Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa, nan ma dae idanun sa suka sake sauka akan Ammin, toh ko dae da gaske ita d'in yake gani? Ba mafarki yake ba? Ba irin mafarkan daya saba yi bane, a hankali ya sake furta

"Fatima kece?!!" Runtse ido Ummi tayi sannan ta bud'e cikin d'aga murya ta fara fad'in

"Qarya ne ba Fatima bace wallahi, wlh ba ita bace, babu ma ta yadda za'a yi ace fatima ce, ni da malam yace min in dae ta yadda abinda ta haefa da hannun ta ba zata ta6a dawowa hayyacin ta ba? Kuma an tabbatar min da ta yadda abinda ta haefa d'in da kan ta, ya kuma zaka ga wata mata yanzu kace itace? Bari mana, wlhi ko sutura ta da dukiya ta zata k'are sena tabbatar maka wannan ba fatima bace" tunda ta fara magana Don ke kallan ta without even blinking, haka en d'akin ma gaba d'aya kallan ta suke yi, Meemarh da Meemee kuwa gaba d'aya sun kasa fuskantar inda al'amarin ya dosa musamman da suka ji uwar data haefe su na ambatar Malam, shin meke shirin faruwa ne? Alhaji Abbakar ne ya kalli Ummi zuciyar sa na bugawa cike da tsoran kalaman ta yace cikin sarewa

"Habeeba, me kike k'ok'arin fad'a ne?" Ummi tace

"Ehh cewa nayi k'arya ne ba fatima bace, wlh ba ita bace, malam yace ba zata ta6a dawowa hayyacin ta ba matuk'ar ta jefar da abinda ta haefa da hannun ta" Yakumbo ce ta d'auki salati hadda sallallami se dae ta kaasa d'ora komae daga hakan, mamakin abinda taji daga bakin Ummin ya kusa kashe ta a zaune, dafe kansa Abba yayi yana jin inama inama ze farka daga wannan mummunan mafarkin, a 6angare guda kuma me dad'i?, Dad dake gefen sa yace yana kallan yadda yake numfashi da k'yar

"kasan dae baka da lafiya, so ka bari mu d'auki komae a hankali, kada ka k'arawa kan ka wani ciwon" Abba ya bud'e idanun sa a hankali yace

"Na d'auka ko mafarki nake yi" Dad ya girgiza kae kana yace

"Noo, this is reality, ka kwantar da hankalin ka komae zezo da sauk'i In Sha Allah, ka tsaya ka mana bayanin abinda ke faruwa, me Habeeba take fad'a? Sannan wacece wadda ka kira da Fatima a wajen ka?" Abba ya sauke idanun sa akan Ammi, yana sake tantama wa zuciyar sa ita d'in ce? Ko ba ita bace, Mik'ewa zaune Ammi tayi tana sake runtse idanun ta saboda tsananin sara mata da kanta yake yi, a hankali ta mik'e tsaye, Mami ta mik'e tana rik'e da ita ganin yadda take layi, Mik'ewar da Mami tayi se idanun ta suka sauka akan Don da har lokacin kallan Ummi yake yi kamar me tunani ko nazarin wani abun, ta kauda kanta tana tuna case d'in su, Allah dae yasa be yadda da abinda aka fad'a masa ba, koda yake tama san babu yadda za'ayi ya yadda sema Azrah d'in da zata sake kashe kan ta, Ammi ta k'arasa tana kallan Ummi a hankali ta kamo hannun ta, Ummi ta fizge hannun ta tana bin Ammi da wani banzan kallo, zuciyar Ammi na bugawa da k'arfin gaske tace

"Ina babyn dana haefa?, ina take?, don Allah ki sanar dani inda take zuciya ta tana dab da tarwatsewa" Ammi ta fad'a hawaye na zuba a fuskar ta, Ummi tace

"Karki tambaye ni maganar banza mana, keda kan ki fa kika yar da ita sannan zaki zo ki tuhume ni, ke wlh ma ba kece fatima ba, fatima ta dad'e da haukacewa" Ummi ta fad'a tana zubewa a k'asa ta fashe da wani matsanancin kuka, Meemarh da Meemee kawae fashewa suka yi da kuka suna fatan inama ace mafarki ne wannan suke yi? Me Ummin su ta aekata haka ne?, Dad kuwa girgiza kae kawae yayi cikin takaecin halin matar abokin nasa, Yakumbo dake kusa da ita tace

"Kae Abbakar zoka fitar mana da wannan matar, duk yadda akayi muguwa ce akwae abinda ta k'ulla wanda baku sani ba" Ammi ta cigaba da kallan Ummi tunda ta fara magana take rarrabe abinda take fad'a, kamar ji tayi tana cewa ta jefar da er data haefa da hannun ta fa? Me yake shirin faruwa? Kawae se tayi baya hannun ta dafe da kanta tayi taga taga zata fad'i, Abba ya mik'e dan ya gama tabbatarwa yanzu kam ba mafarki yake yi ba, a k'asa Ammi ta zube har lokacin hannun ta na dafe da kanta, Dad yace yana kallan Mami

"Maza kamata mu wuce asibiti yanzun nan" Babu musu Mami ta taemakawa Ammi suka fita zuwa compound d'in gidan, tuni drivers suka taho ganin mutanen da zasu hau motar na da yawa, suka fara bud'e motoci, Yakumbo ta mik'e tana kallan su Meemarh da suka rik'o Ummi data zube a wajen, ko kallan su Yakumbo ba tayi ba ta fice daga d'akin, a haka dae suma suka samu suka d'aga Ummin da har lokacin kuka take tana surutae kamar zararriya, suma kansu kuka suke yi duk da basu san akan aenahin abinda ake magana ba, kawae dae duk wasu alamomi sun nuna Ummin tasu bata da gaskiya.. Sanda suka fita ya rage saura shi kad'ae, yau kam abubuwa da dama se faruwa suke yi wad'anda ke neman saka wa k'wak'walwa da zuciyar sa su buga, meya kamata ya yadda dashi? Me wannan matar ke fad'a? In dae ya fahimta yaji dae_dae kamar abinda matar nan ke fad'a yana kama da abinda aka fad'a musu akan Azrah, saboda wannan sabon abu ne, tunda yake be ta6a jin kalar labarin ba se a kanta, toh kodae hakan ne? Abinda yake zargi gaskiya ne?, Mik'ewa yayi da sauri, yadda kansa ya sara masa ya sanya shi tilas ya dakata, wajen minti 1 ya d'auka a tsayen seda yaji dama dama sannan ya fito daga d'akin ya k'arasa ya hau motar sa ya fige ta ya bar gidan gaba d'aya, yana gama parking ya fita daga cikin motar ya shige cikin gidan, kae tsaye ya wuce upstairs da sassarfa, a k'ofar d'akin ya tsaya, bayan wajen second 3 ya tura k'ofar d'akin dake a ture, a zaune take se dae ta jinginar da kan ta kamar me bacci, gefen ta ledar data had'a kayan ta ne, ji tayi kamar an turo k'ofa dan haka ta d'ago kan ta da idanun ta da suka yi ja ta kalli k'ofar, da sauri ta gyara zaman ta ganin me shigowar, se dae tana mamakin ganin sa cikin d'akin na ta, be san dalilin da yasa ya tsinci kansa da tambayar kansa dalilin daya sanya idanun ta suka yi ja ba, kuka tayi ko kuma ciwon ido take yi? Ya tambayi kan sa, gaba yayi yana kallan yadda ta kasa d'aga ido ta kalle shi, yace fuskarsa a had'e yana sake kallan ta

"Tashi" ba tare data d'ago kanta ba ta mik'e, yana bayan ta hakan na nufin kenan nufin sa tayi gaba? Seta dakata kawae tayi shiru tana fatan tsoran nan nasa ya fice mata daga zuciyar ta kafin ta bar gidan, muryar sa ta sake jiyowa har lokacin ba fara'a yana fad'in

"Muje nace koh?" lumshe idanun ta tayi sannan ta saka hannu ta share k'wallar dake idanun ta kana taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta juyo, kusancin da taga sun samu sanda ta juyo d'in ne ya sanya tayin baya kad'an tace

"Ina buk'atar takardar saki, zan koma k'auyen mu" ta fad'a ba tare data kalle shi ba, shi kam tunda ta fara maganar yake kallan ta, se a lokacin ya gane abinda yasa tun farkon ganin ta yaga tana masa kama da wata fuska, ashe fuskar Abba ce, shi kam yana da tabbacin abinda yake zargi gaskiya ne, jin shiru ya sanya ta d'aga ido dan ganin koma dae ya bar mata d'akin ne, karaf idanun su suka shige cikin na juna a karo na farko kenan, da sauri ta janye idanun ta saboda yadda taji k'irjin ta ya buga da wani irin k'arfi, kenan yaji abinda tace amma ya mata shiru? Ta sake had'e rae sannan ta sake cewa

"Ina son zan koma k'auyen mu ne"

"Toh akwae wanda ya hana ki ne?" ya fad'a har lokacin yana kallan ta, seta k'arasa kan gadon ta d'auki jakarta ta sannan ta fara k'ok'arin juyawa jikin ta na er rawa amma ta maze, da k'arfi ya sanya hannun sa ya janyo ta ta dawo da baya sannan ya juyo da ita, runtse idanun ta tayi tana jin kamar ta fasa ihu, ya zuba mata jajayen lumsassun idanun sa yace da muryar sa data bayyana 6acin ran da yake ciki

"Kada ki k'ara kuskuren nan, so kike ki kara dani? Toh kada kiyi wannan kuskuren dan ba zaka kici nasara ba" ya k'arasa fad'a yana sakin ta, mamaki ne ya kamata ta d'auka idan yaji hakan zefi kowa farin ciki tunda dama tasan abinda yake buk'ata yaji daga bakin ta kenan, muryar sa ta sake ji yace yana yin gaba

"Wuce muje.." yadda duk ya cika d'akin da kwarjinin sa da tsoran sa ne ya sanya ta yin gaba tana share k'walla, a haka har suka isa compound d'in gidan, ta riga da tasan ya tsani had'a wajen zama da ita dan haka seta tsaya daga gefe ganin ya nufi motar sa, ganin ta tsaya ya juya ya watsa mata wani kallo daya sanya ta taho har tana shirin yin tuntu6e, ya shiga driver seat ya zaune, daga inda yake zaune ya saka hannu ya tura k'ofar me zaman banza sannan ya tashi motar, k'arasowa tayi kamar wata munafuka ko wadda za'a ce mata kett ta gudu, ta shiga ta zauna a d'arare, be kalle ta ba ya cigaba da tsayawa saboda bata kullo k'ofar ba, seda ya gaji dan kansa ya kalle ta yace a fusace

"Wani kike jira ya kulle miki k'ofar?" ita harga Allah mantawa tayi ma gaba d'aya, ta saka hannu ta janyo k'ofar sannan ya tashi motar.. Gudu yake sosae kamar wanda ze tashi sama, ita duk tsoro ma ya kamata amma ta baasar kawae amma fa ita kad'ae tasan yadda zuciyar ta ke bugu, a haka suka k'arasa wani hospital ya shiga yayi parking motar sannan ya fito, binsa tayi da kallo gudun kar ya fad'a mata magana ya sanya ta fito daga cikin motar, yanzu ma be kalle ta ba kawae yayi gaba, ganin haka ya sanya ta yin shiru ta tsaya a jikin motar tana rarraba idanu, dakatawa yayi da tafiyar, daga inda take ta hango hakan, kawae seta cigaba da tafiya harta cin masa... Dae_dae wani waje ta sake ganin ya dakata da yake ta d'an bada tazara tsakanin su ya sanya bata jin me yake cewa sedae taga ya kira waya daga baya kuma ya maeda ta cikin aljihu ya cigaba da tafiya.. Tunda suka doshi wajen ta fara hango mutane fall zaune a bakin k'ofar wani d'aki, Fawaz da shima be dad'e da zuwa asibitin ba ya taso zuwa wajen su yana kallan Don yace

"Bhai, ashe kuna hanya?"

"Ehh yaushe kazo?" Don ya tambaya har lokacin yana tafiya, Fawaz yace

"Ban dad'e da zuwa ba, Aunty Azrah ina wni?" ya k'arasa maganar yana kallan Azrah,

"Alhamdulillah" kawae ta iya fad'a shima ba tare data kalle shi ba, tana mamakin abinda ya kawo su asibiti, ga kuma mutanen da take hangowa a zaune, kawae se taji jikin ta yayi wani mugun sanyi, ta k'arasa ta gaeda Dad da Abba wanda ya bita da kallo tun shigowar ta wajen, Meemarh dake zaune tayi tagumi ta kalla tace

"Meemarh lafiya kuwa?"

"Ehh..toh..." bata k'arasa maganar ba wani likita ya fito daga d'akin ya kalle su yace

'Zaku iya shiga" dukkan su suka mik'e, Yakumbo na kallan Don tace

"Salon dae d'agawa mace hankali, mene na d'akko matar ka kuma? Ae daka barta tunda bata san kan abinda ya faru ba" shi dae be bi ta kanta ba kawae shima ya wuce cikin d'akin, hannun Azrah cikin na Meemarh suka k'arasa cikin d'akin bayan ta gaeda Yakumbo, ita bama ta kula da Mami da keta ra6ewa ba, Ammi dake kallan k'ofar ta kalle su su duka, Azrah ta saki hannun Meemarh ta k'arasa wajen Ammi da sauri tace

"Ammi baki da lafiya ne?, meya same ki?" ta fad'a a jere, Ammi tayi murmushi kad'an tana kamo hannun Azrah tace

"A'ah na warke" seta maeda duban ta kan Abba tace hawaye na zuba daga idanun ta tace

"Ku kira min Habeeba tazo ta fad'a min ina 'ya ta take don Allah, shine kad'ae abinda ze faranta min ba komae ba" Abba ya k'arasa kusa da gadon Anmin yace yana kallan ta

"Ki kwantar da hankalin ki, In Sha Allah zamu ganta, zamu ganta cikin k'oshin lafiya" Ammi ta girgiza kae tana tashi zaune har lokacin hannun ta na cikin na Azrah, ita dae Azrah binsu da kallo kawae take yi dan bata gane akan maganar da suke yi ba, Ammi tace

"Ina son sanin inda 'ya ta take, tana raye ko akasin hakan, don Allah ina Habeeba? Barin ta kuka yi ta tafi ba tare data fad'a muku inda 'ya ta take ba?" Don dake tsaye ya k'araso yana kallan Ammi yace a nutse

"Ammi, Abba.. Wannan ce er ku" ya fad'a yana kallan Azrah, kowa dake cikin d'akin seda ya d'aga kae ya kalli wacece er Ammin da Abban, ciki kuwa hadda Azrah, ganin dae basu fahimci abinda yake nufi ba ya sanya shi kamo hannun Azrah, bin hannun Azrah tayi da kallo kamar wata baby fuskar ta d'auke da mamaki, sannan yace

"In dae hasashe na ya zama gaskiya, sannan maganar da Ummi ta fad'a na had'ashi da labarin wannan yarinyar toh tabbas itace d'iyar ku, amma zaku iya amsar hakan ta hanyar gwajin k'wayoyin halittar ku.." Tunda ya fara magana take kallan sa babu ko k'iftawa, Abba ya saka hannun sa ya goge k'wallar dake a idanun sa yace

"Tabbas kuwa Adnan wannan ko ba' ayi gwaji ba 'yata ce, tabbas 'yata ce naji hakan a jikina sannan ga hoton fuska ta nan a fuskar ta, Abba ya fad'a yana rik'o hannun Azrah da Don ya kama d'azu, Ammi kuwa suman zaune tayi, shin mafarki take yi ko kuwa dae me? Me yake shirin faruwa anan?, Azrah dae Azrah itace erta? Toh ta yaya hakan ta kasance? Seta sake rik'o hannun Azrah sosae tana kallan ta wasu hawaye masu d'umi suna zubowa akan kuncin ta tace

"Azrah!! Kece?" A hankali Azrah ta shiga zame hannayen ta dake cikin na Abba da kuma na Ammi, sannan ta fara matsawa baya tana girgiza kae, hawaye kamar ruwa na ambaliya a fuskar ta, gaba ki d'aya en d'akin binta suka yi da kallo ciki hadda Mami dake mak'ure a gefe kamar munafuka, Abba yace

"Zo nan, mu ne iyayen ki kinji, wannan ce mahaefiyar ki" ya k'arasa fad'a yana nuna Ammi, Wani murmushi Azrah ta saki na yak'e wanda akace yafi kuka ciwo, kamar k'adangaruwa haka ta cigaba da girgiza kan ta kafin tace cikin kuka

"A'ah Ammi, kada kiyi k'ok'arin chanja soyayyar dake tsakani na dake zuwa k'iyayya, kada ki saka k'afa kiyi fatali da wannan soyayyar da nake miki Ammi, saboda nasan iyaye na ba zasu ta6a zama ku ba, nawa iyayen akwae su da son zuciya, son kansu kuma duk k'addarar data same ni sun kasance sune sanadi, ni iyaye na sune Sanadin kaddarata, kuma na tsane su kamar yadda na ta6a fad'a miki, toh ta yaya ma zaku kasance wad'annan mutanen?, Ammi ki bari, baba kaema ka bar fad'in haka Don Allah.. " ta k'arasa fad'a sanda taje k'arshen bangon d'akin, Mamaki gami da tu'ajjabi haka Meemarh da Meemee ke kallan Abba Ammi da kuma Azrah, suna jin kamar suna yin wani yare ne wanda basa ji, girgiza kae Ammi tayi tana tuna kalmomin tsana da Azrah ta ta6a furta mata akan iyayen ta, yau ma gashi ta maemaeta, hakan na nufin abinda ta fad'a kenan?, lallae itama ta yadda ko babu gwaji Azrah erta ce, ba tun yanzu ba take jin k'aunar yarinyar a gaba d'aya jikin ta, dan dae lokacin ta manta tana da 'ya ne da babu abinda ze hana ta fahimtar Azrah erta ce, seta mik'e tsaye a hankali ta fara takawa zuwa inda Azrah take, Abba ya kalle ta yace

"Yi a hankali dae" jinjina kae kawae tayi kana tace tana mik'awa Azrah hannu

"Zo nan Azrah mune iyayen ki, zo kinji.." ta fad'a tana cigaba da tafiya

"Kada ki matso kusa dani, kada ki k'ara kusantowa gare ni, ashe dama ina tare ne dake bansani ba, ina tare ne da matar data kasance SANADIN KADDARATA!? na saki jiki da matar da bata k'aunar kasancewa ta a cikin duniya? Matar data tsuguna ta haefe ni kuma ta jefar dani a ranar saboda rashin k'auna ta? ina raye ko bana raye wannan duk ba damuwar ku bace, ina hannu me kyau ko ina hannu mara kyau shima duk ba damuwar ku bace, kuna can cikin farin ciki abin ku tunda kun rabu da k'arfen k'afa, sannan kuka cigaba da rayuwar ku ba tare da kuna tunawa da abinda kuka aekata ba, kun manta Allahn daya halicce ni yana so na? Toh gashi na rayu, na rayu ba tare da ko sisin ku ba, na rayu ba tare da kulawar ku ba, kamar yadda kuka nuna bakwa sona nima bana son ku bana son ku har abada... " Azrah ta fad'a tana fashewa da wani matsananincin kuka me tsuma zuciyar me sauraro, saboda tsananin 6acin rae gaba d'aya idanun ta sun rufe..........



08124818273



✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION41_42*




___Fashewa da kuka Ammi tayi tana jin tausayin Azrah na sake lullu6e ta, haka zalika a lokaci guda tana sake kad'aeta Allah me kowa komae, me yin al'amari a duk sanda yaso, lallae wannan ba k'aramin ikon Allah bane, ta sake kallan Azrah dake zube a k'asa kanta akan gwuiwoyin ta tana rera wani marayan kuka, da wane ido zata kalle ta ta sanar da ita ita kanta bata san da faruwar hakan ba? Tana k'aunar ta tun kafin tazo duniya? Tana k'aunar ta fiye da kowa a duniyar nan, toh ta yaya ma zata haefe ta da kanta kuma sannan ta k'i ta? 'ya d'aya tilo da Allah ya bata ita a duniyar nan? Ashe ashe bata sani ba tana tare da d'iyar ta, d'iyar ta ta cikin ta, Dad ya kalli Abba dake girgiza kae yana kallan Azrah yace

"Mu d'an bata lokaci kad'an, zuwa anjima se muyi magana" Abba ya kalli Dad yace

"Ka bari mu fara mata bayani, muyi mata bayanin yadda muke k'aunar ta tukun na" Dad ya girgiza kae yace

"Ba yanzu ba, bata ko 20mins ne kafin nan ta huce zata iya saurarar ku" Abba ya kalli Ammi da har lokacin kuka take yi tana kallan Azrah wadda itama kukan take yi, sannan yace k'asa k'asa

"Zo mu fita" d'aga ido tayi ta kalli Abba jin abinda yace, ya jinjina mata kae kawae, seta mik'e bayan ta sake kallan Azrah ta fice daga d'akin hawayen idanun ta na k'aruwa, duka ragowar en d'akin suma waje suka yi kowa da abinda yake sak'awa a ransa, yayin da wasu daga ciki suka k'agu suji aenahi kuma kan zancen.... A hankali ya fara takawa zuwa inda take zaune, ya tsaya yana kallan ta yadda take kukan bilhak'k'i, seya lumshe idanun sa kafin ya k'arasa dab da ita ya sanya hannu ya fara k'ok'arin d'ago ta, fusge jikin ta tayi da sauri, ya share ta ya cigaba da abinda yake yi har ya k'arasa mik'ar da ita tsaye yana kallan ta, kawae seta sake fashewa da wani sabon kukan, ya lumshe idanun sa kafin a hankali ya jata zuwa cikin jikin sa, k'ok'arin mik'ewa ta fara yi amma be bata damar hakan ba sema d'auko d'ayan hannun sa da yayi ya d'ora akan ta dake kwance a k'irjin sa, cigaba tayi da kukan, a hankali ya fara tapping kan nata yana jin yadda numfashin ta ke sauka a kusa da wuyan sa, ya sake lumshe idanu kafin yace a hankali dae_dae saetin kunnen ta kamar me rad'a

"Ya isa haka" ba tayi shiru ba amma dae ta hak'ura da k'ok'arin tashin da take yi, ta cigaba da kukan, seda tayi me isar ta sannan tayi shiru ta koma sauke ajiyar zuciya har lokacin tana jikin sa, da sauri ya d'ago ta jin hakan na saukar masa da kasala, seda ya d'ago ta sannan ya cigaba da kallan ta, hannun ta ya kamo ya sanya shi cikin nasa, ya d'an saci kallan hannun jin yadda laushin sa har yana neman yayi yawa, kamar hannun jariri ga wani taushi, seya d'auke kae daga hannun nata yana kallan ta da lumsassun idanun sa yace cikin rarrashi kamar ba Don Adnan ba

"Kalle ni.." abinda take ganin ba zata iya ba kenan, Dan haka kawae tayi shiru tana jan hannun ta dake cikin nasa, ya sake rik'ewa gam kana yace

"Ki san irin kalmomin da zaki dinga fad'awa iyayen ki, komae lalacewar su iyayen ki ne, ballantana ma bana tunanin abinda kike zargi shine gaskiya, kawae ki basu lokaci kuyi magana, ba wae kalmomin kare kae zasu fad'a miki ba, a'ah zaki ji gaskiyar labari ne.." maganar tasa ta sanya ta tilas ta d'aga kae tana so ta kalle shi amma ta kaasa, mamaki take dama haka yake? Ko kuwa dae?, bata k'arasa tunanin ba ta jiyo muryar sa yana fad'in

"Let's go.." ya fad'a fuskar sa a d'an had'e, girgiza kae tayi kana tace ba tare data kalle shi ba

"A'ah ni k'auyen mu zan koma, ka bani takadda ta bana son ganin su" fuskar sa ya sake had'ewa sannan yace bayan ya saki hannun ta

"Bakya jin magana koh?, wuce muje nace" Seta d'an yi gaba kad'an tana share k'wallar idanun ta, ya d'an ja k'aramin tsaki a ransa yana ayyana wace irin yarinya ce wannan? se kuma ya koma gaban ta yace a hankali

"Koma inda kike, na dae fad'a miki kisan maganar da zaki dinga fad'a" daga haka yayi gaba, kawae seta samu kanta da binsa da kallo har lokacin mamaki be sake ta ba, yau dae d'aya yayi mata magana cikin kwantar da kae da lallami, seta koma ta sake zama can inda take a zaune d'azun, ta sake kifa kanta akan gwuiwoyin ta.. Wajen mintuna 2 aka turo k'ofar d'akin, bata d'aga kae ba har mutanen suka gama shigowa, Ammi dae har lokacin ta kasa dena kuka, Abba ne ya fara magana cikin rarrashi

"Ki d'ago ki saurare mu, ki tsaya kiji uzurin mu, da kinsan halin dana ke ciki na tsawon shekaru 17 akan rashin ki dana mahaefiyar ki da sekin tausaya min" daga inda take zaune ta d'an d'aga kan ta tana mamakin jin furucin Abban, dae_dae nan Mami da Twins suka shigo d'akin rik'e da Ummi da hawaye keta sintiri akan kuncin ta, se dae bata umm bata umm umm, se a lokacin Don ya lura da Mami, bece komae ba kuma be nuna wata alamar ba ya d'auke kae fuskar sa ba annuri kamar ko yaushe, Meemarh ce ta kalli Abba tace tana share k'wallar idanun ta

"Abba Ummi ce tace a kawo ta wajen ka zaku yi magana" Abba be kalle ta ba dan shi kad'ae yasan abinda yake ji akan ta tun kafin ta fad'a masa maganar data kawo ta, Dad ya mik'e yana kallan Abokin sa yace

"Bari mu baku waje" Abba yace

"A'ah kuyi zaman ku, kome zata fad'a ta fad'e shi a gaban kowa, nima yanzu inaso na bawa 'ya ta labarin abinda ya rabamu tsawon shekaru ne.."






*TUSHEN LABARI*


... Alhaji Kabeer Tajuddeen da Alhaji Abbakar Abdallah sun kasance abokae ne tun na k'uruciya, sun tashi ne tare har zuwa girman su, haka kuma Allah ya azurtasu ne kusan lokaci guda duk da dama dae can da arzik'in su, auren su na farko sun yishi ne da k'awaye 2 wato Mami da Ummi, suma k'awaye ne tun na yarinya ta, kuma da Allah ya had'asu duk se suka sasanta kan su har ta kae ga auren su, suka zauna nan cikin garin kano, tafi tafi dae Allah yana k'ara bud'awa kowanne daga cikin su se dae har bayan fiye da shekaru 2 babu wadda ta ta6a ko 6atan wata a cikin su, hakan ba damuwar kowanne daga cikin su bane tunda sun san haehuwa ta Allah ce, A cikin shekarun ne kuma Dad yaje Sudan wani aeki

Please Login or Register in order to submit comment