Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

plate d'in dake d'auke da egg into egg ta d'auke shi ta koma cikin kitchen d'in ta ajiye sannan ta fito ta koma sama... Bata dad'e da zama ba taji wayar ta na k'ara, ganin me kiran ya sanya ta d'agawa da sauri, Meemarh tace

"Azrah!" Azrah tace

"Na'am, Meemarh ya kike?" Meemarh tace

"Alhamdulillah" Azrah ta d'an yi shiru sannan tace

"Naji muryar ki wani iri?" Meemarh ta d'an yi yak'e sannan tace

"Noo, babu komae, amma Azrah.." Se kuma ta d'an yi shiru, kafin Azrah tace komae ta cigaba da fad'in

"Meye gaskiyar abinda ke yawo a social media?" Azrah tace cikin rashin fahimta

"Kamar yaya?, meya faru?" Meemarh tace

"A'ah ba wani abu bane, baki ga komae ba kenan?" Azrah tace

"Kema dae Meemarh kin san bani da babbar waya, koda yake ma ni kin san ba burgeni take ba.." Meemarh tayi d'an murmushi tace

"Hakane.." Azrah tace

"Amma meya faru?"

"Zamuyi maganar a school" Meemarh ta fad'a, daga haka Azrah ta amsa da "toh" sannan sukayi sallama.




___Fawaz ya k'araso cikin d'akin hannun sa d'auke da wayar sa yace

"Mami, kalli fa abinda ake yad'awa.." Mami ta kar6i wayar tasa tana kallon abinda yake nuna mata, seta d'ago ta kalli Fawaz fuskar ta d'auke da mad'aukakin mamaki tace

"Waye ya d'ora wannan d'in?" Fawaz yace

"Mami bansani ba, bansan shi ba, kawae gani nayi zancen na yawo" Mami tace

"Mik'omun waya ta.." Mik'ewa yayi kamar ze tafi se kuma ya dawo yace

"Mami kiyi kiran a tawa mana" Mik'a masa wayar tayi tace har lokacin mamaki be bar fuskar ta ba

"Kamo min number sa" babu musu Fawaz ya kar6i wayar ya kamo number Don ya kira sannan ya mik'a mata wayar, yana d'agawa Mami tace

"Son.." Don yace

"A'ah Mami barka da wannan lokaci" Mami tace

"Barka dae Son, ya aekin?" Yace

"Alhamdulillah" yana shafa sumar kansa, Mami tace

"Amm, maganar dake yawo yanzun na gani, meya faru?" Don ya d'an yi shiru sannan yace

"Mami bansani ba, bansan yadda akayi hakan ta faru ba" Mami tace

"Ikon Allah, amma abin akwae mamaki sosae, ya kamata a sanar da Dad d'in ku komae saboda a d'auki mataki tun farko ayiwa tufkar hanci" Don yace

"No Mami babu buk'atar sanar dashi, na saka ayi min bincike, and ina da tabbacin kafin dare za'a samo min abinda nake nema, so ba se an fad'a masa ba.." Mami tace

"Toh shikenan Allah ya taemaka"

"Ameen" Fawaz dake gefe ya amsa yana kar6ar wayar da Mami ke mik'a masa yace bayan ya sake neman waje ya zauna

"Mami wallahi banji dad'in abin nan da ya faru ba" Mami tace

"Toh waye ma al'amarin ze masa dad'i?" Fawaz ya sake yamutsa fuska yace

"Mami kinji fa kuma wae tsintacciya ce abin hadda sharri.." Mami ta girgiza kae kafin tace

"Haka kasan wasu idan basuyi wa wani sharri ba basa jin dad'i" Fawaz yace

"Amma Mami su kam mutane me Bhai ya musu da zasu masa haka?" Mami ta kalli Fawaz ce

"Toh Fawaz ya zanyi in sani?"....





___D'aukar wayar sa dake ringing yayi ya sanya ta a hands free sannan ya cigaba da driving hankalin sa dukka na kan titi, daga can 6angaren akace

"Yalla6ae an gama komae" Don yace

"Weldone, ina driving ne zan kira ka idan na isa gida" daga haka ya katse wayar, gudun da yake ya k'ara yi a haka harya isa gida, tun kafin ya k'arasa shiga gidan ya danna kiran mutumin sannan ya cigaba da tafiya wayar kare a kunnen sa, daga can 6angaren mutumin yace

"Nabi diddigin daga inda labarin ya fara fitowa harya watsu a social media, naga sunan mutumin daya wallafa labarin wato daga wajen wanda rahoton ya fito, Sunan sa Abdussamad Yusuf, yana aeki ne a wani sabon gidan radio wanda ko 2month ba'ayi da bud'e shi ba, shine ya fara fitar da labarin a gidan radion, sannan wani shi kuma ya watsa labarin a social media, da shi na fara magana shine wanda na samu duk wannan information d'in a wajen sa, yace min wae daga farko Abdussamad d'in be amince ba akan fitar da zancen daga gidan radio zuwa wasu kafofin ba seda sukayi yarjejeniya da akan baze sanar da su daga inda zancen ya fito ba, zeyi kamar shine ya nemo labarin, so daga farko ma yaso ya 6oye min nima seda na sakar masa kud'i sannan ya fad'amin, amma ya rok'i na rufa masa asiri kada nace shine ya tonawa Abdussamad d'in asiri.." Don ya lumshe idanun sa kafin yace

"Ka turamin account number ka, sannan ka tura min da address d'in gidan radion.." Mutumin yace

"Toh ranka ya dad'e nagode sosae.." Daga haka Don ya sauke wayar sa yana bubbuga ta a hannun sa yana tunanin da kuma fad'ad'a k'wak'walwar sa ko ze tuna inda ya san sunan mutumin, amma be tuna ba, kwata kwata ma be ta6a jin sunan ba, toh kenan waye shi? Meye had'in sa da shi?, yana wannan tunanin wayar sa ta sake yin k'ara ya d'aga, mutumin ya fad'a masa ya tura masa address d'in sannan ya katse wayar... Tashi ya sake yi ya fita ya hau motar sa ya sake ficewa daga gidan, se da ya fita sannan ya kira wayar Sameer yana d'agawa yace

"Ina kan hanyar gidan ku, ka shirya akwae inda zamuje.." Sameer yace

"Ina?"

"Idan nazo zan fad'a maka" daga haka ya katse wayar ya cigaba da driving.... Befi minti 5 da tsayawa ba Sameer ya fito daga cikin gidan sanye cikin shadda blue ya k'arasa ya bud'e front seat ya shiga ya zauna yana kallan Don yace

"Gidan ne ba zaka shiga ba?" Don yace

"Noo, sauri nake" Sameer yace

"Ohk ina zamuje?" ya fad'a yana kallan Don d'in sanda yake k'ok'arin kunna motar, ba tare daya kalle shi ba ya fara driving d'in sannan yace

"An samo daga inda maganar ta fito, yanzu haka wajen zamu je dan jin daga aenahin inda maganar ta samo tushe.." Sameer yace

"Wow, hakan yayi sosae" daga haka babu wanda ya k'ara cewa komae har suka isa wajen Don na bin kwatancen da aka turo masa....




......Dad ya kalli Mami yace

"Sannu da k'ok'ari ranki ya dad'e" Mami tayi murmushi sannan tace

"Yawwah yalla6ae, ya aekin?"

"Aljamdulillah" Mami tace

"Masha Allah" Dad yayi sipping juice d'in da Mami ta kawo masa sannan yace

"Yawwah dama magana ce akan sabon companyn da zan bud'ewa Son, naga Alhamdulillah wancan d'in yana tafiya yadda ya kamata, shiyasa zan bud'e masa wani, ko da bashi ze kula da shi ba toh ya zama na dae mallakin sa ne idan yaso seya samo wad'anda ze d'ora akan wasu abubuwan nima kuma zan nemo masa, se su san yadda zasuyi shi da Sameer d'in su cigaba da kula da dukka companyn" Mami tayi murmushi tace

"Kae Masha Allah, Allah ya taemaka, hakan yayi kyau sosae" Dad yace

"Ameen Ameen, naga alama d'an naki ya rage shashanshi da wasa, bansani ba ko darajar auren da yayi ne.." Mami ta sake yin murmushi tace

"Hakane kam" Dad yace

"Zan samu muyi maganar dashi In Sha Allah" daga haka suka cigaba da tattaunawa har zuwa sanda Mami ta baro part d'in nasa..... Mami ta k'arasa ta zauna kan gadon ta tana danna wayar ta ta kira number Hajja kaltum, daga can 6angaren akace

"Hajiya hadeeza barka da wannan lokaci, yau ma an tuna da baewar Allah Kaltume kenan" Mami ta d'an yi murmurshi kad'an sannan tace


"Kina gida ne?" Hajja kaltum tace

"Ehh ina fatan lafiya?"

"Lafiya, yanzu zanzo.." Hajja kaltum tace

"Toh Hajiya se kin zo, Allah yasa k'aruwa ce" Mami ba tace komae ba kawae tayi murmushi tana katse wayar, ta tashi ta bud'e wardrobe ta d'auko mayafi ta yafa sannan ta d'auko jakar ta da takalmi dukka ta saka kana ta fito daga d'akin. A parlour suka had'u da Fawaz dake shigowa cikin d'akin ya kalli Mami yace

"Mami ina zaki je?" Mami tace

"Unguwa zanje" yace

"Yawwah Mami pls zan biki ku ajjiye ni a zooroad mana" Mami tace

"A'ah ba hanyar zanyi ba" ya turo baki yace

"Kae Mami.." Mami tayi gaba tana fad'in

"Se kuma kayi ae" daga haka ta fice daga d'akin, tana shirin hawa motar wayar ta tayi ringing ta dakata ta d'auki wayar tana karawa a kunnen ta tace

"Son.." Don yace

"Mami barka da wannan lokaci" Mami tace

"Barka kadae Son, ya ake ciki?" Yace

"Dama akan maganar ne, na saka an bincika min kuma an samo k'arin bayani, In Sha Allah zuwa anjima zan kira ki na fad'a miki yanda ake ciki" Mami tace

"Kae Masha Allah, nima dama yanzun zan fita ne zuwa anjima zamuyi waya.."

"Ohk" ya amsa yana shirin katse kiran ya jiyo muryar Mami na fad'in

"Son" seya dakata daga katse wayar ba tare da yace komae ba, Mami tace

"Son..ina fatan dae yanzu gaba d'aya baka zuwa club?" Don ya d'anyi shiru yana mamakin tambayar Mamin ganin kamar ba'a muhallin daya dace tayi ta ba, yace cikin k'osawa

"Mamiiiii.." Ya fad'a yana jan k'arshen sunan nata Tace

"Na'am..just tell me.." Yace bayan ya lumshe idanun sa

"Small small" Mami ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Ina fatan nan gaba ma zaka dena gaba d'aya" Ya yamutsa fuska sannan yace a tak'aece

"Zan kira ki anjiman.." Daga haka ya katse wayar sa, ya kalli Sameer yace

"Muje.." Fitowa sukayi dukkan su suka jera a tare har zuwa cikin wajen, suna shiga Sameer ya k'arasa suka gaesa da wani da tunda suka shigo yake kallan su, Sameer yace

"Pls muna neman Abdussamad Yusuf ne.." Mutumin yace

"Ohk..ohk can shine office d'in sa" ya fad'a yana nuna musu wata k'ofa, Sameer ya kalli Don wanda bama su yake kalla ba fuskar sa kamar ko yaushe ba annuri hannayen sa zube cikin aljihun sa. Sameer yace

"Friend, muje koh?" Bece komae ba ya k'arasa suka wuce office d'in, mutumin ya bisu da kallo yana sak'awa a ran sa tabbas d'aukaka tazo musu tunda gashi har Don Adnan da kansa yazo gidan radion su.... A hankali Sameer ya tura k'ofar office d'in ya shiga da sallama Don na biye da shi, Abdoul dake waya ya d'ago yana kallan su, seya ajjiye wayar ba tare daya k'arasa ba ya cigaba da kallan su har suka k'arasa shigowa, seya mik'e cike da mamakin ganin su yace yanayin sa gaba d'aya ya nuna tsoro yace

"Bismillah..ku zauna mana" Sameer ne ya fara jan kujera ya zauna sannan ya kalli Don yace

"Sit mana.." Don ya d'an yamutsa fuska sannan yace

"No, nan ma ya isa" Abdoul ya d'an k'ak'alo murmushi sannan yace yana kallan su su duka

"Ko zan iya sanin taemakon da zan muku?" Sameer ya kalle shi hannayen sa duka 2n sak'ale a ha6ar sa yace

"Bari na sanar da kae.." Daga haka ya d'auko wayar sa dake cikin aljihun sa yayi danne_danne sannan ya mik'a wayar ya ajjiye kan bench d'in gaban Abdoul sannan ya sake kallan sa yace

"Muna buk'atar k'arin bayani akan wannan.." Seda Abdoul d'in ya d'an yi jimm kafin ya d'auki wayar ya kalla tsawon sec 30 sannan ya d'aga kae ya kalli Don dake binsa da wani banzan kallo kana ya sauke ajiyar zuciya yana jin yadda jikin sa yayi sanyi.......




08124818273




✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION34*



___Cigaba da kallan sa sukayi su duka, kowa yana jiran jin amsar da zata fito daga bakin sa, Abdoul ya sake maraeraece fuska yace

"Yalla6ae zance ne da yake ta yawo a gari, nima cikin hakan na tsince shi na kawo shi gidan nan" Lumshe ido Don yayi ya bud'e su akan sa kana ya d'ora duka hannun sa kan bench d'in gaban Abdoul kamar ze naushe shi yace

"Qarya kake.."

"Noo Friend, mubi komae a sannu" Sameer ya fad'a yana dafa kafad'ar Don, Mik'ewa Don yayi daga rank'wafawar da yayi yana saurara yaji abinda Abdoul d'in zece dan idan beyi wasa ba ze iya kae masa duka, Sameer yace

"Kaaga mun riga da mun san daga gidan nan zancen nan ya fara fita, so ka fad'a mana daga wajen wa maganar tazo nan..koda yake ko kaene ka fara samo labarin?" Abdoul yace

"Nii, no yalla6ae wallahi ba daga waje na bane plss abar maganar haka nan mana" Sameer yace

"Yadda kaso, idan kana so mu bar maganar daga wajen ka toh ka sanar damu daga inda ta fito, shikenan" Abdoul ya sake d'aga ido ya kalli Don yaga bama su yake kalla ba seya maeda duban sa ga Sameer yace

"Sunan ta Simrah.." Ya fad'a yana jin har zuciyar sa be kyauta ba, Sameer yace

"Simrah.." Kallan sa Don yayi yana maemaeta sunan da suke fad'a, yace akan la66an sa

"Wace ce ke?" Sameer ya kalli Abdoul yace

"Her Address pls" Abdoul ya sake kallan Sameer yace

"Harda Address kuma?"

"Ehh muna buk'ata.." Abdoul ya girgiza kae kana yace

"Yalla6ae da an bar address d'in nan pls"... Basu bar wajen ba seda suka sami Address d'in gidan su Simrah sannan suka fice, Abdoul ya sauke ajiyar zuciya yana dafe kan sa, a ransa yana tunanin tsautsayin da ya sanya ya kar6i wannan rahoton...



____Da wayar kare a kunnen ta ta fito parlourn, daga can 6angaren Irfan yace

"Kina free ne?" Simrah tace

"Ehh meya faru?" Yace

"Ohk mu had'u a las vegas mana" shiru tayi kad'an sannan tace

"Ohk" daga haka ta katse wayar ta kalli Momy dake zaune tana kallo tace

"Momy zan d'an fita.." Momy ta kalleta sannan tace

"Ni kuma?, Dama idan zakiyi wani abun kina neman shawara ta ne? A'ah yi ficewar ki Simrah.." Simrah ta maraeraece fuska tace

"Momy pls mana.." Momy ta girgiza kae tace

"Qarya nayi?, Yau da kin bar komae a hannu na kin jira kinga abinda zanyi da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, Dan kuwa wlh Hadeeza da kanta seta saka Adnan ya aure ki kinsan dae wacece ni kuma kinsan wacece Hadeeza.." Tura baki Simrah tayi kafin tace bayan ta gama yafa mayafin ta

"Nidae Momy na tafi"

"Toh, nima dama fita zanyi, kar dae ki dad'e".





.....K'arasawa tayi taja kujera ta zauna sannan ta d'an had'e rae kad'an tace tana kallan Irfan

"Wae lafiya kake bina da wannan kallon?" Irfan yace yana gyara zaman sa

"Lafiya mana kinzo lafiya?"

"Qalau" ta fad'a a gajarce, Irfan ya jinjina kae sannan yace

"Yanzu fisabilillahi meye amfanin abinda kika aekata d'in nan? Kina tunanin wannan abinda kikayi shine zesa ya aureki? Kalli yanda abin ke trending bakya tunanin meze faru idan yaje kunnen sa?"

"And so what?" Simrah ta fad'a a zafafe sannan ta cigaba da fad'in

"Dama abinda yasa ka kirani kenan? Pls ka k'yale ni haka, abinda nayi shine dae_dae, dama nasan ba lallae ka bani had'in kae ba shiyasa nayi abinda nayi niyya kaena tsaye ba tare da neman shawarar kowa ba"...... A 6angaren su Don kuwa suna fitowa daga gidan radion kae tsaye gidan su Simrah suka nufa kowannen su na tunanin wacece Simrahn nan?, a haka suna bin kwatancen da Abdoul ya basu har suka shiga layin su Simrah, Sameer ke driving dan haka ya tsaeda motar ya kalli Don daya kwantar da kansa kan kujera idanunsa a lumshe yace

"Mun iso fa" bud'e idanun sa yayi a hankali ba tare daya kalli gidan ba yace

"Ya za'ayi yanzun?" Sameer na shirin yin magana Momy ta fito daga cikin gidan, Sameer ya bud'e k'ofar ya fita ya k'arasa wajen Momyn fuskar sa d'auke da murmushi yace

"Ina yini?" Momy ta kalle shi tace

"Lafiya lau.." Sameer yace

"Amm pls Simrah fa?" Momy ta sake kallan sa sannan tace

"Eyyah Simrah bata dad'e da fita ba lafiya dae koh?" Sameer yace

"Ehh lafiya lau, Adnan ne yazo wajen ta." Ya fad'a yana kallan cikin motar da d'an munafikin murmushi akan fuskar sa, itama Momyn cikin motar ta kalla sannan tace cike da mamaki

"A'ah wana ke gani kamar Adnan?" Ta fad'a har lokacin tana kallan cikin motar, Seya d'an juyo a dak'ile ya kalle ta yace cikin basarwa

"Kina lafiya?" Mami tace

"Lafiya k'alau, inje dae lafiya ko?" Ta tambaya tana kallan Don wanda tunda ya gaeshe tan ya d'auke kan sa, se dae mamaki yak'i barin sa saboda yasan wannan matar, yayar Mamin sa ce, toh ko abinda yake zargi ne? Idan kuwa hakane Simrah ba zata ji da dad'i ba, Sameer ya galla masa harara sannan ya kalli Mami yace

"Uhmm wato dama zuwa mukayi mu gaesa tana ciki ne?" Momy tace

"A'ah bari dae naje na kira muku ita nasan dama yanzu duk inda take hankalin ta yayo gida.." Sameer yace

"Toh mungode" daga haka Momy ta koma cikin gidan shi kuma Sameer ya k'arasa ya tsaya jikin motar yana kallan Don yace

"Mtsww kawae zaka 6ata mana budget.." Bece dashi komae ba shima be damu ba ya jingina jikin motar hannun sa hard'e a k'irjin sa..... Da sauri Momy ta k'arasa ta d'auki wayar ta ta danna kiran Simrah tace cikin zumud'i

"Ke en nan, maza maza ki dawo ga can Adnan yazo wajen ki" Simrah ta d'an mik'e tsaye sannan tace

"Don Allah da gaske Momy?" Momy tace

"Wallahi kuwa, maza ki dawo karsu gaji da jira su tafi" Simrah tace

"Toh Momy gani nan" tana katse wayar ta kalli Irfan dake kallan ta tace tana murmushi

"Ka gani koh? Yanzu gashi har yazo gidan mu, may be besan wace ce aenahin matar daya aura ba kawae an caka masa ne, ni kuma nazo na rage masa wahala kaga kenan dole ya nemi k'arin bayani a waje na.." Irfan ya tsaya yayi jimm kafin ya kaega cewa komae har Simrah ta sa6i jakar ta tayi wucewar ta, se kawae ya bita da kallo yana ta6e bakin sa......



.....Tun a bakin layin nasu ta umarci me napep ya sauke ta anan, ta sauka ta bashi kud'in sa sannan ta k'arasa cikin layin nasu, tun daga nesa ta hango motar tasu ga Sameer dake jingine a jikin motar, ta chanja tafiya harta k'arasa wajen nasu tana murmushi ta kalli Sameer tace

"Sannun ku da zuwa, ina fatan ban 6ata muku lokaci ba.." Sameer yace

"Noo ae girman ki ne, yanzu dae tunda kin dawo muje mu samu ko wani restaurant d'in ne seku tattauna a can" kanta taji ya k'ara girma ta kalli cikin motar sannan tace

"Ohk, 1mint pls"

"Ohk" Sameer ya fad'a yana komawa cikin motar, Da gudu ta fad'a cikin d'akin ta rungume Momy tana fad'in

"Momy ni dama nasan abinda nayi shine dae_dae wallahi, yanzu baga shi ba, kinga ekudena ganin laefi na koh.." Momy tace

"Hakane kam, me yace miki?" Simrah tace

"Zamu d'an je wani waje ne zuwa anjima zamu dawo.." Momy tace

"Toh se kun dawo" Simrah tace

"Ohk Momy bye" ta fad'a tana d'aga mata hannu sannan ta fice daga d'akin... Sanda ta fito har Sameer ya tada motar, ta k'arasa ta bud'e back seat ta zauna tana sake sakin murmushi, Sameer yaja motar suka bar layin, saboda toshewar basira bata ta6a kawowa kanta cewar laefi ta aekata ba, sema tunanin da take na yadda zata k'ara zage dantse wajen juyo da hankalin sa kanta gaba d'aya....




___Mami taja tsaki tana kallan gate d'in gidan dake a kulle, wayar ta ta janyo ta danna kiran number Hajja kaltum tana d'agawa tace

"Meyasa zaki min haka? Kamar na fad'a miki zanzo gidan nan amma nazo na ganshi a kulle" Hajja kaltum tace

"Eyyah Hajiya kiyi hak'uri, wallahi wani kiran gaggawa ya sakani fita shiyasa.." Mami tace

"Yaushe zaki dawo?"

"Zuwa anjima kad'an zan dawo" Mami tace

"Ohk zan jira ki.." Hajja kaltum tace

"Hajiya har abin yakae haka? Ina fata dae lafiya?" Mami ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Idan kinzo zaki ji koma meke tafe dani" Hajja kaltum tace

"Toh shikenan Hajiya.." Daga haka Mami ta ajje wayar ta jingina da kujerar da take kae.... Suna nan zaune wajen awa 1 sega Hajja kaltum ta dawo ta k'araso wajen motar da Mami ke ciki, ganin ta ya sanya Mami zuge glass d'in, Hajja kaltum tace

"Eyyah Hajiya kiyi hak'uri, ashe kina nan?" Mami tace

"Ehh" kawae, Hajja kaltum tace

"Ku k'araso ciki, bari na bud'e.." Tayi gaba zuwa wajen gate d'in, Driver yaja motar ya shige gidan sannan yazo ya bud'ewa Mami motar ta fito, tare suka jera zuwa cikin gidan har parlourn Hajja kaltum, Mami ta k'arasa ta zauna tana ajje jakar ta a gefe, Hajja kaltum ta cire mayafin jikin ta sannan ta nemi waje ta zauna tana kallan Mami tace

"Sannun ki da zuwa" Mami tace

"Yawwah ina kika je hakane?" Hajja kaltum tace

"Wallahi ke dae bari kawae, yau kuma se gaki a gida na" Mami ta d'an ta6e baki sannan tace

"Kamawa tayi, zuwa nayi muyi magana" Hajja kaltum ta gyara zama tana kallan Mami tace

"Ina jin ki Hajiya meya faru?" Mami ta dafe kan ta sannan tace

"Wato Kaltume ban san yadda zan 6ullowa al'amarin nan ba, Alhaji ya sake fara shirin bud'ewa Adnan sabon company, saboda duk wata shiririta yanzun Adnan ya rage ta gashi wae har yanzun be fara cin abincin yarinyar nan ba, ke komae ma ni ya ca6e min, bansan me zanyi ba.." Hajja kaltum tace

"Iyii lallae ma wannan mutumin, toh ya dena shaye shayen ne?" Mami ta lumshe ido sannan ta bud'e tace

"Waya fad'a miki dama yana shaye shaye Hajiya? Taba da shisha kawae yake sha suma ba wani sosae ba" Hajja kaltum tace cike da mamaki

"Neman mata fa?" Mami tace bayan ta dafe kan ta

"A'ah wannan ma baya yi fa.."

"Toh amma ae yana zuwa club koh?" Mami tace

"Ehh shima ba sosae ba kuma ba wannan ke kaeshi ba"

"Toh tare kuke zuwa ne?" Mami ta d'aga kae tayi wa Hajja kaltum kallan banza, dariya Hajja kaltum tayi sannan tace

"Ahh toh naga yanda kike bada sheda a kansa ne kamar tare kuke zuwa, toh Hajiya sanda ze nemi matan kina zaune a gida sani zakiyi?" Mami tace

"Kee wallahi baya yi, da yanayi zan sani ne, abinda ma baki sani ba shi Adnan sam mata fa basa gaban sa" Hajja kaltum ta ta6e baki tace

"Toh ae koma menene kece kika ja, yanzu dawa take shirin 6arewa?" Mami ta sauke doguwar ajiyar zuciya sannan tace tana kallan Hajja kaltum

"Meye mafita?"

"Mafita d'aya kawae itace ki dank'a komae a hannu na zuwa sati me zuwa kiga yadda komae ze chanja, rayuwar Adnan seta sake ta6ar6arewa wallahi" Mami tace

"A'ah barshi haka nan, yanzu kawae muyi duba akan yadda zeyi yaci abincin yarinyar can, kingane me nake nufi ae..?" Hajja kaltum tace bayan tayi wani murmushi

"Hakane hajiya, amma da an had'a biyu saboda tsaro koh?" Mami tace

"Ba zasu had'u bane ae, kiyi tunani mana" Hajja kaltum ta d'anyi shiru sannan tace

"Hakane kuma.." Kafin ta d'an yi shiru sannan ta d'ora da fad'in

"Amma yanzu idan hakan ta faru, kina ganin Alhaji ze d'ora Fawaz akan komae ne?" Mami tayi d'an murmushi sannan tace

"Noo, Fawaz ae yaro ne bari ya taso tukun na, ni da kaena zan iya kula da komae.." Hajja kaltum tace

"Qwarae hakane, yanzu kin san menene mafita game da yarinyar nan?" Mami tace

"A'ah se kin fad'a.." Gyara zama Hajja kaltum tayi itama Mamin ta gyara zama tana sauraron ta....




___Tana cikin kitchen taji shigowar mota cikin gidan, ta riga da tasan shine dan haka ta cigaba da aekin ta kawae, se dae ga mamakin ta se ta jiyo sallama daga cikin parlourn, ajiye carrot d'in hannun ta da take yankawa tayi ta fito zuwa parlourn, annurin fuskar ta ya dad'u ganin me sallamar tace

"Sannu da zuwa Mami.." Mami ma ta mayar mata da murmushin tana neman waje ta zauna kana tace

"Sannunki dae Azrah" Azrah bata zauna ba ta koma kitchen d'in ta d'auko plate da cup tazo ta bud'e fridge ta d'auko ruwa da lemo sannan ta koma ta ajje a gaban Mamin kana ta zauna kanta a k'asa tace

"Barka da wannan lokacin Mami"

"Barka kadae, ya karatu?" Azrah tace

"Alhamdulillah" Mami tace

"Toh madallah, Son na nan ne?" Girgiza kae Azrah tayi sannan a hankali tace

"A'ah.." Mami tace

"Ohk toh taso ki zauna akan kujera" nan ma girgiza kae tayi, Mami tace

"Haba babu komae Azrah ki tashi ki zauna mana" Seta d'aga kae ta kalli Mamin sannan tace a hankali

"A'ah Mami nan ma ya isa" Mami tace

"Bansan musu taso ki zauna magana zamuyi" seta mik'e a hankali ta zauna kan kujerar har lokacin kan ta nà a k'asa, Mami ta d'anyi shiru tana tunanin ta inda zata fara, se kuma can tace

"Azrah.." Azrah ta d'aga kae ta kalli Mami sannan ta maeda shi k'asa ta cigaba da wasa da yatsun hannun ta, Mami ta cigaba da fad'in

"Kinsan wacece ni a wajen Son koh?" Jinjina kae Azrah tayi kawae, Mami tace

"Ohk, kinsan wacece ni a wajen ki koh?" Nan ma ta jinjina kae

"Dat's gud, kin san yadda nayi k'ok'ari wajen ganin kin dawo mace koh?, har na san yadda nayi kika fara zuwa makaranta, na tsaya duk dan inga kin chanja daga Azrahr k'auye zuwa ta birni, daga tsohuwar Azrah zuwa wata sabuwar Azrah d'in, ni kad'ae nasan yadda nayi aeki tuk'uru da hannaye na da jiki na da kuma

Please Login or Register in order to submit comment