Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kae tana wasa da en yatsunta, Se Meemarh ta mik'e suka gaesa da Yakumbo, Meemee ma ta gaesa da ita ta nemi waje ta zauna ta cigaba da danna wayarta, Suna nan zaune ita dae Meemarh ba tace komae ba se dae gaba d'aya mamaki ya gama kashe ta, amma ba wannan ne lokacin daya dace suyi maganar ba, saboda haka seta yi shiru kawae... A ranar seda taje ta gaeda Ammi a gidanta saboda rashin zuwan da batayi ba sakamakon rashin lafiyar da take, sanda zata tafi ne ta kalli Ammi tace

"Ammi zan tafi, Allah ya k'ara lafiya" Ammi tace

"Ameen Ameen Azrah, zamu yi waya" daga haka ta fice daga d'akin, tana shitin fita daga gidan, Zarah ta dawo daga aeken da Ummu ta mata, Zarah ta rungume Azrah tana fad'in

"Oyoyo.." Azrah ta dakata da murmushi kan fuskarta tace

"Nayi sa'a na sameki" Zarah tace bayan ta saketa

"Amma gaskiya naji dad'in ganinki, yaushe rabon dana ganki?" Ta fad'a da fara'a akan fuskarta, Azrah tace kamar zatayi kuka

"Kuma tafiya zanyi" Zarah tace

"Eyyah.. In Sha Allah zanzo gidan se muyi hira" Azrah ta jinjina kae sannan Zarah ta rakata har gida kafin sukayi sallama.. Se wajen k'arfe 7pm na ranar sannan ya shigo gidan, kae tsaye ya wuce part d'in Dad, bayan sun gaesa Dad yace masa

"Yanzu zaku wuce?" Seya d'aga kae ya kalli Dad sannan yace yana d'auke kae

"A'ah akwae inda zan biya tukunna" Dad yace

"Ohk ka fara zuwa ka sauketa a gida sannan ka wuce inda zakaje d'in" da "toh" kawae ya amsa ba dan yana da niyyar aekata hakan ba, ya fice daga d'akin ya wuce part d'in Mami, ya k'arasa ya zauna kan kujera suka gaesa da Mamin kafin Mami tace

"Ka shiga ka gaeda Yamumbo?" Yace cikin basarwa yana cigaba da danna wayarsa

"Ehh.." Mami tace

"Toh madallah, ya wajen aekin?" Ya lumshe idanunsa yana fad'in

"Alhamdulillah" dae_dae lokacin da Azrah ta shigo cikin parlourn, tunda ta hangeshi cikin parlourn taji k'irjinta na bugawa haka dae ta k'arasa ba tare data kalleshi ba tacewa Mami

"Dad yace wae ku fito.." Mami tace

"Ohk toh gamu nan" daga haka ta juya ta fita daga cikin d'akin cike da sassarfa, Mami ta kalli Don tace

"Tashi muje.." Babu musu ya mik'e Mami na gaba yayinda yake biye da ita har zuwa compound d'in, Dad ya kalleshi bayan ya fito yace

"Ka wuce ku tafi dare nayi.." Don ya d'aga lumsassun idanunsa yana kallan Dad dan yana so ya fahimci abinda yake nufi, kafin ya gama tunanin ya sake jiyo muryar Dad na fad'in

"Toh Azrah ku gaeda gida koh?" Azrah tayi k'asa da kanta tace

"Toh Dad" Seta k'arasa a hankali ta shiga k'ofar da wani driver ya bud'e mata zuciyarta na bugawa, Don ya runtse idanunsa yana jin yadda zuciyarsa ke zafi

"Ku gaeda gida.." Ya sake jiyo muryar Dad, seya bud'e idanunsa a hankali da suka fara rinewa saboda tsabar bak'in ciki, Sannan ya taka a hankali kamar wanda baya son taka 'kasa zuwa wajen motar yana sake kallan mutanen dake compound d'in, kawae seya shige cikin motar yana jin Dad da Mami na masa seda safe, amma be bi ta kansu ba yaja motar da wani irin gudu ya fice daga gidan... Tunda suka fara tafiya taji bugun zuciyarta ya k'aru, seta rik'e saetin zuciyarta tana lumshe idanunta, Seda suka d'anyi nisa da unguwar tasu sannan ya gangara gefen titin ya kashe motar fuskarsa a cunkushe haka zalika har lokacin idanunsa be koma aenahin coloursu ba yace cikin kaushi

"Fita!!" Ta riga da tasan babu wani cikin motar daga shi se ita, dan haka ta tabbatar maganar ma da ita yake, seta bud'e idanunta da suka mata nauyi saboda tun d'azu data lumshe su bata bud'e su ba se yanzun, ba tare data kalleshi ba tayi shiru tana sauraren bugun zuciyarta tare da sake jiran jin furucinsa dan sake tabbatarwa da zuciyarta abinda taji, se kuwa ta sake jiyo muryar tasa sedae yanzun cikin tsawa yace

"Get out!!" Seta saka hannunta ta bud'e k'ofar jikinta na wani irin rawa kamar ana kad'ata, tana fita ta rufe k'ofar tana kallan yadda garin yayi duhu sosae gashi babu mutane saboda yadda dare ya farayi, se yadda motoci keta wucewa akan titin kamar zasu tashi sama, tana rufewa kuwa ko second 1 be k'ara ba yaja motarsa da wani mahaukacin gudu ya bar wajen...........


Jama'a wae ya labarin su Inno kuwa????



08124818273

✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION27*




______A hankali ta sake runtse idanunta tana jin wasu hawaye masu d'umi na zubo mata, seta saka hannayenta duka biyun ta goge hawayen tana tuna a inda take, se ta fara takawa a hankali ta k'arasa bakin titin tana rungume jikinta yadda taji sanyi na wani irin ratsa ta, a haka ta tari mota ta fad'a masa inda ze kaeta sannan ta shiga har lokacin hawaye be bar sintiri akan kyakykyawar fuskar ta ba.. Tana isa gidan kae tsaye ta wuce d'akin ta ta fad'a kan gado ta saki kukan data keta rik'ewa tuntuni, kuka ne dake fitowa tun daga k'asan ranta me zafi, seda tayi har ya ginsheta sannan ta dena ta cigaba da sauke ajiyar zuciyar akae_akae.....


......... Irfan ya fito da wayarsa daga aljihunsa ya danna number Don, be d'aga a kira na farko ba se a kira na biyu, yana d'agawa Irfan yace

"Don, ka ganni a k'ofar gidan ku pls, yanzun wani yake fad'amin nonsense wae kayi aure..." Don ya hautsina sumar kansa yace

"Me zaka min?" Irfan yace

"Idan da gaske ne kawae kamin kwatancen gidan nazo idan yaso sena gaesa da Madam ma" Don ya d'anyi shiru kad'an kafin can yace a hankali

"Waje na zaka zo ko kuwa?" Irfan yace

"Ehh..ehh wajen ka zanzo mana.." Don yace

"Ohk we will talk later.." Irfan yace

"Ohk..Don bari.." Yana shirin d'orawa da wata maganar yaji Don d'in ya katse wayar, seya maeda wayar cikin aljihunsa yana kallan wata dake k'arasowa cikin layin, dab da zata giftashi ta d'ago ta kalleshi tace cikin mamaki

"Irfan!" Irfan ya matsa kusa da ita shima da mamakin kan fuskarsa yace

"Simrah.." Ta jinjina kae tana fad'in

"Ashe kana duniyar?" Irfan ya shafa gefen kumatunsa yana fad'in

"Haba ae ku za'awa wannan tambayar, mu kam muna nan"

"Amma nayi mamakin ganinka anan, ina zakaje" Irfan yace

"Wallahi kuwa nazo wajen abokina ne Adnan, a cikin layin nan yake" Simrah tace

"Adnan Kabeer Tajuddeen?" Irfan ya kalleta yace

"Yeah, shi..kin sanshi ne?" Simrah tayi murmushi tace

"Sani kae, d'an mijin k'anwar mama na ne.." Irfan yace

"Wowww, gaskiyane..yanzu ma can zakije?" Simrah ta girgiza kae sannan tace

"Noo, ba nan zani ba, zanje wajen wata k'awata ne, itama anan layin take.." Irfan yace

"Eyyah..amma ya maganar auren sa da naji ance yayi kwanan nan?" Simrah ta d'ago ta kalli Irfan tace

"But u said Adnan is ur friend, ya akayi baka sani ba?" Irfan ya d'aga kafad'a yana ta6e baki yace

"Yeah, bansan meyasa ya 6oye min ba, but koma dae menene there is something fishy.." Simrah tace

"Exactly, bani contact naka zamuyi waya yanzun sauri nakeyi" Nan sukayi exchanging number, Simrah ta wuce gidan da zataje yayinda Irfan ya shige motarsa shima ya wuce inda zeje......



........Washe_gari da asuba ta farka daga bacci, a hankali ta bud'e idanunta takae hannunta cikin ta da taji ya murd'a mata kad'an, a haka dae ta sakko daga kan gadon ta fad'a toilet tayi wanka sannan ta fito ta shirya tayi break kad'an dan har lokacin cikin nata tana ji yana murd'a mata, a haka dae ta tafi makarantar... Sanda taje Meemarh basu zo ba sun makara dan seda malami ma ya shigo sannan sukazo, har ya gama karatunsa ya fice daga ajin wani malamin ya shigo ba suyi magana da Meemarh ba, seda aka fita break sannan Azrah ta kalli Meemarh tace

"Yau kun makara?" Meemarh ta d'an yi murmushi tace

"Wallahi kuwa.." Daga haka bata sake cewa komae ba, Azrah tayi rau rau da idanunta da alama haushin ta Meemarh keji dan haka se tace a hankali

"Meemarh!" Meemarh ta kalle ta kana ta harare ta ta d'auke kae, Azrah tace bayan tayi murmushi

"Maganar jiya ce koh?" Meemarh ta jinjina kae, Azrah tace

"Toh ki juyo kiji mana" Meemarh ta juyo har lokacin wani wajen take kalla tace

"Nikam bansan kuma me zaki fad'amin ba, bayan tuntuni baki fad'amin ba seda na gano da kaena" Azrah tace

"Ba haka bane Meemarh, wannan auren nawa ba kamar kowanne aure bane.." Se a lokacin Meemarh ta kalli Azrah kafin ta juya kanta tace

"Bangane ba?" Haka kawae Azrah taji ta yadda da Meemarh har cikin ranta dan haka tace

"Ehh Meemarh, saboda mijin ma besan da zamana ba, be san sha na ko cina ba, haka sutura, baya kulani kona gaesheshi baya amsawa, yana rayuwarsa ne kàmar shi kad'ae yake zaune cikin gidan" Meemarh tace fuskarta d'auke da mad'aukakin mamaki

"Yaya akayi akae auren toh kenan? Ko kece ke sonsa?" Azrah ta girgiza kae tace

"Bansani ba Meemarh, bansani ba, kawae ni dae ance min an d'aura min aure, daga baya kuma akace shine miji na.." Meemarh ta cigaba da kallan Azrah har lokacin mamaki ya'ki barin fuskarta tace

"Ikon Allah..nima nayi mamakin yadda aka miki aure yanzun da k'ananun shekarun kin nan haka Azrah.." Azrah tayi yak'e kawae, Meemarh tace

"Karki damu Azrah, kinga yanzu za'a dawo break, amma In Sha Allah zanzo gidan ki semu k'arasa maganar uhmmm?" Azrah ta jinjina kae tana lumshe idanunta a hankali gami da sauke numfashi tana sake jin yadda cikin ta ke murd'awa, a daddafe suka gama karatun yau ta koma gida tana share er k'walla dan a lokacin cikin nata sosae yake ciwo, haka dae ta k'arasa cikin d'akin ta tana dafe da cikin nata, kae tsaye ta fad'a kan gado ta cure waje 1 tana jin kamar numfashin ta ze d'auke, se kawae ta fashe da kuka tana sake rik'e cikin nata wanda take jin sa kamar ze cire dan azaba.......... A hankali yake takawa zuwa cikin parlourn wayarsa kare akan kunnensa yana waya, idanunsa ya sauka akan dinning bega komae ba, sannan kafin ya gifta ta inda ta saba zama kullum be ji gaesuwar data saba yi ba kullum, then something cross his mind, kada dae ace itace ke masa girki yana zaunawa ya share a cikin sa, wani tunanin ne ya sake fad'o masa sanda ya k'atse wayar da yake wato yadda ya barta a titi jiya, bayan nan be sake ganin ta ba, kada dae bata dawo gida tun jiyan ba? Ya tambayi kansa, Dad ne ya fara fad'o masa a rae dan yasan tabbas idan yaji abinnan daya faru kuma hakan ya zamo silar 6acewarta may be ya tsine masa, a hankali ya taka zuwa saman har lokacin tafiyarsa bata chanja ba haka zalika yanayin fuskarsa be chanjaba, Dab da ze gifta ta wani d'aki dake a saman wanda be ta6a bud'e shi ba tun zuwansa cikin gidan ya jiyo sauke numfashi da takeyi gami da sheshshek'a, seya dakata yana mamakin wace halitta ce kenan a cikin d'akin? Shi dae yasan babu wanda ke rayuwa a saman bayan shi toh waye kenan a cikin d'akin?, A hankali ya sauya akalar tafiyar tasa zuwa wajen d'akin, ya sanya hannunsa a hankali ya murd'a hannun k'ofar, ga mamakin sa se yaji ta a bud'e, har lokacin fuskarsa a cunkushe take ya saka kansa cikin d'akin, yanayin yadda yaga d'akin ya nuna masa da alama an dad'e ana rayuwa a cikin d'akin, ransa ya sake 6aci yana sake ayyana wani abu a cikin ransa, idanunsa suka sauka a can k'arshen gadon inda yake jiyo ajiyar zuciya, tana kwance cikin blanket ta nannad'e kanta gaba d'aya bacci ya fara d'aukarta, seya k'arasa cikin d'akin a hankali, ya tsaya yana kallan abinda ke kan gadon, kana ya fara kae hannunsa zuwa kan blanket d'in ya sanya hannu ya janye shi da sauri, kwance take tana bacci sedae da alama baccin ma ba dad'i yake mata ba dan yadda yanayin fuskarta ya nuna ta 6ata rae ne, gashi kuma se had'a gumi take yi kamar me jin zafi bayan ga uban blanket data jibga akanta, karo na farko kenan daya ta6a tsayawa ya kalli kyakykyawar fuskarta da tayi fayau kamar mara lafiya, and yaga she looks familiar, kyakykyawan gashin kanta dake a tsefe ya barbaje akan gadon, seya tsaya yana kallan fuskarta ta ko ze tuna da wanda yaga tayi kama, se kuma yaja tsaki a ransa yana ayyanawa what concern him? Se kawae ya juya da niyyar fita daga d'akin, dae_dae lokacin da tayi juyi seta sake rik'e cikin ta tana sakin wata er k'ara, kamar wanda aka tsikara ya dakata daga tafiyar da yakeyi ya juyo a hankali ya koma da baya zuwa inda take a ransa yana mamakin tsaurin idonta da har ta iya hawowa saman take zaune a ciki, koma dae menene ta fara tashi ta bar saman benen nan, ta koma ta dinga kwana a parlour dan shine ya dace da ita, seya k'arasa saetin inda take ya sanya hannunsa kan pillow ya daka kad'an, seta fara bud'e idanunta a hankali harta gama bud'e su tarwae akan fuskarsa, cikin er razana ta saki k'ara tana tashi zaune daga kwanciyar da take, tsaki yaja yana dafe kansa kafin ya kalleta cikin had'e gira yace

"Tashi" babu musu ta tashi zaune tana toshe bakin ta idanunta k'walla fall, yace

"Tashi nace.." Seta janyo hijab d'inta dake gefe ta zura sannan da sauri ta sauka daga kan gadon k'irjinta na bugawa, seya fara k'ok'arin wucewa dae_dae lokacin da idanunsa suka sauka kan gadon da kuma hijab d'in data saka, seya runtse idanunsa gami da dafe kansa a hankali yace yana yin gaba

"Go back" daga haka ya fice daga d'akin har lokacin hannunsa na dafe da kansa, binsa tayi da kallo harya fice sannan ta dawo ta koma tana shirin zama idanunta ya sauka kan gadon, seta zaro ido waje tana jin yadda zuciyarta ke farfari, kawae seta fashe da kuka ta tsuguna a wajen kamar wadda aka daka, tana jin kunyar duniya tazo ta taru ta rufeta......... A hankali ya tura k'ofar d'akin ya shige ciki ya k'arasa ya zauna kan gado, so yake ya gasgata ko da gaske ita d'in ke masa girki duk wad'annan kwanakin da aka d'auka? Kenan girkinta yake ci be sani ba, toh ya akayi yake jin d'and'anon girkin Ammi? Kae hakan ma baze kasance ba, wannan er k'auyen babu abinda ta iya saboda haka may be yau ne aka samu akasi ba'a kawo ba, seya lumshe idanunsa ya tashi ya fad'a toilet, seda ya fito daga wankan sannan ya d'auki wayarsa yayi dialing number Mami ya kira, ringing 1_2 ta d'auka kafin yace komae tace

"Son ya kake?" Yace

"Alhamdulillah, barka da rana.." Tace

"Barka dae.." Seya d'anyi shiru sannan yace

"Ammi fah?" Mami tace

"Eyyah Ammi bata ji dad'i ba kwana 2n nan bata shigowa, d'azun nan ma na dawo daga duba ta" Don ya sauke ajiyar zuciya kana yace

"Ohk.." Mami tace

"Akwae wani abu ne?" Don yayi kamar beji abinda tace ba ya katse wayar, yana sake neman waje ya zauna, shikenan abinda yake zargi ya tabbata ya dad'e yana cin girkin er k'auyen can, seya yamutsa sumar kansa yana jin yadda zuciyarsa ke zafi, ace kamar shi ya k'are acin abincin waccan abar, se kuma wata zuciyar tace masa "toh meye a ciki? Tunda dae kana ci ka k'oshi, kuma baka ji banbanci tsakanin girkin nata dana Ammi ba?" Se yayi shiru yana saurarar zuciyar tasa kafin ya sake jan wani siririn tsaki ya mik'e yana sake hautsina sumar kansa....... Washe_gari da safe bayan ya shirya ya gama komae ya fito daga cikin d'akin dan wucewa inda zeje, cikinsa na kiran chiroma dan tun jiya rabonshi da abinci couz ko restaurant be je ba, saboda dama ya riga daya gama sabawa da girkin Ammi, indae yaje restaurant toh akasi aka samu be samu girkin Ammi ba, dan haka yana saukowa daga stairs d'in ya wuce dinning area, duk da babu komae akan dinning d'in haka ya k'arasa ya zauna yana danna wayarsa.... Tashin ta kenan daga bacci taji cikinta ya murd'a alamar yunwar da take ji tun jiya ce ta taso mata, dan haka ta mik'e ta shige toilet tayi wanka sannan ta shirya cikin doguwar riga da hijab kana ta sauko k'asan, sam bata lura da mutum a wajen ba kae tsaye ta wuce kitchen, ta had'a tea, kana ta soya chips da k'wae ta fito daga kitchen d'in, tana shirin zama ta hangi mutum akan dinning kamar koda yaushe fuskarsa babu annuri ya zubawa wayarsa ido da alama wani abun yake me amfani, kawae seta k'arasa da plate da cup d'in a hannun ta ta ajje kan dinning d'in tama manta shi besan abincin ta yake ci ba, kafin tace cikin er rawar murya

"Ina kwana?" Seya d'aga ido a hankali ya kalli abinda ta ajje d'in sannan ya lumshe idanunsa, yace yana cigaba da kallan wayarsa wato ba tare da ya kalleta ba

"Nace miki ina buk'atar gaesuwar ki ne malama?, na fad'a miki ki kama kanki a daddafe har zuwa sanda iyayenki zasu gaji suzo su d'auke ki, and tunda an yaudareni na fara cin girkin nan, i will manage kafin Ammi ta warke, but u have to know a bisa rashin mafita yasa zanci abinda hannunki ya girka, dan haka ki tabbatar kin ajje komae anan wajen kafin nazo, ba sena zauna kizo ki samin ciwon kae ba, ki kama kanki.." Ya k'arasa fad'a yana sauke numfashi saboda tsayin lokacin daya d'auka yana magana, tunda ya fara magana take kallansa tana jin yadda jikinta ke rawa, seta runtse idanu kafin a hankali ta d'aga k'afafunta da suka mata nauyi tayi gaba tana jin yadda zuciyar ta ke tafasa, meyasa kullum maganar sa a gareta bata wuce ta cin mutunci? Wae ta kama kanta, ita kuwa me take yi haka ne na ballagazanci daze dinga fad'a mata wannan maganar? Seta sake runtse idanunta tana cigaba da tafiya zuwa cikin d'akin ta...... 'Bangarensa kuwa seda ya gama jan ajinsa duk da bata wajen, yaga dae duk wani muzurae nasa ba amfani zasu masa ba, sannan ya maeda wayar tasa cikin aljihu ya janyo plate d'in ya hau cin chips d'in yana sake mamakin yadda komae ya kasance iri 1, aekuwa ya cinye tass, duk da ba wani k'oshi yayi ba amma dae ya toshe wata kafar ya mik'e ya fice daga d'akin....... Tana kwance kan gadon, ta d'ora fuskarta akan pillow ta jiyo ringing d'in wayarta, seta tashi ta k'arasa ta d'auki wayar tana kallan number dake yawo akae, se kawae ta d'aga ta kara a kunnenta

"Surprise!!" Ta jiyo muryar Meemarh na fad'in haka, se tayi sauri ta tashi zaune tana sake mak'ale wayar a kunnen ta kafin tace

"Meemarh.." Meemarh tace

"Na'am ki fito ina k'ofar gidan" da mamaki Azrah tace

"Serious..?" Meemarh tace

"Ke dae ki fito mana" daga haka Azrah ta ajje wayar ta mik'e kae tsaye ta fice zuwa waje, tana zuwa ta bud'e gate d'in aekuwa sega Meemarh ta shigo da sauri suka rungume juna, Meemarh na fad'in

"Yau dae gani a gidan ki" Azrah dae kawae tayi yak'e tana kama hannun Meemarh suka shige cikin parlourn, Seda suka zauna sannan Azrah ta kalli Meemarh tace

"Ya akayi kika zo wae?" Meemarh tace

"Yanzu dae ba wannan ba, ba gani nazo ba?" Azrah tace

"Ehh, kinzo lafiya?, bari na kawo miki ruwa" ta fad'a tana mik'ewa, Meemarh ta kamo hannunta tace

"Kinga dawo ki zauna, ni kam ba abinda nake buk'ata, magana zamuyi" se Azrah ta koma ta zauna, Meemarh tace

"Uhmm k'awata wae da gaske yah Adnan ne mijin ki?" Azrah tace

"Ki jiki dan Allah ki bar wannan wasan mana, mijin da aka aura min dae.." Meemarh tace

"Hmm wlh kinsan komu muna zuwa gidansu, amma magana bata ta6a had'amu dashi ba, sedae kawae mu gaeshe shi ya amsa ba tare daya kallemu ba" Azrah tace

"Hmmm" kawae, Meemarh tace

"Yanzu dae kina jin abinda ze faru?" Azrah ta girgiza kae ba tare da tace komae ba, Meemarh tace

"Kema hakan yake miki koh?" Azrah ta sake jinjina kae k'walla na kawowa idanunta, Meemarh tace a hankali tana kallanta

"Solution.." Ta fad'a tana gyara zama, jin abinda Meemarhn ta fad'a yasa itama Azrahn ta gyara zama tana kallanta.............


Bari mu waewayi su Inno kuma..............


.........Bayan kwana 3 ta tafiya da Azrah zuwa gidansu Don, Inno na zaune a tsakar gida tana tankad'e gari, taji sallama daga 'kofar gidan, seta amsa tana kallan me shigowar, nan take annurin fuskarta ya chanja, Umma ta k'araso cikin gidan ta nemi waje ta zauna tana fad'in

"Barka da wannan lokaci Habee" Inno tayi wani yak'e tace

"Barka..kece a tafe?" Umma tace

"Wallahi kuwa nice, ya wajen amarya kuwa?" Inno ta sake yin wani murmushin tana kae hannunta kanta sannan tace

"Amarya tana nan k'alau"

"Toh madallah, ina kuwa aka kaeta?" Inno tayi d'an jim kana tace

"Nan cikin kano ne.." Umma tace

"Kae Masha Allah..Allah ya sanya alkhaeri" Inno tace

"Uhmmm" kawae, Umma ta gyara zama sannan tace

"Kin ganni dama da shiri na nazo, se a samu wani ya rakani zuwa can gidan nata, in duba d'iyar tawa.." Da wani irin sauri Inno ta d'ago tana kallan Umma cikin rashin sanin abinyi har seda taji cikinta ya wani murd'a mata a lokaci guda..........



08124818273



✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION28*



_____Inno ta sake yin wani yak'e sannan tace

"Eyyah, aekam kin daki gurbi dan yanzu haka ma basa k'asar suna k'asa me tsarki" ta fad'a tana d'auke kae dan kaucewa kallan da Umman ke mata, Umma tace

"Kae Masha Allah, Allah yasa ayi ibada kar6a66iya, babu damuwa don Allah idan sun dawo a sanar dani" ta fad'a tana d'akko wayarta daga cikin jaka sukayi exchanging contact sannan ta mik'e tana fad'in

"Toh ni zan koma" farin ciki kamar ze kashe Inno tace

"Toh ki gaeda gida, muna godiya sosae da kulawa" Umma tayi murmushi tace

"Babu damuwa ae" daga haka ta fice daga gidan, Inno ta sauke wata k'atuwar ajiyar zuciya sannan ta koma ta zauna ta d'akko wayarta ta danno number Mami, tana d'agawa tace

"Hajiya ina wuni?" Mami tace

"An yini lafiya?" Inno ta sake sauke ajiyar zuciya kana tace

"Alhamdulillah, hajiya inaso nazo gidan er tawa ne idan babu matsala.." Mami ta d'anyi jimm sannan tace

"Ko dae kud'in da ake baki ne sukayi kad'an" Inno ta d'an sosa kae kana tace tana d'an murmushi

"Ehh toh hajiya da wannan ma kinsan yanzu abubuwa ne sunyi tsada.." Ta k'arasa fad'a tana sake yin murmushi, Mami ta girgiza kae sannan tace

"Toh babu damuwa zansa a k'ara miki, sannan zan turo a d'aukeki se kiga er taki" Inno tace

"Nagode sosae hajiya Allah ya k'ara arzik'i"

"Ameen" Mami ta fad'a daga haka ta katse wayar, dae_dae nan Baban ilyasu ya shigo gidan, ya kalli Inno da keta sakin murmushi yace

"Hala wani abun muka samu kuma?" Inno ta sake yin murmushi kana tace

"Kae ka bari kawae, mutanen nan ne, matar ke fad'amin zasu k'ara mana kud'in da suke bamu" Baban ilyasu yace

"Ko dae kece kika rok'esu ne?" Inno ta masa wani kallo sannan tace

"Toh idan ma ni d'in ce akwae wani abu a ciki? 'Ya sukutum guda fa muka d'auka muka basu..in kuma kud'in ne baka so fad'amin inji, se in sake sabon bajet (budget)" Baban ilyasu yace

"Ke fa kiji ki nine na fad'a miki hakan?" Inno tace

"Ahh toh"... Tun daga lokacin ma Mami ta manta da zancen kwata kwata, ita kuma Inno tunda aka k'ara mata kud'i bata sake tunawa da wata Azrah ba ta cigaba da harkokin ta..( oh me hali dae baya fasa halinsa...)



*** *** ***

Meemarh tace

"Nunawa yake be san da zamanki ba a cikin gidan nan, kema ki nuna tamkar ke kad'ae ke rayuwa a cikin gidan nan, kiyi harkar ki as if baki san akwae wata halittar a cikin gida ba" Azrah da tunda ta fara magana take kallan ta tace bayan ta d'an tura baki

"Toh ni dama ae babu ruwana dashi, gaesuwa kad'ae ke had'a mu" Meemarh ta harare ta sannan tace

"Ina nufin har gaesuwar ma ki dena" Azrah ta zaro ido tana sake kallan Meemarh ba tace komae ba Meemarh tace

"Yeah i mean what i said" Azrah ta girgiza kae kad'an kamin tace

"Eyyah ni tsoro nake ji" Meemarh tace

"Toh zauna ki cigaba da jin tsoron ya cigaba da wulak'antaki.." Azrah ta d'an yi jimm sannan tace

"Shikenan zan gwada.." Meemarh tace

"Yawwah wata shawarar ma..." Ta fad'a tana d'an

Please Login or Register in order to submit comment