Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

seta d'auki duk wani kud'i da tazo dashi ta bawa Hajja Kaltum d'in amma se cewa tayi tana ta6e baki

"Na tsani mammak'o wallahi mtsww" ta fad'a tana ficewa daga d'akin, binta da kallo Mami tayi tana jin wasu k'walla na tarar mata, wae yau itace Hajja Kaltum kewa haka, matar dake bin ta sau da k'afa lokacin da take gidan Alhaji Kabeer, wato tunda yanzu ta bar gidan da ita da banza duk d'aya kenan? Ke duniya...





... Rufe Hadith d'in da kullum Ammi ke koyawa Azrah tayi ta ajje shi kan side drawer sannan ta kalli Azrah tace

"Zuwa goben ki iya shi" Murmushi tayi kana tace

"Toh Ammi a k'ara wani se in had'a duka"

"A'ah hakan ma ya isa, abinda nake so dake yanzu ki samu ki d'auko hisnul muslim kiyi isthikara akan al'amarin nan, idan Adnan alkhaeri ne a gare ki Allah ya tabbatar daku a tare, idan kuma ba alkhaeri bane Allah ya chanja miki da mafi alkhaerin sa kinji koh?" gyad'a kae Azrah tayi, Ammi tace

"Ki bud'e baki ki amsa min"

"Toh Ammi..amma fa baya sona.." Kallan ta Ammi take sosae cike da mamakin yarintar d'iyar ta ta, ace duk abinda Adnan keyi bata fahimci soyayya bace? Duk abinda yake yi bata fahimci kishin ya yake yi ba? Se ta d'an yi murmushi kana tace

"Ae ke dae za6in Allah zaki nema kawae" ta jinjina kae tana kallan Ammin

"Jeki duba en uwan ki, kafin na shigo nan na lek'a su.." Mik'ewa Azrah tayi tabi bayan Ammi suka fita tare, Ammi tayi hanyar d'akin mijin ta yayin da Azrah ta tura k'ofar d'akin da Twins d'in ke ciki, suna zaune dukkan su a kan gado kowacce tayi shiru, har yanzu sun kasa sakin jikin su, ji suke yi tamkar sune suka yiwa Ammi da Azrah laefi, ita kuwa Azrah da zasu gane su dena wahalar da kansu, akan meye zata d'ora musu laefin da bana su ba? Duk da dae uwar su ce ta musu wani abun amma ae su basu da laefin komae, ta k'arasa ta zauna gefen gadon tana kallan su tace

"Kunci abincin?" Meemee ce ta d'an wanzar da murmushi a fuskar ta tace

"Ehh munci tun d'azun" itama Azrahn murmushi tayi kana ta mik'e tace a hankali

"Bari naje seda safe" se a lokacin Meemarh tace


"Allah ya tashe mu lafiya" Azrah ta bita da kallo sannan ta fice daga d'akin..




... Wajen k'arfe 1 ne na dare lokacin da kowa ke buk'atar hutu amma banda shi, dan kam tun d'azu ya kaasa rintsawa, shi kam wannan al'amari har tsoro yake bashi, wae akan mace ya kaasa rintsawa, runtse idanun sa yayi yana hango kyakykyawar fuskar ta, dara daran idanun ta, dogon siririn hancin ta, uwa uba kuma d'an k'aramin jajawur d'in la66an ta masu d'aukar hankali, seya cije lips d'in sa na k'asa kana ya bud'e idanun sa kafin ya tashi zaune ya hargitsa sumar kansa yace cikin er d'aga murya

"Oh god.." Baccin da beyi ba kenan, da sassafe kuwa ya shirya ya d'auki wayar sa ya jefa cikin aljihun bayan wandon sa sannan ya fita compound ya tada motar sa ya bar gidan... Yana gama parking d'in motar sa a cikin compound d'in ya fito ya k'araso zuwa inda Ammi ke tsaye ta fito raka Abba daze fita, ta kalle shi yadda taga lumsassun idanun sa sun sake shanyewa kamar me jin bacci, yace a nutse

"Barka da safiya!"

"Barka dae Son, ka tashi lafiya?" Abba ya fad'a shima yana karantar yanayin sa

"Alhamdulillah" Ammi ce ta kalle shi tace

"Wuce ciki, gani nan zuwa" bece komae ba ya wuce cikin parlourn, Abba ya bishi da kallo kafin ya dawo da duban sa kan Ammi yace

"Wato kun kasa gane abinda yaron nan yake nufi koh? Toh kubi dae a hankali kada azo ayi abin kunya dan haka tun wuri gwara ku tattara ku bashi matar sa kafin ya gaji ya furta abinda yake nufi da bakin sa" Murmushi Ammi tayi wani irin farin ciki mara misaltuwa na mamaye ta tace

"In Sha Allah, dama Ummu ce ta nemi abatta zata kaeta a mata kitso da lalle kafin ta koma gidan nata" Abba yace

"Toh hakan ma yayi" daga haka ya shige motar sa ita kuma ta koma cikin gidan... Shi kam tunda ya shiga d'akin zuba ido kawae yake yi ko zega fitowar ta amma shiru babu ita babu labarin ta, amma fa komae nacin ka k'aryar ka ka gane yanayin da yake ciki, dan kuwa babu abinda ya chanja ko daga yanayin fuskar sa ne, Ammi ta k'araso cikin parlourn ta nemi waje ta zauna tana kallan sa da murmushi tace

"Kazo lafiya?"

"Alhamdulillah" ya fad'a a gajarce, daga haka kowa yayi shiru, yau d'aya yaji yana jin kunyar fad'in abinda yake niyyar fad'a d'in, wanda tuntuni ya gama tsara abinda ze fad'a d'in, amma ya basar kawae sannan ya d'an gyara zaman sa kana ya lumshe idanun sa ya bud'e su a lokaci guda yace ba tare daya kalli inda Ammin take ba......

✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION48*




___Ammi ta cigaba da kallan sa tana jiran taji abinda ze fad'a d'in, se can yace kamar wanda a kawa dole

"Ammi..zuwa nayi na d'auke ta.." ya fad'a cikin basarwa, har ga Allah duk kunya ce ta kama Ammi, wannan wane irin abun kunya suka aekata, gashi seda ya gaji da kansa yace a bashi matar sa, wannan abu har ina?, seda Ammi ta nisa kad'an sannan tace

"Ayyah kayi hak'uri yalla6ae, tana gidan su Zarah amma In Sha Allah ba za'a wuce gobe ba zata koma gidan ta.." ya lumshe idanun sa yana tunanin kenan yau ma baze ganta ba? Mik'ewa kawae yayi yace yana tafiya

"Na koma"

"Ka tsaya in kawo maka abinci kayi break mana" ya girgiza kae yace

"Noo Ammi zan biya restaurant" ya fad'a ba dan yana nufin abinda ya fad'a d'in ba, Ammi tace

"Toh Allah ya tsare" sauke ajiyar zuciya Ammi tayi kana ta dawo da duban ta kan wayar ta dake ajje kan kujera ta d'auka ta danno number Ummu, seda suka sake gaesawa sannan Ammi tace

"Don Allah Ummu kuyi hak'uri ku maeda yarinyar nan gidan ta, nikam rashin kunyar nan ta isheni, yau da kansa ya cire kunyar yace yazo d'aukar ta" Murmushi Ummu tayi a ranta tana hamdala, se kuma tace a fili

"Toh shikenan Ammi, amma don Allah a bani ko 3 days ne, inaso na gyara d'iyar tawa kafin a maeda masa ita.." Ammi dae ba tace komae ba ta katse kiran, murmushi Ummu tayi kana ta ajje wayar... Da yamma Ummu ta shiga d'akin Zarah, Azrah da Zarahn suna zaune Azrah na taya Zarah ninkin kayan ta data hautsino su daga cikin wardrobe, ta kalli Azrah tace

"Tashi ki shirya zamu je unguwa" kallan Ummu Azrah tayi kafin ta mik'e tana kallan Zarah, Zarah ta maraeraece fuska tace

"Ummu don Allah zan biku, kar kice a'ah don Allah" girgiza kae Ummu tayi tana murmushi se kuma tace

"Toh kuyi maza ku shirya, ina jiran ku kada fa ku tsaeda ni"

"Yawwah Ummun mu" Zarah ta fad'a tana dariya, Ummu ta fita yayin da su kuma kowaccen su ta janyo hijab suka saka sannan suka fito parlourn, tare suka fita compound d'in, dae_dae lokacin da Abunnas ya shigo gidan, ya kalle su su duka yace

"A'ah Ummu ina zaku je?"

"Inda ka aeke mu" Ummu ta fad'a tana jefa masa harara, Zarah ta k'yalk'yale da dariya, ya murgud'a mata baki sannan yace

"Bafa haka nake nufi ba Ummu, naga zaku bar gidan ba kowa ne" Ummu tace

"Ehh ba dad'ewa zamu yi ba, ka zauna kawae" yace

"Toh se kun dawo, Allah ya tsare" suka amsa da "Ameen" dukan su, yana dab da shirin shiga parlourn ya juyo kamar wanda yayi mantuwa yace

"Aww, Azrah na manta ban fad'a miki ba wallahi har yanzu yasayyadi be bar zancen ki ba" Ummu ta juya gefe da gefen ta ko zata samu abinda zata jefa masa, ganin haka ya sanya ya shige d'akin da sauri, Azrah tayi murmushi kawae, daga haka suka shige mota sabon ma'aekacin Abbu ya d'auke su suka bar gidan.... A cikin wata k'atuwar plaza yayi parking, dukkan su suka sauka, Zarah da Azrah kuwa bin wajen su kayi da kallo suna mamakin abinda ya kawo su nan d'in, amma Ummu bata basu damar tambaya ba tayi gaba, duk se suka bita kawae tana gaba suna bin ta a baya, a haka suka hau bene, basu suka tsaya ba seda suka je hawa na k'arshe sannan Ummu ta shiga wani waje dake kamar parlour, dukka suka rufa mata baya zuwa cikin wajen da tun daga k'ofa wani shahararren k'amshi yake dokar musu hanci, wata mata na ganin Ummu tace

"Barka da zuwa Hajiya" murmushi Ummu tayi ta nemi waje ta zauna, seda ta zauna d'in sannan suma suka zauna kamar wasu yaran goye, Ummu tace

"Yawwah sannun ki dae"

"Ina wuni?" Azrah da Zarah suka had'a baki wajen fad'ar hakan, matar ta kalle su tace da murmushi kan fuskar ta

"Lafiya k'alau.. kae masha Allah wad'annan yaran ki ne?" ta k'arasa fad'a tana kallan Ummu, murmushi Ummu tayi sannan tace

"Ehh.."

"Gasu kuwa kyawawa tubarkallah" Zarah da Azrah suka had'a ido, su kam sun k'agu suji abinda ya kawo su nan d'in, duk da dae sun fahimci wajen menene, dan ko ba'a fad'a maka ba k'amshin dake tashi ya isa ya fad'a maka wajen gyaran jiki ne

"Wacece za'awa gyaran a cikin su?" dukkan su suka d'ago suka kalle ta, Ummu ta nuna Azrah

"Gata nan, yanzu za'a fara koh?" Matar tayi murmushi sannan ta kalli Azrah tace

"Toh tashi muje a fara.." kallan Ummu Azrah tayi sannan ta kalli matar, so take ta tambayi Ummu toh gyaran me za'a mata? In dae ba wani abun suke nufi ba toh meyasa ba za'ayi musu tare da Zarah ba? Mik'ewa tayi kamar zata saka ihu tabi bayan matar zuwa wani d'aki da yafi wanda suke zaune a ciki haske sosae, suna shiga matar ta kalle ta da murmushi tace

"Ki cire Hijab d'in zamu fara.." kallan ta ta cigaba dayi, ita fa bata san cire hijab cikin mutanen da bata saba dasu ba, wae ma ita gyaran jikin mene za'a mata haka ne? Seda matar ta sake maemaeta mata maganar sannan ta zame hijab d'in a hankali ta ajje shi gefe, matar ta k'arasa ta ciro wani sabon milk d'in towel ta mik'a mata tace

"Ga toilet nan kije ki sako shi" lokacin kuwa hawayen da take ta rik'ewa seda suka sakko zuwa kuncin ta, ta kar6a ta wuce toilet d'in tana matse k'walla, seda ta kwashe wajen minti 5 sannan ta fito tana sissinne kae har lokacin k'walla fall cikin idanun ta sannan ta k'arasa ta zauna inda matar ke nuna mata, wajen mintuna 30 matar ta d'auka tana gyarawa Azrah jiki kafin ta had'a wani turare me k'amshin gaske ta turara jikin ta sannan ta had'a mata wani tayi tsuguno a kae, sannan ta mata na jiki, ranar dae jikin ta yaga abubuwa kala kala se kace wadda za'a chanjawa fata, ita dae Azrah binta kawae take yi, ta rasa gane me suke nufi da ita, dan ita a shashancin ta ma ta manta tana da wani aure, basu suka bar wajen ba se dab da magribh.. Washe_gari ma haka suka sake komawa wajen, yanzu kam Azrah seda ta kasa shiru tace wa Zarah

"Wae gyaran jikin me muke zuwa ne haka?" Zarah tace

"Oho, ki tambayi Ummun mana" ta tura baki kawae bata sake cewa komae ba, haka ranar ma suka kwashi awanni a wajen har gyaran yau ma yafi na jiya, dan yau seda aka k'ara wani abun akan na jiya, sannan suka koma gida, farar fatar Azrah ta sake haske kamar ka ta6a jini ya fito har wani shining take, ga wani irin laushi da taushi data k'ara, k'amshi kuwa ba'a magana dan ko zama tayi a waje ta tashi se kaji k'amshin da take, ko turare ma Ummu hana ta sakawa tayi, sannan ta hana ta fitowa parlour, daga d'aki se d'aki, ita kanta idan tana zaune seta samu kanta da dinga kallan jikin ta, gaba d'aya ta chanja kamar ba ita ba...






... A 6angaren Dad kuwa sosae ya saka malamae sunawa Adnan addu'a da saukar qur'an, shima kuma kansa da Yakumbo ba'a barsu a baya ba wajen yi masa addu'ar ba dare ba rana... Da safiya ne bayan Asuba, Abba ya fito daga wanka, Ammi na zaune kan gado tana gyara kayan data fito dasu daga cikin wardrobe, wayar Abba ce tayi k'ara, ya kalli wayar sa mamakin me kiran nasa a irin wannan lokaci dan ko gari be gama yin haske ba, Ammi ce ta mik'a masa wayar, Abba ya kalli me kiran, da sauri ya d'aga yana karawa a kunnen sa, kukan da yaji daga cikin wayar shi ya sanya jikin sa yayi sanyi, yace cikin kwantar da murya

"Kiyi shiru Meemee, meya faru?"

"Abba Ummi ta rasu, yanzun nan ta rasu Abba, tana ta cewa a kira mata ku ta nemi gafarar ku, Abba Ummi ta rasu" ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka

"Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" shine abinda Abba ya shiga maemaetawa, Ammi ta dakata tana kallan sa dae_dae lokacin daya ajiye wayar se dae ya kasa cewa komae, Abba yace

"Habeeba ta rasu" Dakatawa Ammi tayi da abinda take yi tana jin yadda ilahirin jikin ta yayi wani mugun sanyi, tace a hankali

"Allah yaji k'an rae.."

"Fatima!" Abba ya fad'a yana kallan Ammi data cigaba da abinda take yi, seta dakata amma har lokacin bata juyo ba yace

"Taso a kira ku ta nemi gafarar ku, amma Allah be nufa ba, toh zan rok'ar mata afuwa a madadin ta ki yafe mata" shiru Ammi tayi se kuma can tace

"Allah ya yafe mana baki d'aya" Abba yace

"Ameen Ameen" daga haka ya shirya dan tafiya asibitin, seda ya gama shiryawa sannan ya kalli Ammi yace

"Bansan yadda zanyi na samu Azrah a waya ba, ki samu ki sanar da ita zancen rasuwar nan, sannan itama ta yafewa Habeeba don Allah" Ammi tace

"Allah ya yafe mata, amma mu kam mun yafe mata" Abba ya amsa da "Ameen" kana ya fice daga gidan... Kae tsaye asibitin ya nufa lokacin Twins na zaune k'ofar d'akin suna kuka sosae, ya k'arasa cike da tausayin su, suna ganin sa suka mik'e da gudu suka rungume Abba, Abba ya rik'e su wani tausayin su na ratsa shi, Meemarh tafi k'ulafucin Ummin dan haka tafi shiga damuwa, kuka take tamkar ranta ze fita tun d'azu take sumbatu, Abba yace

"Ya isa haka, kuyi shiru, Allah ya gafarta mata" da k'yar Abba ya lallashe su suka rage kukan... Daga nan aka d'auki gawar ta zuwa can gidan su aka sallace ta acan sannan aka kaeta gidan ta na gaskiya (Allah yasa mu cika da kyau da imani).




...
Sameer ya kalli Don da yake wa magana wanda da alama sauraron sa kawae yake yi ba tare da yana fahimtar abinda yake cewa ba d'in, dan haka kawae yayi shiru, se can da Don d'in ya lura yayi shiru sannan yace

"Umhum.."

"A'ah ka gama tunanin tukunna sena k'arasa maka" d'an k'aramin tsaki Don yaja bece komae ba, Sameer yace

"Man.. Wae me yake damun ka ne kwanan nan?" ya kalli Sameer sannan yace yana yamutsa fuska

"Wani abun ka gani?" Sameer yayi murmushi sannan yace

"Ni kuwa naga abubuwa kala kala, amma ko dae ka fad'a...." ya d'an yi shiru yana sake sakin murmushi, Don ya kalle shi fuskar sa a d'inke

"What..?"

"Soyayya mana" Don ya cigaba da kallan Sameer kafin ya ta6e baki gami da d'aga kafad'a, Sameer yace

"Ah toh duk wani alamu sun nuna hakan, kaaga kawae ka bada kae bori ya hau, wace me sa'ar ce wannan?" murmushin gefen baki Don yayi kafin ya kae hannun sa ya shafa kwantaccen sajen sa yace a nutse

"Mata ta mana" wata dariya Sameer ya saki da k'arfi hadda saukowa daga kan kujerar da yake, Don yayi kicin kicin da fuskar sa, seda Sameer yayi me isar sa sannan ya koma ya zauna, dama shi kam ya san za'a rina, ba tun yanzu ba ya fahimci abokin nasa ya fad'a soyayya kawae dae shi kansa Don d'in be fahimci hakan ba se yanzu, yace har lokacin wata dariyar na cinsa

"Matar ka dae? Yanzu kae baka ji kunya ba Friend?"

"Kunyar mene malam?" Sameer yace

"A'ah babu komae, amma fa dole seka tashi tsaye ina fad'a maka.." Don na shirin magana wayar sa tayi k'ara, tare suka kae duban su kan wayar, Sameer ya d'auke kae yana ta6e baki, yayin da Don ya d'auki wayar ya kaara a kunnen sa, daga can 6angaren Irfan yace

"Don don Allah taemakon nan dae zaka k'ara min"

"Wanne?" Don ya fad'a a gajarce, Irfan yace

"Ka ganni a tasha wallahi bani da kud'in dawowa kano, shine nace bari na maka magana"

"Ohk" kawae Don ya fad'a yana katse wayar, be ajje wayar ba seda ya turawa Irfan kud'i dan dama yana da Account number sa, sannan ya ajje wayar, Sameer bece masa komae ba sema mik'ewa da yayi yace

"Ni na tafi, amma koda yaushe ka dinga tuna Irfan ba mutumin kirki bane" be jira amsar Don d'in ba ya wuce, binsa da kallo Don yayi kafin ya ta6e baki.....


.... A k'ofar gidan ya had'u da Abunnas dake shirin shiga gidan, dama ya tsaya da driving d'in amma motar a kunne take, kiran sa yayi, Abunnas ya k'araso ya rusuna yace

"Yah Adnan barka da wannan lokaci"

"Barka dae..bud'e min gate d'in zan shigar da mota ta"

"Toh" Abunnas yace yana mik'ewa yaje ya bud'e masa gate d'in, shi kuma ya tura hancin motar sa cikin gidan ya kashe ta, Abunnas yace

"Yah Adnan ka shiga parlourn" bece komae ba ya sakko daga motar, tare suka wuce zuwa cikin parlourn ya nemi kan kujera ya zauna, Abunnas yace

"Bari na kira maka Ummun" ya fad'a yana shirin fita, Don yace kamar wanda akama dole

"Ina Az..rah.." ya fad'a kamar me koyon yadda ake magana, shi kansa seda yaji wani banbarakwae daya kira sunan, dan ze iya cewa wannan ne karon farko daya ta6a fad'ar sunan ta, Abunnas yace yana nuna wani d'aki

"Tana can d'akin.." bece komae ba se bin d'akin da yayi da kallo, Abunnas yace

"Bari na dubo Ummun" gyad'a masa kae kawae yayi yana cigaba da kallan k'ofar d'akin, kamar wanda ake ja kawae ya mik'e a hankali yana tafiya zuwa d'akin ya sanya hannun sa ya d'ora ze bud'e k'ofar..... Fitowa tayi daga toilet d'in d'aure da madaedaecin towel, kan ta babu d'an kwali, kwantacciyar bak'ar sumar kan ta a jik'e jagab da ruwa, ta riga tasan babu wanda ke shigowa d'akin se Ummu da Zarah, dan haka taja stool d'in dake gaban mirror ta zauna ta janyo sabbin maya mayan da take shafawa, a hankali ta fara mulke fatar ta me santsi da man, tana kallan kanta a mudubi dan ita kanta tasan ta chanja ba k'arami ba, dae_dae lokacin daya turo k'ofar d'akin, bata ta6a kawowa ranta shi ne ba, tafi tunanin Zarah ce, dan haka ta juyo tana shirin ganin Zarah se taga abinda bata ta6a tsammani ba, mik'ewa tayi cikin matuk'ar tsoro k'irjin ta na bugawa ta juya da gudu zata koma cikin toilet, cikin zafin nama ya sanya hannun sa ya rik'o hannun ta da taushin sa ya ratsa hannun sa, ya tsayar da ita ta wani 6angaren, idanun ta da suka yi rau rau ta saka ta kalle shi, shi kam gaba d'aya yadda ya gantan yana so ya hautsina masa lissafi, dan haka ya lumshe idanun sa, yana shak'ar wani sassanyan k'amshi dake tashi a jikin ta wanda saboda tasirin sa seda ya danne nasa k'amshin, a hankali ta fara k'ok'arin komawa baya hawaye na zuba akan kuncin ta, seya bud'e idanun sa sannan shima ya fara takawa, duk wani taku da zatayi na komawa baya shi kuma seya taka yayi gaba, bata hak'ura ba har seda taji ta a jikin bango sannan ta gane tayi shirme, dan shi kam hakan ba k'aramin dama ya bashi ba, ya d'ora hannun sa a gefen ta yana sake kallan ta yadda ta k'ara wani shahararren kyau, ga k'amshin dake sake neman hautsina shi, ganin yadda ya sake lumshe idanun ne ya sanya ta yin amfani da wannan damar tace cikin kuka

"Don Allah ka fita, ni nace maka ka sake ni.." kafin ta kaega k'arasawa ya katse ta da fad'in

"Akan meye zan sake ki?" ya fad'a cikin k'arfin hali, hakan ya sake bata k'arfin gwuiwa tace

"Saboda baka sona nima kuma bana son ka.."

"Ni nace miki bana son ki?" d'aga ido tayi ta kalle shi cikin mamakin jin furucin sa, wae ma anya kuwa wannan mutumin shine wancan kuwa? Ko dae an chanja shi ne?

"Ke wallahi ma daga yau kika sake min zancen saki zaki ga abinda zan miki, ba za'a sake kin ba idan kuma kina da k'arfi ki k'wata" ya d'an dakata yana sake lumshe idanu sannan ya bud'e yace

"Ki fad'a musu kina son komawa gidan ki, idan ba haka zan nuna miki waye ni" ya fad'a yana k'ara kusancin dake tsakanin su, ita kam ta kaasa cewa komae dan gaba d'aya tsoro ya gama cika ta yadda taga yana sake matsowa dab da ita kamar ze shige cikin jikin ta, dan haka cikin k'arfin hali kuma hawaye na sake zuba akan kuncin ta tace tana girgiza kae

"Ni ka cika ni" shi kuwa ya kaasa rik'e kansa wannan k'amshin dake tashi daga jikin ta na neman rikita masa lissafi ga kuma laushin fatar ta da yake ji saboda hannun ta dake hannun sa, wanda tun d'azu take kici-kicin k'wacewa amma yak'i bata damar hakan, dan haka be nuna ma yaji abinda tace ba, ya sake ware lumsassun idanun sa da suka kad'a suka yi ja ya watsa su a kanta, seya sake sauke idanun nasa kan jajayen la66an ta dake motsi saboda kukan da take yi, jikin sa duka rawa yake yi, ita kuwa kuka take yi da taga kamar tunanin wani abun yake yi tayi amfani da wannan damar zata zame ta k'asa yayi saurin rik'o ta, da sauri ya saka fuskar ta cikin tafin hannun sa sanda take yunk'urin k'wacewa, saboda rik'on daya mata bana wasa bane dan haka bema lura da k'wacewar da take yi ba, ya sake tsurawa bakin nata idanu kamar wani maye, sannan a hankali ya kae bakin sa kan k'aramin cute lips d'in ta ya sanya shi cikin nasa, zaro ido tayi tana jin yadda ilahirin jikin ta ya d'auki rawa, shi kam a hankali ya shiga bata wani lafiyayyen kiss, iya k'arfin ta ta saka zata ture shi, se taji towel d'in jikin ta na neman kwancewa, ita se a lokacin ma ta tuna mene a jikin ta, kawae seta sake fashewa da kuka, ita kam yau tata ta k'are, ta saka hannu ta dafe towel d'in jikin ta tana cigaba da mutsu mutsu, shi kam ko a jikin sa ya cigaba da kissing nata idanun sa a lumshe yana sake shak'ar daddad'an k'amshin dake tashi daga jikin ta, a hankali ya kae hannun sa ya rik'o nata hannun ya fara jan ta, dae_dae lokacin da Zarah ta turo k'ofar d'akin, se a lokacin ya dawo hayyacin sa ya sake ta da sauri kana ya runtse idanun sa ya bud'e su sannan ya fara takawa da k'afafun sa da suka yi laushi kamar wad'anda ba zasu d'auke shi ba, Zarah na shirin komawa bayan mummunan ganin da tayi, ya k'araso ze fita daga d'akin, yana shirin fita Zarah tace cikin kunya

"Barka da wannan lokaci Yah Adnan" ko kallan ta beyi ba yayi ficewar sa, ta bishi da kallo tana k'unshe dariyar ta, seda ta shiga d'akin ta kalli Azrah dake durk'ushe gefen gado tana rabzar kuka sannan ta samu damar fashewa da wata dariya hadda rik'e ciki, ta nemi kan gadon ta zauna tana cigaba da dariya kamar cikin ta ze k'ulle, Azrah ta sake k'uluwa ga haushin wancan mutumin, ga haushin abinda ya mata ya sake cika ta, kawae seta sake fashewa da kuka tana saka hannun ta kan lips d'in ta tana gogewa da k'arfi, ita kuwa Zarah me zatayi idan ba dariya ba, ta cigaba da dariyar ta, d'aukar pillown dake gefen ta tayi ta jefawa Zarah, Zarah ta rik'e tana dariya tace

"Sorry Sorry, wallahi ni dae dasu Ummu zasu ji shawara ta da sun bawa Yah Adnan matar sa, idan ba

Please Login or Register in order to submit comment