Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Momy na ganin su ta k'araso da sauri tana fad'in

"Adnan.." tare suka juya dan ganin daga inda maganar take fitowa, mamaki ya kama shi yana tunanin abinda yasa ta tsaeda shi, Simrah kuwa tunda ta gansu ta koma inda ta fito, Momy ta k'araso ta fashe da kuka tana kallan Don tace

"Don Allah ka yafewa Hadeeza ko Allah ze yafe mata ta dena ganin wad'annan bala'an dake ta fad'a mata, kaga yanzun nan suka yi hatsari ita waccan k'awar ta ta Kaltum k'afar ta ta lalace se an yanke ta, ita kuma tana can a kwance ana tunanin 6arin jikin ta ya shanye.." Kallan ta yake fuskar nan tasa a d'inke tsaff ya koma aenahin miskilin sa, kamar ba zece komae ba se kuma ya bud'e bakin sa a hankali yace

"And so?" ya fad'a yana tsare ta da idanun nan nasa, Momy ta girgiza kae tana kallan likitan dake gefen su yana karantar su su duka tace

"Don Allah likita ka saka baki ya yafe mata, sunan da kaji tana ambata bana kowa bane se nashi.." d'an murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar DR ARMAN ALQASEEM ARAB (Baby) sannan ya girgiza kae yace yana kallan Don, seya matsa ya dafa kafad'ar Don dake k'ok'arin tafiya yace

"Haba mana Mr Man, daga ganin yanayin ta tayi nadama pls kace ka yafe mata" bin hannun Dr Arman d'in yayi da kallo sannan ya d'auke kansa yana fad'in

"Is ohk.."

"Allah ya yafe mana baki d'aya?" Arman ya fad'a yana kallan Don, lumshe idanu yayi kafin yace akan la66an sa

"Ameen.." daga haka yaja hannun Azrah da tunda suka fara magana take kallan su amma ba tace komae ba.... Tunda ya fara driving yake k'ok'arin saeta kansa kar ya 6ata wannan muhimmiyar ranar, amma hakan ya citira, seya koma asalin Don d'in sa miskili me yawan had'e rae, mara fara'a.. Tana lura da yanayin sa amma da yake tasan abinda ya maeda shi hakan seta maze ta bari idan suka koma gida tasan yadda zata sakko dashi. Yana shirin sauka daga motar dan zuwa ya bud'e mata kamar koda yaushe ta sanya hannun ta ta dafe nasa hannun, seya dakata ya juya ya kalle ta, ta langa6ar da kae tana ta6e baki kamar zatayi kuka gami da girgiza kae kamar wata yarinya er goye, tilas abinda tayi d'in ya sanya shi sakin murmushi yana sanya hannun sa yaja kumatun ta, yana sake shirin fita ta sake rik'o hannun nasa

"Kayi hak'uri ka dena fushi, Allah kuwa bakya kyau" ta fad'a a narke, seya lumshe idanun sa yana sanya hannu ya janyo ta sosae ta dawo kusa dashi sosae yace yana kallan cikin idanun ta

"Koh?" jinjina masa kae tayi, ya d'auki hannun sa ya d'ora akan marar ta yace

"Ko dan wannan ae na dena fushin" hannun ta ta kae ta d'ora akan nasa hannun tana murmushi, ita har yanzu ta kasa yadda wae ita Azrah ita keda ciki

"Ina k'aunar ki Babe.." ya fad'a yana sake zuba mata lumsassun idanun sa, seta lumshe nata idanun kafin ta rungumi shi sosae bayan ta zagaye bayan sa da hannayen ta ta furta a hankali

"Nima ina k'aunar ka miji na.." wani irin farin ciki ne yazo ya sake masa dirar mikiya, ya sake k'ank'ame ta cikin jikin sa yana jin kamar ya maeda ta cikin nasa, sunfi minti 1 rungume da juna kowannen su na saurarar bugun zuciyar d'an uwan sa.


Kwanakin da suka biyo baya wata irin kulawa ta musamman yake bata, da k'yar yake barin ta tayi komae k'ank'antar aeki, k'aunar ta kuwa se wadda ta dad'u kullum ji yake kamar ana k'ara masa son ta ne, ta 6angaren ta ma haka take ji kullum k'ara son shi take yi, tuni ya chanja daga Don zuwa Adnan, wannan girman kan gaba d'aya tayi amfani da soyayyar da yake mata ta sauya shi, ta sake nuna masa muhimmacin wanda ya girme shi, se dae har yanzun miskilancin nan yana nan, idan yana tare da ita ne kawae yake manta waye shi, ya maeda ta kamar wata jaririya saboda kulawa, jin ta take kamar wata sarauniya, tana sake godewa Allah akan ni'imomin da yayi mata. Tuni Meemarh ta dawo gidan saboda Ammi da tace baze yiwu kullum seya fita restaurant ya siyo abinci ba, idan Meemarhn tazo ta d'an yi kwanaki seta koma gida Meemee kuma tazo, a gaban kowa nuna mata soyayya yake shiyasa idan suka zo su kafi zama a d'akin da suke sauka, tuni kuma Ammi ta hana ta shan kayan zak'i da sanyin nan da suka zame mata kamar abinci, duk da hakan dae wasu abubuwan kawae take iya ci dan haka dole se an had'a mata dasu yoghurt d'in ko furar take iya sha, amma Ammi tace ko zata sha d'in toh kar tasha me sanyi, haka dae ba dan taso ba take shan su a hakan babu sanyi har daga baya dae tazo ta saba.


... Yana zaune akan gadon ya kishingid'a da pillow a bayan sa yayin da take kwance akan cinyar sa, waya yake dannawa yayin da d'ayan hannun nasa ke kan sumar kanta dake a bud'e yana d'an shafawa, jin da yayi ta fara sauke numfashi ya sanya shi d'ago ta yana fad'in

"Matso kiyi baccin ki.." ya fad'a yana mata masauki akan faffad'an k'irjin sa dake yalwace da kwantacciyar gargasa bak'a sid'ik, seta kwanta kuwa tana shak'ar daddad'an k'amshin dake fita daga jikin sa, tana k'ok'arin lumshe idanun ta idanun ta ya sauka akan wayar sa da yake cikin photos yana deleting abubuwa marasa amfani a wayar sa, yana shirin goge hoton data gani ta rik'o hannun sa, seya dakata yana kallan ta sanda take fad'in

"Mu gani.." ta fad'a tana kar6ar wayar, hoton Irfan ne seta runtse idanun ta tana tuna inda tasan mutumin, ashe shine? amma yaso ya yaudare ta da sifar sa, duk se taji babu dad'i yadda da take wa Irfan d'in kallan mutumin arzik'i shi kuma take masa kallan mutumin banza, ashe abin ba daga nan bane, kar6ar wayar yayi ya ajje ta gefe sannan ya sake gyara mata zama yace

"Tunanin fa?" se tayi rau rau da idanun ta amma ba tace komae ba, ya sanya hannu ya d'ago fuskar ta yana kallan ta ya lumshe mata idanu, seta d'an yi murmushi kad'an sannan tace

"Meemarh na jira na" ta fad'a tana d'an tura baki kad'an, yakae bakin sa ya ciji lips d'in ta na k'asa wanda har seda tayi er k'ara kad'an tana yamutsa fuska tace a shagwa6e

"Allah sena rama.."

"Oh really?" ya fad'a yana d'age mata girar sa d'aya, seta jinjina kae kawae tana sake 6ata fuska

"Uhmm toh rama" ya fad'a yana matso da bakin sa saetin nata, seta maeda kanta k'irjin sa tana dariya kawae, shima murmushin yayi sannan ya d'ora hannun sa kan shamulallen cikin ta sannan yace

"Ki barni nayi hira da baby na.." ya fad'a yana zagaye cikin nata da hannun sa, sannan ya d'ora da

"Kinsan itama yanzun tana can suna hira da nata Babyn Uhmm?"

"Yunwa nake ji toh" ta fad'a bayan ta d'ago kanta

"Ohk bari na samo miki wani abun" ya fad'a yana zame ta daga jikin sa, yana shirin fita tace tana zaro manyan idanun ta

"Babe ba riga a jikin ka fa.." murmushi yayi yana shafa sumar kansa dan shi sam ya manta ba rigar a jikin sa, hankalin sa gaba d'aya ya tafi kan abinda ze samo mata tacin, ya dawo ya d'auki rigar ya sanya sannan ya fita.







_BAYAN WATA BAKWAE_

*** *** ***
Abubuwa da dama sun faru a cikin watannin, ciki kuwa hadda komawar Baban Ilyasu gida sedae ya koma ne da ciwon 6arin jiki sakamakon wata mummunar fad'uwa da yayi, kamo Ilyasu aka mik'a shi ga hukuma, bikin Hauwa'u, yankewa Hajja Kaltum k'afar ta d'aya data lalace, komawar Mami gidan su Simrah itama da shanyayyen jiki, fitowar Irfan daga gidan yari...




.... Fitowar sa daga wanka kenan yana tsaye bakin mirror yana goge jik'ak'k'iyar sumar kansa, tunda ya fito take bin sa da idanu, idan ta kalle shi seta maeda kae ga chocolate d'in da take sha, tun d'azun yana kallan ta ta cikin mudubin amma bece mata komae ba, seda ya gama shiryawar sannan ya koma inda take zaunen sanye cikin doguwar rigar yadi wadda ta tsaya mata iya gwuiwa, ta sake yin haske sosae ta kuma yi k'iba ta zama babbar mace sosae, ga ciki nan turtsetse a gaban ta haehuwa yau ko gobe, k'arasawa yayi ya kar6i ledar chocolate d'in yace a lokaci guda

"Ko dae in zauna ki cinye ni.." turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace

"Chocolate d'ina.." ta fad'a tana tashi daga kishingid'en da take kamar zata k'wace, yace

"Uhmm ko dae zamu gwada k'wanji ne?" ya fad'a yana kafe ta da idanun sa, ganin tana sake yamutsa fuska kamar zatayi kuka ya sanya shi mi'ka mata chocolate d'in ta yana fad'in

"Madam rigima" ta kar6a tana murmushi, a hankali ya furta iya kan la66an sa

"Er lukuta ta.." seta kalli bakin nasa sannan tace kamar zatayi kuka

"Me kace?"

"A'ah babu komae..muje in kae ki parlour" ya fad'a yana sake matsawa kusa da ita, ya kama bakin ta cikin nasa ya shiga kissing nata seda ya tsotse duk wani zak'in chocolate d'in dake bakin ta sannan ya sake ta yana lumshe idanu kana ya d'auke ta gaba d'ayan ta zuwa parlourn, ya sauke ta akan kujera sannan ya gyara k'asan carpet d'in ya shirya mata pillows kafin ya sakko da ita k'asan yace

"Zan tafi.."

"Allah ya tsare.." ta fad'a da murmushi kan fuskar ta tana kallan kyakykyawar fuskar sa, yace

"Ki kula min da kanki da baby na" ya k'arasa maganar yana shafa cikin nata, ta lumshe idanu tana d'ora hannun ta kan nasa, wayar sa ya d'akko ya kira number Meemee, ringing 1_2 ta d'aga yace

"Ki fito ki mata hira zan fita.."

"Toh yaya.." ta amsa masa sannan ya katse wayar, ya sake kissing gefen fuskar ta sannan ya mik'e ya fice.. Fitowa Meemee tayi daga cikin d'akin hannun ta d'auke da waya, ta k'arasa ta zauna kujerar dake facing inda Azrah ke zaune, ta kalle ta tace

"Laela majnun an gama shan soyayyar?" harara Azrah ta jefawa Meemee sannan tace

"Ke koh.." murmushi kawae Meemee tayi dan su kansu yadda mijin er uwar ta su ke nuna mata k'auna ba k'aramin burge su yake yi ba. Suna nan zaune jefi jefi suna hira Meemee na danna wayar ta yayin da Azrah ke kallo a T.V, gaba d'aya yau d'in se take jin zaman wajen sam beyi mata ba, dan haka ta d'an muskuta ta gyara zaman ta, duk da haka dae be mata ba, ta kalli Meemee tace tana yamutsa fuska

"D'an gyara min pillown nan.." mik'ewa Meemee tayi ta k'araso inda Azrahn take tana fad'in

"Wannan k'aton cikin baki ba dae mu sani ba ko en 3 zaki juye mana" dae_dae lokacin da Zarah tayi sallama cikin d'akin, Meemee ta kalle ta da murmushi kan fuskar ta tace

"Oyoyo sister.." murmushi Zarahn ta maeda mata sannan ta maeda duban ta kan Azrah dake cigaba da yamutsa fuska saboda yadda taji marar ta ta mata wani gingirin, tace

"Hajjaju Ummu Unborn wa ya 6ata miki rae haka?" d'an yak'e tayi sannan tace cikin k'arfin hali

"Ni ba kowa.." ta fad'a dae_dae lokacin da take mik'ewa daga zaunen da take dan komawa kan kujera wae ko zata samu sauk'i, seji tayi kamar marar ta zata 6alle wanda hakan ya tilasta mata sakin k'ara tana dafe cikin ta, dukan su suka yo kanta suna had'a baki wajen fad'in

"Lafiya?" cikin nata ta rik'e tana jin wani irin ciwo da tunda uwar ta ta haefe ta bata ta6a jin irin sa, seta fara yarfe hannu d'ayan da baya kan cikin ta kafin ta koma durk'ushen da take tana kiran sunan Allah, cikin gigicewa Meemee ta d'auki wayar ta ta danno number Don, yana d'agawa kafin yace komae tace

"Yah Adnan Azrah ba lafiya.." ta fad'a tana kallan Zarah dake kusa da Azrah d'in tana ta jera mata sannu, be iya cewa komae ba se katse wayar da yayi, ya fito daga cikin wajen da yaje zasu gabatar da wani wasa, da wani irin sauri ya k'arasa ya fad'a cikin motar sa ya fige ta da gudu se gidan sa.. Sanda ya iso gidan tuni ta soma ficewa daga hayyacin ta, cikin matuk'ar tashin hankali ya d'auke ta a hannun sa zuwa cikin motar kafin ya tashe ta da gudun gaske se asibiti. Kae tsaye d'akin haehuwa aka wuce da Azrah d'in, se dae tasha wahala sosae da sosae tafi awa nawa ta kasa haehuwa da kanta, har an fara shirye shiryen yi mata aeki se kuma cikin ikon Allah ta haefo kyawawan babies guda 2 duka mata.. Suna zaune su da yawansu kowa da addu'ar da yake, shima yana tsaye ya kasa zaune ya kasa tsaye se safa da marwa yake yi yana tuna a halin daya kawo Azrah d'in, can sega wata midwife ta fito daga cikin d'akin, shi da Ammi suka mik'e tare suka isa wajen ta kafin tace komae yace

"My wife..!" ya fad'a ba tare da yayi la'akari da Ammi dake wajen ba, ita kanta Ammin abinda take buk'atar ji kenan

"Ku kwantar da hankalin ku, yanzu kam ta samu kanta kuma babu wata matsala" tare suka sauke ajiyar zuciya kafin midwife d'in ta sake fad'i tana kallan Don

"Congratulations sir matar ka ta haefi en biyu duka mata.." lumshe idanun sa yayi yana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa, Ammi ma ta kulle idanun ta tana jin wasu k'walla na taho mata

"Alhamdulillah Alhamdulillah" suka had'a baki wajen fad'in hakan.


... A hankali ya tura k'ofar d'akin ya shiga sannan ya maeda ta ya rufe, ya k'arasa yana kallan kyakykyawar fuskar ta da tayi wani irin fayau kamar mara lafiya, seya sake lumshe idanu wata irin k'aunar ta na sake ratsa duk wata ga6a ta jikin sa, a hankali ya sunkuya yayi kissing bakin ta sannan yayi kissing gefen fuskar ta kana ya koma ya zauna ya rik'o hannayen ta ya sanya cikin nasa, d'an motsawa kad'an tayi eye lashes d'in ta suka fara motsi, seya sake matsar da kujerar kusa da gadon yana sake kallan ta sosae, dae_dae lokacin data bud'e idanun ta seta sauke su akansa, ta sake rufe idanun ta kana ta bud'e su still dae a kansa, bata ta6a tunanin zata kuma bud'e ido ta ganta a cikin duniyar nan ba saboda gagarumar wahalar da tasha

"Sannu kinji, sannu Babe, sannu.." ya dinga jera mata sannu har seda taji wani murmushi ya su6uce mata akan fuskar ta, har a lokacin ma ita kad'ae tasan yadda take ji a jikin ta kawae dae tana daurewa ne

"Ina Ammi?" abinda ta fara tambaya kenan dan yau d'in wata k'aunar Ammin ce ta sake lullu6e ta, tana sake tausayin Ammin irin wahalar da tasha kenan sanda zata haefe ta kuma aka raba ta da ita

"Tana can tare da masu shirya Babies d'in" kallan sa tayi cike da mamaki dan lokacin data haehu gaba d'aya ta fita a hayyacin ta bama tasan meta haefa ba

"Babies kuma?" ta tambaya cikin mamaki tana runtse idanu, seya sakar mata tattausan murmushi sannan ya sake mik'ewa yayi kissing goshin ta yace

"Ae kinyi k'ok'ari sosae Babe, twins fa kika juye mana" ya k'arasa fad'a yana jin wani irin mad'aukakin farin ciki, lumshe idanun ta tayi kafin ta sanya hannun ta akan cikin ta cikin mamakin wae itace ta haehu, haehuwar ma kuma ta en 2, kawae se taji wasu hawaye na bin kuncin ta amma kuma murmushi ke fita daga fuskar ta, dae_dae lokacin da wata nurse ta turo k'ofar d'akin ta kalli Don tace

"Yalla6ae tana buk'atar hutu fa.." bece mata komae ba ya maeda duban sa kan Azrah yace

"A huta lafiya, zan je wajen Babies d'ina" daga haka ya saki hannun ta ya fito daga d'akin, ta bishi da kallo tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa.


... A hankali ya tura k'ofar d'akin ya shiga idanun sa suka sauka akan Babies d'in nasa wanda d'aya take hannun Ammi, d'aya kuma na hannun Aunty Hindu, da sassarfa ya k'arasa ya zube akan k'afafun sa yana kallan su su duka, kusan lokaci d'aya duka suka mik'a masa Babies d'in kowaccen su d'auke da mad'aukakin murmushi akan fuskar ta, ya sanya hannu ya kar6e su su duka yana kallan fuskar kowaccen su, kyawawa dasu wanda tun a kallan farko daka musu zaka fahimci identical twins ne, dukan su bacci suke yi calmly, amma ko a haka zaka iya fahimtar wadda take sauke numfashi a hankali da alama itace tafi shan wahala kafin tazo duniya, ya lumshe idanu wani irin sanyi na ratsa shi, yau shine da 'ya'ya kuma 'ya'yan ma har biyu, be damu da a gaban kowa yake ba ya sanya bakin sa yayi kissing goshin su su duka, sannan ya musu hud'uba yana sake jin wata matsananciyar k'aunar su, ita dae Ammi tuni ta bar wajen, cigaba da kallan su yayi da alama bashi da niyyar maedawa wanda ya kar6e su a wajen su yaran ba, seda Aunty Hindu tace

"Adnan, kawo su nan mana" ya kalli Aunty Hindun kafin ya d'an yamutsa fuska cikin basarwa yace

"Wa za'a bawa?" kafin Aunty Hindun ta sake cewa komae d'aya daga cikin Babies d'in ta fara kuka tana kae hannun ta baki da alama yunwa take ji, duk seya rud'e ya rasa yadda zaeyi dan sam besan yadda ake rarrashin jinjiraye idan suna kuka ba

"Yanzu dae ka kawo su koh?" Aunty Hindu ta fad'a, murmushi yayi kana ya mik'a mata Babies d'in, ta kar6e su sannan tace

"Wa muka samu?" ya d'an lumshe idanun sa kad'an sannan yace

"Mom ce da Ammi.."














"Masha Allah, Allah ya raya mana su" Aunty Hindu ta fad'a, dae_dae lokacin da Fawaz ya shigo d'akin, ya k'araso da sauri ya tsuguna a gaban Aunty Hindu da wani irin murmushi akan fuskar sa yace

"Aunty kawo su" ya fad'a fuskar sa akan kyawawan Babies d'in, mik'a masa su tayi ya had'a su su duka ya kar6a cikin wani irin farin ciki, wanda fuskar sa kad'ae zaka kalla ka tabbatar da hakan

"Kamar su d'aya da kae Bhai.." ya fad'a yana kallan Don da shima shi yake kalla, d'an murmushi ne ya bayyana a saman fuskar sa bayan ya lumshe ido yace

"Koh?"

"Sosae fa.." Fawaz ya fad'a yana sake maeda idanun sa kansu.




Kwanan Azrah 2 a asibitin sannan suka sallame ta duk da har lokacin jikin ta ba wani k'wari yayi ba, dan haka Ammi tace base anyi suna ba lafiyar ta tafi komae. Ranar da suka koma gaba d'aya yana gidan, ya kasa matsawa ko nan da can yana kusa da matar sa dake kwance kan gado, ganin baccin take ji ya sanya shi fad'in

"Bari na barki kiyi bacci.." girgiza kae tayi kafin a hankali tace

"A'ah ka zauna inyi ta kallan fuskar ka me kama da Babies d'in mu" murmushi yayi kana ya lumshe idanun sa yace

"Ohk.." ya fad'a yana gyara zaman sa yadda zata fi jin dad'in kallan sa, dae_dae nan wayar sa tayi k'ara, ya d'akko ta ya d'aga kana ya kara a kunnen sa, daga can 6angaren Sameer yace

"Gani fa a k'ofar gidan.."

"Ohk.." kawae yace sannan ya katse wayar, ya kalli Azrah da take kallan sa bilhak'k'i, ya sake lumshe ido sannan ya hura mata iska akan idanun nata, seta rufe su tana dariya, shima murmushi yayi kana ya mik'e yace

"Zanje in shigo da Sameer zega Twins, kiyi baccin ki Uhmm?" ya fad'a yana kafe ta da idanun sa, jinjina masa kae tayi tana murmushi, yana dab da juyawa ta rik'o hannun sa, ya dakata yana kallan kyakykyawar fuskar ta tace

"Kayi alk'awarin in dae na haehu ranar suna zaka saka manyan kaya koh?" ya lumshe ido yana tunanin yadda za'a gansa cikin manyan kaya, dan shi dae tunda yayi wayo be ta6a saka manyan kaya ba, amma kuma tunda yayi alk'awari dole ya cika, ya d'an maraeraece fuska kamar k'aramin yaro yace

"Toh ae ba kyau zanyi ba" yadda yayi maganar ya bata dariya dan haka tayi dariyar ta son ranta yayin da shi kuma ya shagala da kallan ta har zuwa sanda take fad'in

"Ae komae ka saka yana maka kyau, ballantana kuma manyan kaya" tayi maganar tana sakin wani k'ayataccen murmushi

"Ammi tace ba za'ayi suna ba ae.." ya sake kawo wani k'orafin, ta tura baki sannan tace

"Allah ni dae ina son ganin ka da manyan kaya, yanzu fa kae Abba ne" murmushi yayi yana shafa sumar kansa sannan yace

"Ohk zan gwada sakawa, amma idan aka min dariya kece kika jamin"

"Wae dariya" ta fad'a tana er dariya

"Uhmm lemme go, nasan wancan bawan yana can yana mita" ya fad'a bayan ya bata light kiss a goshi ya fice daga d'akin. Be dad'e da fita daga d'akin ba (Afaaf) wadda itace me sunan Ammi (Fateema) ta fara kuka, a hannun Ummu take dan haka itace ta shigo d'akin, dae_dae lokacin da Ammi ma ta shigo da wasu kaya cikin d'akin, dan kuwa daga Abba har Dad akwati d'ad'd'aya suka had'awa Twins d'in wad'anda ke shak'e da galla gallan kaya na gani na fad'a, rufe idanun ta tayi ruff dan su zata bacci take yi dan ita kad'ae tasan yadda take ji idan tana feeding jariran, Ummu ta kalli Azrah d'in tace

"Allah sarki baewar Allah ashe ma ta samu bacci.." cigaba da kukan da yarinyar tayi ne ya sanya ta kallan Ammi tace

"Inaga fa ya zama dole a had'awa yaran nan da madara, yara biyu ba wasa bane Ammi musamman a wajen Azrah dududu nawa take" kallan ta Ammi tayi sannan tace

"Toh shikenan, hakan ma yayi..yanzu dae a tashe ta kafin a siyo madarar"ta fad'a dae_dae sanda take ficewa daga d'akin yayin da Ummun ta k'arasa inda Azrah take ta fara tashin ta.

... Shi ya fara shigowa cikin parlourn ya kalli Ammi dake zaune kan kujera wata mak'ociyar ta tana mik'a mata (Iffah) wadda itace me sunan Mom (Sa'adatu), seda ta fita sannan ya k'araso yace

"Ammi Sameer ne yazo ze shigo" murmushi tayi sannan tace

"Ka fad'a masa ya shigo.." mik'ewa yayi ya fita babu dad'ewa se gashi sun dawo shi da Sameer, da sallama dukan su suka shigo parlourn, dae_dae lokacin da Meemarh ta fito daga d'akin da Azrah ke ciki, sanye take cikin doguwar rigar atamfa, saboda bak'in da keta shigowa ya sanya ta yafa mayafi akan ta

"Ammi se kuma wa zan kira? Ko rubuta min za'ayi?" bin ta Sameer yayi da kallo dae_dae sanda suke zama akan carpet d'in d'akin, Ammi ta kalle ta tace

"Bari zamu yi maganar.." kallan su Don tayi duk da sun gaesa tun d'azun amma ganin sa da bak'o ya sanya ta fad'in

"Ina wuni?" Sameer daya fahimci dashi take yace

"Lafiya k'alau.." ya fad'a yana d'an satar kallan ta sanda take komawa cikin d'akin sannan ya dawo da duban sa ga Ammi suka gaesa sannan aka gabatar masa da Iffah, Meemarhn ce dae ta kar6o Afaaf d'in daga hannun Ummu, wadda yanzu tayi shiru ta koma baccin ta, shi kansa Sameer yaran sun burge shi, sunyi matuk'ar kyau cikin shigar kayan sanyi kasancewar garin da aka tashi da sanyi yau, gasu kyawawa tubarkallah masu kama sakk da uban su, mintina wajen 10 yayi sannan ya ajje su cikin d'an k'aramin gadon su kana ya ajje abinda ya kawo musu ya sake addu'ar Allah ya raya kana ya mik'e

"Toh angode, ka gaeda gida.." Ammi ta fad'a su kuma suka fice daga d'akin, sanda suka isa wajen motar Sameer d'in yayi dae_dae da lokacin dasu Fawaz suka iso cikin wata k'atuwar mota, kayan Babies ne da sauran abubuwan amfanin su har ma dana Azrah, wanda Don ne ya siye su ya saka Fawaz d'in ya d'akko su, seda ya fito suka gaesa dasu Don din sannan ya koma suka fara fito da kayan.. Sameer ya kalli Don yana shafa kansa yace

"Man nifa naga mata a gidan nan" yamutsa fuska Don yayi sannan yace

"Ohh..kace kallan 'ya'yan mutane kake yi"

"Pls joke apart, Allah kuwa da gaske nake.."

"Wacece?"

Please Login or Register in order to submit comment