Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasan hakan tun kafin a baka ita" daga nan ya fara zayyano musu tun ranar da aka tsinci Azrah har zuwa sanda aka dank'awa su Inno ita.. Shiru sukayi dukkan su sanda suka gama jin labarin nata, kowannen su da abinda yake sak'awa a ransa, gaba d'aya sun kasa cewa komae saboda tsananin mamaki da al'ajabin wannan labari na wannan baewar Allah, mutumin yace

"Ae dole kuyi mamaki, wallahi yarinyar nan ta sha tsangwama a cikin garin nan kamar ita ta yadda kanta da sanin ta, ni d'in ba mazauni bane shiyasa sena dawo nake sanin abinda yake faruwa kuma da yake ba dad'ewa nakeyi ba shiyasa bana samun zuwa har can gidan nasu naji ya take, yanzu haka ma seda na dawo nake sanin an aurar da ita.." Sameer ya sauke ajiyar zuciya kafin yace

"Toh mungode sosae, Allah ya saka da alkhaerin sa"

"Ameen_Ameen, zaku koma ne?" Mutumin ya fad'a yana kallan su sanda suke k'ok'arin mik'ewa, Sameer yace

"Ehh zamu koma"

"Toh ku gaeda gida.." Sameer yayi gaba yana kallan Don da har ya fice daga soron.. A wajen me zaman banza Don ya zauna, ganin haka ya sanya Sameer shiga driver seat, ya kalli Don daya kwantar da kansa kan kujera idanun sa a lumshe, bece komae ba yaja motar suka fice daga unguwar, tunda suka fara tafiya babu wanda yace komae, a 6angaren Don kuwa gaba d'aya kansa ya kulle yayi shiru kamar me nazari, Anya kuwa uwa zata iya d'aukar d'an data haefa ta jefar dashi kuma a ranar data haefe shi? Can dat be possible?, Lallae akwae wani abun, akwae wani 6oyayyen al'amarin wanda shi kansa besan ta yadda ze fara binciko wannan lamari ba... Sanda ya koma gidan duk da tana zaune kan kujerar bebi ta kanta ba ya wuce saman abinsa, yana zuwa ya kwanta kan gadon ringingine ya d'ora hannun sa a kansa yana kallan ceiling d'in d'akin, wannan abu ya tsaya masa sosae, ya kasa koda magantuwa ne akan wannan lamari, a hankali yaji wani abu na tsirga masa me kama da tausayi, ya lumshe idanun sa yama kasa gane wane tunani ya kamata yayi, ranar gaba d'aya be sake fitowa ba yana kwance cikin d'akin, ko abinci be sakko yaci ba. Tayi mamaki matuk'a da taga har bayan awa 1 be sakko ba, ta kalli stairs d'in na wajen minti 1 sannan ta ta6e baki a k'asan la66an ta ta furta

"Oho masa ae dae cikin sa ne ba nawa ba.."




__Washe gari ma haka yayi ta zama a d'aki, zuwa masallaci kad'ae ke fitar dashi, yanzu ma haka wajen k'arfe 2 ne ya gama shiryawa ya fice zuwa masallaci...


... Tana gama shiryawa ta d'auki mayafi ta yafa sannan ta d'auki wani k'ullin leda data d'auko shi daga cikin drawer ta jefa shi cikin jakar, kana ta d'auka ta sa6e ta a hannun ta.. Fitowa compound d'in tayi ta kalli driver tace

"Muje zaka sauke ni gidan Adnan.." babu musu drivern ya shiga motar bayan Mami ta shiga itama yaja motar.. Sauka tayi ta kalli drivern tace

"Kaje idan kana da wani abun da zaka yi, zuwa anjima seka dawo ka d'auke ni" da "toh" ya amsa, ita kuma ta shige cikin gidan. Sakkowar ta kenan daga saman sanye cikin doguwar riga sannan kamar koda yaushe da hijab, ta d'anyi turus kana ta k'araso cikin parlourn tana kallan Mami har lokacin tana jin yadda bugun zuciyar ta ke k'aruwa, Mami ta kalle ta sama da k'asa sannan tace

"Gani nazo da kae na ba sak'o ba, ayi komae a gaba na" bugun zuciyar Azrah ya k'aru idanun ta sukayi rau rau, Mami tace

"Muje kitchen d'in.." ta tsaya tana neman maganar da zata fad'a Mami tace

"Muje mana" kawae se tayi gaba har suka isa kitchen d'in, Mami ta sanya ta gaba har seda ta dafa abinci har colour 2 sannan tayi juice, ita dae bin Mamin kawae take yi, seda ta gama tana shirin kwashe su a warmers tace

"Mik'omin nan in kwashe" seta d'auka ta mik'a mata hannun ta na rawa, Mami taja flask d'in sannan ta bud'e jakar ta ta ciro ledar ta bud'e ta zuzzuba a kowanne flask bayan ta kwashe abincin, Mami tace tana rufe flasks d'in

"Ke ki saki jikin ki haka nan malama, taemakon kanmu zamuyi ba wani abun ba" Azrah dae binta da kallo kawae take yi harta gama komae ta d'auki jug ta kalli Azrah tace

"Taya ni mu fitar dasu.." Azrah ta d'auki warmers d'in zuwa kan dinning d'in suka ajje kafin suka dawo cikin parlourn, Mami ta nemi waje ta zauna sannan tace

"Yau kam ina zaune cikin gidan, har seya gama cin abincin sannan zan tafi" ita dae Azrah bata ce komae ba dan hankalin ta gaba d'aya yana wani wajen.. Wajen minti 5 da zaman su se gashi ya shigo cikin d'akin, Mami na ganin sa ta fad'ad'a fuskar ta da murmushi tace har lokacin tana kallan sa

"Sannu da zuwa Son" Yace shima bayan ya mayar mata martanin murmushin a lokaci guda kuma yana k'arasawa ya bata side hug

"Yawwah Mami, yaushe kika zo?" Tace

"Ban dad'e da shigowa ba" yace yana neman waje ya zauna

"Barkan ki da zuwa, an yini lafiya?"

"Alhamdulillah" Azrah kallan Mami kawae take yadda take masa magana cike da k'auna komae abin ka ba zaka ta6a cewa bana gaskiya bane, ya sake kallan Mami yace yana yamutsa fuska

"Mami I need rest.." Mami ta maraeraece fuska

"Eyyah, tun d'azu naga matar ka nata wahalar yi maka abinci, ya kamata ka tsaya ka fara ci" yace

"Noo Mami, barshi kawae"

"Haba kae kuwa, ae ba'a haka, kaci ko yaya ne mana saboda bansan matar ka tayi fushi bayan duk wannan wahalar da tasha" ya d'an saci kallan inda take, tana ganin yana shirin d'aga idanun sa ya kalle ta ta d'auke kae, se ya sake kallan dinning area d'in dama yunwar yake ji kawae dae baya jin cin abincin ne, amma tunda yanzu an masa tayi yasa ya tuna da hakan yace

"Ohk.." Mami ta mik'e tana fad'in

"Yawwah ko kaefa" tare suka wuce wajen dinning d'in, Don yaja kujera ya zauna ya janyo plate yayi serving kan sa, ya kalli Mami dake tsaye har lokacin yace

"Ki zauna mana?" Jan kujera Mami tayi tana fad'in

"A'ah bari dae na zauna na taya ka hira" tana zama ta fara yi masa hira, hakan yasa be fara cin abincin ba yana sauraron ta, Mami ta kalle shi kana ta kalli abincin tace

"Kaci mana" seya matsar da plate d'in gaban sa kana ya saka spoon ya d'ebi abincin dan kaewa bakin sa. Daga inda take tsaye taji jikin ta ya d'auki rawa tun lokacin daya zuba abincin, seta taka zuwa wajen sanda yake k'ok'arin kae abincin bakin sa, ta saka hannu ta janye plate d'in sannan ta kalli Mami cikin ido tace zuciyar ta na bugawa haka idanun ta sunyi ja sosae

"Ba zeci ba!" Cikin matuk'ar mamaki dukkan su suka d'aga ido suna kallan ta, musamman Don dake kallan ta da mad'aukakin mamakin da be ta6a yi ba, seya mik'e bayan ya k'ank'ance idanun sa yace cikin d'aga murya kamar ze rufe ta da duka

"Kinyi hauka ne?" Seta maeda kallan ta kan sa tace shima tana kallan sa cikin ido

"Ehh ba zaka ci ba" a'ah mamaki fa ya kusa kashe Don, seya fara tunanin shin ko dae tayi hauka ne? ko kuwa rashin kunyar da take ji da shine ya k'aru haka?, Tuni jikin Mami ya d'auki rawa, ta fara janyo salati tana fatan ace ba ranar tonon asirin ta ne tazo ba, ita wannan yarinyar zata yiwa haka? Ta dinga nunawa kamar tana tare da ita, bata ta6a mata musu ba tun farko, Ashe duk k'arya ce, so take ta nunawa duniya wacece ita? Ta tona mata asiri ta tozarta ta a gaban jama'a, yau ita kam ta shiga 3 ta lalace, tana cikin tunanin ta jiyo muryar Azrah na fad'in fuskarta babu annuri ko kad'an se dae cikin zuciyar ta ita kad'ae tasan tsoron da take ji

"Ke kici abincin" ta fad'a tana matsar da abincin gaban Mami, shi dae seya zama kamar wani sak'ago, kallan ta kawae yake yi ya kasa cewa komae, wane tunani ma ya kamata yayi ne?, Se kuma ya mayar da dubansa kan Mami wadda rashin gaskiya ya gama bayyana k'arara a tattare da ita, Mami ta mik'e kamar zata sanya kuka haka ilahirin jikin ta rawa yake yi tace

"Kamar yaya inci abincin? Ke dae kici mana waye yasan abinda kika saka a ciki? Seki fara ci mu gani sannan muma muci" Azrah tayi wani yak'e sannan tace

"Kin san kina zargin na zuba wani abu meyasa shi kuma kikace yaci?" Seta kalli Don mutumin da bata tunanin maganar kirki ta ta6a shiga tsakanin su tace ba tare da ta kalli cikin idanun sa ba

"Kada kaci abincin nan, ta saka wani abun a ciki" ta fad'a tana share k'wallar data zubo mata a fuska, cigaba da kallan ta yayi babu ko k'iftawa duk wani abun da ta fad'a yake rarrabewa yana so ya fahimci maganar ta ta, ya musu fassara dae_dae, amma ya kasa, kawae dae ga abinda take fad'a d'in a ransa amma ya kasa fassara su dae_dae, kansa yayi masa wani mugun nauyi gingirin haka yake jin sa, Mami ta fashe da kuka tana kallan Azrah tace

"Na shiga 3 ni ennan, ke ni zaki yiwa sharri?, Yanzu duk halaccin dana miki amma da abinda zaki saka min kenan?, Na shiga 3 ni Hadeeza".......



Ba'a nan naso tsayawa ba ycn 🥺 amma zamu had'e gobe in Allah y kaemu 🥺

✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION39*




___So yake yayi k'ok'arin marin ta amma yadda take magana da k'arfin gwuiwa yasa ya kasa aekata hakan, gashi sam ko alamar rashin gaskiya 1 be bayyana a tattare da ita ba, ta katse masa tunani da fad'in

"Idan baka yadda ba kace mata ita taci tunda kae so take kaci" Lumshe jajayen idanun sa yayi yace yana kallan Mami

"Mami me wannan shashashar yarinyar take fad'a ne?"

"Shirme da hauka mana, da son rama alkhaeri da sharri" Mami ta fad'a kamar zata fashe da kuka, Azrah tayi gaba ta matsa kusa da Don da har lokacin yake kallan su kawae tace

"Ko ka yadda ko baka yadda ba ni dae ina rantse maka da girman Allah gaskiya nake fad'a maka, na gama nawa aekin , yadda kuma ta rage naka, ko kuma zaka iya d'aukar abincin kayi bincike akan sa" daga haka ta wuce sama tana jin yadda kuka ke shirin k'wace mata amma ta rik'e shi har seda ta shiga d'akin ta sannan ta sake shi, kuka take sosae wanda bata san dalilin yin sa ba, seda tayi me isarta sannan tayi shiru tana nazarin abinda ya kamata tayi next, so take ta tashi ta had'a kayan ta dan kuwa bata ga amfanin cigaba da zaman ta a cikin gidan wanda be san darajar ta ba, gwara ta koma k'auyen su kawae tunda ta ankarar dashi abinda be san dashi ba, amma kuma se tayi tunanin ae kusan duk kayan da take amfani dasu ba itace tazo dasu gidan ba a gidan ta samu, mik'ewa tayi ta k'arasa cikin wardrobe d'in ta ta d'auko wata jaka ta d'auki kayan da tazo dasu daga k'auyen su da wanda Ammi ce ta bata su dukka ta had'asu cikin jakar sannan ta koma ta zauna... Cigaba da kallan Mami yayi wadda ke ta sharar k'walla yace cikin dakakkiyar murya

"Maaami!" Kafin ya sake cewa komae Mami tace cikin shasshek'a k'irjin ta na bugawa

"Kada ka damu nice na samo ta koh? Ae laefi na ne ni da nayi mata rana yanzu gashi tana nema ta saka min da akasin hakan, nayi danasanin taemakon mace kamar ta" cigaba yayi da kallan ta haka kawae yake jin wani yanayi na ziyartar sa, wani yanayi na d'arsuwa a cikin ransa, Mami data lura da kallan da yake mata tace

"Aou ko yadda zaka yi da abinda tace Son? Nice fa! Nice fa Mamin ka! So take ta raba mu, ina ga dama da wannan manufar ta shigo gidan nan, ka bari yanzu zan d'auki abincin nan naje na zubar, daga yau ka dena cin abincin ta, kae gaba d'aya ma ka gama zama a gidan nan tunda na lura so take ta kashe min kae ta cuce ni" Ya sake lumshe idanun sa na tsawon second 3 sannan ya bud'e yana tuna yadda Azrah ke magana cike da k'arfin hali har hakan yasa ya kasa k'arya ta ta ko kuma ya d'auki mataki akan maganar da take fad'a akan Mamin sa, toh amma meyasa zata masa k'arya? K'aryar ma akan Mamin sa, lallae akwae lauje cikin nad'i, Flask d'in da Mami ke k'ok'arin d'auka ya dafe da hannun sa ba tare da yace komae ba, Mami ta girgiza kae hawaye na zuba daga idanun ta, seya sake runtse idanun sa kafin ya janye shi kawae yayi waje dashi a hannun sa, zubewa Mami tayi a wajen ta saki k'arar da bata shirya yin ta ba, ta toshe bakin ta tana fad'in

"Na shiga 3 na lalace, wayyo ni" se kuma ta mik'e ta koma parlourn ta d'auki jakar ta kawae ta fice daga gidan ko takan drivern ta bata bi ba. Koda ya fita daga cikin gidan yana cikin driving ya tsaya a gefen titi, ya dafe kansa dake wani mahaukacin sara masa, meyasa yake neman ya tuhumi Mami? Idan yayi hakan kuwa ya kyauta? Anya kuwa yayi halacci? Toh amma kuma baya tunanin wannan yarinyar zata masa k'arya akan Mami tunda tasan wacece Mami a wajen sa, seya lumshe idanun sa kana ya bud'e ya tashi motar ya cigaba da driving, kae tsaye wani asibiti ya nufa, yana zuwa compound d'in yayi parking sannan ya sake yin shiru, wayar sa ya d'auka yayi dialing wata number, kira 1_2 ya d'auka, a hankali cikin muryar sa da bata fita yace

"Ina cikin hospital d'in ku pls.." daga haka yayi shiru, daga baya kuma ya ajje wayar. Wajen mintina 5 sega wani ya bud'e motar ya shigo da murmushi kan fuskar sa yace

"Ina fatan dae lafiya? Dan nasan babu dalili dae ba abinda ze kawo ka asibitin nan" ya fad'a annurin fuskar sa na chanjawa da ganin yanayin Don d'in, flask d'in dake back seat Don ya janyo ya mik'awa mutumin yace a hankali

"Bincike nake so amin pls" Kallan flask d'in yayi sannan ya kalli Don yace

"Da wurwuri kake so ne?"

"Yeah ko yanzu ma" Don ya fad'a ba tare da ya kalli mutumin ba

"Ohk, In Sha Allah yanzun zan kae a bincika, zuwa anjima kad'an zan kira ka"

"Thanks" kawae Don yace, mutumin ya fita daga motar ya kullo k'ofar, ba tafiya yayi ba dan baya tunanin zema iya tafiyar beji matsayin da ake ciki ba dan yadda yake jin zuciyar sa kamar zata faso k'irjin sa, yana nan zaune kan sa kife akan steering, wajen awa 1 wayar sa tayi k'ara, da sauri ya d'ago kansa ya kalli wayar, ganin me kiran ya sanya shi saurin d'agawa, daga can 6angaren akace

"Amma Don kana da alak'a ne da wannan abincin?" Runtse idanun sa yayi lokaci guda yana dafe kan sa yace

"Just tell me meke faruwa?" Daga can 6angaren shiru ya d'an yi kafin daga bisani yace

"Ehh toh anyi anfani da wani sinadari ne cikin abincin wanda ka iya janyo lalacewar wasu 6angarori na jikin d'an Adam, kamar lakar jikin mutum kan iya lalacewa idan yaci abincin nan..amma abinda bangane ba shine wanene ya dafa abincin kuma wa aka bawa yaci?" Qitt ya katse kiran bugun zuciyar sa na k'aruwa, yana jin yadda tunanin sa ya tsaya cakk, k'wak'walwar sa na dakatawa da aeki na wucin gadi, gumi ya shiga tsatstsafo masa, haka ciwon kan da yake ji ya k'aru, ya kwantar da kansa kan kujerar da yake kae, ya kasa tunanin komae ji yake kamar k'wak'walwar sa zata tarwatse, wajen minti 10 ya d'auka a haka kafin ya fara dawowa hayyacin sa ya bud'e idanun sa da suka chanja colour ya tashi motar ya fice daga cikin asibitin da wani irin mahaukacin gudu, ba wani sosae yake ganin gaban sa ba a haka ya isa wani k'aramin joint, Ikon Allah ne kawae ya kaeshi, yana tsayawa ya sauka daga motar ya shige cikin wajen, Irfan da tun shigowar sa cikin wajen ya lura dashi ya mik'e ya k'arasa wajen sa yace

"Barka da zuwa Don, mu k'arasa can" ya fad'a yana nuna masa inda yake zaune, be bi ta kansa ba kawae yayi gaba ya zauna yana sake lumshe idanun sa kamar wanda ya sha wani abun, Irfan be zauna ba seda yaje ya samo shisha da taba ya kawo ya ajje gaban Don, beyi wata wata ba ya fara bankawa k'wak'walwar sa hayak'i, Irfan kam kallan sa kawae yake yi, yana mamakin abinda aka masa haka daya 6ata masa rae kamar hakan nan, can dae ya kalli Don yace

"Ko a kawo babbar?" Shiru yayi ba tare da ya kalle shi ba, ba tun yau ba yake jin kamar idan ya sha giya ya aekata wani babban laefi ne, dan haka bece komae ba ya cigaba da busa hayak'in har lokacin bugun zuciyar sa be koma normal ba, he just can't believe cewar Mami ce take shirin aekata masa haka, his beloved Mami, Mami dae Mamin sa, anya kuwa?...Wayar sa dake ajje tayi ringing, be ko kalle ta ba ya share, Irfan daya kalli me kiran yace yana kallan Don

"Dad ne fah.." nan ma be kalle shi ba kuma bece komae ba, kira ya sake shigowa cikin wayar, Irfan ya sake cewa

"Dad fah.." se a lokacin ya ajje abinda yake yi sannan ya kalli wayar sa data sake yin ruri a karo na barkatae ya d'auka yana karawa a kunnen sa, daga can 6angaren Dad yace

"Me kake yi haka ina kiran ka baka d'aga ba?" Ya bud'e idanun sa dake lumshewa da kansu kawae yace ba tare da yana da tabbacin Dad d'in zeji abinda yace ba

"Ina.."

"Its ohk.. yau dae Alhaji Abbakar zezo gidan nan, jiya jiyan nan ya dawo kuma gashi yau zezo saboda haka duk abinda kake yi kazo ku gaesa" yace da muryar sa da bata fita sosae saboda tsananin 6acin rae

"Dad...!!"

"Complain.." Dad ya fad'a, seya d'an yi shiru yana sauraron abinda Dad d'in yake fad'a

"Zaka zo ne, ko kuma na saka a raena bani da d'an da zemin biyayya?" Idanun sa a lumshe yace muryar sa a cushe

"Ohk.." daga haka ya katse wayar ya ajjiye ta kawae....


__Tana gama had'a kayan nata ta d'auki jakar ta sakko daga saman, babu kowa a parlourn hakan ya alamta mata cewar duk sun fita kenan, hakan na nufin dole ta jira dawowar sa kenan? Babu yadda ta iya haka taja k'afafun ta ta koma cikin d'akin tayi shiru tunani barkatae na yawo a k'wak'walwar ta, tana zama wayar da ko ta kanta bata bi ba tayi ringing, ta k'arasa ta d'auki wayar ta kara a kunnen ta dan taga wadda ta kira wayar, daga can 6angaren Meemarh tace

"Hello Azrah kina lafiya?" A hankali ta furta

"Lafiya k'alau"

"Kina lafiya kuwa?" Meemarh ta fad'a tana jiran amsar Azrah, Azrah ta girgiza kae sannan tace

"Babu komae fah.." Meemarh tace

"Ohk, dama kira nayi na fad'a miki yau zamu shiga gidan su Yah Adnan dasu Ummi kin san Abba ya dawo toh In Sha Allah zan biyo ta nan in dae mun fito da wuri" Azrah ta d'an yi yak'e tace

"Eyyah, Madallah amma.. Meemarh ba lallae ki same ni a gidan ba akwae inda zanje, zamuyi waya kawae" ta fad'a kafin Meemarh tace komae ta katse wayar ta kashe ta ma gaba daya ta jefar da ita gefe, sannan ta sake jinginar da kanta kan gado idanun ta a lumshe, yanzu burinta d'aya ne kawae taji dawowar sa ita kuma taje ta tambayi takaddar saki tunda dama tasan ya dad'e yana jiran wannan rana....


__Seda ya k'ara fiye da 1hour sannan ya mik'e, Irfan ya kalle shi yace shima yana mik'ewa

"Ko zaka tafi da wasu ne?" sake lumshe idanun sa yayi kafin yace yana yin gaba

"A'ahhh" daga haka yayi gaba, Irfan ma ya biyo shi yace har lokacin tafiya suke yi

"Ko nazo nayi driving na ka?" shigewar da yayi driver seat ya zauna ne ya bawa Irfan amsar tambayar sa, yana shiga ya tashi motar ya fige ta da gudun gaske, tafiyar mintuna ce ta kae shi gidan nasu, yayi parking motar sa a compound d'in, seda ya kwashe wajen mintuna 2 yana cikin motar kafin ya fito cikin wani irin taku dana gaza gane a wane fannin zan saka shi, a hankali ya k'arasa part d'in Dad kae tsaye ya kutsa kae cikin d'akin, be kalli kowa dake cikin d'akin ba direct ya k'arasa kujerar da yake hanga ya zauna, seda ya zauna sannan ya jiyo muryar Alhaji Abbakar na fad'in

"Welcome my Son" ya bud'e jajayen idanun sa sannan yayi wani d'an murmurshi yace

"Barka Abba" Alhaji Abbakar yace

"Barka dae Son, ya aekin? Ya gida kuma?" Akan la66ansa ya amsa da

"Alhmdlh" dan baya jin ze iya doguwar magana a yanayin da yake ciki, Dad ya bishi da kallo yadda ya ganshi duk a wani hargitse, sumar kansa duk itama a hargitse, kawae seya cigaba da bin duk wani motsin sa da kallo ba tare da yace masa komae ba, Ummi ta kalle shi da murmushi kan fuskar ta tace

"Sannu da zuwa Adnan, ya aekin ?" ba tare daya kalle ta ba yace

"Alhamdulillah" Yakumbo dake zaune kusa da Ummi ta ta6e baki a ranta tana fad'in

"Mutum se bak'in hali da bak'ar zuciya, ayi mutum kullum cikin fad'in rae" Ummi ta kalli Meemarh da Meemee suma da suke zaune a kujera d'aya tace

"Hala baku iya gaesuwa ba?" ta fad'a tana jefa musu harara, Meemee ta turo baki tace

"Ummi ba fa amsawa ze yi ba.." Kafin ta k'arasa maganar ta jiyo muryar Meemarh na gaeshe shi, ta juya itama ta jefa mata harara, daga haka ya koma ya kwantar da kansa kan kujerar ya lumshe lumsassun idanun sa... Ammi ta fito daga kitchen d'auke da warmers a hannun ta, ita kuma Mami ta shigo d'akin kamar wadda aka koro duk a hargitse, Ammi ta kalle ta tace

"Yawwah sannu da zuwa, tunda ma kin dawo taemaka ki d'auki ragowar abincin, dama yalla6ae ne yace akae parlourn sa yana da bak'i" Mami dae babu abinda jikin ta yake se rawa kawae yak'e take yi tace

"A'ah kije kawae" Ammi ta kalle ta sosae sannan tace

"Hajiya hadeeza ko dae wani abun ya faru ne?" Mami tayi yak'e tace

"A'ah me kika gani? Muje na taya ki kae kayan" Mami ta fad'a tana k'arasowa ta d'auki wasu kayan sannan suka fara tafiya, Mami dae ita kad'ae tasan yanayin data ke ciki, Mami ce a gaba Ammi a baya a haka suka shiga parlourn Dad d'in, Mami dama ta riga data sadak'ar ba zata samu Adnan a gida ba kafin lokacin tasan yadda zata 6illowa al'amarin, Mami na ajjewa itama Ammi ta k'arasa tana shirin ajjewa, Alhaji Abbakar da d'agowar sa kenan idanun sa suka sauka akan Ammi, cikin wani irin tashin hankali, mamaki, firgici gami da tsoro ya furta

"Fatima!!!" Mami, Dad, Yakumbo, Ummi, Meemarh, Meemee har ma da Ammi dukkan su seda suka kalli Alhaji Abbakar (Abba), cikin sakannin da basu wuce 3 ba idanun Ammi suka sauka akan Alhaji Abbakar, a take kuma a lokaci guda abubuwan dake hannun ta suka tarwatse kowanne yayi nasa wajen, sannan itama a hankali ta sulale a wajen bayan tayi wata muguwar zabura kana ta zube babu alamar rae a tattare da ita.........



08124818273


✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION40*



___Alhaji Abbakar da kuma Mami ne suka yi kan ta, Mami ta rik'o ta tana fad'in

"Mik'omin ruwa" ta fad'a ba dan tasan da wanda take maganar ba, Meemarh ce tayi k'arfin halin mik'ewa ta isa fridge ta d'auko rubber water ta mik'awa Mami, ta tsaya ta cigaba da kallan matar, Mami ta kar6a ta shafawa Ammi a fuskar ta, se da ta safari mata sau 2 sannan Ammi ta sauke doguwar ajiyar zuciya kana ta fara bud'e idanun ta, Ummi dake zaune tun d'azu ta kaasa tashi idanun ta suka sauka akan Ammi, se tayi zumbur ta mik'e, Alhaji Abbakar da yayi collapse kan kujera idanun sa a rufe hannun sa akan fuskar sa ya bud'e idanun

Please Login or Register in order to submit comment