Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take masa girki na fad'a miki, yanzu bansan yadda zanyi wannan shegen yaron nata yaci wani abun daze fito daga hannu na ba, ni yanzu ya zanyi sa'adatu ta riga ta zame min k'arfen k'afa.." Kanta ne ya sake sarawa jin abinda Mamin ke fad'a, a hankali a daddafe ta tafi d'akin ta, bata san kuskuren data aekata ba na k'in tsayawa taji k'arashen zancen ba, haka ta koma cikin d'akin kawae ta fashe da kuka tana mamakin halin d'an Adam, abin ya d'aure mata kae sosae ace Mami ce ke fad'ar abinda taji yanzun, ita kanta idan da wani ne ya fad'a mata wannan zancen ba zata ta6a yadda ba, cikin k'ank'anin lokaci zazzab'i me zafi ya rufe ta, taja blanket ta rufe jikin ta sannan ta janyo wayar ta ta kira Dad, cikin rashin sa'a taji wayar a kashe, kawae seta k'ara fashewa da kuka ta rasa abin yi, tana nan zaune Adnan ya dawo daga makaranta ya shigo d'akin da gudu yana fad'in

"Mom kiyi sauri kizo inji Ammi" Mom ta rik'o hannun sa tana kallan sa cike da k'auna tana jin yadda tausayin sa ke sake lullu6e ta dan ita kad'ae tasan yadda take ji a jikin ta, cikin k'arfin hali tace

"Jeka kira min Ammin, ka fad'a mata bani da lafiya" rau rau yayi da idanun sa yace kamar ze saka kuka

"Mom baki da lafiya?" jinjina kae tayi sannan ta sake fad'in

"Maza jeka kira min ita" seya saki hannun ta sannan ya fito daga d'akin zuwa parlourn ya kalli Ammi dake zaune yace

"Ammi Mom tace ki shigo" kallan sa tayi kafin tace komae ya maraeraece fuskar sa yace

"Bata da lafiya fa, tace ki shigo" ya fad'a yana jan hannun ta, seta mik'e kawae tabi bayan sa har zuwa bedroom d'in Mom, da sauri Ammi ta k'arasa tana fad'in

"Subhanallahi ashe baki da lafiya?" Jinjina kae kawae Mom tayi wasu zafafan hawaye na zuba akan kuncin ta, ta sanya hannun ta ta kamo hannun Ammi tace bayan ta d'an tashi zaune, Adnan ya samu damar shigewa cikin jikin ta ya kwanta, da d'ayan hannun ta ta saka ta rik'e shi sannan tace tana kallan Ammi

"Nayi k'ok'arin kiran Abban Adnan amma na kasa samun shi, ke kad'ae ce nake tunanin zaki iya yi min wannan alfarmar, kin san iyaye na da en uwa na basa kusa saboda haka nake son na rok'eki wata alfarma" ta d'an dakata sannan ta cigaba da cewa har lokacin Ammi kallan ta take

"Ashe bansani ba Hadeeza ba k'auna ta ni da Adnan take ba, ban tashi sani ba se yau, yau d'in da nake tunanin itace rana ta ta k'arshe a duniyar nan" Ammi ta rik'e baki wasu k'walla na taho mata tace

"Ki bar fad'in haka ae cuta ba mutuwa bace, zaki tashi In Sha Allah" Mom tayi wani yak'e sannan tace

"Ayyah ke kuwa, ni dae don Allah ga amanar Adnan na baki akan kula da abinda zeci, kiyi min wannan alfarmar koda ita kad'ae ce alfarmar k'arshe da zaki min bayan na bar duniya, kiyi k'ok'arin sanar da Abban sa abinda be sani ba don Allah, har abada kada a chanjawa Adnan me masa girki dake kad'ae na yadda, dake kad'ae na amince, sannan shima Adnan d'in ki sanar dashi wacece Hadeeza daga zarar ya mallaki hankalin kan sa, kimin wannan alfarmar" Ammi kam ta kasa furta komae banda kuka babu abinda take yi, tana jin al'amarin kamar a mafarki, Mom ta shafa kwantacciyar sumar kan Adnan tace

"Kada ka ta6a cin abincin wata matar a gidan nan idan ba Ammi ba kaji koh?" shi dae Adnan jinjina kae kawae yayi yana sake lafewa jikin Mom d'in tasa, Mom tace a hankali

"Me nace?"

"Kince kar naci abincin kowa in ba na Ammi ba"

"Dats my boy" Mom ta fad'a tana rungume Adnan d'in sosae a cikin jikin ta k'walla na zuba akan sumar kan sa, daga nan kuma ta sake shi ta koma ta kwanta a hankali, se kuma ta fara tari kamar wasa, Ammi ta mik'e dan samo mata ruwa Mom ta rik'o hannun ta tana girgiza mata kae, a hankali Ammi taga bakin Mom na motsawa kamar me karanta wani abun, daga baya kuma taji ta saki hannun nata, Mom passed away, dawowa da baya Ammi tayi tana kallan Mom d'in wadda ko ba'a fad'a ba tasan shirun nata me yake nufi, ta kalli Adnan da har lokacin yana zaune kan gadon yana kallan Mom, bata san sanda ta fashe da wani marayan kuka ba, tausayin Adnan na lullu6e ta, shi kam ta6a ta yake yana fad'in

"Mom ki tashi mana" ya fad'a yana jijjiga ta se dae bata san yana yi ba...

( Shikenan fa rayuwar, ciwon kwana d'aya amma yanzun babu Mom a duniyar, Allah yasa mu cika da kyau da imani )

.. Mutuwar Mom ta girgiza duk wanda yaji labarin ta daga en uwa har abokan arzik'i, Dad ma ya jiga ta sosae kafin ya hak'ura ya dangana, hatta Mami seda taji mutuwar amma idan ta tuna mutuwar ta na nufin cikar burin ta se taji wani sanyi na ratsa ta, idan kaga yadda Mami ke nunawa a zaman makokin se kace wadda uwar ta ce ta rasu, haka zaka ga ta rungume Adnan tana kuka, shima yana yi, tayi wani iri da k'yar ma take amsa gaesuwar mutane, shi kam Dad har tausayin ta yake ji idan ya tuna yadda suka shak'u yasan dole ne taji mutuwar, nan kuwa be san duk pretending bane, da en uwan Mom suka zo tafiya suka nuna suna son tafiya da Adnan, Dad be amince ba dan shi kad'ae ne d'an sa, haka suka koma k'asar su babu Adnan d'in ba dan sun so ba, Seda aka share makoki sannan Ammi ta fara tunanin yadda zata sanarwa da Dad maganar da Mom ta fad'a mata amma gaba d'aya ta rasa k'warin gwuiwa, dan yadda Mami ke nunawa ko zata daka tsalle ta rantse babu wanda ze yadda da abinda zata fad'a d'in, da dae taga babu sarki se Allah kawae seta samu Dad da zancen cewar Mom tace mata kafin ta rasu kada a ta6a samawa Adnan wata er aekin, haka zalika tace bata yadda da wasu mutanen ba ya taemaka ya kula da d'an ta kada ya bari ya ta6a cin abincin wani a cikin gidan, ga mamakin ta se taga Dad d'in ya amince da abinda ta fad'a d'in, se taji data sanin k'in fad'a masa aenahin zancen, yanzu kuma babu damar ta koma baya hakan zesa yayi ko kwanto a kanta, Dan haka kawae seta hak'ura.. A cikin kwanakin ne kuma Adnan ya shiga shekaru 10, farin ciki wajen Mami kamar tayi mene, nan ta sanarwa da Dad ya kamata su sami k'arin er aeki wadda zata dinga tayata aeki, anan ya nuna mata k'in amincewar sa, dan haka kawae seta hak'ura da taga ko maganar baya so ayi, haka suka sake komawa wajen Malam, mutumin da yayi musu aeki akan Adnan kenan, chanji na farko da aka fara samu akansa shine lalacewar karatun sa, ya tsani duk wani abu daya shafi karatu, mamaki ya kama Dad ganin da ba k'aramin son karatu ke gare shi ba, haka dae ya tashi tsaye sosae akan sa, da k'yar da fad'a haka yake karatun, ita kam Mami se dae ta dinga cewa yayi hak'uri ae yaro a hankali ake bi dashi bada fad'a ba, a cikin tsukun ne kuma Mami ta fahimci tana da juna biyu, zo kaga farin ciki akan hakan, shima Dad yayi farin ciki sosae, haka dae ta cigaba da raenon cikin ta lokaci guda kuma tana shagwa6a Adnan kamar me, abu d'aya ne ta kasa fahimta shine duk yadda suke da Adnan baya ta6a cin abincin ta kome zata yi kuwa, haka ta shashantar da hakan har dae ta haefi D'an ta namiji wato Fawaz, wani irin k'aunar sa ce ta daban a cikin zuciyar Adnan, k'aunar data kasance daga Allah ne, Mami tayi mamakin yadda taga Adnan d'in ke k'aunar Fawaz.. Haka dae rayuwar ta cigaba da tafiya Mami na bawa d'an ta tarbiyya yayin da tun Adnan ke yaro ta nuna masa babban mutum ba kowa bane in dae bashi da arzik'i, ko yana da arzik'in ma ya nuna masa ya fishi, da farko yana gaeda Ammi da duk wani wanda ya girme shi amma daga baya duk ya watsar da hakan, chanjin Adnan d'in ba k'aramin mamaki ya bawa Dad ba dan haka har kiran sa yayi ya masa fad'a sosae. Tun yana junior secondary school aka kawowa Dad k'arar sa akan kama shi da akayi da wasu abokan sa suna shan taba, ranar kuka ne kawae Dad beyi ba, yayi duk iya k'ok'arin sa wajen bawa Adnan tarbiyya amma da abinda ze saka masa kenan? Dad yayi fad'an yayi dukan amma duk a banza Adnan be rage abinda yake yi ba, kuma ba'a dena kawo masa k'arar sa ba har lokacin, sema abinda yayi gaba, dan kullum idan be sha tabar nan ba ji yake yi kamar ya rasa wani abu muhimmi a rayuwar sa, girman kae kuwa se wanda ya k'aru, be san darajar kowa ba daga k'anana har na gaba dashi baya ragawa kowa, be san banbancin dake tsakanin magana da iyaye manya da kuma sa'annin sa ba, yadda yakewa kowa magana haka yake yiwa Dad har Mamin ma be raga mata ba, se dae dan kawae yafi jin maganar tane akan kowa, ita tana iya tank'warashi cikin k'ank'anin lokaci, mahaefiyar sa kuwa bana jin tayi shekara d'aya da rasuwa ya manta da rayuwar ta gaba d'aya, dangin mahaefiyar sa kuwa suma tun rasuwar babu wadda ta sake zuwa wajen sa ko ta neme shi a waya, shima kuma be nema ba, ya rik'i Mami tamkar itace uwar sa itace uban sa harma da dangin sa gaba d'aya, yafi jin maganar ta akan ta kowa, ya fara shan shisha ne sanda suka shiga senior school ranar da wani d'an cikin team d'in su yaja shi zuwa wani club, daga nan kuma haja ta bud'e, tun daga wannan lokaci Adnan ya rik'i shan taba da shisha kamar ibada, sauran kayan maye ne dae kawae baya sha, amma ragowar abokan sa duk suna sha, anan ne ma ya had'u da Irfan suka cigaba da shek'e ayar su, yayinda a gefe guda kuma Sameer abokin sa tun na primary kullum cikin fad'a yake masa haka Dad ma amma kullum kamar ana k'ara tunzura shi, musamman kuma daya fahimci shan tabar da shisha harma da zuwa club d'in da yake yi be damu Mami ba se hakan ya k'ara masa k'aemi, dan sau da dama Mami ta san inda zeje abinda kawae take fad'a masa shine kada ya dad'e, Dad kuwa kullum cikin addu'a yake masa dan yaga kamar fad'an baya shigar shi, sanda suka gama secondary school Mami ta nemi alfarmar Dad akan yakae Adnan k'asar waje yayi University a can, Dad ya nuna sam sam be amince ba, ya lafiyar kura dama bare tayi zawo, yana gaban su ma ya aka cika ballantana ya bar gaban su, haka Mami ta hak'ura aka sama masa University anan cikin Kano yayi karatun sa, sanda ya shiga Universityn seya sake had'uwa da abokae masu bud'ad'd'un idanu wad'anda ke jansa club akan suje su huta da mata, shi kam besan dalilin da yasa tun tashin sa wata halitta mace bata ta6a burge sa ba, ballantana harya kae ga neman ta, hakan ne yasa basu wani d'ore da wad'annan abokan ba, suka cigaba da harkar su da Irfan dan shi baya tursasa shi akan mata, sedae ya dinga nuna masa alfanun mace a tare dashi, tunda ya karta masa wani warning shikenan ya rabu dashi kawae, a 6angare guda kuwa wataran idan Ammi ta ganshi se dae kawae tayi kuka harta gaji ta godewa Allah, ga dae girman ya same shi amma babu hankalin da ze d'auki maganar da zata fad'a masa, dan a lokacin ko gaesuwa bata had'a ta dashi se dae yaci abinci kawae ya mik'e, se dae kuma wani lokacin idan yaga dama ya gaeda ta shima kamar yana gaeda sa'an sa, ga kuma wata shak'uwa dake k'ara shiga tsakanin sa da Mami, hakan ba k'aramin sake tada mata da hankali yake yi ba amma babu yadda ta iya haka ta kama bakin ta tayi gumm se dae tana kula da duk wani motsin Mamin tunda kusan a gidan take wuni, akwae lokacin da Mami kamar ta fahimci tana zargin ta sanda ta fara mata magana akan er aekin da Dad yak'i amincewa a kawo dan a rage mata aeki, Ammi tace

"Ki bar komae a hannu na in dae batun girki ne zan iya"

"Toh shikenan kuma ni Adnan baze dinga cin abin hannu na ba kullum se naki? Hakan namin ciwo fa" Mami ta fad'a, Ammi ta kalle ta sannan tace

"Meyasa hakan ze dame ki?" waskewa Mami tayi ta hanyar fad'in

"A'ah a'ah babu komae" daga nan kuwa Mami ta kama kanta dan kada Ammin ta gano ta.. Haka rayuwar ta cigaba da tafiya Mami na sake nuna kamar tafi kowa k'aunar Adnan ne, yayin da Adnan ke matuk'ar k'aunar d'an uwan sa baya son wani abu da ze ta6a shi, tunda yake shan abubuwan sa baya ta6a shigo dasu gidan kuma baya bari Fawaz ya gane yana shan wani abun, hakan na nufin yasan abinda yake aekatawa ba dae_dae bane amma ya kasa denawa bema san yadda za'ayi ya dena d'in ba, sema kullum soyayyar su dake k'ara zaunar masa a ransa...



__A 6angaren Abba kuwa a ranar da Ammi ta haehu ya dawo gidan da yamma, a parlour ya tadda Ummi na kuka magashiyyan kamar wadda akama mutuwa, Abba yace

"Subhanallahi, meya faru?" Ummi ta cigaba da kukan sannan tace cikin kuka

"Lek'a kaga cikin d'akin nan, d'azun nan Fatima ta haehu a ciki, tana haehuwa ta d'auki jinjirin cikin jinin haehuwa ta fice dashi daga gidan nan, wae dama bata son ta haehu da kae fad'a maka ne bata yi ba, kuma ka bi ta da saki dan ba zata sake dawowa cikin gidan nan ba, ka ganni babu yadda banyi da ita akan kada ta tafi ba amma ta nuna min ni ba kowa bace, babu wanda ma ya isa ya hanata abinda tayi niyya koda kae ne kuwa, kaganni tunda ta fita na kasa tashi mamaki da tsoron al'amarin Fatima ya kasa saki na" baya Abba yayi kansa ya wani juya masa sannan cikin sakanni ya fara wani irin tari, da sauri Ummi ta mik'e tana fad'in

"Na shiga 3 ni ennan" ta fad'a tana k'arasawa ta d'auko ruwa ta bashi ya sha ya koma sauke ajiyar zuciya, toh wannan dae shine mafarin rashin lafiyar Abba wadda ta janyo har seda aka fitar dashi waje saboda ciwon zuciya daya kama shi, gashi dae kusan kullum cikin tunanin Fatima da abinda ta haefa yake amma ya kasa sakawa a bincika masa inda take, koda kuwa gidan iyayen ta ne, rayuwar Abba da Ummi ta zama kusan gaba d'ayan ta a k'asar waje suke yin ta saboda jinyar Abba da ciwon sa kan tashi lokaci zuwa lokaci, seya zamana ma Twins suka koma wajen kakar su ta wajen uwa da zama, se idan Ummi zata dawo k'asar ne se su koma gidan su, itama kuma ba wani dad'ewa take yi ba kota dawo d'in dan bata wuce sati 1 take komawa, shi kam Abba gaba d'aya ma rayuwar sa ta koma can da zama sedae matar tasa da 'ya'yan nasa su ziyarce shi sannan su dawo Nigeria.....



*CIGABAN LABARI*
✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION44*




___Abba ne ya fara bada labari tun daga farko sannan Ummi ta kar6a ta d'ora da labarin tana kuka tana fad'ar irin abubuwan data aekata, daga nan kuma Abbu da suka shigo lokacin da Abba ya fara bada labari shi kuma ya k'arashe labarin. Shiru d'akin ya d'auka na tsawon mintuna kowa da abinda yake sak'awa a ransa, masu alawadae da halin Ummi nayi haka ma masu kuka suna yi, a hankali ta mik'e cike da sassarfa zuwa inda Ammin take, kanta na wani irin sarawa har hakan ya janyo mata jiri wanda ya sanya tana dab da k'arasawa wajen Ammin ta d'an yi baya kad'an, da sauri ya kae hannun sa yana shirin tare ta se kuma ta mik'e akan k'afafun ta, ya shafa sumar kansa yana cigaba da kallan ta, jikin Ammi ta fad'a ta fashe da kuka me cin rae, itama Ammin kukan ta saka ta rungume d'iyar ta ta cikin jikin ta, babu wanda ya tanka musu koya hana su kukan, suka cigaba da kallan su cike da tausayawa, se daga baya Azrah tayi shiru a jikin Ammin tana jin d'umin mahaefiyar ta wanda aka hana ta ji tun ranar haehuwar ta, lallae tayi rashi tayi babban rashi ma kuwa, dan kuwa yanzun wata irin nutsuwa taji tana saukar mata, se yanzu ta gane ashe ba iyayen ta ne Sanadin kaddarar ta ba, KUD'I shine SANADIN KADDARARTA, akan kud'i aka yiwa ita da mahaefiyar ta wannan mummunan aekin, akan kud'i aka raba ta da jin d'umin iyayen ta, aka rabata dasu tun ranar da aka haefa ta, seta lumshe idanun ta wasu k'walla masu d'umi na zubowa akan kuncin ta, sunfi minti 3 a haka sannan Azrah ta mik'e a hankali ta k'arasa wajen Abba shima ta rungume shi, ya kae hannun sa idanun sa ya goge k'wallar data zubo masa, a hankali ya furta

"Allah yayi miki albarka en nan" yana sakin ta ta koma kusa da Ammi ta sake kwantar da kanta akan kafad'ar Ammi, Ammi ta lumshe idanun ta tana jin wani matsanancin farin cikin da bata ta6a tsintar kan ta a ciki ba, Abba ya kalli Ummi dake kuka magashiyyan ta kasa koda d'aga ido ne ta kalli mutum 1 dake cikin d'akin, Twins d'in ta na gefe suma kukan suke yi suna mamakin wannan hali na mahaefiyar su, abin mamakin ma da kanta ta tonawa kan ta asiri, wannan wace irin rana ce a gare su sukam? Kowa kallan ta yake cikin sake yin tirr da alawadae da halayen ta, Ammi kuwa har lokacin tak'i d'ago kae ta kalli Ummin koda sau d'aya ne, Mami na gefe gumi ya gama jik'a ta sharkaf gaba d'aya tsoro da rashin gaskiya ya gama bayyana a tattare da ita, tana kuma tsoron kada fa allura ta tono garma, kada Ummi ta tona mata asiri, ita kam Ummi gaba d'aya ta kanta take yi ba takan kowa ba, a hankali taja k'afafun ta da suka mata nauyi ta isa gaban Abba tace har lokacin tana kuka

"Don Allah kayi hak'uri, Fatima kema ki yafe min, wallahi nayi nadama nayi nadama don Allah ku yafe min" D'aga mata hannu Abba yayi alamar ta dakata yayin da Ammi ta d'ora hannun ta akan Azrah har lokacin bata kalli Ummi ba, Abba yace

"Kin cuce ni Habeeba, kin cutar da mutane da dama wad'anda basu ji ba basu gani ba, yanzu baki ji kunya ba akan kishi ki raba 'ya da uwar ta ranar data haefe ta? Ki hana su jin d'umin junan su? Wannan wace irin zuciya dake mara tausayi? saboda haka na gama zama dake har abada, kije dan kanki, sakayya kuma itama kije zaki ganta ko da bamu had'a ki da Allah ba, saboda haka kije na sake ki saki 3" K'walla k'ara Ummi tayi cikin ficewar hayyaci ta zube a wajen, babu wanda yace komae, se Twins da suka nufi mahaefiyar tasu cikin tsananin tashin hankali, ganin kamar ma bata motsi ya sanya Meemee fita da gudu ta kira nurses ita kuma Meemarh ta fashe da kuka tana fad'in

"Don Allah Ummi ki tashi, mun shiga 3" A haka nurses d'in suka zo suka fitar da ita kamar matacciya, kuka kawae Mami ta fashe dashi cikin rashin sanin abinyi da nadama, yau ga asirin aminiyar ta ya tonu a baenan nasi, a gaban 'ya'yan ta, babu yadda suka isa su iya, ta k'ara fashewa da kukan ta, seda aka fitar da itan sannan Abba ya kalli Azrah da har lokacin take kwance jikin Ammi yace

"Daughter kinyi aure ne?" k'asa tayi da kanta ba tare da tace komae ba, Dad yayi murmushi kana yace

"Albishirin ka?"

"Goro" Abba ya fad'a yana k'ak'alo murmushi dan har lokacin be fita daga shock d'in abinda ya faru yanzun nan ba

"Toh ni da kae surukae ne, dan kuwa Adnan ke auren Azrah"

"Wowww wowww, abokina da gaske?" Abba ya fad'a cikin matuk'ar farin ciki, Dad yace

"K'warae ma kuwa, ae ni bansan ashe da 'yata nake tare ba se yanzu" Abba yace

"Amma naji dad'i sosae, nayi farin ciki, amma ya akayi hakan ta kasance ?" Dad yayi murmushi kana yace

"Kada ka damu, zamu k'arasa maka labarin" Abba ya kalli Azrah sannan ya kalli Don yana mik'a masa hannu yace

"Naji dad'i sosae Son.. " ya fad'a yana rungume Don... Yakumbo ta kalli Dad tace

"Toh mu semu tafi koh?" Dad yace

"Ehh zamu iya tafiya, kae Adnan ka bar musu ita anan zuwa wani lokaci" ya fad'a yana kallan Fawaz dake kusa da Mami yace

"Ku wuce muje" haka kawae ya tsinci kan sa da satar kallan inda take zaune tana kallan Ammi, ita sam bata lura dashi bama dan tun d'azu ta manta da rayuwar sa, Ammi ce ta lura da tsayawar da yayi ta kalli Azrah tace

"Ko zaki tashi ku tafi?" Ammi ta fad'a ba dan zata so hakan ta kasance ba, tura baki Azrah tayi bayan ta saci kallan inda yake tsaye kamar me amsa kiran waya tace

"Aena dawo kenan Ammi, ze aeko min da takadda ta ne" k'irjin Ammi ya buga da k'arfi ta cigaba da kallan Azrah sosae yayin da Azrah tayi k'asa da kanta kawae, wani murmushin gefen baki ne wanda be shirya masa ba ya su6uce masa, kawae seya fice daga d'akin,

"Azrah kece kika nemi sakin ?" Ammi ta fad'a cike da tsoro, ta jinjina kae har lokacin bata kalli Ammi ba, Ammi tace

"Yah salaam, kuma ya amsa miki?" tura bakin ta tayi cike sa sakarci tace

"Yamin banza fa Ammi" komawa Ammi tayi ta jinjina da gadon da take kae, komae rashin son da baya mata ba zata so erta k'arama kamar Azrah tayi zawarci ba, duk dama ita yanzu ta lura da wani babban al'amari dake cikin idanun Don d'in, kawae dae zata cigaba da musu fatan Allah ya daedaeta tsakanin su.. Ummu (Maman Zarah) ta kalli Ammi tace

"Toh Ammin yara mu zamu tafi, se Allah ya kaemu gobe"

"Toh Allah ya kaemu Ummu, ni bana fatan ma mu kae goben"

"Toh ya za'ayi" Ummu ta fad'a tana mik'ewa kafin tace

"Inaga zuwa gobe za kiji wani bayani daga bakin Abbu" Ammi tace

"Toh Allah ya kaemu" daga haka Ummu ta fice daga d'akin, ya rage daga Azrah se Ammi, Ammi ta k'agu taji labarin Azrah a k'auyen Kima se dae tasan mahaefin tama zeso yaji labarin, hakan ne yasa ganin baya nan ta hak'ura ta bari idan ya dawo d'in seta basu labarin.. Ranar Azrah gata ga mahaefiyar ta haka ta kwana cikin farin ciki mara misaltuwa, zata iya cewa tunda take a rayuwar ta bata ta6a jin rana me dad'i a wajen ta irin wannan ba....



__A 6angaren su Don kuwa sanda suka fito daga cikin asibitin zuwa compound d'insa se Dad ya kalli Don yace

"Can gidan zaka wuce ko kuwa?"

"Zan fara zuwa gida ne" ya fad'a a hankali, Dad yace

"Ohk kuyi gaba da Fawaz da Yakumbo zamu taho ni da Mamin ku" Kallan Yakumbo dake tsaye a gefe yayi kana ya ta6e baki ya k'arasa ya shige motar sa, Fawaz ya k'arasa ya bud'ewa Yakumbo back seat ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya koma front seat ya zauna, Don ya tashi motar ya fice daga asibitin a hankali, seda ya hau kan titin sannan ya fara sharara gudu kamar yadda ya saba, Yakumbo tace

"Haba kae kuwa d'an nan wannan gudu kamar zamu tashi sama? Kaewa Allah da Annabin sa ka rage wannan gudun" be ko kalle ta ba koya nuna alamar yaji abinda tace ba ya cigaba da gudun sa, Fawaz kam se dariya yake k'asa k'asa, se can yace

"Bhai ka d'an rage gudun tsoro fa take ji" kallan Fawaz yayi kana ya cigaba da driving d'in sannan yace kamar baya son

Please Login or Register in order to submit comment