Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da biro, pencil, math set, da dae sauran abin buk'ata na d'alibi, seta sake k'arasawa tana kallan kanta a mudubin, ita kanta ta san ta chanja sosae, kamar ba ita ba tayi wani irin fresh, tayi kyau acan acan abinta, er k'aeama da ita kamar ka sace ka gudu, kawae seta samu kanta da yiwa kanta murmushi tana sake kulle fuskarta da hannayenta, sannan ta janyo k'ofar d'akin kana ta sauko k'asa a hankali tana kallan agogon d'akin dake nuna k'arfe 7:20, ta fita compound d'in gidan tana jinta wata daban kamar ba ita ce ba, tana nan tsaye kamar yadda ta tsaya jiya, se gashi ya fito daga cikin d'akin kamar koda yaushe cikin k'ananan kaya, ya k'arasa ya bud'e motarsa ya shige ba tare daya kalli inda take ba, tana ganinsa ta sake yin k'asa da idanunta tana fad'in cikin rawar murya

"Ina kwana?" Shirun dae shine amsar sa yayi shigewarsa cikin motar ya tasheta, ba tare daya kalleta ba ya fice daga gidan gaba d'aya, seta bishi da kallo tana jin yadda 'kwalla ta ciko a idanunta, kawae seta lumshe idanunta tana barin hawayen na zubo mata, tana nan tsaye ta jiyo horn d'in mota a k'ofar gidan, bata iya ko motsi ba tana tsaye har lokacin idanunta a lumshe, se jiyo murya tayi a kusa da ita yana fad'in

"Aunty Azrah zamu makara fa" Seta d'ago da sauri jin muryar Fawaz ta kalleshi da mamaki, seya sakar mata murmushi yana fad'in

"Kuka kuma?" Seta saka hannunta ta goge hawayen tana k'ak'alo murmushi kana tace

"A'..ah ba kuka nake ba"

"Ohk ki taho mu tafi" babu musu tabi bayan Fawaz d'in zuwa k'ofar gidan, wato inda sukayi parking na motar da sukazo da ita kenan, Fawaz ya kulle gidan sannan ya dawo ya shiga front seat yayinda ta shige backseat driver yaja motar suka fara tafiya, shiru tayi tana nazarin wannan mutumin, shi kuwa wane irin mutum ne shi da kwata kwata besan darajar d'an Adam ba? Seta sake yin shiru tana bin titi nan da suke wucewa da kallo har suka k'arasa makarantar.... Fawaz ne ya kaeta ajinsu wato SS1 kenan science department, sannan ya kalleta ita dae ba abinda take cewa tayi shiru duk a kunyace take yace

"Idan kina buk'atar wani abu, ga class d'in mu can" ya fad'a yana nuno mata wani class dat is far from them, ta kalleshi kawae ba dan ta gane ajin ba kawae ta gyad'a kae, yace yana gyara zaman jakarsa

"Zan iya tafiya matar Bhai? Babu wata matsala?" Ya k'arasa maganar da sigar zolaya, a hankali ta bud'e bakinta tace

"Ehh" yace

"Ohk bye" ya fad'a yana wucewa bayan ya d'aga mata hannu, seta d'aga k'afafunta a hankali ta k'arasa zuwa cikin ajin da sallama d'auke a bakin ta, duk se hankalin en ajin ya dawo kanta, kowa ya zubo mata idanu, wasu na kallanta ne a matsayin bak'uwar fuska yayinda wasu ke kallan zallar kyawunta ne, duk seta diririce ta rasa mema zatayi kawae seta dakata daga inda take ta kasa d'aga ido ta kallesu, wata yarinya da ba zata wuce sa'ar Azrahn ba ta taso ta k'araso tana murmushi ta rik'o hannun Azrahn tace

"Welcome sabuwar zuwa" Azrah tayi yak'e bayan ta d'aga ido ta kalli yarinyar, seta jata zuwa cikin ajin ta nuna mata inda zata zauna ta k'arasa ta zauna har lokacin a d'arare take, wata yarinya da kamarsu d'aya da wadda ta tarbi Azrah da alama en 2 ne ta kalli Meemarh tana ta6e baki tace

"Uhmm ae dama anan kika fi kauri" ita dae Meemarh bata ce komae ba ta kalli Azrah tace tana mik'a mata hannu dan haka kawae taji ta burgeta gata kyakykyawa kuma gata nutsatsiya, ga wani irin idanu da take dasu masu kyawun gaske brown

"Am Meemarh Abubakar U?" Azrah ta kar6i hannun da Meemarh ke mik'o mata tayi d'an murmushi kana tace

"Azrah!!"

"Wow nyc to meet u" Azrah tayi murmushi kawae ba tace komae ba... Suna nan zaune har wani malami ya shigo ya cinye period d'insa ya fita sannan wani ma ya shigo haka dae har aka fita break, Sanda aka fita break ita dae tana zaune kan bench, Meemarh ta kalleta tace

"Ki tashi mu fita break" Azrah ta girgiza kae

"A'ah kuje kawae" Meemee dake tsaye bakin k'ofar ajin tace

"Wae kema Meemarh kamar wata mayya, tace miki ba zata je ba base ki k'yaleta ba?" Meemarh ta watsawa Meemee harara kana ta kalli Azrah

"Ohk bari muje.." Daga haka suka fice daga ajin, Azrah ta bisu da kallo ba tare sa taji mae game da abinda Meemee ta mata ba, dan ba kanta farau ba, indae irin wad'annan maganganun ne ta saba jinau daga bakin mutane da dama a k'auyensu, toh may be bata mata bane, dama kuma ae ba lallae kayiwa kowa ba, daga haka Azrah ta dawo da dubanta kan blackboard d'in da aka musu rubuta akae, seta ciro littafin da tayi rubutu a ciki, ta sake duba abinda aka koya musu sosae har zuwa sanda su Meemarh suka dawo, Meemarh ta kalli Azrah da murmushi kan fuskarta tace

"Gaskiyane, wae dama karatu kika zauna yi?" Azrah ta d'ago ta kalli Meemarh sannan tayi murmushi tace

"Ehh.." Meemarh tace

"Toh bari na zauna nima a koyamin" ta fad'a tana zama, Azrah tace

"Ni so nake ma ince ki koyamin abubuwan da akayi bana nan" ta fad'a innocently, Meemarh tayi murmushi sannan tace

"Ohk ba damuwa.."......... A gajiye lik'is ta koma gidan, dan babu k'arya an sha karatu ga wani irin yunwa da take ji, dan haka tana dawowa wanka kawae tayi ta koma kitchen ta d'ora girki, cikin awannin da basu wuce 2 ba ta gama girkin gaba d'aya hadda juice, ta saka a fridge sannan ta jere abincin kan dinning kana ta dawo ta d'ebo abincin ta zauna a cikin parlourn taci abincin sannan ta mik'e ta koma saman ta d'akko jakarta ta sake dawowa k'asan, ta haye kan kujera tana fito da littafan da akayi musu note yau ta fara dubawa, seda ta d'an fara dubawa sannan ta mik'e ta ciro lemon data saka a fridge wanda yayi sanyi ta maedashi kan dinning sannan ta koma ta cigaba da duba littafanta.... Zamanta babu wuya ya shigo cikin parlourn, dan ita bama taji shigowar motarsa ba saboda yadda gaba d'aya hankalin ta yayi kan karatun da take, seda ya shigo kuma sannan ta lura da shigowarsa, ta d'ago da sauri bugun zuciyarta na k'aruwa, tace kamar zata saka ihu

"Ina..yini.." Ta fad'a tana maeda dubanta kan littafinta, kae tsaye ya wuce saman benen without even looking at her, seta dawo da dubanta kan dinning tana sake sauke ajiyar zuciya, seta ji kamar ta mik'e kawae ta tafi d'akinta amma se wata zuciyar tace kawae ta zauna, dan haka kawae ta zauna ta cigaba da karatunta....... Seda yayi wanka ya shirya cikin k'ananan kaya marasa nauyi sannan ya sauko zuwa k'asan, direct dinning area ya wuce yaja kujera ya zauna yana bud'e warmers d'in dake ajje, yayi serving kansa kana yaci abincin, seda ya gama tass ya kora da juice me sanyi har lokacin besan tana cikin parlourn ba, wayarsa tayi k'ara, ya kalli me kiran sannan ya d'auki wayar yana karawa a kunnensa, daga can 6angaren Mami tace

"Son kana gida ne?" Yace

"Ehh.." Mami tace

"Ohk taemaka ka bawa Azrah wayar zamuyi magana, na kira ta ta ne ban sameta ba"

"Az..rah!" Ya maemaeta sunan akan la66ansa a rarrabe kamar me koyar magana kana yace

"Waye hakan?" Ya k'arasa maganar sounding seriously, dan shi harga Allah da gaske yake besan sunanta ba kuma besan wace hakan ba, Mami tayi kasak'e daga inda take tsaye kana tace

"Sannu kaji Son, toh Matar ka, ina nufin matar dake zaune a cikin gidan ka"

"Ohhhh.." Ya fad'a yana dafe kansa sannan ya jefa idanunsa cikin parlourn, seya hango ta a d'an kishingid'e kan kujera da alama wani abin take, yaja k'aramin tsaki kafin yace

"Bansan inda take ba" Mami tace

"What?, Son!! Baka san inda take ba? Pls ka dubamin ita yanzun ka bata wayar Uhmm?" Kamar baze tanka ba se kuma ya mik'e a nutse zuwa cikin parlourn fuskarsa a tamke sedae be cewa Mami komae ba, tana zaune tana rubutun ta se jin alamar tafiya tayi, da sauri ta tashi zaune tana k'ok'arin saeta bugun zuciyarta, ya k'araso cikin parlourn ba tare daya kalleta ba ya ajje wayar kan centre table ya juya, seta kalli wayar daya ajiye kana ta kalleshi sanda yake k'ok'arin komawa saman, seta dawo da kallanta kan wayar ganin alamar waya ake, kuma ga sunan "Mami nah" ya bayyana akan screen d'in ya sanyata d'aukar wayar tana karawa a kunnenta, ji da Mami tayi shiru ne ya sanyata fad'in

"Hello.." Dae_dae lokacin da Azrah ta kara wayar a kunnenta, tace

"Hello" daga can 6angaren Mami tace

"Yawwah Azrah.. Kina jina?"

"Ehh ina yini?" Azrah ta fad'a, Mami tace

"Alhamdulillah.. Ya kuwa fara cin girkin naki?" Azrah tayi shiru tana tunanin maganar da Ammi ta fad'a mata, amma bata tunanin har Mami take nufi, amma dae bari seta tambayeta daga baya dan haka tace a hankali

"A'ah Mami tukunna dae.."

"Toh kisan yadda zakiyi da kissa da kisisina ya fara cin abincinki, daga haka kuma shikenan, kinsan girki ba k'aramin tasiri yake yi wajen kama zuciyar me gida ba" duk se kunya ta kama Azrahn tayi k'asa da kae kamar Mamin na gabanta, se taji bata ji dad'in k'aryar data mata ba, haka zalika lokaci guda kuma tana mamakin yadda matar ke k'aunar Don d'in wanda har hakan seda ya shafeta itama tana nuna mata k'auna yadda ya kamata, gashi har shawara take bata akan d'an nata, se taji ta sake birgeta dan haka tace

"Toh Mami nagode"

"Babu komae Azrah.." Daga haka Azrah ta mik'e ta d'auki books d'in ta sannan ta ajje masa wayarsa kan centre table d'in tayi wucewarta sama......



*** *** ***

Qarfe 5 ne na ranar tana zaune kamar koda yaushe cikin parlourn tana maemaeta karatun da Meemarh ta koya mata ta ji ana knocking daga bakin gate, abinda bata ta6a ji ba kenan tun zuwan ta gidan, seta mik'e a hankali jin an cigaba da bugun, ta saka takalmi kana ta fito zuwa compound d'in, ta k'arasa a hankali ta tsaya bakin 'kofar bata ce komae ba taji ance

"Me gidan baya nan?"

"Ehh" ta fad'a a d'an tsorace, wanda yayi maganar ya sake cewa

"Ohk..toh gashi a bashi wannan takardar don Allah, gobe da sassafe ne za'ayi taron, a battar anyi serving nasa pls" Seta d'an bud'e k'ofar kad'an ta kar6i takardar da aka mi'ko mata ba tace komae ba, ta kulle k'ofar kana ta dawo cikin gidan, tana nan zaune bayan ta gama karatunta ta cigaba da zaman jiransa cikin d'akin ko Allah zesa ya shigo ta bashi sak'on, sedae har bayan k'arfe 11 mutumin nan be shigo gidan ba, gashi wani irin bacci me dad'i se sakad'arta yake, a haka ta mik'e da takaddar a hannunta ta ajjeta kan centre table sannan ta wuce saman, tayi wanka kana ta nemi wajen bacci, aekuwa babu dad'ewa wani bacci me dad'i ya kwasheta..... Firgigit ta farka daga baccin daya d'auke ta, ta kunna 'karamin light d'in d'akin dake kusa da ita kana ta janyo wayar ta dake kan mirror taga k'arfe 1:30, seta mik'e a hankali ta sakko daga kan gadon tana murza idanunta ta shige toilet ta wanke fuskarta sannan ta fito daga d'akin kae tsaye ta wuce zuwa downstairs, ta k'arasa tsakiyar parlourn tana fatan taga ya d'auki takardar, sedae ga mamakin ta se taga takardar na nan inda ta barta, dan haka ta k'arasa kamar zata fashe da kuka ta d'auka sannan tayi sama da ita, seda ta hau saman sannan ta tsaya tana tunanin mafita, ita kam yau ta shiga 3 ya za'ayi ta bashi wannan takardar?, ko dae ta ajjiye masa a k'ofar d'akin, ae kuma ze iya yiwuwa be gani ba se sanda yazo fita daga gidan, kamar me k'irga adadin tsayin wajen ta fara takawa a hankali kamar mara laka harta k'arasa wajen k'ofar d'akin sa ta tsaya zuciyarta na bugawa haka zalika idanunta sunyi rau rau kamar zata saki kuka, ta kae hannunta kusan sau 3 kamar zatayi knocking se kuma ta fasa, se daga k'arshe kawae tayi shahada bayan ta runtse idanunta tayi knocking k'ofar...... Wajen k'arfe 1:00 ya shigo gidan, dan haka yana shigowa direct toilet ya fad'a yayi wanka ya fito d'aure da towel madaedaeci se zuba k'amshi yake, gargasar jikinsa wadda ke d'auke da damshin ruwa ta kwanta tayi luff luff akan k'irjinsa hannunsa d'auke da comb yana taje kwantacciyar sumar kansa, ya k'arasa gaban mirror ya fara taje sumar kan nasa, kamar a mafarki yaji ana knocking k'ofar tasa, seya tsaya daga taje kan nasa da yakeyi, ya dubi k'aramin agogon dake manne a bangon d'akin wanda ya harba k'arfe 1:45, "a'ah toh waye kenan a cikin wannan daren?" Ya tambayi kansa fuskarsa a cunkushe, kafin ya ajje comb d'in saboda tsananin mamaki yama manta towel ne kad'ae a jikinsa ya k'arasa zuwa wajen k'ofar.................



08124818273



✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION26*


_____Yana dab da k'arasawa k'ofar ya tuna abinda ke jikinsa, seya dawo da baya ya zura wata farar singlet da boxers sannan ya koma zuwa wajen k'ofar ya bud'e a hankali yana son ganin me yin knocking na k'ofarsa a wannan dare, Da wani irin mamaki ya kalli abinda ya gani a k'ofar d'akin, wato Azrah dake shirin ajiye takadda zata juya, cikin wata kausashshiyar murya ya furta

"Kee" seta tsaya cakk tana rik'e saetin zuciyarta hawayen da suka mak'ale suka samu damar zubowa, seta juya a sukwane kamar zata fasa ihu a hankali ta furta

"Ina wu..ni?" Ta fad'a a rarrabe, kafin ta k'arasa maganar ya katse ta da fad'in

"Wace ce ke?" Runtse idanunta tayi tana jin tambayar kamar saukar aradu, seta gaza furta komae har seda ta sake jiyo muryarsa cikin tsawa yace

"Wace ce ke?" Seta bud'e bakinta da yayi mata nauyi a ranta tana ayyanawa kada taje ya mata wata fassarar dan haka tace murya na rawa

"Takaddar nan akace na baka" ta fad'a da siririyar muryarta wadda take rawa, ya kalli inda ta nuna d'in sannan ya sake tamke fuska yace

"Kada ki sake aekata hakan, kada ki sake wannan kuskuren, stay away from my life, ki kama kanki and kiji da rayuwarki..." Daga haka ya d'auki takaddar sannan ya koma cikin d'akin ya buga k'ofar da k'arfi wanda har seda hakan yasanya ta toshe kunnenta tana sake runtse idanunta, Zubewa tayi akan k'afafunta tana jin yadda jikinta yake rawa, ta fashe da wani marayan kuka fuskarta d'ore akan gwuiwoyinta, yau karo na farko kenan taji dama mahaefiyarta na kusa da ita ta d'ora kanta akan kafad'arta tayi kuka sannan ta fad'a mata damuwarta ko zuciyarta zatayi sauk'i, sedae kashh ita ba irin kowacce uwa gareta ba, tata uwar bata san ganinta bata k'aunarta tun ranar data haefeta, seta sake fashewa da kukan kana ta mik'e a hankali ta shige cikin d'akinta tana goge hawayen da keta tsere akan kuncinta......


.........Washe_gari data tashi gaba d'aya jikinta a matuk'ar sanyaye yake, haka kawae ta tsinci kanta da jin zafin abinda mutumin nan ya mata a daren jiya, sedae hakan be hanata shiryawa ta tafi makaranta ba, ko da taje makarantar ma seda Meemarh tayi noticing yadda yanayin ta ya chanja, amma ganin bata ce mata komae akan hakan ba ya sanya bata tambayeta ba, Se can suna zaune tace

"Ina assignment d'in ki?" Azrah ta kalli Meemarh dake mata magana tace

"Bari na d'akko" ta fad'a tana bud'e jakarta ta fito da wata fulls cap da rubutu a jiki tace

"Kin gani na fara amma ban gama ba, saboda ba wayar browsing a wajena" Meemarh ta kar6i takaddar ta kalla sannan tace

"Baki da yaya ne?" Seta d'anyi k'asa da kae tace

"Ehh bani da"

"Meyasa baki kar6i wayar wani daga en gidan ku ba?" Azrah ta d'anyi jimm sannan tace

"Uhmm" ta fad'a kwae, Meemarh tace

"Ohk shikenan..ae naga kinma kusa gamawa bari na duba miki, sena sake nuna miki yadda zaki k'arasa" Azrah tayi murmushi sannan tace

"Nagode Sosae Meemarh" Meemarh tayi murmushi har lokacin kanta na kan takaddar tace

"Always welcome dear".... Sanda aka fita break a ranar Meemarh ta tilastawa Azrah fita break, yau dae Azrah ta amince da hakan dan karta zama mara kirki, suka fito zuwa filin makarantar a tare, kae tsaye suka wuce wajen me siyar da yoghurt, Meemarh ta kalli Azrah tace

"Wanne zaki sha?" Azrah tace

"Duk wanda zaki sha" Murmushi Meemarh tayi tana fad'in

"Ke koh!" Suna nan tsaye aka saka musu yoghurt d'in a leda sannan suka fara k'ok'arin juyawa daga wajen nasa, Wani da baze wuce sa'an Fawaz ba ya k'araso yana kallansu da murmushi kan fuskarsa ya kalli Meemarh yace yana shafa k'eyarsa

"Yaane Meemarh..wannan k'awar taki fa?" Ya fad'a yana kallan Azrah wadda ta d'anyi gaba dan ta basu damar tattaunawa, Meemarh ta jefa masa harara tace

"Haka dae, ni don Allah ka k'yaleni" Yace

"Haba mana Meemarh, wallahi tamin fa" Meemarh tace tana yin gaba

"Toh" daga haka taja hannun Azrah sukayi gaba, Azrah duk jinta take a matuk'ar takure yadda duk inda suka gifta se an kallesu, suna shiga ajin ta sauke numfashi sannan ta sake k'udura a ranta ba zata sake fita break d'in ba, tunda dae ta riga data sani duk lalacewar mijin nata ita matar aure ce, tana cikin wannan tunanin ta tsinto muryar d'aya daga cikin en ajin na fad'in

"Hajiya Meemarh me k'awa!" Ta fad'a maganar da izgili a cikinta, ko kallan inda take Meemarh ba tayi ba sema kallan Azrah da tayi tace

"Yau kam da wuri zan koma gida, Mum ce zata dawo yau, kinga ma Meemee ko zuwa ba tayi ba" Azrah ta kalli Meemarh dan bata ji dad'in jin hakan daga bakinta ba, saboda har yanzu ta kasa sakin jiki da kowa a cikin ajin se Meemarhn kawae, A hankali ta lumshe idanunta tana tunanin ko yaya masu uwa sukeji? Yaya suke rayuwarsu? Ko yaya soyayyar uwa da uba take? Se ta d'ago tace a hankali

"Allah ya dawo da ita lafiya!"

"Ameen Ameen Azrah nagode"


.........Washe_gari ya gama shiryawa yana shirin fita daga cikin d'akin zuwa wasan da zasu gabatar yau wayarsa tayi k'ara, ya d'auki wayar ya manneta akan kafad'arsa yana saka takalminsa, Dad yace

"Kana gida ne?" Don yace

"Ehh.."


"Ohk..ka d'auko matar taka kuzo gida ku duba Yakumbo bata ji dad'i ba, sannan jiya matar Alhaji Abubakar ta dawo zata shigo gidan yau seku gaesa" Kamar ze musa da abinda Dad d'in yace se kuma ya tuna k'orafin Dad d'in akansa, dan haka yace

"Oh..k" daga haka Dad ya katse wayarsa, ya k'arasa saka takalminsa ya fito daga d'akin zuwa k'asa, yana shirin fita daga d'akin ya tuna bashi kad'ae Dad yace yazo ba, dan haka seya koma da baya cikin parlourn ya d'auki biron daya gani ajjiye akan book yayi rubutu kamar haka

"U should go home, inji Dad" abinda ya rubuta kenan sannan ya ajje wasu kud'i kan table d'in yayi waje dan kuwa besan yadda zeyi ya had'a numfashi da ita kad'ae cikin mota ba, wancan karon ma dan tare suke da Sameer ne, kuma anyi na farko anyi na k'arshe, ya fice daga d'akin yana sake mamakin yadda akayi har yanzu daga Dad har Mamin ko iyayenta suka gaza zuwa su d'auke ersu tunda dae shi kam yasan be ta6a ajjiye ko k'wayar abinci a gidan ba ballantana akae ga na sakawa, ya ta6e baki yana fadad'a tunaninsa ko akwae wata mafitar bayan wannan......



.........Wajen k'arfe 10pm ta fito daga d'akin zuwa kitchen saboda yau tunda ta tashi bata fito ba ko break bata yi ba, kae tsaye ta wuce kitchen ta d'ora sassauk'an abinci sannan ta fito zuwa parlourn ta zauna a hankali ta fara tsakurar abincin, zuwa can hankalinta ya sauka akan wani kud'i wanda bata lura dashi ba se yanzun, seta ajjiye plate d'in dake hannunta ta d'auki kud'in a hannunta se wata er takadda ta bayyana a k'asan kud'in, seta rik'ota da sauri kafin ta fad'i k'asa, ta kae idanunta akan takaddar ta karanta abinda ke jiki, seta sake kallan kud'in tana juyasu a hannunta, seta ajjiye ta k'arasa cin abincin sannan ta mik'e ta koma d'akin, wata zuciyar na zugata akan ta rabu dashi tayi zamanta se dae wata kuma na tuna mata waye shi a wajenta, dan haka kawae ta fad'a toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa sannan ta d'auko jalbab hijab d'inta dogo har k'asa ta zura kana ta fito daga d'akin, a hankali ta wuce zuwa compound d'in gidan ta k'arasa tana kallan cikin gidan, sannan ta fita ta saka mukulli ta kulle gidan.... Seta juya a hankali ta fara takawa zuwa titin unguwar tasu dake da d'an nisa daga gidan, a haka harta k'arasa titi, ta samu adaedaeta ta hau....... A k'ofar gidan ya ajiye ta, ta sauka ta bashi kud'insa sannan ta wuce zuwa cikin gidan, kae tsaye ta wuce part d'in Mami...da sallama ta shiga part d'in cike da nutsuwarta, Mami dake zaune kan kujera tana kallo ta kalli Azrah tana fad'in

"Oyoyo..Azrah" Azrah ta k'arasa cikin d'akin a kunyace ta zauna a k'asa tana fad'in

"Barka da warhaka Mami" Mami tace

"Barkanki dae, kuna lafiya?" Ta sake yin k'asa da kae tana wasa da jakar hannunta tace

"Alhamdulillah" Nan suka sake gaesawa kafin Mami ta kalli kalli Azrah tace

"Kin shiga wajen Yakumbo kuwa?" Azrah tace

"A'ah" Mami tace

"Ahh toh tashi kije ki duba ta bata ji dad'i ba" babu musu Azrah ta mik'e ta fita daga d'akin, Mami ta bita da kallo kana ta dawo da duban ta kan T.Vn ta cigaba da kallo..... Tana nan zaune taji sallama cikin d'akin ta juya tana kallan masu sallamar, seta mik'e tana fad'in

"Kae...barka da zuwa mutanen U.S, oyoyo" Wad'anda aka kira da hakan suka k'arasa cikin d'akin, Hajiya Atine tace

"Yawwah barka dae Hajiya.." Suka k'arasa suka zauna, Meemarh da Meemee suka gaesa da Mami sannan suka nemi waje suka zauna, Mami da Hajiya Atine suka cigaba da hira da alama akwae sabo sosae a tsakaninsu, Mami ta kalli Hajiya Atine tace

"Kinga yadda kika yi wani fresh kuwa?, meye sirrin?" Hajiya Atine ta kalli su Meemarh da kowaccensu hankalinta na kan waya tace

"Kuje ku gaeda Yakumbon kafin na k'araso" ta fad'a dae_dae lokacin da Fawaz ya shigo cikin parloun, ya kallesu yace

"A'ah yau kune a gidan namu?" Sukayi murmushi sannan ya maeda dubansa ga Hajiya Atine yace

"Barka da wannan lokaci Ummi" Hajiya Atine tace

"Barka dae Fawaz, ka raka k'annen naka d'akin Yakumbo, yanzu zan k'araso nima" Yace

"Ohk" dukka suka mik'e sukayi gaba Fawaz ya rufa musu baya zuwa sashen Yakumbon...... Da sallama ta shiga d'akin, Buhaesa da fitowarta daga d'aki kenan ta kalli me sallamar kana ta d'auke kae, ta k'arasa ta zauna kan kujera, Yakumbo ta amsa sallamar sannan ta d'ora da fad'in

"Lale da kishiya ta" d'an murmushi kad'an Azrah tayi ta k'arasa ta nemi k'asan kujera ta zauna sannan tace kanta a k'asa

"Barka Yakumbo, ya jikin?" Yakumbo tace

"Jiki Alhamdulillah, ciwo ne dae daya zama na jiki kinsan yanayin shekaru" seta sake yin murmushi kawae tace

"Allah ya k'ara sauk'i"

"Ameen" Yakumbo ta fad'a tana kallan Buhaesa tace

"Kije ki kawo mata abin sha" Buhaesa ta zu6uro baki tana fad'in magana k'asa k'asa, Yakumbo ta rik'e ha6a tana fad'in

"Iyeee, toh ko dukana zakiyi ne en nan?" Bata ce komae ba ta mik'e ta k'arasa zuwa inda fridge yake ta bud'e ta d'akko lemo da ruwa ta k'araso ta ajje da sauri a gaban Azrah kana ta wuce d'aki ba tare da tace komae ba, Yakumbo ta bita da kallo a ranta tana tunanin ko lafiya?, Sallamar su Fawaz ce ta katse mata tunanin da take, ta amsa sallamar tasu, Fawaz yace

"Aunty Azrah ashe kina cikin gidan" seta d'ago ta kalleshi kana ta maeda kanta k'asa tace

"Ehh"

"Azrah!!!" Meemarh ta fad'a da mad'aukakin mamaki akan fuskarta, Azrah ta d'ago tana kallan wadda ta kira sunan nata, se tayi kasak'e tana kallan ta, Meemarh ta k'araso da sauri tana fad'in

"Ya na ganki anan? Yakumbo tace

"Aou kinji wani ikon Allahn kuma, ina shirin gabatar muku da matar yayan naku, ashe ma ku kun santa!" Meemarh ta kalli Yakumbo jin kamar tayi wani yare se kuma ta maeda dubanta kan Azrah da alamar tambaya a fuskarta, Azrah tayi k'asa

Please Login or Register in order to submit comment