Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba tare dana sani ba sedae idan abin ya lafa na dawo sa kaena gida, ko kuma idan wasu sun ganni su dawo dani gida sumin fad'a akan abinda nake yi, sedae na fad'a musu bansan ina aekatawa ba, zafin ciwo ne kawae, mutane kad'an ke lek'oni a wannan yanayin suna taemaka min, seda na kusa wata ina fama da wannan ciwo se kuma cikin ikon Allah Allah ya sawwak'e min ya yaye min ciwon amma nayi muguwar ramar nan, wasu mutanen ma har gudu na suka fara suna tunanin ko k'anjamau gare ni shiyasa kullum nake ramewa, wasu sun yadda yayinda wasu basu yadda ba, a wannan lokacin ne gaba d'aya hankali na ya koma yadda zanyi na nemi Azrah na nemi yafiyar ta dan bana tunanin ciwon ya tafi kenan, koma bashi ba nasan wani ciwon ze iya kuma zuwa min saboda abubuwan da suka dinga fad'o min daga wannan se wannan, banyi tunanin zan sake ganin ki ba Azrah, se gashi cikin ikon Allah mun sake had'uwa, ni kuma bazan ta6a bari wannan damar ta wuce ni ba koda menene kuwa Azrah zaki min sena tabbatar kin yafe min tukunna, bazan 6oye muku ba wallahi na cutar da rayuwar Azrah, na cutar da ita sosae, amma ki kalle ni Azrah, ki kalli yadda rayuwa ta juya min, ki kalli yadda na zama kiyi duba da tarin dana sanin nan da nayi ki yafe min don Allah...." ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka, Azrah ma kukan take yi sosae hawaye na zuba akan kuncin ta, daga inda yake ya runtse idanun sa yana jin yadda kukan nata ke masa zafi dukda babu sauti yana jin kamar yaje ya rarrashe ta, amma kuma idon Ammi dana su Dad ya hana shi yin hakan, Ammi ta share k'wallar data taru a idanun ta sannan ta kalli su Abba da suka mik'e tare, Abba yace

"Bari zamu d'an tattauna ne.." jinjina kae Ammi tayi su kuma suka fice daga gidan, Inno ta bisu da kallo sannan ta dawo da duban ta kan Azrah tana share hawayen da yak'i tsayawa da zuba tace

"Azrah ke nake jira don Allah ki furta cewar kin yafe min har cikin ranki, koda yake nasan hakan me wuya ne, ba lallae ya samu ba" Ammi tace

"Kada ki damu, duk wani d'an adam ajizi ne, kuma In Sha Allah Azrah ta yafe miki har abada.. Ki fad'a mata da bakin ki taji" Ammi ta k'are maganar tana kallan Azrah, se a lokacin ta d'aga jajayen idanun ta ta kalli Inno cikin tausayawa halin data tsinci kanta a ciki tace

"Na yafe miki Inno, dukan ku ma ni na yafe muku, Allah ya yafe mana baki d'aya.." ta k'arasa maganar tana sake share k'walla

"Kin yafe mana Azrah?.." Inno ta fad'a hawayen dake zuba a idanun ta na tsayawa cakk da zuba, ta mugun yin mamakin yadda lokaci d'aya Azrahn ta yafe mata, seta sake fashewa da kuka cikin sake dana sanin halin ta da nadama

"Tirr da halin mu mukam, wallahi naji kunya" Inno ta fad'a tana girgiza kae cikin kuka, har yanzu Azrah ta kasa dena mamakin yadda Innon ta chanja kamar wadda tayi shekaru da dama tana jinya... Dad ya kalli Abba yace

"Yanzu me kake tunanin za' ayi kenan?" gyara tsayuwar sa Abba yayi yana rungume hannayen sa a k'irji sannan yace bayan ya d'an sauke ajiyar zuciya

"koma dae menene ya faru, kome suka mata sun dae rik'e min 'ya, sun mata ba dae_dae ba amma gata nan tana cikin k'oshin lafiya babu abinda ya same ta cikin ikon Allah, kuma ga dukkan alamu sunyi nadamar abinda suka aekata saboda haka In Sha Allah zanyi abinda ya dace, maganar mijin nata ma In Sha Allah semu duba al'amarin idan yaso shi yaron nata a nemo shi a mik'a shi hannun hukuma tunda dae me laefi ne" jinjina kae Dad yayi cikin na'am da zancen aminin nasa yace

"Hakane, Allah ya taemaka ya bada lada.."... Da wani irin sauri ta shigo cikin gidan ko sallama bata iya yi ba jikin ta na rawa ta fad'o tsakar gidan, babu wanda ya lura da shigowar ta dan duk ba k'ofar gidan suke kalla ba, Inno kad'ae ke facing wajen ita kuma har lokacin kanta na k'asa ne, seda ta tsaya ta d'an kalli mutanen data gani sannan cikin rawar murya ta furta

"Azrah!!" da sauri Azrah ta juya dan yadda taji muryar kamar tasan me ita, aekuwa tayi kyakykyawan gani, da sauri babu 6ata lokaci ta mik'e tana kallan ta tace itama muryar ta na rawa

"Hauwa'u.." ta fad'a tana yin gaba, itama hauwa'un matsowa tayi cike sa sassarfa suka had'u a tsakiyar tsakar gidan, babu 6ata lokaci suka rungume junan su lokaci d'aya suna fashewa da kuka, Ammi da Don duka suka bisu da kallo, babu wanda ya musu magana har seda suka saki junan su da kansu sannan Hauwa'u tace tana kallan Azrah

"Azrah ke d'in ce?" ta fad'a tana k'arewa Azrahr kallo da ganin yadda ta chanja gaba d'aya kamar ba ita ba, jinjina kae kawae Azrah tayi tana rik'e da hannun Hauwa'u tace

"Nice Hauwa'u.." sake kallan ta Hauwa'u tayi sannan takae hannun ta fuskar ta ta goge hawayen sannan tace

"Azrah ina kika shiga? Ina kika tafi babu labarin ki kwata kwata? Ina mijin naki? Shine ya 6oye ki ko kuwa?" ta fad'a dan duk wasu alamu sun nuna Azrahn bata hannu mara kyau ne, d'an satar kallan inda yake zaune tayi, ganin inda take kallan yasa itama Hauwa'un ta kalla, yana nan kamar wanda aka sassak'a har lokacin a wajen gaba d'aya hankalin sa nakan Azrah, Hauwa'u ta d'auke kae daga kallan sa tace

"Shine mijin naki?" a hankali ta gyad'a kanta kawae, kafin Hauwa'un tace komae Azrah ta kama hannun ta tace

"Muje ku gaesa da Ammi na.." A'ah mamaki fa ya sake rufe Hauwa'un, kawae dae tabi Azrahn kamar wata doluwa har suka k'arasa inda Ammin take dukan su suka zube, Ammi tayi murmushi tana kallan Hauwa'u tace

"Sannu kinji en nan.." se a lokacin Hauwa'u ta iya furta har lokacin mamaki be bar fuskar ta ba

"Ina yini?"

"Lafiya k'alau, mun same ku lafiya?" Hauwa'u ta k'ak'alo murmushi sannan tace

"Alhamdulillah" ta fad'a tana maeda duban ta ga Azrah cikin neman k'arin bayani, murmushi Azrah tayi sannan ta kalli Hauwa'un sanda take cewa Don

"Ina yini?"

"Kina lafiya?" ya fad'a cikin basarwa yana sake kallan matar sa, dan harga Allah ya gaji da ganin kukan nan nata, Hauwa'u ta dawo da duban ta kan Azrah sannan tace

"Kin had'u da iyayen kine Azrah?" jinjina kae Azrah tayi sannan a hankali ta fara bawa Hauwa'un labari tiryan tiryan, tunda ta fara maganar yake kallan ta yadda take magana cikin nutsuwa d'an k'aramin bakin nan nata na motsawa a hankali, seya lumshe idanu yana sake jin wata k'aunar ta na ratsa shi, abin har mamaki yake bashi, be ta6a tunanin ze tsinci kansa dumu_dumu cikin k'aunar yarinyar ba, se gashi lokaci guda k'aunar ta ta masa mugun kamun da baze iya misaltashi ba... Wajen k'arfe 3 ne suna zaune a tsakar gidan ita da Hauwa'u suna sake hirar yaushe gamo, yayin da Ammi ke gefe tana d'an jan Inno da hira wadda ta kasa sakewa dan gani take kamar iyayen Azrah ba zasu yafe mata abinda ta yiwa d'iyar su ba, wayar Ammi ce tayi k'ara ta duba me kiran sannan ta d'aga, daga can 6angaren Abba yace

"Ku shirya ku fito yanzun zamu je gidan me gari" da "toh" ta amsa sannan ta kalli Azrah da suke ta hirar su da alama tuntuni akwae sabo me tsanani a tsakanin su tace

"Azrah..ku tashi Abban ku na jiran mu a waje zamuje wajen me gari.." tare suka mik'e ita da Hauwa'un, bayan Ammi ma ta mik'e ta kalli Inno tace

"Ba zaki je ba?" girgiza kae Inno tayi kana tace

"A'ah Hajiya kuje kawae" ta fad'a ba tare data kalli Ammin ba, Ammi tayi murmushi sannan ta girgiza kae kawae suka fice daga gidan tare, se a lokacin Hauwa'u ta gaesa dasu Abban sannan Dad ya kalli Azrah yace

"Ina ita matar gidan take?" Azrah tayi k'asa da kanta sannan tace

"Ammi tace tazo muje tace baza taje ba"

"Maza kuyi mata magana ta fito muje, meye amfanin hakan" ya fad'a yana bud'e murfin motar ya shiga bayan ya bawa bodyguards d'in sa umarnin su jira anan base sun bishi ba, babu musu Azrah ta juya zuwa cikin gidan.... Girgiza kae Me gari ya shiga yi bayan ya gama sauraron jawabin su Dad, cike da mamaki da al'ajabin abinda suka fad'a d'in, seda yayi shiru na wajen minti 1 sannan yace

"Lallae Allah me iko da d'aukaka, Ikon Allah" ya fad'a har lokacin da mamaki sannan ya d'ora da fad'in

"Toh Allah ya tsare ya kuma kare mu, kuma In Sha Allah yau base gobe ba za'a wanke er tahalikar nan daga kallan da ake mata, ikon Allah kenan" ya k'arasa zancen da fad'in haka yana sake jinjina kae... Taron gaggawa me garin yasa aka shirya a cikin k'auyen mata da mazan su yara da manya, cikin k'ank'anin lokaci kuwa aka taru a k'ofar gidan me garin inda aka saba taruwa idan za'ayi taro ko wani abun makamancin wannan, gyaran murya me garin yayi sannan ya fara da fad'in

"Assalamu Alaekum, ba wani abu bane yasa muka tara ku anan ba illa dan mu sanar daku wani muhimmin abu, wannan da kuke gani.." ya fad'a yana nuna Azrah dake zaune kanta a k'asa sannan ya d'ora da fad'in

"Da yawan ku nan kun santa, ba wata bak'uwa bace, Azrah ce er gidan Malam Habu.." nan fa kallo ya dawo kan Azrah da har lokacin kanta ke k'asa, dan mutanen sun mata yawa gaba d'aya ta kasa sukuni, shi kam gogan na can gefe ya cika yayi fam, haushi kamar yayi me, ba dan wannan d'in wani abu ne da za'ayi dan a wanke ta ba, da wallahi baze barta ta zauna a cikin wad'annan mutanen da aka had'a harda maza ba

"Kamar yadda mutane da dama ke mata kallan tsintacciya wadda bata da iyaye, toh yau kam komae ya k'are domin kuwa wad'annan da kuke gani sune iyayen ta" ya k'are maganar yana nuna inda su Ammi ke zaune, take wajen ya d'auki hayaniya kowa na mamakin yadda aka nuna wasu wad'anda da alama kud'i ya gama wadatarsu akace sune iyayen ta, ga kuma yadda itama Azrahn ta chanja kamar ba ita ba.. Ba'a tashi daga taron ba seda me gari ya tabbatar ya wanke Azrah tass, nan da nan gari ya d'auka ko'ina zancen dawowar Azrah da kuma bayyanar iyayen ta akeyi, abinka da k'aramin gari kafin kace mene wannan maganar ta ratsa lungu da sak'o na k'auyen, kowa da abinda yake fad'a, wasu na fad'ar albarkacin bakin su, wasun kuma da basu je taron da me garin ya had'a ba suna fitowa dan su kashe kwarkwatar idanun su su ganewa kansu abinda ake fad'a d'in, shin gaskiya ne ko kuwa kawae rad'e rad'i ne.. Basu suka bar k'auyen Kima ba se dab da maghrib, bayan Dad ya ajjewa Inno kud'i masu dama, ba suyi mata maganar Baban Ilyasun ba sun bar maganar a tsakanin su ne, Inno ta dinga kuka sosae tana sake dana sanin abubuwan data aekatawa Azrahn, lallae Allah me iko da d'aukaka yau ga Azrah da iyayen ta, iyayen nata kuma masu kud'i da mutunci, wad'anda duk irin abinda ta aekatawa d'iyar su hakan be hanasu taemaka mata ba, ko bayan da suka tafi ma ba tayi shiru ba ta cigaba da kukan tana sake dana sanin abinda tayiwa Azrahn, sanda zasu tafin kuwa Azrah da Hauwa'u sun sha kuka sosae, amma babu yadda suka iya haka suka rabu ba dan sunso ba, se dae sunyi exchanging contact saboda saurayin Hauwa'un ya siya mata waya, haka suka rabu da alk'awarin dinga kiran juna.


... Gaba d'aya jikin ta a sanyaye yake sanda ta shiga d'akin nata, ta nemi gefen gado ta zauna k'wak'walwar ta gaba d'aya a cunkushe, seda dae taga tunanin ba abinda ze tsinana mata sannan ta mik'e ta fad'a toilet tayi wanka kana ta fito d' aure da towel da hijab dogo a saman towel d'in, a hankali ta k'arasa ta tsaya gaban wardrobe ta bud'e tana kallan ciki, komae take a sanyaye take har yanzu ta kasa dena tunanin mutanen duniya, rayuwar ta ta baya da kuma ta yanzu tana sake dawo mata, sam bata ankara da shigowar sa cikin d'akin ba se sanda ya matso dab da ita, k'amshin turaren sa na Trussardi ya ziyarci hancin ta, seta d'an yi baya kad'an wanda hakan ya bata damar shigewa cikin jikin sa, ya kuwa saka hannu ya rik'e ta sosae ta hanyar zagaye ta da hannayen sa sannan yace kamar me rad'a

"Tunanin na mene?" bata iya cewa komae ba se bugun zuciyar ta daya k'aru tayi shiru, seya sanya hannun sa ya juyo da ita suka koma suna facing juna, hakan ya k'ara musu kusanci sosae kanta na a k'asa, ya saka hannun sa ya d'ago face d'in ta yana kallan ta sosae, ta runtse idanun ta dan yadda taji bugun zuciyar ta ya k'ara gudu, ya fahimci yadda take a tsorace dan haka ya saki fuskar ta ta, sannan yaja hannun ta zuwa kan gadon ya zaunar, kana ya koma cikin wardrobe d'in ya d'auko wata doguwar riga me taushi sannan ya dawo kan gadon, tana nan zaune inda ya barta, ya k'arasa zuwa inda take ya ajje rigar kan gado kana ya matsa kusa da ita sosae, a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in jikin ta sannan ya fara k'ok'arin cire shi, da sauri ta d'ora hannun ta kan nasa hannun ta d'aga idanun ta da sukayi rau rau ta zuba su cikin nasa lumsassun idanun ta fara girgiza kae, ya d'an kalli hannun nasu sannan ya maeda cikin nata idanun, seya lumshe idanun sa kana ya bud'e har lokacin a kanta yace a tausashe

"Nasan kin gaji, pls lemme help u.." ya k'arasa fad'a yana sake zuba k'wayar idanun sa cikin nata, seta janye nata idanun da sauri, ya maeda kansa kan hannun sannan ya sanya hannun sa ya d'auke shi, ya saka hannun sa ya cire hijab d'in ya ajje gefe, runtse idanun ta tayi tana jin yadda wata irin kunya ke lullu6e ta amma ta rasa dalilin da yasa yau d'in ya mata wani irin kwarjini da har ta kasa masa musu, ya d'an yi jimm yana kallan ta lokaci guda kuma yana k'ok'arin saeta bugun zuciyar sa, seda taji hannun sa akan towel d'in jikin ta sannan ta d'aga kae ta kalle shi kamar zatayi kuka tace

"Pls...ka bari zan iya sakawa" seya lumshe ido sannan ya d'auke hannun sa ya zagaya ya koma kan gadon ya kishingid'a yayi pillow da hannun sa idanun sa a lumshe, mik'ewa tayi a hankali sannan ta saci kallan sa, ganin idanun sa a rufe ya sanya ta d'aukar rigar ta zura kana ta zame towel d'in ta k'asa, tana shirin d'aukar hijab d'in zata saka ta jiyo muryar sa bayan ya bud'e idanun sa duka a kanta

"A'ah fa ki k'yale jikin ki ya huta Madam, kayan sunyi yawa" ya fad'a hannun sa dafe da hijab d'in ya d'auka ya jefa shi gefe sannan ya sake watsa mata idanun sa yana mik'a mata hannu yace

"Zo.." hannun nasa tabi da kallo kafin ta maeda idon ta kan fuskar sa, ya jinjina mata kae gami da lumshe idanun sa kusan lokaci guda, kamar tayi tafiyar ta ko kuma ta rabu dashi haka take ji amma se taji kamar hakan be dace ba, dan haka a hankali ta taka ta zauna kan gadon kana ta mik'a nata hannun, ba tayi tsammani ba seji tayi ya jata ta fad'a cikin jikin sa sannan ya sanya hannu ya lullu6e ta a cikin k'irjin nasa yana rufe idanun sa, shiru tayi yana jin yadda zuciyar ta ke bugu wanda ya wuce misali, bece komae ba seda yaji ya fara saetuwa sannan a hankali yakae bakin sa kan kunnen ta ya furta

"Oh yah Sleep..." ya fad'a da wani irin salo kuma kamar me rad'a, seta lumshe idanun ta a hankali tana jiran baccin ya d'auke ta amma seda suka fi minti 10 a haka kafin baccin ya fara fizgar ta, babu jimawa ya kwashe ta gaba d'aya, seda yaji tana sauke numfashi akan k'irjin sa wanda hakan ya tabbatar masa tayi bacci sannan ya sake gyara mata kwanciya still dae a jikin nasa kana shima ya lumshe idanun sa dan yin baccin... Da sauri ya bud'e idanun sa k'irjin sa na bugu da k'arfin gaske saboda wani mummunan mafarki da yayi, a hankali ya tashi zaune sannan ya zame ta ya kwantar kan gadon ya lullu6e ta da bargo kana ya mik'e ya fice daga d'akin, kae tsaye d'akin sa ya nufa ya kunna light d'in d'akin, sannan ya koma ya zauna kan gado zuciyar sa a matuk'ar cunkushe, haka bugun zuciyar sa yak'i saetuwa, yafi minti 5 a haka kamar me tunani sannan ya mik'e ya janyo wata tsohuwar k'aramar akwati akan wardrobe wadda be dad'e da d'akko ta daga d'akin sa na gidan su ba ya dawo ya zauna kan gadon sa ya sake karkad'e akwatin saboda yadda tayi k'ura, seya saka hannu ya danna password ya bud'e ta sannan ya fara fito da hotunan dake ciki duka ya zube su kan gadon, seya sanya hannu ya d'auki d'aya daga cikin hotunan sannan yayi amfani da hannun sa wajen goge jikin hoton yana kallan kyakykyawar matar da take ciki, ya dad'e yana zagaye hoton da hannun sa kafin yakae hoton kan k'irjin sa ya rungume kana cikin k'aramin sauti ya furta

"Mom..."





✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION55_56*



___Ya fad'a idanun sa a kulle, da gudu bugun zuciyar sa ke fita yana sauke numfashi a hankali, rabon sa da bud'e akwatin nan har ya manta, rabon daya tuna Mom d'in ballantana yabi ta da addu'a shima duk ya manta, me yake damun k'wak'walwar sa? shin wane irin d'a ne shi? Kowacce uwa na fatan ta riga 'ya'yan ta mutuwa ne dan ta dinga samun masu yi mata addu'a, amma kenan banda shi a cikin masu yiwa uwar data riga shi mutuwa addu'a, wannan wane irin abu ne

"Ya Ilahil alameen" ya furta akan la66an sa sannan wani hawaye me d'umi ya samu damar gangarowa daga idanun sa na dama, sosae zuciyar sa ke masa zafi yana jin yadda yake tuhumar kansa da da laefi, meyasa yayi hakan? Meyasa baya ma tuna Mom d'in a gaba d'aya rayuwar sa, kullum tunanin sa na kan Mami matar da ba ita ta haefe shi ba amma ya d'auki gaba d'aya soyayyar mahaefiyar sa ya d'orawa Mamin, baya ko bi takan uwar data haefe shi

"Ya Allah ka yafe min, Astagfirullah" ya fad'a har lokacin idanun sa na rufe.... Sanda ya dawo daga masallacin kae tsaye wayar sa ya d'auka ya danna kiran Dad, daga can 6angaren Dad da mamaki ya kalli sunan Son dake yawo akan screen d'in wayar, ya kauda duk wasu tunani sannan ya d'aga wayar ya kara a kunnen sa, Don yace

"Barka da wannan lokaci Dad" shiru Dad yayi yana karanto sauyi daga cikin muryar d'an nasa dan haka ya kasa amsa gaesuwar tasa yace

"Lafiya dae naji muryar ka wani iri?" Ya d'an shafa kwantacciyar sumar kansa sannan yace

"Ehh Dad, dama kira nayi na sanar dakae inaso naje Sudan ne.." daga inda Dad ke tsaye ya nemi waje ya zauna yana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa wanda har seda ya bayyana a cikin muryar sa sanda yake fad'in

"Yaushe zaka je" ya d'an yi jimm, baya tunanin ze iya wata tafiya a yanzun ba tare da ita ba dan haka yace

"Cikin kwana 2 dae In Sha Allah nake so muyi tafiyar, toh amma ita bata ta6a zuwa wata k'asar ba shiyasa bansan kwanakin da zamu d'auka ba.."

"Toh shikenan, daga zarar ka gama d'in seka sanar dani, saboda nima inaso naje" Dad ya fad'a

"Ohk In Sha Allah" daga haka ya katse wayar ya ajje ta kan gadon sa sannan ya fice daga d'akin zuwa nata. A hankali ya tura k'ofar d'akin idanun sa na a cikin d'akin, akan dadduma ya hango ta tana zaune tana karatun Qur'an, ya k'arasa ya nemi kan gadon ya zauna yana cigaba da kallan ta, seda takae k'arshen surar da take sannan ta rufe Qur'anin ta ajje shi kana tayi addu'a ta mik'e, se a lokacin ta lura dashi yana zaune hannayen sa hard'e a k'irjin sa yana kallan ta, ta sadda kanta k'asa sannan tace a hankali

"Ina kwana?" Ya lumshe ido dan yadda muryar ta ta ta ratsa shi yace

"Kin tashi lafiya?" Ba tare data sani ba ta d'aga narkakkun idanun ta ta zuba su akansa tana so ta karanci a yanayin da yake, saboda yadda taji muryar sa ta chanja haka kuma tayi wani irin sanyi, bata iya amsawa ba se yin gaba da tayi bayan ta d'auke idanun ta daga kansa tana shirin fita daga d'akin yace

"Ina zuwa?"

"Kitchen.." ta fad'a a sanyaye, ya jinjina kae kana yace

"Ohk.." daga haka ita kuma ta fice daga d'akin zuwa kitchen.. Sanda ta gama had'a break d'in seta kwashe su kamar yadda ta saba ta ajje su kan dinning, bata jin yunwa gaba d'aya dan haka tana gama jerawa ta fara k'ok'arin komawa saman, dae_dae lokacin shi kuma yake sakkowa daga saman, ganin sa ya sanya ta dakatawa a inda take, ya k'araso yana kallan cute face d'in ta wadda kamar kullum k'ara mata kyau akeyi, ita kam ta kasa kallan sa kanta nata wani wajen tana kallo, yace sanda ya k'araso dab da ita ba tare data lura ba, seda ta fara jiyo muryar sa dab da ita sanda yake fad'in

"Ina zaki je?" Seta fara k'ok'arin yin baya ya sanya hannu ya rik'o ta sosae har jikin su na gogar na juna, duk seta diririce ta kasa furta komae, bata san meyasa yake yawan son jikin su ya had'u ba

"Uhmm?" Ya katse mata tunani da fad'in hakan, a hankali ta d'aga bakin ta tace

"D'aki" ya d'an 6ata rae kad'an sannan yace

"Abincin fa?"

"Am full" ta fad'a a tak'aece har lokacin bata kalle shi ba

"Da kika ci mene?" Ya fad'a yana sake zagaye fuskar ta da idanun sa, seta girgiza kawae tana d'an tura baki, yabi bakin nata da kallo sannan ya maeda idanun sa kan fuskar ta yace bayan ya d'an had'e fuskar sa

"Ashe kuwa zanyi ma wata d'ura" ya fad'a yana janta zuwa kan dinning d'in sannan yaja mata kujera ta zauna kana yayi serving nata, ya tura plate d'in gaban ta sannan yace

"Uhmm ci..." Bata iya d'aga ido ta kalle shi ba se taja plate d'in ta d'an tsakura kad'an sannan ta ture tace

"Na k'oshi.." ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa, yace

"Ahh wait mana Madam.." yaja kujera ya zauna yayi serving kansa sannan yace

"Bari na gama ci den i will let u go" ya fad'a yana fara cin abincin, ba yadda ta iya haka ta zauna yana cin abincin gaba d'aya hankalin sa na kanta, duk wani motsi nata idanun sa na kanta, gaba d'aya ta kasa sukuni se mutsu mutsu take yi idanun sa sun mata mugun nauyi amma haka ta daure ta cigaba da zama har seda ya gama sannan ta kwashe da sauri ta kae kitchen... Tun daga ranar ya kasance da safe idan ta tashi zata gaeshe shi, zata yi break ta ajje kan dinning se kuma abincin dare da takeyi saboda a kwanakin gaba d'aya baya yini a gida, idan ya fita tun safe se cikin dare yake dawowa lokacin ma tayi bacci basa sake had'uwa se safiya, a 6angaren sa kuwa gaba d'aya hankalin sa ya tafi kan shirye shiryen su na tafiya Sudan da kuma ginin da yasa aka fara masa dan ya gaji da wannan gidan, shiyasa abubuwa suka masa yawa, ba sosae ma yake samun kansa yanzun ba, be sanar da ita zancen tafiyar ba se ana saura kwana d'aya zasu tafi.. Ita dae taga kwana biyun nan gaba d'aya kamar he is busy, dan ko ita kanta ba sosae take ganin sa ba musamman kuma da rana amma yau wajen k'arfe 10 ne taga ya shigo d'akin nata, ta d'aga

Please Login or Register in order to submit comment