Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata shi ke iko da ita ba kowa ba... A 6angaren ta kuwa taji dad'in tafiyar tasa dan haka ta mik'e, tana shirin shiga d'akin Ammi tace

"A'ah Azrah!" tsayawa Azrah tayi tana kallan Ammin kawae seta tsinci kanta da tunanin zaman da suka yi kafin tasan itace mahaefiyar ta, lallae Ammin ta ta macece me kirki, ba tare da tasan wacece ita ba amma ta d'auke ta kamar er data haefa

"Ina yake?" Ammi ta katse mata tunani da fad'in hakan, seta juya ta kalli cikin parlourn kafin ta maeda idanun ta kan hannun ta tana wasa dashi tace

"Nima bansani ba Ammi"

"Azrah.." Ammi ta fad'a tana kallan ta sosae, ta d'aga idanun ta da suka yi rau rau ta kalli Ammin, girgiza kae kawae Ammi tayi kana ta wuce itama Azrahn ta shige d'akin ta....



...
Wajen k'arfe 7 ne ta farka daga nannauyan baccin daya d'auke ta, tana shirin sauka daga kan gado aka turo k'ofar d'akin, Zarah ta k'araso sanye cikin uniform tana kallan ta tace

"Wato ke dad'i gida koh? Kin manta yau akwae test d'in English?" Zaro manyan idanun ta tayi kafin ta mik'e ta fad'a toilet, minti 10 se gata ta fito tana kallan Zarah fuskar ta a maraeraece tace

"Fisabilillahi meyasa baki tuna min ba, gashi ko karatu banyi ba, kuma uniform d'in ma suna wancan gidan" Zarah tace

"Kwantar da hankalin ki, kinsan dae Uniform biyu akamin, so gashi na taho miki da d'ayan seki saka"

"Yawwah my luv" Azrah ta fad'a tana murmushi kana taja ledar dake gefen Zarah ta koma toilet d'in ta sako su sannan ta fito, babu abinda ta shafa a fuskar ta amma kyawun ta ya fito sosae, ta d'auki hijab d'in ta saka, seta dakata ta kalli Zarah tace tana d'an bud'a ido

"Kinga fa hijab d'in?" dariya Zarah tayi kafin tace

"Wallahi kuwa a haka suka bani, ya zanyi toh?" dae_dae lokacin Ammi ta shigo d'akin ta kalli Zarah da murmushi kan fuskar ta tace

"Fatan dae kinji dad'in makarantar?"

"Sosae ma kuwa Ammi, makarantar akwae dad'i haka d'aliban cikin ta ma suna da kirki" Ammi tace

"Toh Masha Allah" ta fad'a tana maeda duban ta kan Azrah dake ta 6ata rae tana jan hijab d'in kamar wanda ze janyu, Ammi tace

"D'auki abaya ki d'ora akae, idan kika je makarantar seki cire" wayar Ammi ce tayi k'ara ta duba me kiran sannan ta kalle su tace

"Sekun dawo Allah ya tsare" daga haka ta fice daga d'akin, Zarah ta kama hannun Azrah tace

"Don Allah ki taho mu tafi kawae, bafa titi zamuje ba, daga cikin mota se class fa" Azrah tace

"Nidae duk da haka.." Zarah bata jira Azrah ta sake cewa komae ba ta jata suka fice daga d'akin....



...
A hankali ya dakata da driving d'in da yake yi yabi makarantar tasu da kallo, kamar wanda ake ja haka ya chanja akalar tafiyar tasa zuwa cikin makarantar, seda masu gadi suka duba shi saboda glasses d'in sa dake a rufe sannan ya shige ciki, ya nemi waje yayi parking motar tasa har lokacin glasses d'in na a rufe ne, ya cigaba da bin cikin makarantar da kallo.. Dukka en ajin ne suke fitowa daga class d'in saboda malamin da yace ba'a ajin zeyi test ba, ze had'e su a wani Hall yayi musu test d'in, dan haka yanzu ma can suke tafiya, ita da Zarah ne suke tafiya a tare, ita dae duk a takure take, wani d'an ajin su ya k'araso inda suke yace yana murmushi

"Hajiya Azrah nifa yau banyi karatu ba, ina fatan zaki bani amsa" ba tace komae ba illah murmushin yak'e da tayi tana sake bada wata er tazara a tsakanin su, shi kuma ya d'an sake matsawa kusa da ita yana sake fad'in

"Bak'uwa ki saka baki mana".. Runtse idanun sa yayi daga inda yake zaune kana ya sake bud'ewa, a hankali ya tura murfin motar ya fita daga ciki ya fara takawa zuwa inda suke idanun sa a kansu zuciyar sa na masa wani irin zafi da besan dalili ba, Zarah ce ta fara hango shi ta k'ank'ance idanun ta tace har lokacin tana kallan sa

"Yah Adnan?" jin sunan data ambata ne ya sanya Azrah d'aga kae ta kalli inda Zarahn ke kalla, idanun ta suka sauka a kansa yana dab da k'arasowa inda suke, kawae se suka dakata a inda suke, d'an ajin nan nasu yace

"Wowww, ku duk haka kuke da kyau, da alama wannan ma yayan ku ne dan naga...." shak'o wuyan sa da yaji anyi ne ya sanya shi dakatawa be k'arasa fad'ar abinda yayi niyya ba, idanun sa suka yo waje cike da tsoro, Azrah ma da Zarah gaba d'aya tsoran ya gama bayyana a tattare dasu musamman Azrah da jikin ta ya d'auki rawa, Zarah ta kalli gefe da gefe sannan ta dawo da duban ta kan Don dake fad'in cikin 6acin rae

"Kana so ka mutu?" cikin matuk'ar tsoro ya girgiza kansa hannun sa akan hannun Don, har lokacin be sake shi ba yace

"Kada ka sake zuwa inda take ballantana har magana ta had'a ku idan ba haka ba zanyi maganin ka" daga haka ya sake shi da k'arfi yayi baya yana tari, ya kalli inda take tsaye kamar wadda aka dasa ta, ya sanya hannun sa ya kamo tsintsiyar hannun ta da k'arfi ya jata, yanayin tafiyar su ba d'aya bace dan haka tafiyar da yake ita kuma seya zamana sauri take yi kamar zatayi tuntu6e, be tsaya ko ina ba seda ya isa wajen motar sa, ya bud'e front seat ya jefa ta ciki sannan ya koma driver seat ya zauna ya fizgi motar kamar ze tashi sama, Zarah ta bi motar da kallo cike da mamakin al'amarin Don d'in, anya kuwa shine? ... Tunda suka fara tafiya tayi shiru ta kaasa gane tunanin me zatayi, shi kam se sharara uban gudu yake yi, seda yayi tafiya sosae sannan ya nemi gefen titi ya tsaya, ya jinginar da kansa jikin steering idanun sa a lumshe, se can ya d'ago ya kalle ta da jajayen idanun sa, wani takaecin na sake kama shi, haka kawae wannan figigin hijab d'in nata ya bak'anta masa rae, ga kuma wani shege harda mata magana

"Saboda baki san mene aure ba, baki san mutuncin sa ba shine zaki saka wannan figigin hijabin, ki shiga makaranta dashi kowanne k'ato da gardi ya kalle ki, ki kula duk wanda kika ga dama sannan kiyi hira da kowanne k'ato, toh daga yau na soke zuwa wata makaranta, wannan umarni ne daga waje na" d'agowa tayi ta kalle shi a ranta tana sak'a "kae a matsayin ka na waye? Ka manta saki na zaka yi?" kawae seta fashe da kuka ta maeda kanta jikin window ta jinginar tana yin kukan a hankali, ya lumshe idanun sa kana ya tada motar duk da yadda yake jin kukan nata har cikin jikin sa, me wannan yarinyar take so ta zama ne a wajen sa?.... Da kuka ta shigo d'akin kamar wadda aka fad'awa labarin mutuwa, Ammi taji gaban ta ya fad'i amma saboda Ummu data mik'e ta rik'o Azrahn yasa ita ta zauna kawae, Ummu ta rungume ta tana fad'in

"Subhanallahi Azrah meya faru?" Shiru ta cigaba da kukan ta, seda tayi me isarta sannan tayi shiru ta tashi daga jikin Ummu tana sheshshek'a tace

"Ummu kinji wae ya hanani zuwa makarantar"

"Waye?" Ummu ta fad'a tana kallan ta

"Shi mana, daga can makarantar ma fa yaje ya d'akko ni" Ummu tace

"Toh amma saboda me?" share hawayen ta tayi kana tace

"Ni bansani ma Ummu, kawae fa mun fito da wasu en ajin mu zamu yi test, muna cikin magana da wani d'an ajin mu akan test d'in se gashi yazo wae ze kashe d'an ajin namu"

"Toh fah babbar magana, dan kawae kunyi magana da wani d'an ajin ku se ace an hana zuwa makaranta?" Ummu ta fad'a, yayin da Ammi ta lumshe idanun ta tana jin wani farin ciki mara misaltuwa na mamaye ilahirin jikin ta, Azrah tace

"K'yale shi mana"

"Tashi kije ki hutawar ki kinji? Ae zancen k'in zuwa makaranta ma be taso ba"

"Ummu ni kawae ya sake ni shikenan ba ruwan sa da rayuwa ta"

"Toh shikenan jeki abin ki kinji?" Murmushi Azrah tayi kana ta mik'e zuwa d'akin ta, Ummu ta bita da kallo cikin jin dad'i, dan indae harta fahimta dae_dae ba komae ne ya sanya Don yin abinda yayi ba illa kishi, kuma ba'a kishin abu se idan ana son sa, Ummu ta kalli Ammi tace

"Da alama lokacin Azrah yazo, inaga lokaci yayi da zamu maeda masa da mata" Ammi tace

"Hakan ma yayi" Ummu ta d'an yi murmushi sannan tace

"Amma fa ba yanzu ba Ammi, se mun koya masa hankali, seya gane muhimmancin Azrah sannan zamu maeda masa ita, dan kuwa har yanzu be kae ga gane kuren sa ba" Ammi tace

"Eyyah kuyi wa Adnan hak'uri, haka yake tun yarinta miskili ne na k'arshe kuma ga dad'in halin kishiyar uwa" Ummu tace

"Uhmm Ammi, makaranta dae tunda yace baya so a k'yale shi, idan yaso duk sanda yaga ze maeda ta ya mayar da ita d'in amma dae mayar da ita kam se randa na tabbatar yasan daraja da kuma muhimmancin 'yata" Ammi ta girgiza kae kana tace

"Ae shikenan"



... Da daddare ne wajen k'arfe 8 tana zaune kan gadon ta, so take taji ya labarin su Meemarh dan har yanzu basu dawo gida ba, sedae bata san yadda zatayi taji labarin nasu ba, Ammi ta shigo cikin d'akin ta nemi waje ta zauna kan gadon, ta kalli Azrah tace

"Azrah..."

"Na'am Ammi.." Ammi tace

"Kina jina koh? Inaso ki bar maganar makarantar nan kinji koh? Tunda yace miki baya so ki hak'ura uhmm? Nan gaba se kiga da kansa ze mayar dake, yanzu dae tunda ya nuna baya so ki k'yale shi kinji?" jinjina kae kawae Azrah tayi, Ammi ta mik'e tana murmushi tace

"Yawwah" daga haka ta fice daga d'akin, seda ta fita sannan Azrah ta fashe da kukan da take ta rik'ewa, meyasa mutumin nan ya zama me son kansa da yawa ne haka? Shi koda yaushe burin sa ya wulaqanta ta? Yanzu makarantar ma da take zuwa seda yayi yadda zeyi ya hanata zuwa? Kuma Ammi tabi bayan sa kamar shine me gaskiya, seta sake fashewa da kukan tana jin yadda haushin sa da tsanar sa ke k'aruwa cikin zuciyar ta..



... Tana zaune cikin parlourn sanye cikin riga da wando fallazo, kanta sanye cikin wata hula me taushi wadda bayan ta a bud'e yake hakan ya bawa gashin ta damar zuba kan kafad'ar ta, kallo take a tashar MBC bollywood inda suke nuna Humraaz, sam ba taji shigowar mutum ba dan gaba d'aya hankalin ta na kan TVn ne, kuma da yayi sallama kamar yadda kowa keyi to tabbas zata ji, muryar Ammi taji tana fad'in

"Lale, yalla6ae barkan ka da zuwa" Se ta d'aga kae ta kalli inda Ammin ke kalla dae_dae lokacin da yake k'ok'arin zama kan kujera, tana shirin mik'ewa Ammi ta watsa mata harara seta koma ta cigaba da zama tana tura baki, Ammi ta nemi waje ta zauna suka gaesa sannan yace

"Ya jikin?"

"Jiki Alhamdulillah, na warke ma" ta fad'a tana bin Azrah da kallo, ita kam bata san sanda Azrah ta zama haka ba, tana kallan mutane amma ko gaeshe shi tak'i yi, ganin kallan da Ammi ke binta dashi ne ya sanya ta fad'in ciki ciki kamar me shirin yin dambe

"Ina kwana?" ya d'aga ido ya kalle ta dama tun d'azu yake son kallan nata yadda tayi wani shahararren kyau, kayan sun matuk'ar amshe ta, dan ze iya cewa yau ce rana ta farko daya ta6a ganin ta babu hijab kuma cikin haske haka, se yaga tama fi kyau a hakan, shi kam lamarin jinsa yake kamar asiri wae yau shine yake son kallan wata halitta, halittar ma mace, har idan ya kalle ta yaji dad'i a ransa, Ammi kam mik'ewa tayi tace

"Bari a samo maka ruwa" daga haka ta mik'e, itama Azrah mik'ewar tayi tana shirin tafiya yace cikin dakushashshiyar murya

"Wallahi kika k'ara taku d'aya zaki ga abinda zan miki" dakatawa tayi daga inda take tsaye, se kuma ta juya fuskar ta a had'e kamar ba waccan Azrahn ba me tsoron Don tace

"Kayi hak'uri ka bani takadda ta kona samu enci gaba d'aya, na cigaba da zuwa makarantar da kake k'ok'arin hanani zuwa saboda kana tak'ama da kae ke aure na, meyasa ne kae koda yaushe cikin son datse min farin ciki kake yi? yanzu haka ina tare da iyaye na cikin farin cikin da bana tunanin zan same shi har abada, ka fad'a da bakin ka baka sona to ka huta mana nima ka hutar dani ka sake ni mana tunda nima bana sonka..." ta fad'a ba tare da ta kalle shi ba, runtse idanun sa yayi saboda yadda yaji zafin kalaman nata, yaji zafin su matuk'a, take bugun zuciyar sa ya k'aru, se kawae ya mik'e daga inda yake zaune ya matso dab da ita ya rik'o hannayen ta ya sanya ta tana kallan sa yace yana kallan cikin k'wayar idanun ta

"Kalli cikin ido na kice bakya sona?!" wani murmushin takaeci tayi idanun ta a rufe dan tasan k'arya ne ta iya kallan cikin idanun sa ta masa magana

"Ni ka cika ni" ta fad'a tana iya k'ok'arin ta dan k'wace hannun ta, yace

"Bazan saki ba, se kin fad'a min meyasa kika hanani cin abinci me guba har sau biyu idan har kinsan bakya sona?" Se a lokacin ta bud'e idanun ta akayi sa'a idanun nata basu sauka a cikin nasa ba tace fuskar ta a had'e, bata san meyasa duk wani tsoron sa da take ji yanzun ya ragu da kaso 90 cikin d'ari ba

"Bakae ba, koma wane musulmi ne na ganshi cikin irin yanayin da kake ciki zan taemaka masa, saboda haka kada ka yaudari muguwar zuciyar ka tayi tunanin so ne ya sanyani yin hakan ballantana ka sake samun wata damar da zaka wulak'antani, meyasa zan so mutumin da baya sona? Besan mutunci na ba besan daraja ta ba? Rashin ajin nawa be kae nan ba.." kamar wanda ya gane miciji ya rik'e ya saki hannun ta da sauri, da mad'aukakin mamakin ta da be ta6a yi ba yake kallan ta, maganganun ta sun bashi tsoro haka zalika sun bashi mamaki, ya cigaba da kallan ta babu ko k'iftawa...........

✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION47*



___Ya akayi yau shine ake fad'awa magana yaji kuma ya shanye ba tare daya tanka ba, kuma mace ce ma me fad'a masa maganar, macen ma k'arama kamar wannan, lallae akwae wani abun, k'wafa yaja kawae ya fice daga d'akin, seta samu kanta da binsa da kallo tana mamakin anya kuwa shine? Mene ma'anar wannan shishishige matan da yake yi? Seta shiga tariyo abinda ta fad'a d'in, Allah yasa 6acin rae besa ta fad'a masa maganar da bata dace ba, kaasa motsawa tayi ko nan da can har lokacin da Ammi ta taho da plate a hannun ta, ta k'arasa ta ajje sannan ta kalli Azrah ranta a d'an 6ace

"Azrah bana son rashin kirki fa, me kika masa ya tafi?" Shiru Azrah kawae tayi ta kasa ko d'aga ido ta kalli Ammi, hakan ya tabbatarwa Ammi wani abun ta masa kenan, lallae kam soyayya me chanja mutum, ko ba'a fad'a mata ba tasan Adnan na k'aunar d'iyar ta ta, Allah me yadda yaso a lokacin da yaso, kauda duk wad'annan tunane tunanen tayi tace har lokacin tana kallan Azrah

"Wae waye yake koya miki wasu abubuwan ne yanzun? Duk wani abu da kike yi bashi zesa ya sake ki ba se lokacin da yayi niyya kina jina koh?" d'aga kae tayi kana ta wuce cikin d'akin ta, Ammi ta bita da kallo..




... A kwance yake kan gadon hannayen sa d'ore akan fuskar sa idanun sa a lumshe, sosae bugun zuciyar sa ke fita a guje kamar wanda yayi tsere, duk da irin wad'annan maganganun data fad'a masa amma ya kasa mayar mata da martani ko ya d'auki tsatstsauran mataki, meyasa? Kodae son ta yake yi? Idan kuwa hakane zuciyar sa bata masa adalci ba, meyasa zata masa haka? Meyasa zata fad'a son wata a lokacin da be shiryawa hakan ba? Kuma son ma me zafi hakan nan, be ta6a tunanin ze ta6a son wata d'iya mace ba tuntuni dan shi sam mata basa gaban sa, se gashi yanzu ya tsinci kansa dumu_dumu cikin k'aunar wata yarinya wadda ya ta6a furtawa kalmar rashin so, anya kuwa be makara ba? Tabbas yana buk'atar ta a kusa dashi, yana buk'atar ya dinga ganin ta kullum, amma ta yaya? Kae ya zama dole ya samarwa zuciyar sa abinda take so, ashe duk da ba abinda ke had'a su cikin gidan, ganin ta kawae daya keyi wani abun ne? Be tashi sanin hakan ba seda tayi masa nisa, Lallae yana buk'atar yayi wani abu akan lamarin nan.....




... Tana gama maemaeta Hadith d'in ta ajje shi a gefen ta sannan ta d'auki qur'an tayi muraja'ar izu biyu kana ta ajje tayi addu'a sosae ta shafa, seta mik'e a hankali ta maeda su cikin wajen su kana ta fita daga d'akin zuwa parlourn.. Hango su Meemarh da tayi zaune cikin parlourn ya sanya ta k'arasawa da sauri ta rungume Meemarh cikin farin cikin ganin er uwat ta ta, fashewa da kuka Meemarh tayi se dae ba tace komae ba, Meemee tace a sanyaye

"Azrah don Allah ki yafewa Ummi" waskewa Azrah tayi sanda ta saki Meemarh ta zauna kusa da ita sannan tace tana kallan ta

"Yanzu kuka dawo?" Meemarh ta jinjina kae kana tace

"Ehh k'anwar Ummi ce yanzu ke zaune da ita, Abba ne yace mu dawo gida mu huta tukunna" Ammi tace

"Toh ya kamata kuje kuyi wanka kuci abinci sannan kuyi bacci ku huta" Da "toh" suka amsa dukkan su kafin suka mik'e tare har Azrah zuwa d'akin dake kusa da nata, d'aya suka shiga, Azrah na k'ara kad'aeta Allah wae ashe su Meemarh en uwan ta ne.. Abba ne ya shigo parlourn bayan fitar su, Ammi ta mik'e da murmushi kan fuskar ta tace

"Barka da zuwa yalla6ae" ya mayar mata da martanin murmushin sannan yace

"Yawwah barka dae.." ya d'an dakata sannan ya d'ora da fad'in

"Yana ganki ke d'aya ina Azrah?" Ammi ta kalli d'akin da suka shiga sannan tace

"Tana d'akin en uwan ta, basu dad'e da shigowa ba suma" Abba yace

"Toh madallah, ya kamata ta koma gidan ta haka nan, idan komae ya lafa se muje can k'auyen, dan yanzu nima akwae wasu ayyuka da dama da ban kammala su ba" Ammi tace

"Toh ranka ya dad'e" Murmushi yayi kana suka wuce tare...


...
A 6angaren Mami kuwa tun sanda ta bar gidan nan kae tsaye gidan yayar ta wadda suke uba d'aya ta wuce, yayar ta ta ta kalle ta ganin yadda tayi wani zuru zuru idanun ta sunyi luhu luhu tace tana kallan ta

"Lafiya hadeeza? Meya faru?" Fashewa da kuka Mami tayi ta shiga girgiza kan ta

"Na shiga uku na yau, Alhaji ya sake ni"

"Ya sake ki kuma? Giyar wake ya sha daze sake ki? Shekara d'aed'aed'ae har kusan talatin be ta6a sakin ki ba se yanzu, toh meyasa yayi hakan?" Mami tace

"Sam sam bashi da laefi wallahi, nice na janyowa kaena, laefi na ne, maganar nan dae tun ta kwanakin baya da kika ji munayi da Momyn Simrah kika hanani aekatawa, toh ban hanu ba seda na aekata abinda nayi niyya da taemakon zugar wasu mutanen, amma don Allah kiyi hak'uri ki barni na zauna a cikin gidan nan zuwa sanda komae ze lafa.. "

"Wace? Ni kuma? A'ah wallahi, in zauna in nuna miki ga abinda zaki yi ki saka k'afa kiyi fatali da hakan sannan yanzu ki dawo min?, wad'anda kika zauna dasu wajen shekaru talatin ma kin cuce su ballantana ni? Ae wallahi ya miki da sauk'i ma da saki ne kawae ya shiga tsakanin ku, kina tunanin da wani ne ze k'yale ki haka nan? Don Allah kiyi hak'uri ki tashi ki tafi, dama yanzun nan baban su ze dawo kuma kinsan ba wani shiri kuka cika yi ba, dan haka ki d'an hanzar ta don Allah"

"Kiyi hak'uri wallahi na chanja, wannan wata sabuwar Hadeeza ce ba waccan ba"

"Sorry for ur self, don Allah ki tashi, babu yadda za'ayi na yadda kin chanja halayen ki na tsawon shekaru da dama a cikin awanni" Mik'ewa Mami tayi jikin ta a matuk'ar sanyaye, hawaye fall a cikin k'wayar idanun ta, taja akwatin data shigo da ita ta fice daga d'akin, girgiza kae tayi cike da tausayin er uwat ta ta, amma gwara ta fara nuna mata laefin ta ta d'anga rayuwa ko kad'an ne, idan ba haka ba ba zata gane tayi wani abu mara kyau ba, tace a hankali

"Allah ya shirye ki Hadeeza" Mami na fita daga gidan kae tsaye adaedaeta ta tara ta fad'a masa inda ze kaeta, tafiyar mintuna kad'an ta kaesu unguwar, ta sauka ta bashi kud'in sa sannan ta shige cikin gidan, bata tsaya ko'ina ba se cikin parlourn, dae_dae sannan Hajja Kaltum ta fito daga d'aki tana kallan Mami ta dafe k'irji lokaci d'aya tana fad'in

"Innalillahi wa inna ilaehi raji'un, Hajiya Hadeeza me zan gani haka? Wanene ya mutu?" ta fad'a tana k'arasowa cikin parlourn, zama Mami tayi ta kaasa cewa komae se hawayen dake kwarara akan kuncin ta, Hajja Kaltum ta k'arasa fridge ta d'auko sanyayen pure water ta mik'awa Mami, babu musu Mamin ta kar6a ta shanye shi tass, Hajja Kaltum ta nemi waje ta zauna tana kallan Mami tace

"K'awata fad'amin abinda yake faruwa mana?" Mami ta girgiza kae kana ta fara fad'in

"Yau k'arya ta ta k'are Kaltume, yau an gane nike da saka hannu a al'amuran Adnan"

"Na shiga 3" Inji Hajja Kaltum

"Ke ae ba wannan ne babban tashin hankalin ba, ya sake ni fa" Mami ta fad'a cikin kuka, sauke wani uban numfashi Hajja Kaltum tayi tana komawa tayi zaman da6aro, seda ta dawo daga shock d'in da maganar ta jefa ta sannan tace

"Garin yaya ni Katta? Ya akayi kika bari suka gano?"

"Toh ya zanyi ni? Ya zanyi?" Hajja Kaltum ta sauke ajiyar zuciya kafin tace

"Shikenan, amma dae kin kwaso rabon ki kafin ki taho koh?" Mami ta girgiza kae

"Ina naga wannan nutsuwar, nidae nasan na d'auko gold da azurfar dake cikin drawer ta, amma wayata da ATM d'ina duka suna wajen Fawaz" Murmushi Hajja Kaltum tayi kana tace

"Yawwah ta kwana gidan sauk'i tunda suna wajen d'anki, kinga kar6ar su baza suyi mama wahala ba" Murmushin yak'e Mami tayi tana girgiza kae tace

"Baki san Fawaz ba shima bayan su yake bi, ae ni dae inaga k'arshe na ne yazo"

"Mtsww ke fa dad'i na dake kenan wallahi, kin cika saurin sarewa, ba dae kina da kadara ba? Toh zamu koma wajen Malam ne ya sake buga mana aeki akan su su duka, daga nan kuma ba shikenan ba?" girgiza kae Mami tayi tana kallan Hajja Kaltum tace

"A'ah, wallahi ba dani ba, har abada na gama zuwa wajen boka, ki barni da wancan zunubin ma dana kwaso" shek'ek'e Hajja Kaltum ke kallan Mami cike da mamakin jin furucin ta, se kuma can ta ta6e baki tace

"Allah malama, toh kenan meya kawo ki gidan nan?"

"Zuwa nayi ki taemaka min da wajen zama kafin komae ya daedaeta" Hajja Kaltum tace

"Ki zauna fa kika ce? Amma dae kinsan halin da ake ciki yanzu koh?" Kallan ta Mami tayi cikin rashin fahimta, Hajja Kaltum tace bayan ta sake ta6e baki

"Se dae idan kuma zaki dinga ciyar da kanki toh se inyi tunani akan hakan" Mami ta kalli Hajja Kaltum da matuk'ar mamaki wanda har seda ya bayyana akan fuskar ta tace

"Toh shikenan, ba komae hakan ma nagode" Hajja Kaltum ta d'an ta6e baki kana tace

"Toh yayi.." Daga nan Mami ta fara zama a gidan Hajja Kaltum d'in, se dae chanjin data gani a fuskar k'awar ta ta ba k'aramin mamaki yake bata ba, daga farko dae ta fara bata abincin, daga k'arshe kuwa se cewa tayi ta bada ko zobe d'aya ne a siyar a siyo wasu abubuwan naci komae ya k'are mata itama, da farko Mami ta nuna k'in amincewar ta, nan Hajja Kaltum ta nuna mata idan zaman nasu baze yiwu ba kawae ta k'ara gaba ita bata san rashin yadda, haka dae Mami ta bata hak'uri dan ta cigaba da zama a gidan amma bata bada zoben ba,

Please Login or Register in order to submit comment