Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fad'a yana nuna wata leda dake ajje kan gadon d'akin sannan ya d'ora da fad'in

"Wayar ki ce..and abu na k'arshe shine I love u so much, I really really luv u and I will always do" ya fad'a a tausashe kuma har lokacin k'wayar idanun su na cikin na juna, seta tsaya kawae tana cigaba da kallan sa kafin a hankali ta lumshe idanun ta, ita kam me take jira a yanzu? meya rage mata banda ta godewa Allah? wane irin ni'ima ne Allah beyi mata ba? abu d'aya ne ya rage mata a halin yanzu shine ta amshi mijin ta da hannu bibbiyu sannan tayi amfani da k'aunar da yake mata ta chanja shi, babu 6ata lokaci ta fad'a jikin sa ta rungume shi hadda sanya hannayen ta ta rik'o shi ta baya, ya lumshe idanun sa yana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa dan haka ya sake rungume ta kamar wanda za'a k'wacewa ita, sun kae kusan minti 1 a haka sannan ya fara magana a cikin kunnen ta

"Plss kice kina sona.." ya fad'a yana sake jin wata matsananciyar k'aunar ta na lullu6e ilahirin jikin sa, seta sake lumshe idanun ta tana tunanin yadda zata iya furta masa kalmar, amma dole tayi amfani da wannan damar wajen chanja shi dan haka cikin sanyayyiyar muryar ta tace

"Zan fad'a maka amma akwae sharad'i" seya d'ago ta d'aga jikin sa yana kallan ta yace

"Uhmm, wanne sharad'i ne wannan?" Seta d'auke kae daga wannan kallan da yake binta dashi sannan tace tana kallan k'asa

"Zaka dena.." ta d'an dakata tana jin kunyar abinda zata fad'a d'in, gaba d'aya ma bata san tunawa amma ya zama kamar dole seta fad'a d'in dan haka tace

"Zaka dena shan duk wani abu da kake sha..." Ya runtse idanun sa yana tuna mummunan tabo da Mami tabar masa, ba dan Allah na son masu yafiya ba da har abada baze yafewa Mami ba, amma ko a yanzu yana godewa Allah da yasa ya gane ta dalilin Mami yake wasu abubuwan, kuma tun daga lokacin ko yayi k'ok'arin sha idan ya tuna Mamin seya fasa, yana ganin idan ya cigaba da sha d'in kamar Mamin zata sake cin galaba ne a kansa, ya k'ura mata idanu sannan yace

"Bayan taba da shisha babu wani abu da nake sha, kuma babu wani sa6on Allah da nake yi suma kuma ashe duk ta dalilin Mami ne nake sha.." da sauri ta d'aga dara daran idanun ta ta kalle shi, ya jinjina mata kae alamar tabbatarwa, cigaba tayi da kallan sa tana sake mamakin halin d'an Adam, Mami wace irin mace ce mara imani? duk akan kud'i ne ta 6atawa wanda beji ba be gani ba rayuwar sa, meyasa wasu matan basu da adalci kamar dae Ummi? dukkan su SANADIN KADDARAR SU kusan iri d'aya ne, akan kud'i ne kowannen su k'addarar sa ta soma

"What next?" ta jiyo maganar sa, se tayi shiru kawae yanzu kam bata tunanin akwae wani abun da zata iya cewa, koma dae menene a hankali zata isar dashi zuwa wajen sa, seta girgiza kae kawae, murmushi me taushi ya sakar mata kana ya kama hannun ta yace

"Muje muyi sallah" babu musu ta mik'e, so yake yayi wanka yasan yanzu kuma idan yace suyi wankan gaba d'aya wata rigimar ze 6allo dan haka kawae seya fita zuwa nasa d'akin yayin da ya batta ita kuma anan d'akin, ita kanta data shiga toilet d'in kawae se tayi wanka tayi alwalar gaba d'aya, ta fito tana sake kallan d'akin ba k'arya ya mata kyau sosae, ta k'arasa ta bud'e wardrobe d'in a shirye take kamar ita ta shirya, da mamaki kawae ta cigaba da kallan wardrobe d'in tana mamakin wanda ya shirya matan, da dae taga babu me amsa mata tambayar seta janyo wata doguwar riga me laushi ta sanyawa jikin ta sannan ta k'arasa wajen mudubi ta fara mulke jikin ta da turarukan dake ajje masu dad'i da sanyin k'amshi, tana gamawa ta d'auki dogon hijab ta sanya, dae_dae lokacin daya shigo d'akin, ya kalle ta sannan ya k'araso inda take yana shak'ar k'amshin dake fita daga jikin ta, amma be ta6ata ba ya shimfid'a musu dadduma suka yi sallah, ta ninke daddumar ta ajje ta inda ya dace, bata ankara ba se ji tayi ya janyo ta ta fad'a cikin jikin sa, ya sanya hannu ya cire hijab d'in jikin ta yana fad'in

"Ni fa nafi so muna idar da sallah a cire wannan hijab d'in.." shiru tayi itama tana shak'ar k'amshin dake tashi daga jikin sa, seya d'ago fuskar ta ta yana kallan cute lips d'in ta yace

"Umhum, naga kamar akwae magana a bakin kin nan" ya fad'a yana lumshe idanu, bin idanun nasa da kallo tayi tana tuna yanda da take masa kallan d'an giya musamman saboda wad'annan lumsassun idanun nasa, seta tura baki kawae kamar baza tace komae ba se kuma ta bud'e bakin da niyyar cewa wani abun, be jira tace komae ba ya had'e bakin su waje d'aya, yau kam barin sa tayi yayi yadda yake so ba tare data hana shi ba, ya nuna mata soyayya iya soyayya, musamman daya kasance yau babu kukan nan daya zame mata jiki se yau d'in ta kasance wata ta daban a cikin rayuwar su su duka... Wajen k'arfe 8 ne ya shigo kitchen d'in yana kallan yadda take ta 6ata rae, ya k'arasa ya rik'e k'ugun ta ta baya sannan yace

"Meya faru babe" tura baki tayi kafin tace a shagwa6e

"Ni kam bana son komae, fura nake so me sanyi, ko yoghurt.."

"Shine kuma kike 6ata rae? Toh bari naje na samo miki, amma kafin nan ki soya min k'wae naci" ya fad'a yana sakin ta dan ya bata damar yin aekin a nutse, seta k'arasa ta kunna gas d'in sannan ta d'ora frying fan kan wutar ta zuba mae kana ta juye k'wan data riga da had'a shi da kayan had'i, yana tsaye yana kallan ta da murmushi kan fuskar sa, tun kafin k'wan yayi nisa da fara soyuwa taji sam k'amshin beyi mata ba, zuciyar ta ta fara tashi amma ta danne, se daga baya dae data fahimci idan ta cigaba da zaman komae ze iya faruwa seta fita daga kitchen d'in da sauri, binta da kallo yayi yana mamakin abinda yasa ta fita haka da sauri, seya k'arasa ya kashe gas d'in sannan yabi bayan ta, a parlour ya same ta tana sauke numfashi kamar wadda tayi gudu, ya k'arasa da sauri ya rik'o ta yana fad'in

"Meya faru?" seta yamutsa fuska tana d'ora kanta a kafad'ar sa tace kamar zatayi kuka

"K'amshin ne bemin ba kawae.."

"Ohk kiyi zaman ki karki k'ara shiga kitchen d'in, zan fita se nayi mana take away Uhmm?" jinjina kae tayi sannan yayi kissing bakin ta kana ya sake ta yace

"Bari naje" ta lumshe idanun ta sannan tace

"Allah ya tsare" ta bishi da kallo har ya fice, tana sake nazarin rayuwa, bata ta6a tunanin rayuwa zata chanja musu shi da ita ba, bata ta6a tunanin daga ita har shi zasu wayi gari cikin k'aunar junan su ba se gashi yau tana jin mutumin har can cikin zuciyar ta, kae gaba d'aya ma jin sa take a duka jikin ta.. Be dawo gidan ba seda ya tabbatar ya siyo yoghurts da dama da kuma fura da nono ya juye su a fridge sannan ya d'aukar mata wani daga ciki ya juye mata cikin bowl ya bata, farin ciki kamar tayi mene, a gefe can ta zauna tana kallan sa yana cin abincin sa dan kwata kwata bata san k'amshin abincin, yana daga gefe yana kallan wannan sauyin da aka samu daga gare ta, ya riga ya gama karantar bata da son cin abinci sosae se gashi yanzu tunda ta durfafi yoghurt d'in bata ajjiye ba seda ta shanye shi tass....


Kwanakin da suka biyo baya wata irin shak'uwa ce me tsanani ta shiga tsakanin su, ita kanta Azrah yanzu ta sake soyayya take nunawa mijin nata ba kama hannun yaro, ta fannin sa kuwa kullum ji yake kamar ana k'ara masa k'aunar tane, in dae yana gida toh zaka gansu ne koda yaushe manne da juna, dan sun riga sun sabarwa junan su hakan, idan kuwa ya fita toh In Sha Allahu ze kira ta babu adadi, girki kuwa tuni ta ajiye shi kullum se dae yayo take away yaci ita kuma ya samo mata abu me sanyi shi kad'ae take iya sha, amma ta 6angaren su har yanzu basu san takamaemae menene dalilin sauyawar ta ta ba...


... Fitowar ta kenan daga wanka d'aure da towel, sumar kanta da bata kae ga d'aure ta ba tana zube akan kafad'ar ta, a hankali ya turo k'ofar d'akin ya shigo ya k'arasa inda take yana lumshe idanun sa, beyi wata wata ba ya rungume ta ta baya yana sakin ajiyar zuciya kansa d'ore akan kafad'ar ta, seya daga kae ya kalle ta ta cikin mudubin kullum k'ara kyau take yi tana sake yin fresh, ga wata k'iba data fara yi, dan kuwa hatta kumatun ta seda suka nuna k'ibar, hips d'in ta suka bud'e ta d'an yi fad'i daga k'asa, haka daga sama ma ta sake cika kamar ba Azrah ba, seya sake maeda kansa kan wuyan ta sannan ya hura mata iskar data sanya ta lumshe ido yace

"Babe fad'a min sirrin k'ibar nan da kike yi mana.." turo baki tayi sannan tace a shagwa6e

"Nifa Allah bansani ba" ya d'age mata gira sannan yace

"Koda yake wannan uban fura da kike d'irkawa cikin ki kullum ae dole kiyi k'iba" se kuwa ta fara bubbuga k'afar ta a k'asa tana kuka wanda kana gani kasan bana gaske bane, seya juyo da ita da sauri yace bakin sa na dab da nata

"Wannan bakin naki.." se tayi sauri ta maeda bakin ta taune, yayi murmushi kana yace

"Da kin barshi ae..bari na shirya ki" ya fad'a yana zaunar da ita kan gadon, ya k'arasa ya d'auko mata wata doguwar rigar atamfa ya k'araso ya taemaka mata ta saka amma da k'yar ta shiga, shi kansa daya zuge mata zip seda yaji jiki, ya gama zugewar yana sauke numfashi kamar wanda yayi aekin wahala, ta kalle shi kamar zata yi kuka tace

"Menene?"

"A'ah babu komae" ya fad'a dan yasan idan yace k'iba tayi se tace zata kuma wata rigimar, shi kuma so yake ya fita kada ta sanya shi ya makara, mik'ewa yayi yana kallan ta sanda yake k'arasawa kusa da ita yace

"Zan fita.." ya fad'a yana janyo k'ugun ta da hannun sa na dama, seta lumshe ido kana ta bud'e a kansa sanda yake fad'in

"Oh yah gimme a kiss.." ya fad'a yana sakin ta gami da juyar da fuskar sa, seta k'arasa matsawa kusa dashi, amma da yake yafi ta tsayi seta kasa kae bakin nata kan fuskar sa, dan haka a hankali ta taka k'afar sa, seya d'ago yana kallan ta, fahimtar abinda zata yi ne ya sanya shi sake gyara tsayuwar sa ta taka duka k'afafun nasa sannan ta rik'o shi da duka hannayen ta kana ta rufe idanun ta takae bakin ta gefen kumatun sa, ganin da yayi idanun ta a rufe suke ya sanya shi juyo da fuskar sa gaba d'aya sannan ya kae bakin sa saetin bakin nata, ta d'auka za taji bakin ta akan kumatun sa se taji sa6anin hakan, taji bakin ta dumu dumu kan nasa, tana shirin janye nata taji ya sake rik'e shi cikin nasa sosae yana sake gyara mata tsayuwar kuma yana sake shigar da ita cikin jikin sa, dan haka kawae ta saki jiki itama ta bashi lafiyayyen kiss, sun d'auki wajen minti 2 a haka sannan ta sake shi tana cire bakin ta da taji ya fara mata zafi, seya sake tan yana shafa kwantacciyar sumar kansa yace

"Akwae yoghurt d'in ne ko in k'aro wasu?"

"Ehh a k'aro" ta fad'a tana gujewa kallan k'wayar idanun sa, yayi murmushi kana yace

"Ohk bye.." daga haka ya fice daga d'akin ta sake binsa da kallo tana lumshe idanu... Wayar ta dake ajje ce tayi k'ara ta d'auko ta da sauri ta kara a kunnen ta kafin Ammin tace komae ita tace

"Barka da safiya Ammi"

"Barkan ki dae Azrah kuna lafiya?" Azrah tace

"Alhamdulillah ina su Meemarh?"

"Suna nan k'alau, yanzun nan ma suka fita gidan Ummu" murmushi Azrah tayi

"Kina lafiya dae koh?"

"Ehh Ammi ba abinda ke damu na"

"Toh madallah" Ammi ta fad'a kana Azrahn tace

"Ammi Abba fa?"

"Shima yana lafiya"

"A gaeda kowa da kowa" daga haka suka yi sallama kowacce ta ajje wayar, 6angaren Ammi kuwa girgiza kae kawae tayi tana mik'ewa, ita kuma Azrah wayar ta ta ce ta sake yin k'ara, ta kalli me kiran seta d'aga tana kara wayar a kunnen ta, daga can 6angaren Hauwa'u tace

"Mrs Adnan yah kike?" murmushi Azrah tayi sannan tace

"Lafiya k'alau Hauwa'u Yah kike ya Umma?" ta tambayi Umman Hauwa'un dan yanzu in dae suka yi waya da Hauwa'un seta shaeda mata Umman ta na gaeshe ta

"Alhamdulillah ya kwana biyu?"

"Wallahi Alhamdulillah, ya wajen Inno kuwa?"

"Jikin ta Alhamdulillah da sauk'i, tana k'ara samun lafiya, and wani abun farin cikin ma na samo miki number Umma (matar me gari)"

"Woww, don Allah da gaske Hauwa'u?" Azrah ta fad'a tana jin sanyi har cikin ranta

"Wallahi kuwa, zuwa anjima In Sha Allah zan turo miki, yanzu dae kira nayi na fad'a miki yau zasu kawo lefe" ta fad'a tana d'an murmushi k'asa k'asa

"Masha Allah Allah ya sanya alkhaeri Hauwa'u"


.... Daga cikin d'akin ta fito sanye cikin doguwar rigar shadda ta yafa d'an kwalin da yak'i d'auruwa saboda santsin shaddar da kuma santsin gashin ta, da sauri ta k'araso cikin parlourn tana fad'in

"Laaa Aunty Hindu.." itama murmushi Aunty Hindun tayi tana fad'in

"Na'am, yau dae gani cikin gidan nan" Azrah ta k'arasa ta zauna a k'asa tana fad'in

"Amma naji dad'in zuwan ki Aunty.." murmushi Aunty Hindu tayi tana kallan Azrah d'in da taga ta chanja sosae, suka gaesa sannan ta mik'e ta wuce kitchen ta d'auko plate ta dawo ta bud'e fridge ta d'akko ruwa da lemo sannan ta kawo ta ajje mata su, kana ta koma ta d'akko jarkar yoghurt guda d'aya ta zauna a gefen Aunty Hindun, suna zaune jefi jefi suna hira idan taji bakin ta babu dad'i seta d'an kur6i yoghurt d'in ta maeda ta rufe har zuwa sanda yayi sallama ya shigo cikin d'akin, duka suka amsa sallamar tasa, kamar koda yaushe idanun sa suka sauka akan ta, ta matuk'ar yi masa kyau dan lokacin daze fita ba wannan kayan ne a jikin ta ba, ya k'araso ya nemi waje ya zauna yana fad'in

"A'ah Aunty saukar yaushe?"

"Saukar yanzun.."

"Barka da zuwa kinzo lafiya?" ya fad'a a nutse kamar yadda ya saba, ta amsa masa gaesuwar tasa sannan ya ajje ledar daya shigo da ita ya mik'e ya shiga kitchen ya fito da plate ya k'araso ya zauna, Aunty Hindu ta bishi da kallo dan ganin abinda zeyi, Azrah data fuskanci abinda zeyi seta mik'e tana shirin barin wajen, binta da kallo Aunty Hindu tayi tace

"A'ah ina zuwa kuma?" ta 6ata fuska dan sam bata san k'amshin wani abu na gishiri yanzun, Don ne ya kalle ta sannan ya maeda duban sa kan Aunty Hindu yace

"Bansani ba ko abincin k'asar ku take bid'a, dan tunda muka dawo ta k'auracewa na nan d'in, ko k'amshin sa bata so kullum sedae tasha abu me zak'i.." kallan sa Aunty Hindu take tana karanto zallahr gaskiyar sa cikin maganar da yake, ita dama tunda tazo ta fuskanci wani abu game da Azrahn, da alama kenan su basu gane ba? Amma dae bari ta sake tabbatarwa, se tayi murmushi dan da alama daga shi har itan duk zamuce ta tadda mujemu

"Baki da lafiya ne?" tambayar da Aunty Hindu ta yiwa Azrah kenan, seta girgiza kae alamar "a'ah" tana k'ok'arin tafiya, Aunty Hindu tace

"Dawo ki zauna kema kici abincin" 6ata fuska tayi tana jin kamar ta sake yi mata musu, amma se taga hakan kamar be dace ba dan haka ta dawo ta zauna, shi kuma ya cigaba da abinda yake, yana gama zubawa ya mik'awa Aunty Hindu tace

"A'ah bata taci.." seya mik'a plate d'in gaban ta yana kallan yadda take ta tura baki, a cikin ransa yake ta mata dariya, Aunty Hindu tace

"Yawwah kici kinji?" jan plate d'in tayi tana had'iye yawu da k'yar, sannan ta saka spoon ta fara juya abincin, nan da nan k'amshin sa ya sake cika d'akin, seta fara sauke ajiyar zuciya a jere a jere kafin daga k'arshe ta runtse idanun tana jin yadda wani irin kyakykyawan amae ya taho mata, da gudu ta tashi tayi cikin d'aki se toilet ta dinga kwarara shi kamar zata amayar da 'ya'yan cikin ta, binta su duka suka yi da kallo, Aunty Hindu tayi wani murmushi tana kallan yadda ya tashi da sauri yabi bayan ta, ta lumshe idanu tana fad'in

"Alhamdulillah".. Har cikin toilet d'in ya bita, shiya taemaka mata ta gyara jikin ta sannan ya rik'o ta suka fito ya zauna kan gadon ya kwantar da kanta a k'irjin sa sannan yace a tausashe

"Dama baki da lafiya amma baki fad'a min ba?" turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace

"A'ah fa ni lafiya ta k'alau, kawae k'amshin ne bana so" ya lumshe idanun sa yana tuna ashe fa sun bar Aunty Hindu a parlour dan haka yace

"Tashi mu koma kinga Aunty Hindu na can" babu musu ta mik'e ta sauya kayan jikin ta da wata abaya sannan suka fito tare, Aunty Hindu ta kalle shi sanda yake k'ok'arin zama

"A'ah ae zama be kama ka ba, Azrah jeki shirya kizo ku wuce asibiti.." dukkan su da kallo suka bita sannan Don yace

"Aunty tace lafiyar ta k'alau, kawae k'amshin ne be mata ba" ita kam wannan shiriritar tasu mamaki da dariya take bata amma seta dake tace

"Ehh ae saboda hakan zaku je a duba ta.." kallan Azrah yayi sannan ya mik'e yana fad'in

"Ohk.." tare suka koma cikin d'akin, ita dae Azrah bata san rashin lafiyar me take ba kuma da za'a ce se sun je asibiti ba, shiya d'akko mata hijab ta saka sannan suka fito, Aunty Hindu ta mik'e sanda suka fito d'in ya kalle ta yace

"Badae tafiya ba?"

"Tafiyar ce, tunda yanzu fita zakuyi zan dawo se muyi hira sosae" ta k'arasa maganar da murmushi kan fuskar ta

"Allah ya bada lafiya" ta fad'a tana d'aukar jakar ta, tare suka fita su duka, drivern daya kawo ta ya d'auke ta sannan su kuma suka d'auki hanyar asibitin... Ko a cikin motar ma da hannu d'aya yake driving yayin da d'ayan hannun nasa ke cikin nata ta rik'e da duka hannayen ta biyun, a haka har suka k'arasa asibitin sannan ya kashe motar, ta maraeraece fuskar ta sanda yake shirin sauka dan zuwa ya bud'e mata k'ofa, ya kalli cikin idanun ta dake kashe masa jiki sannan ya tari numfashin ta da fad'in

"Menene kuma Babe?" ya fad'a yana tsare ta da lumsassun idanun sa, ta tura bakin ta kafin tace bayan ta tattare girar ta waje d'aya

"Nifa Allah lafiya ta k'alau, kada daga cewa nayi amae suce zasu min allura.." yayi murmushi sannan ya d'ora hannun sa kan nata hannun yace

"Ba wanda ze miki allura Uhmm?" seta jinjina kae sannan ya saki hannun ta ya k'arasa ya bud'e mata k'ofar suka shige cikin asibitin... Dab da zasu shiga wata mota ta shigo cikin asibitin da gudu sannan drivern ciki ya fito da gudu zuwa ciki, babu dad'ewa nurses suka fito aka d'auki mutanen daya kawo d'in, daga can sega Momy da Simrah sun sauka daga wata adaedaeta data shigo dasu cikin asibitin sannan Momy ta k'arasa tana kallan mutumin tace

"Wae meya faru ni Ameena?" mutumin ya girgiza kae sannan yace

"Wallahi mota tace ta daki ta ita wadda ke tuk'a motar shine ta buge er uwatta ki anan ta fad'i sumammiya, yayin da motar waccan d'in kamar wadda aka yiwa baki tak'i tsayawa waje d'aya ta dinga juyi akan titin nan se kuma da Allah yayi zata tsaya d'in seta daki wata bishiya dake gefen titi sannan ta tsaya, toh dae yanzu haka da k'yar aka ciro matar nan saboda k'afar ta data mak'ale a k'asan motar bana ma tunanin k'afar ta ta zata sake aeki!" Momy ta d'ora hannu aka tana fad'in

"Na shiga uku, yanzu ina Hadeezan ta farka ne?" yaja ajiyar zuciya sannan yace

"Har dae muka iso bata farka ba.. Bansan kuma me likitocin zasu ce akan ta ba.."


Daga haka se nace mu had'u a Last Page 😭, going to miss u guys 🥺, su kan su Don da Azrah d'in ina jin bansan rabuwa dasu wlh 🥺😭



✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION60*

( _Last Page_)



_This page is dedicated to Mama 🥺🤧 jiya dae ta gaji tayi qorafi kan ko ita ban ta6a sadaukarwa da page ba 😩🤧 saboda haka wannan page d'in nata ne bana kowa ba 💃Allah y qara miki lpia d nisan kwana 🥰_


___Cikin aenahin asibitin suka isa hannun sa na cikin nata, basu samu layi ba dan haka kae tsaye cikin office d'in suka shige, suka nemi kujera suka zauna, yau ma cikin sa'a likita mace suka samu bayan sun gaesa ta kalli Don tace

"Dame zan iya taemaka maka?" Seya kalli likitar sannan ya kalli Azrah yace

"Tayi amae ne d'azun.." seya d'an dakata kad'an kafin ya sake cewa komae likitar tace tana kallan Azrah

"Meya janyo aman?" Azrah ta d'aga kae tana kallan Don sannan ta d'an 6ata fuska kana tace

"K'amshin abincin ne be min ba, shiyasa da naji k'amshin kusa dani zuciya ta ta tashi.." kallan su su duka likitar tayi sannan tace

"Ba matar ka bace?" Kamar baze amsa tambayar ta ta ba se kuma yace a dak'ile

"Yeah she's my wife.."

"Ohk Hajiya yaushe rabon da kiga bak'on watan ki?" Shiru Azrah tayi tana tunanin meye had'in aman da tayi da wannan, amma kuma seta tsaya idan har zata tuna dae_dae toh rabon ta da ganin sa tun kafin su tafi Sudan, seta d'aga kae ta kalli likitar sannan ta maeda kan Don daya kafe ta da idanun sa tace

"Na manta.." murmushi likitar tayi dan ta fuskanci abinda ke tattare da Azrahn amma Dan sake tabbatarwa se tace

"Ohk za'a yi miki pregnancy test.."... Suna zaune har lokacin cikin office d'in lokacin da likitar take duba wata takadda, seta d'aga kae ta kalli Don sannan tana mik'a masa takaddar hannun ta tace

"Congratulations..ur wife is pregnant.." da wani irin yanayi ya kalli likitar yana jin kamar wani yaren take masa, seya maeda duban sa kan Azrah wadda itama likitar take kalla kafin ya saki wani murmushi har besan sanda ya furta

"Like serious?" Jinjina kae likitar tayi tana d'an murmushi, kiran wayar ta da akayi ne ya sanya ta mik'ewa dan amsa wayar, ya dawo da duban sa kan Azrah yama rasa ta ina ze fara, ita kam tana zaune ta kasa koda motsi ne kamar wadda aka sassak'a a wajen, akan k'afafun sa ya sauka ya kamo hannun ta cikin nasa sannan ya kalli cikin idanun ta se kace ze karanci gaskiyar abinda likitar ta fad'a daga cikin idanun nata, seta langa6ar da kanta gefe tana zame hannun ta daga cikin nasa ta shafa shamulallen cikin ta, seya lumshe idanun sa yana tunanin meye ma ya kamata yayi shi kam? Beyi wata wata ba ya janyo ta cikin jikin sa a k'asan ya bata wata kyakykyawar runguma idanun sa a lumshe yana jin kamar yafi kowanne d'a namiji dace, a hankali ya zare ta daga jikin sa be sake ta ba duk da haka seya shiga jera mata kiss a duk inda bakin sa ya sauka, seda ta ankarar dashi inda suke sannan ya dawo hayyacin sa yana fad'in

"Alhamdulillah Alhamdulillah.." yana cigaba da bin ta da wani mayen kallo, kama hannun ta yayi yana jin kamar ya d'auke ta ya goye abar sa dan kada ma ta wahala, amma hakan baze yiwu ba ko dan idanun mutane dan haka ya rik'o hannun ta gam, ita kam har lokacin ta kasa cewa komae har zuwa sanda suka fito daga office d'in, dae_dae lokacin da suke fitowa yayi dae_dae da lokacin da Momy da Simrah suke tahowa tare da wani likita cikin shigar kayan likitoci hannun sa d'auke da wata takadda,

Please Login or Register in order to submit comment