taji takun sa se kuwa ta kwasa da gudu tayi cikin d'akin ta tana sauke numfashi, shi kuwa be ma lura da ita ba ya shige cikin d'akin ya nemi waje ya zauna kan kujera yana d'aukar k'afar sa d'aya ya d'ora akan d'ayar, Yakumbo dake kwance jin shigowar sa yasa ta mik'e zaune tana kallan sa tace

"Yanzu ka shigo gidan ne?" Yace a tak'aece

"A'ah" Yakumbo tace

"Toh sannun ka" ta fad'a tana kallan yadda yayi da k'afafun sa, ta girgiza kae tana sake janyo masa addu'ar shiriya a cikin zuciyar ta, kamar ba zece komae ba se kuma yace

"Ya kike, ya jikin?" Yakumbo tace

"Aou kae se yanzu kasan bani da lafiya?" Yayi shiru bece komae ba ya cigaba da danna wayar sa, Yakumbo tace tana gyara zaman ta

"Ya wajen matar taka?" A fakaece ya d'an d'aga ido ya kalle ta sannan yace a hankali bayan ya maeda kallan sa kan wayar sa

"Wani wajen ne haka?" Yakumbo ta rik'e ha6a tana sake girgiza kae sannan tace

"Duk yadda akayi hadeeza bata kwa6ar ka wallahi, ko dan ba ita ta haefe ka ba? Ka dinga zaro magana kamar wanda ba'a gasawa baki ba?" Kafin ta kaega k'arasa maganar ya mik'e dan shi idan akwae abinda ya tsana ace Mami na masa wani abun ko dan ba ita ta haefe shi ba? Wasu mutanen ko me mutum zeyi basa gani, duk irin k'ok'arin da Mami take yi ba'a gani, Yakumbo ta bishi da kallo wato an ta6o sa kenan, maeda wayar sa yayi cikin aljihu ba tare daya kalle ta ba yace yana ficewa

"Se anjima" Yakumbo ta sake bin sa da kallo, dae_dae nan Buhaesa ta fito daga d'aki cikin doguwar rigar abaya maroon taci kwalliya ta kalli Yakumbo tana turo baki tace

"Yakumbo ina Yah Adnan d'in?" Yakumbo tace

"Hala ajiya kika bani?" Buhaesa tayi rau rau da ido tace

"Amma Yakumbo base kimin magana ba?" Yakumbo tace

"Iyeee!! Toh sannu uwata, bashin sa kika ci ko menene?" Ita dae Buhaesa ba tace komae ba ta sake zum6ura baki tana komawa cikin d'akin ta..... 'Bangaren sa kuwa yana fitowa kae tsaye parking lot ya wuce ya d'auki motar sa ya fice daga gidan.... Sanda ya isa gidan ta gama komae, sedae murar da take yi ne ya sanya ta sakko dan had'a shayi me citta ko zata ji dad'in mak'ogwaronta, tana kitchen d'in dan haka bata ji shigowar sa ba, tana gama had'a shayin ta fito daga kitchen d'in kae tsaye ta wuce upstairs hankalin ta na kan shayin tana juyawa da spoon, kamar daga sama ta jiyo magana sama sama, seta d'aga kae da sauri dan ganin daga inda take jiyo maganar, sakkowa yake daga saman da waya kare a kunnen sa yana magana kamar baya son yi, da sauri ta koma baya tana sake rik'e cup d'in hannunta gudun karya su6uce daga hannun ta, seda yazo dab da ze gifta ta sannan tace cikin sanyi

"Ina wuni?" Tayi shiru tana saurara taji amsar sa, se dae ga mamakin ta se taji ya cigaba da tafiyar sa yana amsa wayar dae har lokacin, ta watsawa bayan sa harara sannan tayi gaba tana murgud'a baki tana mita, da farko ta fara gaeshe shi baya amsawa, ta dena yace bata gaesuwa, yanzun kuma tayi ma be amsa ba, wannan mutumin sam bashi da alk'ibla, da wannan tunanin ta shige d'akin ta......


_____Simrah ta zare glass d'in dake fuskar ta sannan ta k'araso taja kujera ta zauna tana kallan Irfan da murmushi kan fuskar ta tace

"Barkan ka" Irfan ya d'ora hannun sa akan bench d'in gaban su sannan yace

"Yawwah barka dae.." Simrah tace

"Fatan dae ban zaunar da kae ba?" Irfan yace

"Noo, nima zuwa na kenan" Simrah ta gyara zama tana fad'in

"Yawwah, toh yanzu ya ake ciki?" Irfan yace

"Yawwah..kina ji?" Ya fad'a yana sake gyara zaman sa sannan ya d'ora da fad'in

"Gobe nake so mu gabatar da komae saboda na k'agu wallahi a matse nake.." Simrah tayi murmushi sannan tace

"Ina jin ka, yaya komae ze tafi?" Irfan yace

"Zamu had'u a Green Club, zan san yadda za'ayi Don yazo wajen, se kuyi spending night d'in acan ke dashi, yayin da ni kuma zanje can gidan sa nima mu shoshale kin gane koh?" Ya fad'a yana sakin wata shu'umar dariya, Simrah ta kalle shi kana tace

"Amma kana tunanin ze zo kuwa bayan abinda ya faru?" Irfan yace

"Na dad'e tare da Don, so nasan yadda zanyi masa yazo wajen nan, kada ki damu ke dae kawae ki shiryo goben.." Simrah tace

"Toh shikenan Irfan, Allah ya bamu sa'a" Irfan ya sake sakin wata dariya yana kallan Simrah yace

"Ahh lallae fah malama"


......... Yana zaune akan kujerar d'akin sa yana wani aeki a laptop, wayar sa dake ajje kan gado tayi k'ara, daga inda yake zaune ya hangi me kiran nasa, ya d'auke kae yana cigaba da aekin sa, wani kiran ne ya sake shigowa se yaja tsaki yana mik'ewa ya k'arasa ya d'auki wayar ya kara a kunnen sa a fusace yace

"Heyy lafiya?" Daga can 6angaren Irfan yace

"Haba mana Don, don Allah kayi hak'uri komae ya wuce, wallahi ba da wata manufar na fad'a ba amma kayi hak'uri.."

"Enough malam, meye na kira na?" Irfan yace

"Dama kira nayi na fad'a maka yau za'a kawo shisha.." yace

"And so?" Irfan ya sake maraeraece murya yace

"Shikenan dama, yasa nace bari na kira ka na fad'a maka ko zaka je!" Shiru Don yayi dan harga Allah yayi missing nata two days da be sha ba, dan haka cikin basarwa yace

"A'ina ne?"

"Green Club" Irfan ya bashi amsa, be sake cewa komae ba kawae ya katse wayar, Irfan yayi wani ja'irin murmushi yana jinjina kansa.... K'arasawa yayi ya rufe laptop d'in sannan ya fad'a toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin k'ana nan kaya ya feshe jikin sa da turaren sa na Trussardi sannan ya zura takalmin sa samfurin slip_on kana ya d'auki wayar sa ya jefa a aljihu ya fito daga d'akin nasa kae tsaye ya wuce ya d'auki motar sa sannan ya fice daga gidan....... A 6angaren Azrah kuwa sanda ta farka daga bacci seta rik'e kan ta tana jin yadda yae mata wani gingirin, seta mik'e a hankali ta fad'a toilet tayi wanka sannan ta fito ta shafe jikin ta da maya mayan ta da turarukan ta na jiki kana ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi ta d'auki hula me taushi ta sanya a kan ta, sannan ta feshe jikin ta da turaren ta na Xplore, kana ta koma tayi lamo kan gadon taja blanket ta lullu6e ilahirin jikin ta saboda yadda taji alamar zazza6i na shirin kama ta ne........



__Minti na kad'an ne suka kae shi wajen, yana zuwa yayi parking motar sa sannan ya fito yana fitowa wayar sa da yanzun ke hannun sa ta d'auki k'ara, ya kalli me kiran nasa, sannan ya saka wayar a silent ya cigaba da tafiya zuwa ciki........ Irfan na zaune shi da Simrah dake sanye cikin wasu shu'uman kaya riga da wando tiet, ta yafa wani mayafi wanda marabar sa da babu kad'an ne, wannan glass d'in dae daya kasance koda yaushe yana idon ta yanzun ma shine a fuskar ta ta, Simrah ta maraeraece fuska tana kallam Irgan tace

"Anya kuwa zezo?" Irfan yace

"Tunda yace zezo zezo d'in ne, ki bari kawae" ba tace komae ba kawae tayi shiru, Irfan dake zaune ya mik'e yana fad'in

"D'an haka gashi nan.., bari naje.." Be jira amsar da zata bashi ba ya wuce, Yana zuwa inda Don d'in yake yace

"Welcome Sir.." Don yace yana cigaba da tafiya

"Yawwah.."

"Sauri nake, mu k'arasa ciki!" Inji Don, Irfan yace

"Ohk" shima yayi gaba, suna fara tafiya wayar Don tayi k'ara ya kalli Irfan yace

"May be akwae wani abun, Sameer ke kira na, gobe ma had'e.." Irfan yace cikin er daburcewa

"Gobe kuma?" Wayarsa dake ringing a karo na biyu bayan shigowar sa wajen ya kalla dae_dae sanda Irfan ke fad'in


"Pls Don...muje ko shisha ce ka sha kafin ka tafi" Lumshe idanunsa yayi sannan ya bud'e yana sake kallan wayar yace a nutse


"Noo Irfan I have to go.." Irfan yace


"Pls ko kad'an ne mana" Shiru Don yayi se kuma can yace


"Ohkk.."


"Yawwah" Irfan ya fad'a yana murmushi sannan suka wuce cikin club d'in, kae tsaye wajen da suka saba zama idan sunzo wato wajen VIPs suka nufa suka zauna, tunda suka zauna take kallan su, tana kallan Don kamar ta cinye shi, a yanzu da take ganin sa se take ji kamar ta tashi taje ta rungume shi, Irfan ya kalli Don yace


"2mins pls" d'aga masa kae kawae yayi ba tare da yace komae ba, Irfan yayi gaba can se gashi ya dawo da wasu lemuna a cikin cup guda 2 ya ajje su gaban Don yana fad'in


"Sorry Don ba'a samu shishar ba" da mamaki Don ya d'aga ido ya kalli Irfan, ganin haka ne ya sanya Irfan yin ya'ke yace


"Yess..shiyasa na samo mana juice.." Kafin yakae 'karshen maganar tasa har Don ya mi'ke yace 


"Bana bu'kata" Ya fad'a yana shirin wucewa, Irfan ya ri'ko hannun Don ya maraeraece fuska


"Plss in kamin haka ba zanji dad'i ba, and zanga kamar kaji haushi na ne friend, nima labarin za'a kawo ne ya sani na sanar da kae, bansan za'a samu akasi ba" Kamar ba zece komae ba se kuma ya koma ya zauna ya d'auki lemon dake cikin cup ya kae bakinsa ya shanye tass sannan ya ajiye, Irfan yayi wani murmushi yana kallan Don d'in seya juya wani side d'in ya kalle ta ya kanne mata idanu, itama murmurshi tayi tana jin kamar ta tashi ta taka rawa, dae_dae sanda Don ya lumshe idanunsa sannan ya bud'esu a lokaci guda yana mi'kewa ba tare da ya kalli Irfan ba yace


"Zamu had'e gobe" be jira amsar Irfan d'in ba yayi gaba yana jin yadda mood d'insa ke chanjawa lokaci guda wanda besan dalilin hakan ba, Irfan ya mi'ke yana shirin bin bayansa, sedae shi tuni ma ya fice daga wajen gaba d'aya..... Da sauri ta 'karaso fuskarta a maraeraece tana kallan Irfan tace


"Meyasa ka barshi ya tafi?" Harara ya jefa mata yace


"Kamar kina ganin yadda nayi 'ko'karin ri'keshi da hira amma ya'ki tsayawa koh?" Jinjina kae tayi tana kallan Irfan sannan tace


"Meye mafita yanzu?" 


"Mafita shine kiyi maza ki bishi duk inda ze je" ya 'karasa fad'a yana ta6e baki, Se tayi d'an shiru kad'an kafin tace


"Kana ganin hakan babu matsala?" 


"Yeah" Irfan ya fad'a a ta'kaece


"Ohk.., ka bani aron motarka kasan banzo da tawa ba" Irfan yace


"Ohk..amma fa se kinyi da jiki wallahi, nima ina gama abinda nake zan wuce can d'in" ya fad'a yana ciro key daga aljihunsa ya mi'ka mata ta kar6a tana kallansa sanda yake fad'i yana sakin wani miskilin murmushi


"Fatan nasara"


"Thank u" ta fad'a tana ficewa daga wajen........ Da wani irin sauri ya 'karasa ya bud'e motar tasa ya shiga ya mata key ya jata da 'karfi kamar ze tashi sama, cikin mintunan da basu wuce 2 ba wani gumi ya fara tsatstsafo masa, shi kad'ae yasan halin da yake jinsa a yanzu, "me yake faruwa da ni?" Ya tambayi kansa, jan motar yayi ya gangara gefen titi yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da 'karfin gaske, seya jingina kansa akan steering motar yana sauke numfashi, ya kae wajen mintu na 5 a hakan se kuma ya sake kunna motar ya tashe ta kae tsaye ya wuce gidansa.....Tunda ta fito daga club d'in take binsa dan daga farko bata ganshi ba saboda irin gudun da yake, tsayawar nan da yayi itace ta sanya ta ganshi, seta dinga binsa a hankali a hankali har ya isa gidan sa ya sauka ya bud'e ya shige gidan, tana tsaye da motar a bakin 'kofar gidan tana jira ya gama shigewa itama ta shiga taga ya kullo 'kofar, seta sauka a hankali ta fara takawa tana kallan cikin layin da yake shiru babu hayaniyar mutane ta saka hannu ta ta6a gate d'in kamar zata tura....... Da sauri ya saka key ya bud'e 'kofar d'akin nasa ya shige kae tsaye ya fad'a kan gado yana jin yadda 'kafafunsa gaba d'aya suka ri'ke, seya kwanta akan gadon yayi rigingine har lokacin bugun zuciyarsa be dawo dae_dae ba, "Me yake shirin faruwa da shi ne? He asked himself again, runtse idanunsa yayi har lokacin gumi na sauka daga goshinsa dukda sanyin A.Cn dake kunne a cikin d'akin, Yana nan kwance kan gadon ya juya can 6angaren ya koma can 6angaren yama kasa tsayawa yayi tunanin mafita, seya tashi ya zaune ya zuro 'kafafunsa 'kasa yana sake lumshe idanun sa ya cusa hannayensa cikin sumar kansa, so yake ya tashi ya watsa ruwa amma 'kafafunsa sun'ki bashi wannan damar, sake komawa yayi ya kwanta yana kuma runtse idanun sa, tunda yake a rayuwar sa be ta6a jin irin wannan yanayin ba, wani sabon al'amari yake ji yana ziyartar gangar jikin sa, a hankali ya sake tashi zaune yana sauke numfashi a wahalce, ya kae wajen mintuna 10 a haka amma babu abinda ya ragu a abinda yake ji, seya mik'e cike da sassarfa ya fara takawa kamar wanda baya son taka k'asa, ya fice daga d'akin nasa har lokacin hannun sa na dafe da kansa dake wani mahaukacin sara masa, dab da d'akin ta ya dakata daga tafiyar da yake yana sake lumshe idanun sa, ya kae wajen minti 1 tsaye a wajen yana sauke numfashi sannan A hankali ya tura 'kofar d'akin dake a bud'e babu mukulli a jiki sedae a rufe take sosae, yana shiga ya saka hannunsa yayi switching light d'in d'akin yana kallan cikin d'akin, ya d'aga shanyayyun idanunsa da suka sake lumshewa haka zalika suka chanja daga aenahin colour d'in su zuwa wata daban ya kalli kan gadon, tana kwance acan 'kuryar gadon a takure cikin blanket kamar me jin sanyi, abubuwa da dama ne suka dinga bijiro masa a cikin ransa, se ya lumshe idanun sa fuskarsa babu annuri yakae hannu ya kashe 'kwan d'akin sannan ya 'karasa cikin d'akin.................



08124818273





✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION31*




____Cigaba da tafiya yayi zuwa wajen gadon wani irin sanyi na ratsa duk wata ga6a ta jikin sa, duk da A.Cn d'akin ba'a kunne yake ba saboda kashe shi da tayi dan zazza6in daya soma rufe ta, dae_dae k'arshen gadon ya tsaya yana bud'e idanun sa da suka sake shanyewa, se ya kae hannun sa da sauri ya yaye bargon gaba d'aya ya sauke tsumammun idanun sa akan ta, har lokacin baccin ta take calmly, kan ta babu d'an kwali se sumar kan ta dake d'aure da ribbom, ya lumshe idanun sa kana ya haye kan gadon yana sake jin wani sanyi na ratsa shi kamar me zazza6i, tun kafin ya gama kwanciya ya sanya hannun sa ya janyo ta da hannun sa, d'umi ne a jikin ta sosae da alama zazza6in ya rufe ta, beyi wata wata ba ya jata jikin sa cikin azama, d'umin jikin ta na k'arawa yanayin da yake ciki k'aemi, saboda sanyin da yake ji yasa d'umin jikin nata ya masa dad'i dan haka ya k'ank'ame ta cikin zafin nama kamar ze 6alla ta, a hankali hancin sa ya sauka a kanta wanda ke tashin wani irin k'amshi seya sake lumshe idanun sa ya kae hannun sa dake rawa ya fara cire ribbom d'in kan nata hakan ya bawa gashin nata damar fara barbajewa a kanta, se ya cusa kansa cikin sumar ta ta yana sake lumshe idanun sa, Cikin bacci taji ta kamar an mata wani bahagon rik'o seta d'auka ko duk zafin zazza6i ne ya sanya ta jin ta kamar a cikin kurkuru, se ta fara bud'e idanun ta a hankali harta gama bud'e su tarr, ga mamakin ta se taji ta shak'i wani sassanyan k'amshi wanda yake dab da fuskar ta, kamar ma fuskar ta akan k'amshin take, seta sake bud'e idanun nata harta gama bud'e su tarr, sake jin ta tayi kamar a cikin wani abun dan haka ta fara k'ok'arin tashi seta sake jin ta gam gam a jikin sa, bata san sanda ta saki k'ara ba tana sakin iya k'arfin ta dan ta mik'e, k'arar data saki ce ta sanya ya fara dawo dashi cikin hayyacin sa, a hankali ya sassauta rik'on daya mata wanda hakan ya sake bata damar yunk'urawa zata tashi, da sauri ya k'ara rik'o ta sosae, cikin kid'imewa ta bud'e baki zata k'walla k'ara, ya runtse idanun sa yana janyo ta jikin sa da k'arfi har lokacin bugun zuciyar sa be dawo dae_dae ba, aekuwa ta fasa ihu, kafin ta kaega rufe bakin ta yayi nasarar d'ora nasa akan nata, a zafafe ya shiga bata kiss d'in kamar ze tsinke bakin nata, tsoro, rud'ewa, firgici gami da gigicewa duka sukazo suka mata dirar mikiya, se kawae ta saki wani marayan kuka tana girgiza kae, jikin ta na wani irin kyarma har lokacin bakin ta na cikin nasa, duka k'arfin ta ta saka tana dukan sa amma be san tana yi ba, seda ya d'auki wajen minti 1 a haka sannan ya sake ta yana sauke ajiyar zuciya, aekuwa ta saka iya k'arfin ta duka ta fashe da kuka tana dafe bakin ta dake mata wani irin zugi, sannan ta sake k'ok'arin tashi daga kan gadon, ya rik'o hannun ta idanunsa a lumshe yace cikin wata murya dana gaza gane tasa ce ko kuwa dae?

"Plss help me.." Bama tajin abinda yake fad'a d'in tsabar yadda ta gama gigicewa gashi kuma gaba d'aya hankalin ta a mugun tashe yake, da azama ya janyo ta jikin sa ya sake rungume ta tietly lokaci guda yana sakin taggwan ajiyar zuciya, duk yadda take k'ok'arin k'wacewa tana kuka duk hakan be dame shi ba hasalima hancin sa ya sake kaewa kan ta yana k'ara shanshanar k'amshin dake tashi, kafin ya saka hannu ya k'arasa zare ribbom d'in gaba d'aya wanda hakan ya bawa gashin ta damar warewa gaba d'ayan sa, ya sake lumshe idanun sa yana saukar da hancin nasa kan wuyan ta da shima ke tashin wani k'amshin, gaba d'aya k'arfin ta ta sake sakawa ta ture shi se dae ko motsi beyi ba haka zalika be fasa abinda yake k'ok'arin yi ba, dan haka ta sake bud'e murya tana sakin kuka me k'arfin gaske... Se a lokacin ya fara tuna a'ina yake? Me yake k'ok'arin aekatawa? Wacece yake tare da ita? K'aramar yarinyar nan wadda ko gama zama cikakkiyar budurwa ba tayi ba, and bazawara ragowar wani, kamar wanda aka tsikara ya sake ta da k'arfi, wanda dama k'iris take jira aekuwa ta yi gefe da sauri, mik'ewa yayi har lokacin idanun sa suna a lumshe ne ya ja k'afafun sa da har lokacin suka masa nauyi ya fice daga d'akin, kae tsaye d'akin sa ya nufa ya tura k'ofar ya shige ya fad'a kan gado yayi rub da ciki yana sake lumshe idanun sa haka zalika yana sake sauke ajiyar zuciya, ya kasa tunanin komae dan koma yace zeyi ba iyawa zeyi d'in ba, yafi mintuna 10 a hakan be san sanda wani wahalallen bacci yayi awon gaba dashi ba.... A 6angaren ta kuwa gyara zaman rigar ta data fara zamewa tayi tana sake fashewa da kuka, ta kama gashin ta daya tarwatse shima ta d'aure shi, tana ganin ya fita ta sauko daga kan gadon ta kulle k'ofar d'akin sosae dan ita dae bata ga key d'in d'akin ba, seta koma kan gadon har lokacin tana jin yadda bugun zuciyar ta ke fita da sauri da sauri, ta kifa kan ta akan cinyar ta tana sake fashewa da kuka hannun ta akan bakin ta wanda take ji in dae be tsinke ba toh fa taji ciwo a jikin sa, haka ta cigaba da zama kawae dan tasan bacci dae kam babu zancen sa......


______Simrah kuwa sanda ta k'arasa k'ofar gate d'in hannu ta saka ta sake turawa se dae ga mamakin ta se taji gate d'in a rufe gam, ta sake saka hannu ta ta6a taji shi a rufe, ji tayi kamar ta saka ihu ta dawo baya jikin motar Irfan ta tsaya tana sake kallan gate d'in cikin rashin sanin abinyi...Tana nan tsaye kamar me tunanin mafita sega adaedaeta ta shigo layin, ko kallan inda adaedaetan take batayi ba har lokacin idanun ta nakan gate d'in gidan... Irfan ya biya me adaedaetan sannan ya k'araso yana kallan Simrah wadda tunda suka shigo layin yake kallan ta da mamaki, yana zuwa ya kalle ta da mamaki shimfid'e kan fuskar sa yace

"Simrah!" Juyowa tayi a hankali tana kallan sa se kuma ta fashe da kuka kamar ranta ze fita, Irfan yace

"Lafiya? Meya faru? Me kike anan?" Ya jefa mata tambayoyin duka a lokaci guda, Simrah ta share hawayen fuskar ta sannan tace tana sheshshek'a

"Nan ya taho fa!"

"Kamar yaya?" Simrah ta sake kallon gidan sannan tace

"Ehh nan dae, nan ya taho duk da haka ban sare ba na bishi se naji gidan a kulle" Irfan ya kalli gidan da mamaki kan fuskar sa sannan yace

"Kina nufin wannan gidan?" Simrah ta jinjina kae, Irfan yace

"Toh ae nan ne gidan sa!" Simrah ta d'aga kae ta kalle shi da mamaki, Irfan yace

"Shetttt!! Wallahi nan ne gidan sa, amma lallae guy d'in nan ya kwafsa mana" ya fad'a kamar ze fasa ihu dan ya riga daya gama tamawa yau ze rak'ashe ne, Simrah ta sake goge k'wallar idanun ta sannan tace ranta na suya

"Wallahi duk wata hanya da zan bi sena lalata rayuwar Azrah, bata isa ta zauna lafiya ba tunda ta shiga tsakani na da Yah Adnan, wallahi ko nawa zan kashe kuwa" Ta fad'a da alama tana jin ciwo har cikin ran ta, Irfan yace

"Noo, ki tsaya kin riga kin san bake kad'ae kika tamawa yau d'in nan ba, ni kaena wallahi na tama, amma ya zamuyi, yanzu dae ki fad'amin me zakiyi?" Simrah tace

"Kae dae kawae zaka gani" ta fad'a tana yin gaba, Irfan yace

"Ki fara sanar dani kome zakiyi kafin ki aekata mana Simrah" tace har lokacin tana tafiya

"Zan sanar dakae" Irfan yace

"Amma kya tsaya na sauke ki inda zaki je koh?" Ba tare data kalle shi ba tace

"Nagode" Irfan ya d'aga kafad'a yana shigewa cikin motar sa yaja ya bar layin cike da takaeci......



______Washe_gari kafin Asuba ya farka, a hankali ya bud'e idanun sa da suka masa nauyi har ya gama bud'e su tarr, ya mik'e zaune yana jin jikin sa kamar wanda aka masa duka, se ya dafe kansa shima da yake sara masa, a hankali kwanyar sa ta fara tunano masa abinda ya faru jiya, seya k'arasa tashi da sauri zuciyar sa gaba d'aya a cunkushe, tsaki yaja yana tunani yanzu wane kallo yarinyar nan zata dinga masa? Ya sake jan tsaki, ya kasa gane abinda

Please Login or Register in order to submit comment