Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata magani sannan ya dawo cikin gidan, nan ma da k'yar da jan ido sannan tasha maganin ta koma ta kwanta tana sake share k'walla.. Da dare kuwa da taga alamar bashi da niyyar fita daga d'akin seta fara k'ok'arin mik'ewa daga kan gadon, ya kalle ta da mamaki ganin tana k'ok'arin d'aukar pillow amma ta kasa tashi yace

"Meya faru?" dama k'iris take jira aekuwa ta fara share k'walla tace cikin kukan

"Zan bar maka d'akin ne.." yace

"Kin ganni fa a inda zan kwana" ya fad'a yana gyara zaman pillown sa dake akan carpet

"Nidae Allah ka barmin d'aki, bana son ganin ka" ya runtse idanun sa yana jin zafin abinda ta fad'a d'in, amma da yaga alamar da gasken take kuma bata iya baccin indae yana d'akin, seya mik'e ya fita daga d'akin tunani fall ransa, ta bishi da kallo harya fice bayan yaja mata k'ofar, bata da k'arfin mik'ewa dan har yanzun zazza6in be gama sakin ta ba, dan haka bata iya mik'ewa ta kulle d'akin ba taja bargo tayi kwanciyar ta, ranar kuwa ta samu tayi baccin ta cikin kwanciyar hankali.. Da safe kuwa da kanta ta tashi dan sosae taji jikin ta ya d'an sakar mata ba laefi, tayi wanka ta shirya a cikin toilet d'in sannan ta fito tana sake jin jikin nata ya sake mata dad'i, sallah tayi, kuma data idar ta cigaba da zama kan sallayar bata mik'e ba, tana nan zaune ya turo k'ofar d'akin ya shigo, bata kalle shi ba ta cigaba da addu'ar da take yi, seda ta idar sannan ta mik'e a hankali ta ninke daddumar ta koma kan gadon ta zauna tana shirin jan blanket ta sake kwanciya ta jiyo muryar sa cikin tsokana yace

"Ina kwana?" d'auke kae tayi fuskar ta a had'e dan har yanzu haushin sa take ji, shi da alama baya jin kunya ita ya barta da jin kunyar gaba d'aya, fara matsowa yayi inda take yana fad'in

"Tunda kink'i amsa wannan bari na miki wata" be jira tace komae ba ya matso kusa da ita ya rungume ta duk da k'ok'arin k'wacewa da take yi besa ya sake ta ba sema kissing d'in goshin ta da yayi, sannan ya sake ta ya mik'e ya fita daga d'akin, ta bishi da kallo k'walla fall na taruwa a idon ta... Tana nan zaune cikin d'akin ta jiyo sallama daga k'asan, seta mik'e a hankali ta bud'e k'ofar d'akin ta sauko, Buhaesa ce cikin atamfa riga da skirt ta ca6a kwalliya a fuskar ta, ta kalli Azrah da taga ta k'ara wani shahararren kyau, brown eyes d'in ta sunyi zuru zuru amma hakan seya k'ara musu kyau, seta d'auke kae, Azrah tayi k'arfin halin fad'in

"Sannu da zuwa"

"Yawwah" Buhaesa ta fad'a tana sake d'auke kae, abinda ya bawa Azrah mamaki kenan dan haka seta kama kanta, tana shirin ce mata ta zauna ta jiyo muryar Buhaesan tana fad'in

"Wajen Yah Adnan nazo ni" Azrah ji tayi kamar tace "toh kije ki nemo shi mana, ko yaron goye ne?" amma se tace bayan ta sake tattare annurin fuskar ta waje d'aya

"Yanzun ya fita.." kafin ta rufe bakin ta se gashi ya shigo cikin parlourn d'auke da leda a hannun sa, Buhaesa tayi murmushi tana wani yauk'i da iyayi ta k'arasa inda yake tace

"Sannu da zuwa Yah Adnan, kawo ledar" ta fad'a tana mik'a hannun ta zata kar6i ledar, ya d'an kalle ta kad'an sannan yace cikin basarwa

"Ba buk'ata" ya fad'a yana shirin wucewa inda Azrah ke tsaye, wadda ganin sa ya sanya ta fara k'ok'arin wucewa sama, Buhaesa tace cikin iyayi tana wasa da mayafin jikin ta

"Yah Adnan Dad ne ya aeko ni wajen ka, yace ya kira wayar ka bata shiga.." ta k'arasa maganar a shagwa6e ita a lallae dole dan taja hankalin sa kamar wata babba, ba tare daya lura da yanayin yadda take maganar ba yace

"Lafiya dae koh?" ya fad'a fuskar sa a had'e kamar ko yaushe.......




✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION53*



___"Ehh lafiya k'alau" bin Azrah data gama shigewa d'akin ta yayi da kallo sannan ya dubi inda Buhaesa ke tsaye yace

"Umhum.."

"Dama shine kawae.."

"Ohk I will call him.." ya fad'a yana wucewa saman, bin sa tayi da kallo kamar zata saka kuka, ta share k'wallar data fara tarar mata tana cigaba da kallan saman, ganin dae babu wanda keda niyyar sake sakkowa a cikin su ya sanya taja k'afafun ta ta fice daga d'akin.. Sanda ya shiga d'akin idanun ta a bud'e suke, tana ganin sa ta rufe idanun nata gam, yayi murmushi kawae sannan ya k'arasa ya ajje ledar daya shigo da ita kan side drawer sannan ya fita daga d'akin, wayar sa ya janyo ya kunna ta sannan ya kira Dad, seda suka gaesa sannan Dad yace

"Ku shirya zuwa gobe idan Allah ya kaemu zamu shiga can k'auyen Kima inda suka rik'e ita Azrah.."

"Toh Dad, Allah ya kaemu" ya fad'a yana ajje wayar, mik'ewa yayi ya fita daga d'akin zuwa nata d'akin, ya k'arasa yaja stool zuwa jikin gadon sosae sannan ya sanya hannun sa ya d'ago ta ya zaunar da ita, kafin ya cika ta ya nemo fararen kyawawan hannun ta da bak'in lallen ya d'an fara fita, rau rau tayi da ido tana neman k'wace hannun ta amma yak'i sakin hannun sema saka shi da yayi sosae cikin nasa yana d'an murzawa a hankali, ta kasa bud'e idanun ta dan haka har yanzun a lumshe suke tana sake k'ok'arin zame su, sannan ya fara magana a hankali yana kallan fuskar ta duk da yadda idanun ta ke a rufe

"I want apologize for my behaviour and the way i treated u, na miki abubuwa wad'anda ba zasu misaltu ba, I so much hurt u, nasani u have d right to be angry amma kin san am not perfect, am deeply sorry for everything.." ya k'arashe maganar a tausashe, tsayawa tayi da niyyar k'wace hannun ta da take yi, anya kuwa shine? Shine mutumin nan me girman kae, fad'in rae da wulak'anci? Toh amma meye ya chanja shi haka? Me yake k'ok'arin nuna mata ne?

"Ki shirya gobe zamu je k'auyen Kima" ba tare data shirya ba ta bud'e dara daran idanun ta, ae kuwa se suka sauka cikin nasa, yadda ta bud'e idanun ba tsammani yasa suka k'ara girma da wani irin kyau har seda hakan ya sanya shi lumshe nasa idanun har besan sanda ya furta

"Ya ilahy.." ya sake lumshe ido saboda wani shahararren kyau da yaga ta masa, yayin da ita kuma tayi saurin janye nata tana jin wani iri, se tayi amfani da wannan damar ta zame hannun ta cikin sanyin jiki, babu abinda ya fara zuwar mata kae se Hauwa'un ta, Allah sarki baewar Allah Hauwa'u ko yanzun tana ina?

"Bari na d'aukar miki kayan da zaki saka" ya fad'a yana mik'ewa, hannun sa ta rik'o da sauri tana girgiza kae, yabi hannun nasu dake cikin na juna da kallo wanda da alama bata san tayi hakan ba dan yadda yaga bayan taga abinda ta aekata d'in ta saki hannun da wani irin sauri, murmushin gefen baki ya saki sannan yace yana sake kallan cikin idanun ta dake da wani irin kyau

"Alright".... Ranar ma be takura akan kwana a d'akin nata ba dan shi kansa zeso ta samu ishashshen bacci ko dan inda zasu je goben.


...Washe gari da safe wajen k'arfe 8 ta shirya cikin riga da skirt na atamfa kayan sun matuk'ar amsar ta sun zauna sosae a jikin ta, tun jiya ta k'agu yau tayi dan ta ganta a k'auyen nasu, dan haka yanzun ma kasa sukuni tayi shiyasa ta shirya da wurin nan, dae_dae sanda take k'ok'arin d'aura d'an kwalin kayan ya turo k'ofar d'akin, ya tsaya daga bakin k'ofar yana k'are mata kallo yadda tayi wani kyau na musamman, seya k'arasa a hankali ya sanya hannu ya kar6i d'an kwalin yana cigaba da kallan ta sosae, se kuma ya k'arasa ya ajje break d'in da yayo musu take away sannan yace

"Maza zauna kici abinci, yanzun zamu fita" ba tare data kalle shi ba tace kamar zatayi kuka

"Ni ka bani d'an kwali na" binta da kallo yayi yadda tayi maganar da shagwa6a kamar tana sane seta k'ara yin kyau sosae, k'uruciyar ta na sake fitowa muraran

"Nak'i, kici abincin ko kuma kinsan sauran" yayi maganar yana had'e giraffe sama data k'asa dan idan ba hakan yayi ba cewa zatayi ta k'oshi bayan ba abinda taci, seda taga ba sarki se Allah sannan taja abincin ta fara tsakura, shi kuma ya cigaba da kallan ta hannun sa d'auke da d'an kwalin nata, kiran wayar sa da akayi ne ya sanya shi ya ajje d'an kwalin sannan ya fita, se a lokacin ta samu damar ajje abincin ta tashi ta k'arasa shiryawa, tana nan cikin d'akin sanda take k'ok'arin yafa mayafi ya shigo ya lumshe idanu ganin yadda kyan nata ya k'ara fitowa, ya kasa hak'uri seda ya k'arasa ya jata cikin jikin sa ya rungume ta tightly, k'irjin ta ya shiga bugawa da sauri sauri har seda ya saketan sannan ya rik'o hannun ta, suna k'ok'arin fita daga d'akin yace

"Ba abinda zaki d'auka" da k'yar ta iya d'aga kanta kawae mamakin mutumin na neman kashe ta, ta 6angaren sa kuwa tunanin sa ya ta'allak'a ne da yadda ze koya mata sonsa, dan duk wata alama ta nuna bata sonsa, kuma yasan ba kowa yaja hakan ba seshi da kuma halayen sa, amma yanzun yayi nadama kuma yana fatan zata yafe masa, a haka suka fita compound d'in gidan ya zagaya ya bud'e mata k'ofar me zaman banza, ta k'arasa a hankali ta shiga har lokacin zuciyar ta tak'i hutawa da tunane tunane, seda ta shigan sannan ya koma ya shiga driver seat ya tashi motar... A cikin compound d'in gidan Ammi yayi parking motar, ita ta fara k'ok'arin fita se taji motar a rufe, ta juya kad'an ta d'an saci kallan sa shima ita d'in yake kalla, seta tsinto muryar sa yana fad'in

"Pls kada ki bari Ammi ta gane akwae wata matsala tsakanin mu, pls ki min wannan alfarmar" yayi maganar kamar bashi ba, gyad'a kae kawae tayi sannan ya bud'e mata k'ofar ta fice daga motar yabi bayan ta da kallo yana dawo da kansa cikin motar, yasan kome ya faru laefin sane, but for now ya kamata ace ta yafe masa tunda ya gane kuskuren sa, kuma ya saka hannu biyu ya kar6i kuskuren nasa.. A parlour ta sami Ammin sanye cikin wani less had'ad'd'e da mayafi wadatacce, hannun ta d'auke da jaka, ta k'arasa da sauri ta rungume ta tana fashewa da kuka, girgiza kae Ammi tayi tana murmushi dan daga jin kukan kasan na shagwa6a ne tace

"Oyoyo, kun k'araso kenan?" Ammi ta fad'a sanda Azrah ta d'ago kanta tana goge fuskar ta, sosae Ammin taji dad'in ganin yadda d'iyar ta ta ta k'ara haske da wani fresh, tayi kyau abinta kamar wata babbar mace

"Toh menene kuma na kukan?" Ammi ta fad'a tana goge mata fuskar, dae_dae lokacin daya shigo d'akin da sallama a bakin sa, idanun sa a kanta suka sauka, seta tura baki gaba kafin tace

"Nayi kewar ki Ammi na" murmushi Ammin tayi dan ita kanta tayi kewar d'iyar ta ta tace

"Toh yanzu ba kin ganni ba?" ta fad'a tana maeda duban ta kan Don tace

"Sannun ku da zuwa"

"Yawwah Ammi an tashi lafiya?" ya fad'a bayan ya d'an risina, duk sa ba wani sosae ya risina d'in ba amma seda hakan ya sanya Ammi jin dad'i sosae, ko ba komae Adnan d'in ya fara chanjawa, Fitowar Abba ne ya sanya duka suka d'aga ido suka kalle shi, ya k'araso cikin parlourn yana kallan su da murmushi kan fuskar sa yace

"A'ah kun k'araso kenan? Toh sannun ku da zuwa" k'arasawa Azrah tayi inda Abban yake ta tsuguna tace

"Barka da safiya Abba"

"Lafiya k'alau Daughter, ku wuce mu tafi ga Dad d'in ku nan ma yazo yana compound" ya had'e amsar ya fad'a a lokaci guda.. Dukkan su suka fito compound d'in, nan aka tsaya aka sake gaesawa, Azrah ta gaeda Dad cikin girmamawa, tana kusa da Ammi sanda aka fara shiga mota, ya d'aga lumsassun idanun sa ya kalle ta, dae_dae sanda itama ta kalli sashen da yake se kuwa ya karyar da kae kamar wani maraya yana girgiza mata kae, Ammi ce ta shiga motar da Abba ya shiga sannan ta kalli Azrah tace

"Ki shiga motar mana" ba tace komae ba amma ita kad'ae tasan yadda taji bata ji dad'i ba, yanzun ma shiya bud'e mata motar ta shiga sannan ya koma ya tada motar.. Tunda suka fara tafiya ba wanda yace komae se dae shi da lokaci zuwa lokaci yakan juyo ya kalle ta, ta wani takure waje d'aya kamar me jin sanyi.. Tunda suka fara shiga k'auyen jikin ta yayi wani mugun sanyi, rayuwar ta ta baya ta fara dawo mata, abubuwa da dama ne sukazo suka yiwa kwanyar ta dirar mikiya, ta lumshe idanun ta tana jin wani irin yanayi data kasa fasaltashi. Tunda motocin su suka fara giftawa suna kutsawa zuwa cikin aenahin k'auyen mutane aka fara kallan su, dan harda motoci 2 da aka taho dasu na masu tsaron Dad, ga kuma wadda Abba da Ammi ke ciki sannan ga wadda Azrah da Don suke ciki, basu tsaya ko'ina ba se k'ofar gidan Malam Habu, nan fa mutane aka sake taruwa ana kallan ikon Allah, Don ya zuge glass d'in motar sannan ya yafito wani yaro dake tsaye shima yana kallan su yace

"Shiga gidan nan ka fad'a musu sunyi bak'i" yaron ya amsa da "toh" yana shigewa cikin gidan da d'an gudun sa, bayan wajen minti 1 se gashi ya fito yace ance su shiga, se a lokacin dukan su suka fara saukowa, Azrah ta bud'e 6angaren da take ta fito a nutse, da farko babu wanda ya gane ta seda wata yarinya tace

"Laaaaa Azrahr Inno.."ta fad'a da mad'aukakin mamaki a fuskar ta, se a lokacin kowa idon sa ya koma kan wadda aka kira da Azrahn, nan da nan kuma se aka koma fad'in

"Laaaaa itace, wallahi itace" abinda kafatanin en wajen ke maemaetawa kenan, kafin kace menene wannan mutanen wajen sun fara darewa kowa na tunanin inda zeje ya fara sanar da wannan labarin, aekuwa kafin kace menene labari harya fara baza gari cewar Azrah ta dawo gida da wasu mutane masu kud'i.... Ammi ce a gaba sannan Abba da Dad, kana Azrah da Don sune a k'arshe a haka suka shiga gidan da sallama dukkan su a bakin su, Azrah na sake kallan gidan da taga ya sake lalacewa, dan hatta k'ofa ma yanzu babu da buhu aka rufe k'ofar gidan saboda kada a hango tsakar gidan. Fitowar ta kenan daga cikin d'akin bayan ta d'akko hijab d'in ta, kallan su ta tsaya yi tana mamakin su waye wad'annan? Me sukazo yi gidan nan? Bata iya amsa sallamar su ba se cigaba da tayi da kallan su, wadda ta hango a k'arshe itace ta sanya ta k'amewa a inda take, indae ba gizo idanun ta ke mata ba kamar Azrah ce, ko cikin mafarki taga fuskar tabs Azrah seta gane ta ballantana kuma gata ta ganta in reality, se dae yadda ta ganta d'in ta matuk'ar chanjawa ya bata mamaki, se dae duk da mamakin da take ciki hakan be hanata furta

"Azrah!!" ta fad'a cikin d'aga murya, bin matar Azrah tayi da ido tana mamakin jin muryar Inno a tattare da ita, dan Inno akwae jiki wannan kuma gata nan siririya kamar ka hure ta ta fad'i, seda ta sake yin gaba sannan ta gasgata lallae Inno ce a gaban ta

"Azrah" Inno ta sake fad'a tana matsawa kusa da Azrah da itama take k'arasowa wajen Innon, rik'o ta Inno tayi hawaye na taruwa cikin idanun ta tace

"Azrah ke d'in ce ko kuwa dae gizo ne ido na kemin?" kasa cewa komae Azrah tayi ta cigaba da kallan Innon wadda ta wani kwarzale tayi bak'i sosae sannan jikin ta ya yamushe kamar wata tsohuwa

"Ki fad'a min don Allah kece?" maganar Innon ta dawo da ita hayyacin ta, seta d'aga brown eyes d'in ta da suka gama cika taf da hawaye tace

"Ehh nice Inno.." muryar da Inno taji ya tabbatar mata Azrahn ce, seta fashe da kuka kawae kamar k'aramar yarinya, Ammi da tun d'azu take kallan su ta k'araso duk da yanayin yadda jikin Innon yake hakan be sanya tak'i rik'e ta ba, ta rik'o ta tana fad'in

"Mu samu waje mu zauna tukunna" Ammi ta fad'a tana jan Inno ta zaunar da ita kan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gidan, se a lokacin dukkan su suka samu suka zauna kan tabarmar, Don kuma ya zauna kan wata kujera daya gani gefen sa, har lokacin Inno kuka take ta k'agu taji ya akayi aka kwana a ragaya?

"Azrah kimin bayani hannun wa muka damk'aki? Ina wanda muka aura miki? Ki fad'a min don Allah" tayi maganar tana share k'walla, Dad ne yayi gyaran murya sannan yace

"Wato ni da kaena nazo na nemarwa d'ana auran Azrah, amma ina mae gidan naki? Zanso yazo yayi mana bayani, dama baku san wa kuka aurawa Azrah ba? Ko kuwa menene?.."

"Ashsha, Alhaji wallahi bamu sani ba, amma tun ba'a dad'e ba muka yi dana sani, wallahi se daga baya na fara tunanin ko mun mik'awa mugwaye ita ne.." ta k'arashe maganar tana kallan Azrah da har lokacin mamakin yadda ta ganta yak'i sakin ta, ita kanta Azrah d'in kallan Inno kawae take yi tana jira taji abinda ya maeda ta haka, Inno ta cigaba da fad'in

"Se ranar nan naji a gari cewar wanda ke auren Azrah d'in yazo k'auyen nan neman asalin ta, se dae kafin labarin yazo kunne na har ya bar k'auyen, kaji dalilin da yasa bamu had'u ba" da sauri Azrah ta d'aga idanun ta ta kalli inda yake zaune, tun d'azu dama idanun sa na kanta ne, duk da yadda idanun su suka shige cikin na juna seta kasa d'auke idanun nata dan mamakin jin furucin Inno ya hanata yin hakan, wae shi kam toh wane irin mutum ne? Lumshe idanun sa yayi yana bud'ewa lokaci d'aya akanta, karo na farko kenan da taji wani abu ya tsirga mata har bata san sanda ta lumshe ido ba sannan ta d'auke kae ta maeda kan Inno

"Ina mae gidan naki?" Dad ya fad'a, kuka ne ya k'wacewa Inno ta fara yi ba k'ak'k'autawa seda ya tsagaeta sannan tace

"Don Allah ku fad'a min su waye ku? Meye had'in ku da Azrah?" Abba ne ya gyara zaman sa sannan tiryan tiryan ya fara yiwa Inno bayanin wacece Azrah, da duk wani abu daya kamata ta sani, yanzu kam kuka me sauti ya k'wacewa Inno, ta dinga yin shi babu wanda ya hanata, seda tayi me isarta sannan ta dakata tana kallan Azrah tace

"Kiyi hak'uri don Allah Azrah, na shiga uku ni ennan, na shiga uku ni Habee, ashe ke d'in wata ce bamu sani ba Azrah? Ashe ke d'in er halak ce bamu sani ba? Ashe inda muke ta cusa ki alkhaeri ke kiran ki, had'uwa da iyayen ki ke kiran ki? Innalillahi wa inna ilaehi rajiun Azrah ki mana aekin gafara don Allah, mun cutar da rayuwar ki, mun cuce ki, munso mu lalata miki rayuwar ki, sedae inda Allah ya taemake ki ke d'in tsarkakakkiya ce gashi nan shiyasa Allah ya kare ki, ki yafe mana Azrah, wallahi munyi nadama daga ni har Baban Ilyasu, munyi munyi mu nemo inda kike amma bamu samu ba, matar da tazo neman auran ki gaba d'aya watsar damu tayi, tama dena d'aga kiran mu gaba d'aya, Azrah ki yafe min hantararki dana dinga yi, maeda ki kamar jari da muka yi.. amma da yake er halak ce ke baki ta6a nuna 6acin ranki akan hakan ba, don Allah ki yafe mana.. tun bayan tafiyar ki babu dad'ewa Ilyasu yayiwa wata yarinya fyad'e ya gudu, iyayen ta basu da k'arfi amma suka samu wani me kud'i ya tsaya musu, aka nemi Ilyasu ba'a same shi ba, shine sukazo gidan nan akan mu fito dashi dan sun san munsan inda ya 6uya koma mune muka 6oye shi, muka nuna musu bamu san inda yake ba amma duk da haka basu yadda ba, sukace idan suka tafi da Baban Ilyasu sunsan dole zan fito da Ilyasun, ba irin rok'an da ban musu ba amma haka inaji ina gani suka tafi da Baban Ilyasu, daga nan rayuwa ta ta chanja.."ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka me cin rae, se can ta d'ora da

"Dama kafin tafiyar ki kamar kece me ciyar damu, tunda sekin siyar da abu muke samu muci abinci, se zuwan matar nan ne dae abin ya chanja, itama kuma a lokacin ta d'auke mana k'afa, bansani ba ko daga hannun wadda kud'in ke biyowa ne ake samun tsaeko amma ni dae gaba d'aya se aka dena bamu ko sisi, sannan ta dena d'aga waya ta gaba d'aya, toh se Baban Ilyasu ke d'an buga bugan sa mu samu muci abinci, se kuma ga abinda ya faru na kama shin da akayi, shikenan na zama babu me taemako na, ba wanda ke nemo abinci ya bani inci, bani da kud'i ballantana nace zanyi sana'a, haka dae nake samu na shiga mak'ota in samo wani abun inzo inci, tun suna bani suma seda sukazo suka gaji suka dena, dama ba wani zaman mutunci muke yi da mafi yawan en k'auyen ba se d'aed'aeku, toh wa zan tunkara a wannan yanayi daya sameni, suma wad'anda muke mutuncin yanzu sun gaji sun dena bani, rayuwa ta k'untata min, kuma a lokacin na gane ba en sanda ne suka kama Baban Ilyasu ba wasu ne dae suka kama shi bansani ba ko en uwan wadda aka yiwa abin ne, dan har wannan lokacin ba labarin Baban Ilyasu ba dalilin sa, shi kansa Ilyasun bansan inda yake ba, bansan ina yake ba, ni dae gani nan haka na cigaba da rayuwa ta wataran sena wuni banci komae ba, haka zan kwana ina shan ruwa, se daga baya ne wata shawarar ta fad'o min, na fara bin gidajen masu kud'in garin nan ina kar6ar musu wanki da wanke wanke suna biya na, duk da biyan be wani kae ya kawo ba, dan se in wuni ina aekin wanki, wanke wanke da sauran su a gida amma a k'arshe a bani 300, da dae naga hakan ma ba mafita bace ga ciwon hannu da nake yi wanda hannun nawa seda yayi kanta yayi wani iri kamar wadda ta k'one sena hak'ura na cigaba da tunanin mafitar da zan samawa kaena ko dan in tsira da koda ciki na ne........




✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION54*



___..haka dae na cigaba da rayuwar babu taemakon kowa sena Allah, lokaci guda kuma ina tunanin yadda zanyi in san inda Baban Ilyasu yake, haka dae tun ina 6oye abin da dae naga babu haza se naje na samu me gari akan maganar na tonawa kaena asiri da abinda Ilyasu ya aekata, me gari yace za'a bincika aji inda yake, nan ma dae aka bincika babu labarin Baban Ilyasu kwata kwata, haka dae na hak'ura, rayuwa ta sake min k'unci, na rasa inda zan tsoma kaena inji dad'i, nayi dana sanin rashin zaman lafiya da mutane dan badan haka ba nasan zasu taemakamin, inda Allah ya taemake ni se me gari yace wa matar sa ta dinga bani abinci idan aka daft a gidan, da farko tana bani kamar yadda ya umarta d'in amma daga baya seta dena bani kwata kwata, na d'auka ma ko me garin ne ya gaji yace a dena bani se daga baya na fahimci ita da kanta ta dena bani, haka na cigaba da rayuwa abincin da zanci ko sau d'aya ne a rana ya gagare ni, idan na tuna rayuwa sedae in yita kuka kawae, na kuma rasa yadda zanyi na samu Azrah, dan da farko abinda yasa nake neman ta dan in samu in jingina a jikin tane ko dan in dinga samun abinda zanci, amma daga baya se wannan ya fita a raena lokacin da nayi wata rashin lafiya me tsanani, daga ciwon yatsa shikenan abu ya kusa samin ta6in k'wak'walwa, a lokacin ne nayi jinya sosae, sedae in yita sumbatu ni kad'ae, wataran har fita nake daga gidan nan

Please Login or Register in order to submit comment